Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsoka, akasa maki kashi, kika girma acikina, ki hanani bacci, kocin abinci, kika hanani sukuni, sannan nasha wahalar haihuwarki, seda nadauki tsawon awa 1 ina nakudarki kafin kika buda jikina kika fito.

Nashayar dake daga jinin jikin, suk dare duk rana kina tare dani, bana bacci sekinyi, kimun fitsari da kashi in wanke, har kika girma ina dawainiya dake harzuwa yanzu.

Shin akwai wani umarni dazan baki ki kasa binsa? Kai tashiga girgizawa tana kuka, jin yanda Umminta tasha wahala akanta. Murmushi Zarah tayi ganin yanda jikin Jalila yayi sanyi.

Tace Jalila amatsayina na mahaifiyarki, inaso duk abinda zakiga ya canza agidan nan kada kiyi magana ko kuma kiyi tambaya akanshi.
Daga yanzu tarayyarki da Falak tazo karshe abanason ina ganinku tare, bazata kara zuwa isilamiyya ba, kuma ayau zata bar dakinki, zata koma store itada kaninta dan renonshi yakoma hannunta, kuma daga yau itace sabuwar me yimun wanke wanke da wanki, harma dazuwa kasuwa.

Idan harkika kara yima Dadynku maganar Ameer ko Falak, sena tsine maki, dasauri Jalila tadago kanta tana kuka, tace Ummi dan Allah kada kitsine mun, wlh wuta zanshiga, nayarda zanbi duk abinda kikace, amma kijanye maganar tsinuwa.

Murmushi Zarah tayi, tace bazan janyeba harsenaga kinbi umarnina, ko Alh, yamaki maganar makaranta, nasan naze saka da Falak ba, danshima yamanta da ita, bance kimashi maganarta ba. Kinji abida nafada maki ko? Tace E Ummi, kiyi hakuri dan Allah, tace shikenan nayi tashi ki kiramun Falak.

Fita tayi tana wani irin kuka, tana zuwa takalli Falak gaba daya tausayinta yakamata. Falak tace Jalila lafiyarki kike kuka? Tace bakomai kije Ummi nakira, fita tayi tana murmushi tace yanzu haka laifi kikayi mata ko, bara inje inji mekikai mata, idan har bata mata rai kikayi kisani nima baruwana dake. Wani sabon kuka ne yazoma Jalila, tanajin tausayin Falak sosai.

Tana zuwa tayi sallama tace Ummi hala Jalilace tayi...... Saukar marin datajine yahanata karasa maganar datakeyi, zaki tsugunna ko kuwa sena takaki agurin nan, munafuka me kama da Uwarta. Mamaki ne yakama Falak jin yanda Ummi take zagin Ummanta, zama tayi akasa, taan fitar da kwalla.

Zarah, tace kibude kunnuwanki da kyau kiji abinda zan fada maki, daga yau rayuwar gidan nan, tacanza. Babu ke babu sauran jin dadi, dake da shegen kaninki, inaso kije kicire kayan jikinki daga yau kin koma yar aiki agidan ana, zaki rika wanke wanke, da wankina.

Kuma daga yau zaki koma store da kwana, koda wasa naga kafarki ta taka falon Alh, ranki seya. Baci, ga kaya nan kidauma ki kai store domin shine dakinki, tashi kibani guri.

Fitowa tayi tana kuka, tanufi dakinsun haka tazauna taci kukanta dan Jalila tana dakin Baba mairo, haka falak ta cire kayan jikinta tana tunanin wasiyar da ummanta tayi . Mata, akan kada tabar gidan harse aurenta. Wani irin kuka tashigayi.

Kayan jikinta tacire tadauki wanda Zarah tabata tasaka, kayan sunyi mata yawa, gashi duk sun kode, kuka kawa Falak takeyi, haka Tanufi store ta gyara shi sannan ta aje kayanta. Agurin domin yayi mata kadan.

Jidda ce kwance abisa kirjin. Al,amin yana wasa da gashinta. Al,amin yace baby na akwai wani friend dina bature ne ahi dazu muna chrt, yaga pic dinki akan fp na, yace mun gaskiya yana sonki, kuma zeso kije mashi hutu, a london yake dazama, me kudine na karshe, idan kikayi harka dashi zakizamo Babbr Hajiya.

Ammafa kisani bawai dan banasonki nace zakije ba, kawai abokina ne sosai, kuma yamun mutunci lokacin muna school, koyanzu ma yana temaka mun sosai, idan banida kudi, shine yake bani, nayi mashi alkawrin wata rana zan kawoki wajenshi kiyi mashi koda wata 1 ne.

Ammafa bayanzu ba, bamma saka rana ba, amma kowane lokaci zaki iya tafiya, yakika ce. Murmushi tayi tace da gske zan samo kudi? Yace sosai ma, kinga dakin dawo semuyi aurenmu ko? Tace hakane, insha Allah zamuyi aure dana dawo. Dariya yayi yajawota yarungume.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/30, 2:45 PM] Nabeela lady: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 65.....70

Tun daga wannan rana Falak takoma me aikin Zarah, Alh yamanta da Falak, ko Ameer yadena tambayarshi, tunda Zarah tace mashi ya warke, kuma tana kula dashi, gashi yanzu baya zama sosai,

Kudi sosai Zarah take samu agurinshi, yazama matar dazama mijin, Baba mairo da Jalila kuwa sunzama yan kallo, sosai suke tausayin Falak, aboye Baba mairo take temaka mata,ga aiki ga renon Ameer, kusan kullum seyayi suma tafi 3 saboda baya iya cin komai.

Damma Falak tana yimashi addu,a shiyasa yake dan samun sauki, Baba mairo tace mata idan zata bashi abinci tarika yin addu,a, dahaka yake samu yana cin loma 3 ko 4.

Falak duk ta rame tayi duhu, gashi bata samun bacci sosai, dan store din wasu kwari ne, suke cizonsu, kullum cikin dare Ameer kuka yakeyi, se idan ta goyashi ne kadai yake bacci, ita tahakura da bacci, wani lokacin a kitchen take samu tayi bacci, idan Zarah bata leko ba.

Jalila kanta tayi rama, saboda bakaramar damuwa tashiga ba, datayi nufin temakon Falak seta tuna kalaman Umminta, gashi tana tsoron fushin Umminta, saboda a islamiyya anfada masu muhimmancin Uwa.

Akwai ranar da Alh, yadawo cikin dare yarika jin kuka kamar na yaro, tashi yayi yace Zarah kamar kukan Ameer nakeji, tashi tayi tace wane Ameer kuma, bacin ya dade dayin bacci, kila de makwafta ne,

Alh, yace yaushe harzamu iyajin hayaniyar makwafta agidan nan, muda mukeda da nisa dasu, Zarah tace to karya nakeyi, kasan ai nasaba yinta. Alh, yace Allah yabaki hakuri bahaka nake nufi ba, tace zauna bara inje inlekosu.

Fita tayi tana surutai, store tanufa, Falak tagani se kuka takeyi Ameer kuma yana hannun Baba mairo yanata suma, Zarah tace wai meye haka, dan iskanci zaku fito ku hanamu bacci, Baba mairo tace Haba Hajiya kalla fa kiga yanda yaron nan yake suma, ki kira Alh, mukaishi asibiti, tundazufa beci koma ba.

Zarah tace wlh babu inda za,a kaishi, daukarshi kushiga dakinki kiyi mashi wanka ze farfado, kuma ki kulle dakin banason karajin kukanshi, wlh idan kuka bari Alh, yafito sekinbar gidan nan gobe, wucewa tayi tana zage zage.

Dakin Baba mairo suka wuce, ruwan sanyi Falak tadauko suka samashi da kyar yafarfado, kuka yasaka, haka sukayita lallashinshi Falak tana mashi addu,a se can suka samu yayi bacci. Kwantar dashi Baba mairo tayi,

Kuka Falak tasa tace shikenan Baba mairo shima kila tafiya zeyi yabarni, nashiga 3 ni kuma rayuwata haka zata kare, wlh gara mutuwa ta da rayuwata, rufe mata baki Baba mairo tayi itama tana kuka.

Tace Falak kiyi hakuri, duk tsanani yana tare dasauki, kuma duk wanda yayi hakuri yana tare da nasara, ninasan wata rana komai zewuce, Falak tace Baba mairo kina ganin yanzu ko Dady baya nemammu.

Ina alkwarin daya dauka akan rikemu da amana, gaskiya Dady yazama butulu. Baba mairo tace Falak, akwai abinda nasani wanda baki sani ba, banyi niyar fada maki ba, amma dole infada maki kodan ingoge bakin panting da Zarah tayima Alh, agurinki.

Anan Baba mairo takwashe komai tafada ma Falak, kuka sosai, Falak takeyi, Baba mairo tace ko tan tama banayi wannan maganin da Zarah tasama Alh, maganin mallaka ne, domin rannan inajinsu tana yimashi tsawa, shi kuma duk yarude, yana bata hakuri, bakiga yanzu kamar itace mijin shine matar ba?

Kiyimashi uzuri, wata rana asiri zetonu, Jalila ma tana cikin damuwar halin dakike ciki, babu yanda zatayine, dan Zarah tace idan har tarika shiga harkarki zata tsine maki, shiyasa tace makarantar kwana zata tafi bazata iya cigaba dazma tana ganinki cikin damuwa ba.

Falak tace yanzu Baba mairo haka zamu zauna da Ameer babu magani, tace kiyi hakuri gobe idan zakije kasuwa zanbaki kudi kitsiyo mashi magani, haka Baba mairo tayita lallashin Falak, harta hakura, kuma tayi alkwarin saka Alh, cikin addu,a. Dahaka suka kwanta, rabon datayi bacci medadi kamar na yau harta manta.

Washe gari bayan tagama aikinta, taci abinci tayi wanka, tasaka kodaddar atamfarta, ta amshi kudi agurin Baba mairo dan zataje kasuwa, dakin Zarah tashiga da sallama tace mata tashirya, kallonta tayi tace dauka ga kudin nan, kidauka, saura kije kidade,

Fita tayi taje yima Baba mairo sallama, tace Baba mairo natafi, kudi Baba mairo takara bata tace amsa, Falak tace nameye Baba? Tace idan kinje kisiyo turare naga naki yakare, kwallan idonta tagoge, tace nagode Baba mairo, tace haba Falak ai bakomai, yisauri kije kidawo ki amshi Ameer inshiga kitchen kafin Zarah tafito. Kallon Ameer tayi yana bacci, duk yarame,fita tayi tana goge idonta.

Abakin gate taci karo da Alh, yana kokarin shiga mota, binta da kallo yayi, Zarah wadda take gefenshi tace lafiya de naga kana kallonta? Yace naga bansanta agidan nan ba ne shiyasa, murmushi tayi tace oh, sabuwar me aikina ce, mota yashiga yace yatafi.

Bayan Falak tagama siyen abinda zata siya, taje chemist tasiyoma Ameer maganinshi, sannan taje gurin siyen turarenta. Bayan tasiya, tajuya kenan taji kamar ana kiranta. Haka tawuce batare data juya ba.

Malama Falak, yau kuma babu magana inata magana, juyawa tayi domin taji muryar malam. Sameer, ido suka hada dashi, yana cikin wani yadi mekyau yakara haske, duk se kunya takamata ganin kayan dake jikinta,gashi duk tayi baki.

Bayan sungaisa yace Falak yagida, nima jiya nadawo, shine yau nafito shago, ashe dama kina shigowa kasuwa, ke kadai, yau ina Jalila ne? Shiru tayi kanta yana kasa tana wasa da ledar hannunta, idonta har yafara kawo kwalla.

Yace Falak lafiyarki kuwanaga kamar kina cikin damuwa, gashi naga duk kin rame, inafatan de lafiya? Hadiye kwallanta tayi, tace malam, rana tanayi kada ajirani agida, zanwuce. Murmushi yayi yace shikenan, tunda bazaki fadamun ba, kodan nan kasuwa ce, amma anjima zamu hadu a islamiyya ko? Shiru tayi, yace Falak bani no wayarki mana, tace aikam banda waya, yace tobani ta Jalila, tace barade Inbaka ta Baba mairo, kallonta kawai yakeyi hartagama saka mashi, tamika mashi, amsa yayi yace sena kiraki ko.

Godiya yayi mata ta tafi, kallonta yacigaba dayi, jikinshi yana bashi kamar tana cikin damuwa, ammade bari anjima zan tsareta seta fadamun koma meke damunta, ko intambayi Jalila, haka yajuya yana me farin cikin ganin abin sonshi, dan tunda suka gama makaranta yake dokin dawowa yaganta, kuma wannan karin yayi alkwarin fada mata abinda ke cikin ranshi.

Tun daga nesa tafara ganin mutane akofar gidansu, haka takarasa, gabanta yana faduwa, da kyar tasamu tashige cikin gidan, Jalila tagani tana kuka, saurin matsawa tayi tana tambayarta meyafaru, hannunta Jalila taja suka shiga cikin gida, dakin Baba mairo suka shiga.

Yarda ledar datake hannunta tayi, tasaka wani irin kuka ganin Ameer shimfide akasa bisa tabarma, duk ya mimmike, kuma anrufeshi da zani. Baba mairo shikenan shima ya mutu ko? Kamata Jalila tayi suka zauna, tana bata hakuri.

Baba maito tace kidena magana Falak kada kiyi sabo, kinsan Allah yafimu sonshi tunda har ya amshi abunshi, addu,a yakamata kiyi mashi, kuka kawai Falak keyi, dahaka wadda zatayi mashi wanka yashigo, komawa gefe Falak tayi tana kallon yanda akeyima Ameer wanka ko motsi. Bayayi.

Bayan angama Alh, yashigo shima yana kuka, hankalinshi duk yatashi da kyar yadauki Ameer yafita dashi akayi mashi sallah sannan suka kaishi makwancinshi. Zarah kuwa tana falonta, tarufe fuskarta. Da hijabi duk wanda yashigo gaisuwa seya dauka kuka takeyi, haka yan unguwa suka rika shigowa yin ta,aziya.

Washe gari Falak ta tashi da zazzabi me zafi, bata iyama tashi ga ciwon kai, Baba mairo duk tashiga damuwa, Jalila cetasamo mata magani adakin Zarah, haka akayita karbar gaisuwa har kwana 3, su Asabe da kawarta Dije ma sunzo.

Jidda kuwa batama san abinda akeba dan suna Lagos ita da Al,amin. Bayan sadakar 7 su Asabe suka koma suna cike da farin cikin abinda Zarah tayi masu dan tabasu kaya da kudi masu yawa saboda tana cikin murnar aikin boka yayi.

Malam. Sameer zaune a dakinshi yana tunanin kome yahana Falak da Jalila zuwa makaranta, gashi no da Falak tasa mashi yakira harya gaji tun aranar amma bata shiga, jawo wayarshi yayi, yaduba agogo yaga karfe 9 n dare.

No yakara kira, cikin sa,a kuma tashiga, zaune au Baba mairo da falak suke adakinta, dan tunda Ameer yarasu adakin Baba mairo take kwana, wayar Baba mairo ce tayi kara, dauka tayi da sallama, bayan sun gaisa yace Baba mairo dan Allah ko Falak tana nan? Cike da mamaki tace e tana nan, wayene, yace Malaminsu ne na islamiya Sameer.

Washe baki Baba mairo tayi, dan tanajin labarinshi agurin Falak da jalila,hartake tonan Falak tana cewa kode siriki tasamo mata. Baba mairo tace e gata nan bari abata, mika mata wayar tayi, bayan sungaisa, yace haba Falak tunda kika bani no kuma bansake ganinki a makaranta ba, gashi idan nakira ma bata shiga.

Na tambayi yan ajinku sunce wai kindena zuwa Jalila ce kadai take zuwa itama ba sosai ba. Meyafaru dan Allah, kinsan tun rannan naga kamar akwai abunda kedamunki.

Shiru tayi saboda wani kuka daya taho mata, Baba mairo kallonta kawai takeyi, tama karajin tausayinta. Hello Falak kinajina kuwa, sautin kukanta kawai yaji daga nan takashe wayar, tafada bisa katifa tana kuka

Kara kiran wayar akayi, ganin harta kusa katsewa yasa Baba mairo ta dauka. Sameer yace hello Falak kinajina, dan Allah kiyi shiru, bana son jin kukanki wlh, yana tadamun hankali, tunranar damuka hadu akasuwa naga kamar kina cikin dakuwa nima nashiga damuwa. Kiyi hakuri idan akwai abinda yake damunki. Wlh ashirye nake da intemaka maki.

Hawayen idonta Baba mairo ta goge aranta tana mejin dadin yau Falak tasamu wanda yake damuwa, da lamuranta. Hello Falak kiyimun magana. Baba mairo tace yaro kanajina, yace e,e Baba inajinki ina Falak din?

Tace Falak bazata iya maka magana yanzu ba, dan kamata fami akan abinda kedamunta, sede bansani ba, kawai naji ka kwanta mun arai, dama kuma inajin labarinka agurin su Jalila, tun lokacin daka bama Falak addu,a tayima Ummanta sanda batada lafiya.

Agaskiya Sameer bazan iya boye maka abunda yake damun Falak ba, saboda inaji ajikina, kaine zaka temaketa, idan harkaji labarinta, idan harzaka iya sauraron labarin Falak, kabari se gobe idan kasa kudi awaya kamar irin wannan lokacin seka kira inabaka labarinta.

Sameer yace a,a Baba mairo wlh inada kudi awayata zasu isa inji labarin Falak, bazan iya hakuri xuwa gobe kamar yanzu ba. Gyara kwanciya Baba mairo tayi, tace zanbaka labarinta, amma inaso kazam merikon gaskiya da amana idan kaji labarinta............. Anan Baba mairo tafara bashi tarihin Falak.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[5/30, 9:17 PM] Nabeela lady: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 70.....75

Kuka kawai Sameer yakeyi, yana sauraron Baba mairo, hartagama bashi labarin Falak, be iya magana ba, yace nahode Baba, Sautin kukanshi kawai takeji,da haka yakashe wayar.

Tunda yake arayuwarshi betaba jina labari me firgitarwa kamar na Falak, jiyake kamar a film akayi abun, da ace ba Baba mairo bace tafada mashi, labarinta ba, naze yarda ba.

Wata irin soyayyar Falak ce take shigarshi, gatausayinta daya ke shigarshi jiyake kamar yaje yadaukota tadawo kusa dashi, kuka kawai yakeyi, yana jin zuciyarshi kamar zata fito, aranar kasa bacci yayi, sede yayi alwala yafara nafila, har asuba tayi, seda yayi sallar asuba sannan ya kwanta, saboda ciwon dayaji kanshi yana yimashi.

Falak ma haka ta tashi da ciwon kai me tsanani, da zazzabi, da kyar tayi sallah ta kwanta, Baba mairo tana gama sallah taji Zarah tashigo ta watso kayan wanki tace idan wannan AGOLAR tagama sallah kice mata tayi mani wanki, saura kuma tabari gari yawaye infito bata gama ba.

Fita tayi takoma dakinta ta kwanta, Kallon Falak Baba mairo tayi wadda batama san me akeyi ba, saboda bacci me nauyi yadauketa, saurin tashi Baba mairo tayi tadauki kayan tashige bandakin dake cikin dakin tafara wankesu. Dayake bawani yawa garesu ba, kuma basuda datti, cikin minti 20 tagama, cikin sando tafita taje ta shanya, tadawo.

Kitchen tawuce tayi wanke wanke sannan takoma daki ta kwanta ganin haryanzu gari be ida haske ba, kuma dama bata fara girkin safe se karfe 7. Kwanciya tayi tana tunanin hanyar dazata bi Falak tabar gidan, sede tana tunanin Falak bazata yarda tabar gidan ba, inde ba aure tayi ba, saboda tana riko da wasiyar da Ummanta tabar mata. Addu,a tashiga yi Allah yasa Sameer yace ze auri Falak, da cikin lokaci kadan zatace yafito, sede bata sani ba ko Zarah zata yarda Falak tayi aure yanzu.

Har karfe 10 Sameer be fito daga daki ba, ummanshi Halima data gama saida kosanta harta gama aikinta, tajishiru, kuma besaba yin haka ba, dakinshi tashiga da sallama. Tsaye tayi ganinshi zaune yabuga tagumi yana tunanin, ga kuma hawaye suna fita daga idonshi.

Kusa dashi tazauna jikinta duk yayi sanyi ganin danta yana kuka, dan tasan kila mahaifinshi yatuno. Sameer lafiyarka kuwa, kake kuka? Goge idonshi yayi yace Umma ina kwana, kiyi hakuri yau natashi banajin dadi shiyasa banfito dawuri ba.

Lafiya lau, Sameer amma bawannan na tambayeka ba, rashin lafiyar ce tasa kuka kome? Tashi yayi yace Umma bara inyi wanka zan fada maki damuwata, waje yanufa domin yin wanka.

Seda Falak tayi wanka sannan Baba mairo takawo mata abinci, fa kyartaci tasha magani, dan tadanji sauki datayi bacci sosai, kallon Baba mairo tayi tace Baba mairo yaushe aka wanke ma Ummi kayanta harnaga kina linkewa? Anan Baba mairo tafadima Falak abunda yafaru da tana bacci, kwalla ce tacika idonta, tace bansan da abinda zan saka maki ba, Baba mairo, Allah yabani tsawon rai nima inyi maki wani abu wanda zakiji dadi arayuwarki.

Murmushi Baba mairo tayi tace ai keda Ummanki kungama mun komai tunda har kuka daukeni amatsayin uwa, kinga ko babu abinda yafi wannan dadi, nide fatana Allah yabani tsawon rai in kaiki dakin mijinki. Murmushi Falak tayi tace Uhm Baba mairo kenan, aini bana sa rai zanyi aure, dan nasan Ummi bazata barni inyi aure ba, tunda batason cigaba na.

Baba mairo tace insha Allahu sekinyi aure Falak, kuma ni harna zaba maki miji ma, Allah yasa zakiyi na,am da zabina. Dariya Falak tayi tace lallai Baba mairo kinkosa kirabu dani, to afadamun wanda aka zaba mun, ina fatande ba tsoho bane?

Dariya Baba mairo tayi tace a,a wanda kike sone kika boyema ranki na zaba maki, fiddo ido Falak tayi tace kai Baba mairo, yaushe mukayi haka dake, ni babu wanda nakeso. Har Malam. SAMEER din? Rufe fuska Falak tayi tana murmushi, tace yaushe nacemaki inason malam. Sameer kuma? To inma baki sonshi ni shina zaba maki. Kai Baba mairo shifa bece yana sona ba,

Yace mana, jiya ai naji abinda yace, da kika aje waya nadauka, haka yayita surutai, yadauka kece awayar. Dariya Falak tayi tace nide banyarda ba, Baba mairo tace Allah Falak a aje batun wasa agefe, dama inaso muyi magana dake akan Sameer, nide tabbas nayarda dashi, shiyasama jiya nakasa boye mashi labarinki.

Inaso Falak ki nutsu kigane mesonki, kada kiyi la,akari da Sameer malamin makaranta ne, kice bakisonshi, nide nayarda dashi , kuma nasan zerikeki da amana, inaso insamu lokaci inganshi koda awani gurine, ko kuma yazo yakaini gidansu muyi magana dashi. Allah yasani inaso inga kinbar gidan nan. Falak tace to Baba mairo Allah yazaba mana abinda yafi zama alkairi. Amma kisani duk ranar dazan bar gidan nan kafata kafarki, idan bahaka ba, sede na hakura da auren dan kowa zan aura, seya yarda zaki bini. Dariya Baba mairo tayi tace ti naji insha Allahu ma bakida mijin daya wuce Sameer. Murmushi Falak tayi tadauki kayan Zarah tafara gogewa.

Zaune suke afalo Alh, yakalli Jalila, yace Alhamdulillahi gashide na amso maki, admission dinki, kuma nabama wani abokina yayi maki registration ana A,B,U tunda de kince bazakiyi karatu anan kadunaba, wato kinfison makarantar kwana ko? Dariya Jalila tayi tace ai Dady anfi yin karatu acan, amma nan kila inacikin yin karatun wani abun yadaukemun hankali.

Zarah tayi murmushi tace can dinma ai gidane, damma tace bazata zauna agida gurin Inna asabe be, tafison hostel, me suka bata ne? Biological science ne suka bata, to Allah ya bada sa,a seki dage.

Alh, yace Hajiya watodesu Inna su kwace mana Jidda ko? Yanzu ko lekomu batayi, naso ace tadawo insa ayi mata exam ta kudi itama tafara karatun tunda taki fidda miji, dazama haka nan, amma gaskiya banajin dadin rashin zamanta agida kusa damu. Zarah takalleshi fuska ahade tace to mekake nufi? Tunda yarinya tace batason karatu abarta mana aiba dole bane, ni karatun nayi dakake zaune dani. Kuma menene bana yi maka, wama ze kalleni yace secondary kawai nayi, itama ta gwamnati, ina laifi ma ita tayi makarantar kudi tasan yes tasan no.

Nifa banason takura wlh, kuma dakake maganar tadawo gida tazauna, kana nufin gidanmu ba gida bane kome? Inma kyamarsu kake nima acan nataso harka ganni kace kanaso, idan tadawo nan, mezatayi maka, kaima da bazama kakeba, kuma acan tana taya Inna zama tunda ita kadai ce.

Allah yabaki hakuri Hajiya wlh ba haka nake nufiba, kawaide nafada ne, amma kiyi hakuri ba za,a sakeba. Kallon mamaki Jalila take bin Umminsu dashi, ganin yanda takema Dadynsu fada, wanda ada ko gardama batayi mashi, amma wai yau shine yake bata hakuri, har muryarta tana fin tashi yin sama. Tunowa tayi da wa,azin da malam Sameer yayi masu akan hukuncin matar datake daga ma mijinta murya. Wasu zafafan hawayene suka rika fiyo mata, saurin gogesu tayi.

Alh, yace Jalila zaki iya tafiy, amma kizama cikin shiri nan da sati mezuwa zaki tafi, anjima kizo ki amshi kudi seki siyo abunda kike bukata. Tashi tayi jikinta duk amace, tafita.

Halima tace Sameer lallai akwai abinda yake damunka, kuma ba karamin abu bane, kallifa dan abincin daka ci. Sameer yace wlh Umma banajin dadin abincin ne. Rufe kwanon tayi tace inajinka fadamun damuwarka.

Gyara zama yayi, ya kwashe duk abinda Baba mairo tafada mashi yafada ma Ummanshi. Kasan cewar Halima mace me tausayi, bata san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba.

Tana goge idonta tace wai Sameer wannan labarin ba ta tsunniya bace kake bani kuwa. Wlh Umma ni kaina faba Babbar mace bace tabani labarin Falak ba, dabazan yarda ba, kuma nima naga wasu alamomi agurinta lokacin damuka hadu kasuwa, bakiga kayan jikinta ba, bazakice daga gidan masu kudi tafito ba.

Umma tace tabbas nima bantaba jin abinda yabani tausayi da tsoro irin labarin Falak ba, agaskiya Sameer ina yimaka sha,awar aurenta, koda bakace kana sonta ba, nizanyi maka umarni da aurenta kodan kafidda ta daga rayuwar datake ciki, dan wannan mata batada imani zata iya kasheta wlh.

Kuma naji dadi, dakace kana sonta, tunkafin kaji labarinta, hakan zesa nayarda bawai tausayinta ne yasa zaka aureta ba, dama nafison ace akwai soyayya atsakaninku kafin kuyi aure, hakan zesa auren yafi dadewa.

Tunda baze yuwu kaje gidansu ba, meze hana kadauko Baba mairo kuzo nan muyi magana ba. Yace shikenan Umma zanyi yanda kikace. Yauwa Sameer amma dan Allah kacire damuwa aranka, insha Allahu bakada mata se Falak, zantayaka da addu,a har Allah yadoramu akan wannan muguwar mata. Sameer yayi murmushi yace ai damuwa takare, dama ina tsoron kiji labarinta kice bazan aureta ba. Dariya tayi tace haba Sameer ai yakamata kamun sheda mekyau, Allah kada yakawo ranar dazan tauyemaka hakkinka, kamar yanda kakemun biyayya dolene nima inso abunda kakeso, matukar baze cutar da kaiba.

Sameer yace amma Umma anan gidan zamu zauna ko? Kinsan banason nisa dake, tace a,a kada ma kafara, bazan zauna da surika agida daya ba, gara de muna nesa, idan kata fima akwai A.isha diyar yaya Zainabu tagama makaranta kuma dama tace mun zata bani ita, tunda tana da yan mata, seta dawo nan mucigaba da zamammu.
Sameer yace to umma ina zan zauna? Tace bade ka gama karatunka ba, haya zaka kama kafin Allah yabude se kafara gina wancan filin naka. Amma Allah bazamu zauna tare ba. Dariya yayi yace toshikenan Umma ai base kinrantse ba, yanzu de bani abincina incinye. Dariya tayi tace oh baka koshiba kenan.

Sati yana zagayowa Jalila tagama hada komai, nata, dakin Baba mairo tashiga, zaune ta iskesu suna fira, mikama Falak takaddu tayi, idonta yana kallon kasa, saboda gab take da fashewa da kuka, ita kadai tasan abinda takeji. Falak tace nameyene Jalila? Budawa tayi tafara dubawa, cike da farin ciki ta rungume Jalila, ganin result dinta ne ta amso mata kuma gaba daya tacinye both waec dan Neco.

Kuka sosai Jalila tasak tana kara kankame Falak, cikin muryar kuka tace Falak kiyi hakuri nasan Ummice tasakaki cikin halin da kike ciki, gashi yanzu zantafi makaranta batare dakeba, wlh saboda ke nazabi intafi boarding saboda bazan iya kallonki cikin damuwa ba, ki kara hakuri akan wanda kikeyi.

Kuma dan Allah ki amince da malam. Sameer yafito kuyi aurenku kema kibar gidan nan, dan wlh koni bansan lokacin

Please Login or Register in order to submit comment