Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

se sudawo. Haka aka fita da Falak, dan babu wani fada da Zarah tayi mata, Falak taso taga Alh, amma Zarah tahana, dan boka yace duk ranar dasuka hada ido da Falak da Alh, asirin ze karye. Haka Falak tafita tana kukan rashin Uwa. Mutanen unguwa se gulmar Zarah sukeyi suna cewa takasa rike amanar da,a barmata. Su Baba mairo basu dade ba, suka juyo, Falak kuka kawai takeyi. Bayan tafiyarsu Jalila ta kirata awaya, tana kuka tana bata hakuri, tace. Wlh Falak bazan iya zuwa inga irin auren da Ummi tayi maki ba, kiyi hakuri Falak, insha Allahj wata rana komai zewuce. Falak tace bakomai Jalila nagode, haryanzu de kinkasa zuwa gida ko? Jalila tace Falak banason abinda Ummi takeyi agidan nan, shiyasa nafison zama. Makaranta akan gida. Falak tace banason Haka Jalila, da kunsamu hutu kidawo gida, ko kin manta wa,azin da Malam Sameer yayi mana akan muhimmancin uwa? Kome Ummi tayi dole kibata hakkinta amatsayintana Uwa, idan har kinaso mushirya to da kunyi hutu kizo gida. Jalila tana kuka tace shikenan Falak zanzo, nagode da tunin da kijayi mani. Allah yabada zaman lafiya, yasunan mijin naki? Falak tace nimade Ummi tace mun sunanshi Asid. Jalila tace dan Allah jiwani suna, kiyi hakuri Falak nasan Ummi tasakaki kowace rayuwa kika shiga. Sallama tayi mata takashe wayar. Murmushi Falak tayi tace Jalila Umminki tabiyani tunda hartayi sanadiyyar sama mun farin cikina.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[6/3, 12:52 PM] Nabeela lady: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)

Part 85.....90

Zaune take ita kadai tana ta tunanin irin rayuwar da tayi, addu,a tayi Allah yasa aurenta yazamo karshen yankewar wahalarta. Sallama taji anyi, Sameer ne yashigo bayan ya kulle gidan sannan yanufi dakin da Falak take.

Zaune take da ganin idonta taci kuka, harta gaji, zamayi kusa da ita tare da cire mayafin data rufa, hannu tasa tarufe fuskarta, murmushi yayi yace Falak yau kuma rowar fuskar akemun? Ai yanzy munzama daya, nazama ke kin zama ni. Cire hannunta tayi tana kallonshi tana murmushi.

Falak nagaji dayawa, tashi muje muyi wanka, kafin muzauna ko? Aini nayi wanka sede kaje kayi, uhm bawani nan banyarda ba, to koma kinyi zaki sakene, ai bance kiyi ke kadai ba, tashi tayi tashiga bandaki ta hada mashi ruwan wanka sannan tafito, kokarin cire riga yake yana fadin da gaske fa nake tare zamuyi, ai tun kafin yakarasa fadi tayi waje.

Dariya yayi yace matsoraciya, wata rana zamuyi ne, shiga yayi bandakin yayi wanka, seda yagama shiryawa sannan tashigo itama tawuce bandakin, daga cikin dakin yake mata magana, kiyo alwala kafin kifito fa.

Bayan tagama tafito tadauki diguwar rigarta a durowa takoma bandaki tasaka sannan tafito, turare kadai tashafa tashimfida masu abin sallah, shiyajasu sallah har suka, gama, sannan yayi mata tambayoyi akan addini, dayake Falak akwai kokari duka ta amsa tambayar da yayi mata,

Tashi yayi yadauko ledar daya shigo da ita, kitchen ya koma ya dauko plate sannan yazuba masu, shiyarika bata shima yana ci, harsuka koshi, Falak de kunya takeji takasa sakin jikinta. Kwashe kayan yayi ita kuma takoma bandaki tayo brush, abandakin yasameta tana shirin fitiwo, hannunta yakama, seda yagama sannan suka fito tare, rigar jikinshi yacire dagashi se gajeran wando da vest, saurin rufe idonta tayi, jitayi itama yana kokarin cire mata riga, tace sanyi fa nakeji.

Dariya yayi yace ai bargo zamushiga, haka yacire mata riga daga ita se under wear da vest yabarta, bisa gado yajata, bayan aun kwanta yajawota yadorata bisa kirjinshi, yanata shafa mata kanta, tuni jikin Falak yafara rawa. Murmushi yayi yace Falak sarkin tsoro, ni babu abinda zan maki, magana zamuyi, kuma nafiso injiki ajikina shiyasa.

Ajiyar zuciya tayi dataji kalamansa. Falak, Sameer yakirata, na,am. Dole mugodema Allah daya nuna mana wannan rana, bazan iya kwatan tamaki irin farin cikin danake ciki ba, Allah yasani duk da ga yanda akayi aurenmu. Wlh banajin haushi kokadan, nasan dayawa mutane suna gulma akan aurenmu, amma ni beda meni ba.

Nasan Falak zakiji haushi da irin yanda na aureki, kiyi hakuri, komai ze canza, duk da kinfi kowa sanin yanda aurenmu yakasance amma dole inbaki hakuri, insha Allahu gobe tela zekawo maki dinkunanki, akwatinanki kuma suna gurin Umma, suma gobe zan daukosu.

Nayi hakane saboda banaso Umminku ta fahimci wani abu, shiyasa nakawo kaya marasa kyau, inaso kidaukeni abokin rayuwa na har abada, banida niyar cutar dake, kuma insha Allahu zan zamo maki abin alfahari, idan komai yayi mana dede zaki koma makaranta kema kiyi karatu kamar kowa,

Banaso idan kina da damuwa ki boyemun, yanzu bakida kowa seni, Baba mairo tayi maki nisa, yanzu nine makusancinki, idan har muka gina rayuwarmu ahaka, tabbas zamuji dadi kuma wani abu baze shigo ya tarwatsa zamammu ba.

Kamar yanda Umma tace nan da kwana 2 Baba mairo zata koma gidanta, itama bazata kara zama amatsayin me aiki ba, shikuma Dady insha Allahu zamu sa shi acikin addu,a kawu ma yace zetayamu da addu,a domin tun ranar daya ganshi yagane yana cikin yanayi na asiri.

Allah yanbani ikon rike amanar dana dauko, kuka sosai Falak takeyi, jawota yayi yakara rungumeta yana lallashinta, shiru tayi tana maida numfashi. Dagowa tayi ahankali tace Bansan dame zan gode maka ba, Allah ya..... bata karasa ba, jin yahade bakinsu guri daya, kissing dinta yake sosai, tuni jikin Falak yafara rawa, jin irin abubuwan dayake mata. Daga haka labari ya canza.

Zaune suke adaki suna ta faman dariya, Zarah tace yakukaga irin aikina, ai nafada maku bazan taba barin Falak tayi rayuwa me dadi ba, haka zata kare daga karshe tayi mutuwar wukakanci. Dije tace gaskiya hajiya kema kin iya aiki, yanzu dasunyi shekara 1 ze saketa?

E haka nace mashi, daga farko, amma daga baya nace mashi dayaji ta isheshi ze iya koromun ita, kuma nace mashi yatabbatar yayimata raga raga, kada ya saukaka mata dede da kwana 1, kuma nace karyayi mata riko mekyau, kinsan dangiya akwai dukan matansu, haka ze maidata kamar jakarshi, ga aiki ga duka, kafin tadawo gidan nan setakoma kamar me kanjamau.

Asabe tace, amma inafatan idan tadawo ba,anan zata cigaba dazama ba ko? Zarah tace haba de, nikam mezanyi sa wannan yarinyar, ai dama burina ta wulakanta, idan da halima sonake tafito da ciki. Dije tace duk da haka idan tafito kada kibarta tashiga duniya haka, kinsan mutane akwai tausayi, wasu zasu iya daukarta su temaka mata rayuwarta zata iya yin kyau nan gaba.

Kawai itama ayi mata yanda akayima uwarta, asamata ciwo me tsanani kinga kota tafi acan zata mutu. Zarah tace kwarai kuwa wannan shawara taki tayi, zanjira fitowarta, sekuje gurin boka yayi mata aiki. Haka sukayita fira daga nan Zarah tayi masu seda safe tawuce gurin Alh,.

Jidda da Joseph suna nan suna cin duniyarsu, Jidda tayi kyau hartagaji, lokaci zuwa lokaci suna waya da al,amin shima idan yakirata seta ga dama take dauka, ayanzu yanda takejinta cikin daula, gani take tafi karfin Al,amin, shiyasa yanzu take mashi wulakanci. Tunbaya damuwa haryafara damuwa, ganin abin nata yana kara gaba, yasa yayima Joseph magana akan zezo yadauketa.

Dayake agaban Jidda sukayi wayar tun kafin Joseph yabashi amsa ta anshi wayar, cikw da masifa tace wai kai Al,amin ana so dole ne? Nifa yanzu babu wanda zetakuramun nima inada yancin dazanyi rayuwar danakeso, saboda haka dan Allah ka sauraramun kafita ahanyata, wlh yanzu nafi karfin ace wai kai saurayinane, ko ada rashin wayo neyasani biye maka, amma yanzu kasani ni Jidda nafi karfinka, bani ba kai.

Kashe wayar tayi tacema Joseph kada yakara daukar wayarshi, ita baruwanta dashi, anan zata zauna idan taso tafiya gida zata tafi ita kadai. Wani irin mugun murmushi Joseph yayi, dama yana lallaba tane saboda idan Al,amin yadauketa, idan yakara neman tazo zata iya dawowa.

Al,amin kuwa mamaki ne yakamashi, tsayawa yayi yana kallon wayar hannunshi. Wasu irin zafafan hawayene suka rika zubi mashi, har ga Allah yaso ace Jidda ta saurareshi, yanaso tadawo kodan yafada mata shiyanzu yatuba, yanaso itama ta tuba kuma shize aureta, tunda dama shine farkon lalata ta.

Tunda yaga wani abokinshi agabanshi yarasu, tundaga ranar tsoron Allah yakamashi, kuma yayi alkawarin baze kara aikata zina da duk wani laifi marar kyauba. Hakan yasa yakira joseph dan yaje yadauko Jidda amma tayi mashi rashin mutunci. Kuka sosai yakeyi yana fadin why Jidda, meyasa zakimun haka, kinsan ina sonki, tsautsayi ne, da rudin shedan yasa harna iya bama wani banzan arne ke yake kusantarki kamar matarshi, nayima Allah laifi megirma da har na iya amincewa da makiyin Allah.

Tashi yayi yashiga bandaki yayo alwala yafara sallah, bayan yagama yakira wani abokinshi yace mashi yanason visa zuwa ummrah idan ze samu, yace mashi babu damuwa yazo gobe. Al,amin yace gara intafi inje inemi yafiyar Allah shine abinda yafimani. Ke kuma Jidda zancigaba dayi maki addu,a insha Allahu ko ban aureki ba, yanda na kaiki nine zan daukoki, nasan Allah baze yafemunba matukar ban raboki daga gurin kafirin Allah ba.

Washe gari dasafe Sameer yatemaka ma falak tayi wanka yagyra gurin bayan sunyi sallah suka koma bacci, rungume yake da ita kamar ze maidata ciki, se albarka yake samata. Segurin karfe 10 sukatashi, alokacin Ummanshi ta aiko masu da abinci, haka suka ci , ya gyara gurin, fita yayi yace zeje gida daga can yawuce kasuwa gurin me dinki.

Shatara ta arziki Zarah tayi masu Asabe, Godiya sukayi mata tasa driver yamaidasu. Komawa tayi daki tadauko wayarta domin takira jidda, dan jiya Alh, yake tambayarta ita, harcewa yayi tadawo gida hakanan, duk da yana tsoron Zarah amma bayajin tsoron yimata magana akan yaranshi, sede idan ta taso mashi da masifa ne, yake rudewa.

Itama Zarah hankalinta yafara taahi ganin haryanzu Jidda bata dawo ba, tsaki taja ganin haryanzu wayar taki shiga, hakan ya tabbatar mata basu dawo ba. Oh ni Zarah kada fa yarinyar nan tajawo mani abun fadi agari, daga zuwa hado kayan aure shikenan. Kuma gashi ko sunan kawarta ta bansani ba, bare insan gidansu. Danaje na tambayo ko lafiya. Gaskiya nima nayi sakaci, kuma Inna Asabe ai tacemun babu inda Jidda take zuwa kullum tana gidanta. To ina tasamo wannan kawar?

Baba mairo ce tayi sallama harya zauna Zarah batasan tashigo ba, seda ta tabata sannan taji shigowarta, Hajiya lafiya kike irin wannan tunani haka? Ai nadauka bakida sauran damuwa yanzu, Murmushi Zarah tayi tace nikam damuwar mezanyi yanzu, kawai ina lissafin wasu kuda dene.

Murmushi Baba mairo tayi, dan taga alamar Zarah batasan duk abinda take fadi afili tafadeshiba. Hajiya dama zuwa nayi ince maki inaso zanje ganin gida, kinga na dade banjeba, amma wannan karon gaskiya zan jima, kila ma zanyi kamar wata 5. Waro ido Zarah tayi tace haba mairo, wata 5 fa? Yanzu yakike so inyi da aikin gidan, to hajiya gashi bansan inda zan sama maki wata ba, sede ki bincika nasan zaki samu.

Toshikenan, yaushe zaki tafi? Gobe nakeson tafiya. Allah yakaimu, bara zanfadama Alh, anjima seya sallameki, godiya tayi mata ta fita.

Falak tana zaune ita kadai afalo gashi babu kayan kallo, sede game kawai takeyi da wayarta. Sameer ne yashigo da sallama yana fadin yi hakuri baby na, nabarki gida ke kadai, wlh ina kasuwa tundazu. Murmushi tayi ta taso takarbi kayan daya shigo dasu tana fadin sannu dazuwa.

Komawa yayi yadauko sauran kayan, ruwa takawo mashi, sannan takoma tadauko abincin da aka kawo masu daga gidansu Sameer. Jawota yayi yana fadin kinzauna shiru ko? Kiyi hakuri zamu sa kayan kallo kinji. Abinci tamika mashi abaki tana fadi bakomai wata rana ai bazan zauna shiruba ko? Yace hakane, karbar cokalin yayi yacigaba da bata shima yana ci.

Bayan sungama takwashe kayan ta kai kitchen, seda ta wankesu sannan tafito, zama tayi yafara fiddo mata kayan dinkinta, sosai kayan sukayi kyau, ga kuma sauran daba,a dinka ba, acikin akwati da kayan shafa, akawatina 3 da kit yayi mata, kayan sunyi kyau sosai. Haka yasata tayi ta gwada dinkunan.

Washe gari. Da safe Baba mairo tashiga yima Zarah sallama, dubu 5 tabata tace inji Alh, yace tahau mota, se kuma kudin aikinta na watan tabata dubu 15, ita kuma takara mata dubu 2. Duk da dubu 50 Alh, yabata yace tabata hada kudin aikinta sauran kuma tayi tsaraba da kudin mota. Amma seda tarage. Godiya tayi mata tadauki kayanta tafita tana fadin nida aiki agidan nan har abada, Allah yatoni asirinki ke kuma.

Nima nace Ameen.

Urs,

NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[6/5, 3:11 PM] Nabeela lady: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 90.....95

Zaune Baba mairo take adakin Falak kasancewar Sameer yafita, bayan tagama cin abincin da Falak takawo mata, takalli Falak tace, akwai sakon da ummanki tabani, tunkafin tarasu, kuma tacemun inbaki shi bayan kinyi aure.

Alhamdulillahi yau zancika wasiyar data bani, bude wannan jakar kifara ganin abinda ke ciki, wannan kuma wasika ce tabani ita aranar dazata rasu. Karba Falak tayi tabude jakar.

Awarwaro ne tun wanda kakarta tabata, lokacin tana yarinya, se kuma takardun makarantar ta, da takardun filin da Alh, yabama Ameer. Se A,T,M. Bude wasikar tayi zata fara karantawa afili Baba mairo tace a,a Falak ki karanta aranki tunda wasiyace. Goge kwallan data zubo mata tayi tace, haba Baba mairo nifa ina maki kallon Ummata ce, kinga ko babu abinda zan iya boyemata, saboda haka kada kiyi tunanin zan iya boye maki wani abu. Murmushi Baba mairo tayi tace nagode Falak.

Fara karantawa tayi kamar haka......



Falak nasan alokacin da wasikar nan zata iskeki nadade dabarinku, inaso kiyi hakuri da duk yanayin rayuwar da kika tsinci kanki, dukkan tsanani yana tare da sauki. Inaso kirike kaninki kada kibarshi yayi kukan rashin Uwa, duk da nasan shima da kyar zeyi tsawon rai.

Ga awarwaronki nan kisakasu ahannunki, saboda kirika tunawa dameshi. Nasan bakisan kowa nawa ba, yan uwan mahaifinki ma bawani yawa garesu ba, Kawunki kadai kika sani, kuma bana fatan ki kara ganinshi arayuwarki.

Nikaina bansan yan uwana ba, nare inyi maki kwatancen inda zaki samesu, kuma ba,a nigeria sukeba, a niger suke, sede bansan a inda zaki nemesu ba. Inaso kiyi hakuri ninasan Allah ne yakawo mana Alh, domin yazame mana dan uwa, kuma yazama Uba agareki, nasan kobayan babu raina, Alh, ze iya rikeki kamar nice narikeki. Kiyimashi biyayya kamar mahaifinki.

Banyarda ko bayan raina kibar gidanshi ba, kowane hali zaki shiga, gara kizauna agabanshi yafi kishiga duniya, nasan Zarah batasonmu, amma tunda Alh, da Jalila suna sonki kiyi hakuri kizauna dasu, kowace irin rayuwa zaki gani agidan kiyi hakuri wata rana zaki zamo haske agaresu.

Aure ne kadai nayarda idan kinyishi kibar gidan Alh, Falak dan Allah ki kula da Ameer, nasan beda lafiya amma kiyi hakuri dashi, insha Allah zakici nasara arayuwarki, idan kuma shima ya rasu, inaso kiyi hakuri, kirike Baba mairo tamkar nice agabanki.

Nima kaina namaidata uwa agareni, kema kiriketa zata zamo haske arayuwarki, kobayan kinyi aure idan har kina da hali inaso kidauketa zuwa gidanki, idan kuma mijinki be amince ba, acikin kudinki kisiya mata gida tazauna, kicigaba da kula da ita kamar ni.

Banyarda kirika boyema mijinki komai ba, shine gatanki, nasan In Allah ya yarda zaki samu miji nagari, wanda baze taba cutar dake ba. Kibashi dukiyarki, yakula maku da ita, dake da kayanki duka mallakinshi ne, kada kizamo me rowa arayuwarki, kuma kizama me temako, saboda temako shine yakawoki halin da kike yanzu.

Ga takardun makarantarki nan idan har kinyi aure baki karatu ba, inaso kinemi yardar mijinki kiyi karatu dan nasan burinki ne, idan har ya yarda, kiyi idan kuma beyarda ba, ki hakura. Kuma koni zan baki shawara zance kiyi hakuri da karatu, domin dukiyarki zata isheki kiyi kasuwanci.

Gara kizauna kirike mijinki zefi maki dakirika fita kina zuwa makaranta,
Kiyi hakuri da duk irin mijin dakika samu, kada kizama me tona sirrin gidanki agurin kawayenki, domin hakan ze bata zamanku da mijinki, kuma banaso kizamo meyawan kawaye,duk wata shawara dazakiyi kada yawuce Baba mairo da mijinki.

Ga takardun filin Ameer nan, idan har yarayu, wannan filin nashi ne, amma banyarda kimaidasu agurin Alh, ba harse idan shine yanema dakanshi, nasan Zarah tanajin haushin Ameer idan har tasan da Filin nan zata iya amshe shi. Idan kuma yarasu, toki mikasu zuwa ga Alh, dan yanada iko akansu.

Akwai A,T,M acikin jakar, wannan gadonki ne na Babanki, tunkafin yarasu yarika ajiye kudi aciki, kuma da sunanki aka bude accaount din. Bayan aurenmu da Alh, yayi mani kyautar kudi dayawa, kuma da wanda nasamu, hakan yasa nace mashi yarakani inje insaka abanki, kuma akayi maki A,T,M.

Haka narika tara duk wasu kudi da Alh, yake bamu, bantaba cin komai ba, dan bana bukatarsu alokacin. Kuma nasan zasuyi maki amfani wata rana, kudine masu yawa, kibama mijinki yajuya makisu, kada kidamu da cewar ze iya cinye makisu, insha Allahu babu abinda ze samesu zakici moriyarsu.

Daga karshe kimikamun gaisuwata ga duk mijin da kika aura, Allah yayi ma rayuwarku Albarka, ya tsaremun ku, kada kuncin rayuwa yasaki ki sabama Allah, kiyi hakuri aduk halin da kika tsinci kanki.

Nabarku lafiya. UMMANKI HAJJO.😭😭.

Bisa cinyar Baba mairo Falak tafada tana kuka, jitake kamar yanzune Ummanta ta rasu, itama Baba mairon kuka takeyi, haka suka dauki lokaci suna kuka, har Sameer yashigo basu saniba.

Zama yayi kusa da Baba mairo hankali tashe yana fadin lafiya de Baba mairo, ko wanine yarasu? Se alokacin sukansan yashigo. Gyara zama Baba mairo tayi tana goge kwallan idonta, Falak kuwa kwanciya kawai tayi ajikin Baba mairo tana maida numfashi.

Bayan sun gaisa da Sameer Baba mairo tamika mashi wasikar hannun Falak, zama yayi yashiga karantawa, har yakai karshe, shima hawaye ne, suke fita a idonshi. Baba mairo tace ina fatan ka karanta abinda ke cikin wasikar?

Saboda haka Sameer inaso kabude kunnuwanka kaji abinda nakeso infada maka. Da farko de kai ba yaro bane, kuma malami ne na addini, nayarda da kai, hakan yasa nadauki Falak na baka, nasan bazaka iya cutar da ita ba, saboda marainiya ce, kuma nasan kasan hukuncin cutar da maraya.

Duk da ummanta bata sanka ba, amma hakan behana ta mika amanar Falak agurinka ba, kuma harsakon gaisuwa tayi maka. Tunkafin tasan wanda yarta zata aura tabashi amanar dukiyrta, dan haka inaso kadubi girman Allah karike amanar da aka baka.


Nasan kanada zuciyar nema, kada hakan yasa kace bazaka iya amfani da kudin matarka ba, nasan wasu mazan suna yima mata kudin goro suce gori garesu, dan Allah ka auri Falak, baka taba tunanin tanada dukiya ba, ita kanta batasan dasu ba, dan haka inaso amatsayinka na miji, uba, wa, dangi na Falak,ka karbi kudin nan karikesu tamkar naka.

Kada kaji shakkar daukarsu kayiwani amfani dasu, inaso ka gina filinka dasu, kuma ka kara jari kabude shagonka kaima katsaya da kafarka, kada kace zaka jira aikin gwamnati, itama Falak kabata tayi sana,a acikin gidanta, kasiya maku komai na rayuwa, banaso kuzauna cikin kunci, domin Allah ne yakawo maku sauyin rayuwa.

Banaso wani yaji wannan maganar se Ummanka, itama nizanyi matabayani da kaina, dan Allah banaso kace wani abu acikin maganar danayi idan har kadauki Falak amatsayin yar uwarka, to kada kayi duba ga dukiyarta. Allah yabaka ikon rike gaskiya da amana, kuma ya albarkaci dukiyarku.


Sameer yace amen Baba mairo, agaskiya kinbani aiki me matukar wahala, sede yanda nayarda da Falak nasan macece ta gari, da ace wata ce bazan iya amsar dukiyarta ba, domin gaskiya ni mutum ne meson tsayuwa da kafarshi, sede Allah yaga zuciyata, zanrike kudin Falak da amana, kuma insha Allah bazanyi almubazzaranci dasu ba, zanyi amfani da abinda kika ce, amma se idan Umma ta yarda.

To Sameer gaskiya naji dadin abinda kace, kuma dama yanzu zantafi can gidan dan nabaro gidan Zarah, seku tashi mutafi gaba daya ayita takare, dan gaskiya ina mejin haushin inshigo gidan nan inga wai kayan auren diyata ne, haka, ada danasan babu halin yi na hakura, amma yanzu tunda Allah yakawo mana canji dole ne, komai ya canza.


Jidda ce kwance adakin Joseph, tana hutawa, shigowa yayi tashi tayi tarungumeshi, dama bawasu kaya bane ajikinta, shima cire kayanshi yayi, yafara sarrafata, ahaka harsuka fada gado, wani irin salo yake mata, can tayi saurin tashi jin yana kokarin shigarta ta baya, cike da tsoro tace Joseph kanada hankali kuwa, wane irin abune haka, angaya maka ni namiji ce dazaka so yin amfani dani ta abaya? Wani irin wawan mari yadauketa dashi, jawota yayi, tana kuka tana bigeshi, dayake Joseph irin manyan mazan nan ne ana take ya murdeta ya hayeta. Kuka da ihu tasa amma takasa kwacewa, tanaji tana gani yayi amfani da ita ta baya. Kaca kaca yayi mata sannan yatashi yafita, kuma yasa key ya kulleta tabaya.

Kukan ma da kyar yake fita, wani irib azaba takeji ajikinta. Ko tashi takasayi, haka ta kwanta har barci yadauketa. Se can ta farka, dawani irin ciwon kai, da kyar da rarrafa tashiga toilet tayi wanka, seda ta gasa jikinta sosai, sannan tafito, riga kawai tasa takoma ta kwanta.

Can cikin baccinta taji anbude kofa, Joseph tagani shida abokanshi har 2, saurin tashi tayi tana kokarin saukowa dag gadon, hannunta yarike yana murmushi, cikin turanci yake magana, Baby ga friends dina nakawo maki sutayaki bacci. Kallonshi tayi tana kuka tace dan Allah kayi hakuri wlh banason kudinka ka maidani gida plsssss.

Dariya suka dukansu, ya shafa fuskarta yace Baby keda gida har abada, zatayi magana ya fincike rigar jikinta, abokinshi yana ganin kaya, shima yamatso, abinka da bature babu kunya, agabansu yayi amfani da Jidda ta ko ina, tun tana kuka har takasa, yana gamawa shima dayan yayi, haka suka yimata kaca kaca, sannan suka fita suka barta asume, kara kulleta yayi suka tafi.

Lokacin data farka, gari yawaye, rarrafe tayi tashiga toilet, dan bazata iya tashi ba, jikinta duka ciwo yake mata, wanka tayi sannan tayi wankan tsarki, tayi alwala, wanda rabonta datayi wankan tsarki bare sallah tunda tazo london.

Da kyar tasamu tahada kayanta suka rufe mata jiki, dan batada wasu kayan kirki,rasa inda zata kallatayi sallah tayi, hakanan tayi sallah, rokon Allah tafarayi akan yakawo mata dauki. Byan tagama taje bude kofa domin samun abinci da yunwa takeji, amma taji kofar arufe, kuka tasaka tana kiran Al,amin.

Seda aka dade sannan aka bude mata kofa joseph yashigo da plate na abinci da kuma glass cup, ashe giya ce aciki yaxuba wasu kwayoyi aciki. Kusa da ita yaje yamika mata abincin, krba tayi tafaraci, tana gamawa yamika mata cup din, sha daya tayi taji warin giya, saurin zubar dana bakinta tayi, tace Joseph, nizaka ba giya? Mari yadauketa dashi, shake mata wuya yayi yadauki cup din yamatse bakinta, ya dura mata duk giyar, seda taji tana niyar mutuwa sannan tashanye. Bakinta yarike dan kada tayi amai.

Cikin lokaci kankani idanuwanta auka juye, wata irin sha,wa ta taso mata, ashe mganin daya samata na sha,awa ne. Nan take tajawoshi suka fada gado.
Tundaga wannan rana joseph yamaida Jidda yar kwaya, da giya, batada abinsha se giya, tun bataso har tazamar mata jiki, ga kwayoyi tayake bata, duk ta inda yaso yake amfani da ita. Kuma abokanshi babu wanda baya hadawa da ita, gaba daya Jidda tafara lalacewa, idanuwanta sunkoma jajaye.

Al,amin kuwa yana Umarah, banda ibada babu abinda yakeyi, kullum cikin tunanin Jidda yakeyi, duk da yanzu yadena sonta, amma cike yake da danasanin kaita london yake, idan yakirata ma bata dauka, wata rana yakira wani abokinshi makwabcin joseph ne, shine ma yake fada ma Al,amin halin da Jidda take ciki. Sosai Al,amin yatausaya mata, yace ma abokinshi ze iya dauko mashi ita. Yace ai Joseph baya barinta fita, kullum kulle gidan yakeyi. Al,amin yace yana nan zuwa cikin sati insha Allah ze daukota, abokin yace shikenan nima zantemaka maka, dan Joseph mugune.

Haka Baba mairo tayima Umman Sameer bayanin komai, da kuma neman yardarta akan abinda tace, itama ta amince da maganar Baba mairo, kuma takara yina Sameer nasiha akan yaji tsoron Allah, tasan kudi yana iya canza mutum.


Cikin kankanin lokaci aka fara gini filin Sameer, kuma yashayi wani babban shago an kara gyarashi yaxuba kaya aciki, yayi yar karamar plaza, wadda aka sa sunan Ameer Plaza, sosai Falak taji dadin abinda Sameer yayi. Dayake gini ne nasamu kudi ahannu dan da nan yakeyin sauri, har kayan da za,a sa agidan Sameer yasiya, sun ajesu agidansu, komai na more rayuwa seda suka siya. Zama suke me cike da so da kauna.

Baba mairo da Halima ma sauna zamansu lafiya, wanda ayanzu tadena kosan saudawa, abinci sukeyi me kyau, har cikin gida ake zuwa siye, almajirai sunafiddawa.

Jalila ma gab take dagama makarantar ta, hakan yasa taroki Falak data bari seta gama sannan taxo gida, Falak tace shikenan, Allah yabada sa,a.

Zarah kuwa hankalinta

Please Login or Register in order to submit comment