Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_01_*


*_MALAYSIA (SABAH)_*

..........A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani fara waige-waige a falon. Tabbas ba'a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine.
            Takun sakkowa da stairs ɗin da'aka kawata adon falon da shi ya sani maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_* a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.
         “Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fashi zuwa Nigeria ki zauna agareki, k idan ma kika ƙuleni ALLAH kin koma can da zama kenan keda ƙasar nan sai yawo”
      Sautin kukan da aka sake fashewa da shi ya sani waigawa da sauri, ƙyaƙyƙyawar budurwa black beauty mai ɗaukar hankali da sam bata kama da matar a yanayin jiki sai na kamannin jini kaɗan. A ƙiyasi na yanayin jiki kai tsaye zance bata wuce shekaru sha bakwai ba. Sai dai a mizanin hankali da sanin masu irin yanayin jikinsu wajen ɓoye shekaru zan iya karyata zuciyata. Amma kai tsaye ban san shekara nawa zan bata ba. Dan sam bata da wani tsaho, tana nan dai ƴar cif-cif ga karamin jiki ga rashin tsayi kamar wata ƴar kanwata can (😂🤣ban dai faɗi suna ba ato😜). Tabbas kyaƙyawa ce, dan duk da kukan da idanunta suka nuna alamun taci hakan bai hana bayyanarsu dara-dara ba duk da suna a cikin farin siririn gilashi. Ga gashin gira da dogon hancinta (kamar na bilyn Abdull🙄 saura wani yace ba haka ba, bansan jealous😒😜). Kai atakaice dai yarinyar masha ALLAH. Sosai hawaye ke cigaba da bin kumatun ta tamkar an bude fanfo. Matar daketa masifar ta sake zuba mata harara a kausashe tace,
          “Haɗiye min kukan nan kafin nazo na sassafa ki a wajen sakarar banza”.
     Da ƙyar ta shiga ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Sai dai hawayen sunƙi riƙuwa. Cikin rawar murya ta dubi kamilar matar da take kamani da ita a ɗan fisge, “Mamie na tuba ALLAH na daina duk abinda baƙwaso ke da Abie ”.
      “Dainawar taki ko cigaba bazai miki amfanin komaiba ai, dan zuwa Nigeria dai babu fashi tunda kin san abu mai muhimmanci ne zai kaiki. Dolene kije kiyi saves ɗinki a ƙasar haihuwarki kodan gaba zai miki amfani, dan nan ɗin da kika ɗauka ƙasar uwa da uba ta aro ce lokaci kaɗan ya rage mu barta muma ta ishemu”.
       Kuka ta sake fashewa da shi tana daddaga ƙafa. “Ni wlhy bana son Nigeria, zafi, sauro ga shegen hayaniya. Ni basai nayi saves ɗin ba dan bazan taɓa rayuwar Nigeria ba balle har na damu dayin aiki saves yaymin amfani. Please Mamie....”
      Cikin katseta Mamie taja wani tsaki. Kota kanta batabi ba ta nufi wata ƙofa a fusace tana faɗin, “Ki wuce driver ya kaiki wajen gyaran jiki dan Abie ɗinki yace da wuri zaku wuce, kin san kuma baya son wasa da lokaci”.
     Kuka ta sake barkewa da shi kai kace Abie ko Mamie ɗinne aka aiko mata sun mutu. Harga ALLAH bata son zuwa Nigeria dan tana matuƙar wahala da yanayin zafinsu. Ga shegen sauro ɗinnan na kano tamakar kasuwancinsa sukeyi. Uwa uba zaman gidan Uncles ɗinta data tsana saboda mugun halin matar Daddy, na matar ma bai cika damunta ba dan sai ka shiga sabgarta take takuraka. Tafi tsanar babban ɗansa mai shegen baƙin hali da mugunta da har ya zarta uwar tasa. Sam bata ko ƙaunar ganinsa dan basa haɗa ko hanya bare shan inuwa guda, shiyyasa a mafi yawan lokaci idan taji zai zo malaysia take guduwa wajen Aunti Mimi. Da ance kuma zai je wajen aunty Mimi ɗin itama dake aure anan ƙasar malaysia ɗin sai ta gudo ta dawo sabah. Har ya gama zamansa bata yarda su haɗu. Kai itafa a kaf rayuwarta ma bai fi sau uku ta taba ganinsa ba. Tun kuma a ganin farko taji ta tsanesa saboda tsawa da yay mata dan ta fasa glass cup a mistake a gidansu, ita kuma ta murguɗa masa baki yako kama lips ɗin ya murje har sai da sukai kumburi duk da shekarunta basu wuci goma ba a lokacin ta kasa mantawa ta kuma kasa daina jin haushinsa. Hakama haɗuwarsu ta biyu sai da yay mata mugunta, kai idan bata mantaba ma dukansu yay ita da Aysha ƙanwarsa saboda sunje wajen bikin birthday na ƙawar Ayshan ba'a sani ba. Aiko dukan nan ya shigeta dan harda zazzaɓi kasancewar tunda ta tashi da wayonta da hankalinta ba'a taɓa dukanta ba sai shi mugu.........
          Ta jima a wajen tana saƙa mai fishsheta kafin ta haura saman stairs. Cikin mintunan da basufi sha biyar ba ta fito sanye cikin wando da riga ta ɗaura jibgegiyar rigar sanyi data kai mata har gwiwa kasancewar lokacinsa ne, duk da veil data naɗo a kanta kamar yanda larabawa keyi hakan bai hanata jan hular rigar da bakinta keda gashi mai laushi har saman kanta ba. side bag dake hanunta ta saƙala cikin wuyanta sai faman tura baki take. Duk da Mamie na zaune a falon tana yanka tufa ko kallonta batai ba....
      “Mamie na shirya kuɗin to”.
Batare da Mamien ta tanka mata ba ta tura mata card ɗinta na ciran kuɗi. “Na gode ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”. Ta faɗa tana kama hanun Mamie ta sumbata tare da ɗagowa ta sumbaci kumatunta kamar yanda dai larabawa sukanyi. Mamie bata kulata ba, hakan yasa taƙi tafiya idanunta har sun cika da kwalla, dan tunda taga Mamien bata maida mata murtanin sunbar datai mata ba tasan har yanzun tana fushi da ita.
       Haka kawai murmushi ya suɓucema Mamie, ta girgiza kanta da kamo hanun tilon ƴar tata da a kullum cikin jimamin ranar da aure zai rabasu take, dan ta tabbatar hakan na gab da faruwa. A ido zaka ɗauka Anam bata da wani shekaru saboda ƙaramin jiki da ALLAH ya bata. Sai dai kuma a zahiri shekarunta ashirin da uku kenan a duniya. Itama sumbatarta tai da ɗanjan kumatunta, hakan yasa Anam yin ƴar dariyar jin daɗi ta rungume Mamien. Mamie tai murmushi.
        “To sarkin taɓara tashi kije ko ƙya dawo da wuri”.
     “Okay Mamie bye”.

      Batafi awa uku da fita ba sai gata ta dawo, ta kara wani irin ƙyau da kwarjini tabbacin taci gyara tako ina. Dan babu abinda fuskarta keyi sai shining da glowing, ga wani uban ƙamshi mai saka nutsuwar mai shaƙa. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufi ƙyaƙyƙyawan dattijon dake tsananin kama da ita dan shima black beauty ɗinne, amma kasancewar akwai jin daɗin rayuwa baka ganin komai tare da shi sai ƙwarjini da ƙyawun haiba. Ga baƙin sajen fuskarsa daya ƙara ƙawata ƙyawun nasa. Shima dai bashi da wani jiki, dan komai na Anam bashi da maraba da nashi, hakan na nufin dai kamaninta ɗaya da mahaifinta.
      Zuwa tai ta rungumesa ta gefe tana dariyar farin cikin ganinsa. Shima fuskar tasa da murmushi ya riƙo hanunta cikin nasa. “Uhhm Mamana irin wannan ƙamshi haka kamar amarya”. Fuskarta ta ɓoye a kafaɗarsa tana dariya. “Nidai Abie ba wani amarya”. Dariya kawai yayi baice komai ba. A haka Mamie ta fito daga kitchen ta samesu. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon mijin nata abin sonta da ƴar tasu tilo ɗaya a duniya. Anam ta zame veil ɗin kanta tana nunama iyayen nata kanta daya sha gyara masha ALLAH, sai sheƙi yake da ƙamshi gashi da tsaho sosai. Gaba ɗaya kamaninta irin na Abie, gashin kai da gira zuwa gashi ido ne kawai irin na Mamie, sai ko maganarsu dake kama itama.
    Sosai suka shiga yaba ƙyawun da gyaran nata yayi, cikin tsokana Abie ke faɗin, “Mamana kin zama kamar wata amarya da gaske, kodai kawai idan munje na aurar dake ma?”.
    Idanu tai mugun zarowa, sai kuma ta kwaɓe fuska har hawaye na cikon mata ido. Lips ɗinta sai rawa suke tama rasa mizatace. Dariya Mamie da Abie suka shiga yimata, hakan yasata tashi da gudu ta haura sama. “Kin gani kin kunnata”.
     “Na kunnata ko ka kunna abarka”.
Cewar Mamie tana murmushi. “To aini abin na damuna, idan na tuna wataran aure zatai ta barmu hankalina na matuƙar tashi, gashi shekaru sunyi nisa, kamata yay ma data gama saves ɗin nan kawai a wuce wajen Humairah”.
     Ajiyar zuciya mai nauyi Mamie ta sauke. Murya a raunane tace, “Hakane ya dace, sai dai kuma a kullum cikin korar samarin take ai taƙi bama kowa dama anan ɗin balle Nigeria. A kullum kallon kanta take a yarinya”.
     “To ai yarinyarce, duka yaushe kika haifamin ita. Ni badan auren ya zama doleba dana bar abuta naita kallo kawai”.
      Sosai Mamie ke dariya, cikin riƙe baki tace, “Lallai ashe mu iyayenmu basa sammu kenan da aka ɗakko aka baku. Lallai ashe lokacin auren munada kallo kenan dan za'a sha show rabuwar ƴa da uba”.
     “A zakusha kam. Dan mijin nan zai sha gargaɗi, shiyyasa nafi son ma ta auri ɗan Nigeria dan ƙasar nan ta isheni haka”.
        “To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Ya kawo nagari”.
  Da amin Abie ya amsa cikin jimami da damuwar rabuwa da tilon ƴarsa.

*_Washe gari_* kamar yanda Mamie ta faɗa hakance ta kasance. Dan kuwa dai Abie da Anam sun wuce ƙasar haihuwarsu Nigeria. Tasha kukan rabuwa da Mamie duk da tasan bazatai shekaran Mamie bataje ba tunda ita sunce bazata zo ba har saita kammala. A jirgi barci ta dinga ramuwa wanda ta gagara yi a daren jiya saboda alhinin yin nisa da iyayenta datai matuƙar shaƙuwa da su take mu'amula da su tamkar ƙawayenta. Sune abokan shawararta, sune abokan kukanta, sune abokan dariyarta, sune abokan rayuwarta. Bata da kamarsu dan su tafi sani fiye da kowa a duniya.

*_04: 25pm_* jirginsu ya sauka ƙasar Nigeria Aminu kano international airport, a gajiye Anam take matuƙa duk da barcin da tasha, sai faman langarema Abie take, shiko lallaɓa abarsa yake dan yasan yanayinta bata son wahala sam. Abu ƙalilan ke galabaitar da ita tai laushi tiɓis. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali lokacin da suke fitowa idonsa ya sauka akan ƴan uwansa abin ƙaunarsa. Suma da alama idonsa na kansa, dan tuni suka nufosa fuskarsu ɗauke da murmushi. Abie yay azamar nufarsu shima suka rungume juna suna maijin farin cikin haɗuwa.
       Sosai Anam take dubansu da murmushi, tana ƙaunar uncles ɗin ta kam, dan suma suna ƙaunarta. Matar big Uncle ɗin nata da ɗansa babba ne dai sai a slow, amma sauran matan small Uncle da yaransu duk bata da matsala da su musamman Aysha aminiya.
      “Oh my Mah-mah welcome”. Uncle ɗin da suke kira da Daddy ya faɗa lokacin da suke sakin juna da Abie ya buɗe mata hannayensa alamar tazo garesa. Hanun trolley ɗinta ta sake da nufarsa a kasalance fuskarta ɗauke da murmushi ta matsa ya ɗan rungumeta ta gefe.
        Small Uncle ɗinta da suke kira da Abbah yay murmushi tare da shafa kanta yana faɗin, “Ayya Mamana kina nan dai a ƴar ficikar ki ba tsaho ba girman jiki ga ragwantaka”. Fuskarta ta ɓoye jikin Daddy tana dariya da faɗin, “Lah Abbah na ƙara girma fa, kuma yanzu bana ragwanci”.
     Daga Daddy har Abba da Abie dariya sukeyi, Daddy yace, “Nima dai ban gani ba, jibeki a galabaice a ƴar wannan tafiyar ta awoyi, shekara huɗu kenan ban ganki ba amma kina nan yanda kike fa”.
     Sosai ta shagwabe masa ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta tana ƙyafta idanunta manya ta cikin glass ɗin da alamu suka nuna na ƙarin gani ne.

      Ko amota ma Abie da Daddy da abbah dake a baya zaune tuni sun balle hira, itako kallon hanya kawai take dan tana gaba a gefen driver. Jikinta liƙis yake da gajiya, ga wani irin zafi dake shigar ƙofofin gashinta kamar ta fasa kuka dan bata ƙaunar zafi, shiyyasa duk sanda zasu zo Nigeria sai tai kuka bana wasa ba, idan sunzo kuma sam zaka sameta babu sakewa inhar lokacin zafi ne. Shiyyasa mafi yawan lokuta Abie yafi son shirya musu zuwa Nigeria a lokacin sanyi ko damuna saboda ita.
        Sun sami tarba ta mutuntawa daga matan gidan guda biyu, wato aunty amarya da mom. Amma babu Big mom balle alamarta. Hakan ba sabon abu bane, shiyyasa daga Abie har Daddy da Abbah basu nuna sun damu ba. Yaran gidan dai duk sun wuce islamiyya, sai ma'aikatan ne keta shigowa suna mika gaisuwarsu domin duk wanda ya kwana ya tashi a gidan yasan muhimmancin Abie ga Daddy da abbah dama jama'ar gidan gaba ɗaya. Sai da suka kwashe kusan mintuna arba'in sannan Mommy ta shigo tana wani ciccin magani. Babu wanda yabi takanta harta samu waje ta zauna tana gaida Abie. Cikin sakin fuska ya amsa mata tamkar sauran ƴan uwanta, ya kuma tambayeta yara.
     Duk wannan bidiri Anam na kwance a kujera lamo tana kallon kowa a galabaice, dan ma ta samu sauƙin zafin tunda suka shigo sanyin ac'n falon Daddy na ratsata. Gaishe da Mommy tayi itama a ɗan shagwaɓe, bata wani amsa mata da ƙyau ba. Sai taji duk babu daɗi har fuskarta ta nuna hakan dan ita yarinyace mai son kulawa. Hakan yasa Mom tai murmushi da shafa kanta cike da kulawa take faɗin, “Mamanmu har yanzu dai ke raguwa ce”.
       A langabe Anam take dubanta har idanunta na nuna alamar tara kwalla. Murya a raunane tace, “Mom na gajine ga zafi”.
      Dariya duk aka sanya a falon, aunty amarya cikin dariya tace, “Babbar magana. A haka za'ai saves ɗin kuma.....?”.
      “Kema dai ƙya faɗa Hafsatu. Dan wannan ƴar taku ragwantarta harta wuce tunani, ina tausayama mijin da zaku mannawa”.
           Mom da aunty Amarya suka shiga kare Anam da faɗin koma waye zasu iya dashi ai. Mommy kam sai faman taɓe baki take da yatsine fuska tamkar bata a falon ma....

         A duk sanda suke a ƙasar gidansu dake jikin nasu Daddy ne masaukinsu, wannan karon kuma babu Mamie sai Daddy yace bai yarda su sauka anan ba duk da Abie ya nuna shi dai zai shiga can ɗin dan bazai so takura iyalan ƴan uwan nasa ba duk da kanine shi a garessu. Babu yanda su Daddy suka iya suka haƙura kawai suka barsa akan zuwa anjima sai ya shiga can ɗin yanzu masu aiki zasuje su gyara. Hakan kuwa akayi, masu aiki sukaje suka tsaftace ko'ina da taimakon aunty Amarya, ita kuma  ta koma sashen Mom ɗin kodan kawarta Aysha da basu san da zuwanta ba dan su Daddy sun ɓoyema kowa. Duk da jin zafinta bata wanka da ruwan sanyi, dan haka ta haɗa mai zafi sosai tai wankan a bedroom ɗin Mom kafin su Aysha su dawo islamiyya, tana fitowa kobi takan abincin da Mom ta ajiye mata bataiba ta ƙure ac ta kwanta sai barci. Yin barcin nata babu jimawa sai ga yaran gidan an dawo dasu daga islamiyya cikin katuwar bus ɗinsu ta zuwa makaranta. Kowannensu sashen uwarsa ya nufa, mazan kuma suka nufi sashensu na samari duk da kuwa babu wanda ya haura ashirin a cikinsu.
     Basu san da zuwan Anam gidan ba sai bayan sallar magrib, samarin suka fara cin karo da Abie a massallaci, ana idar da sallar isha'i sai gasu da gudu sashen Mom. Sune suka fargar da ƴammtan gidan, aiko cikin ƙanƙanin lokaci suka hargitse ɗakin Mom da hayaniyarsu wadda ta tashi Anam ɗin dake tsaka da jin daɗin barci dan bata salla tana fashi. Tsawa Mom ta musu dan tana salla amma suke ihun nan, tsitt bedroom ɗin yayi suna sauraren faɗan da take musu na wannan shirmen nasu. Sai da ta gama suka bata haƙuri tare da janye ra'ayin ƴar uwarsu suka bar ɗakin.
         Kai kawai ta ɗan girgiza fuskarta da murmushi, dolene yanda suke murna da ganin ƴar uwar tasu ya birgeka. Ita kaɗaice ware a cikinsu amma suna nuna mata tsananin so kamar yanda suma kawunansu yake haɗe duk da dai wataran Mommy kan birkita kan yaran idan tanajin fitinarta, musamman idan ta takalesu basu kulataba sai tabi duk hanyar son zuciya ta cusama yaranta ƙananun magana a zuciya da zakaga sun janye jikinsu da ƴan uwansu har wataran ma kaga an taɓah faɗa, a wasu lokutan faɗan nasu nayin nauyi, amma wani sa'in sukan fahimci juna da wuri musamman idan wanda suke shakka a gidan yana ƙasar dan shi babu ruwansa ubansu yakeci gwargwadon iko. Duk da mutum ne shi mai haƙuri da rashin son yawan magana, sam baya son raini da damuwa. Sannan duk da halin uwarsa bazaka taɓa ganinsa ya nuna banbanci akan yaran gidan ba, matan kuma yana girmama kowa yanda ya kamata duk ɗa nagari yayi........✍


KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
[10/2, 12:27 PM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_02_*


.........Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu.
      Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a

2 Comments On BABU SO
avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

Please Login or Register in order to submit comment