Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka gani face mu tambaye ku.”

Yarinya ta ce, “Wallahi kun cuce mu, ya ku bakimmu, gayar cutuwa, da kuka gabato mu, muka gabatar muku sharadi, kada ku yi magana a kan abin da babu ruwanku, ku ka amince, muka sa ku gidammu, muka ciyar da ku, muka shayar da ku, ashe ku ba abin amincewa ba ne. Ba ku daga cikin nagartattun mutane.”

Yayin nan ta zare damuttsanta, ta bugi kasa sau uku, ta ce, “Ku gaggauto!”

Daga nan sai ga wata kofa, daga kasa, ta bude, bayi bakwai, bakake, karfafa, suka fito da takubba, zararru ga hannuwansu. Ta ce “Ku daure wadan nan masu yawan magana, ku daure junansu ga juna.” Suka gaggauta abin da aka umurce su, suka ce da ita, “Ya abar bautarmu, ki ba mu izini mu sare kawunansu daga jikinsu.”

Ta ce, “Ku jinkirta kadan har in tambaye su ga halin kasancewarsu kafin ku kashesu.”

Dan dako ya ce, “Don Allah, ya shugabata, kada ki kashe ni da alhakin wanina, cewa dukkansu sun yi kuskure, sun shiga cikin laifi, face ni, Wallahi tilastani suka yi akan in tambaye ku labarinku. Wallahi darenmu ya yi dadi, ba domin shigowar masu ido dayan nan ba, da ba mu samu laifi ba, ko sun shiga alkarya rayayyiya, wallahi sai sun rusata domin shu’umcinsu.”

Ko da yarinya ta ji zancen Dan dako, sai ta yi dariya, fushinta ya yaye. Ta fuskanta zuwa ga daurarrin mutanen nan, ta ce, “Ku labarta mini labarinku daya bayan daya, ran dayanku ba zai wanzu ba face kowanne ya fanshi kansa da labarinsa.”

Halifa ya dubi Ja’afaru ya ce, “Kaitonka ya Ja’afaru, ka sanar da ita ko mu su waye tun kafin ta kashe mu.” Ja’afaru ya ce, “Haka bai kamata gare mu ba.”

Yayin nan yarinya, shugabar yam mata, ta fuskanta zuwa ga samari uku, ta ce, “Yalla ku yan uwa ne da wadan nan mutane?” Su ka ce, “A’a, wallahi mu talakawa ne.” Ta ce da dayansu, “Yalla kai an haifeka da ido daya ne?” Ya ce, “A’a, sai dai al’amari mai ban al’ajabi ya gudana a gare ni har na rasa idaniyata guda. Hikayar wannan al’amari, da za a rubuta shi da tsinin allura bisa ga gefen gani, da ta kasance abar lura ga masu hankali.”

Ta tambayi saurayi na biyu da na uku, suka fada mata tamkar yadda saurayi na farko ya fada ma ta. Kuma su ka ce, ko wanne dayanmu, garinsu dabam, cewa al’amarinmu sabo ne, zancenmu mai ban al’ajabi ne.

Yarinya ta waiwaya zuwa garesu, ta ce, “Kowanne dayanku shi hakaita hikaya tasa har ya zuwa ga wannan bigere namu, sannan shi tube kansa daga cikin wannan igiya da aka daure shi da ita, ya yi tafiyarsa. Na farkon wanda ya fara zuwa garemu, Dan dako.”

Dan dako ya ce, “Ya shugabata, hikayata dai ita ce, ni namji ne, mai dakon kaya, ina tsaye a cikin rumfar kasuwa, sai wannan Jekadiya ta kira ni domin in daukar ma ta kaya. Ta labto mini kayan sayayyar da ta yi, ta ce, na biyo bayanta, na kawo ma ta gida. Ta zo da ni nan, abin da ya gudana gare ni tare da ku ya gudana. Wannan shine hikayata, ya shugabata. Wassalam.”

Ta ce da shi, “Ka tube kanka da ranka. Ku kwanceshi ya tafi.” Bayan an kwance shi, sai ya ce, “Wallahi ba ni tafiya har sai na ji hikayoyin samarin nan masu ido daya-daya, da wadan nan sauran mutanen.”

Sai saurayi na farko, mai ido daya, ya gabata zuwa ga yarinya, ya fara labarta hikayarsa kamar haka:

Mu hadu a na 3 domin jin labaran nasu yadda Zata kasance003. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Labarin Saurayi Na Farko Mai Ido Daya (1)

Saurayi na farko, mai ido daya, ya gabata zuwa gaban yarinya, shugabar yam mata, ya fara labarta hikayarsa kamar haka:

Ya ce, “Ya shugabata, ki sani, ubana ya kasance sarki ne, ya na da dan uwa da ya ke saurata a wani birni dabam. Aka yi gamo, uwata ta haifeni, ranar da aka haife ni kuma ranar dan uwan mahaifina, watau bappana, ya sami karuwar da namiji, kuma a ranar ce ya kai shekara sittin a duniya.

Bayan na girma, sai ya kasance daga lokaci zuwa lokaci, na kan ziyarci bappana a birninsa da ya ke sarauta, mu hadu da ‘ya ‘yansa, mu yi ta wasa tare. Wata rana na kai masa ziyara, a lokacin ya kasance na girma sosai, na zama mutum, na samu bappana ya tafi farauta, sai dansa na samu. Ya karbe ni da murna, ya yi mini karimci, gayar karimci, ya yanka mini kaji da tumaki, ya tace mini abinsha mai kyau. Muka zauna muna ci muna sha tare da shi.

Yayin da sha ya haumu, ni da dan bappana, mun fara fita daga cikin hankalinmu, sai ya ce da ni, “Ya dan uwana, ina da bukata tare da kai, mai girma, ina son kada ka saba mini ga abin da na yi nufin in aikata tare da kai.” Na ce da shi, “So da girmamawa, ni mai biyayya ne a gare ka.”

Ya daure ni da manya manyan rantsuwa. Ya tashi, ya faku kadan daga gare ni. Ya komo da wata kyakykyawar budurwa, adantacciya a bayansa, ta na bin sa da kayan ado a gare ta, wadanda suke dai dai da diyan sarakuna.

Ya waiwaya zuwa gare ni, ya ce, “Ka riki wannan yarinya, ka tafi da ita zuwa ga unguwa kaza!” Ya kwatanta mini unguwar, na gane. Ya ce, “Ka shiga da ita gida kaza, ka jiraye ni a nan, zan same ku.” Ban yi gardama ba, kuma ba ni da ikon in tambaye sa dalili, saboda rantsar da ni da ya yi.

Na riki budurwan nan, na wuce gaba tana biye da ni, har muka isa wurin da dan bappana ya misalta mini, muka shiga gidan da ya ce, ni da ita, muka zauna muna jiran isowarsa. Can jimawa kadan, sai ga shi ya shigo, hannunsa daya na rike da wata tasa da ruwa a cikinta, a daya hannun yana rike da wata jaka, akwai garin magani da magirbi a cikin jakar.

Yana zuwa, sai ya ajiye tasar, ya bude jakar ya dauko magirbi, ya tafi bisa ga kan wani abu, mai kamar kabari, ya sa magirbi ya tone shi, ya fitar da duwatsu daga cikin kasar, yayin nan ya yi tono mai zurfi daga cikin kasar, har ya bude rufi, gwargwadon karamar kofa. Tsani ya bayyana daga karkashin rufin, yayin nan ya waiwaya zuwa ga matar da ishara, ya ce da ita, “To, maza! Me ki ke jira?” Matar ta zo, ta tattaka matakalar tsanin ta yi kasa.

Sannan ya waiwaya zuwa gare ni, ya ce da ni, “Ya dan uwana, ka cika alheri, ka cika alkawari, idan na sauka ga wannan wuri, ka maida rufin, ka maida kasa bisa gare shi tamkar yadda muka isko shi. Wannan ruwan da ke cikin tasa da wannan garin maganin da ke cikin jaka, ka cuda garin nan, ka like kabarin ta tsakanin duwatsun har yadda wani ba ya iya shaida an bude shi, Ni zan yi wani aiki a cikin wannan wuri, ba ni son kowa ya san inda na ke, sai Allah. Wannan shi ne bukatata a gare ka. Ka zamo mai cika alkawari.”

Yayin nan ya ce, “Sannunka da rashina, ya dan uwana.” Sannan ya tattaka tsani ya sauka kasa. Yayin da ya faku ga idona, na tashi na maida rufi, na maida kasa, na mayar da kabarin nan tamkar yadda shi ke da fari, har wani ba ya iya gane an tona shi.

Na komo gidan bappana. Na kasa kwana, saboda tunani, ga wannan dare. Yayin da gari ya waye, na tuna daren jiya, da abinda ya gudana a cikinsa na daga tsakanina da dan bappana da matar nan. Na yi nadama ga abin da na aikata tare da shi, yayin da nadama ba ta da amfani. Yayin nan na fita zuwa ga gidan nan da na bizne shi, na yi neman wurin da kabarin nan yake, na kasa ganewa.

Na komo gida, na kasance ba ni ci, ba ni sha, raina ya shagala da dan bappana domin rashin sanin halin da ya ke ciki. Na yi bakin ciki, bakin ciki mai tsanani, na kwana darena ina mai bakin ciki ya zuwa ga asbahi. Na kara komawa gidan nan karo na biyu, na kara dubawa ko’ina cikin gidan nan, amma kabarin nan ya yi kasa ko bisa, ban gane shi ba. Ban gushe ba ina bincikawa har dare ya gabato, ban shiryu da inda kabarin ya ke ba. Na komo gida, na yi nadamar amsawa dan bappana wannan bukata tasa.

Na hakura, kuma gashi har yanzu mahaifinsa bai dawo daga farautar da suka tafi ba. Na shirya na nufi garinmu, wurin ubana. Bayan na yi kusa da garinmu, na fara shiga karkara tasa, sai ga wasu mutane sun nufo ni, suka kama ni suka daure, ina al’ajabi, gayar al’ajabi, cewa ni dan sarkin garin ne, su ko, da suka daure ni, bayin ubana ne da yaransa. Tsoro ya kama ni, tsoro mai yawa, na ce a cikin raina, ya Allah, me ya gudana ga ubana?

Ya zamana ina mai tambayar wadan nan mutane bisa ga dalilin daure ni da suka yi, ba su mayar mini da jawabi ba. Bayan wani lokaci, wani daga cikinsu, wanda ya kasance bawana ne, ya ce da ni, ka sani ubanka, zamani ya warware masa, askar sun ha’ince shi, Waziri ya kashe shi, ya aiko mu nan domin jiran zuwanka, mu kama ka mu kai ka gaba gare shi.

Saurayi na farko mai ido daya, ya ci gaba da labartawa yarinya, shugabar yam mata, hikayarsa da yadda ya rasa idonsa daya, ya ci gaba da cewa:

“Bayin ubana da suka daure ni, suka ci gaba da cewa, waziri ne ya turo mu domin mu kama ka mu daure, mu kai ka a gabansa cewa kai kana daurarre.

Yayin da na ji haka game da ubana, hankalina ya kada. Yayin nan suka kawo ni gaba ga wazirin nan da ya kashe ubana. Dama akwai adawa dadaddiya tsakanina da waziri. Ya kasance wata rana ne, tun ina yaro karami, na ga wani tsuntsu a kan bishiyar gidan waziri, sai na sa bakan danko na harbo shi, ashe kuma dutsen da na yi harbi da shi, ya sauka bisa ga idaniyar waziri, ta hagu, wanda ya yi sanadiyyar tsiyayewar idaniyar. Kasancewar ubana ne sarki, babu abin da waziri zai iya yi face hakuri. Wannan shi ne sababin adawata da waziri.

Yayin da aka kawo ni gaba ga waziri, ina daure cikin igiya, ya yi umurni da a sare wuyana. Na ce, “Yalla ka kashe ni ba da alhakina ba?” Ya ce, “Wane laifi ya fi girma daga wannan?” ya yi ishara zuwa ga idaniyarasa cirarriya. Na ce da shi, “Na aikata wannan bisa ga kuskure ne.” Sai shi kuma ya ce, “To ni, na aikata maka shi da gangan.” Ya ce a kawo ni kusa da shi. Aka kawo ni gaba gare shi, ya mika farcensa, ya kwakule mini idaniyata ta hagu. Na zama mai ido daya a cikin wannan lokaci, tamkar da kuke ganina, ya shugabata.”

Saurayi ya ci gaba da labarinsa, ya ce: “Yayin nan aka daureni, aka sa ni cikin sanduki. Waziri ya ce ma dogari, fita da wannan ka shayar da takobinka jininsa! Rike shi, ka fita da shi bayan birni ka kashe shi, ka bar ma ungulai su ci shi.

Dogari ya tafi da ni, har ya fita bayan birni, ya fisshe ni daga sanduki, ina mai daurarrun hannuwa, mai dabaibayayyun kafafu. Yayi nufin shi rufe idanuna, shi kashe ni, na yi kuka, na waka wadansu baitoci masu ban tausayi.

Yayin da dogari ya ji wannan waka tawa, ya ce, “Ya shugabana yaya zan yi? Ni bawa ne umurtacce. Amma ba zan kasheka ba, ka rabanta da ranka, kada ka komo zuwa ga wannan kasa, ka hallaka, ka hallakani tare da kai. Yi sauri ka fita daga cikin wannan kasa.”

Da na ji zancensa, na yi godiya, na sumbanci hannuwansa, ban gasgata kubutata ba har sai da na ga na ba wa garinmu tazara mai yawa. Na nufi garin da bappana yake mulki. Na ci gaba da tafiya har na iso birnin bappana, na same shi sun dawo daga farautar da suka tafi. Na sanassheshi da abin da ya gudana ga ubana, da abin da ya gudana a gare ni na rasa idaniyata.

Ya yi kuka, kuka mai yawa, ya ce, “Ka dada mini bakin ciki bisa ga bakin cikina da bacin zuciya bisa ga bacin zuciyata, cewa dan uwanka mun rasa shi tsawon kwanaki, ba mu san abin da ya gudana gare shi ba, wani bai labarta mana da labarinsa ba, tun da muka dawo daga farauta ba mu same shi ba, kuma babu labarinsa.”

Bappana ya ce, “Bai kamata mu yi kurum kan wannan al’amari na batan dana ba, ya kamata mu nemo duk inda ya ke.” Ko da naji haka, sai na sanar da shi abin da ya gudana duka akan dansa da budurwar da na rufe su tare. Bappana ya yi farin ciki da samun labarin inda dansa ya ke. Ya ce da ni, “Ya dana, mu je ka nuna mini wurin da ka bisne shi.” Na ce, “Ka sani cewa, na kokkoma wurin da yawa, amma na kasa gane inda kabarin yake.”

Yayin nan muka tashi ni da Bappana muka tafi zuwa gidan, ko Allah ya sa mu shiryu da inda kabarin nan yake.

Sai gobe Zamu Cigaba Ana 4004. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Labarin Saurayi Na Farko Mai Ido Daya (2)

Saurayi na farko, mai ido daya, ya ci gaba da ba da labarinsa da cewa: “Lokacin da na gaya wa bappana abin da ya faru da dansa, sai ya ce in kai shi gidan da na bisne dan nasa tare da matar nan, ko Allah ya datar da mu da gane bigiren da na rufe su.

Muka tashi muka je gidan. Muna zuwa, da dubawa haka, sai na shaida wurin da kabarin nan yake, muka yi farin ciki mai yawa.

Muka samu magirbi, muka tone kasar, sai ga rufi ya bayyana, muka cire shi sai ga tsani ya sauka kasan ramin. Na tattaka tsani na sauka kasa, gwargwadon tsawon ramin nan zira’i hamsin, bappana ya biyo ni daga baya. Yayin da muka riski karshen tsani, muka sauka kasa, sai ga wani hayaki ya bayyana bisa garemu, sai na ji bappana ya fadi kalmar nan da mafadinta ba shi tsorata, ita ce, Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un!

Muka ci gaba da tafiya, sai ga mu a cikin daki cikakke da abinci da kayan marmari, da ruwan sha. Mun gani a cikin dakin babban gado mai labule, muka samu dan bappana kwance a kan gado tare da matar nan da suka shiga da ita cikin wannan rami, sun zama bakin gawayi , suna rungume da juna, ka ce su an jefa su cikin rijiyar wuta.

Yayin da mahaifinsa ya ga haka, fuska tasa ta sake, ya ce, “Haka ya kamata da kai, ya kai daddauda, wannan azabar duniya ce, saura azabar lahira, ita ce mafi tsanani, mafi wanzuwa.”

Yayin nan saurayi mai ido daya, ya ce wa yarinya da sauran jama’ar da ke sauraren labarinsa, “Kuna jin zancena! Yayin nan bappana ya shuri dansa da takalmi. Na ce da shi, abin da suke ciki bai ishe ka ba har sai ka shure shi da takalmi?”

Ya ce, “Ya dan dan uwana, wannan da nawa, ya kasance a lokacin kurciyarsa mai tsananin son yar uwarsa, wannan da suke kwance tare, na hane shi gare ta, ina cewa a cikin raina don su yara ne, yayin da suka girma barna za ta auku a tsakaninsu. Na tsaya bisa ga haka. Na tsawace su, tsawa mai tsanani, a kan su rabu da son juna don babu aure a tsakaninsu. Na tsare shi daga gare ta, na tsare ta daga gare shi. Ita kuma ta kasance ta na sonsa, so mai tsanani. Shaidan ya tabbata tsakaninsu. Shi ya yi wannan gidan karkashin kasa a boye, ya tara abinci a ciki, tamkar da ka gani, duk lokacin da ya ga na shagala da wani abu, ko na fita zuwa ga farauta, sai ya zo shi da wannan yar uwa tasa, su boye suna aikata abin da ransu ya kawata musu.

Yayin nan ya yi kuka, muka yi kuka tare da shi. Ya ce da ni, “Kai ne da na maimakonsa!” Yayin nan na yi tunani kadan na duniya da zantuttukanta da al’amurranta, masu faruwa, na tuna Waziri da yadda ya kashe ubana, ya riki matsayinsa, ya cire mini idaniya da gangan, da wannan dan bappah nawa, da abin da ya same shi na konewa shi da yar uwarsa.

Sannan muka hawo tsani, muka mai da rufi, muka mayar da kasa, muka aikata kabari tamkar yadda shi ke, muka komo zuwa ga gidanmu.

Tun ba mu gama zaunawa ba, sai muka ji bugun tambari, da ganguna da algaitu, muka hangi masu da takubban mayaka su na walkiya a cikin rana. Duniya ta cika da kura, karar kofatan dawaki da kukansu ya gauraye ko’ina, hankulanmu su ka kada, ba mu da labari.

Sarki ya tambayi labari, su waye haka? Aka ce da shi, Wazirin dan uwanka ne, ya tara askar da runduna don shi abka maka da yaki, ya ci birninka ba tare da kun shirya ba. Domin shi yana jin tsoron ka sami labarin ya kashe dan uwanka, ka abka masa da yaki.

Koda na ji haka, sai na ji tsoro, na ce a cikin raina, idan na sake na sake fadawa hannun Waziri ba shakka zai halaka ni. Bakin ciki ya rufe ni, na tuna abubuwan da suka faru, na daga musibu da suka abka wa mahaifina, da dan bappana, na rasa yadda zan yi.

Na tabbata idan mutanen Waziri suka gan ni, za su shaida ni, su kama ni su kai ni gabansa, ba ni samun daya da zan tsira daga hannunsa. Sai na aske gemuna, na sake tufafina, na fice daga birnin na nufo wannan birni.

Wassalam, wannan shi ne labarina. Yalla ko wani ya kai ni ga Sarkin Musulmi Halifa, in labarta masa da wannan hikaya tawa, da abin da ya gudana gare ni. Na shigo wannan birni a cikin wannan dare, na tsaya, ina madimauci, ban san inda zan nufa ba, sai ga wannan mai ido daya yana tsaye. Na yi masa sallama, na ce da shi ni bako ne! Ya ce da ni, ni ma bako ne! Mu na cikin haka sai ga wannan abokin namu, na uku ya zo mana, ya yi sallama a garemu, ya ce ni bako ne! Mu ka ce da shi mu ma baki ne.

Muna tafiya duhu ya yi mana, kaddara ta koro mu zuwa nan gidanku, muka nemi masauki, kuka saukar da mu, har abin da ya faru yanzu ya faru. Wannan shi ne dalilin rasa idaniyata ta hagu, da aske gemuna da na yi.”

Suka yi mamakin zancensa, Halifa ya kaikaici yan mata ya ce da Ja’afaru, “Da dai ban taba jin tamkar abin da ya gudana ga wannan saurayi ba.” Yarinya Shugabar yam mata ta ce, “Tube kanka daga igiya, ka kubutad da ranka. Maza ka kama tafarkinka.” Ya ce da ita “Ba ni tafiya, sai na ji labarin wadan nan sauran mutane.”

Yayin nan saurayi na biyu, mai ido daya, ya gabata gaban yam mata, ya yi gaisuwa ga shugabarsu, ya ce “Ni ba a haife ni da ido daya ba, akwai abin mamaki mai yawa ga hikayata wanda ya fi na wannan aboki nawa da ya gama bayar da labarinsa.” Ya fara bayar da labarinsa kamar haka:

Sai da safe zamu cigaba Na 5005. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (1)

Saurayi na biyu mai ido daya ya gabata, ya yi gaisuwa ga yarinya shugabar yam mata sannan ya ce, “Ya shugabata, ni ba a haifeni da ido daya ba, akwai abin mamaki mai yawa ga labarina. Da za a rubuta shi da tsinin allura, a duba da kaifin ido, da ya zama abin lura ga masu hankali.

Da farko dai ni Dan Sarki ne jikan Sarki. Na karanta Alkur’ani bisa ga ruwaya bakwai, na karanta littattafai ga masu su, sannan wakoki, na yi kokari a cikin dukkan saninsu, har na tserewa mutanen zamanina, na wuce su.

Sunana ya watsu, labarina ya isa ga dukkan Sarakuna na yankinmu. Sarkin Hindu ya ji labarina, ya aika wa ubana cewa yana son in tafi kasarsa in kai masa ziyara, yalla ko sa karu da wani yanki na daga tarin ilimina.

Ubana ya amince da wannan bukata ta Sarkin Hindu, ya shirya mana jirage shida cike da guzuri. Muka kama hanya cikin bahar har tsawon wata shida cikakku sannan muka isa bisa tudu.

Muka sauke kayanmu daga cikin jirgi, muka labtawa rakuma, muka tafi kadan-kadan. Daga nan, sai muka hangi kura ta daukaka, ta tokare sararin samaniya. Da aka jima, sa’a guda, sai ga mahaya sittin sun bayyana a gabanmu, duka zakokin fada ne. Muka lura muka ishe su duka Larabawa ne, mafasa tafarki.

Yayin da suka iso wurinmu, ga mu, mu jama’a kadan, muna dauke da kaya niki-niki, sai suka abka mana. Muka yi musu ishara da cewa, mu manzanni ne zuwa ga Sarkin Hindu, kada ku cuce mu. Suka ce, mu ba mu kasance karkashin hukuncinsa ba, ballantana mu ji tsoronsa. Suka kashe wasu daga cikinmu, mu kuma saura muka yi ta kammu, kowa ya kama gabansa, muka bar wa ‘yan fashi kayan.

Na kasance ban san inda zan nufa ba, da ina Dan sarki madaukaki amma yanzu cikin sa’a guda na komo wulakantacce. Na tafi har na iso kan wani dutse, na shiga cikin wani kogo na kwanta na huta. Da rana ta fito, na ci gaba da tafiya har na iso wani Birni rayayye, cikakke da alheri, lokacin tsananin dari ne, sai ka ce damina domin ni’ima tasa da kamshinsa, na yi farin ciki da isowata wannan Birni.

Saboda tsananin gajiya da tafiya da bakin cikin abin da ya same ni da kurar hanya, duka suka hadu suka canja mini kama, idan an gan ni sai a dauka wani miskini ne. Bayan na iso Birnin, ban san inda zan nufa ba, sai na karkata zuwa ga gefensa, na ga madinki cikin rumfa, na yi sallama gare shi, ya mayad da sallama gare ni. Ya yi mini shimfida. Ya tambaye ni labarina. Na labarta masa duka abin da ya faru gare mu na daga mafasa.

Bayan ya ji labarina, ya tausaya mini a kan abin da ya faru, sannan ya ce da ni, samari kada ka bayyana wa kowa wannan labari naka, domin ina ji maka tsoro ya kai ga kunnen Sarkin wannan Birni, domin kuwa shi ne babban abokin gabar mahaifinka, akwai wata fansa da ya ke so ya dauka ga mahaifinka, da kasarku da wannan kasa ba a ga-maciji da juna.

Madinki ya halarta mini abinci da abin sha, muka ci tare da shi, muka zauna muna zance har dare ya yi. Ya gyara mini wani wuri kusa da turakarsa, ya kawo mini abin da nake bukata duka na daga shimfida da abin rufa. Na zauna tare da shi kwana uku, yayin nan ya ce da ni, ba ka san wani aiki da za ka fara yi ba a matsayin sana’a domin samun abinci? Na ce masa, ni almajiri ne, bayan karatu ban san wata sana’a ba.

Ya ce, aikinka a cikin Birninmu baya da martaba, babu wanda ya san rubutu haka nan karatu, kowa dukiya kawai ya sani. Amma zan gaya maka wata sana’a idan za ka iya yi. Na ce, wace sana’a ce? Ya ce, ka tashi, ka riki gatari da igiya, ka tafi itace cikin daji, kaga da wannan sana’a, mutane da yawa sun yi arziki a cikin wannan Birni.

Na amince da wannan zabi na madinki. Ya hada ni da wasu masu yin wannan sana’a, sannan ya yi mini wasicci da kada in gaya wa kowa labarina ko asalina. Na fita tare da su, na yiwo itace, na komo da kaya bisa ga kaina, na sayar da su rabin dinari, na ci rabi na ajiye rabi. Na dauwama bisa ga wannan hali har tsawon shekara guda.

Wata rana na fita zuwa yin itace, na zurfafa cikin daji ban sani ba, sai na samu wata matacciyar itaciya da itace da yawa a kanta. Na shiga karkashinta, na ga tamkar shuri mai zuma, na tona gefensa na gusad da kasar

Please Login or Register in order to submit comment