Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba da tafiya har rana ta yi zafi. Na kwanta a karkashin wata itaciya domin in dan sarara, sai barci ya dauke ni.

Yayin da na farka daga barci, sai na ga wata kyakkyawar yarinya tana yi mini tausa ga kafafuna. Na yi zumbur na tashi zaune, na ce wace ce ke? Yarinya ta ce, haba ya shugabata, amma kin cika mantuwa, yanzu har kin manta ni? Ke ce wadda kika aikata mini alheri, wanda ba zan taba mantawa da shi ba har tsawon rayuwata. Ke ce kika kashe makiyina wanda yayi niyyar ya halaka ni, ba domin kin cece ni daga gare shi ba, da tuni ya kashe ni. Ni ce macijin nan da kika taimaka dazu.

Ni aljana ce, macijin nan ma aljani ne, shi makiyina ne, babu wanda ya kubutar da ni daga gare shi, face ke, hatta aljanu yan uwanmu tsoronsa suke ji. Yayin da kika kubutar da ni daga gare shi, na kada cikin iska, na tafi zuwa ga jirgin nan da yan uwanki suka jefar da ke daga cikinsa. Na kwashe dukan abin da ke ciki na dukiya, na kai miki shi gidanki, na dulmiyar da jirgin. Yan uwanki kuwa, na sihirce su karnuka, babbakun karnuka.

Ni, na san dukan abinda ya gudana tsakaninki da su, amma saurayinki ya halaka cikin ruwa, na yi nema ko gawarsa ban gani ba, ban san abinda Allah ya nufa da shi ba.

Bayan aljana ta gama ba ni labari na abinda ya faru da yan uwana, ta dauke ni tamkar kibtawar ido, ta ajiye ni a cikin gidana. Na samu dukan dukiyata, ko allaura ba ta bata ba a ciki. Sannan kuma na ga karnuka biyu a daure.

Yayin nan aljana, macijiya, ta ce da ni cikin kakkausar murya: Da girman rubutun nan da ke jikin zoben Annabi Sulaimanu, idan ba ki bugi kowace daya daga cikinsu, a cikin kowane dare, bulala dari uku ba, babu rangwame, zan zo in yi miki azaba mafi tsanani daga tasu, in maishe ki tamkar su.

Na ce, na ji, na dauka! Ban gushe ba, ya Sarkin Musulmi, ina dukan su wannan duka, ina kuma jin tausayinsu bayan na gama dukan nasu. Wannan shi ne labarina da wadan nan karnuka, ya Sarkin Musulmi.

Halifa da sauran jama’a suka yi mamakin wannan labari na yarinya, mamaki mai yawa. Yayin nan Halifa ya yi umurni da a rubuta wannan labari a ajiye shi domin ya zama abin misali ga al’umma mai zuwa. Sannan ya dubi yarinya mai jiran kofa ya ce, ki labarta mana da abinda ya same ki na daga tabon bulala na jikinki. Yarinya ta fara bayar da labarinta.

Zamuci gaba insha Allah kuma rubutun mu nangaba zaizamo shine karshen wannan hikaya.014. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Yarinya Mai Jiran Kofa (1)

Bayan yarinya shugabar yan mata ta kare bayar da labarinta, sai Halifa ya dubi yarinya ta biyu, mai jiran kofa, ya ce, ki labarta mana da abinda ya same ki na daga tabon bulala da muka gani a jikinki. Yarinya ta fara bayar da labarinta, da kuma dalilin tabon bulala da ke jikinta, ta ce:

Ya Sarkin Musulmi, ubana ya kasance attajiri ne, ya mallaki dukiya mai tarin yawa wadda Allah kadai ya san yawan adadinta. Kuma na kasance ni kadai ce ‘ya tasa. Bayan ya mutu, na gadi dukkan dukiya tasa. Bayan yan shekaru kadan na yi aure. Na auri wani saurayi wanda shi ma ubansa ya mutu ya bar masa gadon dukan dukiyarsa.

Bayan aurenmu da shekara guda, sai Allah ya yi masa rasuwa. Na gada daga gare shi dinari dubu tamanin da gidan da mu ke ciki, shari’a ta bar mini. Bayan na gama takabarsa, na sa aka dinka mini riguna guda goma, aka kawata kowace riga da kayan ado kala-kala, a takaice dai kowace riga sai da aka kashe dinari dubu wurin dinka ta.

Ina zaune a gidana, wata rana sai ga wata tsohuwa ta shigo, mai daurarriyar fuska, mai nadadden goshi da nitattsun idanu, da wawilon baki, harshenta na rawa, wuyanta karkatacce tamkar da wakar wani mawaki da yake cewa:

“Muguwar tsohuwa mai sanar da Ibilis da abin da bai sani ba, a cikin aikinta mafi sauki ta kan dabaibaye alfadara dubu da abawar tautau da aka wadarta. Muguwar tsohuwa mai halasta haram da kaifin zamba da kissarta, da za a auna makircinta da nauyin dutsen Uhudu da ya rinjaye shi.”

Yayin da tsohuwa ta shigo wurina, ta yi mini sallama, na amsa mata. Sannan ta durkusa ta gaisheni da girmamawa, ta ce da ni, ‘yata, na zo ne in nemi wata alfarma a gare ki. Yarinya ta kasance a gare ni, yau ne kuma daren amarcinta, ina so ki sami ladarta da tawa, ki hallarci zaman amarcinta, ki zamanto bakuwarta ta musamman, ita mai yawan tunani ce domin rashin gata, ba mu da kowa sai Allah madaukakin Sarki.

Yayin nan tsohuwa ta yi kuka, ta sumbaci kafafuna. Tausayinta ya kama ni, na yanke shawara zan karbi goron gayyatarta. Na ce da ita, na ji na dauka. Ta ce da ni, ki shirya da isha’i zan zo mu tafi tare da ke. Yayin nan ta sumbaci hannuna ta fita.

Na tashi na yi wanka, na yi kwalliya sosai na shirya jikina tsaf, na debi kudi masu yawa wanda zan ba amarya, na zauna ina jiran isowar tsohuwa. Jim kadan sai ga ta, ta gabato ta ce da ni, ya shugabata tashi mu tafi, jama’a na can duk sun hallara, na shaida musu da zuwanki, sun yi farin ciki da kasancewarki babbar bakuwa ta musamman, suna can suna jiran zuwanki.

Na tashi na bi tsohuwa a baya, muna ta tafiya tinkis-tinkis har muka shiga cikin wani kwararo, da shigarmu kwararon na ji wani irin kamshin turare na tashi a cikinsa. Muka nufi kofar wani katafaren gida, muna dada dosar gidan kamshin nan na karuwa, har muka iso kofar gidan. Na gan shi gida ne ginanne na kasa, an adanta bayansa da zane. Muka ishe masu gadin kofa a tsaye. Da suka gan mu sai suka bude mana kofa muka shiga.

Muka ishe zaure, an rataye fitulu a kowace kusurwa ta zauren suna ci, suna haske tamkar rana. Muka wuce cikin gidan muka shiga cikin wani soro, muka ishe shi da shimfida ta kilisai masu taushi, ga fitulu ko’ina suna haske tamkar rana. Ga kuma gado na mirmir an yi masa ado da lu’ulu’u da jauhari, an lullube shi da shifida Siniya da hadalashi namusiya.

A zaune akan gadon, na ga yarinya cikin sitira, ka ce ita farin wata ce a cikin taurari. Tana gani na, ta sauko daga kan gado ta tare ni da murna da farin ciki tana cewa, maraba, marhabin da ‘yar uwata da ta zo ta debe mini kewa, ta faranta zuciyata. Ta kama hannuna ta zaunar da ni akan gadon nan, sannan ita ma ta zauna kusa da ni, tsohuwa kuwa ta fita ta bar mu.

Bayan mun zauna, yarinya ta dube ni ta ce, ya ‘yar uwata, aminiyata, ina da dan uwa wanda ya gan ki wata rana, ban san lokacin ba, ya ji yana son ki da aure. Shi saurayi ne mafi kyawo daga gare ni, zuciyarsa ta so ki, so mai tsanani, ya rasa yadda zai yi ya bayyana miki. Ya ba wannan tsohuwa kudi ta shirya wannan hila a gare ki domin ki yarda ki zo nan gidan dan uwana, shi kuma ya sami damar da zai bayyana miki abun da yake cikin ransa. Dan uwana yana son ya aure ki bisa ga sunnar Ma’aiki, babu aibi ga halal. Ko kin yarda na kira shi domin ku daidaita da juna?

Yayin da na ji zancen wannan yarinya, na dubi kaina, na ga na abku a cikin gida, ga masu gadi tsare da kofa, babu hanyar guduwa. Na ce da ita na yarda. Ta yi farin ciki, ta tashi ta bude wata kofa da take boye a cikin soron. Na ga saurayi ya fito daga cikin wani daki. Wannan saurayi da kyau ya ke tamkar wakar wani mawaki da ya ke cewa:

“Alheri ya yawaita ga Allah da ya yi baiwa a gare shi, ya halicce shi, ya daidaita shi, ya tara masa dukkan kyawo, ya sa dukkan talikkai su dimauta da ganin kyawonsa. An rubuta kyawo karkashin kundukukinsa, mun shaida babu birbishinsa da kyawo a cikin talikai”

Yayin da na dube shi, nan take kibiyar sonsa ta daki zuciyata, na ji babu wanda na ke so kamar shi. Lokacin da ya shigo sai ya sami kujera ya zauna. Ya gabatar mini da bukatarsa ta son aurena, na amince da ita.

Bayan an daura mana aure da wannan saurayi, a daren amarcina muna zaune tare da shi, sai ya dube ni ya ce, amaryata ina so ki yi mini wani alkawari, alkawarin kuwa shine, zuciyarki ba za ta taba karkata ga wani na ba, muddin ina raye kuma a matsayin mijinki, domin ni na kasance mai tsananin kishi ne. Na ce da shi na yarda da wannan alkawari ya shugabana. Ya dauko Alkur’ani mai tsarki ya ce in rantse akan wannan alkawari. Na rantse masa da ba zan kula ko wane da namiji ba.

Na zauna tare da mijina, cikin jin dadi da annashuwa har tsawon wata guda. Wata rana na nemi izini ga mijina, ina so in tafi kasuwa in siyo wadansu zannuwa, ya yi mini izini da in tafi. Bayan na rufe jikina kaf da tufafi, na riki tsohuwa domin ta raka ni zuwa kasuwa. Muka tafi har muka iso cikin kasuwa.

Tsohuwa ta ja ni zuwa rumfar wani yaro tajiri mai sayar da zannuwa na ado. Da muka isa muka yi masa sallama, bayan ya karba muka sheda masa cewa mun zo ne domin sayen zannuwa, na ce ya kawo mana zannuwan da babu irin su wajen kyau a cikin shagonsa, komai tsadarsu. Ya ce, to. Ya kawo mana kujeri muka zauna, shi kuma ya shiga cikin shago domin zabo mana kalar zannuwan da muke so.

Bayan saurayin nan ya shiga cikin shago, sai tsohuwar nan ta dinga yabonsa da koda shi a wuri na. Tana cewa ai wannan yaro mutumin kirki ne, yana da ladabi, ubansa ya mutu ya bar masa dukiya mai yawa. Na dube ta na ce, ba na bukatar ki yabe shi a wurina, muradina mu sayi abin da ya kawo mu mu juya zuwa gida.

Bayan yaro ya dawo da zannuwa, na zabi wadan da na ke so, na ce su yi ciniki da tsohuwa, suka yi ciniki, na ba tsohuwa kudi na ce ta ba shi. Da ta ba shi kudin sai ya ki karba, ya ce, haba wannan shi ne zuwanku na farko shagona, bai kamata na karbi kudinku ba. Tsohuwa ta ce idan bai karba ba me ya kamata mu yi? Na ce mu mayar masa da zannuwansa, mu tafi wani shago mu siya.

Yaro ya dube ni ya ce, wallahi ba na karbar ko daya, dukkan abin da ke cikin shagon nan, sumba daya da zan yi miki ta fi shi. Da za ki amince na sumbace ki, sumba daya, da na ba ki dukkan kayan da ke cikin wannan shago nawa. Na ce, tir da kai! Allah ya kare ni da in ha’inci mijina, shin ko ba ka san cewa ni matar aure ce ba?

Tsohuwa ta dube ni ta ce, haba ‘yata! Don dai sumba guda me zai same ki, ki yarda da wannan yaro, hakika ya jarrabu da son ki, ki ji tausayinsa ki biya masa da bukatarsa. Na ce da ita, hala kin manta da cewa ni rantsattsiya ce daga kula wani namiji ba mijina ba?

Ta ce da ni, bar shi ya sumbace ki sumba daya, babu abin da zai same ki, ya ‘yata da me sumbatar ki za ta amfane shi? Abin da zai yi cikin yan dakiku ya gama, mu kuwa mu yi tafiyarmu. Tsohuwa ba ta gushe ba tana kyautata mini wannan abu tana gusar da laifin aikata haka har na amince da bukatar yaro.

Na rufe fuskata da mayafi, yaro ya zo kusa da ni, ya sumbaci kundukukina ta cikin mayafi. Yayin da ya sumbace ni, sai ya gatsa mini cizo da hakoransa, cizo mai zafi har sai da ya cire fata daga kundukukina. Na fadi kasa somammiya saboda zafin wannan cizo.

Yayin da na farka, sai na ga tsohuwa rungume da ni, shago a rufe, babu yaro babu dalilinsa. Tsohuwa ta ce, abin da Allah ya so shi ne mai yiwuwa, wannan yaro ya cuce mu. Ki tashi mu tafi gida, ni na zo miki da maganin da za ki warke daga wannan cizo da gaggawa. Bayan jimawa muka tashi ina cikin gayar tunani da tsannin tsoro har muka iso zuwa gida.

Ban dade da dawowa ba, sai ga mijina ya shigo, ya na duban fuskata sai ya ce da ni, me ya ji miki ciwo a kundukukinki, wuri mani’imci? Na ce da shi, ya yin da muka fita zuwa kasuwa, mun hadu da rakuma akan hanya, an yiwo mata laftu na itace, garin in kauce in bata hanya, itacen ya karce ni a kundukuki har ya ji mini ciwo.

Mijina ya ce, babu shakka gobe in yi karar mai rakumar nan ga alkali, a daure shi kuma a rataye wanda ya dauko wa itacen ko wane ne a cikin birnin nan. Na ce da shi, na roke ka don Allah kada ka ga laifin kowa. Ni jaka na hau sai ta yi tutsu da ni, na fadi kasa, dutse ya ji mini ciwo. Ya ce, gobe kuwa na tafi gun Sarkin Musulmi, in hakaita masa da wannan hikaya, a kashe duk mai jakin da ke cikin birnin nan. Na ce, yanzu kai ka sa a kashe mutane duka saboda ni? Wannan al’amari ne da Allah ya gudanar bisa ga ikonsa da hukuncinsa, me za ka yi?

Ya ce, babu makawa ga haka. Ya zabura ya mike tsaye cikin fushi, ya yi kururuwa, kururuwa mai tsanani. Kofa ta bude, babbakun bayi guda uku suka fito ta kofan nan, suka jawo ni daga shimfidata, suka yashe ni tsakar gida.

Ya umurci bawa daya daga cikinsu da ya rike kafadata ya zauna bisa ga kaina. Ya umurci na biyu da ya zauna bisa gwiwowina, shi danne kafafuna. Na uku ya zo da takobi ga hannunsa, ya ce, ya shugabana in sare kanta da takobin nan, ko in raba ta gida biyu kowa ya dauki daya?

Mijina ya ce, sare ta gida biyu, kowa ya dauki daya ku jefa ta cikin kogin Dujillati, kifi ya cinye ta, wannan shi ne sakamakon wanda ya yi ha’inci ga rantsuwar masoyi.

Zamuci gaba insha Allah015. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Yarinya Mai Jiran Kofa (2)

Yarinya ta ci gaba da labarinta da cewa: Lokacin da mijina ya ji jawabina, ya zabura ya mike tsaye cikin fushi, ya yi kururuwa, kururuwa mai tsanani. Sai na ga kofa ta bude, bayi guda uku, bakake suka fito daga cikinta, suka jawo ni daga kan shimfidata, suka yasar da ni tsakar gida.

Ya umurci bawa daya da ya danne kaina, ya umurci na biyu ya danne kafafuna. Bawa na uku ya zo da takobi a hannunsa ya ce, ya shugabana in sare kanta ko in raba ta biyu kowa ya dauki rabonsa. Mijina ya ce, raba ta gida biyu da takobinka, kowa ya dauki daya, ku tafi ku jefa ta a cikin kogin Dujillati kifi ya cinye ta, wannan shi ne sakamakon mai yin ha’inci ga rantsuwar masoyi. Sannan sai ya waka wadan nan baitoci:

“Idan abokin tarayya ya kasance ga masoyiyata, na haramtawa kaina son ta. Ya raina mutuwata ita ta fi alheri, ga son da ya kasance akwai kishiya a cikinsa”

Bayan ya gama wannan waka, ya dubi bawan nan ya ce, raba ta biyu ya Sa’adu! Bawa ya tsiraita takobi, ya daga ta sama, sannan ya dube ni ya ce, ki na da sauran bukata? Ki na da wata wasiyya da za ki yi? Wannan shi ne lokacin rayuwarki na karshe a duniya.

Yayin nan na daga kaina, na dubi halin da na ke ciki. Na tuna da da daukakar da na ke da ita, yau ga shi na zamanto makaskanciya, na tuna irin dukiyar da na ke da ita, da matsayina, sai hawaye ya zubo daga idona, shar shar shar. Na waka wadan nan baitoci:

“Na zaunad da zuciyata cikin so, ta zauna. Na hana idona barci, suka hanu. Na saukad da ku cikin zuciyata, ta karbe ku. Kun yi mini alkawarin zama cikin so, amma da kuka mallaki zuciyata sai kuka warware. Ba kwa jin tausayin bakin cikina a gare ku? Shin kun amince da juyawar zamani ne? Shin ba ku yarda da kaddara ba ne? To ina rokon ku, domin Allah da Manzonsa, idan na mutu ku rubuta a kan allon kabarina, wannan mai bege ce, ta sadaukar da ranta ga abin da ta ke so, kuma ta mutu a kan soyayya.”

Yayin da mijina ya ji wannan waka, sai fushinsa ya karu a kan fushi, sai ya yi wannan waka ya na cewa:

“Kin bar abin son zuciyarki, kika so abin zargi, kika nado zunubi wanda ya halasta kisanki. Kika nufi abokin tarayya cikin tsarkakakken son da ke tsakanimmu. Gaskiya ni zuciyata ba ta yarda da abokin tarayya a cikin soyayya.”

Yayin da ya gama waka tasa, na yi kuka, na rarrashe shi, na ce shi yafe mini daga kisa, ya dauki dukkan dukiyata ta zama fansar laifin da na yi masa. Na kuma ce da shi, da girmanka idan ka bar ni, ba ka kashe ni ba, Allah zai hukunta tsakaninmu, hukunci tsarkakakke. Ka daukaka mini nauyin bege, ni na gajiya daga daukar riga biyu in ribanya. Ba na al’ajabin tallafar raina, amma ina al’ajabin ina za ka da alhakina?

Da ya ji wannan magana tawa, sai ya shure ni, ya zage ni, sannan ya yi wannan waka ya na cewa:

“Kun shagala da mu, kuka so wanimmu. Kun bayyana kaurace mana, ba tare da mun yi muku laifi ba. Tilas mu bar ku, tun da kuka bar nufinmu. Mu hakura da barinku, tamkar da kuka bar mu.”

Yayin da ya gama wannan waka, ya daka wa bawan nan tsawa ya ce, raba ta gida biyu, ba ta da wani amfani a gare mu.

Lokacin da bawa ya gabata, ya daga takobinsa sama zai sare ni, na sakankance da mutuwa, na debe kauna daga rayuwa, na bar al’amarina ga Allah, Madaukakin Sarki. Na yi kalmar shahada, na rufe idona ina jiran na ji saukar takobi a jikina. Daga nan sai ga tsohuwa ta shigo. Ko da ta gan ni cikin wannan yanayi, sai ta fahimci abin da ya faru. Nan take ta fadi gaban mijina, karkashin kafafunsa, ta na sumbatarsu.

Ta ce, ya saurayi, don martabar goyon da na yi ma ka, ka yafi wannan yarinya, ita ba ta aikata wani zunubi da wannan hukunci ya wajabta gare ta ba. Kai yaro ne karami, ina ji maka tsoro daga addu’a tata, domin addu’ar wanda aka zalunta abar karba ce ga Ubangijin talikkai. Yayin nan tsohuwa ta fashe da kuka.

Tsohuwa ba ta gushe ba tana rarrashin mijina, tana kuka tana buga kanta ga kafafunsa, har ya ce da ita, tashi na yafe mata, amma babu makawa in aikata mata tabo mabayyani a jikinta tsawon rayuwarta.

Ya umurci bayi suka tube ni daga tufafina, aka hallaro masa da tsumagiyar giginya, ya saukar mini da duka a jikina, duka mai tsanani. Bai gushe ba yana duka na, bisa ga bayana da hakarkarina, har na suma na faku ga barin duniya domin tsananin bugu. Ya umurci bawa daya da ya dauke ni, idan dare yayi, ya jefar da ni a cikin gidana.

Lokacin da na farka, na gan ni a yashe cikin gidana, na yi godiya ga Allah da ya kubutar da raina. Na yi ta jiyyar wannan duka da mijina ya yi mini, har na warke sarai. Amma wannan tabo na bugu yana nan tamkar da gan shi a jikina, ya Sarkin musulmi.

Bayan na warke, na dawo gidan mijina, sai na tarar da gidan nan a rushe daga farkonsa har karshe, na yi mamaki a kan faruwar wannan abu. Daga nan sai na ziyarci wannan ‘yar uwa tawa a gidanta. Na same ta tare da wadan nan karnuka, ta labarta mini abin da ya faru duka, gare ta da kuma yan uwanta. Na debo dukiyata na dawo gidanta muka ci gaba da zama tare.

Muna zaune a cikin gidan nan, sai ga wannan yar uwa tamu, wacce ta kasance ita ce karamarmu, muka dauke ta a matsayin Jekadiyarmu, wadda ke zuwa kasuwa tana sawo mana kayan abinci da na marmari. Muka zauna a wannan gida babu ruwanmu da maza, saboda abin da ya faru da mu a baya, na daga maza. Na kasance duk lokacin da na ji wakar soyayya, tsikar jikina ta kan tashi, hankalina ya kan gushe har na suma, saboda wannan abu da ya faru da ni. Wannan shi ne labarina da kuma dalilin tabon bugu da ke jikina, ya Sarkin Musulmi.

Halifa ya yi matukar mamaki da al’ajabin labarun wadan nan yan mata. Ya yi umurni da a rubuta wadan nan hikayoyi na yan mata da kuma na samari masu ido daya-daya a littafi, a ajiye su a dakin adana littattafai, domin na baya su karanta su amfana da darussan da ke cikin wadan nan hikayoyi.

Sannan ya juya ga yarinya shugabar yan mata, ya ce, yalla ko kin san inda aljanar da ta sihirce yan uwanki ta ke? Yarinya ta ce, a’a, amma ta ba ni wani yanki na gashin kanta, ta ce duk lokacin da na ke son ganinta, na kona sili daya za ta bayyana da gaggawa, ko da kuwa tana bayan dutsen kaf.

Halifa ya sa yarinya ta kawo gashi daya na aljana, ya sa aka hada garwashin wuta, ya jefa gashin a ciki. Lokacin da hayaki ya tashi, iska ta kada shi ko’ina, sai suka ji kasa na girgiza, kamar za ta tsage. Wata irin tsawa da hargowa ta cika fadar. Jim kadan sai ga aljana ta bayyana, cikin kyakkyawar shiga ta musulunci, da ma Allah ya yi ta musulma ce.

Tana bayyana, sai ta gabatar da sallam ga Halifa da cewa, amincin Allah ya tabbata a gare ka, ya Sarkin Muminai. Halifa ya amsa mata da cewa, amincin Allah ya tabbata a gare ki.

Sannan ta ce, ka sani ya Halifa, wannan yarinya ta yi mini taimakon da ba zan manta da shi ba har duniya ta nade, domin ita ce ta kashe mini babban makiyina a duniya. Domin in saka mata da wannan alheri da ta yi mini, na sihirce wadan nan miyagun yan uwa nata, wadan da suka yi niyyar halaka ta, zuwa karnuka. Da na yi niyyar in kashe su ne, sai na lura da cewa za ta damu da hakan, shi ya sa ban kashe su ba. Amma bisa ga girmamawarka da yardar yarinya, ya Sarkin Musulmi, idan kuna so in mayar da su ga siffarsu ta asali, to zan mayar da su, na kasance musulma mai biyayya ga shugabanni.

Halifa ya ce, na roke ki tare da yardar yarinya da ki mayar da su ga siffarsu ta asali. Bayan wannan sai mu binciki al’amarin wannan yarinya da aka yi wa duka, mu nemo wanda ya zalunce ta, mu fitar mata da hakkinta.

Aljana ta ce, na ji na karba. Yanzun nan zan mayar da su ga siffarsu ta asali. Amma wanda ya doki yarinyar nan, mutum ne makusanci da kai, karewa ma, a cikin iyalinka ya ke. Ta ce a kawo mata tasa da ruwa. Da aka kawo mata, ta yi wani zance ta tofa a cikin ruwan. Sannan ta yayyafa wa karnukan nan ruwan, ta ce, ku fita daga cikin wannan siffar, ku komo ga siffarku ta mutane. Nan take karnukan nan suka juye zuwa kyawawan yan mata, son kowa kin wanda ya rasa, tamkar yadda suke a da. Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wadan nan yan mata.

Bayan aljana ta mayar da yan matan nan ga siffarsu ta asali sai ta ce da Halifa, ya Sarkin Musulmi, ka sani cewa ba kowa ne yayi wa yarinyar nan duka ba face danka Aminu. Shi ne ya ji labarinta, da kyawonta. Ya nemi yardarta suka yi aure. Aljana ta kwashe labari duka ta fada wa Halifa, tamkar dai yadda yarinya ta fada masa.

Da Halifa ya ji haka, ya ce, tsarki ya tabbata ga Allah, wanda ta sanadiyyata ne wadan nan yan mata, da suka shafe lokaci mai

Please Login or Register in order to submit comment