Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi jifa da ni chikin bahar daga jirgin. Na kasance na iya ninkaya, na yi ta iyo a cikin wannan rana ya zuwa ga dare, damutstsana suka gaji, kafaduna suka kasa, na zama cikin halaka, yayin nan na yi kalamash shahada, na sakankance da mutuwa.

Zamuci gaba gobe insha Allah
010. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Saurayi Na Uku Mai Ido Daya (2)

Bahar ya tashi da yawan iska, kumfa ta zama tamkar duwatsu, ta dauke ni, ta jefar da ni, na zama bisa tudu. Yayin da Allah ya yi nufin im fita tudu, na taka, na matse tufafina, na baza su bisa ga kasa, na yi kwanche.

Yayin da gari ya waye, na saka tufafina, ina tunanin inda zan nufa sai na tsinkayi jigawa da itatuwa, na nufi zuwa gare ta, ina gewaya ta, na ishe wurin nan da ni ke jazira che karama, bahar ya kewaye ta. Na che a chikin raina ko yaushe na kubuta daga masiba sai kuma im fada wata.

Ina chikin tunanin al’amarina, ina burin mutuwa domin na huta da wannan wahala, sai na hangi jirgi daga nesa ya nufo wannan tsibiri.

Na tashi, na hau bisa itachiya. Bayan wani lokaci jirgin ya iso bakin tudu, bayi goma suka fito daga gare shi da magirbai ga hannuwansu. Suka zo har suka iso tsakar jazirar, suka tona kasa suka daukake rufi, suka share, sai ga kofa ta bayyana, suka bude kofar. Yayin nan suka koma zuwa ga jirigin, suka zama suna debowa daga gare shi waina, da gari da mai, da zuma, da ganimomi, da dukkan abin da mai-zama ke bukata.

Bayi suka zama suna kokkomawa tsakanin jirgi da rufi, suna tarawa a chikin rufin, har suka debe dukkan abin da ke chikin jirigin. Yayin nan bayi suka komo tare da tufafi kyawawa da wani tsoho, duddugagge, dogo, ya kasance zamani ya dade tare da shi, ya zama kararre, daga kashi sai fata.

Na ga kuma wani yaro, saurayi tsohon na rike da hannunsa. Wannan yaro ya cika duk wata siffa ta kyawo, har ana buga misali da kyawonsa, cewa shi tamkar danyar sanda ne a cikin rairayin hamada, shina kore kowache zuchiya da kyawonsa, shina tu6e wayon mai wayo da chikar halittar sa.

Wannan saurayi na sanye da kyawawan tufafi. Ba su gushe ba suna tafiya, ya shugabata, har suka iso zuwa ga rufi suka sauka chikinsa, suka faku ga ganina. Yayin da suka shige karkashin kasa, na tashi, na sauko daga bisan itachiya, na tafi zuwa ga wurin na share kasar na chire rufin, na saurara kadan ko na ji motsinsu, ban ji motsin kome ba.

Na duba rufin, na ishe itache ne tamkar duwatsun dahunu, na daukake su, tsani ya bayyana daga Karkashinsa, na tattaka tsanin na sauka kasa, na iske wuri tsatstsarka, na ga gona, da ta biyu, da ta ukku, har ya zuwa ga chikar talatin da tara. Kowache gona na ga abin da ya gajiyad da kwatanchi a chikinta na daga itatuwa, da Korammu, da ‘ya’yan itatuwa, da kayan taska daga jauhari zuwa ga waninsa.

Na ga wata kofa, na che a chikin raina, yalla menene a chikin wannan bigire? Babu makawa im bude ta, in ga abin da ke chiki. Yayin nan na bude kofar, na ishe a chikinta wani doki fari fat, da sirdi, da linzami, a daure, na kwanche shi na hau. Ya kada da ni zuwa ga kuryar gidan, ya ajiye ni bisa ga tsakar gida bakin kofar wani soro. Ya saukad da ni, ya buge ni da wutsiyarsa ga idaniyata ta hagu, nan take ta tsiyaye, ta tallafa, ya juya ya koma ta inda muka fito.

Na shiga cikin soron na samu samari goma, masu-ido daya daya. Yayin da suka gane ni, suka che, Babu maraba a gare ka! Na che da su, kwa tarye ni da haka, ni mai niyyar zama a gare ku? Suka che, Wallahi, ba ka zama a gare mu, suka kore ni daga wurinsu. Na fita daga gare su, ina mai bacin zuchiya, mai-kuka ga ido.

Bayan na fito daga cikin rufin nan na karkashin kasa, na shiga cikin jirgin da tsohon nan da saurayi suka zo da shi, na fada cikin bahar, Allah ya kaddara iska ta yi mini kyawo, ya kubutad da ni, na sadu zuwa ga Bagadada, na aske gemuna. Na shigo cikin wannan gari da dare na sami wadannan biyu, masu ido dai daya, na yi sallama a gare su. Na che da su, Ni bako ne! Suka che, Mu, ma, baki ne. Wannan shi ne dalilin tallafar idaniyata da aske gemanyata, ya shugabata.

Yarinya shugabar yam mata ta che da shi, ka samu kanka! Kwance kan ka daga dauri ka tafi! Ya che, Wallahi, ba ni tafiya, sai na ji kissar wadan nan fataken.

Yayin nan yarinya ta waiwaya zuwa ga Halifa, da Ja’afaru, da Masruru. Ta che da su, Ku labarta ma ni da labarinku. Ja’afaru ya gabata, ya hakaita ma ta hikayan nan da ya gaya wa yarinya mai jiran kofa yayin shigowarsu wannan gida.

Yayin da ta ji zanchensa, ta che, Na ba da sashenku ga sashe, ku tashi ku fita ku barmu. Suka fito, Dan Dako ya nufi gida yana mai matukar mamaki, gayan mamaki, akan yam mata da samari uku masu ido daya da hikayoyinsu.

Bayan sun fito har sun iso chikin kwararo. Halifa ya che ma samarin nan, Ya ku, jama’a ina za ku? Suka che, Ba mu san inda za mu ba. Halifa ya che da su, ku tafi, ku kwana a gare mu. Ya che ma Ja’afaru, rike su, ka zo ma ni da su da safe, har in ga abin da zai kasance. Ja’afaru ya bi abin da Halifa ya umurche shi da shi. Yayin nan Halifa ya shiga zuwa ga gidansa, barchi bai zo ma sa ba chikin wannan dare.

Yayin da gari ya waye, ya zauna bisa ga gadon sarauta, Sarakuna suka shiga, fadanchi ya kankama. Ya waiwaya zuwa ga Ja’afaru, bayan ma’abutan daula sun taru, ya che, ka zo mini da samarina ukku, da yam mata ukku, da karnuka biyu. Ja’afaru ya zabura, ya hallarasu gaba gare shi. Mata suka shiga bayan sitira.

Ja’afaru ya waiwaya zuwa ga yam mata, ya che da su, Mun yafe muku daurin da kuka yi mana jiya domin abin da kuka gabatar na daga kyautatawa gare mu, ba tare da kun san mu ba. Yanzu kuna gaba ga Halifa na biyar daga Banu Abbas, shi ne Harunar Rashid. Kada ku labarta ma sa, fache gaskiya.

Yayin da yam mata suka ji zanchen Ja’afaru bisa ga harshen Sarkin Musulmi, suka fadi suka yi gaisuwa. Babbarsu ta gabata ta che, Ya Sarkin Musulmi, ina da zanche na daga wadan nan karnuka, wanda da za a rubuta shi da tsinin allura bisa ga gefen idanu, da ya zama abin lura ga mai hankali. Ta fara bayar da labarinta kamar haka:

Zamuci gaba insha Allah

WhatsApp only pls
08032767547
Menu

011. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Yarinya Shugabar Yam Mata (1)

Yarinya shugabar yam mata ta ce da Halifa da sauran jama’a, wadan nan karnuka biyu yan uwana ne, ubanmu daya amma su biyu mahaifiyarsu dabam, na kasance ni ce karamarsu. Mahaifinmu ya mutu ya bar mana gadon kudi, dinare dubu biyar, bayan an raba kudin nan sai su biyu suka yi aure, suka damka amanar dukiyarsu ga mazajensu suna yi musu fatauci tsawon zamani. Ni kuwa ina cininiki a cikin rumfata.

Bayan shekara hudu, mazajen yan uwannan nawa suka banzatar da dukiyar yan uwana suka wulakanta su sannan suka kore su. Yan uwana suka zo wurina, da farko ban gane su ba domin duka wahala ta tsufar da su. Yayin da na shaida su na ce, ya yan uwana me ya faru da ku bayan aurenku? Suka ce, ya yar uwar mu, zance ba shi da amfani a halin yanzu, bakin alkalami ya riga ya bushe, abin da Allah ya hukunta ba shi canjawa, cewa mu kaddara ta fada mana na daga asarar dukiyarmu, yanzu ba mu mallaki ko dirhami ba.

Koda na ji haka sai na kwantar musu da hankali, na ce haka Allah ya kaddara, babu mai ikon juyad da ita. Na aika da su gidana, na tufatar da su tufafi masu tamani. Sannan na ce da su, ya yan uwana kune manya ni kuma ni ce karama daga cikin ku, don haka yanzu ku ne a matsayin iyayena. Rabon da na samu na gadon kudin mahaifinmu, Allah ya sa albarka a cikinsa, na juya shi ta hanyar kasuwanci, na kuma sami riba mai yawa don haka ya ishe mu, ni da ku, mu raba shi daidai.

Ya Halifa, na kyautatawa yan uwan nan nawa, gayar kyautatawa, mu ka zauna tare muna kasuwanci tsawon shekara guda, suka zama masu arziki da dukiyata. Wata rana sai suka ce da ni, suna son su koma ga mazajensu. Na ce da su, ya yan uwana ku sani cewa kyawawan maza masu amana kadan ne a wannan zamani, za su karbe dukiyarku ne su wulakanta ku, su kore ku daga wurinsu, shin kun manta abinda ya faru da ku a baya? Suka ce, su dai za su koma. Na yi na yi da su, suka ki. Na barsu suka koma gun mazajensu.

A cikin sa’a kadan da komawarsu, mazajen suka rude su, suka karbe dukiyarsu suka tafi suka bar su. Suka komo zuwa gareni suna matsiraita, suna mai kawo mini hanzari cewa, ya yar uwarmu, kada ki rike mu da laifimmu, ke ce karama daga gare mu amma kin fi mu hankali, cewa mu ba za mu sake yarda da maza ba har abada. Na ce, maraba da ku ya yan uwana, ba ni da tamkar ku a duniya, ta yaya zan juya muku baya. Na sumbace su, na dada musu karimci.

Muka zauna tare da su tsawon shekara cikakkiya, na yi nufin zuwa fatuci birnin Bisira. Na shirya babban jirgi, na cika shi da kayan fatauci da guzurim ma su jirgi. Na ce da yan uwana, ko za ku zauna a gida har in tafi Bisira in komo, ko kuna da sha’awar mu tafi tare? Suka ce, za mu tafi tare, mu ba mu iya rabuwa da ke.

Na raba dukiyata, ta kudi, kashi biyu, na boye daya a gida na riki daya domin ban sani ba kila wata kaddara ta asara ta fada mana a can. Idan mun koma ma samu abinda zai amfane mu.

Bayan mun gama shiri, muka shiga jirgi muka tsunduma cikin bahar. Muka yi ta tafiya, dare da rana babu tsayawa. Muka yi kwanaki muna tafiya, ashe ba mu sani ba mai jirgi ya bata hanya, muka shiga wani bahar wanda ba mu sani ba. Bayan tsawon wani zamani, sai muka hangi wani birni daga nesa. Muka nufe shi har muka isa kan tudu.

Muka tambayi mai jirgi sunan wannan birni. Ya ce, Wallahi ban sani ba, ni ban taba ganin wannan birni ba, ban taba zuwa gareshi ba. Ku sani cewa mun bace hanya, amma al’amari yayi mana kyau tunda mun samai wannan birni. Ku fitar da kayan ku, ku shiga cikinsa ku yi ciniki. Amma ku bari na shiga cikin garin na duba yanayinsa da yanayin mutanensa.

Mai jirgi ya shiga cikin birni ya jima, bayan wani lokaci ya dawo garemu. Ya ce, ku tashi mu shiga cikin wannan birni ku yi al’ajabin ikon Allah don ku nemi tsari daga fushinsa. Ku bar kayan ku a cikin jirgi.

Muka shiga cikin birni. Muka iske dukan halitta mai rai da ke cikinsa an shafeta ta koma siffar bakin dutse. Muka yi mamakin ganin wannan abu. Muka shiga cikin kasuwa muka ga kayayyaki, zinariya da azurfa, zube ga rumfunan sayar da su. Ga mutane, wasu a tsaye, wasu a zaune, wasu suna ciniki, wasu suna gaisawa, wasu na cin abinci, amma duk an shafe su zuwa siffar dutse. Sai kayayyakin siyarwa ke kyalkyali a cikin rumfuna. Muka yi mamakin wannan abu, muka ce watakila wani babban al’amari ya gudana ga jama’ar wannan birni.

Muka fita daga cikin kasuwa muka rarrabu cikin kwararo kwararo na wannan birni, ko wanne dayanmu ya manta da abokinsa domin dimbin dukiyar da ke cikin wannan birni. Kowane kwararo akwai mutane da dabbobi, amma dun sun zama bakaken duwatsu.

Amma ni na hangi wani babban gida, na shiga cikinsa. Na same shi abin gajiyarwa ga ido gun kallo, ashe nan ne fada. Na shiga cikin soro, na sami dukan koran da ke ciki an yi su ne da zinariya da azurfa. Yayin nan na ga Sarki zaune akan karagar mulki, hakimai da fadawa sun zagaye shi, suna sanye da tufafi wadanda ke dimauta wanda ya gansu.

Yayin da na kusata da Sarki, na gan shi akan karaga abar aikatawa da lu’ulu’u da jauhari, ko wace fuska ta na haske tamkar taurari. Da tufafi a jikin Sarki zanannu da zinariya, da wasu dakaru mutum uku, daya a kowane gefe da kuma daya a bayansa, kowanensu na rike da zararren takobi, duka suna cikin siffar duwatsu. Yayin da na ga haka hankali na ya tashi da ikon Allah.

Na shiga cikin gida, na iske sarauniya da adon lu’ulu’u mai yawa a jikinta, ta saka hula a kanta wacce aka yi wa ado da zinariya da jauhari, da wata babbar sarka ta zinariya a wuyanta. Ga kuyangi, kowace da dangin kayan ado dabam a jikinta, suna masu yin hidima ga sarauniya, duka an shafesu bakaken duwatsu.

Na shiga wata budaddiyar kofa na ga matakai masu hawa zuwa sama, na tattaka su na hau sama. Na samu wuri shimfidadde da shimfidun darduma mai tasuhi, da gado na marmar an yi masa ado da zinariya da azurfa, da katifa akan gadon. Na ga wani haske yana tashi daga wani bangare na wannan daki, na iske jauhara tamkar kwan jimina, ita ce mai hasken. Na yi al’ajabi, matukar al’ajabi, na dukiyar da ke cikin wannan gida.

Na ga fitilu a kunne cikin wani daki, na shiga ban ga kowa a ciki ba, na ce a raina, babu makawa wani mai rai ne ya kunna wadan nan fitilu. Na zama ina bincike cikin wannan gida, na dulmiya cikin tunani har dare yayi. Na yi nufin fita in koma inda jirgimmu, na kasa gane kofar fita. Na juya ga dakin da na ga gado a ciki, na haye kan gado na rufa da mayafi domin inyi barci, na kasa.

Can zuwa tsakiyar dare, ina kwance na kasa barci, sai na ji am fara karatun Alkur’ani da wata murya mai dadi. Na sauko daga kan gado, na fito, sai na ji karatun na fitowa ne daga dakin da na samu fitilu a kunne. Na zo a hankali na leka cikin dakin, sai na ga saurayi a zaune kan shimfida, mai kyakkyawar magana, da Alkur’ani a gabansa yana karantawa. Na yi mamaki da ya kubuta daga sauran jama’ar wannan birni da aka mayar da su duwatsu.

Zamuci gaba insha Allah012. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Yarinya Shugabar Yan Mata (2)

Yarinya shugabar yan mata, ta ci gaba da labarinta da cewa: Bayan na gama kallon abin mamaki, da ikon Allah, a cikin gidan nan, sai na yi nufin fita domin in koma inda yan uwana. Na nemi hanya na rasa, sai na koma dakin da na ga gado da shimfida. Na haye gado na yi kwance, da nufin in yi barci, amma ya gagara.

Can zuwa tsakar dare, sai na ji karatun Alkur’ani na fitowa, daga cikin dakin da na ga fitilu a kunne, da wata irin murya mai dadi. Na tashi na nufi wannan daki, sai na ga wani saurayi ne yake wannan karatu. Na yi mamakin ganin cewa shi kadai ne ya tsira a cikin wannan birni, ba a mayar da shi dutse ba.

Na shiga na yi masa sallama. Ya dakatar da karatunsa, ya juyo ya dube ni, sannan ya mayar mini da sallama. Na ce da shi, na roke ka, don girman wannan littafi da kake karantawa, ka yi mini bayani a kan tambayar da zan yi maka.

Ya yi murmushi ya ce: Ki labarta mini dalilin zuwan ki wannan gari namu, har kika shigo wannan gida, sannan in labarta miki duk wani jawabi da za ki tambaya gare ni.

Na ba shi labarina, da na yan’uwana, da kuma niyyarmu ta zuwa birnin Bisira wurin fatauci, da yadda muka bace hanya har muka iso wannan birni. Ya yi al’ajabi, gayar al’ajabi. Yayin nan ni kuma na tambaye shi bayanin wannan birni, da abin da ya sa aka shafe su zuwa duwatsu, da kuma dalilin da ya sa shi ba a shafe shi dutse ba.

Ya ce: Ki jinkirta mini. Ya nade takardu, ya saka su a cikin jikka ta hadalashi, ya zaunar da ni a gefensa. Na yi duba izuwa fuskarsa, na gan shi tamkar farin wata, mai kyawawan siffofi, da tattausan lafazi, mai kwarjini ga magana, madaidaicin tsayuwa, matsakaicin kundukuki. Na yi duba zuwa gare shi, dubar da ta azabtar da zuciyata, son shi ya huru, tamkar wuta, a cikin zuciyata. Na yi burin ina ma ya zamanto mijina.

Na ce da shi, ya shugabana, ka yi mini bayani a kan abin da na tambaye ka. Ya ce: Na ji, na dauka. Sannan ya fara ba ni labari kamar haka:

Ki sani, wannan alkarya birnin ubana ce, shi ne wanda ki ka gani a cikin wannan fada, da dukkan jama’ar da ke cikinta, da dimbin dukiyar da Allah ya ba su. Kuma Sarauniyar nan da ki ka gani, ita ce uwata. Jama’ar wannan gari, da Sarkinsu duka, sun kasance majusawa ne. Suna bauta wa wuta, suna barin bauta wa Allah Mai iko. Sun kasance suna rantsuwa da wuta, da haskenta, da inuwarta mai kuna.

Ubana ya kasance ba shi da da tsawon lokaci, sai Allah ya arzuta shi da ni. Bayan na fara girma, ya bayar da ni ga wata tsohuwa mai reno, ya ce: Ki rike shi, ki rene shi, ki koyar da shi dabarun addinimmu.

Tsohuwar nan ta kasance mai yawan shekaru ce, ta san ilimi na taurari, da na zaman duniya, da dukkan ilimomi. Ta kasance musulma ce, ta bayar da gaskiya ga Allah da Manzonsa a boye. Tana shiryar da mutane addinin musulunci ba tare da sanin Sarki ba. Ta rike ni, tana koyar da ni addinin Islama, maimakon addinin bautar wuta. A wurin ta na koyi tsarki, da farillar alwala, da salla. Ta koyar da ni karatun Alkur’ani.

Yayin da ajalinta ya yi, ta ce da ni: Ya dana, ka boye wannan al’amari ga ubanka, kada ka sanar da shi, ya kashe ka. Bayan tsohuwa ta mutu, na ci gaba da bauta wa Allah a boye. Mutanen gari kuwa suka kara kafircinsu, da butulcinsu, suka kara zurfafa a cikin sabon Ubangiji.

Suna nan cikin wanan hali, sai wata rana, daga cikin ranaku, suka ji mai kira yana kira da madaukakin sauti, tamkar tsawar aradu. Na nesa da na kusa duka sun ji wannan murya tana cewa: Ya mazauna wannan birni! Ku juya zuwa ga barin bautar wuta! Ku bauta wa Sarki Mai iko, wanda yake saukar muku da ruwa daga sama, ya ba ku dukiya da abinci!

Mutane duka suka tsorata da jin wannan murya, da gargadin da ta yi musu. Suka tafi wurin ubana, Sarki, suka ce da shi: Ya Sarki, mene ne wannan sauti, mai tsanani, da muka ji ya tsoratar da mu? Ya ce: Kada jin wannan sauti ya tsorata ku, kada ku juya ga barin addininku na bautar wuta. Mutane suka dauki maganar ubana, suka ci gaba da bautar wuta.

Basu gushe ba suna ci gaba da bauta wa wuta, da yin butulci ga Allah Madaukakin Sarki, tsawon shekara guda da jin sautin nan na gargadi. Aka kara gargadin su da barin bautar wuta, ba su bari ba. An yi musu wannan gargadi sau uku, kowace shekara sukan ji wannan murya mai gargadi, har shekara uku, amma ba su bar bautar wuta ba.

Ba su gushe ba suna madurkusa, wurin bautar wutarsu har masifa ta saukar musu. Abin ya faru ne wata rana bayan hudowar alfijir, aka shafe su zuwa babbakun duwatsu, haka nan dabbobinsu, wani bai kubuta daga mazauna wannan birni ba, face ni. Daga ranar da wannan abu ya faru, ina bisa ga wannan hali, na karatun Alkur’ani. Na tabbata a kan haka, har zuwa wannan lokaci da kika same ni.

Yarinya ta ci gaba da ba Halifa da sauran jama’a labarinta, ta ce: Ya Sarkin musulmi, lokacin da na ji labarin saurayi, da dalilin da ya sa aka mayar da mazauna wannan birni duwatsu, na yi mamaki, matukar mamaki. Sannan na tambayi saurayi, na ce da shi: Ya shugabana, yalla ko za ka bi ni zuwa garimmu, ka hadu da masana, ka karu da iliminsu, ni kuma in zama kuyangarka? Ina da jirage madaukaka da ake zuwa mini fatauci, da dukiya mai tarin yawa. Watakila Allah ya turo mu wannan birni ne naku domin mu tafi da kai zuwa garimmu. Na yi ta lallashin sa dai, har ya yarda zai tafi tare da mu.

Bayan gari ya waye, muka tashi, ni da saurayi, muka shiga cikin taskoki, muka debo daga dukiya, abubuwa masu saukin dauka amma masu tsada. Muka fito daga gidan, muka kama hanyar zuwa inda jirgimmu ya ke, a bakin bahar na garin.

Muka hadu da bayina, da mai jirgi suna nema na. Yayin da suka gane ni, suka yi farin ciki. Suka tambaye ni inda na shiga, tun jiya suna nema na. Na labarta musu da abin da na gani, da kuma kissar mutanen wannan birni, da kuma dalilin da yasa aka shafe su. Suka yi mamaki.

Yayin da yan’uwana suka ga wannan saurayi, da irin kyawon da Allah ya yi masa, sai suka yi kishi na, suka hassade ni, suka kulla makirci a cikin zuciyarsu, amma ni ban san nufinsu ba.

Muka shiga cikin jirgi. Muka zauna muna jiran iska, har ta yi mana dadi. Muka saki jirgi, muka nausa cikin bahar, muka tasamma jahar da birnin Bisira ya ke.

Yan’uwana suka tambaye ni, muna cikin zance, suka ce da ni: Ya yar’uwarmu, me kike nufi da wannan kyakkyawan saurayi? Na ce da su, Ina so in aure shi, ya zamanto mijina, kuma in damka masa amanar dukiyata, amma sai idan ya yarda.

Bamu gushe ba muna tafiya, iska ta yi mana kyau, har muka fita daga bahar abar tsoro, muka shiga bahar mai aminci. Muka tafi kwanaki kadan, har muka kusato Bisira, gine-ginenta suka bayyana a gare mu.

Lokacin da dare yayi, muka shiga barci, yan’uwana suka tashi, suka dauke mu, ni da saurayin nan da shimfidummu, suka kunduma mu cikin bahar.

Zamuci gaba insha Allah013. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Yarinya Shugabar Yan Mata (3)

Yarinya shugabar yan mata ta ci gaba da labarinta da cewa: Muka ci gaba da tafiya a cikin bahar, kwana da kwanaki, har muka fara hango gine-ginen birnin Bisira. Wata rana da dare, jirgimmu na tafiya a cikin bahar, barci ya dauke mu duka, sai matukin jirgin ne kawai ke ta faman tuki. Sai yan uwana suka lallabo, suka dauke mu, ni da saurayi da shimfidummu, suka kunduma a cikin ruwa, jirgi yayi gaba.

Allah ya nufa da saurayin nan bai iya ninkaya ba, nan take ya dulmuye a cikin ruwa yayi shahada. Ni kuwa, sai Allah ya koro mini da wani itace, na kama shi na hau, iska ta yi ta tura ni har na zo bakin gabar wani tsibiri, na taka na shiga cikin tsibirin.

Ban gushe ba ina tafiya cikin wannan tsibiri har gari ya waye, da na dubi kasa sai na ga sawun kafar dan Adam, amma akwai alamun sawun ya dade. Yayin da rana ta fito, na cire tufafina na shanya su a rana. Ina zaune gindin wata itaciya ina jiran tufafina su bushe, sai na hangi wasu macizai guda biyu, sun nufo inda na ke a guje, daya na biye da daya.

Da suka iso wurina, sai na lura da cewa daya macijin ya biyo dayan ne yana neman ya hallaka shi. Wanda aka biyon sai ya nufo inda na ke, ga alama kamar yana neman taimako daga gare ni. Sai na dauki wani babban dutse nan kusa da ni, na dubi macijin da yake neman hallaka dan uwanshi, na kwantsama masa shi a kai. Nan take ya mutu.

Macijin da aka biyo kuwa da ya ga na kashe abokin fadansa, sai na ga ya fito da fuka-fukai, ya tashi sama, ya kada cikin sararin Subuhana, har ya bace wa ganin idona. Na cika da al’ajabin wannan abu. Na sa tufafina, na ci

Please Login or Register in order to submit comment