Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kewayensa, na gan shi tamkar katanga, na sara gatari bisa ga kansa. Na ga rufi na farin karfe, na share kasar daga nan sai ga rufi na itace, na yaye shi, tsani ya bayyana a karkashinsa, na sauka zuwa ga kasan tsanin sai ga kofa, na shiga cikinta. Na ga soro mai kyakkyawan gini da zane da lailaya.

Na ishe yarinya cikinsa, kai ka ce an gina ta da lu’ulu’u, tana sanyaya zuciyar mai bakin ciki, tana tsarkaka tunanin mai bacin zuciya. Yayin da na dubeta, na yi sujuda ga mahaliccinta domin abin da ya bayar gare ta na daga kyawo da cikar halitta.

Ta yi duba zuwa gare ni ta ce, yalla kai mutum ne ko aljani? Na ce da ita, ni mutum ne! Ta ce da ni, wa ya sadar da kai ga wannan bigiren da ni ke cikinsa shekara goma sha daya ban ga kowa na daga bil Adam ba?

Yayin da na ji zancenta, na ji dadi a cikin raina na ce, ya shugabata Allah ne ya kawo ni zuwa ga wannan wuri, mai yiwuwa ya yi nufin gusad da abin da ke tare da ni na daga bakin cikin rayuwa. Na labarta ma ta hikayata tun daga farko har karshe. Kafin na gama ba ta labarina, tuni idanunta sun cika da hawaye, saboda tausayi. Ta ce da ni, lalle ka gamu da jarabawar rayuwa kwatankwacin irin tawa.

Yarinya ta ci gaba da cewa, ni kuwa labarina shi ne, ni yar Sarkin Hindu ce, mahaifina ya aurar da ni ga dan bappah na, ina ‘yar shekara goma sha biyu. Daren amarcina, Ifiritu ya sace ni, sunansa Jarjarisu dan Rajimusu dan Ibilisa, ya kawo ni cikin wannan wuri. Ya tara mini dukkan abin da nake bukata na daga tufafi da kayan ado da na shimfida, da na kayan abinci da abin sha. A cikin kowane kwana goma, ya kan zo ya kwana gare ni, kwana daya. Amma idan ina son ganinsa kafin lokacin, ya ce in taba wadan nan sharuddan rubutu na bisa kubba da hannuna, yayin da na shafa rubutun kafin in dauke hannuna, ya bayyana.

Yau kwanansa hudu da tafiya, sai ga ka na gani. Ko za ka amince ka kwana biyar gare ni kafin ya sake dawowa, ka debe mini kewar rashin ganin dan Adam na tsawon shekara goma sha daya da ban yi ba?

Sai gobe Zamu Cigaba a na 6
006. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (2)

Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da labarinsa da cewa:

“Sai na amince da bukatar yarinya, ‘yar Sarkin Hindu wadda Ifiritu ya sace ta ya boye a wannan wuri da na same ta. Zan kwana biyar a gare ta, sannan in kama gabana kafin zuwan Ifiritu.

Ta gabatar mini da abinci da abinsha, muka ci, muka sha tare da ita. Muka dade muna zance, tana mai matukar farin ciki da kasancewata a gare ta. Bayan mun gama zance, ta ce da ni ka kwanta ka huta ya shugabana, ka kasance mai aikin wahala ne. Ta kai ni wani daki, ta nuna mini gado, na hau na kwanta. Ban san lokacin da barci ya dauke ni ba saboda tsananin gajiya.

Can da na farka daga barci, sai na ishe yarinya tana yi mini tausa ga kafafu, na kiraye ta da kyakkyawan suna, na gode mata, na yi mata addu’a a kan wannan karimci da take nuna mini. Ta ce, Wallahi ni na kasance mai kunkuntar kirji da zama wannan wuri ni kadai, cikin karkashin kasa, ba ni da abokin zance tsawon shekaru. Na gode Allahn da ya kawo ka gare ni.

Na kara yi mata godiya, sai kuma na ji sonta ya tabbata cikin zuciyata, fushina da bacin raina, na daga abin da ya same ni, ya yaye. Muka zauna muna zance, tsawon dare, daren da babu tamkarsa cikin raina.

Muka wayi gari muna masu farin ciki. Na ce da ita lalle ne sai na fitar da ita cikin wannan wuri, in hutar da ita da wannan aljani. Ta yi dariya, ta ce, “Ya shugabana, ka rufa wa kanka asiri, mu yi zamam mu a haka, cikin kwana goma kana da tara Ifiritu yana da daya, wannan ma ai ya ishe mu. Amma ina ji maka tsoron ka ce za ka fitar da ni daga wannan wuri.”

Da yake sonta ya riga ya mamaye zuciyata, sai na ce da ita, “Ki shafa rubutun kubbar nan, ki kirayi Ifiritu ya zo, ni kuwa na sare kansa da takobin nan in kubutar da ke daga gareshi, ni na saba da kisan Ifiritai.”

Koda yarinya ta ji zance na, sai ta yi waka ta na cewa, “Ya mai neman rabuwa, ka jinkirta da hilarka, ganinka ya ishe ni bege, ka hakura, karshen haduwa rabuwa.”

Koda na ji wannan waka tata, ban waiwaya zuwa ga zancenta ba. Ban san lokacin da na shuri kubbar nan ba, shuri mai karfi. Da yarinya ta ga haka, sai ta rikice, ta fashe da kuka ta ce, “Wallahi ka cuce ni, amma ka yi gaggawa ka tserad da ranka, ka fita ta wurin da ka shigo, babu makawa tunda aka bugi kubbar nan, yanzu Ifiritu zai bayyana, ya ko halaka ka, ya halaka ni.”

Don tsananin tsoro, ya shugabata, na manta takalmi na da gatari na a cikin ramin nan. Yayin da na hau mataka ta biyu, na waiwaya don in duba, na ga kasa ta kece, Ifiritu ya fito mai mummunar magana.

Na ji ya ce, me ya same ki, ki ka yi kira na a wannan lokaci? Ta ce, wani abu bai same ni ba face zuciyata ta kuntata, ina so in sha abin shan da zai sanyaya zuciyata. Na tashi domin dauko abinsha, sai na fadi bisa ga kubbar.

Ifiritu ya ce da ita, karya ki ke, fajira! Ya duba cikin soron sai ya ga gatarina da takalmi, ya ce da ita, wannan ba kayan mutum ba, bil Adama. Wa ya zo miki da su?

Yarinya ta ce, ni ban gan su ba face yanzu da ka shigo nan, wata kila kai ne ka shigo da su, suna a jikinka ba tare da ka sani ba.

Ya ce, karya ki ke, wannan zancen banza ne, ba shi yiwuwa gareni in shigo da wadan nan kaya ba tare da na sani ba. Amma da sannu zan kamo wanda ya shigo da su nan in zo miki da shi. Sannan ya tsiraita ta, ya daure ta bisa ga shisshinai hudu. Ya zama yana azabtar da ita domin ta fada masa gaskiya, amma bai ji kukanta ba. Ta yi kurum.

Na fito ta bisa ga tsanin ina firgitacce, jikina na rawa. Yayin da na taka doron kasa, na mayar da rufin ramin kamar yadda yake. Na yi nadama bisa ga abin da na aikata, gayar nadama. Na tuna yarinya da kyawunta, da yadda wannan la’anannen ke azabtar da ita bayan ta kasance tare da shi tsawon shekaru masu yawa bai azabta ta ba, sai ta sanadiyyar zuwana gare ta. Na tuna ubana da mulkinsa, da yadda na zama mai sai da itace, sai na waka wannan baiti na ce: “Idan zamani ya zo ma ka da musiba wata rana, wata rana ka ga sauki, wata rana ka ga tsanani.”

Na tafi har na zo ga abokina madinki, na same shi yana hura wuta a gaban rumfarsa, ya fito waje yana duban hanyata. Da ya gan ni, ya yi murna ya ce, “Ni na kwana jiya ina tunaninka ina jin tsoron ko ka hadu da miyagun namun daji ko wani hatsari. Na gode Allah da ya maido ka lafiya.”

Na gode masa bisa ga tausayinsa da kulawarsa a gare ni. Na shiga cikin rumfata, na zauna ina tunanin abin da ya gudana gare ni, ina zargin kaina bisa ga shurin kubbar nan da na yi.

Daga nan sai ga abokina madinki ya shigo gare ni ya ce, “Wani mutum, Ajami, ya zo yana neman ka, da gatarinka a gare shi da takalminka. Ya ce abokanka ne, masu saran icce suka yiwo masa kwatance da kai, bayan ya tsinci gatarinka da takalmi a daji, shi ne yanzu ya kawo maka. Yana nan zaune cikin rumfata yana jiranka.”

Yayin da na ji wannan zance, nan take kamata ta sake, hankalina ya tashi, domin na gane ko wane ne Ajamin nan, ba kowa ba ne face Ifiritu, ya rikida mutum domin ya zo ya tafi da ni ya hallaka ni.

Ko kafin na bayyana wa madinki halin da na ke ciki, sai kasa ta tsage a gabanmu, Ifiritu ya fito ya sure ni, ya yi sama da ni, bayan wani dan lokaci kankane, ya komo kasa da ni, sai ga mu a cikin ramin nan, inda na tarar da yarinya. Koda na duba haka, sai na ga yarinya a daure, tsirara, jini na gudana daga gefenta. Idanuna suka kada, hawaye ya zubo mini.

Ifiritu ya rike ta, ya ce da ita, “Ya munafuka, ba wannan ne abin begenki ba?” Ta dubo zuwa gare ni ta ce da shi, “Ban san shi ba, ban taba ganin sa ba cikin raina, bai halatta ba gare ni in yi masa karya.”

Ifiritu ya ce, “Idan gaskiya ne maganar da kike fada, dauki takobi ki sare kansa.”

Ta dauki takobi, ta tsaya bisa ga kaina, na yi mata ishara da kundukuki na, hawaye na gudu. Ta yi mini ishara da cewa kai ne ka aikata wannan duka gare mu, da ba ka shuri kubbar ba, da yanzu muna nan hankalinmu kwance. Ta daga takobi sama za ta sare mini kai. Ta jefar da ita gefe, ta fadi kasa ta na kuka.

Yayin nan Ifiritu ya dauko takobi ya mika mini, ya ce da ni ka sare wuyanta ka kubutar da kanka, in sake ka, in dauke ka im mayar da kai ga ubanka, domin ni, na san labarinka duka. Na riki takobi, na gabata ga yarinya. Na daga takobi sama zan sare kanta, sai na ga hawaye na gudana a idanunta, sai takobi ya subuce daga hannuna, ya fadi kasa.

Na dubi Ifiritu na ce, “Ya kai Ifiritu, mai girma, sadaukin shugaba, idan har wannan yarinya, mai karamin hankali da tunani, ta kasa sare mini kai, ta yaya ni da hankalina zan sare wuyanta ba tare da laifin kome ba? Yadda bai halatta gareta ta sare wuyana ba, haka ba ya halatta gare ni in sare nata. Ba ni aikata haka har abada.”

Ifiritu ya yi fushi, fushi mai tsanani, kamarsa ta juya, ya yi mana tsawa har sai da kasa ta girgiza, ya ce, “Kaiconku ya fajirai! Ya tabbata ke nan da so a tsakaninku, hakika sai na yi muku azaba, azaba mai tsanani wadda za ku gwammace da daya ya kashe daya daga cikinku.

Sai gobe Zamu Cigaba a na 7007. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (3)

Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da labarta wa yarinya, shugabar yam mata, da sauran jama’a hikayarsa, da dalilin da ya sa ya rasa idaniyarsa daya. Ya ce, “Kuna jin zance na? Ya yin da Ifiritu ya ga babu wanda zai iya kashe wani, tsakanin ni da yarinya, sai ya ce, kaiconku! Cewa tsakaninku da so! Ya dauki takobi ya sare hannun yarinya na dama, ya kuma sare na hagu, sannan ya sare kafarta ta dama, ya kuma sare ta hagu. Ni ko ina gani da idona.

Na sakankance da mutuwata, na dubi yarinya, ta yi ishara gare ni da idonta, Ifiritu ya gan ta. Ya ce da ita, kin yi zina da idonki! Ya sa takobi ya fille kanta. Ya waiwayo zuwa gare ni, ya ce, ya kai mutum, mu, ga shari’armu, idan mace ta yi zina, kisanta ya halatta gare mu. Wannan yarinya na zaro ta cikin daren amarcinta, ta na ‘yar shekara goma sha biyu ba ta san kowa ba, face ni.

Na kasance ina zuwa gareta sau daya cikin kwanaki goma, na kan zo mata ne a siffar mutum, Ba’ajami. Yanzu na sakankance ta ha’ince ni, shi ya sa na kasheta, amma kai bai kamata ka ha’ince ni game da ita ba. Amma babu makawa in wofinta ka, in rabu da kai lafiya, amma ba ni kashe ka.

Ifiritu ya tambaye ni, wace irin cuta na ke so ya cuce ni? Na yi farin ciki da murna mai yawa, na yi tsammani ko zai yafe mini. Na ce da shi me zan roke ka, ka yi mini? Ya ce, ka tambaye ni, wace sura, cikin halittu, ka ke so im mayar da kai? Ko kare, ko jaki, ko biri, ko kuma wata sura dabam?

Na ce da shi, ina tsammani za ka yafe ni, ya kai shugaban aljannu, sai Allah shi jikan ka. Na marairaita gare shi gayar marairaita, ina rokonsa yafuwa.

Ya ce da ni, kada ka tsawaita mini magana, amma kada ka ji tsoron kisa, don ba zan kashe ka ba, amma ba ni yafe maka har abada. Babu makawa in sihirce ka. Ya dauke ni, ya kada da ni zuwa ga bisa, har na ga duniya daga karkashina, ka ce ita kwaryar ruwa ce. Yayin nan ya sauko kasa da ni, ya ajiye ni bisa ga dutse, ya debo ruwa kadan, ya gama da kasar bisa dutsen, ya karanta wani zance, wanda ban fahimta ba, cikin ruwan, ya watsa mini shi, ya ce, fita daga wannan sura zuwa ga surar biri a cikin wannan lokaci! Nan take na rikide, na zama biri, mai shekara dari.

Lokacin da na ga kaina cikin wannan mummunar sura, na yi kuka bisa ga raina, na hakura bisa ga karkatar zamani, na sani zamani bai bar kowa ba. Na gangaro daga saman dutsen zuwa ga karkashinsa, na yi tafiya wata guda cur, sannan na iso bakin gabar Baharal Maliha, na tsaya sa’a guda, sai na hango jirgi a tsakiyar Bahar, iska ta yi masa kyawo, ya nufo tudu.

Bayan jirgin ya dangana jikinsa da kasa, sai na lababo na shige ciki. Da mutanen ciki suka gan ni, sai daya daga cikinsu ya ce, mu fitad da wannan shu’umi daga jirgimmu. Wani ya ce, mu kashe shi! Wani kuma ya ce, tsaya in kashe shi da wannan takobi! Ya zaro takobi. Na yi kuka har hawayena ya gudana. Babbansu ya ji tausayina, ya ce, ya fatake, ku sani, wannan biri ya nemi ceto gare ni, don haka na cece shi, ku bar shi cikin kuyangi na, kada kowa ya cuce shi.

Yayin nan uban tafiya ya kasance yana kyautata mini, komai na fada masa yakan fahimta, ina biya masa bukatarsa zuwa ko ina. Ina bauta masa cikin jirgi.

Jirgi ya dace da yanayin Bahar mai dadi, bayan kwana hamsin, muka isa wani Birni mai girma da yawan jama’a, babu mai sanin adadinsu face Allah, Madaukakin Sarki. Da muka iso, muka tsayar da jirgimmu, sai ga masinjojin Sarkin garin. Suka shiga cikin jirgi suna yi wa mutane maraba da zuwa, sannan kuma suka ce, Sarki ya aiko mu zuwa gare ku da wadan nan takardu, ko wanne dayanku shi rubuta shadara na jawabin kayansa.

Na tashi, ina cikin surar biri, na karbi takardu a hannunsu, suka ji tsoron kada in yayyaga su, in zuba cikin ruwa, suka hanani, suka nemi su kashe ni. Na yi musu ishara da cewa, ni ma zan rubuta. Uban tafiyar mu ya ce, ku barshi, shi rubuta! In ya yayyaga takardun, ko ya bata rubutun, mu kore shi daga gare mu, in ya kyauta mu rike shi. Yalla ni, ban taba ganin biri mai fahimta irin tasa ba.

Aka ba ni takarda, na riki alkalami na sa a cikin taddawa, na rubuta shadara, na tsara wannan waka ina cewa, “Hakika Allah ya rabanta ni, zamani ya hukunta alherinsa gare ni bayan mugunta tasa. Ya uban tafiya, alherinka gareni ba ya kidayuwa, Allah ba ya maraita talikkai idan kana nan, cewa kai, alherinka ya mayi mamayin uba.”

Sannan kuma na rubuta, “Idan an bude taddawar daukaka da ni’ima, ka tsoma alkalaminka na daga baiwa da karimci, ka rubuta alheri, in ka kasance mai iko, da haka nan ake daukaka madaukakiyar daraja.”

Bayan na gama rubutu, na mika musu takarda. Masinjoji suka tattara takardu, suka tafi da su zuwa ga Sarki. Lokacin da Sarki ya karanta abinda ke cikin dukkan takardun nan, rubutun kowa bai kayatar da shi ba face rubutuna.

Sarki ya ce da masinjojinsa, ku tafi ga wanda ya yi wannan rubutu, ku tufasassheshi wannan riga, ku hawar da shi bisa ga alfadara, ku zo da shi da kida, ku hallaro shi gabana.

Ko da masinjoji suka ji zancen Sarki, sai suka yi murmushi. Da Sarki ya ga haka, sai yayi fushi, ya ce, yaya zan umurce ku da umurni na daga bakina, ku yi mini dariya?

Suka ce, ya Sarki, ba mu yi dariya ga zancenka ba, face da cewa, wanda ya rubuta wannan takarda ba mutum ba ne, biri ne, yana tare da shugaban masu jirgin.

Sarki yayi al’ajabin zancensu, ya yi nishadi da farin ciki, ya ce, ina so in sayi wannan biri, mai hikima da ilimi. Ya aika manzanni zuwa ga shugaban jirgi da alfadara, da tufafi, ya ce, babu makawa a tufatar da birin nan a aza shi bisa alfadara, a zo mini da shi, da kade-kade da bushe-bushe.

Da manzanni suka ji haka, suka fuskanta zuwa ga mai jirgi, suka riko ni daga gareshi, suka sa mini tufafi na alfarma, aka aza ni bisa alfadara, ana yi mini kida da busa. Mutanen cikin jirgi suka dimauta da ganin haka, suka zama suna kallona cikin mamaki.

Yayin da na tsinkayo fada, na yi farin ciki, aka kawo ni gaban Sarki. Yayin da na gan shi, sai na durkusa na gayar da shi sannan na zauna bisa ga gwiwowina. Fadawa suka yi al’ajibin ladabina. Sarki ya zura min ido cikin mamaki da wannan abu da na yi.

Sarki ya umurci mutane da su watse daga fada, duka suka watse, wani bai yi saura ba a cikin fadar face ni da Sarki, da kuyangi, da kananan bayi. Sarki ya yi umurni da a kawo abinci da abinsha. Aka hallaro da su da gaggawa. Aka gabatar da kabaki da dukkan abin da rai ke sha’awa ke jin dadi a cikinsa, abin kallo ga ido. Sarki yayi ishara gareni da cewa in ci.

Na tashi na durkusa, na yi godiya, yayin nan na zauna ina cin abinci tare da shi. Na ci ya isheni, na wanke hannuwana, na dauki takarda da alkalami da taddawa na rubuta wannan waka, na ce: ” Yau na ci tsokar rago, maganin dukan ciwarwata, na ga kabakin da abin marmari ke cikinsa, matukar buri. Ya bakin cikin zuciyata bisa ga wannan kabaki, yayin da na ishe shi da abin da ban sani ba, an darwaye shi da mai gami da zuma.”

Sarki ya duba abin da na rubuta, ya karanta shi, ya yi al’ajibi da shi, ya ce, lalle akwai ga biri wannan fasaha da wannan rubutu, hakika ban taba ganin dabba mai hankali da kuma hikama tamkar wannan biri ba. Yayin nan ya gabatad da dara, ya ce da ni, ka iya wannan wasa? Na yi ishara da kai na, na ce, na’am!

Na gabata na jeranta dara dai dai sahunta, muka yi wasa da shi sau biyu, na rinjaye shi. Hankalin Sarki ya tashi, ya ce, hakika wannan da bil Adam ne, da ya fi dukan mutanen zamaninsa ilimi da fasaha. Yayin nan ya ce da wata kuyangarsa, ki tafi zuwa ga shugabarki, ki ce da ita, Sarki ya ce, ta zo ta yi wasa da wannan biri ta yi kallon abin al’ajibi!

Kuyanga ta tafi, ta dawo tare da shugabarta, ‘yar Sarki. Koda ta shigo ta gan ni sai ta rufe jikinta ta ce, ya mahaifina, ta yaya za ka aika mini in zo in ga maza, ajanabai? Ya ce, ya ‘yata, babu wani namiji a nan sai ni, sai ko wannan biri, wadan nan saura kuma duka kuyangin ki ne. Wa kike rufewa jikin ki a nan?

Ta ce, wannan biri dan Sarki ne, sunan ubansa, Imar, ma’abucin jazirorin Labunus, an sihirce shi ne biri. Ba kowa ne ya sihirce shi ba face Ifiritu wanda ake kira Jarjarisu na daga zuri’ar Ibilisa. Amma wannan ba biri ne ba, cewa shi namiji ne, masani, mai hankali.

Sarki ya yi al’ajibin wannan zance na ‘ya tasa, ya dubo zuwa gare ni, ya ce, yalla abin nan da ta fada mini gaskiya ne? Na ce da kaina, na’am!

Sarki ya ce ma ‘ya tasa, A ina kika san shi? Da kaka kika sani shi sihirtachche ne? Ta ce, Ya ubana, tsohuwa ta kasance a gare ni tun ina yarinya, makira, sahira, ta sanashshe ni sana’ar sihiri, na boye shi, na tsoraci Allah, Ubangijina, amma na kiyaye shi. Na san kofa dari da saba’in daga kofofin sihiri, mafi karanta daga kofofin nan in cire duwatsun Birninka, in jefa su bayan Dutsin Kaf, im maishe shi kogi, im mai da mazaunansa kifi a cikin kogin.

Ubanta ya ce da ita, Don girman sunan Allah, mai-girma, ki kubutad da wannan yaro, in sa shi Wazirina. Yalla kina da wan nan alheri, wata kila shi amfane ki? Idan kin kubutad da shi, in sa shi Waziri, domin shi saurayi ne, mai mukami, da hankali. Ta ce da shi, So da girmamawa!
Yayin nan ta rike wuka rubutacciya da sunannakin Ibraniya, ta zana da ita hatimi a cikin tsakar soron, ta rubuta sunannaki a cikinsa da dalamusai, ta yi anniya da wani zance, tana karatu da halshen da ba shi fahimtuwa. Bayan jimawa jihohin soro suka duhunta gare mu, har muka zaci duniya ta nade bisa ga kammu. Daga nan sai ga Ifiritu ya bayyano bisa gare mu cikin mugunyar sura da hannuwa kamar reshe, da Kafafu tamkar soraye, da idanduna tamkar murhun da aka hura wuta a cikinsa.
Muka firgita da shi. ‘Yar Sarki ta ce, Babu maraba gare ka, babu farin ciki! Ifiritu ya ce, Ya ha’ina, yaya kika ha’inci rantsuwa? Ba mun rantse bisa ga babu mai-bijiram ma wani, ni da ke ba? Tace, Ya la’ananne, ina kai, balle rantsuwarka? Ifiritu ya yi kururuwa har sai da kasa ta girgiza kamar za ta tsage, ya juye siffar zaki ya tasam ma yarinya ‘yar sarki zai halaka ta.

Sai gobe Zamu Cigaba a na 8008. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (4)

Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da ba da labarinsa, ya ce: Yayin da Ifiritu ya rikida zuwa siffar zaki ya tasar wa yarinya, ‘yar Sarki, bakinsa a bude zai halaka ta. Yarinya ta yi gaggawa ta ciri gashi daya daga gashin kanta, ta shafe shi da yawun bakinta, nan take ya zama takobi, mai zarcewa, ta sare wannan zaki, ya rabu biyu. Nan take ya koma Ifiritu, ya hade wuri daya.

Yarinya kuma ta juye macijiya, mai girma, ta zabura bisa ga wannan la’ananne. Suka yi fada, fada mai tsanani. Da Ifiritu ya ga yarinya ta kusa ta rinjaye shi, sai ya rikida ya zama tsibiri a tsakiyar tabki, da kuraye a kan tsibirin. Yarinya kuma ta zama iska, mai karfi, ta kafe wannan tabki, sannan kuma ta zama mazaje tamkar mutum dari, kowanne rike da makami, suka taru suka karkashe wadannan kuraye.

Da Ifiritu ya ga ba dama, sai ya zama kwayoyin hatsi, a barbaje, ko ina. Yarinya kuma ta rikida zakara, ta bi duk ta tsince kwayoyin hatsin nan, sai kwaya daya ce ta boye daga ganin zakaran, bai tsince ta ba.

Daga nan sai muka ji an yi wata kururuwa, kururuwar da ta dimauta mu, cewa soron da muke ciki ya rushe bisa kammu. Daga nan sai ga wani babban tabki na ruwa ya bayyana a gabammu. Kwayar nan daya ta hatsi da zakara bai cinye ba, ta gangara ta fada cikin ruwa, nan take ta rikede zuwa kifi, ya nitse cikin ruwan.

Daga nan sai zakaran ya daga kansa sama, ya yi cara, ya kada fukafukansa sannan ya juye babbar kifanya a cikin ruwan, ta yi nitso ta faku daga ganimmu zuwa sa’a guda. Can, sai muka ji wata irin kururuwa madaukakiya, muka tsorata. Bayan haka Ifiritu ya fito, wuta na fita daga bakinsa da kofofin hancinsa. Muka yi kusa mu nitsa cikin kasa don tsoro bisa ga rayukammu na daga konewa da hallaka.

Daga nan sai ga yarinya ta fito daga ruwan nan, cikin siffarta ta mutum, babu wani abu da ya sameta na daga rauni. Ifiritu ya juyo wajen da muke ya buso mana wutar nan

Please Login or Register in order to submit comment