Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

da ke fita daga bakinsa zuwa ga fuskokimmu. Yarinya ta yi sauri ta shiga tsaknimmu da wutar da Ifiritu ya buso mana domin ta karemu daga hallaka.

Duk da yarinya ta kare wutar da jikinta, sai da tartsatsinta ya riskemu, tartsatsin garwashi ya sameni ga idaniyata, ta hagu, nan take ta tsiyaye, na zama mai ido daya a cikin wannan lokaci, duk dai ina cikin siffar biri da Ifiritu ya mayar da ni. Tartsatsi ya sami Sarki ga fuskarsa, rabinta ya kone da gemunsa da habarsa, hakoransa suka zube. Tartsatsin ya kuma sami wasu daga cikin kuyangin da muke tare da su a wannnan wuri, wasu suka mutu nan take, wasu suka sami raunuka. Muka sakankance da halaka, muka debe kauna daga rayuwa.

Muna cikin haka, sai mu ka ji mai fada ya na fada, “Allah mai girma! Allah mai girma! Ubangiji ya yi budi da nasara tasa, wanda ya kafirta ya tabe, yayin da ya yi butulci da addinin shugabam mu, Muhammadu, shugaban talikkai.” Daga nan sai muka ga yar Sarki ta yi fushi, fushi mai tsanani akan raunin da Ifiritu ya yi ma ta, lokacin da ta ke kokarin kare mu da jikinta daga wutar da ya feso mana, da kuma raunukan da muka samu daga tartsatsin wutar, yayin nan ta yi wani kalar sihiri ta jefi Ifiritu da shi, nan take ya kone, ya zama toka da gawayi.

Yarinya ta zo gare mu, cikin matsanancin ciwo, ta ce, ku zo mini da tasa da ruwa in kubutar da wannan bawan Allah kafin ta Allah ta kasance a gare ni. Aka zo da shi zuwa gare ta, ta yi wani zance wanda ba a fahimta a cikin ruwan. Yayin nan ta yayyafa mini, ta ce, ka kubuta da girman gaskiya da girman sunan Allah, mai girma, ya zuwa ga siffarka ta farko!

Nan take na koma mutum, kamar yadda ni ke da farko, sai dai babu idaniya daya. Yarinya ta ce da ni, wuta wuta ce, ni ba ni da ikon mai da wani abu na daga idaniyarka da ka rasa, wannan kaddara ce daga Allah, ka gode ma sa da ba ka rasa ranka ba. Ka sani cewa, Ifiritu ya sami damar raunata ku, gami da ni, saboda rashin ganin kwayar hatsin nan daya da ban yi ba lokacin da na ke tsince hatsin, wannan kwaya ta kasance ita ce ta ke dauke da ran shi, da na tsince ta, da ya mutu a cikin wannan sa’a.

Ya kasance ya na bude mini kofa ta sihiri ina bude ma sa ma fi girma daga ta sa, har ya bude mini kofar wuta. Wa ake bude wa kofar wuta ya tsira daga gareta? Cewa kaddara ta taimakeni bisa gare shi har na kone shi. Wannan taimako ne daga Allah madaukakin Sarki. Daga nan sai ta ce, na shaida babu Sarki sai Allah, Muhammadu manzon Allah ne, sai ta fadi, ranta ya fita.

Mu ka yi bakin cikin mutuwarta, na yi burin da ma ba ta kara jikinta ga wutar nan da Ifiritu ya feso ba, domin ta karemu daga halaka, ga shi ita ta halaka kanta wajen ceton rammu, sai dai cewa, ba a juyad da hukuncin Allah.

Yayin da Sarki ya ga ‘yar sa ta fadi ta mutu, ya fige sauran gemunsa ya na marin fuskar sa, ya yayyaga tufafinsa. Na aikata tamkar yadda ya aikata, muka zauna muna kuka. Lokacin da Hakimai da fadawa suka shigo, suka ishe mu cikin wannan hali, suka yi mamakin abin da ya faru, suka kewaye gefen Sarki sa’a guda.

Lokacin da hankalin Sarki ya dawo, ya labartawa fadawa abin da ya faru tsakanin ‘yarsa da Ifiritu. Aka yi masa gaisuwa kwana bakwai, yayin nan ya yi umurni da gina kubba a wurin da aka yi wa ‘yarsa kabari. Aka kunna fitilu da shama’u a ciki. Tokar Ifiritu kuwa, aka hau dogon tsauni aka sheka ta, iska ta tafi da ita, Allah ya la’ance shi.

Wata rana Sarki ya kira ni, ya ce da ni, ya saurayi, mun zauna zamanim mu a cikin dadin rai da aminci, muna tsararru daga musibun zamani, sai da ka zo, musibu suka sabkam mana. Kaito ni! Da ban gane ka ba, da lokacin da na gane ka, in kore ka ga mugunyar zuwan ka, wadda sababin ta na rasa ‘yata da na ke matukar so, na rasa hakorana, rabin fuskata ya kone, amma ba laifinka ba ne, wannan hukunci ne na Allah da ya kasance a garemu, da kai duka. Yabo ya tabbata ga Allah da ‘yata ta kubutad da kai, ta halakad da Ifiritu tare da kanta.

Ka fita, ya da na, daga gari na, abin da ya gudana sababinka ya ishemu, ka fita da lafiya, domin ganin ka kusa dani zai ci gaba da tuna mini da mutuwar ‘yata.

Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da ba wa yarinya, shugabar yam mata, da sauran yam mata biyu, Jekadiya da Mai jiran kofa, da samari biyu, masu ido dai daya, da Dan Dako, da su Halifa da Wazirinsa Ja’afaru, da Sarkin Fadansa Masururu, suna cikin siffar fatake, da bakaken bayin yarinya su bakwai rike da takubba a hannuwansu, cewa:

Na fita, ya shugabata, daga wannan birni, ban gasgata da kubuta ta ba, ban san inda na fuskanta ba, na damu da zuciyata da abin da ya faru gareni. Na yi tafiya tsawon wata guda ina tunanin yadda na fito gida, da yadda yan fashi suka tarwatsa tawagarmu, da shigata Birni ina bako, da gamuwata da madinki, da yadda na zama mai sayar da ice, da gamuwata da yarinya ‘yar Sarkin Hindu a karkashin kasa, da kubuta ta daga Ifiritu bayan ya kashe yarinya ya mayar da ni biri. Na tuna abin da ya faru gare ni, tun daga farko har karshe, na gode wa Allah na ce, ga idaniyata ya kare ba ga raina ba.

Na ci gaba da tafiya, har Allah ya kawo ni wannan gari na Bagadada ko na sadu da Sarkin Musulmi, Halifa, in labarta masa da abin da ya gudana a gareni. Kafin na shigo, na tsaya bakin gari na aske gemuna, na shigo wannan gari cikin dare, ina madimauci, ban san inda zan nufa ba. Sai na ga wannan saurayi na fari, mai ido daya, yana tsaye, na yi masa sallama, ya amsa mini. Na ce, ni bako ne. Ya ce mini, shima bako ne, yanzu ya shigo, bai san inda zai nufa ba.

Muna nan tsaye, sai ga wannan saurayi na uku, yayi mana sallama, muka mayar ma sa. Ya ce shi bako ne. Muka ce, mu ma baki ne. Muka shigo cikin gari, har Allah ya sa muka iso wannan gida na ku, muka nemi ku saukar da mu zuwa wayewar gari. Ku ka amince da bukatar mu, har abun da ya faru, ya faru a wannan gida, mu ka sami kammu daurarri cikin igiya. Wannan shine labarina, ya shugabata.

Yarinya, shugabar ‘yam mata, ta ce, wannan labari na ka abin marmari ne da wa’azantarwa ga masu hankali, tube kan ka daga igiya, ka kubuta da ranka. Maza ka kama tafarkinka. Saurayi ya ce ba zai tafi ba har sai ya ji labarin saurayi na uku, mai ido daya, da kuma labarin wadannan fatake, watau Halifa da Wazirinsa da Sarkin Fadansa.

Yarinya ta dubi saurayi na uku, mai ido daya, ta ce, fada mini labarinka, da yadda ka zama mai ido daya sannan ka tube kan ka daga daurin igiya, ka kubutar da ran ka.

Zamuci gaba insha allah gobe008. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Saurayi Na Biyu Mai Ido Daya (4)

Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da ba da labarinsa, ya ce: Yayin da Ifiritu ya rikida zuwa siffar zaki ya tasar wa yarinya, ‘yar Sarki, bakinsa a bude zai halaka ta. Yarinya ta yi gaggawa ta ciri gashi daya daga gashin kanta, ta shafe shi da yawun bakinta, nan take ya zama takobi, mai zarcewa, ta sare wannan zaki, ya rabu biyu. Nan take ya koma Ifiritu, ya hade wuri daya.

Yarinya kuma ta juye macijiya, mai girma, ta zabura bisa ga wannan la’ananne. Suka yi fada, fada mai tsanani. Da Ifiritu ya ga yarinya ta kusa ta rinjaye shi, sai ya rikida ya zama tsibiri a tsakiyar tabki, da kuraye a kan tsibirin. Yarinya kuma ta zama iska, mai karfi, ta kafe wannan tabki, sannan kuma ta zama mazaje tamkar mutum dari, kowanne rike da makami, suka taru suka karkashe wadannan kuraye.

Da Ifiritu ya ga ba dama, sai ya zama kwayoyin hatsi, a barbaje, ko ina. Yarinya kuma ta rikida zakara, ta bi duk ta tsince kwayoyin hatsin nan, sai kwaya daya ce ta boye daga ganin zakaran, bai tsince ta ba.

Daga nan sai muka ji an yi wata kururuwa, kururuwar da ta dimauta mu, cewa soron da muke ciki ya rushe bisa kammu. Daga nan sai ga wani babban tabki na ruwa ya bayyana a gabammu. Kwayar nan daya ta hatsi da zakara bai cinye ba, ta gangara ta fada cikin ruwa, nan take ta rikede zuwa kifi, ya nitse cikin ruwan.

Daga nan sai zakaran ya daga kansa sama, ya yi cara, ya kada fukafukansa sannan ya juye babbar kifanya a cikin ruwan, ta yi nitso ta faku daga ganimmu zuwa sa’a guda. Can, sai muka ji wata irin kururuwa madaukakiya, muka tsorata. Bayan haka Ifiritu ya fito, wuta na fita daga bakinsa da kofofin hancinsa. Muka yi kusa mu nitsa cikin kasa don tsoro bisa ga rayukammu na daga konewa da hallaka.

Daga nan sai ga yarinya ta fito daga ruwan nan, cikin siffarta ta mutum, babu wani abu da ya sameta na daga rauni. Ifiritu ya juyo wajen da muke ya buso mana wutar nan da ke fita daga bakinsa zuwa ga fuskokimmu. Yarinya ta yi sauri ta shiga tsaknimmu da wutar da Ifiritu ya buso mana domin ta karemu daga hallaka.

Duk da yarinya ta kare wutar da jikinta, sai da tartsatsinta ya riskemu, tartsatsin garwashi ya sameni ga idaniyata, ta hagu, nan take ta tsiyaye, na zama mai ido daya a cikin wannan lokaci, duk dai ina cikin siffar biri da Ifiritu ya mayar da ni. Tartsatsi ya sami Sarki ga fuskarsa, rabinta ya kone da gemunsa da habarsa, hakoransa suka zube. Tartsatsin ya kuma sami wasu daga cikin kuyangin da muke tare da su a wannnan wuri, wasu suka mutu nan take, wasu suka sami raunuka. Muka sakankance da halaka, muka debe kauna daga rayuwa.

Muna cikin haka, sai mu ka ji mai fada ya na fada, “Allah mai girma! Allah mai girma! Ubangiji ya yi budi da nasara tasa, wanda ya kafirta ya tabe, yayin da ya yi butulci da addinin shugabam mu, Muhammadu, shugaban talikkai.” Daga nan sai muka ga yar Sarki ta yi fushi, fushi mai tsanani akan raunin da Ifiritu ya yi ma ta, lokacin da ta ke kokarin kare mu da jikinta daga wutar da ya feso mana, da kuma raunukan da muka samu daga tartsatsin wutar, yayin nan ta yi wani kalar sihiri ta jefi Ifiritu da shi, nan take ya kone, ya zama toka da gawayi.

Yarinya ta zo gare mu, cikin matsanancin ciwo, ta ce, ku zo mini da tasa da ruwa in kubutar da wannan bawan Allah kafin ta Allah ta kasance a gare ni. Aka zo da shi zuwa gare ta, ta yi wani zance wanda ba a fahimta a cikin ruwan. Yayin nan ta yayyafa mini, ta ce, ka kubuta da girman gaskiya da girman sunan Allah, mai girma, ya zuwa ga siffarka ta farko!

Nan take na koma mutum, kamar yadda ni ke da farko, sai dai babu idaniya daya. Yarinya ta ce da ni, wuta wuta ce, ni ba ni da ikon mai da wani abu na daga idaniyarka da ka rasa, wannan kaddara ce daga Allah, ka gode ma sa da ba ka rasa ranka ba. Ka sani cewa, Ifiritu ya sami damar raunata ku, gami da ni, saboda rashin ganin kwayar hatsin nan daya da ban yi ba lokacin da na ke tsince hatsin, wannan kwaya ta kasance ita ce ta ke dauke da ran shi, da na tsince ta, da ya mutu a cikin wannan sa’a.

Ya kasance ya na bude mini kofa ta sihiri ina bude ma sa ma fi girma daga ta sa, har ya bude mini kofar wuta. Wa ake bude wa kofar wuta ya tsira daga gareta? Cewa kaddara ta taimakeni bisa gare shi har na kone shi. Wannan taimako ne daga Allah madaukakin Sarki. Daga nan sai ta ce, na shaida babu Sarki sai Allah, Muhammadu manzon Allah ne, sai ta fadi, ranta ya fita.

Mu ka yi bakin cikin mutuwarta, na yi burin da ma ba ta kara jikinta ga wutar nan da Ifiritu ya feso ba, domin ta karemu daga halaka, ga shi ita ta halaka kanta wajen ceton rammu, sai dai cewa, ba a juyad da hukuncin Allah.

Yayin da Sarki ya ga ‘yar sa ta fadi ta mutu, ya fige sauran gemunsa ya na marin fuskar sa, ya yayyaga tufafinsa. Na aikata tamkar yadda ya aikata, muka zauna muna kuka. Lokacin da Hakimai da fadawa suka shigo, suka ishe mu cikin wannan hali, suka yi mamakin abin da ya faru, suka kewaye gefen Sarki sa’a guda.

Lokacin da hankalin Sarki ya dawo, ya labartawa fadawa abin da ya faru tsakanin ‘yarsa da Ifiritu. Aka yi masa gaisuwa kwana bakwai, yayin nan ya yi umurni da gina kubba a wurin da aka yi wa ‘yarsa kabari. Aka kunna fitilu da shama’u a ciki. Tokar Ifiritu kuwa, aka hau dogon tsauni aka sheka ta, iska ta tafi da ita, Allah ya la’ance shi.

Wata rana Sarki ya kira ni, ya ce da ni, ya saurayi, mun zauna zamanim mu a cikin dadin rai da aminci, muna tsararru daga musibun zamani, sai da ka zo, musibu suka sabkam mana. Kaito ni! Da ban gane ka ba, da lokacin da na gane ka, in kore ka ga mugunyar zuwan ka, wadda sababin ta na rasa ‘yata da na ke matukar so, na rasa hakorana, rabin fuskata ya kone, amma ba laifinka ba ne, wannan hukunci ne na Allah da ya kasance a garemu, da kai duka. Yabo ya tabbata ga Allah da ‘yata ta kubutad da kai, ta halakad da Ifiritu tare da kanta.

Ka fita, ya da na, daga gari na, abin da ya gudana sababinka ya ishemu, ka fita da lafiya, domin ganin ka kusa dani zai ci gaba da tuna mini da mutuwar ‘yata.

Saurayi na biyu, mai ido daya, ya ci gaba da ba wa yarinya, shugabar yam mata, da sauran yam mata biyu, Jekadiya da Mai jiran kofa, da samari biyu, masu ido dai daya, da Dan Dako, da su Halifa da Wazirinsa Ja’afaru, da Sarkin Fadansa Masururu, suna cikin siffar fatake, da bakaken bayin yarinya su bakwai rike da takubba a hannuwansu, cewa:

Na fita, ya shugabata, daga wannan birni, ban gasgata da kubuta ta ba, ban san inda na fuskanta ba, na damu da zuciyata da abin da ya faru gareni. Na yi tafiya tsawon wata guda ina tunanin yadda na fito gida, da yadda yan fashi suka tarwatsa tawagarmu, da shigata Birni ina bako, da gamuwata da madinki, da yadda na zama mai sayar da ice, da gamuwata da yarinya ‘yar Sarkin Hindu a karkashin kasa, da kubuta ta daga Ifiritu bayan ya kashe yarinya ya mayar da ni biri. Na tuna abin da ya faru gare ni, tun daga farko har karshe, na gode wa Allah na ce, ga idaniyata ya kare ba ga raina ba.

Na ci gaba da tafiya, har Allah ya kawo ni wannan gari na Bagadada ko na sadu da Sarkin Musulmi, Halifa, in labarta masa da abin da ya gudana a gareni. Kafin na shigo, na tsaya bakin gari na aske gemuna, na shigo wannan gari cikin dare, ina madimauci, ban san inda zan nufa ba. Sai na ga wannan saurayi na fari, mai ido daya, yana tsaye, na yi masa sallama, ya amsa mini. Na ce, ni bako ne. Ya ce mini, shima bako ne, yanzu ya shigo, bai san inda zai nufa ba.

Muna nan tsaye, sai ga wannan saurayi na uku, yayi mana sallama, muka mayar ma sa. Ya ce shi bako ne. Muka ce, mu ma baki ne. Muka shigo cikin gari, har Allah ya sa muka iso wannan gida na ku, muka nemi ku saukar da mu zuwa wayewar gari. Ku ka amince da bukatar mu, har abun da ya faru, ya faru a wannan gida, mu ka sami kammu daurarri cikin igiya. Wannan shine labarina, ya shugabata.

Yarinya, shugabar ‘yam mata, ta ce, wannan labari na ka abin marmari ne da wa’azantarwa ga masu hankali, tube kan ka daga igiya, ka kubuta da ranka. Maza ka kama tafarkinka. Saurayi ya ce ba zai tafi ba har sai ya ji labarin saurayi na uku, mai ido daya, da kuma labarin wadannan fatake, watau Halifa da Wazirinsa da Sarkin Fadansa.

Yarinya ta dubi saurayi na uku, mai ido daya, ta ce, fada mini labarinka, da yadda ka zama mai ido daya sannan ka tube kan ka daga daurin igiya, ka kubutar da ran ka.009. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA
Labarin Saurayi Na Uku Mai Ido Daya (1)

Saurayi na uku, mai ido daya, ya gabata a gaban yarinya, ya ce, ya ke, shugaba mabayyaniya, kissata ba ta kasance tamkar kissarsu ba, a’a, kissata ita ce mafi al’ajabi daga wadannan, domin su kaddara ta zo musu game da hukumci, amma ni, sababin aske gemuna da tallafar idaniyata, ni, na jawo hukumci ga kaina da bakin chiki ga zuciyata.

Ni, na kasance Sarki, dan Sarki, ubana ya mutu, na yi sarauta bayansa, ina hukunci da adalci, ina kyautata ma talikkai. Na kasance mai sha’awar tafiya cikin bahar, Birane da Jazirori ma su ban sha’awa sun kasance a gefen bahar. Na yi nufin in yi yawo bisa ga jazirun. Na sauka da jirage goma, na riki guzurin wata, na tafi kwana ashirin.

A chikin wani dare na darakku iska ta tashi gare mu da iskoki mabambamta, har asbahin ya bayyana, iska ta lafa, bahar ya nitsu, har rana ta yi fari, yayin nan muka daukaka bisa ga jazira. Muka tsinkayi tudu, muka dakata mu ka sami abin da za mu ci, daga cikin guzurim mu, muka ci, muka zauna kwana biyu ga wannan tudu.

Bayan mun gama hutawa, muka tafi kwana ashirin, ruwaye suka canja mana, tafarki ya sa6a. Mai-jirigi ya iso ga wani wuri, ya che wa masu-tsinkaya, Ku duba chikin bahar, mun isa jazira, mai-wuyar hawa.

Yayin nan masu-duba suka duba, suka che, mun gani daga dama kifi bisa ga ruwa, amma mun ga baki daga nesa ga tsakar bahar, wata sa’a baki, wata sa’a fari, wata sa’a shina haske.

Yayin da mai-jirigin ya ji zanchen masu-dubawar, ya buga rawaninsa ga kasa, ya fige gemanya tasa, ya che wa mutane, Ku ji labarin hallakarmu, dukan mu, daya ba shi kubuta a chikinmu. Ya zama shina kuka, mu duka hankalin mu ya tashi bisa ga rayuwammu.

Muka che, Ya mai-jirigi, ka labarta mana da abin da ka gani.

Ya che, Ya shugabana, ka sani, mu, mun 6ata ranad da iskan nan mabambamchiya ta zo mana, ba ta nitsa ba, fache da hantsi, muka zauna kwana biyu, ran nan muka 6ata ga bahar. Ba mu gushe ba madimauta kwana goma sha daya daga wannan dare, har yau ba mu da iska, mai maishe mu ya zuwa ga tafarkimmu;

Idan ranar yau ta kare, a chikin gobe za mu sadu da dutsi na daga bakin dutsin da a ke che ma sa, Dutsin Maganadishu, ruwa ya ja mu tilas zuwa gare shi. Idan mun isa, jirigi zai farfashe, kowanne allo shi tafi chikin ruwa. Idan mun gamu da wannan dutsi, za mu damfara da shi, ba mu sani ba domin Allah ya kaddara wannan dutsi sirri ne ga dukan karfe;

Chewa dukan bakin karife shina tafiya gare shi, karfuna da yawa na tare ga wannan dutsi, babu wan da ya san adadinsu, fache Allah, madaukakin, Sarki; daga dadadden zamani jirage da yawa sun karairaye, jama’a da yawa sun hallaka sababi da wannan dutsi da ke cikin wannan bahar;

A saman dutsen akwai kubba ta farin karfe da tagulla, zamnanniya bisa ga shikashikai goma, da gatari bisa ga kubbar, ba mu san aikinsa ba, da mahayi bisa gare ta, da doki na farin karfe, da mashi na farin karfe a hannun wannan mahayi, rataye ga kirjin mahayin allo na darma, da rubutu a jikinsa sunannaki da dalamusai;

Ya Sarki, iyakar dauwamar wannan mahayi bisa ga wannan doki, jirgagen da suka biya ta karkashinsa, mahayansu duka sun hallaka. Dukan Karfen da ke jikn jirigin shina damfara ga dutsin, babu kubuta, fache wannan mahayi ya fadi daga kan wan nan doki.

Yayin nan mai-jirigin, ya shugabata, ya yi kuka, kuka, maitsanani, muka sakankance mu hallakakku ne babu shakka, kowammu ya yi ban kwana da abokinsa.

Yayin da asbahin ya yi, muka kusato wannan dutsi, ruwa ya jawo mu gare shi dole. Yayin da jiragem mu suka zama daga karkashin Dutsin Maganadishu, suka bugu da shi, suka kyarkeche, suka tarwatse. Akwai daga gare mu wanda ya dulmuya, akwai daga gare mu wanda ya kubuta, amma yawa yawammu sun dulmuya. Wadannan da suka kubuta ba su san junansu ba, domin wannan iska ta sa6a, ta dimauta su.

Ni kuwa, ya shugabata, Allah madaukakin Sarki, ya kubutad da ni, yayin da ya yi nufin shi kuftutad da ni daga azaba da wahala, na hau bisa ga allo na daga allunan jirgin, iska ta jefa shi game da rakumman ruwa zuwa ga dutsi, na samu tafarki, mai-hawa birbishin dutsin tamkar kwaranga, jingine ga dutsin, amma dutsin ne. Na ambachi Allah, madaukakin Sarki.

Chewa saurayi na ukku ya che ma yarinya, da jama’a daurarru, da bayi na tsaye da takubba ga hannuwansu bisa ga kawunan daurarrun, Yayin nan na ambachi Allah, na kiraye shi, na koma zuwa gare shi, na yi dabarar hawa bisa ga dutsen, na zama ina kama hakorin nan majeranta na jikinsa tamkar tsani, har Allah ya lafad da iska ga wannan sa’a, ya taimake ni ga fita, na hau bisa ga dutsi lafiya, na yi murna da kubutata, gayar murna.

Na nufi kubbar nan, wadda mahayi ya ke kanta, na shige ta, na yi salla chikinta raka’o’i biyu, na gode ma Allah bisa ga kubutata. Yayin nan na yi barchi karkashin kubbar, na ji mai fada shina fada a cikin mafarkina, shina chewa, Ya dan Hasibu, idan ka farka daga barchinka, ka tona karkashin kafafunka, za ka ga baka na farin karfe da kibiyoyi ukku na darma, rubutachche da dalamusai;

Ka riki bakan da kibaun, ka harbi mahayin nan da ke bisa kubba, ka futad da mutane da wannan bala’i, mai-girma. Idan ka harbi mahayin, ya abku chikin bahar, bakan zai fadi daga hannunka, ka dauki bakan, ka bisne shi a gurbinsa;

Idan ka aikata haka, bahar ya biche, shi komo, shi daukaka, har shi daidaita da dutsin, ka ga jirgi a chikinsa da mutum a chikin jirigin, wanin wanda ka harbe shi, zai zo gare ka da abinchi tare da shi;

Ka hau tare da shi, kada ka ambaci sunan Allah, zai tafi da kai kwana goma zuwa wani amintaccen bahar. Idan ka isa can ka samu mai kai ka zuwa ga garinku, chewa idan ba ka ambachi Allah ba.

Yayin nan na farka daga barchina, na tashi da nishadi, na tone karkashin kafafuna na dauko bakan nan. Na harbi mahayin, na harbe shi, ya fadi chikin ruwa, baka ya fadi daga hannuna. Na dauki bakan, na bisne shi. Bahar ya tashi, ya daukaka har ya daidaita da dutsin nan da ni ke bisa kansa.

Yayin nan ban zauna ba, fache sa’a, na ga karamin jirgi daga bahar, ya gabato ni. Na gode ma Allah, madaukakin Sarki. Yayin da karamin jirigi ya sadu da ni, na ishe mutum-mutumi a chikinsa na farin karfe da allo ga kirjinsa na darma, rubutachche da sunannaki da dalamusai. Na shiga chikin jirigin, ina kawai, ba ni magana.

Mutum-mutumin nan ya dauke ni ranar fari, da ta biyu, da ta ukku ya zuwa ga chikon kwana goma. Ran nan na ga jazirar aminchi, na yi farin chiki da murna, mai yawa. Don tsananin murnata ban san lokacin da na ambachi sunan Allah ba, ina mai godiya gareshi da ya kubutar da ni.

Ban gama rufe bakina ba sai na ji an

Please Login or Register in order to submit comment