Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

warned you kar ki dinga fadin duk abinda kika gani?.. " da sauri ta Mike daga kan kafar hajiya tace
"ummah am sorry ban karawa... " ta fad'a kaman zatayi kuka,
"good... Daga yau in na karajin Kinyi irin wannan halin sai nasa an zaneki...kuma Aliyu zan saka... " da sauri tace
"wallahi ban karawa... " ta fad'a voice dinta na rawa,
"good gimbiyata... Shi Kuma fav zanyi maganin shi... " ta fad'a mata, ahankali ta maida kai kan kafarta relaxing again, tasleem's character is some how,( if you always read my novels you will know I don't really love my female characters like my male stars amma I love tasleem saboda straight forwardness dinta...)
"yanzu bari kije kitchen ki fad'a masu a hada maki abinda zaki bukata a islamiya..." hajiya ta fad'a mata,
"OK ummah... Amma zaki karamin da kudi kou... Ban amsa wajen mummy ba... " ta fad'a tana mikewa daga kan gadon,
"babu damuwa... Ki. Fad'a masu bisa umarni na a dafa maki abu Mai shegen dadi yanda ke da kawayenki zakuci ku koshi... " inji hajiya,
"tou ummah... " ta fad'a tana Kama hanyar waje, ummah shuru tayi tana kallon bayanta da gashin kanta dake kwance gadon bayanta, Dan goshinta ta dafa not knowing what to think, it's a very difficult decision for her, she never felt so stranded with decision sai yanzu, ita dai har ga Allah tasleem tayi mata, zata fi kowa farin cikin ta ganta as her daughter in-law amma they might be consequences, tasan koda kuwa zata tsallaka ta and choose another person bazata damu ba because she's carefree person, asalima tasan bata damu da yarima ba. Bayan kaman minti goma tasleem ta dawo dakin rige da mug a hannunta na shayi Mai kamshin gaske alaman an zuba kayan yaji sosai, bakin gadon ta zauna ta dinga kurba har ta shanye tas sannan ta ajiye mug din wajen zata hau gado,
"maza maidashi kitchen... " shine umarnin da ummah tayi mata, babu musu ta Mike ta dauka tayi waje dashi, many people will think tasleem is not fit for the prince amma ita hajiya knows her imperfection can be perfect some day, koda nace yarima na Kama da mahaifinshi ba duka ba because he have some of he's mother's characters, ko kadan hajiya b'ata son iya yi, she love someone that is always himself nor matter what.


Wata yarinya ce zaune wacce bazata wuce shekara 20 zuwa 22 ba zaune a wata falo kusa da wata lady da zata kai kusan 30 plus tana rike da yaro a hannunta, magana take mata cikin lafazi Mai sanyi, daga nesa in kaga yanda takewa hannunta while speaking zaka san magiya take mata, sai da na tako kusa daita naji tana Cewa
"Dan Allah anty.. I beg you... Kawai kice Dan uwanshi ne ke son ganin shi... Nasan he will definitely come... Pls anty save a soul... "beautiful lady din ta fad'awa wacce ke rike da baby, da gani wacce ke rike da baby bata da interest kan abinda yarinyar ke cewa at all, because her face says it
"pls anty mutuwa zanyi... Ki taimaka min... " ta sake fad'a mata,
"amma rashida baki da hankali... Wato in nace mashi brother dinshi na son ganinshi sai yazo sai inyi yaya?... Kawai dai kinason ja min raini... "inji Mai baby a hannu, da sauri wacce aka kira da rashida tace
"no anty ummy... In yazo sai kice... " bata k'arasa ba ummy which is the second daughter inlaw din hajiya amina tace
"pls rashida get a life... Move on...sau biyu Kuna haduwa da Aliyu gidan nan amma kou inda kike yana kallo?.. I see no reason why zakiyi stressing kanki kan Wanda bai damu dake ba alhalin some people are dying to be with you... Wallahi wahala Zakisha a banza... Take a look at yourself... Wake up am Telling you if not wallahi zan fadawa mami tasa abu yayi maki auren dole,... " ta fad'a cikin matsanacin fushi, idanuwa rashida ta zaro cikin tashin hankali because tasan one word from her elder sister to her parent is all it takes and zaayi mata aure, kawai bata ankara ba sai ta fara hawaye, wato rayuwa kenan, yarima da tasleem ke kira da black mamba shine wannan yarinyar kewa hawaye, abincin wani gubar wani, she heard lot about him wajen mutane but never met him personally despite his elder brother is married to her elder sister, kou sanda akayi bikinsu wato yayarta da kuma yayan yarima she's only 14 which is 8 years back, bata damu da ta san who and who is present ba, amma seeing him five months back ranar da sister dinta ta haihu a hospital make her falls for him totally, ta shiga tsahun yanmatan that are dying for him amma nata is too much, ita kanta yar sarauta ce but under he's father, she tries all she could ta manta dashi amma he's handsomeness is not something one xan easily forget, har yau smile dinshi still linger in her heart, duk ta rame saboda tunanin ta, bata iya fadawa kowa amma she have to tell her sister Wato ummy, ita kuma tasan samun Aliyu might not be something easy saboda kou ita dake matar wanshi bata taba ganin smile face dinshi ba and bata taba ganin frown face dinshi ba either, kawai tasan he's not a social person and he's not into women,
"na shiga uku... " shine abinda rashida ta fad'a cikin hawaye sosai, baki ummy ta tabe tace
"baki shiga ba... Zaki dai shiga... Nadia son mason wani kika sawa kanki ba... You will suffer...wallahi it's better ki maida hankali ki gama service dinki ki samu daya daga cikin masu neman auren ki kiyi aure daga baya Allah ya sa maki sonshi than ji zauna kina hauka kan Wanda vai san if you're dead or alive ba... It's an advice.. If you like take it kou kuma leave it... Your business ..." ummy ta fad'a mata, rashida dafa chest dinta tayi sosai tana kuka,
"anty ummy do something... Wallahi mutuwa zanyi sabida yarima hydar.... In na mutu kina da alhaki wallahi... " ta fad'a cikin kuka sosai, wata yar karamar dariya ummy tayi tana cewa
"hehehe... Ashe ina da alhaki... Dayake ni na dora maki kou.... Na you sabi... Kinga na tashi ma..." ta fad'a tana San'a danta a kafada tana mikewa daga kan royal seat da take zaune,, wata budurwa ce tazo ta amshi yaron daga hannun ta, ta Kama wata hanya dashi,
"nidai zan fadawa yaya Muhammad... Nasan kilan he will do something... " a fusace ummy ta juyo tace
"wallahi one word from you to. Mijina zakiga abinda zai biyo baya tunda ana nema maki mutunci baki gani... Just try any stupid and see...wallahi sai na fadawa mami... " ta fad'a mata sounding firm and strong. Rashida rasa inda zata skaa kanta tayi saboda bakin ciki da damuwa, she feels like committing suicide kou ta huta da jarabawan rayuwa, she have her perfect life before she saw him, now yayi destroying everything for her.
"yanzu shikenan haka zan dinga wahala har in mutu?.. Will you watch me suffer yo death?.. " rashida ta tambayeta,
"ai bana son ki mutu shiyasa nake baki shawara... Just imagine ace kin samu kin fad'a mashi kina son shi and at last ya wulakanta ki... That will kill you faster.... Nasan it's hard for you ..amma kou kadan banson Kinyi anything that you will regret... " ummy ta fad'a mata,
"anty kilan ya tausaya Mani... Wallahi mutuwa zanyi... My heart is so heavy... Kou ruwa taste bitter a bakina... "
"wai in ba wawanci ba did you think ke kadai ce Mai sonshi?.. Da akwai dozens girls kaman ki masu mutuwan sonshi.... Aliyu is ranked the most eligible bachelor arewa, so Kinga dole ladies will be dying for him... Pls little sis take it easy on yourself... Banson ki shiga wata hali mara kyau... Kinji... " ta fad'a tana dawowa kusa da inda take zaune tare da zama gefenta, shuru rashida tayi sai hawaye na zuba,
"tou shikenan anty... " ta fadawa yayarta, ba wai because she give up ba, no, but it's because she will look for better alternative, tasan her sister is never going to help at all. Mikewa rashida tayi walking gently, tana da dirin da sai ka rantse she won't cry for a man, but unfortunately destiny have caught her in it's web, hanyar inda bed rooms dinsu take ta nufa ta bude daya ta shiga sannan ta wuce bathroom, tsayawa tayi Tasha kuka sosai har ta godewa Allah sannan ta wanke face dinta, her sister was in the bedroom listening to how she's crying, it really hurt her yanda sister dinta ke wahala saboda Wanda bai Santa ba, amma it's better for her she hurt her with her truth than to make her happy with lies. Shiyasa take fad'a mata ta rabu da tunanin shi Don tasan Sam ba hanya bace Mai bullewa face hanyar wahala da wulakanci. Tana fitowa ummy ta rungumi baby sister dinta suka fito falo tare, bag dinta ta dauka sanann ta yafa Vail dinta ta Kama hanyar waje sai shessheka kawai take, tana fita compound ta nufi Gate walking slowing zuwa waje, duk wnada zai ganta sai yasan something is bothering this beautiful girl, she was walking toward the main road yayi da wani makeken jeep yayi parking kusa daita yana wining glass din motarshi kasa, ciki wani cute guys ne yana cewa
"sister excuse me.... " ya fad'a with quite a firm voice amma kou inda motar ke tsaye bata kalla ba balle ta saurareshi, she gets lots of suitors amma ta dorawa kanta son yarima,.(ladies don't wallow in fantasy... Face the reality... Kar ku tsaya kaje kanku kan wanda bai san da zamanku ba.. Nasan it's not easy letting go but give it a try... Yan mata da dama suna kawo complain din suna san Wanda bai san su ba... Well dear ki. Rabu dashi and face those that wants you... Wannan shine taimakon da zaki iya yiwa kanki) wuce motar tayi ya sake binta da mota this time har fita yayi daga cikin motarshi yana binta da kafa yana magana amma tamkar he's invincible, bata kou kula shi ba, haka ya hakura ya kyaleta ya koma cikin motarshi. Sauran kadan da wani Mai Motan ya bigeta sai zaginta yake amma bata kou daga kai, wani Mai adaidaita ya tsaya yace
"hajiya tafiya ne?.." daga kai tayi ta kalleshi ta nufi inda adaidaitan take tashiga ta fad'a mashi sunan organization da take service. Daman wajen service dinta zata ta biyo ta gida sister dinta. Nan ya jata suka tafi.




thanks[3/14, 6:26 AM] +234 703 008 7807: 6🧡❤💛💚💜
Sak'aci
💜💚🧡💛❤💙




Zuwairat (ummumaryam)



6⃣




Happiness over load... Rabbi more thanks to you💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾




, yarima na kwance har karfe tara nan falo,   bude ido yayi waking up from the sweet sleep,  mika yayi ya koma ya zauna kaman minti biyar sannan ya Mike,  kofa dakin da mahboob ke kwance ya duba yaga har lokacin shi bai tashi ba, hamma ya saki heading back to his own room,  yana shiga ya cire long jallabiya dake jikinshi ya nufi closet da kayan hannunshi,  rataye jallabiyar yayi kusa da sauran kayan sannan ya nemo Jean da riga masu haske ya saka,  bai saka kaya Mai duhu saboda skin colour dinshi,  duk kayan dake cikin closet dinshi have bright colour,  fita yayi ya nufi Bangaren ummah while masu hidima suna ta up and down, wasu suna kula da tsaftar gidan while wasu kuma suna kula da flowers da dai sauransu,  falo ya shiga  yaji kamshin abinci,  yasan dai duk wannan abincin nashi ne sabida most Bangaren Mai martaba hajiya take breakfast da sauran kishiyoyinta,  wannan it's part of their culture.  Wata dake goge dining ta gaidashi ya daga mata hannu kawai with a smile sannan ya nufi bed room din ummah.

Tasleem kam tana maida mug ta dawo kan gado ta hau tare da dora kai kan kafar hajiya sai zuba take,  da ta fadi abinda ba daidai ba sai ta kwabeta,  in kuma ta fadi funny thing sai tayi dariya,  she so Much adores tasleem with her parrot mouth.
"gimbiya ki bari in shiga wanka in fito... " ummah ta fad'a mata,
"AI ummah nan da minti shabiyar za tafi... Kawai ki bari in gama ganin ki in tafi sai ki shiga wankan tunda ba lallai  ki fito Kafin in tafi ba... " ta fadawa tana baje kan gadon hajiya,  sai kawia hajiya ta biye mata,   tayi zaune while ta cigaba da bata labarai kala kala, hajiya na kallonta tana shafa kanta daga gaba zuwa baya feeling her silky hair, kofa aka bude yarima ya shigo smile a face dinshi amma ganin tasleem kafar hajiya yasa ya hada both gabas da yamma,  sai kudu da arewa kaman bai taba dariya ba,  tasleem najin voice dinshi tayi saurin mikewa Tare da dan komawa bayan hajiya alaman tsoro, jiya ta harareshi and she's sure bai mance ba,  karasowa yayi yacr
"ummah kafa yayi sauki kenan tunda har ana hawa... " yafada babu walwala a face dinshi, (rayuwa kenan,  mutanen that people are dying to Met suna chan wasu na ganin su a sanga,  kuma masu ganin nasu basu san value dinsu ba... Duk manyan Cele that were dying to met suna da masu ganin su at all time..they don't even value seeing them.. That's life...if Allah yasa Kana cikin such Cele don't be too proud for it's the will of Allah,  some of those people dying to met you are even far better than you in so many ways... Alhamdulillah )
"ashe ...kaima jiya baka hau ba?.. " inji ummah,  sake daure face yarima yayi yana zama kusa da ummah,  tasleem sai lekenshi kawai take, if you ask her waye dodonta she will tell you Aliyu kou black mamba,  yarima bai kara cewa komai ba  Don kar ummah ta sake yi mashi maganar da zai sa  raini ya shiga tsakanin shi da ita,  if  there's anything he hate is raini,  gyara murya ummah tayi sannan tace
"yanzu fav ka kyauta kenan?.. " da sauri tasleem tace
"ummah zan tafi... " ta fad'a tana sauka from the other side na gadon that is far away from inda yarima yake zaune,  yarima kasa kunne yayi yaji abinda mahaifiyar shi zata ce,  kou Kadan baiyi tunanin tasleem will tell hajiya about the boobs ba so ko kadan bai kawo hakan cikin ranshi ba,  cikin rawar jiki tasleem ta sauka daga kan gadon
"kince nan da minti shabiyar zaki tafi amma kou minti uku baayi ba zaki tafi..."  ummah ta fad'a mata looking at yanda jikinta ke rawa,  shi kam Aliyu vai maida hankali kanta ba sai jira yake hajiyarshi ta k'arasa maganar ta, 
"ummah zan makara... " ta fad'a da sauri Don ko kadan b'ata son ummah ta fara maganar gabanta,  abinka da mara gaskiya despite bata san abunda ummah zata ce ba duk ta tsargu,
"is your food ready?.. " ummah ta sake tanbayan ta,  tasleem data nufi inda hijab da bag dinta suke sai sauri take,  da ka ganta ka gan mara gaskiya,  shi kam yarima bai damu ba saboda daman hardly su zauna under the same inuwa da ita,
"zan duba... Duk Wanda ya samu sai in tafi dashi..." ta amsa mata,  hijab dinta ta saka ta dauki bag dinta ta runguma a gaba like she did before sannan ta komo kusa da ummah tace
"kudin... " ta fad'a ahankali, 
"dauko wancan bag din... " ta fad'a mata tana nuna mata wata expensive bag dake kan kan mirror ta manyan mata,  da sauri tasleem ta dauko ta mikawa ummah, amsa tayi ta bude ta dauko yan dubu dubu sabbi kaman guda uku ta mika mata,  Dan rainin hankali dubawa tasleem tayi taga guda uku ne tace
"ummah sunyi kadan...da mota na fito kuma zansha Mai.." ta fad'a tana turo baki, murmushi hajiya ta saki ta sake dauko uku ta mika mata tare dacewa
"sun iya?.. "
"yes ummah... " ta fad'a tana tura kudin cikin bag dinta,  duk abinda ake yarima bai daga kai ba balle yasan abinda sukeyi, 
"ummah sai na sake dawowa.. " ta fad'a tana juyawa,  kaman walkiya ta fice daga dakin hajiya data bita da kallo tace
"tasleem kenan... uwar rigima... " tafad'a cikin dariya,  baki yarima ya dan tabe amma bai bari ummah ta ganshi ba, sai da ya tabbbar ta kulle kofar falo yace
"ummah me nayi?.. " ya fad'a Don yaji abinda zatace
"yanzu Aliyu haka kake?.. Gaskiya am disappointed in you... Duk neman ilimin mutum indai baiyin amfani dashi ta zama na asara... Ka fi kowa sanin illah ganin tsaraicin macen da ba halal dinka ba... " nan take yarima da ya shiga tashin hankali saboda furucin ummah ya gane what is happening, instantly yayi regretting not listening mahboob, baisan despite tasleem fears him zata samu nerves din yiwa ummah magana ba,
"wayyo ummah sai ki bari wannan yarinyar ta hadani dake?.. " bai k'arasa ba tace
"ashe Kama san abinda kayi kenan... Wato da gaske ne... Lallai ka bani kunya... " ta fada calmly but angry, 
"wallahi it's not like that... " ya fad'a yana kokarin wanke kanshi,  nan  ya fad'a mata exactly what happened,  hajiya was more angry at him because of testing a girl like That
"kasan if tana da laifi kaima kana dashi?.. Why will you even talk about private part with her in the first place... Ai in dai kana da kunya bai kamata such words au fita daga gareka ba both verbally da in written... Gaskiya baka kyauta ba... " ta fad'a cikin fushi sosai,
"gwadata nayi ummah am sorry... " ya fad'a thinking about how to handle tasleem,
"tou gaskiya kar in k'ara ji kuma kar in k'ara gani...so wannan shine gwajin da kakewa yanmata daga baya kace basu dace da kai ba... Duk ka gama gane masu jiki... "
"no ummah sorry... " ya fad'a mata kanshi kasa,
"ni babu laifin da kayi min... Stop saying sorry kaman it's me that you offended... It's not me... It's between you and Allah... So say sorry to him... Tashi ka bani waje..." ta fad'a atakaice,  jiki ba kwari ya Mike,  ya fice daga dakin, yana zuwa falo yayi sauri ko zai tarda tasleem, har kitchen ya shiga Don yaji ana maganar abinci, yana shiga aka ce yanzun nan ta fita,  daman tasleem knows anything can happen Don haka tana shiga kitchen  ta tarda baa gama ba kawai sai ta fice abinta kar yarima ya kamata.Wai kaman dole kasan in kayi Abu zai iya zama matsalar amma sai kayi,  tasleem tasan ummah will surely talk to yarima and she's scared of yarima amma kaman ana zugata haka taje ta fadawa ummah,  vata samu sukuni ba  sai da taga ta fita daga gidan.

A gidansu tasleem kam wajen har karfe 8 alhaji yana jiran tasleem ta shigo ta gaidashi  amma shuru, his so angry da yanda mahaifiyar ta ke sane da faruwar hakan amma bata daukan action  kanta  duk yaran gidan shi babu mai irin abunda tasleem keyi,  they're all mannered saboda suna samun tarbiya amma ita tasleem  saboda goyon bayan mom dinta tana son ta fita daban cikin yaran gidan,  kawai one thing daya is tana son aure,  inda zai tambayi tasleem to define aure da bazata san good defination da zata bada ba because kou kadan bata hango kanta da aureba,   kou sau daya bata taba zama tayi tunanin aureba, kawai a barta da shanshanci as usual. Mikewa alhaji mussadiq yayi da sanye da glasses da kuma jallabiyar  brown ya fita daga part dinshi,  duk asuba duka yaran suke shiga su gaidashi, yau bayan sallah asuba hajiya zainab ta shiga ta gaidashi amma ta zubawa tasleem ido bata zo ba,  bai nufi koina VA sai Bangaren hajiya zainab,  kofa ya bude ya shiga falonta tare da wucewa directly zuwa part din tasleem,  sai sauri yake da ganinshi kasan he's angry,  yana bude falonta ya wuce directly to her bedroom tare da sallama, wayam yaga gadonta, har masu aiki sun gyara gadon kaman baa kwana kai ba,  kawai sai yayi tunanin Bangaren mahaifiyar ta ta kwana, da sauri ya fita ya shiga bed room din hajiya sai ta tardata tana bacci ita kadai,  tsayawa yayi yana kallonta cike da takaici for a  moment tare da rike waist dinshi, 
"where is your daughter... " shine tambayar dayayi wa hajiya zainab that's sleeping peacefully,  arazane ta tashi saboda yanda yayi magana tana mazurai, 
"naam... " ta fada tana murza idanuwa,
"I said ina yarki..." ya sake maimaitawa yana kallon yanda take murza idanuwa,
"ta tafi islamiya..." ta amsa amshi tana hamma tare da rufe bakinta da hannunta na dama,
"by this time shine ta tafi islamiya?..very good... She should keep hiding,  kar ta dawo gidan nan... Nothing will make me change my mind kan decision dina... " ya fada a fusace yana kokarin juyawa,  bayanshi hajiya tabi da harara sannan tace
"wai Meye wannan decision din da kake ta faman maimaitawa... " ta fad'a waiting for he's response, 
"zakiji... " ya fad'a mata yana ficewa daga dakin,  baki hajiya ta tabe not knowing what he meant,  all she knows is nobody will hurt her daughter. Salati ta saki tana komawa ta kwanta abinta.

Yarima na komawa part dinshi ya tarda har lokacin mahboob bai tashi daga bacci ba,  legs dinshi ya buga yana zama tare dacewa
"wake up.. There's fire on the mountain.... " ya fad'a mashi cikin tashin hankali da matsanacin damuwa,  cikin magagin bacci mahboob yace
"where is the fire?.. " ya fad'a yana murza idanuwa,  harara yarima ya watsa mashi da idanuwanshi da suka sauya kala,  kawai inda zai samu hawaye da yaji sauki amma ya kasance mutum da bai da saurin hawaye,  yana da dakakkan zuciya,  amma yau ya san saurin kuka ma is a blessings because yana washing pains away, 
"kanwarka ta fadawa ummah what she saw... " ya fad'a kaman bai san sunan ta ba sannan kaman ya dora hannu bisa kai ya dinga ihu,  shuru mahboob yayi for a moment sannan yace
"I told you so... " ya fad'a mashi atakaice yana juya kwanciyar shi,  kai yarima ya dafa yana girgiza legs daga inda yake zaune, 
"na fad'a maka if har ka tabbatar parrot taga wannan pictures din call her kaja mata kunna amma sai kayi paying deaf ears... Allah kadai yasan how many people she's going to tell... " mahboob ya fad'a mashi hankalinshi kwance,  yarima rasa inda zai saka kanshi yaji dadi yayi,
"wallahi.... sai na... Zaneta" yafada stammer dinshi na. Fita loud and clear,
"tou in zaka zaneta ka tabbatar ka rike kunnenta yanda bazata sake fadawa ummah ka zaneta ba... If not trust me zata dora hannu bisa kai tana ihu ta shigo fada duk ta tara maka mutane... It's tasleem... Believe me Shes unbelievable... " ya fad'a yana rufe kanshi da blanket. Yarima rasa irin hukuncin da zai yankawa tasleem yayi,  he's surprised that she can gossip about him to his own mother,  kai kawai yake girgizawa,  abinka da Mai high temper sai zufa yake kaman Christmas goat dukda sanyin AC dake dakin, 
"Dan Allah ya zaayi in kamata... " shine abinda ya tambayi mahboob,  dariya mahboob yayi daga inda yake kwance yace
"parrot din ce zata yarda ka kamata bayan  tasan ta guma maka.?..youre dreaming.... Kou hanya bazata hada da kai ba.. So kawai ka bari Allah ya saka maka... " mahboob ya fad'a mashi atakaice, 
"never... Sai na koya mata hankali... Korata ummah tayi... " ya fada sounding so tensed,
"ahap... Good luck catching her... " ya fad'a mashi,  cikin fushi ya Mike ya bar daki,  yana zuwa falo ya will mini side table dake gefe guda kaman it's tasleem,  ji kake tasss saboda it's glass, fashewa yayi nan kasa, 

1 Comments On SAKACI
avatar
ummunusrat

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment