Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sir Khaleed a gyefe guda. su mazan duka shigar Suit sukayi,sai kuma mu duka shigar wannan Gown din da sunan Ga Amarya ce,amma nafi ta komai".

A hankali ta kai Hannun ta hadi da hadewa dana Huday cike da sanin duniya ta sakar masa wani irin Murmushi n kaman kissah,nikam sakin Baki nayi,ina furta a zuciya ta Lallai duniya kam tazo karshe,Suhaimart kiyi Gaggawar barin Wurin kar a rubata maku Zuni bi tare,shi Allah ba Ruwan shi da Rako kikazo".🤣

Nidai haka nayi shiru ina zaro ido don ganin wai wannan duk taron menene,Amma abun Haushi sai naji an saka wani irin cool music yana tashi yyn da nan Aysha ce tafara takawa tana juyawa,Nikam sam bana Rawa kuma ban ma iyah ba Sulaym ce mazari,amma nasan ko itane tazo nan bazatayi Rawar ba,kallon Sir Khaleed nayi a raina ina furta,komai nasu dabi'ar nasara,wlh wannan baiyi ba".

Kallo na yayi gami da kokarin rikemun Hannu,aeko nayi Saurin kaucewa,dama kunsan Sir Khaleed Dai ba sai nakuma fada maku halin sa ba". Shidama dan zuwa Club ne,haka kullum yake, amma na lura yanxu sam baya zuwa matan Banxan ma na Rage ganin su,ko sunxo korar Kare yake bin su da Shi ".

Matsowa yy daf dani hadi da mun mgn da babu mai jin ta da cewa" Bakya Rawa ne?"

Daga masa kai nayi saurin yi don na tsira da mutunci na". Tom bari na koya maki,yafadi yana kuma son kara riiko hannu na". Cikin Sauri nace" A'a nifah ba Maharramar ka bane a yanxu,ka barni kawai kai dai kayimun nagani". Shiru yy tabbas mgnan ta Gsky ne, Shiko Huday zame Hannun sa daga na Maryam yy yana mata Kallon kinji gsky nan".

Dariya Khaleed yy kan yace naki Wayon,shikenan Amma ranar namu ae zakiyi ko"?

Murmushi nakuma sannan na daga masa kai Alamar Ehh".

Dani dashi ne duk muka samu wuri muka zauna muna kallon su,yyn da Aysha kam rawar ta takeyi don ita fah ko ainah taji kida sai ta taka,dariya takemun hadi da cewa" Suhaimart sai na Ranan bikin ki,ai ba'a ma mgn".

Haka muka saka Dariya don shi dama Abdoul Manan Mulki da Sarauta baya barin sa yin Rawa tun Asalin sa". Shima zama yy,yyn da Huday ya janye hadi da nufo mu shima ya zauna".

Sosai Maryam taji Haushi,amma sai ta dake bata nuna komai ba".

Niko Jin Ankirani a yar Baby Nokia ta yasani mikewa hadi da nufan Wani dan Wuri mai kama da Coridour,ina wayan ne banyi aune na kuma bansan tayaya ya zo ba najishi a Baya na".

Juyowa nayi ina kallon Huday,takardan dake a Hannu na dama Oready na Rubuta shi tun tuni kawai na kasa basa ne. Saurin kara kai ya tsuna nayi don rinst shi,amma kuma banyi aune ba takardan ya sulube a hannuna,Kashe wayan nawa nayi nayi saurin bin takardan da iska ke kadasa a haka yana kallo na,har ta kardan tazo gaban shi,aiko nan yy saurin saka Hannu ya Dauka yana mai budewa". Cikin Sauri da kyarman Murya nafara masa magiya akan ya bani bana sa bane,amma yakiya,ganin haka yasa nayi saurin barin Gurin da Gumi tuni ya fara karyomun".

Bude takardan yy gami da kallo yana karanta rubutun dana masa,da I luv u tooo Ya Huday".

Cike da wani matsannancin Farin ciki ya ke kara karanta takardan,yyn da Oftyhal tayi saurin Zuming din cameran don kara ganin Abun da Takardan ta kusa".

Sakin baki tayi galala,tana mmki da ta'ajibi, Wani Dariya tasa hadi da cewa" Duka zaki biyu biyu,don kin rasasu har Abada". Sai nabi bayan ka Yah Huday na Raboka da wannan Takarda,sannan ana gobe daurin Aure zan lalata komai naki Suhaimart,nasan dole ki Halarci Wajen Taron Mother's Day,anan zan amsa Speaker na bude takardan na karanta ma kowa daga ranar Mujiya sai tafiki fari..............




Muje zuwa niko Maman teddy nace koya zata kaya a wannan Waje.shin zata lalata komai iftyhal din kuwa????..


Hmmm Tom Allah yasa Kar dai ta lalata ma Suhaimart din kaman yanda tace,Amma kuma nikam nace kila Reshe ne zai juye ma mujiya,wato Kar ta lalata bikin Maryam da Hannun ta".🤣😅


Muje dai zuwa💃🏻
naji Adduoin ku ina gdy sosai da yabawan ku fa kuma nuna soyayyan ku ga wannan Littafi nawa Mai Suna ZUMA DA MADACI, Allah yavar kauna much luv...

Naso na kammala Free page a wannan pagen wato page15. Amma saboda wasu dan Uxurori na mai dashi zan kammala inshaaallh a Pagen na gobe,wato page 16.


Littafin kaman yanda kuka sani ta kudi ce, don haka gamai bukatan wannan littafi zai turo #200 NORMAL,idan VIP nema duka #200 ,SPC kuma #300 Ta wannan Number 08081202932/09137392680.




*#SHARE TO ANOTHER GROUPS*



*Maman teddy🧸*
*Typing...✍🏻*

🎋🎋🎋🎋🎋🎋🎋
🌹🌹🌹🌹
🌿🌿
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_


Na
*Maman teddy🧸*

*Last free page 16*


*_________________________*


*ALHERI WRITERS ASSO.📘🖊️*

*A.W.A*


```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri💪🏻```

*___________________________*


*بسم الله الر حمن الر خيم*


_Dedicated to my teddy🧸Wannan pagen taki ce y'a d'aya tilo😂._


*_Domun samun Littafin Zuma da mad'aci tun daga farkon sa har karshe zaki tuntubi wannan number 09137392680/08081202932._*


Niko da isana falon ne jiki na har dan rawa yake nake cewaa" Sir Khaleed ina son na koma gida yanxu,Oumma na nason gani na".
Ganin yanda nake magana Amma hankali na gaba daya ya tashi kuma buri na kawai na tafi gida yasa Sir Khaleed Saurin mikewa,Yayin da nan Abdoul Manan Yace" Batasan da Zuwan ki ba ko?. Kafin na basa amsa ne Aysha tayi saurin cewa" Wlh kam Hamma bata sani ba,Ai kam Hamma Khaleed kayi maza ka maida ta,gida kaga lokacin tashin su yy shine yasa Oumma kirah".

Murmushi yy mun wanda kan yy mun mgn nayi saurin ficewa daga Falon ina mai nufan Farfajiyan gidan". Haka ya biyo bayana da son ganin ya faranta mun,wato ya mayarda ni gida a wannan lokaci".

Sam ban tsaya bin ta Maryam da gaba daya ranta ya gama kololuwar baci,Amma ya zatayi dole ne ta nuna komai bakomai ba,har Allah ya nuna mata Ranar da zata Mallaki Huday,A lokacin kam ne zata gasa mai Ayah a Hannun sa".

Shiko Huday sai da ya6ata Kusan 30 munite yana mai kallon takardan,yyn da bayan ya fito ne dayaji Suhaimart ta tafi gida,Dariya ya kusa kamasa,don mene yasan Guduwa ne tayi, bawata Oumma da ta kira ta".

__________________________

*MASARAUTAR GOMBE*

Cike da muna funki da tsantsan yaudara da Ha'inci naji muryan Jakadiyya ba cewa" Wannan kuma Ranki yadade,Uwar daki na,za'a sanya masa ne A abincin da In yadawo Zai ci". indai yaci tom zai kwanta jinya mai tsawo wanda babu Uhm,bare Uhu"um don sam baxai iya mgn ba". Kuma bazai kara kwanaki 30 ba,za'ayi basa".

Wani murmushi Fulani ta saki,kan daga bisani takara kishingida tana mai jin dadin maganganun Jakadiyya". Itako Jakadiyya ganin haka yasata cigaba da koro mata Bayani hadi da dauko wata Kwarya datake a Rufe,wannan Kuma zamuyi ma Yarima Abdoul Maman ki ranye ne,wanda damun masa sau uku,gaba daya hankalin sa zai bar jikin sa,kuma komai yake can zai dawo,savoda tsaban saurin yadawo Masarautan tom A hanya za'ayi bashi,don hankalin sa tashin da zai yi,tukin moton nasa vaxai iyah ba,kinga ko ae dole a saki birki akan Kwalta". Murmushin Mugun ta Jakadiyya ta kuma yi,yyn da fulani tace tom in ankirasa ae sai ya amsa in bai kuma amsa ba fah?"

Ranki yadade ko a inah yake karfin wannan magani dole ne ya amsa ko kin mance Uwar sa ce".

Wani kayataccen Murmushi Fulani tayi,tuno da abubuwan dasuka faru shekaru 30 kenan da wanxuwan hakan".

Ganin haka yasa Jakadiyya cewa" Tom dolen sa ya amsa koda kuwa yana kwana kan buzu".

D'an shiru Fulani tayi hadi da tunanin Anyah kaunar da take ma Abdoul Manan zata iya bari a cutar dashi haka? Don Allah yasa kamata Azababben Son Yarima Abdoul din,wanda ita kanta bata son mai yasa take kaunar Yaron kaman jinin ta ba".

Kar kumanta daga wannan Page din Free page ya kare,maza hanxarta wajen biyan kudin ki ki karanta cikin kwanciyar hankali babu Zaullumi, don haka zaki tuntubi wannan Number 08081202932.

Niko Suhaimart tun bayan koma wata gida na rasa Sukuni,sai a yanxu nakejin sam ban kyauta ba,wanda ni har ga Allah bawai na ce inason Huday da wani nufi bane,a'a ni ba wannan son danake mawa Khaleed naje nufin muyi da Huday ba,kuma idan nayi tunani ae wannan bashi ne d first time dana fara fada masa kalmar so ba a rayuwa".
Haka na Zauna na Rafka ta gumi,gashi daya bangaren ta Zuciya ta ina tunanin irin Kaunar da son danaga Maryam na mawa Huday,anyah ban yi cuta ba nace zan Rabasu,nidai gsky ba dani ba". Dole na samar nawa Kaina mafita".

A washe gari kam sam ban isah gidan Hajy.Zaituna da Wuri ba sai da naje Asbiti don duba lfyn jiki na,wanda sosai Hankali na ya tashi kan maganganun da Doctor Zainab ta fadamun,don a halin yanxu ciwon nawa yafara cin karfin jikina,kuma ta sanar mun da nan da Watanni 1 na kawo kudin Aiki na,idan ba haka ba komai xai iyah faruwa,walau Rayuwata ko mutuwa,don idan sa'in ta Wuce koda da kudin aikin sai dai muyi don jahadin kila yayi kila kuma mutuwar ki". Ta fadi tana kallo na". Kasa magana nayi jiki na lubus yy sanyi,yyn da nan na fada Duniyar tunanin ina zan sami wannan Zunzurutun kudi? Har kusan miliyan da rabi,ina yar talaka".

Tana a Zaune ne sai ga wata nurse tazo anan take sanar mata da shigowar wani Babban likita,aiko cikin sauri tace naje na same shi,don dama tayi masa baya ni nah".

Godiya nayi mata jiki babu kwari na nufi Office din wannan likita danaji ana kirar sa da Dr. Vivan.

Abun da yabani Haushi ya kuma daga mun hankalin, buden bakin sa cemun yy" U must die,saboda ciwon ki ko a yau aka kawo komai da komai da matsalar,sai dai muyi aikin cikin kasada". Nan take naji kirjina ta buga,nidama tuni na cire mawa Kaina Rayuwa,Kallon sa nayi kan nace" Dr. a halin yanxu babu wani magani da xa'abani na ringa sha,saboda Sassauci?.

Bai bani amsa ba,illah fitowa da yayi yana cemun na biyo sa,A haka na dinga bin bayan sa Har muka isa Gaden na Asibitin inda muna A tsaye wani mai ba Flawer ruwa yazo wuce da wani Flower a hannun sa matacciya". Yarda Flowern yy cikin dattin Asibitin yyn da naji muryan Dr. Vivan na cewa" Idan kina son kiga zaki Rayu ko mutuwa,ki dauki wannan matacciyar Flowern ki Tayarda da ita har tafara fitar da iri,da ga wannan lokaci kisani tabbas zaki warke,idan kuma ta mace mgnan dana maki ne".

Yana fadin haka ya juya hadi da bari na anan,Hawaye ne yafara bin kunci na,sai kuma cike da jin Haushuin Dr. nace halan kai Allah ne da kaasan zan mutu ko zan Rayu? tuno dani kaina nasan ciwo na ya tsananta matuka yasani saurin nufan Flowern na kuma dauka na fara takowa ina tuno da abubuwa da yawa a rayuwa ta".

A yanxu na daina zullumin komai namika ma Allah komai nawa,komai ya sameni dama Allah ya Kaddara mun ne". Saka takardan Bayanan da Dr.Zainab tayimun nayi a Jakata,a haka na isa gidan Hjy.Zaituna don babu danan komawa gida na ajiye Flowern. Tun da na shuga Part din nasa na hangosa ta saman Benen sa yana kallo na, wanda tun da na kalleshi yana mun Murmushi na kawar da kaina,ina mai kokarin sassauta natsuwa ta".

A falon shi muka hadu,don zuwan da banyi da wuri bane,duk ya damu haka,saurin sa Hannu yy yana karban Flowern hannu na dacemun,mai zakiyi da wannan Ai ya riga da ya mutu,Murmushi nayi masa,kan nace inason shine,kuma inason ya tashi daga matacce Zuwa Rayayye".

Kara bin Flowern yy da kallo kan yace mun" Ki bari muje a kawo maki irin wannan komai da kaman sa".

Nan nayi dan Murmushi kan daga bisani nace masa" A'a Sir Khaleed ga Flowern nan na bari a hannun ka,idai kana sona tsakani da Allah,inaso ka Raine ta kuma ka tadamun da ita".

Cike da Rashin fahimtan komai yace mun" Ina kaunar ki Suhaimarh,kuma inshaallah zan tada maki da Wannan Fulawan,babu abun da zai kuma matar dashi ". Nan nasaki murmushi ina cewa" Na gode fah,kaga bari nayi sauri na fara yin aiki na'. Shima nan yace tom nima bari naje nafara aiki na".

Kallon sa nayi saurin yi kan nace"Aiki kuma? wani aiki kenan?"

Nuna mun Flowern dana basa yy,kawai sai nasa Dariya hadi da nufan Coridourn sa,shima dary yy hadi da nufan Gaden nasa dake ta baya".....

Tun daga wannan Rana Kullum Sir Khaleed yana aikin vaima Flowern nan Ruwa,don masu kula da itah yasamar mata". nikam kullum boye damuwa ta nakeyi kar wani yasani kuma ya fahimta,wanda a iyah yanxu har Oumma na tafara dago ni".

Amma haka nake dannewa na nuna mata bakomai".

A wata rana ne,ina a zaune a falon gidan Sir Khaleed ina hutawa,don kammala aikina kenan,Aysha ce tayi saurin shigowa tana kwala kira na".
Tana gani na anan ta zauna tana cewa" Munga ta kanmu Suhaimah wai shin kiniji Yah Huday yace" Zai hakura da Aurar Maryam,nan take naji kirjina ya buga salati na farayi ,wanda kan na bata amsa naji muryan shi a bayan mu yana cewa" Kehh Aysha dama haka kike,tashi ki bani Wuri"!

Jikin Aysha ne ya hau rawa,nan tarasa inda zata nufah,kawai sai ta kutsa kai Bedroom din Sir Khaleed da yau Weekend vai fita ko inah a wannan Rana".

Zama yy akan daya daga cikin Kujerun falon,yyn da ban san lokacin dana zube a gaban sa ba,hawaye na bin kunci na,nan na fara ce masa" Don Allah yah Huday kayi hakuri,kar ka Ki Aurar Maryam, na tuba wlh wasa nake bada gske bane abun dana Rubuta. Indai ni kana sona ka Auri Maryam,baka sani ba ni Rayayya ce ko matacciya,kila ma Bazanga Bikin ba,ammma ina Rokon ka da Allah ka Auri Maryam, taban Tausayi komai zai iya faruwa da ita idan taji wannan Maganan.

Kauda kai yy bai cemun komai ba,muna a haka sai ga Sir Khaleed da Aysha,aiko nan itama Aysha ta zube gaban sa ganin yanda nayi tana kuma basa Hakuri,don ita batasan Dalilina na hakan ba,ta dauka haka kawai ne nake basa hakurin".

Cike da muryan kwantar da Hankali Khaleed ya fara masa mgn,da basa Baki don ganin ya sauko dashi daga abun da ya doru.

Shiko gaba daya Hankalin sa na kaina,ganin yanda nadaga Hankalin a ne ya kalli Khaleed da cewa" Khaleed naji kuma na amince zan Auri Maryam, amma badon ina son ta ba,ko kuma kaunar zama da itah ba". Kawai dai na amince da hakan saboda wata mahanga tawa".

Murmushi duka mukayi yyn da kaman wani Uban mu nida Maryam muka hau yi masa gdy,hadi da tashi muka basu wuri".

Tun daga wannan Rana sam ban kuma hada ido da Huday ba,shiko yy kukan Zuci,musamman idan yana a dakin shi ya dago haton Little din sa,Duk Jarumta irin na mai Suna Aliyu,baya sanin Lokacun da Kwallah yake sauko masa,sai a yanxu ne yake jin wani irin matsanancin Kewarta da Rashinta da yayi".

Haka Momy ta lura da hakan sosai,amma inta tambaye shi sai yace mata" Ya tuno da Little ne,nan Momy itama zata tuno da tsohuwar famin dake a zuciyar ta,haka zata yini tana Zubar hawaye hadi da mata Addu'a".


A kwana a tashi babu wuya gamai yawon Rai,don ana gobe bikin Huday da Maryam ne,iyaye da Yan Uwa na nesa da kusa,duka sun gama kammalah,Hjy. Zaituna kam itace Hajiyoyi don sune manyan iyaye,a wannan kuma Rana aka shurya Mother's Day da duk wasu manyan Hajiyoyi da Kawayen Su da yan Uwa sun Halirta wannan Wuri,wanda tsara shi kam ya tsaru,komai na wajen Abun burgewa ne". Kowa sanye cikin wata Material mai Launin Ash colour. Abun kam yy matukar tsari, Nikam da Aysha bamu halarci wurin ba sai karfe 4pm. Wanda wurin ya cika ya batse,daga nina Iftyhal tasaki wani Murmushi mai kayatarwa hadi da Saurin nufan Part din Da Huday yake".

Don Tun A ranar taga inda ya ajiye wannan Takadda,kuma haka tayi tasaka ido taki dauka ta bari sai yau, don a cewanta idan ya bude ido yaga babu xai tunanin tabbas da akwai wanda ya dauka shiyasa ta bar shi bata dauka ba".

Gaba daya mutanen Wurin bina da Kallo suke kaman wata yar wata da wani, Don kowa tambayar kansa yake ni wacece yar waye ne??.

Haka kam yan matannan kowa ta nufo mu musamman yanda Aysha ta kasance First lady,shi yasa kowa kaga ya taho wurin mu daga nan sai kaji ance ana sona da kawa,haka dai nake ta murmushi,Duk wannan taron banga Amarya ba,sai daga baya har mun samu wuri mun zauna muka fara ganin shigowan Abokan Ango,wanda cike da mmki a xuciyata nake cewa" Dama maxa na halirta kodai sune da iyayi?"

Sai can daga baya bayan anga komai kowa ya natsu ne,sannan wasu gijagijan iyaye mata wanda sun kai su 8 su hudu a gaba hudu a baya suka sako Ango da Amarya".

Duka mikewa akayi ana tafi,hadi da barin Amarya da Ango su Zauna a mazaunin su da'aka tana dar masu,sannan kowa ya Zauna ".

Bin su da kallo nayi,don sosai suka harsa,bakaramun kyau sukayi ba,Maryam kam sai Walwalin zunarai ake".

M.C ne ya fara magana ta hanyar cewa sunai ma kowa mata Akhairy da godiya,kan daga nan don Allah suna bukatar hankulan kowa,don K'anwar Ango nason yima kowa Barka da zuwa da nuna farincikin ta kan duk wanda ya Halarci wannan Taron".

Aiko nan kowa ya kuma yin shuru aba jiran fitowan gimbiyan wato Iftyhal. shiko Ogan nawa Huday sai a yanxu ya hangoni,aiko sai Murmushi yake mun,nima haka nayi ta mayar masa,Khaleed kam nufomu yy yayin da inajin Yan matan Wurin na kirar sunan sa kasa². Har ya karako,don A wurinnan Sosai Yan mata sukayo kamu".

Sanye yake cikin shigar sa ta wata Sky blue din yadi mai laushi da tsadan gske,hadi da saka hular kube,kai nikaina sai danace mashaallh,don bakaramun kyau yy ba,da isowan sa yace Hayatee na kece haka,shine baki varni na fara ganin ki ba,sai da wasu suka gane mun ke??

Murmushi nayi masa,don kunyah ta hanani cewa komai,Sai Aysha ne ta amshe da Amana Afuwa,Sauri ne ya hanamu amma ae ban yarda da kowa yaga fuskannan ba,kaine kafara ganin kwalliyar. Dariya yy hadi da ceewa" Ai kam har kinsa naji sanyi a zuciya ta". Hamma na ka koma bangaren ku nan namu ne na mata". Kan ya bata amsa ne Abdoul Manan da zuwan sa kenan ya jah hannun sa yana cewa" Ai shi yasa Nazo na tafi maku dashi,aiko nan muka sa Dariya, muryan Iftyhal naji yana amo da ya cike Wurin,Godiya tayi ma kowa na halirtan wurin,kan daga bisani tafara da cewa" A yau inaso na sanar da ku wata muhimmiyar magana, akan tmyaudara da cin Amana da Ha'inci,wanda a haka nayi ta barin ma ciki na damuwata har ba bari sai a wannan lokacin zan Amayar".

tako tayi daga inda take hadi da motsawa ta chanja wuri hadi da tsayawa inda zata iyah hangoni da kyau,sai kuma tayi wawan Dariya hadi dacewa" Da akwai wata yarinya wai ita Suhaimah makira mayaudariyya yar gidan talakawan tilis,amma a haka take juya kwakwalan masu ilimi da Arxiki saboda sakarcin su".kowa ana yasan Khaleed da Huday aminai ne,amma a haka sai da tasa Khaleed ya sota,kai bama wannan ba,har ta shi Huday din soyayya suke,don wannan Auren Allah ne ya nufah za'ayi shi".

Hayaniyan maganganun mutane ne ya kwace a wurin,sao kuma Iftyhal tace wannan takadda da kk gani shaida ce na duk maganan danake fada a yanxu". Niko kan wannan lokaci tuni nafara kukan nadaman Halarta wannan Wuri,cikin sauri ta bude Wannan takadda ta soma karantawa,da Ni Suhaimah na yarda kuma na amince da Soyayyar ya Huday, I luv u too". Sai kawai ta sheke da dariya,bakowa bace wannan yarinya illah wancan mai kyaun Aljanun". ta fadi hadi da nuno inda muke zaune da nuno ni,ae tunda tace mai kyaun Aljanu ko hankalin sa ya tarkata a Kaina anan take abun ka ga taron Mata aka fara gulma da nuno ni,itako Aysha da hankalin ta yagama tashi nan tafara lallashi na hankali tashe,tana son gaskata maganan ko sharrin Iftyhal ne, Amma sai muka tsinkayi muryan Yah Huday yana mai cewa" Dul abun da Iftyhal tafadi haka yake,ni nace inason Suhaimart,kuma a yanxu ma na fasa Auren Maryam,bana Ra'ayi kuma babu mai mun dole,dama itace Suhaimah tace nayi Hakuri ba Aure ta,yanxu kuma banayi,ita itadai Suhaiman nake kauna".

Ihu Maryanmm tasa hadi da mikewa kawai sai ta xube anan Wurin,niko da Da gudu na bar Wurin ina mai wani irin kuka mai taba zuciya da ban tausayi,a yau nagama nadaman Amince ma Wa Yah Huday danayi,yanxun ban da makama".

Shiko Khaleed da yakejin kansa kaman ba'a duniyan yake ba ne,yyy saurin biyo ni amma ina kafinnan tuni Na bace na ganin su ".

Haka shima Huday bai tsaya bin takan mutane ba,duka suka biyo bayana,amma sam basu samu nasarar ganin inda na dosa ba".

A haka nasamu na tara mai Adaidaita wanda da isana gida,Oumma na bata nan,kawai sai na shige daki na ina mai kwanciya kan yar filungen katifah na,ina mai xubar da Hawaye da tuno da komai na Rayuwa ta tundaga Fari..."


*WACECE SUHAIMART*

Wata yarinya ce yar kimanin shekaru 4 a duniya ta fito da gudu tana ihun Murna da kwala kirar Sunan Momy...momy...."

Cikin Sauri Momy Huwaila ta fito daga kitchen don hadin breakfast take masu don tafy school".

Rungumo ta nayi da gudu,yyn da take furta Washhhh Suhaimah so kk ki karya Momyn naki".

Cike da yarinta na d'an turo mata yar micilan baki na,ina mai cewa" Momy Yah Huday ne,ki 6oye wannan kar ya gani...!

Tun da ga kan stairs yake furta plz my littele ki baniiii......

Tsalle nake ina dariya da cewa" No mom"
kar ki bashi duba kiga wai shi yace yafi ni iyawa".



Tomfah muje zuwa,laifin dadi karewa,a yau ne na kammala free page.

Domun samin cigaban Labarin zaki turoNORMAL #200 MTN, Idan kuma SPC kk so #300 ta wannan number
Whatsapp number👇🏻 08081202932.

CALL
09137392680



#Shere to another grps



Mmn teddy🧸

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any

Please Login or Register in order to submit comment