Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin su,wasu kuma suka nufi side din Mhiss Caterine don sanar mata da kammalawan su".

Sulaym kuwa tuni tayi nisa da barin Side din Sir Khaleed ta nufi nasu barayin".

Itako Nana Aysha bayan ta zuba masa break din sane,nan ta kalle sa duk da tasan abune mai wuya ya iyah yin break din nasa a halin yanxu". Haka amma ta daure Wurun cewa" Yah Khaleed Bismillah". No Aysha kiyi break din naki kawai,yanxun ni zan wuce Company".

Da jin haka yasa ta a sanyaye mikewa tana mai cewa" Plz yaya ka natsu wlh Suhaimart fah zata dawo gareka,kuma gobe ma Daddy zai dawo duk mu huta".

Wani kayataccen murmushi ya sakar mata kan daga bisani yace" Aysha nasani,nasan Suhaimart ta wace,ni kuma kadai,vabu mai kwace mun itah,but ki sani,baxan iya cin Wannan Abuncin ba ne,saboda Harshen ne yasa ba dajin dandanon ta,a halin yanxu girkin ta kawai nake bege bana bukatar na kowa". ki kwantar da Hankalin ki my littale,zan dawo cikin Koshin lfy". yana fadin haka ya juya hadi da ficewa daga dakin".

Itako Aysha Zama tayi dabas a kan kujera ta kasa motsawa,tayaya zata fara ganin ta faran ta ran Yayan nata ne,amma bata sani ba".

Zaune na hango ta,sanye cikin wasu dakakkun Bowel lace masu masifar kyau,wanda suke dauke da Launin Cofee brown,Daurin Ture kaga tsiya ne ta tokaro shi,yayin da fuskan ta ke dauke da Kewayayyan farin glss kuma dan siri wato medical. Dattajiwace wanda ashekaru bazata Haura 50 ba aduniya. duk da hutu ya boye wannan shekarun nata,don bazaka ce ba sai an fada maka, mata ce wanda da kaganta zaka fahimci irin matannan ne masu harkan gske,fatan jikin ta kuwa luff² yana sheki da kashe ido.komai nata karr²..... Da ka ganta kaga farar Bafullatana,fara kuma mai Farar Aniyya,Bakowa bace wannan mata Illah Hajiya Huwaila,Amarya kuma Uwar gida ta wajen Ahj. Muhammad Harun. Wato mahaifiya a wajen Arch. Huday da Iftyhal".
"Ohk mashaallah". Tom dear ina jiran isowan ki fah,ta gumi zaman jiran isowa,sai kuma tasaka dariya". tana mai datse wayan nata hadi da mika shi ga Wata Assistant nata".

Da kuka ta shigo falon hadi da nufan Upstairs da dan gudu".

Bin bayan ta Momy tayi cike da damuwan ganin diyar tata cikin wannan halin tayi saurin kirar Sunan ta da Baby Ifty.." Ifty na". Nan Hjy. Huwaila ta fadi gami da mikewwa don nufan Upstairs don ta lura da daru Autan nata ta shigo.

Koda ko taje tun a bakin Bedroom din Iftyhal ta tadda a gar make,wanda bugun duniya taki budewa,haka tayi ta Bata baki amma nan shiru,babu abun da take jiyota tana furtawa sai kalmar Sunan Khaleed".

Shiru Mumy tayi gami da juyawa tana nufan kasa,wanda da saukan ta dai² Maryam da suka gama waya tana shigowa,da sauri tana nufo Momy tana Rungumeta gami da cewa" Oyoyo momy na, I really miss u".

Murmushi momyn Huday tayi kan daga bisani ta sha fuskan Maryam tana furta Nima haka Daugther na ya Mom din ki,tana lfy?".

Lfyl,ta bata amsa a takaice. Momy ina Iftyhal?.

Nisawa Momy tayi sannan tace" Yau ifty yan darun na kusane,amma tana sama kije ki lallashi Aminiyar taki ko kila ta sauko inta ganki".

Tom Momy,ta fadi hadi da nufan Upstairs...

Niko Wuraren Karfe 5pm ne Oummu Sulym tazo mun,akan itama tunda na janye aiki gidan Hjy Zaituna tom itama ta janye,amma a yau taji labarin Wata Company na daukan ma'aikata masu goge² da shara,don haka su shirya da sassafe su tafi can".

Sosai Oumma na tayi na'am da maganan Oummu Sulym yyn da nan ta kalkeni gami da cewa" Suhaimart kin gani ko? ae duk bakin da Allah yatsaga baya taba hana sa Abincin da zaya ci". ki natsu inshaallah goben zakuje can". Da tom na bi Oumma na,kan daga bisani mu cigaba da taba hirar mu da Sulaym mafi yawa dai dariya nake sha,don duk mgn ce akan inna Atine. wanda daga karshe mukayi sallama akan sai goben.

Dako Sulym ta isa gida,sai da aka ta6a daru da inna Atine acewanta dole sai sulym ta debo masu Ruwa,ita kuma tace sam bazatayi ba,ga inna Wuri nan tayi,sosai Sulym tayi ta amayar da abun da ke cikin ta ganin babu Inna Laure da Baba. itako Mama Atine daki tashige don yau ta lura Sulym din dai ² da ita take a gidan".

Da safe ko kaman yanda mukayi da Sulaym karfe 80.00am muka bar gida yyn da Oumma na ta bimu da Addu'a sannan muka fito".

Me Napep muka tara hadi da sanar masa da companyn da zamu nufah a yanxu wanda yake can wajen gari,wuraren Samaru kafin ka kai Abiation.


Bangaren Ko Iftyhal dajin muryan Aminiyan nata ne ta bude kofahn da sauri hadi da koma ta fada kan makeken gadon ta tana mai jawo teddy jikin ta tana wani irin kuka mai dacin gske".

Da sauri Maryam ta saki Wasu doguwar rigar Gown da ta riko,ala dole taxo nuna mata shi duka zasu saka aranar Get togethern da zasuyi shi yasu yasu nan da Kwana Uku,wato su kadai kaman Ita Maryam,Aysha,don dama Aysha kawace a wurin Maryam tun bayau ba,sai Iftyhal,Abdoul manan,Huday,Khaleed sune kadai zasuyi wannan Get togethern wanda duk cikin shagalin bikin da zasu fara Gabatarwa ne.


Hmmm niko Maman teddy nace anyah na za'ayi bikin nan kuwa,naga wuta tafara ballewa ne ta ko inah. Inajiyo Addu'ar ku gareni da kuma gdyn ku ,nima ina gdy kwaran gske,Allah yabar mun ku yabar kauna".

Cike da matsananncun damuwa Maryam ta nufeta hadi da tambayan ra lfy? meya sameta".

Da kyar Iftyhal ta samu ta dai² ta na tsuwarta tafara koramawa Maryam zancen komai da yafaru dangane ita da Suhaimart.

Wani dogon tsaki Maryam tajah,hadi da jawo Asha riyya tana Auna ma Suhaimart dacewa" Yar matiyata kawai,wlh ki bari sai mun batar da wannan Yarinya". Amma ki bari ba yanxu ba,for now ki kwantar da hankalin ki,ki nuna kaman komai ya wuce maki,idan kikayi haka shine nan koda anyu komai vaza'a zargemu ba".

Kisani nan da Kwana 13 ne biki na da Huday, amma kifara kirga rayuwr wannan yarinya da Duk Dangin ta yazo karshe. nayi maki Alkawarin wlh sai munyi bikinan cikin Kwanciyar hankali,kuma kafin nan kinsan Khaleed ya zam naki har Abada".

Dariya suka sheke dashi,wanda Huday da yake bakin kofah don Momy ce ke sanar masa da zuwan Maryam shiyasa ya nufo bedroom din Iftyhal din,kansa ne ya sara masa rasss....

Dajin mugun nufin su akan marainiyan Allah,wani tausayin Suhaimart ne yaji ya tsirga masa". da kyar ransa yagama baci sosai ya juta hadi da nufan varayin sa. a Zuciyan sa yana mai wasiwasin anyah ya samar ma y'ay'an sa Uwa ta gari kuwa??".
Hmm muje Zuwa fans..💃🏻.


Niiko da Oummu Sulym bamu isah wannan Company ba sai Wuraren 9.00am.

Mun dan sha wahala matuka kan Abar mu muka shifa daga cikin companyn,don mun sha bincike har mun gode Allah, don da kyar duk da hakan suka barmu,banda bin mu da kallon wulakanci babu abun da wa'annan securities sukeyi, Suna kare ma surfaffun Atamfan jikin mu kallo,wanda ya dade da fita kamannun sa". Bakar hijab nasaka amma aaboda koda gar jajjah takeyi daga sama".

Da kyar dai suka bar mu muka shifa don ni nayi ta masu magiya akan su taimakemu. A haka suka hadamu da Shugaban Masu Cleaning din da share² n da kyar.

Itama kam fa ba wani arziki ne da itaba,amma abun ka ga mutanen Nigeria da sungan su wani matsayi sai su nima taka mutum,nan itama ta bimu da kallon Wulakanci don taji mai ya kawo mu". Office nata ta nufah damu,hadi da bamu ma sauki. Tana mai mana wasu yan tambayoyi,da tambayar mu inda muka da kata da Karatu,anan duka muka bata amsa da Secondary muka tsaya,don ni a SS 1 na dakata,har gomma Sulaym takai SS3.

Muna a Zauna ne wani mutum sanye da shigar sa ta court ya shigo,wanda nan naga tayi saurin mikewa hadi da dan Rawar jiki tana furta Weldone Sir".


Ammm Mhiss Zayyad Muna son ganin ki yanxu".

Okay Sir ".
Abin da tace kenan hadi da saurin bin bayan Wannan Mutumi da babu shakka ko ba'ace ba wannan bayahude ne. nine mai fadan haka a Raina".

Zama mukayi mukayi shiru,babu mai magana,don Oummu Sulaym hankalin ta nan kan Wurin da ya kayatu komai abun burgewa ne da kallo". Ko wani lungu glass ne,da na'urori gasu nan dai".


Bin wani Hop nayi da kallo,wanda nan take kirjina ta buga,ido ba kuma zarowa waje ina kare ma Hoton dake jikin Garun da kallo,don bakowa na gani ba Face Sir Khaleed,da shigannan nasa kai ka rantse bature ne.

Zaro ido nake ina mai kuna fito dasu,dai² na bude baki ne zanyi ma Sulaym mgn, Mhiss Zayyad ta shigo".

Don Allah ku biyoni. Babu musu duka muka bike hadi da bun bayan ta. Tfy mukayi mai dan tsawo wanda duk wani wuri da zamu wuce sai na Urah tagama lacce mu tass,sannan.


Ahaka muka isah wani Office da girman sa ya tsora tani,amma na dake sam na waje na baya hango mu,amna mu komai ganin sa muke kaman a gaban mu".

Tun daga nesa muka hango shi zaune kujeran nan na juya shi gaba daya hankalin sa na kaina". Wani sanyi yakejin yana ratsa shi.

Zaro ido waje Oummu da sai ayanxu ta ganshi tayi".

Niko da gudu na juya da zummar futa na koma inda na fito,amma sai wani sexurity yy yunkurin tareni. Banyi aune ba naji Sir Khaleed yasar masa wani wawan tsawa akan ya varni. da sauri ba fice hadi sa gudu² sauri² don na bar ma'aikatan".

Napep na tara,hadi da shigewa ciki nan na bar Oummu da Sir Khaleed don bansan dunuyar dasuke ciki ba".

A layin tudun wada ya sauke nidon daganan ne kudi na ta kare,shi yasa na fara takowa dan shifa cikin Zaria da kafah".

Nayi tfyn fiye da Awa daya sannan na isah gida".

A bakin gidan mu ne ta tadda wata moto da sam ban wani tsaya kare masa kallo ba nayi cikin gida,don na kwaso gjy sosai.

Amma kuma da shiga na a bakin Kofan dakin Oumma na ne wazan gani kuma naji?. muryan Sir Khaleed naji yana mgn da Oumma na,wanda hakan takuma haddasamun bugawan kirji.






Mu sani Free page na gab da karewa,inshalh free page zai kare a page 15.

Don haka mai bukatan karanta littafin ZUMA DA MADACI zai turo #200 na NORMAL DA VIP. SPC kuma #300. duka katin MTN ta wannan Number 08081202932/09137392680.




*#SHERE TO ANOTHER GROUPS*






*Maman teddy 🧸*
*Typing...✍🏻*

🎋🎋🎋🎋🎋🎋🎋
🌹🌹🌹🌹
🌿🌿
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_


Na
*Maman teddy🧸*

*page 15*


*_________________________*


*ALHERI WRITERS ASSO.📘🖊️*

*A.W.A*


```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri💪🏻```

*___________________________*


*بسم الله الر حمن الر خيم*


_Dedicated to my teddy🧸Wannan pagen taki ce y'a d'aya tilo😂._


*_Domun samun Littafin Zuma da mad'aci tun daga farkon sa har karshe zaki tuntubi wannan number 09137392680/08081202932._*


_*Plz don't miss dis novel,the latest Hausa nvl in 2021.*_
_*Do not miss this Novel Hajiya ta,idan baki karanta ba an barki a baya Hajjaju....💃🏻*_

*_____________________________*


Wani gumi ne ya hau karyomun,yyn da lokaci guda cikina ya fara murda mun,kasa daga ko kafafuna nayi,so kawai nake najiyo Mai Sir Khaleed da Oumma na suke cewa,amma nakasa jiyowa".

Motsin su danaji alamar kaman fitowa zasuyi yasani saurin motsawa don na gudu,amma inah banyi wani motsi ba". Har ya fito daga dakin,Oumma na kam na tayi masa godiya". Kafe ni yy da wannan mayan kallon nasa,wanda yasani saurin sidda kai na kasa,don sau dayawa inyana mun irin wannan kallon bana fahimtan komai da yake nufi. Wani kasaitaccen murmushi ya sakarmun hadi da bin jikina da kallo ganin yanda nake ta Rawar kyarma kaman wanda nayi gagarumin laifi".

Oumma na tafi".
Tom Khaleed Allah ya tsare". Amin yace da itah kan daga bisani ya fice,niko baki bude nake bin Oumma da kallo,sarai nasan Halin Oumma bata da Kwadayi,amma wannan Abun da nagani mai take nufi kenan?_ Tabbas da akwai wani abun a kasa".

Kallon sama da kasa Oumma tayi mun,kan tace maza kiyo Alwala idan kin kammala inason mgn dake". Niko cike da sakin baki nace tom Oumma hadi da juyawa don nufan Daki na".

Wasu maza ne cike da sallama suka shigo gidan namu,dauke da Caton da buhun hunan Kayan Abinci, Wanda bani ba har Oumma na sai da tayi mamaki,nan tayi saurin cewa" Wannan kuma daga inah yan samari". ta fadi cike da son jin daga bakin su".

Kai tsaye suka bata amsa da Alhaji ne yace a shigo dashi".

Nidai tunda naji haka najah kafa na da sauri hadi da kutsa kai cikin Daki na,ina mai lalubar magani na don nasha".
Da misalin Karfe 8pm.
Zaune duka familyn Gen. Yaqub D'an larabawa duka kowa ka kalli fuskan sa yana cike da matsanancin farin cikin dawowan Dad din nasu". Fira yake da Nana Aysha yyn da take koro masa zance kaman gidan radio". Don dama haka take ita Aysha,nasu sosai yazo daya da Dad. shiyasa kullum take aikin sintirin tsakanin Zaria da gombe".

Kallon Khaleed yy wanda tunanin sa yy nisa kan laptop din gaban sa,wanda sunan yana kallon Laptop din ne,Amma sam hankalin sa ba anan take ba". sosai yayi nisa wajen tunanin Rayuwar Suhaimart don shi a iyah saninsa Tausayi ne yafara shiga masa nata,wanda daga karshe ya fahimci da ya kamu da Azababban sonta". Khaleed kuma irun wannan mutanen ne da idan suna kaunar mutum to ko ainah zai ce yanayi,idan baya kuma Ra'ayin ka kashiga uku da Hantara.

Tuni Mahaifin nasa ya dago da damuwa tare da d'an nasa,don haka ne ya gyara zama yana mai kallon dukan su ta hanyar cewa" Amm Hajiya Zaituna dama ina son wata yar magana ce daku,don haka don Allah inason ku bani hankulan ku".
"Tom genar muna sauraren ka".
Gyara zama Genar yayi kan yafara cewa" amm dama naji mgn ce game da Khaleed da kuma wata yarinya da naji ance mun yar aikin nan gidan ce! tom so nake naji gakyar maganan a yanxu".

Wani kayataccen murmushi Hajy.Zaituna tayi don an tabo inda yake mata kaikayi,don a yau za'ayi ta ta kare dole ne Khaleed ya janye daga soyayyar wannan Yarinya mai kyau Aljanu. Cike da kwantar da murya gamai gidan nata,ta fara cewa" Kwarai kam Genar dama nima inaso nayi maka mgnar,amma sai na bari ka huta sannan,mashaallah tunda yanxu kaji lbarn dai duk da ba duka ne ba!.

Nisawa Hajy.Zaituna tayi kan ta fara koro mawa General komai da yashafi Khaleed da Suhaimart,wanda daga karshe ta sanar masa da natsayan ta akan cewa ita sam bata kaunar ta,kuma dole ne Khaleed ya rabu da itah".
nan ta kuma cewa" Amma Genar kar muji Haushin Khaleed, wannan yarinya ne shaidaniya,don ina tunanin Wlh bata barmun Yaro haka ba".

Jin maganar da Hajy. Zaituna take zibowa yasa Genar saurin daga mata hannu alama na ya isah!!
Sannan cike da d'an bacin rai ya fara cewa" Haba Hjy,da girman ki da hankalin ki kuma? wannan mgn taki sam batayi mun dadi ba,mene naki na shiga Hurumun yara,shifa Khaleed yace yana son ta,don haka ni sam bazan masa dole ba,kuma kema idan kinyi tunani hakan muce zamu masa dole sam ba'abu mai kyau bane,ki natsu ki sa hankalin a mizani Hajy plz.

Mikewa tayi daga kishingiden da tayi daga jikin Kujera da sauri don har zufah tafara tsatstsafo masa,a sarari ta fara cewa" Yalla6ai Genar mai nakeji daga bakin ka??. Kana nufin Zaka Aurar da Khaleed da wannan yar gidan matsayatan yar talaka?.
Kallon ta yayi cike da dattako yace hajy A gaban yara fa muke,wannan duk mgnan ki bari sai mun zauna daga ni sai ke,Amma maganar Aurar da Khaleed da Wannan yarinya babu fashi,inda yana kaunar ta,Nan ya mai da Hankalin sa ga Khaleed da ya sunkuyar da kai tunda Hjy. Zaituna tafara mgnan har ta gama bai dago ba".
Amm Khaleed Ka kwanatar da Hankalin ka zan Aura maka Suhaimart indai kana sonta,kuma baxaka cutar masu da y'a ba". Don haka kaje ku fahimci juna sosai,ni Mahaifin ka na baka go Ahead,duk randa kuka shirya zan nemi iso ga Iyayen Ta". Zaro ido waje Aysha tayi tana d'an ihu hadi da Rungume Genar tana fadin Dad mun gode,Allah yabar mana kai". Murmushi yy hadi da ce mata Bakomai mama na". ku shiga daga ciki inason mgn da Mom din ku ne".
Sai a sannan Khaleed da Farin ciki ya gama cika shi yasamu bakin cewa" Tom Dad na gode,Allah yakara girma da daukaka".

Ameen Khaleed ".
Nan Aysha ta riko Hannun Khaleed cike da Murna sukayi waje".

Shiko A wannan Rana sosai Genar yaso ganin Hjy.Zaituna ta amince da mgnar nasa,amma ina sam ta kiya,har ya gaji yace shi sam Bazaiyi ma Khaleed dole ba,Aure kam zayayi masa nan kusa,tunda Yaro ya nuna yana son yin Aure kuma yana son yarinya".

Niko nace muje dai Zuwa💃🏻 .
Kar dai kumanta free page yakare daga wannan pagen,don haka idan kina bukatar cigaban wannan littafi ki tuntubi wannan Number 08081202932.


Niko tunda na shiga daki sam na kasa fitowa sai Wuraren La'asar wanda da fitowa na natadda Oumma Zaune bakin Wuta a madafi( Kitchen ), wanda da'alama tana hidimar dora abincin dare ne".

Barka Da gida Oumma". Dagowa tayi tana kallo na kan daga bisani tace mun Yowa Suhaimart, bacci kikayi ne?.

Ehhh", Amma yanxun na tashi Alwala ma zanyi".
tom idan kingama kizo inason mgn dake". Tom Oumma na". ina fadin haka na dauki Buta don yin Alwala,bayan na gama ne na nufi da na nayo Sallah.

Fitowa nayi bayan na idda sannan nashiga dakin Oumma na".

Sosai na firgita da Maganar da Oumma na ta mun,wai acewanta Bata yarda na bar aiki gidan Hjy.Zaituna ba". Kuma tayaba da Hankali na Khaleed, bata yarda ta kuma jin wata baraka daga gareni ba". Sosai Oumma ta dinga yimun fada hadi da zagi na,wanda daga karshe ne Tafara lallami na akan nayi hakuri na so Khaleed, ni danake Marainiyya mara gata Talaka,amma irin wannan mai Arxiki yazo yace yana sona nakiya". Don haka nan tace mun na kuma tunani,amma ita tana mai son sanar mun da ajiya tayi masa Alkawarin zata Aurar dani ga Shi Khaleed din,ko naso shi kona kishi wannan duk ni nasani". Nan tace na tashi na bata Wuri,haka jiki na sarai ya mutu da mgnar Oumma na,daki na na shiga don naga Oumma na Ranta ya baci, Tabbas a raina inajin Kaunar Sir Khaleed, amma ni gani nayi ni bakowa bace,bana da Uba da Asali,anyah zai kaunace ni,amma sai naga akasin haka,don a bayanan Oumma na cemun take,wai Khaleed ne Abun tausayi tunda ya kamu da son Ice matacciya wanda batason maiye so ba".

Kuka ne ya kwacemun,tuno da tijaran Hajy.Zaituna, don wlh nasan baxata taba kauna ta naba,Wanda ni kaina a halin yanxu tausayin Sir Khaleed nakeji na kurewa" Yana neman ma kansa illah duk ta kaina,yaya zanyi ni hakanan zan kokari naga hankalin sa ya natsu kaman da". Haka zan amince da shi koda ko Hjy. Zaituna kasheni ne zatayi,tunda Oumma na na kaunar sa dole ne naso shi nima". Tabbas na yarda Sir Khaleed bason yaudara yakemun ba tundaga kan Abun da yafaru a jiya".

Shiru nayi ina a Zaune naji Muryan Sulaym tana Gaisar da Oumma na,wanda kaman ba ita ta gama zagina ba,cike da harka ta amshi Oummu Sulaym hadi da sanar mata da inda nake".

Ae da Sauri ta kutso kanta daki na,muna hada ido muka saka dariya duk da damuwan dake cin Zuciya ta".
Mun ga takanmu Suhaimart, kinga wannan mai mukayi kenan,munyi gaba mun dawo baya". Murmushi nayi mata kan daga bisani nace,tom ya zanyi Sulaym,yanxu Oumma na tace sai na koma bakin aekin gidan Hjy. Zaituna ".

Na fadi cike da nuna damuwa kan fuskata". Tom meye,ae dama komawan mu dole,wai na tambaye ki tsoron Hjy.Zaituna kk ne? Wlh Suhaimart ki natsu,shin da itah zakuyi soyayya ko da d'an ta"? don haka ki share komai,wlh jiya Sir Khaleed ya ban Tausayi yanda yake Rokona akan nasa ki Kaunace shi,Har Kwallah sai da ya kwanta akan idon sa". Haba Suhaimart a wannan Zamani ki samu mai maki Wannan zafin son!?.

Don Allah ki yarda ki amince da Sir Khaleed, a ranar biki mucashe mu jagije".

Dariya nayi mata ina mai cewa" Oummu na Amince da Sir Khaleed dama tuni,amma ni tsoron Hjy.Zaituna nakeyi Wlh ". Na fadi hawaye na sakkomun kan fuska ta". saurin sharemun hawayen Sulaym tayi kan tace" Ni ina ji ajikana babu abun da zai faru,ki natsu ki maida Hankalin ki akan Sir Khaleed, don na gaya maki wani gulma,itafah wannan Iftyhal din ashe son Sir Khaleed takeyi,da yake ita yar wahala ce".
Zaro ido nayi ina cewa" kinganki ko Sulaym wlh tsiwanki shi zai jahxamana fitina".

Taba baki Sulaym tayi kan daga bisani tace" Wlh bakomai,ni wai ina tsoro ne,abun da na fada bayan idon ka shi zan maimaita koda kuwa itace a gaba na,ai kin sanni basai nace maki komai ba".

Dariya nayi ina mai cewa" Kwarai kuwa Aminiya ta kuma".

Haka dai mukayi ta firar mu muna Dariya cike da nishadi kaman kar mu rabu da junan mu".

Bangaren Huday kuwa,a wannan dare yanda yaga rana haka ya ganta,sam ya gaxa rintsawa,wanda daga karshe mikewa yy hadi da nufan Toilet ya dauro Alwala hadi da yin nafila,yana a zaune bayan idar wansa sosai yake addu'a kan Za6in Allah kuma nagari. sannan ya mike hadi da nufan falon gidan nasu". don a gidan Momy Huwailah ya kwana".

Zaxo wuce Dairning Area ne nan take idon shi ya sauka akan fuskar ta,wanda take dauke da ,sanye kuma cikin Uniform din ta mai launin skirt Dark brown da farin riga". kafe ta yayi da ido,wanda nan take lokaci daya yafara tunanin Ta a Zuciyan shi". A sarari kam furta wa yayi I really miss u my little". Cike da jin matsanancin kyewanta ya nufi Dakin ta da yake a gyefen na Momy,kutsa kan sa yayi ciki yana mai tunano abubuwa da yawa,Zazzakan muryan ta na masa amo a kunnen sa Hamma na yau Daddy na zai dawo,kuma Daddy yace next Mounth zamu bar nageria mu koma Abroad da zama,saboda Momy zata tafi karo Couse acan". Plz Hamma Huday kar mu tafi ni bana son na Rabu da Nanny na".
Kallon ta yy hadi da rungumo ta yana kallon ta da A lokacin bata fi shekaru 4 a duniya ba". No my little zamu tafi,amma baxamu dade ba xamu dawo".kuma idan ma kinason wata Nanny ne Daddy zai dauko maki wata mai kula dake,kaman wannan".
A'ahhh...Uhmmmm....Niiiiii Uh"umm. nan tafara kuka hadi da saka masa rigima akan A'a.

Jin yayi bige wani abu kaman Glass yasa shi dawowa daga duniyar tunanin da ya lulah,saurin kallon Wurin yayi yana mai saka Hannun sa yana daukan wani Cup da yake irin na glass ne,amma gyefe guda dauke da Hoton ta da ya zana ta tun a shekarun baya". Kwallah ne ya ciko masa ido kissing din Pic din nata yafara yi yana fadin kalmar I miss u my.....

Niko maman teddy bin ko'ina na dakin nayi da kallo,wanda ta ko'ina hotunan wata diyace y'ar shekara 4\5 a jikin bango dama ko wani Wuri in idona ya sauka akai. ni kaina kyaunta sai da ya fixgeni,yarinya ce kyau har kyau ko Y'ay'an turawa Albarka,nikam mashaallah kawai nake furtawa".

Kan tarkato na fito ina mai son Kawo maku Rahoto dangane da wannan yarinya amma ina gani nake babu isashen lokaci".
Amma maji a gaba".

Tun safe na tashi nayi shiri na tsaff sannan na nufi dakin Oumma nayi mata sallama akan zan tafi aiki na. da Addu'a ta bini dashi,sannan na fice ina mai jin dadi matuka da Yanda Oumma na sam bata gajiyawa da mun Addu'a hadi da samun Albarka".

Iyaye mata plz we have to take note,idan yaran mu zasu fita zasu bar gida,mu ringa kokari muna bin su da addu'a ahaka har su dawo,inshaallh zasu da cikin yardan Allah batare da wani abu ya cutar da su ba". Musamman mun san Bakin Uwa akan y'ay'anta". Don haka mu ringa daurewa munayi,in ma bazaki iyah ba,ki kokarta kisa ko shi yaron yy Addu'a kan ya fita,kaman Ayatul kursiyu,Nasi,ihlas da

Please Login or Register in order to submit comment