Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya kakalo murmushin dole ta hanyar cewa" Ammie wlh bakomai,kawai dai Rayuwar Yarima Abdoul ne yake damuna,wai ace Ammie mutum har ya isa musali ya isa munxali,anki bude masa Sirrin da aka rufe tsawon shekaru,inba a sanar masa yanxu ba tom yaushe zai sani,yaushe zai shaida ni y'ar uwar sa ce ta jini,kullum yana mun kallon bare,wlh na gaji da wannan Buye masa matsayuina da akeyi". Ta fadi tana mai cuno baki gaba".

Murmushi Ammie tayi tana mai zama gyefen Diyar ta ta, A hankali ta fara mata magana cike da taushin murya,Nanah Aysha ki fahimceni,sam bana son Karajin wannan mgn daga bakin ki,kisani idan maganan nan ta fita nice za'a kira da babban kawai,wannan sirri ne datake Rufe tsawon Shekaru 30 da dori,kuma ni na sanar dake tsakanin ki da Yarima Abdol Manan ne badon komai ba sai don Ki samu soyayya daga gareshi,ta haka ne zamu shayar da fulani mmki,kuma abun da take ganin baxai yiwu ba,xataga tayiwu". Amma idan kikayi gaggawan sanar mawa Da Abdoul Manan cewa" Fulani ba mahaifiyar sa bace,tom wazaki ce mahaifiyar tasa?

Dole ne mu cigaba da Rufe wannan sirrin Har Allah ya nuna mana lokacin da komai zai fito sarari makiya kuma suji kunyah,dan hakin dama daka raina shike tsone maka ido. Nanah Aysha kicigaba da hakuri,duk hantaran da Abdoul manan zai nuna maki kar ki damu,kisani bayan wuya sai dad'i".

Nisawa Nana Aysha tayi kan daga bisani tace" Ammie shin kinji Labarin tafiyar Hamma Abdoul kuwa??.
"Wai naji ance zai tafi Zaria ne,but bansan maiye manufar Zuwan sa can din ba".
Dariya Ammie ta sakar ma diyar ta ta,kan daga busani tace" Naji lavarin hakan Aysha,Don maimartaba oready ya sanar mun,Sannan zuwan Abdoul Manan Zaria ki sani ba wani avu bane zai kai sa illah dawowan Aminan nasa wato Huday,da Khaleed.
Ammie da wayyo dadi da gaske???, indai ko Haka ne A satin nan zan tafi Murmmyn Khaleed". Nayi mata Hutu can,cox Ammie na nasan In Hamma Abdoul bai sauka gidan ta ba,to kilah baxai wuce gidan yah Huday ba".

Dan murmushi Ammie tayi cike da jin dadin maganan Ayshan,da cewa xataje yima Yayar ta wato Hajiya Zaituna Holiday don sam Aysha bata son shiga cikin jama'a,amma yau sanadin Yarima Abdoul zata je har ta jima can Garin Zaria. kai masha Allah". Abun da Ammie tace kenan,kan ta mike tana furta Aysha Abban ki na kan Hanya,bari naje na cigaba da shirin dawowan sa!!".

Tom Ammie nima yanxu inna kammala Duba magazine din nan zan fito".

Wahhh ke din ce zaki fito,bayan kin fara duba Magazine din ki na fama"!. Hmm ae nasan fitowan ki ba yanxu ba". Dariya Aysha tayi tana mai cigaba da Gyara Medical glass din ta,tana karanta wasu news.

Ita kam Ammie Juyawa tayi tana mai rufo mata kofah,a ranta tana jajan ta hali irin na Aysha,kullum ka ganta a koke duba Jaridu,idan baka ganta anan ba,zaka ganta tana watching News...Ae wannan ko shi SENATE IBRAHIM DUTSE wato ma haifin Aysha bai wannan Resarch din irin nata lokacin yana da Kuruciya haka".
Haka Ammie tayi ta zancen Zuciya har ta isah Tanfatsetsen falon ta da yasha Ado da kayatuwa har ya gaji".

Ma'aikatan ta ne suka fara mata barka da isowa",yayin da nan ta amshe su cike da karramawa irin ta matan da suka san darajar dan Adam,don yanda take masu sai da na fada duniyar tunanin Anyah Ammie Safiya da Mum Zaituna yaya da kanwa ce???. Hmm Hakan ne tunda da bakin ta Ammie Safiyya ta fadi".

*GARIN ZARIA*
Bangare na kuwa ni Suhaimart A washe gari da sassafe na kammala shiri na na tafiya wajen Aikatau dina dana saba,don haka bayan nayi mawa Oumma na sallama ne na yo waje hadi da tare me napep gudun kar na makara na samu wata matsalan dan gane da aiki nah".
A haka muka shigo G.R.A zaria,wanda jefi² nake kallon wurare dabam².
Ido na ne ya sauka kan wani gida,wanda nan take naji kirjina ya yanke ya buga,saurin dafe kirjina na nayi,ina mai karanto Ayar Allah,har na samu natsuwa,wanda duk da hakan girman gidan har Ilah yau bamu wuce ta ba,gida ne mai mahaukacin girma da tsaruwa,wanda gaba dayan sa yake mamaye da Sojoji da jami'an tsoron lafiya.Zufah ne ta hau karyomin ta koinah,tabbas a jiki na inajin na taba Rayuwa a wannan gida". Amma kuma a yaushe a wani lokaci ni ban sani ba!!!.

Dafa kaina nayi ina mai son tunowa amma na kasa,Wage dankareren gate din da akayi yasa mai Adaidaita danake ciki dakatawa don wanda aka bude ma gate din gidan ya fito sannnan muyi gaba".

Idona ne ya sauka akan sa,wanda a sarari na furta la shakka dama nasan kaine Ya Huday ". kawai sai naji zafafan hawaye na bin koinah na fuskana. Ta jikin madubin me Adaidata na kare ma Fuskata Kallo,yanda nake a kode a kuma jeme,ga wani baki da nayi,uwa duniya baxaka taba cewa Ni Suhaimart fara ce karr ba".
Share Hawayen kan Fuska ta nayi ina mai bai Uzuri A rayuwa,don tabbas wanda yasanni abaya baxaya taba cewa nice dai Suhaimart ba'.

Tayarda da napep din da yy ne yasani ankarewa da Moton Huday ya wuce,nan naga me napep din yana wani irin gudu dani,wanda cike da sanyin murya ta nace Don Allah Bawan Allah kajah ni a sannu".

Tom Hajiya" Wannan saurin dana keyi wlh badon komai bane,saboda Nayi saurin kai ki ne,Saboda kinsan mai neman takarar mataimakin Shugaban k'asa wato Alhj. Muhammad Harun Ya dawo kasannan yau...
inkuma su kafara isowa baxamu samu hanya ba".
Gumm na masa da baki,ina mai kara maimata Sunan Mataimakin shugaban kasa Alhj. Muhammad Harun...
A haka banyi Aune ba naga ya tsaya a daga nesan gidan Hajiya Zaituna don sam mutane basa rabar kofar gidan,saboda wa'annan murda² n sojojin da suke safa da marwa hadi da bin mutane da mazurai".

Sallamar sa nayi ta hanyar basa kudin sa sannan na nufo cikin gidan,ina mai gaisar da Securitie din da sojojin sannan na nufi barayin Hajiya Zaituna,don na gaisar da itah".
Hmm sosai na wulakan ta duk da daman wannan halin tanne wulakanta talaka,mussaman mai mata aiki a karkashin ta".
A haka na nufo side din Sir Khaleed, wanda da isana na tadda mhiss caterine da mataimakin ta wato Mr. faul".
Gaishe su nayi saurin yi ina mai nufan kitchen don na kammala ma Sir Khaleed breakfast.

Cike da natsuwa na fara komai,wanda ba tare da na dauki wasu lokuta ba na kammala masa,hadi da fara jera komai a kan dirning area.
Sai da na kammala komai ne sannan na daga kaina hadi da bin Agogon falon da kallo,yyn da take nuna mun karfe 7:15am.
Shiru nayi ina mamakin rashin fitowansa har yanxu,wanda a haka ina tsaye fiye da mintoci nan na nufi,wani dan daki daga wajen falon nasa yyn da nayi saurin daukan Sweaping Stick,sannan na dawo na fara gyeran falon nasa da kitchen da sauran dakunan da suke a jere a falon. Bayan na kammala ne na dauko Mopper na fara moping din ko inah na falon,da kammala wa nane na fara bin Falon da Room freshner,ina a haka na fara jiyo takonsa hadi da shakan daddadan turaren sa,don dama tuni na fahimci Sir Khaleed ma'abocin son Kamshi ne,komai nasa ka daga sai kaji yana wani irin kamshi na dabam.

Dariyar su naji wanda sam bansan shi da waye suke wannan dariya ba". Don nasan Sam Khaleed ba wani harka ne dashi ba". Ajiye Turaren hannu na nayi a gyefen wani Table,yyn da dai² suna karakowa inda nake a tsaye". dago kai na nayi,yayin da dai² yana kallo na,saurin sidda kai kasa nayi ganin hada idanun da mukayi,shikuwa murmushi ya sakar mun mai kayatarwa".
Sai da suka taho gab da nine cike da Sanyin murya na nace masu Barkan ku da isowa,antashi lafiyahh!!!?
Babu wanda ya bani amsan gaisuwa ta,wanda hakan ya haddasa mun faduwar gaba,tom kodai yaji Duk abun da nayi mawa Sulaym jiya ne???.
Hmmm nisawa nayi sannan na kuma nufan su,yyn da dai² suna zama akan dirning. Kwallah ne ya ciko mun ido,nan nayi saurin mayarwa don kar su lura,amma abun da ban sani ba shine tuni komai nawa a kan idon shi nakeyi". Ya fito ni yayi da Hannu". Cikin sauri na karaka inda suke Wanda a hankali nake komai na nafara serving nasu, don ban kuma ce masu komai ba". Shiko Sir Khaleed tuni yayi nisa a fadawa dunuyar tunani na,don Magana Abdoul manan ke masa bai ma san yana yi ba".

Komai na Suhaimart burge sa yakeyi,sam baya gajiya da kallon ta,binta yake da kallo yana mmkin Saurin kukan ta mai kama da shagwaba!!.
Sam bai san lokacin da labban sa ya furta I love u Suhaimart ba".
Due a hankali yy maganar don ita hankalin ta sam baya tare da ita ta kosa ta basu wuri,don tuni ta lura da dukan su irin samarin nan ne yan duniya idon su carrr yake,shiya sa sam bata ji mai ma yace ba!.

Murmushi Abdoul manan yayi yana Kallon sa dacewa " Yah Mutumin Kodai ita ce?.

Bai basa amsa bai sai murmushi da yy masa,wanda dai² ina kallon su da furta Bismillah!.
Murmushi Sir Khaleed yy hadi da mikewa daga Zaunen da yake Matsowa dab dani yayi hadi da jah mun kujera,Hayateee na Zauna nan muyi break".
Murmushin da ke dauke akan fuska ta ne na daina lokaci guda. saurin waigawa inda Abdoul manan yake nayi,nan take kwallah ya ciko mun ido,lokaci daya hawaye kaman wanda aka buga ya fara xubo mun".
Girgixa masa kai nayi alamar ya rufamun Asiri,kar ya jah mun fitina...





Littafin ZUMA DA MADACI ta kudi ne,Normal and VIP zaki turo #200, idan SPC ne #300. duka ta wannan Number 08081202932./09137392680.



Maman teddy🧸
*Typing...✍🏻*

🎋🎋🎋🎋🎋🎋🎋
🌹🌹🌹🌹
🌿🌿
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_


Na
*Maman teddy🧸*

*Episode 13*


*_________________________*


*ALHERI WRITERS ASSO.📘🖊️*

*A.W.A*


```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri💪🏻```

*___________________________*


*بسم الله الر حمن الر خيم*


_Dedicated to my teddy🧸Wannan pagen taki ce y'a d'aya tilo😂._


*_Domun samun Littafin Zuma da mad'aci tun daga farkon sa har karshe zaki tuntubi wannan number 09137392680/08081202932._*


_*Plz don't miss dis novel,the latest Hausa nvl in 2021.*_
_*Do not miss this Novel Hajiya ta,idan baki karanta ba an barki a baya Hajjaju....💃🏻*_

*_____________________________*


Cikin sauri don bakin shi har Rawa yake sam baya son ganin 6acin ranta ko damuwa a tare da ita,da sauri ya furta i'm sorry Suhaimart bazan sake ba tunda bakya so".
Ban basa amsa ba illah saurin jah baya da nayi ina mai barin falon da sauri yykin da Hawaye har illah wannan lokaci bai dai na Zuba mun ba".

Zama yayi Da6as,jikin sa sam babu isashen kwari,Da kaganshi zaka fahimci yana cikin damuwa matuka". Cike da jin matsanancin tausayin Sir Khaleed Abdoul Manan ya kai Hannu ta hanyar dafa kafad'an Aminin nashi,Alaman Ban hakuri Bisa komai".

Dagowa Khaleed yayi yana kallon Abokin nashi,wa'annan Segxy Eyes din tuni suka kara kankancewa,idon shi kuwa ya kad'a daga fari zuwa jah,da ka ganshi zaka fahimci yana cikin damuwa na kurewa.
Da kyar kuma ya iyah motsa labbansa ta hanyar cewa" Abdoul Manan ya zanyi Suhaimart ta So ni!!.
Itace komai na ya zanyi Wlh bazan iya rasata a Rayuwa ta ba".
Suhaimart ita ce komai na,plz Abdoul Manan ya zanyi ta soni,wlh Son ta nakeyi Auren ta Zanyi,ta haifamun y'ay'a masu kyau irin nata,tare da kyaun Halin ta....I can't do any thing without her Abdoul.
duk maganan nan da yake sam yin su yake baima sanin Abun da la66ansa ke futarwa".

Abdoul Manan ne ya kuma dafo shi yana furta Hee Guy ka fahimta,Haba Khaleed kaman bakai da nasani ba"? Inaso na sanarma ka Suhaimart baxata ta6a kinka ba,Kawai ka fahimta tsakanin ka da ita akwai tazara ne mai tsayi,wanda abu ne mawiya ci Suhaimart ta amince da soyayyar ka,don zatayi tunanin ita fah ba yar kowa bace,kuma zata ga ita bakomai ba ne akan ka".

Ehhhh Abdoul Manan Amma yakamata ta soni,ina mata Reall luv,wlh ina son ta Abdoul, ta soni,inda zata saurare ni ae da tayi tunanin True love never End!!!.

Niko Suhaimart da nake a rakube jikin wani Coridour don na kasa fita a halin da nake ciki,kar na hadu da wani afara sakamun alamon tambaya,shiyasa na dawo da baya na Rakube daga gyefe wanda sam kowaye baxai fahimci da mutum a wirin ba".
Kuka na kara sakawa sakamakon yanda naji Gaba Daya Sir Khaleed ya sauya,tabbbas koba afadamun ba a yanxu ni kaina zan gasgata ba wasa ne Sir Khaleed yakeyi ba,soyayya ta kaman yanda yace tana neman Fitar da hankalin sa,sam zai iyah bayya na ta a gaban koma waye!.
Tuni tausayin kaina ya gama kamani,ga kuma tausayin Khaleed don a daya barayin na zuciya ta ina zullumi da fargaban ranar da Hjy Zaituna xata samu wannnan labari".
Don sam baxata amince dani Suhaimart a matsayin suruka ba.
Cikin sauri na mike hadi da nufan barayin mu don naji shiru babu alamar da akwai wani daga wajen...
Barayin mu na nufa direct,wanda da isana na fada gadon mu ina mai cigaba da Rushewa da kuka mai cin raina da ban tausayi...

A sarari nake furta Hohohi ni yo ya zanyi,maiyasa Khaleed ka bari zuciyan ka ta kamu da sona? Ba kasan wacece ni ba,ba kasan Asalina ba...shin xaka iyah zama dani idan har kaji labari na kuwa,kajiyo asalina...!!! kara rushewa da wani irib kuka nayi,wanda rabon da nayi shi har na manta a duniya.

Oummu Sulym wai wannan wani irin zama ne kikeyi sam kinki motsawa bayan kin san yanxun zaki tafi Aikatau din nan naki".
Hmm nisawa Oummu Sulaym tayi,kan tayi duba ga Mama da tayi nisa wajen saka D'an waken sayarwa mutane kuwa har sun fara rufa mata. Hmm tom Mama bari na mike wlh banjin dad'in jikina ne".
Oummu Sulym ce mai wannan maganan tana mai mikewa daga kan kujeran tuka tuwo ( Stool ).
Kallon ta Mama tayi kana daga bisani tace Oummu wani abun ne ke damunki? Ko dai wani abu ya samu Suhaimart ne!!?.

A'a Mama bari na shirrrr....
Keee...." keeee Oummu uban wa kike jira ya wanke maki wa'ancan kayan eyeee..Ko kina nufin ni ce da y'ay'a na zamu yi wanke² n gidannan?. ke kuma kina can kina aikin Gantali da watsewa,kina fake ma mutane da Aikatau,waye bai san halinki ba,ko aka ce maki komun fakewa da aikatau din da kikeyi ba'asan tsinewan da kikeyi bane? tom ki sani Wlh ko Ubanki ya shigo gidannan baxan barki ki fice ba sai kinyi wanke².

Kallon Mama Oummu Sulaym tayi yayin da cike da rashin nunawa ko ajikin ta duk da maganganun Inna Atine yy mata Zafi matuka. Amma sanin halin mutum sai ta daure ta saki mata murmushi kana daga bisani tace" Inna Atine don Allah kiyi hakuri Wlh na makaran isah wajen aikin nan,kuma naga gasu Innah Wuri nan ki saka ta ta wanke".
Fadin haka da Sulaym tayi yasaka Inna Atine cike da munafunci ta hau kururuwa kaman wanda Oummu tasa hannu ta bugeta,na shiga Uku na malam".

malam..." yau ni zan saka Sulaymu Aiki taki mun,tana kwada zancen ga y'ay'ana nan nasa su ita ban haife ta ba?...ta fadi tana bankada labulayen dakin Baba Amadu.

Cikin sauri cike da Rawar jiki ya fito wanda daka ganshi kasan asallame yake tabbas an gama da shi.bai da tacewa a cikin gidan nashi,gashi daka ganshi kaga malamin Zaure...

Uwa ta". maxa wanke mata kwanukan sannan ki tafi kinji?".

Baba ne ma fada ma Oummu Sulaym wannan maganan cike da rawar jiki da tsron Inna Atine.

"Tom Baba". Oummu ce ta fadi hadi da nufan can karshen gidan don ta fara wanke² kaman yanda Baba Ahmadu ya bata Umarni".

Itako Mama Baiwar Allah,kallon inda suke sam batayi balle tayi nuni da Ranta ya sosu a saka makon cin mutuncin da Inna Atine tayi mata da diyar ta ta".
Baba kam kasa komawa daki yy sai saka takalmi da yy ya fice wajen gidan nasa,don sam idan Inna Atine ta tada fitina baya iyah zaman gidan,Itako Diyar Inna Atine wato Inna Wuri tuni ta fito tana aikin Girgixa kaman mai shurin yin dambe.

Itako dai Sulaym ra6ata tayi ta wuce ta gyefen ta kallon ta batayi ba.

Sosai Oummu Sulaym tafara wanke²n don aiwatar da abun da Baba ya sata. Amma Inna Atine kuwa sam duk da hakan bata daina hargogowa tana zage² ba".


Wata ce da'ake kira da Ramatu makobciyar su da ta shigo sayan d'an wake wanda komai akan idon ta akeyi tace" Haba Atine wannnan fitina da mai yy kama,ki zagi y'a,kin kuma zagi Uwar ta". naga kina da iko da Sulaymu amma baki da iko da Mama Laure,tunda a girme ta girme maki,keba sa'anta bane.gsky gidan nan naku da gyara wlh ku gyara,ki banxa yaya matane da ku,maiye amfanin kullum sai anji Harshenki a makota.... Haba zafa kuso mazan kwarai suxo gurun yayan ku bana banza ba".

Inna Atine shiru tayi don sarai tasan wacece Ramatu da fitinan ta,sam bata da Ragayyah shiyasa ta kasa tsagalgale mata kaman yanda take mawa wasu.

Buden Bakin Inna Atine cewa tayi,a'a ai ni y'ata mazan kwarai ke zuwa wurin ta,kuma a haka har na Aurar da Zainabu,yanxu ma Inna Wuri bazata shekare mun ba da yardan Allah,wanda suka zo zama dai su zauna,babu ko mashin shine saboda bakin jini,wlh anyi asara". Mutum shekara Ashirin kenan bana,amma bb karen dake sallama,tir da wannan bakin jini,mu dai mun gode mawa...!!! Gsky kin bani kunyah Atine, sam ban tunanin jin haka daga gareki ba,amma kisani shi Aure lokaci ne,idan lokacin tayi yi wlh babu mai hanata,ai shi ba'a gori da Aure".

Niko ina wanke² ne amma bansan lokacin da Hawaye yafara mun sintiri a fuska na ba....Tuno da maganar Mama da take fadamun komai lokaci ne kuma bayan Wuya sai Dad'i. A raina kam a yo cewa nayi yaushe ne komai zai karemun A rayuwa? tun banfi shekara 11 ba nake fuskan ta kalubalen Rayuwa? haka dai Sulaym tayi ta zancen zuci,a ranta tana tabbas ita ta d'an dadani Mad'aci,amma har Ilah yau bata samu zumar ba".

Ramatu kam ci gaba da cewa tayi kuma da kike wani mgn,waye bai san Abun da Zainabun tayi ba,da'aka samu da kyar aka kaka mata a Kauyen Fallanki ko?.
Tana fadin haka tajah tsaki hadi da ficewa daga gidan tana mai mitan idan kowa zai gori ai ke bai kamata aji bakin ki ba Atine ".

Mama dai babu uhumm bare uhum'ummm....A haka Sulaym ta kammala aikin ta tanayi tana kallon Mama ta gyefen ido ko zataga wani sauyi a tare da ita amma sam bata ga komai ba. illah sana'ar ta da takeyi abun ta".
Hakan ko bakaramub kular da Inna Atine tayi ba,don tun maganan da Ramatu ta fadi tajah da baya jiki babu kwari ta koma dakin ta...


Itako Oummu Sulaym nufan dakin Mama tayi don ta shirya ta tafi wajen Aikatau din ta". Don a yanxu lokaci sosai ya kure wuraren 11: 30am.

Da shigan ta D'akin Mama laure ta hau bin garun dakin dako plasta babu dabe ne kawai...
Bin ko ina ta hauyi da kallo,kwallah na kara ciko idon ta,duk da wannan halin da muke ciki,ace kwanciyar hankali ma babu. Habawa Inna Atine wlh dani kikeyi,dadin abun kin sanni sarai. Arzikin ki Mama da Baba duka suna nan ne,amma in basa gidan ai bakya mun don kinsan Wlh dai² nake dake".

A haka ta dinga shurin ta ta hanyar saka uniform din Aikatau din tana mai gaggawan fitowa...

Suna a zaune tsawon A wanni Khaleed kam ya tasa abun da ya saba sha wato giyan sa yana daddaka ma cikin sa,sunan Suhaimart ne kadai yake nana tawa. Yayin da Yarima Abdoul Manan kuwa gaba daya hankalin sa ya idah tashi,don bai san wannan wani irin mahaukacin so ne Khaleed kemawa Suhaimart ba". ita ba wani Abu daxaice tana dashi ba,a yanxu fah auren Kwarya tabi kwarya akeyi,babu mai jawo ma kansa talauci,don cewa ma suke talaka gayyar tsiya!!!. Amma shi duk akan wannan Yarinya karama ya gama daga hankalin shi,a tarihin rayuwan shi bai taba ganin Khaleed yayi soyayya da yarinya ba. don shi sam bai kallon macen da bata haura 25 ba,acewan shi sun gi hankali bai son sakarcin yarinya ta,Amma a yau gashi Yarinyan da batafi 17/18 ba tana neman burkita sa gaba ki daya".

Duk wannan Sumbatun da yakeyi akan idon Oummu Sulaym da shigowan ta kenan barayin tana neman Aminiyan ta,don damuwan ta kanta ya ishe ta".

Amma kuma ganin Halin Da Sir Khaleed ke ciki bakaramun firgita ta yayi ba,Abdoul Manan kam Rarrashin sa yake akan zai nemo masa soyayyar wannan Yarinya,amma har a wannan lokaci yaki kwantar da hankalin sa".

Ganin haka cike dajin haushi don tuni Oummu Sulaym ta gama fahimtan komai,nufan barayin su tayi saurin yi,wanda da isan ta dan madaidaicin dakinsu ta cidda Suhaimart kwance tana sharar baccin ta".

Nufo ta tayi cike da jin zafi ta daga hannu hadi da nana mata duka a baya!.

Gigif na mike ina mai kara bude idona don ganin wanda ya dada mun duka haka,ita dince dai nagani Wato Aminiya ta Sulaym.

Saurin mikewa nayi ina mai zaro dakwa² n idona da furta Sulaym mai nayi maki haka?.

Cike da masifan ta tafara cemun,ehhh dole ki tambayen mai kkyi mun!!?,bayan kin bar bawan Allah gayican kin zauta shi bai san duniyar ma da yake ciki ba".

Dajin haka nayi saurin mikewa daga zaune ina mai kara zaro ido,don na tsorata da Maganan Oummu Sulaym. Kwallah ne nan danan ya ciko mun ido.

Itako Oummu Sulaym cigaba tayi da cemun" Wlh Suhaimart kiji tsoron Allah,kar Allah yabaki dama ki masa Butulci,Suhaimart ki kaunaci mai Kaunanci,ki kuma so mai son ki tun kan dama ta wuce maki".
Suhaimart ni kaina na isheki ishara ,gani nan babu saurayi tsayayye sai yan iskahhh....tana fadi n haka sai kawai ta Rushemun da kuka mai taba rai da kuma ban tausayi,wanda ni kaina bansan lokaci n dana fara yin nawa kukan ba".

Ina kuka ne gami da cewa" Oummu Sulaym na tuba ki daina kuka wlh bansan naga damuwar ki,ki fadamun mai kkso ni kuma zan maki".

Ai dajin haka Oummu Sulaym tayi saurin saka hannu tana goge kwallahn kan fuskan ta tana mai nufo ni hadi da cewa" Yowah Aminiya ta,kawai ki Amince da soyayyar Sir Khaleed, komai yace maki kar ki masa jayayya,kisa a ranki Sir Khaleed mijin ki ne mah".

Dariya ne ya kuncemun Wai Sir Khaleed miju na,ko tayaya hakan zaiyi wuuu ohoooo.
Tom Sulaym nayi maki Alkawarin baxan kuma masa musu ba..."

Yauwa yar gari yanxu maza ta shi kinga yau bai fita ba kuma kene da masa hidiman komai. tom nace mata sannan na mike hadi da kama hannun ta ina furta tom ae kinsan aikin side din shi banawa ne kadai,har dake ko!!.

Dariya duka muka saka kan daga bisani mu tashi duka muka nufa barayin nasa".

Muna cikin tafiya ne sai naji cike da tsorata da mamaki Oummu Sulaym ta Furta Iftihal..."

Zuciya nane ta buga lokaci guda kawai jin sunan Iftyhal da Oummu Sulaym ta furta". Juyawa nayi inda naga ma'aikatan gidan kowa hankalin sa na kai".

Wato matashiya ce wanda ashekaru baxata haura 22 ba a duniya". Sanye take cikin shigarta na Golden Abaya da akayi masa adon stone daddabe....Rolling tayi da yar mayafin ta yyn da Hannun ta kedauke da wata yar ficiciyar jaka".
Kafan ta kuwa sanye cikin Half cover mai tsinin gaske....
Fuskan ta kam a daure yake tamau,wanda basai anfada maka ba daka ganta zaka fahimci ita din bata da mutunci sam.

Bin fuskan ta nayi da kallo wanda yake sanye cikin Makeup kaman wanda zata tafi taron fitar da kyawawan Duniya. A takaice dai Iftyhal irin matan nan ne masu fama da hayakin kai,marasa mutunci wanda kowa ya gifta tsakanin su sai sun keta masa rashin mutunci.

Saurin jan Hannu na Oummu Sulaym tayi mukayi baya,yayin da aha cike da takon takama take takawa ma'aikata kuwa cike da Rawar jiki ake gaysar da itah,haka nan mu ma da tazo ra6awa ta gyefen mu,don duk hada baki mukayi muka gaisar da ita,amma sam bamu samu arzikin Ko kallon kirki ba,balle

Please Login or Register in order to submit comment