Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bin fuskan ta da Kwalliyan da ta saba,gyefe kuwa masu hidimta mata ne kowa tsaye cirko² don sunfi awa daya a haka. Itane goga wannan itace goga wancan. Muryan Ammie n ta taji daga bayan ta tana furta mata Nana Aysha wannan kwalliya haka sam bakya gajiya kaman kin san da dawowan Yarima Abdul Manan?. Saurin juyowa Nana Aysha tayi tana furta Ammie da gaske yau Hamma Abdul zai dawo?". Murmushi Ammie tayi tana mai juya baya hadi da furta mata dayake nasaba fada maki karya? yanxu haka ma yana fadan Mai martaba. Wani ihu Aysha tasaka. wanda nan Ammie ta fita tana murmushi hadi da mmkin irin kaunar da Aysha ke mawa Dan yar uwan ta. Itako Aysha da fitan Ammie ta daga Wayan ta tana mai kirar Khaleed wanda kira daya biyu Khaleed dake Zaune kusa da Aminin nashi Huday ya daga Wayan yana furta Ahhh,wannan murna Haka ae ko baki fada ba nasan Abdul Manan ya sauka". Dariya tayi cike da kuma jin kunya ta datse wayan tana furta masa Hmm bakomai shine babu sanarwa ko ?. Kan ya bata amsan ne ta datse wayan tana mai kara ca6a ma Fuskan ta Ado,hadi da Addu'an Allah yasa Ammie ta bar ta a yau taje masarautar Sarki Mai lafiya don taga magamin Rayuwan nata ko tasamu yau tayi Baccin dadi.
*___________________________*

Kaman daga sama naji muryan Oumma na tana furta kiran Sunana Suhaimart" tashi kije dakin ki ki kwanta kinji. ta fadi tana dan girgixa ni. a Hankali na bude darararan idanu na hadi da Sauke su akan nata. Cike da muryan mai Barci na furta Oumma Har kin tashi". Murmushi Oumma tayi sannnan taban Amsa da Ehhh Suhaimart na tashi, tashi kije ki kwanta Allah yayi maki Albarka kinji. Ameen na bata amsa sannnan nafara shurin mikewa daga Kwancen da nake. Cike da muryan Wanda sukayi shaye² sukayi tatul naji Muryan Zaid yana cemun Kehhh Suhaimart ina kudin dan Uban ki. Shiru nayi don bani da amsan bashi. aiko ganin Haka yasa shi nufo ni da niyan dukana. Oumma na ne tayi saurin tashi daga zaune ta dauko Mucciyan gyefen ta ta nufo shi dashi,ganin haka yasa shi fucewa daga dakin yyn da Oumma na ke bin shi da zagi dacewa ya kiyayeni. shiko Zaid duk Rashun jin shi baya son yaga bacin ran Oumma shiyasa ya fice daga gidan. Niko Zama nayi ina mai Rafka uban tagumi har Oumma na ta shigo dakin nata. Suhaimart maza ki kwanta ni yanxu xan je gidan Tani na ranto mana Bashin abun da xamu ci,kan karshen wata a buyaki Albashin Aikatau dinki sai mu biya". Tom" Oumma na ki dawo lafiya". Allah yasa sai na dawo. Ammie tace hadi da ficewa. Ina a zaune fitan Ammie ba wuya sai ga Ya Zaid ya shigo gidan. Keni ne xakisa Oumma tazaga aiko yau sai naci ubanki a gidannnan..... Wani wawan Mari ya kaimun,wanda sai da yasani na kifah sai jini da yafara xubomun ta hanci da baki. Duka na yake yana karawa,nan na hau ihu ina mai Rokon shi kan ya Hakuri nan da gobe xan samo masa,amma ko saurarona baya yi,sai uban duma na da yakeyi kaman sa'ar sa. A haka ya Haujah mun Hannu har wajen soron gidan mu.
*******************************
Yanxu Huday ya zanyi ni bansan ma ta yaya zan sanar mata da soyayya ta a gareta ba.Dariya Huday yy yana mai kallon yanda gabaki daya Khaleed soyayya ta gama sauya sa lokaci guda". Hmm tom yanxun bari mu gani? Huday ne yace yana mai tunano mawa aminin nashi mafuta. Year yanxun dai Ka kirawo Mhiss Caterine kace kana son bama wannan Maaikaciyar Aiki ne". Kallon Sa Khaleed yy kan daga bisani yace ohk. Wata ma'aikaciya ce taxo wucewa mai irin kayan Suhaimart, gaishe su tayi wanda nan Khaleed yace Tayo masa kirar Shugaban tasu. cike da girmamawa ta juya dai² Oummu Sulaym na shigo wa don ta karke aikin Suhaimart da ta tafi ta bari. Barka da Gida Yallabai". Kallon ta sukayi kawai sai suka kware da Dariya. wanda ya sanya ta tsayawa tayi shiru tana kallon sa dama suna dariya haka? tom meye Abun dariya a tare da itah. Huday ne cike da muskilanci yace mata Halan mu mata ne daxaki ce mana Barkan mu da gida"? Tom ai yanxu xamu fice Madam. Ita dai kasa basu amsa tayi sai tace masa toh kayi Hakuri kuskuren Harshe ne. Ohk Khaleed ne ya bata amsa a dakile. mai kikaxoyi nan?. Ehhh yallabai dama dama² uhmmm naxo na karke aikin Suhaimart ne". Kallon ta Huday yy sannan yace ita ina Take mai aikin? Umm bata jin dadi ne shine yasa ta koma gida". Ai dajin Suhaimart babu lafiya tuni Khaleed ya mike daga kwancen da yake,cikin Sauri ya furta mai yasame ta"? Ba wani ciwo ne ba sosai. uhmmm ina ne gidan su sai muje muga lafiyan ta,ko aikin da tayi mun ne yasa ta ciwon. Bude Baki Oummu Sulaym tayi sai kuma tace tom Ranka ya dade a cikin Zaria take". Mikewa Huday yy yana furta a gsky ya kamata mu duba ta Khaleed. yanxu je ki dakko komai naki muna jiran ki a Moto ki same mu,don ke Zaki kai mu". Tom angama ranka yadade ta fadi tana Rawar jiki ta juya. Dariya Huday yy yana cema Khaleed see dis girl like a jorker. kara kwashewa da dariya sukayi suna mai kwasan keys din su don su nufi Parcking space............



Labarin ZUMA DA MAD'ACI ta kudi ce zaki turo #200 VIP, idan SPC #300,NORMAL #100 duka ta wannnan number 08081202932/09137392680.



*Maman teddy🧸*
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/100188104918551/

*Typing...✍🏻*

🎋🎋🎋🎋🎋🎋🎋
🌹🌹🌹🌹
🌿🌿
*ZUMA DA MAD'ACI*
_*(True love never end...)*_


Na
*Maman teddy🧸*

*Episode 9 - 10*


*_____________________________*


*ALHERI WRITERS ASSO.📘🖊️*

*A.W.A*


```Kungiya daya tamkar da dubu,kungiya masu aiki da nazari da ilimi,Alheri sai d'an Alheri💪🏻```

*______________________________*


*بسم الله الر حمن الر خيم*

Haka suka tattara kayan su suna mai nufan Farfajiyan gidan suna mai jiran isowan Oummu Sulym. Itako Oummu Sulym tunda ta nufi Sasan su ta Ma'aikatan gidan sam ranta yaki natsuwa,tabbas tanaji a jikin ta kaman da wani dai abun ne kasa". Haka ta tattara kayan ta a jakanta sannan ta nufo filin Harabar gidan da ya kayatu da Abubuwan more Rayuwa komai na filin abun burgewa ne da ban sha'awa... Nufo su tayi a tafiyan ta na halin ko in kula,don baxaka ce Oumu sulaym wai budurwa ce ba. Ba Ruwan ta ita tafiyan ta kawai take babu Ruwan ta da komai. Binta da Kallo duka sukayi sannan da isowan ta Huday yy murmushi gami da fitowa yana kokarin bude mata Murfin moton. Murmushi tayi masa tana mai furta masa Ranka ya dade Ae na iya budewa,koba haka bane tafadi tana kokarin bude murfin moton wai ala dole xata nuna masa. Dariya yayi yajah ya tsaya yana kallon ta har ta bude sannan ta Waigo tana furta Ranka ya dade kagani?. Nan yayi mata tumb da babban yatsa alaman da kyau. sannan ta shige tana dariya. Yana mai Rufo mata murfin moton.
Shiko Sir Khaleed gaba daya sun fara bashi haushi,shi dai har ga Allah ya kosa yaga hurril aynin shi. A haka cike da zalama yajah moton yana furta Ibeg muje Huday i'm eager. Dariya yy yana furta Okay Rumio,ka kosa kaga Juliet ko,don't worry ai mun kusa isa kaganta.

Haka dai yayi Dariya da jin maganan Da Huday ya fad'a masa,nan ya furta masa waye wani Rumio da Juliet,aeni a Son ta nafi Layla majnun....😂
Dariya duka suka saka.yyn da Oummu Sulaym ta baxa kunni don ta nadi gulma ta sanar ma Aminiyar nata Suhaimart. Amma sai dai kash ita sam tagaxa gane inda zancen su ya dosa ba. Ita dai kawai abun da take ta nanatawa shine Layla majnun gasky dole ne ta tambayi Suhaimart wannan maganan wai Layla Majnoon don ta fahimci inda suka nufa.

A haka dai ta cigaba da nuna masu Hanya tana kwatanta masu inda zasu shiga ahaka har suka isah cikin Zaria city.

"Duka na yakeyi kaman Zai Karni don kiyayya,yyn da tun ina gani har na soma ganin duhuwa,saukar marin da Oumma na ta wanka ma Zaid yasa ni xubewa yyn da sama² na kejin hayaniyar Muryan Oumma na tana Zube masa Bala'i da hargoguwa tana mai Zubar da Hawaye da kirar Suna na".
Suhaimah" Suhaima na bude idon ki ki kalleni".
Girgixa ni take amma ko numfashi bana iya fitarwa don bana numfashi. Hawaye ne yafara bin kuncin Oumma na,dagowa tayi tana kallon Zaid da ya tsaya ya rasa duk wani abun yi,don shi sam baya a hayyacin sa yy mun wannan duka,tun da a bige yake. Ficewan shi yayi yana maganganu kasa² yyn da Oumma na tayi saurin fita daga soron namu tana taro me Napep daga bakin Hanya. nan ta ciccibe ni sannan me Napep yajah muka nufi Asibitin A.B.U hospital.
Wanda da isan mu nan cikin Gaggawa Nurses suka amshe mu hadi da nufan Emergency room dani.

Itako Ommu Sulym a haka suka dinga kurdawa har xuwa Unguwan namu wanda da shiganka basai anfada maka ba kasan unguwan talakawan tilis ne,amma ko a unguwan gidan mu yafi na kowa talauci don Abun ma yy muni matuka. Shikuwa Da Sir Khaleed tun isan su Unguwan yake tunanin dama da akwai Unguwa masu fama da Talauci irin haka?" A gsky shi sam bai san da hakan ba,indai ma kam hakan talaucin take tom bai taba ganin talauci ba a rayuwan shi.
"Dako A kozo dai² gidan mu ne Oummu Sulym tayi saurin cewa Sir Khaleed mun zo fah".
Tsayawa yy hadi da yin parking din moton nashi,sannan yace mata Bismillah". A hankali ta bude side din ta gami da fitowa daga moton tana mai nufo gidan namu".
" Suko Khaleed da Huday shiru sukayi babu mai iya furta kanzil", Musamman Khaleed da a zuciyan shi yake furta Sorry Hayatee na". Nan da yan lokaci kadan baxan barki ki zauna a cikin wannan Talauci ba". Zaman Nageria ma baxa muyi ta ba inshaallh". Abun da Khaleed bai sani ba shine ba a zuciyan shi yake mgnan ba a sarari ne". Huday ne yy murmushi cike da Tausayin Aminin nashi,duba da yanda ya fada soyayya ga Wannan yarinya,soyayya makauniyya wanda sarai yasan Khaleed bai taba fadawa duniyar irin wannan Son da yakeyi ba. gashi yasan irin soyayya r Khaleed don inyafara baijiin bari sam. Shiru yy yana Aiyana Allah yasa Yarinyan nan ta Kaunace shi kar ta Wahalar da Abokin nashi,don a halin yanxu Khaleed ya rasa wannan yarinya bb shakka komai na iya faruwa dashi".

Tabo shi Huday yayi yana mai furta masa A'a Khaleed ka natsu don Allah. Inshaallh Suhamart Matar kace zata kasance ma yanda kake buri,kuma inshaallh zaka sanyata cikin Farin ciki kaman yanda kake mafarkin gani".
Murmushi Khaleed yayi cike da jin kaunar Aminin nashi yace Na gode Huday da Addu'ar ka gare ni". Kafin Huday yace masa Wani abu ne sukaji Muryan Oummu Sulym tana cewa Sir Khaleed wlh mun zo arashin sa'a don gidan ma a rufe take basa nan dukan su". Saurin kallon ta yy don lokaci guda idon shi ya sauya Kala daga Fari zuwa jahhh..." Nan take Zuciyan shi tafara kisima masa kodai Ciwon nata ne yy worst?. Muryan Huday yaji yana bata amsa da Ohk Badamuwa, Amma bakya tunanin Ciwon nata ne yy tsanani???. A'a ranka yadade inshaallh komai zai zo da sauki".

Ohk Allah yasa,shiga mikai ki gida".
da jin haka Oummu Sulym tayi dariya hadi da cewa" A'aa Ku tafi ai nan unguwan mu ce,yanxu zai kai gida inshaallh ". Okay tom shikenan mun gode". Bakomai ranka yadade". Haka dai suka tafi suka bar Sulaym tsaye don ita kanta tana mmmkin inda Suhamart ta tafi da wannan Yammaci haka". haka dai ta tsaya tagama kusifa abubuwa kan daga bisani ta fara tattaki zuwa layin su".

Niko tunda nasamu kulawar kwararrun likitoci tuni na dawo hayyaci na,yyn da Suka yimun Alurar Bacci Hadi da saka mun drip. Oummu na kam taso daga hankalin ta,babu abun da take tunani sai Kalmar Ga Amana ta nan". Safa take da marwa har Wata nurse da doctor suka fito. Cikin Hanxari tasha gaban shi tana mai furta Doctor ya jikin yarinyan nawa?. Kallon ta Doctor n yy cike da tausayi don ko ba'a fada masa ba yasan suna cikin talaucin Rayuwa. Ki kwantar da hankalin Mama inshaallh ba abun da zai sameta,kinga yanxu ma tayi Bacci". Hamdalah Umma na ta hauyi hadi da yima Doctor n Godiya,sannan ta juya hadi da nufo Dakin da aka kwantar dani tana mai tsaye bakin window don ance ba'a bukatan kowa a ciki. Haka Oumma na ta dinga kallona ta jikin tagan,yyn da Wasu Zafafan Hawaye ki bin fuskan ta,bakin ta kam harda ma Zuciyan ta Addu'a kawai take mun.

A haka fiye da Awanni sannan ta nufi farfajiyar Asibitin don tayo Alwala taga batar da sallah don a lokacin har an soma kirar Ishaa'i.

Niko sam ban farkaba sai Wuraren 8:30pm. Mikewa nayi cike da cije labbana don wani irin tsami danaji jikina yy gaba ki daya. Addu'a nakeyi wanda dai² idona na sauka kan file dina da aka ajiyemun gyefen Gadona saman drower".

A hankali na kai Hannu na hadi da dauko File din na bude ina mai duba rubutun dake kan farar takardan. Wanda duk da ban da wani ilimin zamani,makaranta ma na gomnati nayi,wanda a SS 2 Ummma na ta dakatar dani saboda rashi da ya ishemu akan na soma zuwa aikatau.

Duk da Hakan ina da dan ilimi na na boko dai². Karanta takardan na somayi nan take gaba na yayanke yafadi don kirgina sai da Naji bugawan ta. Cigaba da karanta takardan nayi yyn da hawaye kebin kuncina. Wanda sam banji shigiwan Doctor Zainab ba sai muryan ta da naji tana kirar Sunana" Suhamart " Suhamart ar you okay?". kina ganina da kyau ko??.

Goge kwallah nayi ina mai kakalo murmushin da yake a jini na ne nace mata ehh Doctor ".

Yauwa mashaallh. Nan ta zauna kusa dani tana mai fuskantoni hadi da saka hannun ta ta amshi file din" Shiru kusan minti 5 babu wanda yace komai,kowa da abun da yake kisimawa a zuciyan shi.
Suhamart... " kaman daga sama Naji muryan Doctor tana kirar sunana" Kallon ta nayi akaro na biyu na kuma ce mata Na'ammm...!!!"

Suhamart kiyi hakuri komai da kk gani akan file din ki kisashi a mixanin Kaddaran ki". Komai Allah keyi,kisani ana doraki akan magani zaki warke,kuma koda an vata maki rai kidaina Damuwa plz, idan kina sawa a ranki to tabas xaki ringa xubar da jini ta hanya daban², kaman Ha6o da sauran su: Don haka kisani Suhamart zaki warke inshaallh ".
wani irin mun murmushi nayi mata mai dauke da fassarori da dama, kana nace da ita Doctor kina ganin zan warke? wannan Ciwon fah ba karami bane,kuma sannan koda zan warke Doctor ina zan samu wa'annan zunzurutun Kudi???.
Nan Hawaye ya cigaba da mun Ambaliyya akan fuska ta. Wani irin tausayi na ne yagama kama likitan a hankali ta kai Hannun ta tana mai dafo kafada ta da cewa" Kiyi Hakuri Suhamart kije ki cigaba da huddan ki da mutane,bb abun da Zai kuma samun ki,kuma ciwon baxai taso maki ba sai bayan nan da kaman watanni Uku. Kuma nasan kafin nan kinsamu kudin Maganin. Ga wa'annan magungunan su zaki ringa amfani dasu kan wannan lokaci ". Ta idda maganan tana nuna mun wasu magunguna,nusawa nayi ina mai amsan maganin sannan na kalleta ina mai cemata" Doctor don Allah ina so ne kimun wani alkawari daya ina zaki iyah". Cike da bata kwarin kwiwa irin na likita da majinyaci tace mun fadi maganan ki Suhamart.
Nisawa nayi kana daga bisani na ce da ita" Doctor don Allah so nake ki rufe wannan sirrin wani ciwo na,kar ki sanar ma kowa dagani sai mahalliccin ki,saboda sam bana son Hankalin Oumma na ya tashi,wlh itama ba lfy ne da ita ba". Na fadi cike da matsanancin damuwa". Girgixa kai Doctor tayi kan daga bisani tace nayi maki Suhamart, amma don Allah duk bayan wata 1 kiringa xuwa ina dubaki naga lfyn ki kinji"?

Daga mata kai nayi ina dan murmushi na jin dadi. Haka ina A zaune tayo kirar nurse don ta dan gyarani hadi da mun bed making. Doctor Zainab ne ta ciremun Drip din Hannuna don ya kare,nan wannan nurse ta fara aikin ta.
Niko jirgawa kadan nayi duk inda na muskuta ta gyra har ta gama aikin ta. Dai² Oumma na na shigowa gaisawa suka yi da Doctor sannan Dr. Zainab ta fice daga dakin tana mai kara sanar mawa Oumma na da Na sauki sosai kilan mu amsa sallama a daren nan .

Cike da jiin dadi Oumma na ta matso gareni tana furta Sannu Suhamart!!! ya karfin jikin naki???.
Murmushi nayi mata sannan na furta Oumma na naji sauki sosai, don A yanxu Oumma nafi dama jin karfin jikina. duba ki gani !!!... na fadi ina washe mata fararen hakora na". Dariya Oum Rabi tasa cike dajin dadin ganina ta hau cewa" Kai mashaallh" Alhmdllh.

Nufo ni tayi tana zama gab dani,sannan ta bude kwankwatstsayan kwanon da ta tahomun da Tuwo miyar yauki a cikin ta". Kallona tayi hadi da furta Suhamart maza kici abincin nan Ko kyakara jin karfi jikin ki. Murmushi nayi ina daukan ruwa na wanke hannu na a wani Bowl sannan nasaka hannu na da zamman fara cin Tuwon".
Wani magana ne yafara dawo mun a shekarun baya da suka wuce!!!.
Ga Dumamen ki nan ki ci". Tom Oumma Zaid ina spoon?. Hhhhhhh Zaid ne ya kwashemin da dariya,yyn da Oumma ta galla mun Harara da cewa kehhh bana son shashanci,idan kinsaba komai naki na dabi'un nasara,tom nan mu koyi muke da addinin musulunci maza kisaka Hannu kici da yatsun ki kar ki fusata ni".
Ya Hakuri Oumma na bata amsa yyn da nake tsoma hannu na cikin kwanon abin cin.

Murmushi nayi gami da kallon Oumma na da tayimun kurr da ido,a sanyaye na fara kai loman tuwon baki na.

Sai da na kammala sannan na ajiye kwanon tuwon ina Mai Hamdalah ga Allah,sannan na kalli Oumma na ina mai Furta Oumma na I luv u".
Murmushi tayi mun tana mai kallona da cewa" ohh ni Rabiatu!!" Suhamart ni sam nafada making bana jin wannan yaran naki fah".

Okay tom Oumma ya kamata mu amshi sallama don banason kwanan Asibitin nan,suce a biyasu Kudi n gado kuma.

Kallona Oumma na tayi tana zaro ido waje Suhamart haka ne ko???.

Dariya nasaka hadi da ce mata ehmana Oumma ". Ae ko Suhamart bari ki ga tunda dai kin warware mu tafi a ayau din kawai. tana fadin hakan ne hadi da ficewa daga dakin don nufan Doctor.

Niko Bin bayan ta nayi ina mai tunanin furucin Oumma na" Suhamart ni bana jin wannan yaran nake fah". Murmushi nakuma ina mai kuma tuno Abubuwa da yawa" I luv u murmy".
luv u so much too my Daughter". Suhamart ki zo mu tafi kar muyi latti fah"... Tom my boooooo ina zuwa minti 2 kacal. natafi haba Hamma na iyayen Zuciya ina katafi waxai kaini School din?. Basai ki je da kanki ba,ae ke komai naki yi kk kaman wata Babba,amma jibiki Har yanxu baki fi 5 yrs ba... Hohiooooooooo Mummy... Dadddy..." Hamma Huuuuuuuu...


Suhamart ya jikin naki??. saurin juyowa nayi ina furta naji sauki sosai. tom mashaallh yanxu ga takardan sallama nan,bayan Wata daya kai dawo". tom ngd likita. nan Oumma na ta hau gdy hadi da fara tattara komutsan mu.

Me napep ta taro yayin da ya shigo har farfajiyan Asibitin sannan mu ka nufi gida.

A wannan dare sam Oumma na taki yarda ko nan da can na jirga,karoko ma A dakin ta na kwana.

Da Asuba kuwa kan na farka tuni ta fice ta dora ruwan koko sannan bayan ta kammala ta doramun na wanka.

"Khaleed... Khaleed" .... sai da ta yi maganan ya kai sau uku sannan ya dago kan sa yana kallon ta,fuskan sa kam dauke da damuwa fal. Kirjin ta ne ya buga,cikin saurin ta kai Hannun tana safa gyefen fuskan sa da yake kwance kan Resting chair. a sanyeye cike da taushin murya da tsatsan soyayya ta Uwa da dan ta Mum Zaituna ta shafa shi tana furta My baby meke damun ka,baka da lfy ne??.

Saurin girgixa mata kai Yy hadi da juyi akan jikin ta sannan cike da muryan shagwaban d yasaba mata ya fara cewa" Oumma Hayatee na bata da lfy ne". Cikin Saurin tace Ayyah Ita Iftihal din ce babu lfy ai ban sani ba,kuma daxu muka gama mgn da ita tace xata taho Nageria nan da Kwana biyu 2. Wani daddaciyar yawu ya hadiye da kyarrrr....murya can kasan makoshi yace Mummy ba ita ba.

Shiru Hajiya Zaituna tayi kan daga bisani ta tsaya tana observing din yaron nata,lokaci daya ta fahimta tabbas dan nata he fall deply in love...tom amma da waye??? tambayan da ta dinga mawa kanta kenan!!!. Hmm nan ta nisa tana mai ce masa Ohk tom wace ce ita ? fada mun my son" aina take YAR WAYE a Fadin Nageria?. littafin maman teddy wanda bata karanta ba anvar ta back...💃🏻

Shiru yy kan daga bisani yace Mummy ita Hayatee na ba yar kowa bace,amma ki natsu a hankali nan da Kwana 2 xan kawota ki ganta.

Hmm dan murmushi tayi don a tunanin ta shadi fada yake mata". Shafa sumar kansa ta dinga yi hadi da sakat masa AC wanda a haka da kyar Bacci yy awon gaba dashi.

Niko bayan na kammala wanka nayi sallah ne na sha kokon da Umma na ta ajiyemun hadi da korawa da magani na. saka kayan Aikatau dina nayi,sannan na fito a daki na ina furta Oumma sai na dawo".

Suhamart ina zaki tafi kina fama da kanki??.

Oumma naji sauki don Allah kar ki damu.
Shiru Oumma tayi kan daga bisani tace Suhamart don Allah ki kula,idon baxaki iya aikin ba kai dawo gida kinji? tom Oumma na tafi". A dawo lfy.

Haka na nufi gidan Hajiya Zaituna bayan napep ya saukeni na sallame sa sannnn nayi saurin shigewa gidan,don ko sasan Hajiya Zaituna baje ba,saboda makaran da nayi.nufan sasan Ogan nawa nayi direct don nayi saurin Kaddamar da aiki na,a raina ina tunanin hukuncin da zan fuskanta daga gurun sir Khaleed. don nasan yanxu ni yake jira na hada masa breakfast.
Shi yasa nayi saurin nufan barayin sa.

Shiko gaba daya Sir Khaleed yagama cika yy fam,Haushin kowa yakeji,buri n shi kawai yaji halin da Suhamart din sa ke ciki!!.
Ga kuma yan aikin da suka zo su biyu a makofin ta wai su hidimta masa,gaba dayan su sungama wulakanta don ko sun gaishe sa baya amsawa,sai daure fuska da yakeyi,ga wani hararan raini da wulakanci da yake binsu dashi. Gaban sa Laptop ce yake Operating yyn da yake sanye cikin Farar t.shirt sai boxer iya gwiwa,ko shirib nufan Companyn sa baiyi ba. don shi yau sam bai son ganin kowa sai Hayatee n sa.

Da sallama dauke a Abaki na na shigo falon,wanda kallon inda nake baiyi ba sai ma tattara laptop din sa da yy ya nufi resting room din sa. Jiki na ne yy sanyi kalau. a raina ina cewa shikenan yau naga ta kaina,Allah yasa basun sallame ni bane. musamman yanda naga su Atika na aiki na. Daga masu Hannu nayi nan cike da iyayi suka dago mun,su adole yau sun amshi aiki na,kila nima an sallame ni ne.

Sum² nafara aiki na ta hanyar nufan kitchen don dama su goge falon da sharewa suke. Banfi mintoci 30 ba na kammala masa dan abuncuwa da zai samu yy break. Muryan su Atika naji suna gulma ta hanyar cewa" kuga Wahala Matan da Ansallemi kan mhisd Caterine ta dakatar dake kinxo kina wani wahalar banza.

Gaba na ne ya fadi Kwallah ya ciko min ido. duk da haka ban bar aikin ba

Please Login or Register in order to submit comment