You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya ce " hafiz aina ka kalli shi Mansoor din ?" fada mishi hafiz yayi sannan Mr azaad yasake maida kallonshi kan areef ya ce " ka kwantar da hankalinka kafadamin aina kaga Mansoor din ?" duk abinda yafaru a garden din areef ya fada mishi sannan yakara da " yayi tamin magana wanda nakasa gane me yake nufi amma naji yafadi wata kalma 'ku kare kanku daga sharrinta ' wannan kalmar ce kawai zan iyacewa naji "
zeenat kam uwar tsoro tunda taji aka ambaci sunan mansoor ta kankame fawwaz kam ta ki sakinshi. girgiza kai ummi tayi ta ce " karku daga hankulanku akan wannan mansoor yariga da ya mutu kawai sharrin shedanu ne da jinnu amma kun tabajin wanda ya mutu ya dawo ne " zaro ido hafiz yayi shima lokaci daya jikinshi yafara rawa jin wai Mansoor din da ya hadu dashi har sukayi magana wai matacce ne ya rigada ya mutu babban tashin hankalinshi shine inya tuna yar maganar da sukayi na wasu yan mintuna , da mugun karfi zuciyarshi yake bugawa sakamakon jin maganar yayi kamar saukar aradu hakan yasa yadafe kirjinshi da karfi sauka yayi akan kujera yaduqa kasa yana rike da setin zuciyarshi dagashi Mr azaad yayi yadan rungumeshi dan dama yasan hakan seya faru muddin hafiz yaji dan bakowane yake da wannan karfin guiwan tunkarar magana makamancin wannan ba ace kayi magana da wanda yarigada ya mutu baka sani ba daga baya inkaji hakan dole hankalinka yatashi , kokarin zaunar da hafiz Mr azaad yakeyi yaji yakara nauyi nan yagane suma yayi yasa ya kwantar dashi akan kujeran dauko ruwa fawwaz yayi yamikawa Mr azaad ya yayyafawa hafiz shuru be farfado ba , zama ummi tayi kusa dasu ta daura kan hafiz akan cinyar ta tarike hannunshi tana murzawa da dan karfi ko hakan ze temaka duk suna tsaye akanshi , saukowa fanan tayi tana murna tasamo dabinon dataje nema, ta samesu duk sunyi cirko_cirko sannan ga hafiz dake kwance dasauri takaraso falon , tambayar fawwaz tayi meyasa meshi karya yamata yafada mata kancewa sunga yarike kirjinshi ne daga bisani kuma yasuma zama tayi agefen kujeran ta rike hannunshi dede wajan pause dinshi taji yana harbawa da wuri tasake sa hannunta akan kirjinshi nan taji wani irin lugude da zuciyarsa yakeyi hakan ne ya tabbatar mata da tabbas wani abune yagani ya razanashi ko kuma wani abun yaji daya firgitashi kallon ummi tayi ta ce " yadan shigo yar doguwar suma amma zuwa nan da 4hours ze iya farfadowa amma kuma in muka bari ya farfado ahaka tabbas akwai matsala , ze iya samun matsalar brain kokuma yashiga firgici har nan da sati daya " tagama musu bayani tana karasawa kan center table tadauki pen and paper data gani ta rubuta allurai da magunguna ta mikawa fawwaz karba yayi yafice dasauri dukda darene zeyi wuya susamu pharmacy abude sede yadangana asibiti, duk suna zaune fanan ta kalli Mr azaad ta ce " Mr azaad meyasa meshi " bayason yafada mata yasa kawai ya ce mata " baby we don't know kawai ganinshi mukayi ahaka yarike kirjinshi" ta ce " Allah sarki inna mishi alluran nan in sha Allah zeji dama dama dan zesamu baccin 12 to 14 hours kuma baze tashi da wannan firgicin ba " jinjina kai yayi ummi ta ce "zeenat tashi kije ki kwanta dare yayi ko " make kafada tayi alamar ah ah dan duk atsorace take bazata iya kwana ita kadai ba , taso basu dariya areef kuwa shuru yayi yana binsu da ido , haka fawwaz ya dawo da allurai da magunguna , allurai fanan tayi mishi sannan Mr azaad yadaukeshi cak kamar wani yaro karami yayi part din su fawwaz dashi yakaishi dakinshi yakwantar dashi hade da rufeshi da blanket sukafito . Ummi tabasu umarni da kowa yaje ya kwanta haka suka shige part dinsu , Mr azaad maganar mansoor ya tsaya mishi arai amma zesan yanda ze bullowa lamarin .
Duk wannan wainar da ake toyawa mommy bata da masaniya akai tana nan tana neman hanyar da zata kashe kaf yan gidan hatta yayanta suma seta kashesu bazata bar kowa ba dan dukkansu ta tsanesu mansoor ne kadai takeso shikuma yarigada ya mutu, tamafi tsanan anty shayida shisa aduk sanda anty shayida tasamu karamin ciki , tunkafin sunsan da cikin mommy take cinye dan tun a mahaifa, kusan sau takwas anty shayida nasamun ciki mommy tana cinyewa tunkafin yazama hallita take cinyewa. Haka tasoyiwa anty zainab amma dake mijinta atsaye yake gashi babban dan siyasa kuma malami.
Bauchi state
Fitowa suhaima tayi daga bedroom dinta tana rike da waya tana video call da fawwaz har karfe 11:30 nadare ta farajin yunwa tafito tashiga kitchen din ta ajiye wayar yanda yana kallonta ta daura indomie akan wuta yadafu taje falo tazauna tanaci fawwaz ya ce " ba bismillah kenan? " Yar dariya suhaima tayi ta ce " hubby tom ai kona maka bismillah bazeyu kaci ba sede inci mana ka ji " tafada tana ci gaba da cin indomie fawwaz ya ce " to babynah kici mana din " haka suka dinga hira kafin ya kashe kiran dan dare yayi suka sauka a online din .
fanan ta dade dayin bacci while Mr azaad idonshi biyu beyi bacci ba dan so yakeyi adaren nan yayi clearing issues din dasuke faruwa acikin gidan sulalewa yayi yafice adakin yasauko ya bude kofar part din gaba daya yaje garden din shikadai kamar wani maye ko ina yayi tsit se kananun maganganun dayakeji kasa_kasa which is yasan nasu wayene haka yazauna yana girgiza kafa.
Mommy na kwance akan makeken gadonta fatalwar mansoor yabayyana atsaye agefen gadonta, murya da dan karfi yafara kiran " mommy! mommy! mommy! Ki tashi kina bacci wato kin barni inata garari Koh?" adan firgice mommy ta tashi daga bacci tana mustsuka idonta rass ta waresu akan Mansoor dake tsaye yana sanye da fararen kaya tashi tayi tazauna dakyau tana kiran " Mansoor dina kaine? dana nayi kewarka" daka mata tsawa yayi ya ce " karki sake kirana da danki muguwa azzaluma, ke ba uwa ta gari bace annamimiya kawai . hankalinki yakwanta dakikayi sanadiyar barina duniya?" ya daka mata wani gigitacciyar tsawa " nace hankalinki yakwanta yanzu? bazan taba samun salama ba harse asirinki ya tono senayi hanyar dazan fadawa kowa ke matsafiyace yar kungiyar BAPHOMET masu shan jini da shirka , yanzu wato babban burinki shine ki kashesu ko ?" hawayene yake zuba akan kumatun mommy taduqa akasa ta ce " my son kayafemin yanda nakesonka bazan taba barin komai yasameka ba bare har inyi sanadiyar rayuwarka sannan magana akan daukan fansana dole sena kashesu kaf dinsu Koda shugaba tanzarzar be amince min ba sena aiwatar da hakan , daga zaran munyi nasarar gamawa da shafin sarauniyar nasminaya sesune target dina " girgiza kai kawai fatalwar mansoor kafin lokaci daya yabace bat .
Inbanda tsuma da jijjiga babu abinda jikin Mr azaad yakeyi tsabar bacin rai da bakin ciki idon nan yajuya yazama mugun jajir da karfi yake cizan libs dinshi na kasa da har gurin yayi ja sosai yafara tsastsafo da jini . yau bayajin ze iya barin mommy ta kwana daranta seya kasheta dan daga inda yake zaune a garden yana yana jiyo duk wani maganar dasukayi da ita da fatalwar mansoor tabbas mommy ta cucesu ta ha'incesu yanzu dama all this while suna tare da munafuka matsafiya agida daya basu saniba tom tabbas shi zedau mumunar mataki akanta tunkafin abba yadawo daga marley sede yadawo yaji labarin kawai ya kasheta. yana cikin wannan mugun bacin ran fatalwar mansoor yabayyana agabanshi fuskanshi dauke da murmushi ya ce " yayana yanzu nayi farin ciki dakasan gaskiya akan mommy zansamu salama yanzu bazaku kara ganina ba se adarul salam nabarka lafiya " yafada yana me bacewa yanawa Mr azaad bye-bye shima bye-bye din ya mishi duk da yana cikin matsanancin bacin rai, hakan be hanashi maida mishi da martanin murmushin daya mishi ba, domin yafayyace musu komai dangane da mommy.
Tofa ana wata ga wata yaude alhamdulillah asirin mommy yatonu shikenan.
Ina jiran ruwan comments dinku duk wanda yasan ina binshi bashin comment yafito yamin abuna tam.
Se munhadu ranar laraba jibi kenan inme duka yakaimu da Rai da lfy ππ.
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
π§ββοΈπ§ββοΈ NIDA PATIENT DINA π©Ίπ©Ί
π§ββοΈπ§ββοΈ NIDA PATIENT DINA π©Ίπ©Ί
Story & written by βοΈ
MRS πΉ ISHAM πΉ
ππ JARUMAI WRITERS ASSOCIATION π
Gargadi
ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba takowani siga ko akaranta min shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutum zebimin hakkina Kuma yasakamin.
Three pages in one .
Page 5οΈβ£8οΈβ£
Yana barin garden din part din mommy yanufa kofofin part din arufe knocking yayi , mommy dake kuka taji ana knocking yasata goge fuskanta tazo ta bude kofar ganin Mr azaad ne yasa tadaure fuska tamau ta ce " kai lafiya zakazo kana bugamin kofa da wannar uwar Daren?" miskilin murmushi Mr azaad yayi yadan hadiye bacin ranshi ya ce " ehhh to lafiya ba lafiya ba zan iya shigowa ?" shima yajefa mata tambaya ganin taki motsawa daga inda take tsaye ne yasa ya kutsa kai cikin part din nata direct kan kujera yaje yazauna yana ciro wayarsa yakira layin abba, " hello abba sorry natasheka abacci banason kadawo ka ji labarin na kashe maka mata shisa nace bari in sanar dakai tukun" tunda abba yaji abinda Mr azaad yafada yagane kancewa yagano komai hamdala yayi dominshi yasan komai akanta amma shi sun rufe mishi baki Koda yayi kokarin sanar da wasu seya gagara , gyara murya abba yayi ya ce " karka mata komai tukun 4:00am zan biyo flight din safe just make sure bata gudu ba " jinjina kai Mr azaad yayi ya datse kiran.
ganin ya shige mata falo ne yabarta tsaye acan bakin kofa , shigowa falon itama tayi taga ya zauna be da niyar tafiya kuma shi be fada mata abinda yakawoshi wajanta ba ya sa ta ce " katashi ka fita kabani guri " afusace yatashi dan dama haushinta yakeji kamar yakasheta lokaci daya kowa ya huta , ya mata mugun shaqa fiffitowa idon mommy yayi waje taji damkar maza kakari tafarayi idonta yajuya jaa tana kokarin shekewa domin shaqar da Mr azaad yamata bana wasa bane ya daka mata tsawa lokaci da ya yacanza fuskan nan tayi ja tsaban bacin rai " kimin shuru ko kuma kiyi dana sani" mit mommy tayi ganin ya hayayyako gashi yaki sakinta cillar da ita yayi ta kifu akasa tana rike wuyanta hade da nishin wahala ga idonta yayi ja , dakyar ta rarrafa tazauna akan kujera tana tunani iri_iri shi meyasa Mr azaad zeyi mata haka yaron da ma zata iya kirga sau nawa magana yataba hadasu tunda aka haifeshi be taba shiga part dinta ba sede in yanason hira da anty zainab da anty shayida ya kirasu suzo part din ummi ko a garden.
Tanzarzar na kallon abinda yake faruwa ta mudubin tsafi nan yagane asirin mommy yatonu kuma inde taji bakar azaba zata iya tonawa sauran yan kungiya asiri hakan yasa yamata magana ta cikin madubin " hafsat kisan hanyar dazakiyi ki tsere musu domin yarigada yasan komai akanki " jin abinda tanzarzar yafada mata yasa taji wani irin fargaba yakamata bawai dan na asirinta yatonu ba sedan tasan muddin ta fadi wata kalma dangane da yan kungiya to tabbas nata yakare, dago kai mommy tayi ta kalli Mr azaad dashima firgitattun idonshi na kanta , wuff tamike zata da ki kasa domin ta bace kenan , sarauniya ta damki dantsen hannunta ta baya , wurgi da ita kasa sarauniya tayi tana binta da muguwar kallo da idanunta masu firgita abokan gaba fuskan nan babu alamun sassauci ko rangwama atare da ita. Mamaki ne yakama Mr azaad ya akayi fanan tasan da yana nan Kuma ga abinda yakawoshi, laakari da irin shigar dake jikinta dayayine yagane ba fanan bace sarauniya fadima ce , sarauniyar nasminaya, hakan yasa yamike yatsaya yana kallonta ganin ko inda yake tsaye bata kallaba bare yasa ran zatamai magana. abinda yayi laakari dashi shine duk sanda ta bayyana a asalin sarauniyarta tofa wasu dabi'un ta kamar bata sansu ba wata zuciyar ta ce mai " karfin jaaazana ne yasa hakan domin inta bayyana, sarauniya ce bawai fanan ba " gabanshi ne yatsinke lokaci daya, da ya tuna kenan fanan intabar nasu duniyar mantawa zatayi dasu gabaki daya kenan bazama tasan da zamansu ba balle tayi tunanin dawuwa wajan ahalinta, dafe kai yayi dayaji yana juyawa.
daga inda sarauniya take tsaye ta daga hannunta tayi pointing mommy dake yashe akasa , kyasta yatsunta guda biyu tayi nan take igiyoyi suka fara daure mommy dauri bana wasa ba suka mata tamau yanda ko numfashi dakyar take iya fitarwa. tana gama daure mommy kuwa ta bace tabarshi tsaye awajan.
barin part din Mr azaad yayi yasa securities su tsaya akanta kar subarta tayi koda motsine dukda adaure take
. yakoma garden yazauna yana kada kafa har asuba , yayi alwala duk a garden din yanufi hanyar fita a gidan dan zuwa masallaci yaga su fawwaz da areef sunfito su ma. jerawa sukayi sukaje suka gabatar da sallah suka dawo be fadawa kowa abinda ke faruwa ba haka zalika be fada musu abba yataso ba yawuce part dinshi samun fanan yayi tana zaune tana azkar zama yayi akan kujera yana facing dinta harta idar ya ce " morning wifey" ta ce " habiby katashi lafiya ?" ya lumshe idanu kawai. ta ce " habiby ina kaje daren jiya natashi naga baka nan amma naganka amarfakina a part din mommy" " eh naje part dinta ne " daga haka yakawar da zancen ta hanyan dauko wata maganar daban ya ce " gobe zamu tafi yau zankaiki kije kiyiwa su mama sallama yau " cike da murna taji zataje gida ya ce " to Allah yakaimu" bata koma bacci ba ta cire babban hijab din jikinta yarage daga ita se wandon falazo da vest ajikinta tafara gyaran part dinsu tayata shima yayi suka gama , atare suka shiga kitchen sukayi breakfast dan wake tamusu tunda tafara kwaba dan waken da digawa Mr azaad yaketa yamutsa fuska yana " nide bazanci wannan abun ba abu kamar wani kwallo_kwallo " dariya tayi tasan be taba ci ba gashi itakuma shi takeson ci yau din nan gama danwaken tayi ta dafa kwai ta baresu sannan tayanka vegetables salad , tomato, ta yanyanka kwai din a bowl daban taki saka albasa aciki saboda yanzu seyasa bakin mutum yafara warin albasa, plate ta dauko tazuba danwaken dayawa sannan tasaka mai din data soya yaji albasa ta zambada yaji zaro ido waje Mr azaad yayi ya ce " yanzu da wannan pepper zakici baby" murmushi tayi ta ce " kadingayin jam'i zamuci zakace yau zan koya maka yanda akecin danwake" haka taci gaba da saka salad da tomato din da ta yanka tasa kwai din. ( bakaramin daukan hankalina danwaken nan yayi ba lokaci daya naji yawuna ya tsinke, kunsan ni , akwai ni akwai kaunar dan wake sosai. gashi ban Isa ince zanci ba yanzu se Mr azaad yayi kasa_kasa dani ) haka ta dauko plate din taje tsakiyar falo ta ajiyeshi akan carpet takoma taje tadauko bottle water da glass cup ta ajiye ta zauna zama shima yayi dan yaga yau tayi niyar kumburar mishi da ciki ne . sa hannunta tayi tafaraci tana santi babu yanda ya iya haka shima yasa hannu yayi yanda tayi yakai baki, ai ba arziki yafurzar dashi waje idonshi harseda ya kadΓ murya na rawa ya ce " is to spicy kiban ruwa " zuba ruwa tayi a glass cup ta mika mishi yasha yanata shishitan yaji, sannu tamishi sannan tasa hannu dede ta gabanshi ta kwashe yajin yarage dan kadan takara maggi ta gauraya mishi ta ce " to nacire yajin kaci ka ji " make kafada yayi kamar yanda take mishi a shagwabe ya ce " nide bazan iya cin wannan abun ba is to spicy" dariya tayi ganin yanda yake mata shagwaba hakan ya kayatar . diba tayi ta bashi abaki dakyar ya iya cinyewa dukda babu yajin sosai wannan karan, haka suka cinye danwaken tas daga ya ce yakoshi setace ah ah yakara kadan de haka ta mishi wayo tadinga feeding dinshi harsuka cinye ,sunaci suna shishitan yaji kamar wayanda akama dole, sukasha ruwa hancinshi har wani ja yayi dan wahala gaba daya yazama wani kala dukda yaji dadin danwaken amma ya ji ya azabtar dashi .
Karfe 10:00am dede abba yashigo gombe yasauka agida part dinshi yayi , wanka yayi ya kimtsa babu wanda yasan da zuwanshi saboda babu wanda yasani se Mr azaad . Kiran yayanshi yayi awaya yasanar musu yanason ganinsu yanzu yanzu batare da bata lokaci ba , wannan kiran gaggawan da abba yamusu ya tayar musu da hankali yasa babu wacce tabata lokaci kowa suka hallara a main falo harta su Mr azaad da fanan duk babu wanda bezo ba duk suna zaune ,m afalo sukaji sallamarshi , zama yayi akan kujera fuska babu yabo ba fallasa. shan jinin jikinsu sukayi kowa yasake shiga rigar nutsuwa, suka fara gaisheshi.
bude taro yayi da adduah sannan yafara magana " na taraku anan ne bandan komai ba sedan fayyace muku gaskiya" zuba mishi ido sukayi sunason suji meye ze fada , bin kowannesu yayi da kallo.
ya ce " kamar yanda dukkanku kuka sani hafsat itace matata ta farko ! yar wazirin gombe ce tun kafin in kammala karatuna muka fara soyayya da hafsat , amma mahaifiyata wato marigayiya ammi , bata bada goyon baya ba saboda hafsat batada kunya bata son mutane kullum ako da yaushe adaki ake samun hafsat bata mu'amula da kowa seni sekuma yan gidansu ga ta da tsiwa ga shegen rashin kunya, amma dukda wannan dabi'ar nata take sona kuma nima inasanta, me martaba da waziri sunyi farin ciki sosai da kasantuwar wannan al amarin bayan na kammala karatu aka mana aure , me martaba yace tunda yanzu na kammala karatuna kuma nayi aure ni zan karbi sarautar gombe , hankalina yatashi domin ni bantaba kaunar zama sarki ba hasalima abubuwan sarauta baya burgeni ni babban burina shine inzama business man, shisa na ki kuma fulani ta goyamin baya , haka me martaba yakyaleni nayi abinda nakeso .
dede da rana daya ammi bata ta ba son hafsat ba in an tambayeta dalili setace jikinta nabata akwai wani mugun abu atare da hafsat tana ganinta amafarkinta. babu wanda yataba daukan maganar ammi serious kowa gani yakeyi kawai dan ta tsaneta ne yasa take fadar haka. bayan aurenmu da wata daya ammi ta rasu sanadiyar bugawar zuciya haka akayi zaman makoki aka watse tundaga nan ne hafsat ta fara nunamin mugayen dabi'un ta, bata sallah , ba karatun addini ko adduah bantabaji tayi ba,bata kaunar kowa ya rabeni , sannan kullum tana daki yanda na fita nabarta haka zandawo in sameta bata, bantaba sanin ya kalar test din girkin hafsat ba har yau danake muku wannan maganar sede masu aiki suyi mana abinci. bata rayuwarta da kowa tun ina mata fada harna hakura nazuba mata ido domin daga zaran nafarayi mata fada itama zata hayayyakomin kamar zata dakeni nikuma bazan iya sa'in sa da mace ba yasa se inbar mata part din se dare in dawo haka har tasamu cikin zainab ta haifeta, tunda nake arayuwata bantaba ganin macen da ta tsani abinda tahaifa ba se akan hafsat ta tsani zainab har kamata natabayi tashaqe ta tana kokarin kasheta dakyar nakarbi zainab ahannunta jaririya dabatasan komai ba se zabga kuka takeyi . daukan zainab nayi nakaiwa fulani nafada mata abinda yake faruwa hannu biyu ta karbeta renon zainab yakoma gun fulani. mukaci gaba da zaman doya da manja nida hafsat yau lafiya gobe kuma fada da tashin hankali ahaka harta fara fita araina dan nagaji da mugayen dabi'un ta. zainab nada shekara uku hafsat tasake samun wani cikin bata nuna bataso ba wannan karon har ina murna gata iya gata na nuna mata amma tana haihuwar shayida komai yasake dagulewa tsantsan tsana shayida tagani kamar ba ita tasha wahala tahaifeta ba harta abinci bata ba ta haka zata wuni da yunwa se na dawo gida tunku mukecin abinci abin nata da ya isheni ne yasa nafada mata muddin taci gaba da gallazawa shayida to nikuma zan saketa hakan ne yasa tayi sanyi domin tanasona sosai , akan abinda takewa shayida tarage kashi 20 acikin 100 gashi Zainab bata isa tazo part dinta ba seta mata mugun duka , lamarin ya isheni yasa nasaketa saki daya ta tafi gida nikuma nadauki shayida itama namikata gun fulani.
zuwana dubai gabatar da wani meeting da babban Company na A.A AZAAD, bayan mungama meeting kanin sarki azaad me suna arash ya gayyaceni gidansu cin abincin dare dukda inada wani uzuri haka na amsa gayyatarshi naje babban gidan sarautar dubai sunada matukar mutunci da karrama bako yanda suke haba_haba dani hakan yamin dukda nima dan sarki ne . muna zaune munacin abinci sarki azaad ya gabatar min da ahalinshi da matar kannenshi , matar arash dakuma matar asaad, sekuma matarshi wato mahaifiyar umminku aysha kenan se yaransu dasuka kasance dukkansu maza rai 9 jinjina kai nayi nace " Masha Allah,Allah ya azurtaku da yara maza Allah yarayasu" suka amsa da ameen sarki azaad ya ce" ai sunada kanwa guda daya rak ita kadaice mace agidan nan " murmushi kawai nayi bance komai ba , kiran sunanta sarki azaad yayi " Aysha" fitowa tayi tana tafiya cikin nutsuwa yarinyace dabazata wuce shekara 15 ba aduniya kyakyawar balarabiya sanye da doguwar riga baka kanta rufe da mayafi tunda tafito idona akanta yake lokaci daya naji nakamu da santa, gabatar min da ita sarki azaad yayi, fuskanta dauke da murmushi tagaisheni amsawa nayi iname yaba hankalinta komawa ciki tayi duk matan wajan suka bamu waje , harga Allah tunda naga aysha naji inasonta kuma so na aure bazan iya barin dubai batare danayiwa iyayenta magana ba , ban boye musu komai ba na fayyace musu abinda ke raina nahada da fada musu inada mata da yaya biyu. banyi tsammanin zasu amincemin ba cikin ruwan sanyi ba kawai naga sun amince domin ba kowani balarabe ko farin fata bane yakeson hada jini da bakar fata ba sukace in turo iyayena da full confidence dina nabar masarautar zuwa masaukina dukda sunyi sunyi inzauna na ki. haka nadawo nigeria da farin ciki naje nasamu me martaba nasanar mishi shima ya amince da lamarin saboda suna shiri sosai da sarki azaad haka suka nemamin auren aysha, tunda hafsat taji labarin zan kara aure ta dami waziri da sede yanemeni zata koma gidanta haka waziri yanemeni yarokeni da inmaida auren haka kuwa akayi namayar da auren . hafsat takoma gidanta mukaci gaba da rayuwa balaifi dukda bakamar da ba , har a wannan lokacin bansake haduwa da aysha ba saboda a al adarsu inde yarinya zatayi aure bazata sake ganin mijin ba ko jin muryanshi ba se randa aka daura musu aure. Bayan nagama gina wannan gidan ne aka daura aurena da aysha saboda nafison zama awajen masarauta, hafsat itace uwar gidana yasa nabata zabi tazabi part din da takeso haka tazaba , aka kawomin aysha gidana yan uwanta mutane hudu ne suka rakota bayan anyi shagalin biki anwatse , natarasu a part dina dan musu nasiha dukda aysha batajin hausa daga larabci se turanci haka namusu fada sannan naraba musu kwana , hafsat bata nunamin komai ba ta tashi ta tafi abunta , haka rayuwa taci gaba da tafiya nan ne nafara samun kwanciyar hankali. takuramin aysha tayi akan lallai sede indawo da shayida da zainab wajanta haka nakarbosu daga wajan fulani na damka mata su aikuwa suna ganin gata sosai