Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce " ummi yau kinsan irin exercise din data samu sekinji tausayinmu , gashi yarinya nan narasa ya akayi ta iya gudu kamar wata yar tsere" tazauna tana magana hade da murmushi tana kallon twinkle dake kan cinyar ummi ga Mr azaad agefensu, dariya ummi tayi dan tanajinsu ta ce " to bagashi yanzu tasaku kunyi exercise ba " dariya ummi da suhaima sukayi gaishe da Mr azaad suhaima tayi ya amsa da " lafiya " daukanta yayi ya ce " muntafi " harsuka fita tanayi musu bye-bye suma sunayi mata fuskokinsu dauke da murmushi.


Dropping dinta yayi a school har cikin class dinsu yakaita sannan ya koma gida yakoma bacci .

Karfe 11:30 Faisal yakirashi yasanar dashi ankawo order furniture na company da sukayi a London" okay " kawai yace yakashe wayarsa yatashi yayi wanka yashirya cikin suit yafita zuwa Company dan ganin kayan da aka kawo.


Ya Usman da hairah suna zaune afalon gidansu ga yarinyarsu samha tana wasanta akan keken yara ya usman ya kalli hairah ya ce " honey ki kalli samha da kyau " juyawa hairah tayi ta kalli samha din bataga komai ba ta ce " meye ajikin samha din ya usman?" ganin bata fahimci abinda yake nufi bane ya ce " bakomai kawai de naga Yakamata ace tasamu kanwa ko kanine yanzu fa two years take " lokaci daya hairah ta ɓata rai wanda shima seda ya fahimci haka ta ce " ya usman Ni fa daga kan samha bazan sake haihu ba saboda azaban danasha a haihuwar ta kaɗai ya isheni" calmly ya usman ya ce " Yes Honey nasani amma ko da daya ne semu sake haihuwa planning din ya isa haka in yaso kika kara daya se abar haihuwar haka kinji Please" " ah ah ya usman bakasan wahalar danasha ba ni kadai nasha wahala ta ɗan haka nide gaskiya bazan iya haihuwa ba shine kawai " tafada tana haɗe fuska , ran ya usman yayi matuƙar ɓaci ganin yana lallabata amma tana tuɓurewa sekace akanta aka fara haihuwa mata nawane suka sha bakar wahala wajan haihuwa bayan sun haihu din kuma suka sake dauka wasu cikin amma ita tace daga yarinya daya bazata sake haihuwa ba rai abace ya ce" hairah planning ko kinaso ko bakyaso se an tsayar dashi saboda ni inason yara inke bakyaso nagama magana ta " zuciya da shedan suna zuga hairah gakuma tarin yarinta ta ce" to kuwa sede kanemi wacce zata haifa maka yara amma nikam nagama " girgiza kai yayi ya ce" haka kikace ko? Shi kenan karki damu basekince innema ba zannemo kuma zan aurota zata haifa min adadin yaran danakeso " yana gama fadin haka yadauka car key dinshi yafita yabar mata gidan , kuka tafashe dashi jin wai ze sake aure kukanta tasha ma'ishi sannan ta wanke fuskanta tazo tadau samha suka shiga daki .

" Ya yaseer Please inason zuwa gida kusan kwana na uku banga twinkle ba kuma nayi missing su ummi" dariya yaseer yayi ya ce " beb yanda kikace haka za'ayi anjuma da dare zamuje ! nagama ko tambayar ashraff bakyayi ko shi bakiyi missing dishi bane? " gyara kwanciyarta tayi ajikinshi ta ce" to ai nayi missing din shi shima in mukaje yau aiduk zan gansu " ya ce" okay,mubina tayi bacci ne?" Ya tambayeta karamar yarsu kanwar ashraff da take da shekara daya ta bashi amsa da" tayi bacci fah tun dazun " " bari inje office" mikewa sukayi atare tarakashi ya hau motar yafita.


Yau auta bataje makaranta ba wai kanta na ciwo suna zaune suna hira da mama , areef da yatashi a office ne yabiyo gidan , yayi sallama mama ta amsa mishi ya shigo gaisheta yayi yazauna kallonshi auta tayi ta ce " ya areef ina wuni ?" shima kallonta yayi kafin ya ce " lafiya lau auta ya akayi yau bakije makaranta ba?" rike kanta tayi da hannu ta ce " yau da ciwon kai natashi se inji kaina yanason faɗowa " mama ta ce " ko kuma yau bakiyi niyar zuwa ba kawai " dariya areef yayi ɗan yasan bawani ciwon kai din da auta takeyi tafadi hakane ɗan kartaje makaranta ya ce " wai gaskiya ciwon kai be kyautaba sannu kinji " narai_narai tayi da ido ta ce " yawwa ya areef! Ina twinkle sarkin rigima da iyayi " yanda tayi maganar yayi matukar basu dariya mama kam girgiza kai tayi kawai ɗan ita tafi yarda da duk wani hali irin na auta shi twinkle ta gaɗo ga iyayi ga manyance da surutu , ga shi twinkle din tayi saurin magana Shisa insuka haɗu ga auta ga twinkle sede kawai tazuba musu ido , tsagaitawa da dariya areef yayi yace " mama kiji min ikon Allah wai kura ne zecewa kare maye , ke yanzu auta dan Allah har zakicewa wani yanada surutu da iyayi ?" ɓata fuska auta tayi ta ce" ya areef banaso kaga kai kullum seka tsokaneni, nide nasan banida surutu " sa ke tuntsirewa da dariya areef yayi ya ce" eh hakane kam bakida surutu mamar twinkle, birthday din twinkle ranar Friday ne zanje indauki aslam da kawarki Islam se inzo indauke ki daga nan se mu biya mu dauki samha da kuma yan biyun anty shayida adeema da adeena " yar dariya mama tayi ta ce" lallai sannunka da kokari areef" dariya shima yayi daga kai sama auta tayi tana yar tunani ta ce" oh my god ! inata nazarin gift din da zanbawa my twinkle as a birthday gift " mama kam mikewa tayi dan iyayin auta ya isheta dama bacci takeji ta shige dakinta tabarsu a falo se surutu take zubawa areef shikuma ya tsaya biye mata yanacin dariya.



Karfe 5:00pm Mr azaad daga office dinshi shida Faisal suka wuce matrix dauko auta dan yasan sun tashi , suna isowa gida tafara kokarin bude kofar motar zata fito ɗan ta hango suhaima da ashraff da minal a gefen part din suna zaune akan lallausan carpet ga fruit dake wajen ga kuma kayan madaran minal damko hannunta Mr azaad yayi ya ce" twinkle inazakije?" nuna mishi su ashraff tayi ya ce" yanzu kibari kiyi wanka sekije kuyi wasan " to ta ce suka nufi part dinsu Faisal yabi bayansu da school bag dinta da lunchbox din , wanka yayi mata yasa mata riga da wandon jeans yasa mata hula yana gamawa ta manna mishi kiss a kumatu ta ce" bye-bye daddy " tafita da gudu hafiz na zaune afalo yaga wucewar ta ya ce" to anty twinkle se ina? " saurin da takeyi ne yasa bata tsaya mishi magana ba kawai tanuna mishi kofa tayi waje abinta suna zaune suka hango ta rungume suhaima tayi ta ce " i missed you mom one " dake haka take kiran suhaima zeenat kuma ta ce mata mom two shafa kanta suhaima tayi ta ce " missed you too my baby twinkle" bata fruit tayi dasuke a slice tafara sha hartace ta koshi sannan ta hau wasa da ashraff da minal, kan mangrib suka tattara suka koma Ciki ɗan yin Sallah.
Bayan sallar isha yaseer, zeenat da mubina sukazo seda suka kai goma kafin suka koma gida.

Ana gobe birthday party din twinkle Abba yadawo tunda yadawo ta koma part dinshi ita da sauran jikokin shi sauran da basa gidan kuma gobe za'a kawosu, Abba idan yakallesu sanyi yakeji har ranshi ganin shima yanzu yatara jikoki masu yawa alhamdulillah, kuma kaff cikinsu babu mafi soyuwa agareshi irin twinkle yana matukar sonta ko kuka tayi in yana nan tofa seyaji dalili son dayakeyiwa mamanta fanan ne yaƙaru yakoma kanta .

Washe gari da safe bayan sunyi breakfast aka dauko kwararren me decoration yazo yayi decoration me masifar kyau a main falo white and pink color falon bakaramin kyau yayi ba , kamar yanda areef yafada haka kuwa yayi gidan anty amina yaje yakwaso aslam da islam anty amina ta ce se bayan sallar juma'a zatazo sannan yabiya yadauko auta ilham nan suka bude sabon fagen iyayi da surutu ita da islam ɗan itama ba baya ba wajan surutu areef de ta cikin madubi yake kallonsu shida aslam dasuke gaba daga nan yaje yadauki samha se sukaje gidan anty shayida yadau adeema da adeena , gidan anty firdausi sukaje suka dau junior sukayi gida , yau jikoki sun cika gidan hayaniya tako ina se barna dasukeyi acikinsu mubina ce kawai baazo da itaba itama se anjuma zasuzo itada zeenat da yaseer din .

Bayan ansauko daga jumma'at ne anty amina da anty shayida sukazo atare , se yaseer da zeenat kowa ya hallara agida suna nan amma banda anty zainab ita sunyi tafiya garin dangin mijinta, anty amina ita da kanta tayiwa twinkle birthday cake pink color and white babba me three steps yasha decoration a saman an rubuta' happy birthday twinkle ' ga snacks da sweet din da akayi ga drinks da rago an gasa shi komai yazama ready afalon bayan sallar la'asar, anty shayida da zeenat sukayi musu wanka suka shiryasu cikin hadaddun kaya sukaje main falo suka zauna kowa ya hallara a falon harta Abba da kowa suna zaune ana jiran fitowar birthday girl, wanka akayiwa twinkle anty shayida ta shafa mata lotion hade mata gashinta tayi waje daya tayi fakin dinsu tabar mata wasu agaba suka zubo tayi mata light make up kayan barbie girl da ummi tayi mata order daga Dubai tasa mata gown din pink color rigar kansa abin kallo ne dauko mata wasu mayun takalma tayi masu kama da sandals amma yanadan hill kadan white color ta samata , tasamata dankunne dakuma chain din gold da bangules tasa mata crown silver color ta fesheta da perfumes, twinkle tayi matukar kyau bana wasa ba ta hadu iya haduwa , ta daurata asaman mirror kallon kanta twinkle tayi ta zaro brown eyes dinta ta ce " haaaaaa! Haka nayi kyau " tafada tana juyawa tana kallon kanta dariya kawai anty shayida takeyi mata sannan tadinga mata hotuna kala_kala sannan ta dauketa a kafadarta suka fito tunda suka fito suke kallon twinkle suna sakin murmushi musamman Mr azaad sauketa ƙasa anty shayida tayi nan take suka fara "woww baby twinkle kyau kenan " dariya itakuma takeyi wajanta auta taje tace " wow my twinkle you so gorgeous" tafada gyara mata zaman crown din kanta da maganarta na yara ta ce " thank you anty" wani abu ne yasoki Mr azaad azuciya sedayaji kamar yazubar da hawaye saboda zafin rashin fanan gaba daya jikinshi sanyi yakeyi aduk sanda twinkle ta tambayeshi yaushe mommynta zata dawo daga tafiya wani lokacin ya mata karya wani lokacin yama rasa meze fada mata .


Mikewa sukayi dukka aka daura twinkle akan kujera yanda tsayinta ze iso cake din nata suka fara mata wakar " happy birthday to you! Happy birthday to you! happy birthday dear twinkle happy birthday to you" haka suka dinga mata wakar itakuma tana dariya, zeenat tace mata ta wure wutar candle din aikuwa haka tayi ta sunkuyo da karamin baƙinta tawure wutar candles din suka mutu nan sukayi tafi mika mata wuka Mr azaad yayi ya ce" now cut the cake " karba tayi harta daura wukar akan cake din seta fasa ta ce" aini nace bazan yanka cake ba se mommyna tazo " dam seda sukaji kirjinsu yabuga jin sabon rigimar da twinkle takeson daukowa Mr azaad ne ya ce" baby your mom is coming kiyanka cake din" turo baƙi tayi ta ce" nooo i won't cut it se mommy tazo" ummi kam shuru tayi takasa magana domin twinkle ta fama mata inda yake mata ciwo Abba ne ya ce" haba amaryata ki yanka cake din mommynki na hanya" " nooo grandpa" ta fadin haka ta fashe da kuka rarrashin duniyar nan sunyi mata takiyin shuru kuka takeyi harda ajiyar zuciya da shesheka tana kiran " mommy please come " duk jikinsu yayi sanyi tausayinta yakamasu run rasa mezasuyi mata tayi shuru, muryar Mr azaad na rawa dakyar ya iya cewa " twinkle kidena kuka , in angama birthday party zan kaiki wajen mommynki kinji " yanda yake maganar kadai duk wanda yaji yasan akwai babban ciwon dake damunshi acikin zuciyarshi yau kuma anfame mishi , twinkle na kuka ta ce " noooooooo" dafa kafadarshi yaseer yayi da shima jikinshi yayi mugun sanyi , suhaima da zeenat se hawaye suke yi . Cire crown din kanta tayi ta yardashi aƙasa tana cigaba da kukanta.

Unexpected sukaga wutar gidan yadauke sannan falon yayi dubu dishi_dishi kawai suke iya gani tunani suka farayi meyake faruwa suda wuta steady ne baya ta ba dauke musu , zazzakar muryanta ne yakatse musu zancen zucin dasukeyi muryanta me dadi da amo yana rera wakar " happy birthday to you! Happy birthday to you, happy birthday dear my daughter happy birthday to you" ko amarfaki sukaji wannan muryar bazasu taba mantawa dame itaba koda kuwa shekara ɗari aka dauka bazasu taba mantawa da wannan muryar ba arayuwarsu ,yau gashi sunji muryanta shin amafarki ne kokuma gizo ne , rabon da su ji muryanta shekara uku da watanni kenan. Wutar gidan ne yadawo suna tsaye awaje daya sunkasa motsawa zuciyoyinsu nacike da al ajabi da mamakin abinda sukaji , daga kai twinkle tayi ta kalli upstairs da karfi ta ce " yeeeeeeeh my mommy is here" tafada tana saukowa daga kan kujeran tanufi upstairs da gudu , maida kallonsu sukayi upstairs din da twinkle tanufa , idanunsu ne yayi arba da fanan dake saukowa ta tunkaro twinkle itama tana sanye da abaya fara sol tayi rolling din gyale akanta , suman tsaye sukayi suna binta da kallo kamar a film musamman Mr azaad da idanunshi suka ƙada sukayi jaa.

Da gudu tanufi twinkle da take kokarin haurowa upstairs din suka rungume juna fanan ta fashe da marayan kuka tana furta kalmar " am so sorry my baby girl ! am sorry mommynki yanzu ta dawo bazata sake barinki ba " ta fada tanayi mata kiss tanata kallonta tana kuka , yan dugul_dugul ɗin hannayenta tasa ta riƙe fuskar fanan tana girgiza mata kai sannan tasa hannu tana share mata hawayen fuskanta sake fashewa da kuka fanan tayi ta mayar da twinkle jikinta ta rungumeta gam tana jin dumin jikin yarta da tun ranar da ta haifeta batasake ganinta ba ko jin muryanta amatsayinta na uwa , wani irin sanyi ne taji yana ratsata yana shiga dukkan sassan jikinta maida kallonta tayi kan Mr azaad da ya kafeta da rinannun idonshi yana kallonta kamar a mafarki, twinkle dake manne ajikinta ne ta ce " mommy dama nasan yau zakizo birthday dina, I love you mommy" murmushi fanan tayi da muryan kuka ta ce " i love you too mommy's angel " raba jikinta da na twinkle tayi tana kallonta da itama ita take kallon da gudu auta ta rungumeta itama ta rungumeta atare zeenat da suhaima suka rungumesu suna kuka , hada baƙi sukayi wajan fadin " anty fanan kece dagaske kokuma gizo kikeyi mana dan Allah karki sake tafiya kibarmu " tana kuka itama ta ce " ba kizo bane zahirine nice ba wata ba" tabbas yanzu sun sake tabbatarwa da gaske ne fanan dince bawai gizo ba dagaske ita ce ta dawo rayuwarsu addu'a dasuka dade sunayi yau ga shi Allah ya amsa musu roƙonsu matsanancin farin cikin dasuka shiga baze taba misiltuwa ba duk wani bakin ciki dake zuciyarsu lokaci daya sukaji yatafi farin ciki yamaye gurbinsa, raba jikinta tayi danasu tanufi ummi dake zubda hawayen farin ciki ta rungumeta ummi ta ce " my feena nayi kewarki sosai" " nima haka ummina " tafada tana yar murmushinta dake kara mata kyau.
Shafa kanta Abba yayi ya ce " alhamdulillah Fatima munyi matukar farin ciki da dawuwarki cikin rayuwarmu " ta ce" nima haka Abba " cikin tafiyarta kamar mahauniya ta nufi inda Mr azaad yake tsaye kamar wanda aka shuka a wajen , dukkansu ido suka zuba musu suna kallon wa'yannan masoyan na haƙiƙa da labarin soyayyarsu yakai matsayin a rubuta shi a tarihin duniya , kallon cikin kwayar idon juna suke yi bako kyaftawa idonta daya cika da hawayene ya gangaro ta ce" habiby ko de bakayi farin cikin ganina bane ?" sa hannunshi yayi yajawota jikinshi ya rungumeta gam kamar ze maida ita ciki yana mayar da hawayen dasuke kokarin zubowa daga idonshi ya ce" nafi kowa farin cikin ganin ki wifey dama inada yaƙinin za ki dawo gareni bantaba loosing hope ba " murmushi tayi ta ce" karfin son da nake maka ne yadawo dani gareka dakuma son danakeyi ƴata da ahalina Allah nagode maka dayasa ban mutu ba kasake bani dama na biyu domin yin rayuwa da wa'yanda sukafi soyuwa agareni " sake rungume juna sukayi suna fadawa junansu kalamai masu dadin gaske , yaseer da Fawwaz, areef se video sukeyi musu da hotuna gwanin burgewa sosai suka burgesu kuma sunyi matukar farin cikin ganin wannan ranar arayuwarsu, ganin sun manta da suna tsaye awajen ne yasa Abba cikin zolaya yayi gyaran murya dasauri fanan taraba jikinta dana Mr azaad kunya yakamata sosai dan tsabar wutar soyayya yasa ta manta dasu Abba na tsaye awajen sunkuyar da kanta ƙasa tayi sukuwa dariya sukayi kawai Mr azaad yariko hannunta yana kallonta kwata_kwata yakasa janye idonshi akanta gani yakeyi inya dena kallonta zata sake tafiya tabarshi , Hafiz ne ya ce " yeeeeh what are we waiting for let's celebrate" aikuwa dukkansu suka sa dariya harda Mr azaad,anty amina ta ce " ahh lallai yau kam Azaad na cikin matsanancin farin ciki rabon da muga dariya akan wannan fuskantar taka tun bayan tafiyar feena" murmushi kawai yayi yana sake matse hannunta cikin nashi daukan twinkle Fawwaz yayi ya mayar da ita kan kujeran. aka bata wukar daura hannunsu Mr azaad da fanan sukayi akan nata aka yanka cake din ta yanka tabawa fanan abaki tasake yanka tabawa Mr azaad abaki duk wa'yanda ke falon seda tabawa kowa abaki haka akasha birthday party sosai suka dinga mata hotuna da bata gifts masu masifar tsada , har kan mangrib sannan suka samu aka gama ana kiran sallah mazan suka tafi masallaci matan kuma kowa yayi , fanan a bedroom din ummi tayi sallah . Bayan sun dawo ne aka shirya dinner table sukaci abinci dare sannan suka dawo falo suka zauna , sallaman ya usman sukaji tare da na mama, baba da hairah suka shigo amsawa sukayi tundaga bakin kofa mama take kallon fanan kamar a mafarki jin muryan mama ne yasa fanan ta tashi dasauri tanufi mama ta rungumeta, mama da ke hawaye ta ce " dama nasan zaki dawo gareni fanan ga shi Allah yadawomin dake nayi matuƙar kewarki sosai" ta ce " nima haka mamana ,nayi farin cikin dawuwata" karasawa cikin falon sukayi suka zauna suka gaggaisa suna taya junansu murna dawuwar fanan, suna tsaka da farin ciki sukaji sallamar me martaba da waziri se galadima ga kuma Fulani zama sukayi aka sake sabon gaisuwa , dama suhaima ita takira ya usman ta sanar dashi fanan ta dawo sannan takira yan Bauchi nan ma ta sanar dasu , Fawwaz kuma yakira me martaba yafada mishi.

Bude taro da addu'a Abba yayi , me martaba yayi ya kalli fanan dake zaune aƙasa akan carpet kanta a ƙasa ya ce " Allahu Akbar lallai babu abin bautawa da gaskiya se Allah shi kadai ,me kowa kuma me komai meyin yanda yaso ah lokacin dayaso , muna me gode mishi da yadawo mana da yarmu Fatima cikin rayuwarmu. Munyi matukar godiya da hakan kuma munyi murnar dawuwarki Fatima , kuma alhamdulillah kinje kin isar da sakonki wajan ganin bayan wa'yannan azzaluman kin ƙa war dasu adaron ƙasa Allah ne kaɗai ze biyaki domin kinyi na mijin kokarin kin taimaki rayuka da dama , lallai ke din cikakkiyar yar baiwa ce medauke da abubuwan mamaki Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki " du ka suka amsa da" Ameen ya Allah " sannan me martaba yadaura daga inda ya tsaya " Fatima zamuso ki fada mana yanda Allah yayi kika dawo domin mun san ke din kinrigada kinzama shugaba a masarautar nasminaya " duk ka sa kunne sukayi ɗan sunason suji ya akayi wannan lamari yakasance,gyara zama fanan tayi tafara basu labarin yanda akayi ta dawo " aranar da muka fita yaƙi nayi nasarar kashe su dukkansu biyu na tarwatsa kungiyar nasu , sede tanzarzar yayi galaba akaina yasokamin wukar danayi amfani dashi wajen kasheshi wannan wukar kuwa bakamar sauran wuƙaƙe yake ba yana fitarwa mutum duk wani karfi dayake jikinshi sannan seyasa maka guba ajikinka sekuma mutuwa , dasauri suka daukeni suka maidani fada aka kira ainihin wanda ya ƙirƙiri wannan wukar, shi yadingamin magani har na tsawon shekaru uku da ikon Allah se nasamu lafiya amma sede jaaazana dake cikina ya gurɓace adalilin wannan gubar dake jikin wukar , seyazamana babu wani karfin iko atare dani , ganin hakane yasa natarasu gaba dayansu afada nasanar dasu kan cewa ni yanzu babu wani irin taimako da zan iya basu amatsayina na sarauniyarsu domin narigada narasa karfina dan haka nace zanbawa yarima ahil mulkin nasminaya amma duk se suka nuna sude ahaka sunason inci gaba da mulkarsu dakyar de nasamu na nusar da su illar haka , sannan na naɗa yarima ahil amatsayin sabon sarkin nasminaya. sannan nayi musu bankwana nadawo duniyar bil'adama "

Jinjinawa wannan lamarin sukayi sude tunda abinda tajeyi ta aiwatar, su sunyi murna da dawuwarta .

Baba ya ce" tabbas baa cire rai da rahamar Allah ga shi da yardar shi kindawo garemu " haka sukayi ta murna awannan rana sun dade suna hira sannan kowa ya koma gida cike da tarin farin ciki.


Dare yayi Mr azaad yafita ɗan,tana kwance ta sa twinkle dake bacci akan makeken gadon bedroom dinta agaba tana kallonta duk suna sanye da kayan bacci, taji anbude handle din bedroom Mr azaad ne yashigo hawa gadon yayi ya ce" kina kallon twinkle din mune ?" Murmushi tayi ta ce" ehh bana gajiya da kallonta habiby " shima murmushin yayi ya ce" komai nata irin naki fuskanta, yanayin maganar ki rigimarta everything, sede surutunku ba iri daya bane na mommynta auta ta dauko " dariya sukayi atare ta ce" habiby ban taba tunanin zan dawo inci gaba da rayuwa daku ba ashe inada rabo da kasancewa da mijina da kowa nawa" sa hannu yayi yatallafo habarta ya ce" nikuma bantaba cire tsammani da damuwarki ba kullum zuciyata rayamin take komin daren dadewa kina nan zuwa gareni " yagama maganar yana ɗaukarta kamar yar baby ya ce" ina bukatarki shekaru uku ba wasa ba " dariya tayi sukafito yana dauke da ita yajawa twinkle kofa yarufe yanufi bedroom dinshi kwantar da ita yayi akan bed yayi mata rumfa da faffadar kirjinshi sannan ya hade bakinsu waje daya , wani irin hot romance suke yiwa junansu kowa na kewar dan uwansa burinsu awannan daren su gamsar da kansu domin kewar dasukayi yanada matukar yawa , cire mata kayan jikinta yayi ya cire nashi yafara sex da ita itama tana mayar mishi da martani, ina yar goge kwallar tausayinsu danaga abin nasu yanason wuce gona da iri kawai nafito narufo kofar ahankali dan kar in dakatar dasu nashige bedroom din twinkle nayi kwanciyata anan.


Rayuwa me dadi Ako wani ɓangare sukeyi cikin farin ciki da jin dadi twinkle me mommy's dayawa ga ainihin mommynta ga kuma su suhaima da zeenat, Mr azaad da fanan da twinkle, Fawwaz da suhaima da yarsu sukaje Bauchi kai musu ziyara sunyi murna sosai da ganinsu satinsu daya suka dawo domin Ramadan yakawo kai saura kwana hudu .
Haka suka gabatar da ibadar Ramadan sallah yazo akayi bikin sallah cikin nishadi da tarin farin ciki, lokacin zuwa aikin hajji nayi kuwa Mr azaad yabiyawa kowa harda su mama suka tafi suka je sukayi ibadarsu .


Bayan sundawo ne aka rabawa dangi da abokan arziki da mabukata tsara ba.

Wata rana Mr nazaune a office dinshi sakatariya

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment