Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

azaad yace gobe zaku tafi ko ? " " Eh abba haka yace " jinjina kai abba ya ce " masha Allah , Allah yakaiku lafiya " ita da zeenat suka amsa da " ameen" ajiye mishi kular awara tayi ta ce " Abba ga awara " sa hannu yayi yadauki kular awaran yabude cikin barkwanci ya ce " gaskiya Allah yataimakeni da yasa banyi bacci yanzu ba da yanzu awaras ta wuceni " sosai fanan da zeenat suke dariya dan Abba yabasu dariya shima darawa yayi ya ce " to nagode sosai kuwa Allah yayi albarka" ta amsa da ameen, zeenat ce ta marairaice ta ce " abbana nakaina dan Allah in tayaka ci?" hararan wasa yamata ya ce " iyeeeh yau naga abin al ajabi wato baƙin kine yasan dadi nawa besani ba, to aikuwa ko budewa ma bazanyi ba sekin tafi " yayi maganar yaname rufe kular , dariya fanan takeyi na drama abba da zeenat itade ji tayi babu wacce takaita saa saboda Allah yahaɗata da sirkan nai nagari masu kuma sonta kamar yarsu kowa na gidan yana matukar kaunar fanan dakuma girmamata, kullum addu'ar ta shine Allah ya bata iKon kawo farin ciki akan fuskokinsu wannan al kawarine da ta daukawa kanta bazata taba barin wannin su da bakin ciki ba inde har akwai yanda zatayi na ganin farin cikinsu yanda take kaunar familyn ta haka take kaunar su . sallama sukawa Abba suka koma part din ummi shigowa falon sukayi suka samu su fawwaz sun gama cinye nasu awaran yaseer yana ganin shigowarsu ya ce " alhamdulillah my girl gwara da Allah yadawo daku yanzu wallahi Allah ne kawai yasa kinada rabon cin wannan daddadar awaran , saboda dakyar na iya kwace kular ahannun su fawwaz wai tunda bakya nan zasuci rabin naki " yafada yana hararan su fawwaz dasuke kunshe dariya hade fuska zeenat tayi ta ce" Allah ya fawwaz da ya areef da kuncinye min awarata yau da se anyi yakin basasa " dariya fawwaz da areef sukayi Sannan suka tafa sake fusata zeenat sukayi yasa tadauki kular takoma kusa da yaseer tazauna tanaci .

fanan de seda safe tayi musu domin kuwa tasan yanzu haka Mr azaad yanacan yana jiranta harta haura upstairs setayi wani tunani ganin yanda suketa hiransu kamar basu ji labarin anty shayida nada ciki ba hakan yasa tajuyo cikin yar daga murya ta ce " albishirinku ?" dukkansu suka bata amsa da " goro " gyara tsayuwa tayi ta ce " Kuma dole sekun bani goron albirshir dina! Anty shayida tanada ciki takusa haihuwa kusata a adduah Allah yasauketa lafiya " kabbarah sukayi cike da farin ciki suka godewa Allah yanzu darabon zasuga jinin anty shayida zeenat kam harda rawa girgiza kai fanan tayi tabarsu abinta tashige nasu part din tana murmushi itama , haka sukata nishadinsu part din ummi zeenat tafada domin sanar da ita wannan labarin , har ummi tafara bacci zeenat ta tasheta tafada mata jitayi baccin ya yaye babu abinda take furtawa se kalmar alhamdulillah tashiga bedroom din anty amina nan tasamesu rungume anty shayida ummi tayi dukkansu suna farin ciki sosai ummi tadinga mata adduah sannan tabar dakin tashiga nata takira abba ta sanar shima yayi matukar murna sosai haka suka kwanta kowa na cike da farin ciki.


Samunshi tayi adaki yana kwance abinshi yayi shirin bacci cire kayan jikinta tayi tadaura towel tashiga bathroom tayi wanka tafito ta shirya jikinta sannan taje kitchen tazuba musu nasu awaran a plate tashigo hannunta dauke da plate da ruwa zama tayi ta ce " habiby kazo muci awara " yana daga kwance ya ce" wifey kici kawai ni bazan iya ci ba " yanda yayi maganar tasan kota matsa mishi ma bacin zeyi ba yasa taci abunta harta koshi tasha ruwa ta maida komai kitchen ta gyara musu zama .

Dawuwa tayi tahau gadon tashige jikinshi ta kwanta matseta yayi ajikinshi ya ce " se yanzu kenan ?" " uhmm yeap kasanme anty shayida takusa zama mother" ta sanar mishi tana sakin murmushi bata amsa yayi da sexy voice dinshi ya ce " nasani Allah yasauketa lafiya! Saura ke nakusayin ajiya anan wajan " yafada yana shafa shamulallen cikinta murmushi kawai tayi manna mata kiss a goshi yayi, ya kashe light din dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo , duk shuru sukayi kuma basuyi baccin ba dago fuskanta dake kirjinshi yayi yakalli cute face dinta ya ce " gobe 8:30am flight dinmu ze tashi " kamar me rada ta ce" Allah yakaimu habiby " ya ce " ameen " adduah yayi musu sannan kowa yayi niyar bacci suna manne da junansu.




Washe gari


Sungama shirin tafiya yar karamar trolley fanan tadauka dakyar Mr azaad yabarta tadauka nan ma yana tsaye akanta tadauki abubuwan bukata hijabs ne se abayas da kuma jallabiya nayin sallah sekuma abubuwan da anty amina da anty firdausi suka bata daukan trolley din security yayi yakai boot suka fito suma kowa ya hallara afalo fanan na sanye da doguwar rigar abaya dark blue da mayafinshi se Mr azaad dake sanye da kana nan kaya jeans da riga sunyi kyau sosai .

Har kasa fanan ta gaida kowa hade da taaziya, suka amsa cike da so da kauna mikewa sukayi domin yi musu rakiya airport amma banda ummi,abba,anty shayida,anty amina,anty zainab, masu yi musu rakiya iyakacin yaseer, zeenat, fawwaz, areef se hafiz da yau yajishi klau alhamdulillah.

motoci goma ne ke fa ke a compound din gidan suna jiransu, shiga sukayi su ummi nayi musu adduo'in tsare hanya har suka bar gidan komawa cikin gidan sukayi kowa jikinshi asanyaye yau de sunsan zasuyi kewar fanan sosai .


daga ita se habibynta Mr azaad amotar se driver dake driving dinsu tana kwance ajikinshi Mr azaad shikuma yana shafa bayanta tana bashi labari taji ringing din wayarta cirota tayi a handbag dinta ganin my dad tayi yasa tayi murmushi dama sukadai ne basuyi waya da safen ba tayi waya da su baba da mama ya usman da auta Amira ma ta kirata duk sun musu Allah yakiyaye hanya, dagawa tayi da sallama abakinta ta gaisheshi amsawa uncle kabir yayi suka gaisa yamusu adduah shima sannan yamikawa umma rahina itama suka gaisa tamusu Allah yatsare haka suhaima da ya al ameen seda suka gaisa duka sannan sukayi sallama tana kokarin ajiye wayar kiran anty firdausi yashigo itama tayi musu adduah sannan tabawa daddyn junior bayan sun kammala ta kashe kiran.
dede kunnenta Mr azaad ya ce " wow gaskiya wifey ke yar gatace kowa na sonki " fari tayi da ido ta ce " ehh mana shisa yanzu nafika fans " murmushin gefen baki kawai yayi, yasa hannu ya matse libs dinta yamatso da fuskanshi daff da nata har suna shakar daddadar kamshin turaren jikinsu da ya hade yabada kamshi me dadi da tafiya da zuciya yace " baby ai ke din ta dabance dole kifini" yagama maganar yana manna mata kiss a libs din sannan yasake ta gyara kwanciyarta tayi ajikinshi tana shakar kamshin jikinshi hade da lumshe ido, har aka iso airport basu sani ba seda sukaji tsayuwar motar , seda kowa yafito kafin yafito yabudewa fanan murfin motar tafito yarike hannunta suka fara tafiya seyanzu Mr azaad yalura da yan jaridun dasuke wajan tun fitowarsu akeyi musu videos da hotuna hankalin al'ummar airport din duk yadawo kansu ganin wannan shahararren dan kasuwan nan ne tare da matarshi bakaramin burge jamaa sukayi ba kowa se fatan alkhari suke musu wasu na burin Allah yabasu masoya irin Mr azaad, duk yanda sukaso suyi magana da Mr azaad bayuba ko kallon su beyiba jin anfara kiran sunaye yasa suka rungumi juna shida yaseer akunne yaseer ya ce " dude karka yarda ku dawo baku samo mana baby ba " dukan kirjin yaseer Mr azaad yayi Yana fadin" seka hanamu dawuwa ai dan iska " dariya yaseer yayi yace"waneni " haka sukayi bankwana dasu gaba daya suka fara hawa matattakalar jirgin suna daga musu hannu harsuka shige , direct Vip Mr azaad da fanan suka shiga sukadai ne awajan bakowa a vip zama fanan tayi Mr azaad yadaura mata belt , fara tafiya jirgi yayi yana kokarin tashi runtse ido fanan tayi sosai Mr azaad yariketa dan yaga yanda ta tsorata saboda wannan shine karonta na farko hawan jirgi shisa duk tabi ta rikice . duk ta galabaita harwani jin tashin zuciya takeyi kamar zatayi amai yana rungume da ita ajikinshi ahaka hartayi bacci.




19:00pm dede jirginsu yayi landing a Denver international airport , wato karfe 7 nadare kenan alokacin Nigeria duk dacewa akwai tazaran 7hours tsakanin Nigeria da USA . kallon fanan yayi da take bacci duk tayi laushi sau biyu tana amai ƙunce mata seat belt dinta yayi sannan yadauketa cak yafara taka staircase din jirgin hasken da airport din ke dashi tako ina yatashi fanan daga bacci tabude idonta tana karewa airport din kallo , kamar rana kowa se sabgar gabanshi yakeyi airport din kanshi abin kallo ne komai nawajan medaukan hankali.

Wasu jibga_jingar motoci guda hudu sukazo daukar Mr azaad and Mrs azaad kuma dukkansu turawa ne sanye da bakaken suits , har suka sauko daga jirgin fanan bata sani ba hankalinta na kan airport dan ya burgeta sosai , cikin girmamawa turawan nan suke gaishesu beko kallesu ba daya daga cikinsu yabude musu murfin motar tsakiya Mr azaad yashiga dauke da fanan a hannunshi kwantar da ita yayi akan seat yadaura kanta akan cinyar shi shafa fuskanta yayi ya ce " sannu ko wifey munkusa isa gida " da muryanta da baya fita ta ce " to habiby" tafiya sukeyi akan titi slowly kamar wayanda suka dauko sarki ko shugaban kasa har suka iso wani hadedden waje me matukar girman gaske wani katon sign bot kamar tv yana fitar da rubutu da colors kala_kala yana rubuta ' welcome to las Vegas ' babban birnin las Vegas kenan dake cikin kasar america .

Horn sukayi a tangamemen gida masu gadi suka bude aljannar duniyar gidan daya kasance daya daga cikin manyan gidaje a las Vegas komai na more rayuwa akwaishi awannan gidan akashe masa daula iya daula,gidan da ya yakasance mallakin Mr azaad, bude musu gate akayi suka shiga fanan kamar bakauyiya haka takoma domin gidansu Mr azaad na Nigeria bekai wannan kyau ba dukda cewa shima dankararriyar gida amma wannan ya hadu iya haduwa aikunsan banbancin gidajen turai dana gida Najeriya, tsayawa fada muku kyaun gidan ɓa ta ɓaki ne buɗe musu motar akayi yafito dauke da ita ahannunshi, turawa dake aiki a gidan se ɗiban gaisuwa sukeyi haka yashiga da ita cikin gidan kai tsaye wani ƙayitatciyar bedroom yashiga ya kwantar da ita akan makeken gado, luf tayi tana kallonshi daga mata gira yayi alamar tambaya girgiza kai tayi , dukunkune jikinta tayi waje daya saboda sanyi da takeji ganin haka yasa Mr azaad kashe ac sannan ya rufa mata bargo , kayan jikinshi ya cire yashiga toilet yayi wanka da alwala,yafito yasamu harta fara bacci batare da yasa kaya ba yana ɗaure da towel yahau kan makekiyar gadon , yaye bargon yayi yaɗagota yafara cire mata kayan jikinta , bacci ne a idonta duk abinda yakeyi tanajinshi amma takasa koda bude idonta ne haka yadauketa yashiga toilet da ita yamata wanka da ruwan zafi tayi alwala sannan yanaɗota a towel yakwantar da ita akan gadon sosai taji dadin jikinta.

Kitchen din dake cikin part din yashiga ya haɗa mata cornflakes yakawo mata hartayi nisa abacci babu yanda ya iya dole seya tasheta tasa wani abu acikinta baze barta ta kwanta haka ba zama yayi agefenta ya ce " wifey kitashi kisha cornflakes seki koma baccin " tana jinshi sama_sama hakan yasa ta make kafada tare da turo mishi dan karamin baƙinta , murmushi yayi yasa hannu yadagota zama tayi tana marairaicewa kamar wacce tasha maganin bacci dakyar ta iya cewa " habiiiiibyyyyy kabarrrrni inyiiiiiii bacciiiii " yanda take jan maganar nata seda yaji tsigan jikinshi yatashi musamman yanda takira shi se dayaji har cikin ranshi , fa ra bata yayi abaki harta shanye duka batama san tashanye ba kwanciya take kokarin yi yarikota ya ce " ki bari muyi sallah seki kwanta" dressing room yashiga yadauko mata wandon da riga na bacci masu kauri se katon jacket din rigar sanyi domin ana sanyi sosai bude trolley dinta yayi yafito mata da hijab , shima jallabiya yasaka , sannan yadawo bedroom din, sa mata kayan yayi ya shimfida musu sallaya jansu yayi sukayi sallolin da ake binsu bayan sun idar tayi addu'a ta haye gado ta kwanta se bacci murmushi kawai Mr azaad yayi shima agajiyen yake hakan yasa yakashe wutar dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo hade da musu addu'a bacci .



To sekuma gobe inme duka yakaimu da rai da lafiya .



Waiting for your comments and share fisabilillahi 🙏.
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹
( Yar lelen Jarumai)





🔔📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATION 📚📚

⚜️📚 J. W. A 📚🖋️




Gargadi....
Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowani siga ko a karanta minshi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin kuma yabimin hakkina.




PAGE 6️⃣0️⃣




NIGERIA


Adamawa Yola


Shigowa lukman yayi yadawo daga office yasamu nusaiba zaune tana chatting dinta hankali kwance tanajin shigowar shi amma ko dago kai batayi ta kalleshi ba balle yasa ran zatace mishi sannu da dawuwa girgiza kai yayi kawai yana mata fatan shiriya domin tunda akayi aurensu yake fuskantar bacin rai daga wajan nusaiba betaba ce mata uffan ba balle yabiye mata haka zata tsaya ta mishi rashin kunya iya isarta ko kadan bata ganin girmanshi ta renashi ga tsanar datayi mishi tunda akayi auren wani abu be taba shiga tsakaninsu ba a matsayin miji da mata , bata daga tsinke bata da aikinyi se chatting da kawayenta ko girki bata tabayi mishi ba kullum a restaurant yakecin abinci duk da akwai me aiki agidan amma nusaiba tahanata shiga mata kitchen bakomai ne yayi tasiri awajan nusaiba ba fa ce huɗubar da mahaifiyarta madina tayi mata.

wanka yayi yafito yazauna afalon har lokacin tana nan a inda yabarta bata motsa ba se hira takeyi da kawayenta a whatsApp, zuba mata ido yayi yana kallonta kamar wani me nazarin wani abu wata uwar harara nusaiba ta watsa mishi lokacin da ta ankara yana kallonta sannan ta ce " meye haka ? Kazo kawani sani agaba kana kallo mtsssw " ta gama maganar hade da jan doguwar tsaki kamar wacce take magana da sa'anta, ran lukman yabaci sosai da tsakin dataja mishi ya ce " nusaiba ni kika jawa tsaki?" Kallon tara saura takwas tayi mishi tana ƙaɗa kafa ta ce" ehh kai nayiwa wannan tsakin lukman! nace kai nayiwa kadau mataki , inka isa cikekken namiji ka sakeni mara zuciya kawai " murmushi me ciwo lukman yayi kafin ya ce" nusaiba kenan kice gaba da barin duniya tana ruɗarki da kuma hure miki kunne duk abinda zakiyi sede kiyi amma bazan taba sakin kiba wannan alkawarine nadaukawa kawu , amma kisani nikaina bawai kaunarki nakeyi ba kawai de so ne na yan uwantaka bayanshi babu komai araina , tun yanzu Yakamata kizubar da mukaman yakinki ki karbi wannan auren namu hannu bibbiyu tun kafin lokaci yakure miki " duk maganar dayakeyi mata nan cikin sanyin murya yakeyinsa dukda kuwa ranshi abace yake lukman yana da sanyin hali sosai , haka yatashi yabarta a falon tana cika tana batsewa , gani takeyi babu wanda aka cuta sama da ita za'a aura mata lukman ita ai ba sanshi takeyi ba kuma dole taci gaba da yi mishi abinda Madina take fada mata domin ta wannan Hanyar ce kadai zasu samu ya saketa.




Yau de Allah yayi dare gari ya waye se yau Mr azaad yabawa su spider umarnin ƙyale alh Ibrahim tijjani su da kansu suka fitar dashi wajan gari suka hankaɗoshi waje yafadi aƙasa timm kamar wani kayan wanki, duk yabi ya yamutse yafita a hayyacinshi ya canza kamanin wannan tumbin nan nashi duk seda ya sa ce dan baƙar azaban dayasha tabbas yaji jiki bana wasa ba, dede da yatsun hannunshi dakyar yake iya dagawa fuskan nan ya kumbura sumtum ya tara jini musamman idonshi , yana yashe akan hanya motar ambulance yazo suka dauke shi suka wuce asibiti dashi .



_____ jikinta na matukar rawa take magana tana nunashi da yar yatsa ta ce " bazeyuba ! baze taba yiwuwa ba ka cuceni ! in kyaleka? baka isaba kayi kadan amjad" wanda takira da suna amjad yana zaune yazuba mata ido hankalinshi kwance ya ce " keee aneesa karki yarda kice zaki nunamin akuyanci koɗan kinga nayi shuru na ƙyaleki ne ? Ni bance kin cuceni ba se kece zakice na cuceki" aneesa dake tsaye a kanshi tana huce idonta yayi ja sosai duk alamu sun nuna kuka tasha ta koshi ta nunashi da yatsa tana fadin " kayi kaɗan ka shafamin cuta sannan ka hanani magana HIV positive fah nagani toma dakake cewa bakai ka shafamin ba agidan ubanwa nasamu to? iyeeh nace agidan ubanwa nasamu inbakai kasamun ba?" murmushi yayi irin nasu na gogaggun yan duniya yabata amsa da " ai badani kadai kike yawon tazubar ɗinki ba , waye besan ke karuwa bace zaki zo ki dameni kina cemin nina shafa miki HIV kije can kinemo sauran abokan holewarki " kukan kura aneesa tayi ta cukumi kwalar rigar amjad afusace ta ce " amjad nikake fadawa haka halaccin dazakamin kenan , kaine na mijin daya fara amfani dani a matsayin virgin , kyautar budurcina fah nayi maka amma yau kaine kake cewa wai ai bakai kadai kake amfani dani ba , to naji bakai kadai bane amma ai kasani kai da ya ne kake sex dani batare da condom ba kaga kuwa dole kaine ka shafamin HIV " fincike hannunta daga kan rigarshi yayi ya ce " karamar yar iska kema yanzu da kanki kinfada ai bani daya kike sex ba to wallahi nasakejin kince nine nashafa miki HIV ranki se yayi mugun ɓaci "
Azafafe tadau handbag dinta da wayoyinta tafita a hotel room din tana me danasanin sanin amjad a rayuwar ta.





SATANIC

Duk suna tsaye sunyi shuru suna jiran suji abinda shugabansu tanzarzar zece shikuwa yana hakimce akan kujeran mulkinsa cikin murya me amo ya soma magana " hafsat ta kasance daya daga cikin mu, babba me muƙami ce , amma mutuwar nata shine dede agareku domin zata iya tona muku asiri yanzu amanta da babinta, lokaci kara kurewa yakeyi inason yanzu nan da wani lokaci ƙalilan zamuyi sacrifice (sadaukarwa)mata masu ciki da kuma jarirai sekuma mata masu jego duk wani asibiti dayake cikin wannan gari dole ashiga akashesu wannan shine babban sadaukarwar dazamuyi wanda tun bayan shekara ɗari ba'a ƙara yi ba , idan muka yi shi ze taimaka mana wajan samun sarauniyar nasminaya, nan da yan watanni zaayishi .
Akalla muna bukatar masu ciki guda dari se jarirai maza da mata guda hamsin se masu jego hamsin doleeeeee ayi wannan sadaukarwar " yagama magana cikin sake tabbatar musu da hakan ze faru bayan sun gama tattaunawa yabawa kowa izinin tafiya nan da nan suka zama jemage suka ɓace.



U S A

LAS VEGAS ✈️






Gjiyar da sukayi ne yasa tunda sukayi sallah asuba suka koma bacci basu tashi ba har se wuraren karfe 11 na safe kafin suka tashi sukayi wanka, sukayi breakfast sannan suka fito ze nuna mata gidan suna sanye da riga iri daya tshirt se wando jeans tasa hula akanta suna rike da hannun juna suke ta zagaye gidan duk inda suka wuce se ma'aikatan gidan sun gaishe su ita ce ma take amsawa amma Mr azaad ba amsa musu yakeyi ba babban garden din gidan suka shiga dayasha furanni kala da iri wajan ya matukar kayatarwa fito da wayarsa yayi yafara daukanta hotuna sannan yamusu selfie sunyi kyau sosai sun dan jima a garden din suna hiransu gwanin sha'awa kafin suka bar garden sukaje swimming pool yana da girma shima ya haɗu sosai yanda ruwan yake blue in color ne ya burge fanan yasa ta ɗan sunkuya tasa hannunta acikin ruwan tana wasa dashi tana dariya , Mr azaad na gefe yana mata video batare da tasani ba kiran sunanta yayi tadago ta kalleshi ya ce " baby ko zaki shigane " girgiza kai tayi ta ce " noo habiby ai ban iyaba " " yau zanfita meeting dana koya miki amma zan koya miki ko wani lokaci" cewar Mr azaad daya iso inda take yasa hannu yadagota suka koma kan kujerun da suke wajan swimming pool din suka zauna call ne yashigo wayarshi sunan Abba ne yabayyana picking yayi sukayi waya yamusu ya gajiya sannan ya ce yabawa fanan karba tayi sukayi waya da Abba dake falo tare da duk wani dan gidan haka seda suka gaisa dakowa cike da farin ciki sannan sukayi sallama , kiran layin baba Mr azaad yayi yagaisheshi sosai baba yamusu sannu da hanya nan ma seda suka gaisa da duk yan gidan , sun jima awajan suna hira kafin suka koma cikin gida.
Haka rayuwar su taci gaba cike da soyayyar juna da jindadi , haka yan gida Nijeriya kullum sesunyi waya dasu harda video call, ranar da ummi takira Mr azaad yana office sukayi waya dama tun zuwansu takeson fada mishi magana ɗan gane da fanan ta ce " son please ka kula da feena sosai sannan la kaita asibiti amata pregnancy test domin ni naga kamar akwai ciki atare da ita " murmushi Mr azaad yayi shima yayi experiencing hakan amma da sukaje asibiti se yazama ba haka bane ya ce " ummina nima nayi tunanin hakan amma kafin muzo seda mukaje hospital aka mata test babu ciki ajikinta" jinjina kai ummi tayi sannan ta ce " to Allah yakawo babban rabo " ya amsa mata da ameen sannan sukayi sallama.



AFTER TWO MONTHS



yau watan su fanan biyu dazuwa USA kuma haka zalika watansu biyar dayin aure
, Shakuwa me karfin gaske yasake shiga tsakani Mr azaad da fanan wani irin narƙekkiyar da kuma zazzafar soyayya suke nunawa junansu hankalinsu kwance duk sanda yadawo daga office haka ze dauketa sufita yawa wajaje daban_daban , alhamdulillah Mr azaad ya gama meeting dakuma aikin daya kawoshi , sannan ummi tafara mishi maganar dawuwarsu saboda auren amare da angwaye saura sati uku anata shirye-shiryen biki sannan tasake tuna mishi maganar tsayawar da zasuyi a dubai kamar yanda tafada mishi kafin su tafi .

Bacci yake son yi amma fanan ta hana shi tana zaune akan cikinshi ta cusa hannunta acikin gashin kanshi tana mishi tafiyar tsutsa ranƙwafo da kanta tayi dede kunne shi kamar raɗa zata mishi da karfi ta ce " habibyyyyyy ! Katashi muje shan ice cream din" runtse ido Mr azaad dan sautin muryanta data ɗaga seda yakusa kashe mishi dodon kunne yau tunda ta tashi take mishi rigima akan ice cream kuma ya ce zeyi order akawo mata har gida ta ce ah ah sede suje su siyo .

Juyawa yayi da ita tadawo ƙasanshi ya mata rumfa da faffadar kirjinshi daɓe sanya riga ba ga kwantaccen gashin kirjinshi dasuke ƙara mishi kyau kallonta yayi da rinannun idonshi da suke cike da bacci a cikinsu ya ce " haba wifey yanzu baccin ma bazanyi in peace ba " fiki_fiki tayi da ido kamar wacce batada gaskiya ta ce " nide Allah barakayi baccin nan ba semunje mundawo " zuba mata ido yayi yana kallon yanda take motsa dan karamin baƙinta dayasha libstick se sheƙi yakeyi dawo

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment