Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadi da yaji ta samata sannan tasawa Mr azaad dakin ta koma ta ajiye mishi nashi agabanshi tace" oya kaci kaima " sa pillow tayi ta gyarawa fanan din tadan zauna kadan ta fara bata abaki harta koshi , shima Mr azaad yaci amma bawani sosai ba duk hankalinshi na kan fanan da takeci kadan kadan tana yamutsa fuska magani anty amina ta bare ta mika mata kin kallonsu tayi dama tunda yaga an balla magani yasan zaa rina tasowa yayi daga inda yake zaune yazo yakarbi maganin a hannunta yasasu a cikin glass cup ya jiqasu suka narke yabata tasha dakyar tana qaqarin amai lallabata yayi harta dena yunkurin amai din anty amina komawa gefe tayi tana kallonsu sunyi matukar burgeta bugu da kari sun dace da juna musamman yanda Mr azaad yake tarerayan fanan .

drip din karfe 7 nadare ya kare shi yacire mata yadauketa yakaita toilet yamata wanka yakara gasa mata jiki da ruwan zafi tayi alwala,ya nadota a towel kamar wata jaririya kayan bacci yasamata sannan yabata doguwar hijab ya shinfida mata sallaya daga zaune ta rama sallalolin da ake binta . zeenat ce tayi knocking yabata izinin shigowa basket ne a hannunta hade da flask zama tayi akan kujera tace " anty fanan sannu ya jikin ?" " da sauki zeenat ya ummi yau kwata_kwata banje wajanta ba " cewar fanan tana zaune akan sallayar bata tashi ba bude flask din yayi dake dauke da lafiyayyar kunun gyada ummi ce ta hada mata shi da kanta mika mata cup yayi takarba ta kai baki dadi ne yaratsata batasan lokacin da ta shanye ta mika mishi cup ya kara mata ba, zuba mata yayi yabata zeenat ce tace " anty fanan ashe kema kinason kunu ? ummi ce ta miki da kanta" " laah da gaske ummi ce tamin?" cewar fanan dake shan kunun , shide Mr azaad surutun zeenat ya isheshi, fanan seda ta shanye kofi uku kafin taji ta koshi , gyara zama zeenat tayi tace " anty fanan amma meye yake damunki ?" daka mata tsawa Mr azaad yayi yace " tashi ki fita ina ruwanki da abinda yake damunta " tun kafin yagama magana zeenat ta fita da gudu , kunshe dariya fanan tayi tana girgiza kai hararan wasa Mr azaad yamata yace " ke ko ?" Kokarin tashi tayi zata hau kan gado tasa kara zata fadi ya riketa dan ita tamanta akwai ciwo ajikinta kwantar da ita yayi akan bed din yana mata sannu , turo baki gaba tayi tace " nide bazanyi hakurin ba se kamin tausa " nade hannun jallabiyarsa yayi yace " ni awa ai dolena inyi abinda baby takeso " mammatsa mata jiki yafara yana mata tausan tailan hhhh tsabar dadin tausan har tayi bacci.



Bakin hayaki ne yake tashi acikin wata kungurum din kogo da girmanshi baze misaltu ba duk suna sanye da bakaken kaya jikinsu duk gashi yan kungiyar satanic kenan , tanzarzar na zaune akan kujeran mulkinsa su kuma yan kungiyar sunyi circle ga yara da manya dasuke kwance amace kusan rai goma an sare musu kawunan su jini nata zuba a acikin manyan kwarya seda yacikasu dam tukun, na hannun daman tanzarzar yamike yaje gaban jinin yafara wasu surkullenshi da sambatu irin nasu na matsafa walkiya ne ya bayyana akan kwaryar jinin , yasa wata karamar kwarya ya dibo jinin aciki yakai bakinsu yafara sha kamar Wanda yasamu ruwa , mommy ce second haka suka shanye jinin duka tanzarzar na zaune akan kujera yana sakin yar iskar murmushi da wannan muryar tashi mara dadin ji yafara magana " sadaukarwa ya kammala kowa yafadi bukatar shi da yakeso ayi mishi " matsowa kusa mommy tayi tace " ya shugaba nasan kasan abinda akamin an kashemin dana! da yardar ka ina bukatar daukar fansa akanta " bushewa da mugun dariya tanzarzar yayi yace " nasan da hakan amma kisani ke kika fara takalar yaki tsakaninmu da vampires union, duk hurdar mu bama shiga harkan wayanda ba yan kungiyar mu ba amma ke kika kashe musu har mutane uku. yanzu gashi seda sukayi sanadiyar rayuwar danki sannan wacce zaki dau fansar akanta tana dauke da jinin sarauniyar nasminaya duk abinda zaki mata baze tabayin aiki ba ki bari nan gaba inmun shafe tarihin ita sarauniyar tasu semu dawo kansu " durkusawa tayi kafin ta koma wajan tsayuwarta , alh Ibrahim tijjani mahaifin aneesa ne yafito yace " ya shugaba nikuma so nakeyi in kashe azaad muhammad mainasara bayan ya auri yata aneesa " sake bushewa da wata dariyar tanzarzar yayi yace " kar wanda ya sakemin maganan da yashafi wayanda suke tare da sarauniya domin muddin tana raye bazata bari a cutar da wani nata ba so nakeyi in kwace jaaazana atare da ita sannan in aureta ! muddin mukayi nasara akansu dole sena maida ita baiwata sannan in aureta in kashe mijin nata hhhhhhhhhhh" ya gama maganar yana wata muguwar dariya , cikin tsawa dayasa kogon girgiza yace " duk ku bace kuban waje " jinjina mishi sukayi kafin dukkansu suka koma jemage suka fire sama .

Adamawa Yola agidan alh badamasi me ruwa.


Duk ya tara iyalanshi a falo yana zaune yana girgiza kafa ga nusaiba a zaune akasa kan carpet bude taro yayi da adduah yafara da " nusaiba nasan kinsan dan ke na shirya wannan zaman kinason ki nuna min ni ban isa dake ba ! Kin na ce akan azaad mainasara ya nuna baya raayinki amma ke kinqi fahimta na hadaki da dan uwanki dayake sonki nanma kinqi to bari kiji kar insake jin kinje mainasara family kin tayar musu da rigima tunda yanzu yariga da yayi auranshi kuma magana ta karshe nariga da na miki miji ko kinaso ko bakyaso dan uwanki lukman zaki aura" tashi tsaye madina tayi ta tsaya tana rike kugu " baa isa ba! Baa isa ayiwa yata auran dole ba , bazaku kashemin itaba ku cuceni yauwa " taja hannun nusaiba fuuuu suka bar falon girgiza kai alh nasir yayi mahaifin lukman din , hajiya Hussaina de bata da bakin magana tunda alh yagama fadar abinda ze fada, haka zalika alh me ruwa be sake cewa komai ba abinda yasani de shine muddin madina tayi kokarin tarwatsa wannan auren ze dau mummunar mataki akanta .


" auta zoki kaiwa yayanku abincinshi daki nasan yana nan yana bacci be tashi ba " cewar mama da ta gama zubawa kowa abinci tunda akayi wannar case din na tsakanin ya usman da khairaty yadena shiga cikin mutane ko kasuwa ba wani zuwa yakeyi ba yarame yayi baki kamar ba ya usman ba babu yanda basuyi dan ya sake amma abu yaci tura harsuka gaji suka zuba mishi ido koda ya al ameen yaje dan yamishi hira haka zeyi shuru ya barshi harya gaji yayi shuru haka suka zubamai ido kawai kuma tundaga wannan ranar be sake ganin koda me kama da khairaty ba , shigowa dakin auta tayi hannunta na rike da kulan abincin shi wata razananniyar kara tasa da gudun gaske suka shigo dakin nashi cikin tashin hankali dan karan da auta tayi ta firgitasu kwance suka samu ya usman acikin aman jinin da yayi asume innalillahi wainna ilaijiraji unnn kawai suke iya furtawa daukanshi ya al ameen yayi yasashi a mota shida suhaima da auta baba kuma shida mama basu tsaya ako ina ba se a medical center na cikin garin gombe admitting dinshi sukayi a emergency , taimakon gaggawa suka fara bashi kusan bayan 1 hour suka fito suna goge zufa tasowa sukayi suna tambayarsu ya jikin nashi kallon baba da ya al ameen doctor yayi yace " ku biyoni office" yayi gaba suka bi bayanshi duk sun matsu suji me ze fada zama sukayi doctor yacire glass din idonshi yafara magana " am ranka yadade kuyi hakuri da abinda zan fada muku! dan ku gaskiya yana cikin wani halin rayuwa ko mutuwa duk da ranshi baa hannunmu yake ba amma a halin dayake ciki yanzu tabbas inbe samu abinda yakeso ba zaa iya rasa shi domin yakamu da ciwon zuciya kuma saura kadan ya buga , a shawarce kafin nan da awa 2 ku gaggawar samo mishi abinda yakeso saboda inya tashi yayi arba dashi ko hakan ze taimaka amma in ba haka ba yana cikin danger" tunda doctor yafara magana baba da ya al ameen suke zufa kamar wanda aka watsawa ruwa sun jike tashin hankali da baa sa mishi rana yanzu tayaya zasu fara wannan kwamachalan hada aljan da mutum .







via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹



πŸ””πŸ“š JARUMAI WRITERS ASSOCIATION πŸ“š

( J. W. A πŸ“šπŸ“šπŸ“š)





PAGE 5️⃣1️⃣ & 5️⃣2️⃣


Damuwa iya damuwa su baba sun shiga fadawa su mama yayi suma hankalinsu inyayi million seda yatashi duk sun shiga tashin hankali sun kasa tsaye sun kasa zaune yanzu me sukasan zasuyiwa ya usman ko giyar wake suka sha de babu yanda zaa hada aljan da bil adama, matsawa suhaima tayi awajansu ta kira layin fanan , fanan na manne ajikin mijinta suna bacci kadan kadan takejin kamar ringing din wayarta idonta arufe ta dauka tasa akunne tace " assalamualaikum" amsawa suhaima tayi tana " fanan ya usman ba lafiya yanzu muka kawo shi asibiti yana aman jini" duk baccin dake idonta lokaci daya ya kaurace mata ta zauna cikin damuwa tace " innalillahi wainna ilaijiraji unnn! suhaima meyake damun ya Usman din ?" Abangaren suhaima ta bata amsa da " doctor's sunce yanada ciwon zuciya kuma daf yake da bugawa inde baa samo mishi abinda yakeso ba " da karfin gaske kirjin fanan yake bugawa taya sukasan zasu fara wannan kwamachalan , jin maganar ta ne yatashi Mr azaad daga bacci kallo daya yamata ya gane akwai abinda yake faruwa sa hannu yayi ya karbi wayar yasa akunne yaji muryan suhaima tambayar ta yayi meyake faruwa suhaima kamar wata yar jarida ko hadiye yawo batayi se jero mishi jawabi takeyi , sosai lamarin ya girgiza shi jin usman harda aman jini katse Kiran yayi yatashi yasa jallabiya yadau car key dinshi kallonshi fanan tayi kafin tace " habiby ina zakaje da wannan tsohon daren?" dawuwa yayi inda take ya manna mata kiss a kumatu yace " asibitin zanje zanturo miki zeenat ta tayaki bacci" langwabe kai tayi tace " ayyah habiby am zan bika" girgiza mata kai yayi kawai yafice adakin part din ummi yaje ya ma zeenat knocking tasowa tayi tabude dakin tana mustsuka idonta, waro ido tayi ganin mr azaad a bakin bedroom dinta a irin wannan lokacin 12:58am nadare " kije ki taya antynki kwana zanje asibiti " abinda yace mata kenan yafice securities biyu ne suka rakashi har asibitin a zaune yasamesu duk sunyi cirko_cirko suna neman mafita gaishesu yayi ya zauna akusa da baba sukaci gaba da maganar lallai gaskiya lamarin usman akwai rudarwa yanzu mafita kawai suke nema haka suka kwana bakin ward din auta ce kawai tayi bacci sukam sun gagarayin bacci sakamakon jikin ya usman daya tashi numfashinshi yana sama yana kasa idonshi ya sauya kala duk sunyi tsammanin fitan rai ne dan abinda yakeyi kamar wanda zewuce lokaci dayane duk suna waje suna ta mishi adduah likitoci kusan shida sun hadu akanshi domin ceto rayuwarshi , family mainasara ne suka shigo asibitin securities na rike da basket na abinci, ciki kuwa harda fanan da ta nace se ta bisu taga jikin dan uwanta dan yanda take tafiya ma mutum ya lura yasan something is fishy haka de anty amina ce take rike da ita kuma ta daure sosai tana tafiya dede dakyar saboda batason kowa ya fahimci wani abu, anty amina tana rike da ita suka shigo zaunar da ita anty amina tayi suka gaisa da mama da mutanen wajen , Mr azaad beji dadin zuwan da akayi da itaba dan yasan wahala kawai takesha daurewa takeyi saboda irin karfin halinta , ummi na tare da maman tana kwantar mata da hankali, fitowa likitocin sukayi dukansu sukayo kansu suna tambayarsu ko anyi dace daya daga cikin likitocin ne yace " a yanzu de munyi nasarar dedeta numfashinsa da bugun zuciyarshi amma zuwa anjuma kuma duk abinda ya biyo baya muqaddarine daga Allah"jikinsu yayi sanyi sosai babu abinda sukeyi se adduah samun sauki dasuke yiwa ya usman, fanan tayi tagumi tana cikin tsaka me wuya yanzu bata da wani solution inde tayi sanya akan al amarin zata iya rasa dan uwanta na jini mafi soyuwa agareta , wani tunani tayi na meze hana ta mantar dashi komai wata zuciyar tace mata" hakan bazeyuba inde ya manta komai zezama yamanta da kowa dake cikin rayuwarshi hatta shikanshi se yamanta dashi wanene" kallon su mama tayi taga yanda duk suka shiga cikin damuwa aranta tace" yah Allah kadubi wannan bawan naka ka sassauta mishi abinda yake damunshi ka kawo mishi mafita kabashi lafiya" wayar Mr azaad ne yayi ringing yaduba yaga abba ne picking yayi yace " hello abba" abangaren abba ne yake tambayarshi ya jikin usman din yabashi amsa dasauki mikawa baba wayar Mr azaad yayi suka fara magana .
Suna ahaka aka fito da ya usman dake kwance rai a hannun Allah akan gadon marasa lafiya nurse's suna turawa zuwa resting room, wani ward babba shi kadai aka kaishi sannan nurse tace musu " zaku iya shiga " duk shiga sukayi, sukayi shuru , ahankali yabude bakinshi yafara magana jini na fitowa abakinshi yace " khairat karki barni kinji wallahi inasonki" sa tissue ya al ameen yayi ya goge jinin dake fita abakinshi, duk tagumi sukayi sun rasa abinyi , ware idonshi yayi yafara bin yan dakin da kallo kokarin tashi yafara dasauri ya al ameen ya gyara mishi pillow ya zaunar dashi , duk se ya jiki suke mai baya iya ce musu uhmmm balle uhmm uhmmm , se kawai kallonsu yakeyi kamar be sansu din suwaye ba doctor ne yadawo yana mishi preking din drip din .
Dukan kofar dakin ward din akeyi kamar zaa fasa shi dan tsaki doctor yayi yace" ko su waye haka oho kilama wasu daga cikin yan sakatiri ne " mikewa fawwaz yayi ya bude kofar wata matashiyar budurwa ce wacce bazata wuce shekara 16 ba a duniya kayan jikinta duk ya kode yafita a hayyacin sa kodadden hijab dinta har kasa tasa hannu da hijab dinta ta kare fuskarta tana kuka tashigo dakin duk juyowa sukayi suna kallonta , cikin siririyar muryanta tace " doctor dan Allah kazo ka dubamin Yayana karya mutu ya barni " ji yayi kirjinshi na bugawa da mugun karfi muryanta seda yaratsa dukkan wani sassar jikinsa zabura ya usman yayi jin muryan da be taba tunanin jiba ganin ya zabura ne yasa suka rirriko shi sunyi tunanin wani abunne yasa meshi ko kuma ciwon ne , dirkowa yayi daga kan gadon ya tsaya agaban yarinyar hannunshi yasa ya cire hijab din da ta rufe fuskanta dashi ja baya yayi yana furta "khairatyyy" da karfi , kallonsu suka maida kan ita yarinyar bakaramin girgiza sukayi ba ganin sak me kama da khairaty babu abinda ya rabasu sede ita komai nata normal ne saboda ita bil adama ce itakuma khairatyyy komai nata over mikewa sukayi tsaye suna al ajabin wannan iKon Allah , bata ko kalle ya usman da yake mata magana ba taje ta zube guiwanta akasa ta kama kafar doctor tana " doctor dan Allah ! dan annabi kamar yanda Allah yarufa maka asiri ka taimakemu mudin narayu ne, ka cece rayuwan yayana ze mutu wallahi duk duniya shi kadai ne gata na bamuda kowa kayi hakuri kaje ka dubashi" ta gama magana tana sheshekar kuka sude kawai ido suka zuba mata tausayinta ya darsu aransu ganin yar karamar yarinya da ita me kananun shekaru tana irin wannan rokon tabbas suna cikin mawuyacin hali, without thinking twice ya usman ya dagota yana kallon cikin manyan idonta da suka kasance brown masu daukan hankali yace " fadamin meya sami yayan naki ?" Share hawayen fuskanta tayi tace" bashida lafiya ne yanzu kuma dakyar yake numfashi dan Allah ku taimakamin kucewa likitocin nan su dubashi, in yayana ya mutu nima mutuwa zanyi " girgiza kai ya usman yayi yace " my girl bazaki mutu ba babu abinda ze sameki da shidin ! In kika mutu nima mutuwa zanyi" gyada mishi kai kawai yarinyar tayi dan bata gane inda zancen nashi ya dosaba , riko hannunta yayi suka fita a dakin shida ita sukayi dakin da yayan nata yake.
Duk zuru sukayi suna kallon ikon god daga su har doctor bin bayansu sukayi da kallo ganin lokaci daya ya usman ya watsake kamar bashine bashi da lafiya ba yana kwance harda su aman jini amma lokaci daya yakoma rass dashi harda jan hannunta sukayi waje , kallonsu doctor yayi yace " dama itace abinda yakeso kenan ?" Yar dariya sukayi suka amsa mishi da "ehh " kawai dan basusan amsar da zasu bashi ba , dariya yayi yace " soyayya kenan to Allah yabasu zaman lafiya" Ameen suka amsa shikuma yafita yabi bayan ya usman da yarinyar, sude ganin abun sukeyi kamar almara duk da ance dama kowa yanada me kama dashi guda bakwai amma ai khairaty ba mutum bace taya akayi sukayi kama da wannar yarinyar to basuda me basu amsa yasa suma sukayi dakin da yayan nata yake kwance, tunda wanda suke jinyar yayi waje ya barsu suma suka fito, suhaima ce tace " ohhh su ya usman abin nema yasamu " dariya zeenat da fanan sukayi harara fawwaz yamusu na wasa yace " kude Allah yashiryeku ! ke Kuma baby danyi maganinki tunda kowa tsokanan shi kikeyi " nanma dariya su fanan sukayi dan dama sudin ne suka rage abaya su ummi da mama,baba Mr azaad,anty amina,duk sunyi gaba sun barsu abaya. Ya al ameen ne yace " nikam bazan iya shirmenku ba nayi nan kaide da zaka iya sekata fama " yafada yana nuna fawwaz sannan ya shige ciki suma rufa mishi baya sukayi wannan karon zeenat ce take rike da fanan kuma sosai ta daure tana takawa .

A tsaye suka samu ya usman da yarinyar akan yayantan doctor kuma yana dubashi shima kanshi yaro ne matashi da be wuce shekara 19 ba fari kyakyawa suna kama sosai da kanwar tashi yana kwance yana baccin wahala zama sukayi akan kujerun dakin kallon yarinyar doctor yayi yace " Yan mata ki kwantar da hankalinki yayanki ze samu sauki da izinin Allah kinji" murmushin yaqe tayi shikuma ya fita , mama ce tace " zo nan yata " ita se yanzu ma ta lura dasu dan dazun da tashiga tsaban hankalinta baya jikinta bata wani lura dasu ba jiki asanyaye taje wajan mama ta tsuguna har kasa da siririyar muryanta tace " mama gani" wani irin dadi mama taji jin yarinyar ta kirata da mama lokaci daya taji hankalinta ya kwanta da yarinyar gyara murya mama tayi tace " meye sunanki ? Su waye ku?Kuma sannan ina iyayenku?" Share kwalla yarinyar tayi tace " sunana hairah ! Yayana kuma sunanshi hafiz mu yan garin gombe ne iyayenmu sun rasu wata 9 dasuka wuce, kuma tunkafin su rasu dama bamuda kowa tom dama babanmu ne yakeyin sanaar dako yake siya mana abinda muke sawa cikinmu se yazo yarasu bayan ya rasu da sati daya mamanmu ma tarasu , tundaga lokacin komai ya canza mana bama samun abinda zamuci se nayi mana bara tukun wata rana mu samu wata rana kuma mu kwana haka shine yayana yashiga kasuwa shima yafara yin dakon inya samu kudi se ya siya mana waina ko kuma rogo ko garin kwaki shine yazo yafara ciwo wani mutum dayake hayan will bairon agurinshi ya kawo shi asibiti tunda yazo sau daya be sake dawuwa ba babu kudin dazaa dubashi shisa likitocin babu wanda yakebin ta kanmu " ta gama magana tana kuka me tsuma zuciya sun matukar tausayawa rayuwarsu domin yaran sunga rayuwa ba uwa ba uba dole su wulakanta tunda babu dangin iyayen , ga ta mace kuma karamar yarinya riko hannunta mama tayi ta zaunar da ita a gefenta tana lallashinta fanan dake gefensu ta zubawa hairah ido tana kallon tsantsan kamarsu da khairaty amma tayi murna da faruwan hakan , ya usman de ya kame akan kujera se faraa yakeyi kamar wanda aka mishi kyauta da kujeran makka yanata kallon hairah ,Mr azaad shi abun ya usman ma dariya yaso bashi ganin irin murmushin dayake sakewa tsaban abinda yake nema yasamu.
Baba ne yace" mamansu kuje gida mazan zasu zauna da shi ku dauketa kaima usman tashi ka bisu tunda kaji lafiyar dole ja'iri kawai " tunkafin yagama magana ya usman ya mike riko hannunta suhaima tayi duk suka fito dasu ummin sukayi gidansu fanan din a falo suka yada zango fanan kuma takai kanta dakinta tana yar dingisa kafa binta da kallo mama tayi dan tun zuwansu ta lura da tafiyarta murmushi ta sake kawai , nunawa hairah bathroom suhaima tayi ta shiga tayi wanka sosai, tafito sanye da dogon kodadden hijab dinta na roba ,masha Allah itama ba laifi dukda yanzu ta fara tasowa amma tana da sura me kyau, riga da skirt din atamfa suhaima ta bata sabo dal dan tunda ta karbosu agun dinki kala biyar taga duk sun mata kadan ta ajiyesu shine yanzu ta bawa hairah daya ta ajiye mata sauran , das kayan suka zauna mata ajiki be kamata ba tayi kyau sosai shafa mai tayi kawai ta zauna can nesa dasu duk a takure take se dar_dar take ganin haka yasa fanan ce mata " hairah ki saki jikinki damu kinji kidauke mu kamar yan uwanki na jini karki dinga dar dar daga yanzu kinzama yar gidan nan saboda haka feel free " godiya tayiwa fanan sosai harda kwalla , shigowa dakin zeenat tayi hannunta rike da plate din abinci tuwon shinkafa da miyar kubewa bushashshe yaji kifi banda hade da nama se kamshin man shanu yake, lokaci daya fanan taji yawonta ya tsinke mikawa hairah plate din zeenat tayi da ruwa , tana kokarin zama fanan tace " yau naga wariyar launin fata zee nizakiwa haka ?" Cike da mamaki suke kallonta musamman ma zeenat duk tunaninta tayi mata wani laifin ne tace " anty fanan mena miki?" Bata fuska fanan tayi tace" ni shine bazaki dibo min abincin ba ko " kallon juna suhaima da zeenat sukayi kafin suka fashe da dariya harda tafawa hada baki sukayi wajan fadin " kice mun samu karuwa " dalla musu harara fanan tayi da dara_daran idanunta tace " banason iskanci kun fara ko ?" Haka sukata tsokanata tayi banza dasu kiran layin Amira tayi ta tambayeta ko tana gida , daka tsalle amira tayi tace " besty kinzo gida kenan ?" eh kawai fanan tace mata ta kashe wayar aikuwa kafin kiftawa kawai sukaji yo sallamar amira shigowa tayi tazauna tana kallon besty nata da suka kwana biyu basu hadu ba tun rasuwan mansoor dasuka je musu taaziya " ohhh besty kina nan abun ki gaskiya bakida kirki " cewar fanan " sorry besty kinsan yanda abu suka hade min se a hankali ga school ga asibiti abin ba sauki" bude baki tayi zatayi magana wayarta yafara ringing miko mata wayar hairah tayi se anan ne amira ta ganta tace " woww suhaima aina kuka samo wannan beautyn ko de su zeenat ne suka zo da ita?" tayi maganar tana sake kallon hairah da kanta akasa ta gaisheta takoma ta zauna suhaima ce tace " bakisanta bane itama kanwar muce" kin daga kiran fanan tayi ganin bakuwar special number batasan nawaye ba

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment