Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin sirrikanshi yasa watarana da daddare yazo har gida ya same mu ni da iyaye ya basu zaɓin ko ya barsu a raye ya kasheni ko kuma ya barni a raye ya kashe su. Haka ina ji ina gani ya bani bindiga na kashe iyaye na da kaina, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai lokacin da na farfaɗo na tsinci kaina a Alpha Villa." wani gauron numfashi taja mai bayyana abinda take faɗa yana mata zafi a rai kafin ta cigaba da cewa
"Bahagowar Rayuwa muke yi acikin wannan gida ni da wasu daga cikin matan da yanayin rayuwa yakai su wannan wajen, na daɗe kafin nasan wasu daga cikin abubuwan dangane da Alpha a lokacin ne nagane cewa ba shi ne yaje ya samu mahaifina ba wani yaronsa ne domin a yadda ake bani labari babu wanda ya taɓa ganin wani ɓangare na jikinsa wanda za'a iya shaida shi dashi, tun daga lokacin na ɗau alwashin sanin wani abu dangane dashi. A haka na cigaba da neman kusanci da shi har zuwa lokacin da nayi nasarar ganin faratanshi waɗanda zan iya ganewa a ko'ina idan naga mai kalansu ko shi ɗin, bayan ya gano ni ne kuma ya saka aka shigar dani ɗakin duhu inda anan yake horar da yaran dake mishi akai. Ta haka ne nasan Alpha sosai har na kamu da sonshi matuƙa duk da har yanzu bai taɓa bayyana kanshi gareni. Na rantse da sarkin dake busamin numfashi wannan ne iya abinda nasani game da shi ko da kuwa zaku bani qur'ani na dafa iyaka gaskiya ta kenan." daga haka ta cigaba da rera kuka a hankali ta barsu kowanne da abinda yake saƙawa a ranshi.

Zarah ce ta fara katse shirun ta hanyar tambayarta tace
"A wani mataki kika tsaya da karatu kafin afkuwar wannan lamarin."

"Ina shekarar farko a jami'ar Jos na fara karantar Mass com."
Shiru suka kuma yi duka na wani lokaci babu mai tankawa kafin Jiddah tace
"Akwai wani ɓoyayyen al'amari da kika sani dangane da rayuwarsa ko wani nasa?"

Kusan mintuna uku kafin ta ɗago tace
"Ehh na taɓa karanta wani kundin sirri a ɗakinsa, akwai wata da naga hotonta da sunanta Phalmata."

A tare suka kusan haɗa baki wajen faɗin
"Phalmata.??" fuskar Zarah da Jiddah cike da mamaki.

"Meye alaqarsu da ita."

"A yadda na karanta na fahimci cewa ita kishiyar mahaifiyarsa ce kuma tare suka fara duk wannan harkallar, a yadda na gani ma ita kaɗaice yanzu a duniya tasan sirrikanshi na da dana yanzu. Inajin idan kuka nemeta zata iya sanar daku komai akansa musamman a yanzu da suke halin gaba zaku fi samun ingantattun bayanai."

"Kinsan wani abu dangane da inda zamu sameta ne."

"Eh toh ita ɗin fasihiyar na'ura ce bayan haka kuma tana ƴan tsibbace tsibbace, ina ganin ta hanyar tsibbu ne kaɗai zaku iya isa gareta."

"A ina take.?" Saleem ya tambaya cike da ƙosawa domin shi burinshi kawai yaji inda zasu samu wannan matar

"Tana garin Dutse a Jigawa."

"Zaki iya tuna adireshinta da kika gani a kundin."

"Eh zan tuna harda fuskarta ma domin yanzu ba ita kaɗai take aiki ba kamar dai Alpha, idan ba sanin wani abu nata akayi ba zata iya haɗa mutum da wata daga cikin masu yi mata aiki a matsayin itace."

Miƙewa Zarah tayi tana gyara tattarewar da kayanta yayi saboda tsugunno da tayi, kana ta kalli abokan tafiyar tata tace
"Muje koh? Jummai ke kuma zuwa gobe ki wuce da ita gidanki ta cigaba da zama acan amma ki tabbatar da tsaro."

"Toh ranki ya daɗe Allah ya tsare."
Da haka suka fice zuwa inda motarsu take, kai tsaye office ɗin Zarah suka wuce domin tattaunawa.

"Zamu ɗaukarwa Raliya malamin dazai dinga koya mata zane-zane domin lallai da taimakonta ne zamu samu zanen hoton Phalmata da yatsun Alpha." cewar Zarah bayan sun zauna zaman tattaunawa akan matsalar.

"Nima nayi tunanin haka, amma bakya ganin koyamata zai ja lokaci? Ina ganin a neme mai zanen kawai ta dinga fasalta mishi ya zana koh."

"A'a Saleem yarinyar tana da kwakwalwa sosai zata koya cikin ƙanƙanin lokaci musamman idan muka mata barazana, da kanta zata fi iya zana komai da ta sani ba kamar idan faɗa take yi ba."

"Wannan haka yake, amma tsawon wani lokaci kenan.?"

"Sa-Jid yau muna ɗaya ga wata, a cikin sati ɗaya Raliya zat gama koyan zane tare da yi mana zanen da muke buƙata, a sati biyun da zasu biyu baya na binciko inda Phalmata take ne, a satin ƙarshe na wannan watan kuma zanje Abuja na neme takardar shaidar kama Alpha kunga kenan a wata ɗaya zamu gama wannan task ɗin muje na gaba wato binciko inda Alpha yake tare da kamashi."
Tafi suka mata cikin jinjina da barkwanci, Saleem ne yace
"Wani lissafin ƴan sanda ne kaɗai zasu iya shi."
Murmushi kawai tayi sannan tace
"Zanyi magana da Daddy idan yaso shi sai yayiwa M.J maganar tafiyarmu Zamfara"

"Shikenan wato har yanzu kunƙi sasanta kanku" cewar. Saleem
Bata ce komai ba ta fara haɗa abubuwanta domin tafiya gida, tare suka fito ta shige motarta bayan sunyi sallama sannan suma suka tada motarsu suka wuce.

A kwanakin da suka biyo baya sam Zarah bata zauna a gida ba saboda ta tsaya kai da fata wajen ganin Raliya ta koyi abinda suke buƙata, a ɗaya ɓangaren kuma suna shirye-shiryen tafiya Zamfara ita da ɗan'uwanta Sadiq da kuma Jiddah da Saleem domin tafiyar da zasuyi ba ƙarama bace saboda adireshin da Raliya ta basu yana da nisa da garin dutse sosai dan haka suna buƙatar su shirya sosai.
Wannan dalilin ne yasa kwata-kwata basu haɗu da M.J ba.

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

A ɓangaren M.J da Hajara kuwa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ne ya shiga tsakaninsu, basa iya ɗaukar dogon lokaci batare da sunji muryoyin juna ba. Da fari Hajara tanason auran M.J ne saboda kuɗinshi saidai daga baya ta gane shine irin mijin da take so kuma gashi ta samu dan haka ne ma tayi alwashin cewa idan akayi aurensu ta gama aikin da zata yiwa Alpha zata cigaba da zama da mijinta domin ta samu kalarta. Shima a nashi ɓangaren yana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci ya kamu da matsananciyar soyayyarta.

Takurawar da Malam Surajo ke mishi akan idan yanason ƴarsa ya turo magabata ne yasa yau yasha alwashin bayan ya tashi a aiki zai biya ta gidan ya sanar musu komai zai faru ya faru.
Ƙarfe shida ya tashi a office kai tsaye kuma gidansu ya nufa, saida ya tsaya yayi sallar magriba a masallacin dake unguwar kafin ya ƙarasa zuwa cikin gidan nasu.
A harabar gidan ya ga motar Zarah hakan ya tabbatar masa cewa tana cikin gidan, ba ƙaramin daɗi yaji ba kuwa domin yana son duk abun da za'ayi ayi a gabanta. A babban falo ya tarar da su duka suna ƙoƙarin yin dinner Daddy, Momi, Sadiq da kuma Zarah, dan haka shima kai tsaye teburin ya nufa da suci abincin tare. Gaishe da iyayensa yayi kana ya baiwa Sadiq hannu suka gaisa fuska babu yabo ba fallasa ko da Zarah ta gaidashi sharewa yayi batare da ya amsa ba wanda duk su Daddy sun lura da hakan amma babu wanda ya tanka haka suka fara cin abincin cikin nutsuwa kowa da abinda ke ransa.

Bayan gama cin abincin kuwa cikin falon suka koma suna hira har kaɗan kaɗan, cikin dakiya da dauriya tare da fargaba M.J ya buɗi baki yace
"Ehhmm Daddy dama nazo muyi magana ne."
Tun farkon shigowar shi Momi ta fahimci akwai abinda ke tafe dashi amma sai ta basar batayi magana har yanzu da ya furta da kanshu, murmushin manya Daddy yayi kana yace
"Ina jin ka."
Shiru ya kuma yi har sai da Daddy yace
"Ko maganar na buƙatar sirri ne."
Cikin hanzari yace.
"A'a ba wata magana ba ce, dama ehmm dama iyayen yarinyar da nake nema ne suka ce na turo magabata na ayi magana, a taƙaice dai aure nakeson ƙarawa."...✍🏻


_BY_
_JASMINE_.🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 4*

Wata irin zabura Momi da ke kan kujera tayi har saida ta sauko ƙasa ta dira a gaban M.J tana ƙura mishi ido, shikuwa Sadiq wayarsa ƙirar IphoneRx dake hannunshi ne ta saɓule ta faɗi ƙasa ji kake tasss ta fashe akan tiles, murmushin da akewa laƙabi da na ciwo shi Daddy yayi sannan ya kalle Momi da Sadiq yace
"Mene ne haka kamar kun riski saƙon mutuwar wani na jikinku.?"
Jan jiki Momi tayi ta jingina da kujerar da Zarah ke zaune,wacce tun faɗar maganar M.J zuciyarta taki nutsuwa a ƙirjinta sai barazanar fitowa take yi. Daddy ne ya kuma magana yace
"Muhammad Jawwad kace aure zaka ƙara koh.?"
Cikin fargaba da tsoro jin Daddy ya kira asalin sunanshi abinda bai taɓa ji daga bakin uban nasa ba tun yarinta,ya gyaɗa kai yace
"Ehh Daddy."

"Ƙarya kake yi wallahi ba isa ka jamin zagi a gari ba Jawwad, bazai taɓa yiwuwa ba wani kallo kakeso a dinga min idan na shiga cikin mutane." Momi ce ta faɗi haka cikin hargowa tana mai fashewa da kuka.
Kaɗa kai kawai Daddy yayi cikin takaici ya kuma maida hankalin shi ga M.J yace
"Shin zan iya sanin dalilin ƙarin auren ko akwai wani abu da Zarah take maka ne wanda bakajin daɗinsa."

"Babu komai Daddy dama muna soyayya da yarinyar ne yanzu kuma mahaifinta ya ce yana bukatar aurar da ita." ya fada kai a sunkuye.

"Kaji ka amince cewa kanason yarinyar kuma zaka aureta ." Daddy ya kuma tambaya.

"Ehh Daddy." ya amsa a taƙaice.

"Shikenan tunda dai kai kazo da zancen bazan hanaka raya sunnah ba , na yarje maka kaje kayi aurenka amma bawai dan hakan zai min daɗi a raina ba, kaje ka fara shiri sannan ka turomin adireshin gidansu yarinyar nan da sati biyu masu zuwa in sha Allah za'a ɗaura maka aure da ita kamar yadda kake so. Sai dai inaso ka shaida wallahi duk wani abu da ya biyo baya karka tunkareni da shi. Tashi kayi tafiyarka."

"Nagode Daddy." ya faɗi haka da hanzari ya mike ya fice daga falon gudun kar Momi ta kuma yin magana

Baki sake kamar mutum-mutumi Momi ke kallon Daddy kamar wacce taga wani abin al'ajabi mai girma, shikuwa Sadiq sarkin zuciya har ya mike ya finciki hannu Zarah da nufin su fice a falon Daddy ya dakatar dashi, cak! Ya tsaya ita kuwa Zarah tuni ta fara sana'ar tata na kuka.

"Indai ka ɗauke ni a matsayin uba ka dawo ka zauna."
Babu musu suka juyo suka zauna zuciya sam babu daɗi, mintuna suka shuɗe babu wanda ya tanka kafin daga bisani Daddy ya ce
"Ku yi haƙuri da kalan hukuncin da na yanke, akwai wani abu da na hanga ne da sannu zaku ga abinda zai biyo baya domin jikina baya bani akwai alkhairi a ciki. Kiyi haƙuri Zarah faruwar komai jarrabawa ce daga Allah watarana sai labari., labarin ma watarana va za'a samu masu bada shi ba. Kiyi hakuri kinji, Allah ya jiɓanci lamuranki, kai Sadiq tashi ka rakata gida."
Babu musu ya miƙe ita kuma ta yi musu sallama suka wuce, a hanya babu mai magana a cikinsu har lokacin da suka isa har cikin harabar gidan M.J kafin Sadiq ya riƙo hannunta ya ce
"Ki dinga yawan tunawa da nasihar da Abba yake mana a ko yaushe, hakuri shine ribar zaman duniya, nima inaso na dinga kwatanta hakan sai dai zuciyata bata iya jure ganin ɗayan ku cikin ƙunci. Da sannu ni da kai na zanzo har cikin gidan nan na ɗauke ki na kaiki inda zaki samu farin ciki na har abada."
Murmushi kawai tayi mishi kana ta fita a motar ta shige gida, shi kuma ya juya kan motar ya fice a harabar gidan.

Kamar yadda suka tsara cikin sati Raliya ta zana musu fiskar matar kamar yadda ta dage wajen koyan abinda ake koyar da ita. Sai dai batun tafiyar ta su a katse sakamakon tasuwar bikin mijin Zarah.
A wannan lokacin kuwa tuni batun auran M.J ya kankama domin an bada sadaki sannan ankai kayan aure ranar kawai ake jira tazo a ɗaura auran, sai dai mutane da dama basuyi farin ciki da wannan auran ba amma babu yadda aka iya da hukuncin Allah.

Rana dai aka ce bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, kamar yadda ya kasance ranar juma'a bayan zagayowar sati aka ɗaura auran Muhammad Jawwad Sulaiman da Hajara Suraj, bikin daya kasance tamkar na bazawara saboda rashin jama'a.
Haka amarya dai ta tare a gidan mijinta cike da buri a ranta na abubuwan da ta shigo cikin gidan da niyyar aikatawa.

Hausawa kan ce _Rawar da aka fara ta da tsalle ƙarshenta baya kyau_, kamar haka ce ta faru a gidan M.J wanda tun farkon kawo amaryarsa ya nuna mata cewa Zarah bata da wani matsayi a gurinshi face na ƴar uwa domin baya mata kallon matarsa, wannan dalilin ne ya saka sam Hajara bata ganin girmanta bare ayi tunanin zasuyi zaman amana, a wasu lokutan a gaban Hajara M.J ke yiwa Zarah cin kashi tare da cigaba da yi mata ƙazafin zina batare da lura da illar hakan da zai haifar masa anan gaba ba.
Yau ma kamar kullum Zarah ta dawo daga aiki a gajiye liƙis, ta shigo babban falon ɗauke da sallama a bakinta, kamar ko da yaushe suna kwance a dogowar kujera manne da juna suna soyayya tamkar zasu haɗiye juna, yau kwanansu goma kenan da aure amma kullum a haka suke wuni tare batare da M.J yayi tunanin bada haƙƙin addini akan wanda yayi sabon aure ba ko da yake bata zaton hakan daga gareshi domin ko da take ita kaɗai ma baya bata haƙƙinta daya rataya a wuyansa. Tunaninda takeyi ne ya katse sakamakon muryar Hajara da ta daki cikin dodon kunnenta tana faɗin
"Hubby haka kenan gidanka zai cigaba da kasancewa mafakar fasiƙai alhalin da ranka da lafiyarka.?" mikewa yayi daga kwancen ya zauna sannan ya dubi Zarah dake ƙoƙarin shigewa part ɗinta ya ce
"Ina fatan kin wanke janabar da kika ɗebo tun a waje baki shigomin dashi cikin tsabtaceccen gidana ba.?"
Kaɗa kai kawai tayi sannan ta shige ɗakinta cike da takaici domin ya ci ace ta saba da irin cin kashin da mijinta da kishiyarta ke mata a duk kwanan duniya.

*1:45am*

A daidai wannan lokacin ko wani halitta na ɗan adam yana tsaka da bacci in ka ɗauke ɗaiɗaiku da wani uzurin ya hana su bacci, cikin waɗanda basu yi bacci ba a wannan lokacin harda Zarah dake zaune gaban na'urarta tana gabatar da wani aiki gefenta kuwa wani ƙaramin kofi ne da shayi a ciki sai tururi yake yi, tana sanye da riga da wando na bacci mai santsi kalar sararin samaniya ta ɗaura wata hula mai gashi a kanta, gabaɗaya hankalinta ta maida akan aikin da take gabatarwa.
A hankali ta miƙe ta nufi window ɗin ɗakin saboda jin alamun kamar hayaniya na tasowa daga farfajiyar gidan, labulen ta ja kaɗan tare da leƙa tsakar gidan ga mamakinta sai taga kamar gilmawar mutum, ganin dare ne yasa bata wanj damu ba ta koma inda take zaune da ta cigaba da aikinta.
Zamanta ke da wuya ta ji an hayaniya da kururuwar Hajara a babban falon tare da sallallami da M.J ke yi, take ta gane cewa wasu sun shigo cikin gidan, da sauri ta miƙe ta ɗauki jacket ɗinta ta saka sannan ta zari ƙaramar bindigarta ta nufi falon. Ai kuwa kamar yadda ta zata mutane ne a falon su tara kowanne da shiga mai kyau fuska a rufe, uku daga cikinsu ne kawai maza amma duk sauran mata ne, ganin fitowarta ne yasa wasu mata su huɗu suka nufeta da nufin rikota, wani wawan naushi ta kaiwa waɗanda ke da nufin riƙe mata hannu da duka hannuwanta biyu sannan ta sunkuya ta kaiwa wacce take gabanta naushi a ciki take ta durƙushe saboda zafin da taji. Sai dai kafin ta kuma wani yunƙuri wasu suka tura ta ta faɗi ta gaba kafin ta ɗago suka yi nasarar ɗaure mata hannaye. Ɗaya daga cikinsu ne yayi maganar su ƙyale Zarah haka sannan ya juya ya kalli M.J ya ce
"Ran matan ka ko kuma dukiya.?"
Cikin kauda kai M.J dake riƙe a hannun ƙarti biyu da mace ɗaya yace
"Malam ni matata ɗaya ce kuma gata nan" ya nuna Hajara sannan ya cigaba da cewa" Ku kama wacce ta muku laifi ku rabu da mu."

Dariya yayi sannan yace
"Ya za'ayi mu yarda da hakan bayan a mun shaida ɗaurin auren ku."

Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace
"Idan kuna so ma zaku iya shaida warwarewarsa."
Cike da dariya mugunta ya kuma cewa
"Mai zai hana kuwa."

Cike da takaici Zarah tace
"Yaya Jawwad kada kayi abinda zaka zo kana da na sani, ina da rauni sosai sannan ni marainiyace. Kada ka lalatamin rayuwa ta hanyar maida ni ƙaramar bazawara."
Bai kula da maganganunta ba ya ce
"Na sake ki saki ɗaya Zarah."
Tabbas mutuwar aure babu daɗi ko da babu soyayya wannan dalilin ne yasa Zarah taji zuciyarta tayi mata zafi sosai lokacin da ɗan'uwanta ya furta kalmar saki a gareta.

"Kinsan abinda ya kawo mu dan haka ki bamu salin alin saboda yau zamu yi ta mukare tsakanin mu da ke." Mutumin ya kuma faɗa batare da ya kula da halin da take ciki ba, kauda kai tayi gefe tana addu'ar Allah ya bata nasarar kunce kanta duk da suna da yawa tasan zata iya musu mugun lahani ba tare da makami ba ma. Saura ƙiris ta fasa ƙara saboda wani gigitaccen zafi daya ziyarce ta a gefen cinyarta, kallonta ta maida gurin taga ashe ɗaya daga cikin matan nan ne ta yi mata muguwar yanka a cinyarta take kuwa jini ya ce dama hanya nake nema nan ya fara zuba tamkar kwararo shi ake yi, raɗaɗi take ji sosai amma hakan bai sa ta amsa tambayar da ya kuma mata ba, ya ce
"Ba zakiyi magana ba ke wace iriyar yarinyace mai taurin kai ne, mtsssw ku shiga ku bincika min ko ina a cikin gidan nan."
Dukkansu suka nufi hanyar da suka ga Zarah ta fito mutum uku kaɗai suka bari biyu na tsare da M.J da Hajara sun saka musu bindiga akai sai babban dake gefen inda Zarah ke ɗaure yana wasa da wuƙar hannunshi yayinda ɗaya hannu ke rike da bindiga. Kusan mintuna arba'in suna dube-dube a cikin gidan amma basu ko ga wata alamar da zata nuna musu cewa Diamonds ɗin suna cikin gidan ba, cike da rashin kwarin gwiwa suka dawo suka sanar da shi, bai ce komai ba ya zaro waya ya daddanna sannan ya kara a kunnenshi jim kaɗan ya fara magana yace
"Yallaɓai jiya i yau fa, taurin kan yarinyar yayi yawa ta tushe kowace hanya bata bamu damar sanin komai ba."
Huci ya furzar mai zafi kana yace
"Wannan karon inaso ku taɓa Zarah, ina so taji a lafiyarta cewa ba'a gardama dani, ina so taji lallai cewa bazata iya cigaba da ajiyar Diamonds ɗin nan ba, lallai ku yi mata mummunan lahani kamar yadda zuwa yanzu na tabbatar idan Raliya tana raye to tana cikin mawuyacin hali."

"Angama ranka ya daɗe." daga haka ya katse wayar ya kalli matan dake tsaye ya ce
"Ku cika aiki" tamkar suna jira haka suka ruftu su biyar akan Zarah kowa da irin dukan da yake kai mata amma duk da haka ko tari bata yi ba bare ayi tunanin zatayi kuka.
Karo na farko Hajara taji mugun tausayi da dana sani sun baibayeta, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, sosai taji da na sanin haɗa kai da ita da akayi tun farko har zuwa yau da suka shigo cikin gidan nasu. Shikuwa M.J ba yadda za'ayi ka gane yanayin da yake ciki domin fuskarsa tana nan yadda take.
Cikin mintuna ƙalilan farin tiles ɗin dake falon ya fara rinewa yana yin ja saboda jinin dake gangarowa daka jikin Zarah sakamakon bugu da yanka da suke jikinta, ganin kamar ta daina numfashi ne yasa ya dakatar da su sannan suka fice a gidan.
Da hanzari Hajara ta rarrafa ta isa kanta hawaye na biyowa a idanunta ta juya ta kalli M.J ta ce
"Hubby ɗauki key da sauri mu kaita asibiti."

"Ni? Asibiti? Babu inda zan fita da daren nan, ita ta jawo wa kanta."

"Ka dubi halin da take ciki mana dan Allah ka taimaka."

"Yaya Jawwad dan Allah ka kiramin Daddy ko da bazaka kai ni asibitin ba." Zarah ta faɗa a galabaice, numfashinta na fita ɗaiɗai.
Bai kula ta ba ya zo yaja hannun Hajara suka nufi ƙofar part ɗin shi, tsayawa yayi cak! Sannan ya dawo ya tsugunna a gabanta yana ƙare mata kallo shi kansa yasan tana buƙatar taimako na gaggawa amma yana jin zafinta sosai a ƙasan zuciyarsa, gyaran murya yayi sannan yace
"Kinsan yanzu babu igiyar aure tsakanina dake, dan haka zan taimaka miki ne kaɗai a matsayin karuwar da nakeso ta tuba ga Allah kafin ta mutu, wannan ne kaɗai gatan da zan miki, kin amince na taimaka miki.?"

"Zan fi ƙaunar na mutu a haka matukar da wannan ƙudurin zaka taimake ni, na tsane ka, baka da tausayi ko kaɗan, kai mara imani ne."

Kafaɗa ya kaɗa ya mike sannan yace
"Duk yadda kika gani sai ki kira wanda kike jin shi zai iya taimakonki ko a cikin abokan watsewarki ne." daga haka yaja matarsa suka shige suka barta a nan kwance.
Cikin dakiya da juriya ta miƙe zaune tana jan jiki harta isa ƙofar da zata sada ta da farfajiyar gidan cikin tsananin azaba da ciwo.



A firgice ta miƙe daga baccin da take yi, juyawa tayi ta kalli agogo 2:05am kallonta ta maida kan Saleem dake sharar baccinsa hankali kwance, a hankali ta fara bubbuga bayansa har ya farka ya buɗe idanunsa ganinta a zaune ne yasa shima ya zauna yana miƙa ya kalleta yace
"Lafiya kuwa me ya same ki.?"

"Sa-Jid nayi mafarki Zarah na ta kirana tana faɗin na taimaka mata, zuciyata da jikina sun amsa bana jin daɗi sam ina da tabbacin cewa akwai abinda ke faruwa da ita."

"Me zai faru da ita da wannan daren haba dan Allah mafarki fa ba gaskiya bane."

"Na sani amma dai wannan yayi kama da gaskiya, miƙomin wayar can na kirata."

Hannu yasa ya ɗauko wayar dake kan bedside drawer ya bata, cikin hanzari ta fara danna lambar Zarah tana kira amma kusan kira 30 babu amsa. Zuwa lokacin ta gama ruɗewa, kuka ta sakawa Saleem akan lallai sai ya kaita gidan Zarah a daren duk yadda yaso ta haƙura amma taƙi, sanin da yayi cewa idan damuwa zata iya jawowa ƙaramin cikin dake jikinta matsala ne yasa dole ya miƙe ya zura jallabiya ya ɗauki key ɗin motar suka fice a gidan, har zuwa lokacin kuma bata daina kuka da sambatu ba...✍🏻


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*

*BOOK 2*

*Page 5*

... Su uku ne zaune a cikin wani ƙayataccen falo da yaji kayan alatu tamkar na shugaban ƙasa Sadiq, Rahma da kuma Zarah, kallo ɗaya zaka musu ka gane suna cikin tsantsar farin ciki da suka daɗe basu samu ba duba da yanayin yadda fuskokinsu suka kasa ɓoye farin cikin da suke ciki. Rahma ce ta ajiye cup ɗin dake hannunta a center table ɗin dake gabanta sannan ta juyo ta dubi Sadiq dake nunawa Zarah abu a waya suna ƙyalƙyala dariya ta ce
"Bazan iya tuna ranar ƙarshe da naga dariyarku haka ba musamman Zarah."

"Ba mu da wata sauran damuwa ne shiyasa ki ka ganmu haka, ke ba abin farin ciki bane a gareki ace yau wanda yayi sanadin da iyayenmu suka bar duniya shima ya mutu ta dalilinmu, baya ga haka ƴar'uwar mu wacce muke tunanin ta zauce yau ta samu lafiya ingantacciya, kinga kuwa dole mu yi farin ciki." Sadiq ne yayi wannan sharhin bayan ya maida hankalinsa kanta.

Gyaɗa kai tayi ciki da gamsuwa tace
"Haka ne amma naku ne kawai ke fitowa fili, nawa na barshi a zuci."
Zarah waccw tun da aka fara maganar bata tanka ba ta ɗago tace
"Meye zai hana ki fito dashi fili mu haɗu mu yi murnar tare."
Cike da zolaya Rahma tace
"Yau kam naci girma na bar muku."
Ɗaya daga cikin ƙananun pillows ɗin dake kan kujerar Sadiq ya ɗauka ya jefeta da shi cikin harara yace

"Ke banson raini fa"

Itama cikin zolaya tace
"Kwanaki ƙalilan a ne tsakaninmu fa."

"Duk da haka dai ya riga ki shaƙar iskar duniya." Cewar Zarah.

"Haka ne toh na baka girman ka, yanzu daga nan ina

1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment