Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kayana da ke gidansa kuwa tun waahegarin da Ammi ta zo suka je da Jiddah aka kwashemin aka maida min gidan Daddy, part guda aka waremin tamkar wata matar gida.

Gabaɗaya mun gama shirin tafiya Enugu sallamar likita kawai muke jira, dama na riga da na jima da karɓar takardar shaidar kama Alpha dan damƙa shi a hannun hukuma a ko wani hali, dan haka abinda kaɗai nake jira shine na ƙarasa warwarewa don mu tafi Keruba. Tafiyar ta mutane bakwai ce Ni, Sa-Jid, Yaya Sadiq, sai wasu jami'aina na sirri guda uku da zamu yi tafiyar tare.

A daren da na cika sati biyu ne a asibiti likita ya sallameni inda a washegarin ranar kuma zamu wuce Enugu, tafiyar da bamu da tabbacin ko zamu yi nasara, haka dai muke ta shiri zuciyoyi sam babu dadi.
Kasancewar tafiyar mota zamu yi yasa washegari da asuba bayan munyi sallar asuba muka yi sallama da su Daddy muka ɗauki hanyar tafiya cikin motoci biyu.

Sallah kawai ke tsayar damu a hanya amma duk da haka ba mu isa cikin garin Enugu ba sai wajen sha biyu na dare, hotel ɗin da muka kama ta internet muka nufa kai tsaye ba mu sha wahalar ganewa ba saboda munyi amfani da google map, cikin lokaci ƙanƙani muka isa wajen.
Bayan karɓi makullan ɗakin ne muka wuce don kowa ya huce gajiyar da ke tattare da shi.

Kwananmu biyu muna huce gajiyar hanya kafin ranar asabar da yammaci muka shirya tafiya garin Keruba kamar yadda aka kwatanta mana zuciyoyin mu cike da zullumi duk kuwa da kasancewar a daren wannan ranar kwana muka yi sallah muna neman zaɓin Allah a cikin lamarin. Sai Yamma lis kafin muka isa cikin garin wanda yake da kyawun tsari, duk da mun baro arewacin Najeriya a bushe amma wannan yankin ko ina da damshi alamun dai basa dadewa ba ta re da ruwan sama ba. Wani ƙaramin masauki muka kama don mu kwana a ciki kafin washegari mu ƙaddamar da abinda ya kawo mu. Wannan dare kwana nayi a gaban maliccina ina kai mai kukana ya taimaki ne akan abinda na sa gaba. Wallahi ban taɓa sanin cewa addu'a na da wannan ƙarfin ba sai a washegarin wannan dare, ban taba tunanin abubuwa zasu zo mana da sauƙi ba sai a lokacin na tabbatar cewa babu kamar hawayen wanda aka zalunta a wajen Allah.

Washe gari kamar yadda aka faɗa mana cewa Alpha na fita zagayawa a gari cikin ɓadda kama haka muma muka shirya ɓadda kama tamkar wani shirin film. Duk da cewa cikin Jiddah bai wani girma ba amma a haka muka yi amfani da ita. Kasancewarsa mutum mai kaifin basira yasa ba mu yi tunanin yin ƙaryar yin dressing da bandage ba gudun karya gane ƙarya muke yi. Dole ta sa aka yi wa Jiddah rauni a jikinta, duk yadda ta so daurewa sai da ta kasa na gane cewa tana matuƙar jin zafi a jikinta.

Kayan masu aikin Momi da muka karɓo muka saka sannan wata daga cikin jami'an nan ta shafa mana wani abu a fuska da jiki wanda idan ba mutum ya sammu sosai ba bazai gane mu ba. Tunda wuri muka yi wa hanyar da Alpha zai bi tsinkaye, cikin tsananin shiri da taka tsantsan.
A tsakiyar hanya muka zauna Jidda ta kishingiɗa ta yi matashi da cinyata, kasancewar a yanki kudu kowa harkar gabanshi yake yi ya sa babu wanda ya kula da lamarin mu kowa ya zo wuce wa yake yi batare da ya tambayi dalilin da yasa muke zaune a gurin cikin wani yanayin da babu kyan gani ba. Mu na zaune a wajen har kusan mintuna talatin ni da Jiddah, yayin da su Saleem ke can nesa a ƙasan wata bishiya suna zaune.

Tun daga nesa na hango tahowarsa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana taƙama da izza saboda yanayin yadda yake tafiya tamkar mai tausayin ƙasa, duk da shiri ne amma ni da Jiddah mun gaji sosai kallo ɗaya zaka mana kasan mun galabaita. Magana nayi a hankali na sanar da Jidda tahowarsa, ai kuwa tuni ta fara juyi kamar wacce ke naƙuda alhali cikin nata wata 3 ne kacal, ƙamshin turarensa kaɗai ya isa sanar da cewa mai kuɗi ne na gaske, domin indai hancina ya jiyo min ƙamshin nan daidai Abbana yana amfani da kalan turaren nan sanda yake da rai, saboda akwai watarana da na dage sai ya bani kyautarsa shine Mami ke gayamin kuɗin turare yakai dubu ɗari uku.
Cikin takun ƙasaita yazo ya wuce ta gefen mu ba ta re da ya kalli ko gefen da muke ba, take naji hawayen rashin nasara sun sauko daga idanuna, har ya ɗan yi nisa naga ya tsaya sannan ya juyo ya nufo inda muke, farin ciki ne ya kamani dakyar na saisaita kaina gudun matsala.

"Sannunku bayin Allah" Sautin muryarsa naji ta daki kunnena, zan iya rantsewa tun da nake a duniya ban taɓa jin wata murya mai zaƙi irin tasa ba, mintsilin da Jiddah ta yi min a gefen cinya ne ya dawo da ni da ga duniyar tunanin da na tafi. Cikin sanyi na amsa mai da
"Yauwa sannu" na kauda kaina gefe ina matsar kwalla.

"Me ya sa kuke zaune anan gurin da babu tsabta haka."

"Ƴar uwa ta ce ba lafiya cikinta yana ciwo, kuma akwai ƙaramin ciki a jikinta shiyasa na zauna anan mu ɗan huta ta ce ba zata iya tafiya ba." Na faɗa cikin rauni.

"Subhanallah! Taimako ya kamata ke nema a kaita asibiti ai, ciwon cikin masu juna biyu ai ba daɗi." Ya fada da alamun ruɗewa a tare dashi. Bance komai ba illa kwallar da na cigaba da matsa kamar wacce ke cikin wani babban tashin hankali, wata tsadaddiyar waya ya ciro a aljihunshi ya fara dannawa ya ce
"Bari na kira ƴar uwata ta taimaka sai mu kaita asibiti."

Da "Toh" na amsa mishi. Magana yayi da wani yare da ban fahimta ba sannan ya cire wayar a kunnensa ya tsugunna a gabanmu yana jera ma Jiddah sannu kamar wata matarsa. Ban san cewa na da wani shiri a ƙasa ba domin bata faɗamin ba, ni a yadda muka tsara jami'ai ne zasu zo su kamashi lokacin da ya tsugunna a wajen, sai dai ba zato ba tsammani batare da dukkanmu biyun mun ankara ba Jiddah ta zaro wuƙa mai kaicin gaske da alama ma sabuwa ce, cikin zafin nama ta kwace a jikina sannan ta caka mishi wuƙar nan a gefen ciki, wata ƙara ya kwalla ya dafe gurin, kafin yayi yunƙurin guduwa tuni jami'an sirri da Gwamnatin Enugu ta bamu suka zagayeshi wasu daga ciki kuma suka damƙi hannunsa suka maka mai ankwa, cikin mintuna ƙalilan sai ga motar asibiti, nan aka sashi a motar tare da wasu jami'ai aka wuce da su.

Bansan a wani yanayi na tsinci kaina ba lokacin da na ga jami'ai sun kama Alpha har sun saka mishi ankwa, wannan ranar na ɗaya daga cikin ranakun da bazan manta da su ba a tarihin rayuwata, bansan me ya faru ba sai dai bude idona nayi na ganni a gadon asibiti, sai a lokacin Yaya Sadiq ke fadamin wai sumewa na yi, a lokacin ne na fara tariyo abubuwan da suka faru ina daɗa mamakin yadda kama Alpha ya zo min da sauƙi haka tamkar a mafarki, dole na gode ma Allah da ya banj nasara akan makiyina sannan dole zan godewa Almajirata.Lol.
Murnar da na shiga a wannan ranar ko runtsawa na kasa yi, kwana nayi ina sallar godiya ga Allah, wannan ranar kadai nake jira dama na ajiye aikin ƴan sanda, ranar da zan kama wanda yayi sanadin mutuwar mutane masu gurbi na musamman a rayuwata, Abbana, Mami, Kakannina, lukutar ƙanwata da kuma rigimammun ƴan biyun ƙannaina, a wannan ranar na ji ni na kammala ba ni da wata sauran damuwa da ta ragemin. Har ƙaramar walimah muka hada a resturant ɗin hotel ɗin da muka sauka, Sadiq ne ya ɗauki wannan nauyin.

Washegari kamar yadda ya zo a hukumance tunda Alpha ya amsa laifin da ake tuhumarsa sannan yayi bayanin inda za'a samu Phalmata da yadda za'a kuɓutar da matan da ya ajiye a Alpha Villa, bayan an damƙo Phalmata da sauran masu yi musu aiki ne aka wuce da su Abuja inda anan za'a yanke musu hukunci, yaran nan kuwa kowa an haɗasu da jami'ai domin a sada su da iyaye da ƴan uwansu, gabaɗaya mu ma Abuja muka nufa inda zamu haɗu da su Daddy acan don zasu zo ganin yadda shari'ar zata kasance.
Sunayen manyan ƙasar nan da suke da sa hannu a miyagun laifukan da su Alpha ke yi ba zasu kirgu ba, sunan Commissioner na daga farko-farko a cikin jerin mutanen, cikin kwanaki biyu aka cafko kowannensu, masu muƙami kowa tuni Gwamnati ta karɓe abin ta, sai dai mu yi fatan gyaruwar ƙasar mu.

Ranar da aka yi zaman kotu kuwa garin Abuja ta karɓi baƙuncin mutane da dama, sai da aka cika kotun nan maƙil babu masaka tsinke domin wasu a waje ma suka tsaya don babu gurin zama kowa nason ganin mutum ɗaya jal! da ya daɗe yana gallazawa mutane, bayan alkali ya zo ne aka gabatar da tuhumar da ake musu inda lauyan Gwamnati ya gabatar da kansa, babu batun lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma domin ba su da shi, cikin sauƙi ba ta re da wahalar da shari'a ba aka zartar musu da hukunci, Al'amin da Phalmata hukuncin kisa ta hanyar rataya inda sauran kuma hukuncinsu zaman gidan kaso na har abada. Daga haka Alƙali ya sallami kowa sannan aka bada umarnin wucewa da masu laifi gidan yari, kotu fa ta hargitse kowa da abinda ke fadi inda mutane da dama su ka so ɗaukar doka a hannunsu sai dai babu hali.

Sosai na so ganawa da Alpha amma Sadiq ya hana ni gudun kada wani abun ya faru, haka ina ji ina ganin muka bar garin Abuja zuciyata sam babu daɗi saboda yadda na so mu yi sallamar ƙarshe da Alpha, sam a wannan lokacin sai nake jin tausayinshi na kamani matuƙa ta yadda mace ɗaya ta lalata mishi rayuwarsa ta duniya, ko da yake shima yana da laifin biyewa son zuciya don bai tsaya a inda Allah ya ajiye shi, yana da kyau na ɗaukar hankali wanda iya shi kadai zai iya zama jarinsa don ga dukkan alamu mutum ne mai farin jini, dole daga baya na cire tunaninshi a raina. Rayuwa kenan ban taɓa kawowa cewa al'amurana zasu warware cikin sauƙi haka ba. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai wanda baya zalunci sannan baya barin masu aikata zalunci.

Kwananmu biyu da dawowa Gwamnati ta shirya mana ƙayataccen Dinner wanda ya haɗa da ƙarin girma, gabadaya jami'aina an musu ƙarin girma inda ni kuma Gwamnati ta tura ni ƙasar Malasia domin yin course na musamman a harkar tsaro, na so naki karban wannan tayin amma Daddy ya tursasa dole banj da wani zabi daya wuce hakan. Haka dai aka kammala taron Dinner ɗin zuciyoyin mutane cike da murna.

Washe gari gaba ɗaya muna zaune a dinning mu na breakfast, M.J ne kawai bayanan a wannan zaman, cikin nutsuwa kowa ke cin abincin da Momi da kanta ta sarrafa shi, wayar Ammi da ke falo ce ke ta ƙara don haka ta kalleni ta ce
"Little miƙo min wayar nan kinji, na ga wanda ke kirana haka da safe ko karyawa ba za'a barni nayi ba." Dariya muka yi duka kana na miƙe domin zuwa ɗauko mata wayar.
Da sauri na taho na bata wayar sakamakon wani kiran da ya shigo, mijinta da ga ƙasar Egypt Dr. Adam ke wannan kira, cike da mamakin kiransa a wannan lokacin ta ɗaga, bai jira ta yi magana ba ya riga ta, ai kuwa sai gani muka yi ta mike tana faɗin
"Alhamdulillahi Allah mun gode maka Ya Allah kai kadai ke yi a duk sanda ka so ya Allah muna ƙara gode maka da ni'imomin ka gare mu." ba su dade ba ta sauke wayar a kunnenta fuskar ta kaɗai ta isa fallasa farin cikin da ta ke ciki, zuba mata na mujiya mu ka yi cikin son ƙarin bayani, ai kowa fahimtar hakan da ta yi ne ya sa ta ce
"Wani abin farin cikin ya kuma samun mu, wallahi ashe labari mai dadi ne Dr. Ke san gayamin tun dazu shi ke kiran wayar." cike da zumuɗi na ce

"Ammi meya faru ne"

Cikin fara'a ta ce
"Rahama ce ta warke daga Trauma ɗin da ke damunta, yanzu haka ta dawo hayyacinta harta labarta ma Dr. Abinda ya faru waccan ranar shine ta ke daɗa tambayar duk ina muke."

Wani wawan tsalle na daka na rungume Ammi da ke tsaye cikin murna, hamdala duk mutanen da ke wajen suka fara, an ɗau lokaci ana maida magana kafin Daddy ya ce

"Ai kamata yayi a kira Rahama ɗin ta video mu ganta ta ganmu ko hankalinta ya kwanta."

"Wallahi abinda na ce ma Dr. Kenan amma wai an yi mata allurar bacci saboda kukan da ta ke yi."

"Toh masha Allah sai kuma ayi shirin tafiya koh" cewar Baaba. Dariya muka yi ganin yanayin yadda ta yi maganar. Daddy ya kuma ce wa

"Insha Allahu kuwa sai tafiya a yau ɗin nan zuwa dare sai mu wuce. Tunda akwai private jet ɗin kamfani na sai mu wuce gabaɗaya kawai."

"Haka za'ayi kawai Daddy amma dare kamar yayi nisa fa." Jiddah ta faɗa a shagwaɓe.

"A'a Mamana(sunan da Momi ke kiran Jiddah da shi kenan kasancewar sunan Mahaifiyarta ne) babu kyau gaggawa aikin shaiɗan ne a bari zuwa daren mu shirya a nutse, zan kira Hajiyarku (Mahaifiyar Jiddah) na shaida mata nasan itama za ta so ayi tafiyar nan da ita."

"Hakane ya kamata a shaida musu kam."

Bayan mun kammala breakfast ɗin ne duk muka miƙe don fara shirye-shiryen tafiya, inda Saleem ya ɗauki Jiddah suka wuce gida don yin nasu shirin. Bayan na dawo daga rakiyar su Jiddah ne na tarar Sadiq na ƙoƙarin fitowa daga falon don zuwa sashensa, wani tight and friendly hug ya bani, dama nasan ɗazu kunyar su Daddy ya sa bai wani nuna ɗokin shi ba, cike da farin ciki ya ce

"Little ina taya mu murna ragowar farin cikinmu ta dawo hayyacinta, bansan wani irin murna zanyi ba wallahi." sassauta riƙon da yayi min yayi sannan ya riƙe hannuwana biyu ya ce

"Ku kaɗai ne farin cikina yanzu a wannan rayuwar, tabbas a yau na ƙara jaddadawa kaina alƙawarin amanarku da Abbanmu ya bani, zan ɗau alƙawari har a gaban ubangijina bazan taɓa bari ku ji kewa ko maraici ba, zan kasance Uwa, Uba sannan Yaya a gare ku ke da Rahama bazan bari ko ku ƙara yin kukan baƙin ciki ba matuƙar ina numfashi a duniya." hawaye ne ya silalo a kan fuskarsa, hannu na saka na share mai sannan na ce cikin zolaya

"Ka tafi ka shirya ka ji young Abbah."

Doka ya kaimin cikin sauri na sunkuya na wuce ciki da gudu, kai tsaye ɗaki na nufa don haɗa kayana. Wayata na ɗauka na kira Jummai sannan na gayamata ta baiwa Raliya 1million sannan ta sallameta idan da hali ma ta kaita har gaban danginta.

Ƙarfe bakwai na dare muka private jet ɗin Daddy ya ɗaga damu zuwa ƙasar Egypt and here we're tare da Trauma Patient Rahama.

Dukan wasa Rahama ta kaiwa Zarah lokacin da ta kawo ƙarshen labarin. Kana daga baya ta rungumeta tsam a jikinta tare da fashewa da kukan tausayin ƴar uwarta ta, sun jima a haka har sai da Sadiq ya yi magana kafin suka tsagaita yin kukan.

Satinsu Daddy ɗaya a Egypt suka koma Nigeria inda aka bar Sadiq da Zarah saboda daga nan zasu wuce Malasia.
Su ma kwanaki goma kacal suka ƙara jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Malasia.

_Bari mu leƙa amarya da ango._..✍🏻


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 9*

Sai dai kafin ta kai ga miƙewa Sadiq ya ruƙo hannunta ya zaunar da ita ba ta re da ya ce komai ba abincinsa kawai ya cigaba da ci, tuni ta gane abinda ya ke nufi don haka ta zauna cikin takura ta fara cin abincin, duk da bata kallonshi amma ta tabbatar kallonta ya ke yi don haka ta ji sam zaman gurin bai yi mata ba.
Sun rigata gamawa don haka ne ma suka koma cikin falo suna hira. Duk da haka idon mayen nata na kanta.

_Safwan Muhammad Habib shine sunansa matashin saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da bakwai ɗan kwalisa, asalinsa ɗan Nigeria ne karatu ne ya kawo shi waje daga haka kuma suka riƙeshi, babban likitane a ɓangaren da ya shafi mata da ƙananan yara._
_Ya fito ne daga gidan sarauta inda a yanzu haka mahaifinsa shin Sarkin Adamawa, cikin ƴaƴan Mai martaba shida da matarsa Hajiya Zulaihat guda biyu ne maza, ɗansu na fari Mahmud sai auta Safwan shiyasa Mai martaba ya ɗauki gatan duniya ya ɗora shi akansu ba kamar Safwan ba ma da ba ya iya ɓoye son da ya ke masa ko a gaban waye, tun da ya isa shiga makaranta Mai Martaba ya ɗauke shi zuwa saudiyya inda wata ƙanwarsa ta ke aure, anan ya yi karatunsa daga na boko har zuwa addini hutu ne kawai ke maida shi Nigeria, sanda ya isa shiga jami'a ne ya koma London ya haɗa degree ɗinsa na farko daga nan ya koma Malasia yayi Masters ganin ƙoƙarinsa da sanin kan aiki ne yasa bayan ya gama karatun ƙasar ta riƙeshi zai yi mata aiki na tsawo shekaru biyu, ɗan uwansa Mahmud kuwa tunda ya gama karatu mai martaba ya sashi ya kuma Najeriya inda ya buɗe mishi wani babban company tun da dama karatunshi akan kasuwanci yayi, saboda kasancewarsa magaji shiyasa mai martaba bai yarda ya zauna a waje don yin aiki ba, a yanzu haka yana da shekaru 35 kuma har zuwa wannan lokacin bai yi aure ba duk takurar da iyayensa ke masa an haɗashi da ƴaƴan manya sosai sai dai duk cikinsu ya kasa zaɓar ko guda ɗaya._
_Farkon ganinta da Safwan washe garin ranar da suka zo Malasia ne, gidansu da nashi na fuskantar juna ƙaramin titi ne kawai ya rabasu, a ranar Sadiq ke gayamata cewa ya shaida Safwan ɗin don sun taba haɗuwa sau biyu a saudiyya sanda ya je Umrah, anan ne ma ta ke jin tarihinsa da inda ya fito shiyasa wani lokacin bata ganin laifinsa idan yana girman kai bata ganin laifinsa don ya fito ne daga gidan sarauta_

Ta na iya jiyo hirar da suke yi daga inda ta ke, tana mamakin yadda ya ke hira haka harda dariya amma idan ka ganshi a wani wajen kamar mala'ikan mutuwa.

"Zuwa wani sati zanje Egypt." Cewar Sadiq

"Haba dai yaushe ka dawo daga Egypt din da har zaka koma, me Ammi ta ke baka hakane ko kuma akwai wacce ka ajiye acan ne shiyasa kake zuwa ganinta." Safwan ya faɗa cike da zolaya.

"A'a ka bari dai ai yanzu Yola zanje na zaɓo santaleliyar mata jinin Fulani, zanje na taho da Rahama ne kasan har yanzu ba wata isasshiyar lafiya gareta ba."

Hararar wasa ya aika masa sannan ya ce

"Kana shagwaɓa yaran nan dayawa fa, yanzu duk wayar da kuke yi da video calls bai ishe ku ba har sai ka aje aiki kaje ka ɗauko ta."

"No bawai haka bane wallahi, next week little zata ƙara shekara shiyasa nake so tazo mu yi murnar tare."

"La'ilah party zaka koya musu."

Dariya yayi mai isarsa sannan ya ce

"Ba wai party bane, Abbah ya rigada ya saba mana ne duk ranar zagayowar haihuwar wani daga cikin mu sai an haɗu an taya shi murna hatta ni da bana ƙasar ma, har inda nake ake zuwa a same ni ayi komai tare dani. Kuma kaga ita little bata taɓa ƙarin shekara cikin nutsuwa ba aikin nan nata baya barinta ta yi abubuwa cikin lumana ko bata gari anyi ta kiranta a waya kenan har sai ta gaji ta koma."

Dariya ce ta so kwacewa Zarah jin irin sharhin da ɗan uwan nata ya yi, shidai Sadiq akwai surutu idan ba haka ba yanzu me ya haɗa Safwan da wannan dogon zance na family, ko da ya ke Sadiq ɗin ba shi da wasu abokai sai turawa shi yasa idan ya haɗu da bahaushe ya ke zuba kamar ruwan sama.

Gyaɗa kai Safwan ya yi cikin gamsuwa ya ce
"Hakane gaskiya bai kamata ace don Abban baya raye ba kuma a daina musu hakan zasuji kewa ta damesu. Allah ya jiƙansu Abbah ya gafartamusu."

"Ameen" Sadiq ya faɗa sannan ya kalli inda Zarah ke zaune, ganin hankalint baya kansu ne yasa shi cewa

"Ka faɗa a hankali karka tada min rigima dan idan little ta birkice ta fi tsohuwar mota."
Dariya suka yi duka harda tafawa.

Miƙewa ta yi bayan gama cin abincin ta fara tattara kwanukan tana kaiwa kitchen, harta gama ta shige ciki ta barsu suna hira batasan lokacin da Safwan din ya tafi ba don a Malasia dare baya yiwa mutane sai dai idan mutum ne ya gaji da zirga-zirga ya je ya kwanta.



Kwanaki uku tsakani Sadiq ya wuce Egypt, kwananshi ɗaya acan suka dawo tare da Rahama. Ranar kusan kwana suka yi suna hira irin ta ƴan uwa.

Washe gari da safe dukkansu ukun suka shiga kitchen dan haɗa breakfast, sosai Sadiq ke zaƙewa wajen baiwa ƙannen nashi kulawa.
Bayan sun gama breakfast ne kuma suka hau aikin gyaran cikin gida har zuwa farfajeyar gidan, gabaɗaya Zarah da Rahama sun yi kaca-kaca da ruwa sun jika ko ina wai suna baiwa fulawoyi ruwa har abun ya koma suna watsawa juna.

Yana daga ɗakinshi ya ke hangosu ta window, sosai ƙaunar da suke wa juna take matuƙar burgeshi musamman yadda yaga dukkansu suna baiwa alawar zuciyarsa kulawa, murmushi yayi mai sauti saboda wani abu da ya tuna. Safwan kenan.

Wuni suka yi ranar cikin nishaɗi da kulawa da juna, yadda suke nuna ƙaunar juna kowa ya gansu sai sun bashi sha'awa.

Kamar wacce aka yiwa baki tunda Zarah ta kwanta bacci bata tashi ba, kasancewar tana fashin sallah shiyasa Rahama bata tasheta ba lokacin sallar asuba.
Sai wajen ƙarfe goma na safiya ta farka, da wasu haɗaɗɗun greeting cards ta fara yin tozali, da hanzari ta miƙe saboda tunawa da ta yi yau ranar zagayowar haihuwarta, cards ɗin ta janyo guda uku ta fara karantawa cikin jindaɗi sai dai guda ɗaya ya matukar tafiya da ita kuma ga alama ya fi duka kyau da tsada, duba suna ta yi taga an rubuta SMH bata gane ko na wanene ba tunda na Sadiq da Rahama duk sun saka sunansu bata wani damu ba ta miƙe ta nufin zuwa toilet, idonta ya sauka akan dressing mirro wani kwali ta gani dan haka ta yi saurin isa ta buɗe shi, wata haɗaɗɗiyar arabian gown ne a ciki kalar pink mai matuƙar kyau dai wani takalmi golden.
Da hanzari ta shiga bayan gida ta watsa ruwa ta fito dan tasan ƴan uwanta na jiranta.
Simple makeup ta yi a fuskarta sannan ta saka doguwar rigar wacce ta mata kyau matuƙa, veil ɗin rigar ta naɗa akanta sannan ta nufi falo.

Da alamun mamaki a fuskarta ganin falon gabadaya duhu mamaye shi, bata gama mamakin ba kuma haske ya gauraye falo ta re da suwar happy birthday to you, ido ta waro tana kallon mutanen falon cikin mamaki harda maƙotansu da matayensu, tuni ta ƙara rudewa ganin Jiddah da Saleem a gefe ɗaya, hawayen da ake kira na farin ciki ne ya sauko a fuskarta. Da sauri Rahama ta zo ta ja ta zuwa gaban tebur din da aka aje ƙaton cake kalar pink da fari, hannun ta kai da nufin yankawa Rahama ta yi saurin riƙe hannun, kallonta ta yi da alamun tambaya bata amsa mata ba sai ma zura hannayenta da tayi ta rufe mata idanu, kusan sakan goma sannan ta buɗe mata, sai da ta razana saboda abinda ta ga ni ta kuma ji, Safwan ne a durƙushe gabanta riƙe da ɗan ƙaramin akwati na zobe yana faɗin
"Will you marry me (Shin zaki iya aurena)"

Sam ta rasa a wata duniyar ta ke ciki, tana fata idan mafarkine ta yi gaggawar farkawa, kallon gefe da Jiddah ke tsaye ta yi, gira ta ɗaga

1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment