Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiyar zuciya irin na wanda ya farfado daga suma. Miƙewa yayi zaune yana ƙara fashewa da wani sabon kukan duk da rarrashin da Abdallah ke mai amma bai dakata ba, dan haka ya barshi ya cigaba da kukan har yayi mai isarsa, a lokaci anfara kiraye kirayen sallar magriba dan haka suka mike don zuwa masallaci.
Sai da suka yi sallar isha'i sannan suka kuma nufowa gidan.
Sai da aka kai ruwa rana kafin Daddy ya sauraresu, nan Abdallah ke basu labarin abinda Hajara ta aikata, Momi kam taso a kama Hajara a kulle amma Daddy ya ce yanzu abu ya wuce ba za'a tada shi ba. Daƙyar da siɗin goshi suka yafewa M.J laifukan da ya musu sannan Daddy ya jadda mishi cewa lallai ya samu Zarah ya nemi gafararta idan ba haka ba kowa rayuwarshi tana cikin haɗari.
Abu da mai neman kuka jin Daddy ya ambaci sunan wacce yake muradin gani yasa yayi ta taɓa Abdallah kan ya tambayi Daddy inda Zarah take, gyaran murya Abdallah yayi sannan yace

"Emm Daddy ko za'a gaya mana inda ita Zarah take sai muje har can mu bata haƙuri. Bayan haka kuma muna so a sasanta inda rabo ta koma gidanshi."

"A sasanci me Abdallah?" Momi ta faɗa a firgice harda dafa ƙirji kamar wacce taga mugun abu.

Kai M.J ya sunkuyar shi kuma Abdallah ya fara sosar kai.
Murmushi Daddy yayi sannan ya ce

"Ai Zarah ba bare bace duk inda take ma ai zata dawo gida idan tazo sai ya nemi afuwarta, sannan maganar sasantawa banaso na ƙaraji dan babu aurenshi akan Zarah maganar da akeyi yanzu ma ƙarshen satin nan za'a kawo sadakinta daga masarautar Yola dan ɗan sarki ke nemanta na daɗe da bashi umarnin hira saboda sun kawo kuɗin nagani inaso. A taƙaice dai a janye wannan maganar banson kuma jinta kunsan babu kyau neman aure akan aure".

Daga haka Daddy ya sallamesu, M.J ji yayi gabaɗaya duniyar ta mishi zafi, Allah ba azzalumin bawanshi bane, a yanzu yana ji a ranshi lallai idan ya rasa Zarah ba zai iya cigaba da rayuwa ba.

A haka ya tattaro kayansa gabaɗaya ya dawo gidansu ya tare a tsohon sashinsa. Yawan rashin lafiya da yake fama da ita musamman ciwon ƙirji da matsanancin ciwon kai ne yasa ya yanke shawarar zuwa asibiti don duba lafiyarshi.
Gwajin farko likita ya tabbatar mai ya kamu da ciwon zuciya kuma ya kai matakin ƙarshe komai na iya faruwa da shi idan har bai kula ba, a haka likitan yayi mai gwaje-gwaje sannan ya bashi magunguna tare da shawarwari akan matakin da zai ɗauka na rashin sanya damuwa a rai. Da haka ya dawo gida.

Tsawon lokaci yana fama da jinya babu wanda ya sani sai Abdallah shima kuma ya hana ya faɗama kowa, haka yake fama da matsanancin ciwo, baya yin sati ɗaya cikakke batare da ciwon ya tashi ba saboda damuwa da ya sakama kanshi akan Zarah musamman yanzu da ya tabbatar tana gab da kubce masa. Yana galabaita sosai idan ciwon nashi ya motsa don aman jini yake yi sosai amma duk da haka bai sanar da kowa ba.

Watarana irin haka da ciwon nashi ya tashi lokacin yana gida a sashinsa, nan yayi ta aman jini har ya suma, a haka Abdallah yazo gidan ya same shi aikuwa bai ɓata lokaci ba ya sanarwa su Daddy nan aka ɗaukeshi zuwa asibiti hankali a tashe. Sosai Daddy ya ma Abdallah faɗa jin abinda likita ya faɗamai na cewa ya daɗe da cutar a jiki kuma suna zuwa karɓar magani.

Ko da ya nemi jin ba'asin ciwon daga gurin Abdallah kai tsaye ya shaida mishi cewa akan Zarah ne, duk da likita yace a nemowa M.J abinda yake so amma sam Daddy yace baisan wannan zance ba indai akan Zarah yake wannan ciwon sai dai ya ce Allah ya jiƙansa da Rahama dan kuwa ba samunta zai yi.
Nan likita ya bada shawarar sai anfita dashi ƙasar waje anyi mai aiki don kuwa a yanzu zuciyarsa na gab da bugawa, abu na kuɗi nan Daddy ya fara shirye-shiryen fitar da M.J zuwa ƙasar India don ayi masa aikin zuciya.
Hankalin Momi da Baaba ya tashi sosai jin abinda ya samu Jawwad din nan Daddy yayi ta tausarsu daƙyar ya samu suka ɗan kwantar da hankali.

*****************************

Duk yadda Zarah taso dawowa Nigeria hutu abun ya faskara saboda jarrabawar ƙarshe da zatayi don haka dole ta zauna ta fuskanci karatunta dan fitowa da sakamako mai kyau, watanni uku kaɗai suka rage mata ta gama wannan course ɗin mai mahimmanci dan haka tana buƙatar ta ƙara ƙaimi. A gefe guda kuma soyayyarsu da Safwan na ƙara ƙarfi sosai ta yadda har mutane na mamakin irin son da suke yiwa juna dan basa iya ɓoyewa ko a gaban wa suke.
Maganar aurensu tayi nisa dan har ankai sadaki kamar yadda Daddy ya faɗa sannan a tsaida ranar aurensu watanni huɗu masu zuwa, kenan wata ɗaya bayan Zarah ta kammala karatun da take yi a yanzu.

Ammi kuwa tunda aka saka ranar auren ta ɗauko mai gyara guda tun daga Maidugurin Nigeria ta kaita har ƙasar Malasia don gyara mata ɗiyar ta ta. Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu dan a cikin satin kafin Ammi ta wuce Egypt ita kanta ta yaba da irin canji da ta fara gani tattare da Zarah don haka gargaɗi matar akan kada ta bari Zarah da Safwan su dinga yawan haɗuwa gudun aikin shaiɗan. Da haka ta musu sallama ta wuce Egypt.
Gyara sosai Matar mai suna Hajiya Jamila keyiwa Zarah lokaci ƙanƙani ta koma tamkar wata baturiya ko balarabiya saboda tsananin kyau da sheƙi da take fitarwa.

Duk wani shiri na fitar da M.J ƙasar waje an gama shi, inda abokinshi na kwarai Abdallah yace dashi za'ayi tafiyar dan ya dinga kula da shi. Sati na zagayowa suka ɗaga zuwa ƙasar India, sai dai kafin tafiyarsu Daddy ya kira Sadiq ya shaida mishi halin da ake ciki, sosai Sadiq ya tausaya mishi sannan yayi mai fatan samun sauƙi sai dai bai faɗawa Zarah ba, ko meye dalili oho.
Dake sun riga sun gama komai ta internet yasa har airport motar asibitin ta zo ta ɗaukesu, babu ɓata lokaci kuma aka fara baiwa M.J kulawar likitoci, irin asibitocin nan ne da ba'a buƙatar masu jinya dan haka su Daddy na gama duk cukucukun asibitin suka nemi masauki dan hutawa.
Kullum sai dai su shirya su je da safe su dubashi su dawo sannan da yamma su ƙara komawa.
Satinsu ɗaya a ƙasar jikin M.J ya fara samowa dan har yana iya bude idon sannan yana motsi da jikinsa ba kamar a Nigeria ba da tunda ya suma bai ƙara motsawa ba saboda rashin isassun kayan aiki a ƙasarmu.
Kwanansu goma aka yiwa M.J tiyatar kuma cikin sa'a akayi lafiya ba tare da ansamu wata matsala ba sai dai fatan a kiyaye gaba. Sai da ya kwana tara cur! Kafin aka basu damar sake ganinsa kuma Alhamdu Lillahi yaji sauƙi sosai sai dai rama da ya yi. A ranar har video call sukayi da su Momi wanda tunda suka bar ƙasar kullum sai sun kira fiye da goma, har Ammi ma takan kira wajen sau biyar a kowacce rana don jin yanayin jikin Jawwad ɗin.
Wata ɗaya Daddy yayi a India ya tattaro ya dawo gida ya bar Abdallah don kulawa da M.J saboda shirye-shiryen bikin Zarah da za'ayi nan da watanni biyu da satikai ( Su Daddy manya kana namiji mai ya haɗaka da wani shirye-shiryen aure, kodayake ƴar so za'a aurar).
Kafin tahowarshi sai da ya zaunar da Jawwad ya mishi faɗa sosai tare da nasihohi sannan yace ya cigaba da neman zaɓin alkhairi a gurin Allah ya rabu da batun Zarah tunda dai ita Allah ya ƙaddara ba zasu sake zama da juna ba.

Kuma da alama nasihohi da tunatarwan da Daddy ya mishi sun shige shi don yanzu baya yawan tunani da sanya damuwa a rai sai dai sonta na nan danƙare a cikin zuciyarsa babu alamun zai ragu ko ya sassauta mishi.
Da haka suka yi sallama ya taho gida.

Sati uku tsakani aka sallami M.J nan suka tattaro suka dawo Nigeria da tsauraran ƙa'idoji da likitoci suka gindayawa M.J.

Alhamdulillahi jikinshi yayi sauƙi sosai a fili amma cikin ransa kam baiji sauƙi ba, wani lokacin yakan kulle kansa a ɗaki yayi ta kuka da nadamar abubuwan daya aikata ma Zarah gashi yanzu Allah ya bi mata haƙƙinta cikin lumana sai dai bai bari an fahimci halin da yake ciki ba duk da haka sai da Momi ta fahimta kuma ta tausayawa ɗan nata sosai, shiyasa duk abinda mutum zaiyi kada yasa son zuciya a ciki domin shaiɗan zai iya kaishi ya baro shi.


*******Duk da a gajiye take sosai amma hakan baisa can ƙasan ranta takejin daɗi sosai ba, saboda a yau ne ta kammala jarrabawarta na course din da aka turota yi dan haka ne take jinta tamkar ta sauke wani icce mai nauyi akanta.

A matuƙar gajiye ta isa gidan nasu, falon shiru kamar ba kowa a gidan sai dai ta jiyo motsi a kitchen wanda ke tabbatar mata Mama Jamila ce dake sunan da take kiranta dashi kenan.
Jakar hannunta ta wurga kan kujera sannan ta zauna ta tsiyayi ruwan da ta gani a center table ta kafa kai tana sha, ƙarar da wayarta keyi ne yasa ta ajiye kofin ta ɗaga kiran cikin mamakin wanda ke kiran.
A zabure ta mike jin abinda aka faɗa cikin wayar....✍🏻


*BY*
*JASMINE🌸🌸*

*ASP ZARAH*

*BOOK 2*

_About to end_🥰

Wani irin tsalle ta daka tare da ihu sannan ta tsagaita ta ce

"Wayyo Allah na zama uwa Sa-Jid me muka samu ne."

Daga ɗaya ɓangaren Saleem yayi dariya kana ya ce

"An samu baby girl"

"Masha Allah, a gaida Baby da mamanta. Allah ya raya mana ita bisa tafarkin addini. Zan taho zuwa jibi insha Allah."

"Ahh har kin gama jarabawar ne."

"Wallahi na gama ɗazu, idan ta tashi kace zan kirata."

"Tom sai anjima."

Wani daɗi take ji a ranta tana yiwa Allah godiya daya sauki Jiddah lafiya, inda tayi farinciki ma ta gama jarabawarta dan haka tafiya Nigeria bazai mata wuya ba.
Lambar Sadiq ta kira ta shaida mishi aikuwa shima yayi murna sosai dan cewa yayi kafin ya dawo gida zaije ya fara nema musu visa zuwa gida.

Sanda Safwan yaji labarin tafiyarta kuma cewa yayi sam baisan zancen ba dole shima ya bisu su koma tare.

Kwanaki biyu a tsakani suna ta shirye-shirye zuwa Nigeria, duk abinda Zarah ta fita ta gani indai na yara ne sai ta siyawa Baby gefe guda Safwan na taya ta, tun Sadiq na tsokanarsu yana faɗin na marmari har abin ya wuce ƙarfin tunaninshi dan Safwan ko ƴar sa ce iya siyayyar da zaiyi mata kenan.

Ana saura kwana biyu suna suka iso Nigeria,a Gombe jirginsu ya sauka har Safwan dan yace sai angama shagalin suna zai wuce Yola(Kome ya haɗashi da shagalin suna oho). Tarba ta musamman Momi ta musu da ƙayatattun abinci, sosai taji daɗi ganin yadda ƴarta tayi kyau sosai alamun kwanciyar hankali ya bayyana a jikinta, gefe guda kuma ga irin soyayyar da Safwan ke nuna mata dan har a gaban su Momi ba ya kunya musamman da suke mutane ne masu barkwanci.

Sai da suka huta sannan aka haɗu a dinning dan cin abinci. Duk wannan wainar da ake toyawa M.J baisani ba saboda ba shi da labarin Zarah zata dawo don ba'a gaya mishi ba, yaushe ma ya zauna har da za'a faɗa mishi.
Kullum da safe idan ya shigo ya gaishesu Office yake wucewa bayan ya ɗan tsakuri abinci kaɗan wani lokacinma baya iya ci, da Yamma ma idan ya dawo zai shigo yakan jima wani lokacin dan watarana harda shi ake yi dinner.
Kasancewar su Zarah tafiyar safe suka yi yasa baisan da isowarsu ba.


Sosai Baaba ke tsokanar Safwan tana mishi hira lokaci guda. Suka saba tamkar dama sun shekara a tare kodayake haɗuwar fuska ce kawai ba su yi ba.

Bayan Sallar la'asar ne suka shirya zuwa gidan Jiddah harda Sadiq wanda sai da ya gama ƙorafi kafin Momi ta lallaɓashi su tafi tare.
Shiga me kyau suka yi dukkansu, daga nesa idan mutum yaga yadda Zarah da Safwan suka jero ko maƙiyine sai ya yaba da yadda suka dace da juna.

A daidai wannan lokacin kuma M.J na zaune a office yana aikin tunanin daya saba yi na Zarah, lokaci guda yaji ƙirjinsa ya buga da ƙarfi har sai sa ya durƙusa ya dafe gurin, jin kamar ciwonshi zai tashi ne yasa ya mike ya lalubi key ya fita dan zuwa gida saboda magungunan shi duk a gida ya ajiye.
A hankali yake tuƙi har ya iso gaban wawakeken gate din gidan nasu, me gadi ya buɗe masa ya kunno kan motar cikin gidan.
Ai kuwa idanunshi suka yi mugun gani.

Zarah ce tsaye sanye da doguwar riga ba atamfa me kyau, kanta na yane da wani gyale me duwatsu a jiki, gefenta kuwa Safwan ne cikin wank tsadadden yadi kalar fari da hula ɓaka a kansa. Sun yi kyau sosai Sadiq na tsaye a gabansu yana ɗaukarsu hoto duk suna dariya.


Duk da sun ganshi amma sai suka yi biris suka gama abinda suke yi Sadiq ya jasu suka fice daga gidan, jiki ba laka haka ya shige sashin sa a lokacin har jiri ya fara ɗebarsa aikuwa yana shiga ya zube akan doguwar kujera lokaci guda kuma tari me karfi ya turneƙeshi sai kuwa aman jini ya biyo baya.
Ya daɗe cikin wannan yanayin kafin ya samu lafawar ciwon ya mike dakyar ya watsa ruwa sannan ya fito ya sha magani ya fara gyaran gurin da ya ɓaci bayan ya gama ne ya jona ruwan zafi a ƙaramin kofi ya haɗa tea me kauri yasha. Sannan ya kwanta da niyyar hutawa sai dai abu ya gagara domin daya runtse ido hoton Zarah da Safwan ne ke mishi yawo a kwakwalwa.
Ajiyar zuciya me karfi ya sauke dan ya tabbar indai Safwan shine mijin da Zarah zata aura tayi sa'a don hatta shi da yake kyakkyawa babu abinda zai nunawa Safwan din indai wajen kyau ne ko kuma cikar sura, gashi kuma an faɗa mai ɗan gidan Sarauta ne dan haka dole ya koyi yadda zai rarrashi zuciyarsa akan Zarah dan tun farko shi ya jama kanshi.

A haka har wani wahalallen bacci ya ɗaukeshi.


Ɓangaren su Zarah kuwa sosai Jiddah tayi farin cikin ganinsu musamman aminiyarta, sai koɗa yadda Zarah ta koma take yi har tana faɗin itama za'a haɗa da ita a musu gyaran amarcin, sun yi godiya sosai da irin kayan da suka narka musu. Nan su Sadiq suka bar Zarah ta ƙarasa yininta sai dare suka dawo suka ɗauke ta nan suka dawo gida.

Sai dare kafin Daddy ya samu ganawa da ƴaƴan shi da kuma sirikinshi, yayi murna sosai da zuwansu musamman da ya fahimci hankalinsu kwance ya ke babu alamar damuwa a tattare da su.
Sun jima suna hira kafin kowa ya nufi makwancinsa.


Kwanciyarta kenan a kan gado taji ana kwankwasa ƙofar ɗakinta, a tunaninta Momi ko Baaba ne amma tana buɗewa taga M.J tsaye cikin farar jallabiya, ƙofar tayi nufin rufewa amma yasa hannu ya dafe sannan ya tura da ƙarfi ya shiga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe, kallon tuhuma take binshi da shi bai ko kula da yanayinta ba ya durƙusa a gabanta ya haɗe hannayenshi guri guda ya fara magana

"Bansan dame zan fara ba, nasan nayi miki kuskuren da ban cacanci ki yafemin, amma gani a gabanki na cire duk wani girman kai ina roƙonki dan Allah ki yafemin abubuwan da na aikata a gareki bansan da wasu irin kalmomi zanyi amfani da su wajen baki haƙuri ba. Ki taimaka ki yafemin ko zanga haske a rayuwata. Dan Allah wallahi nayi nadamar komai dana aikata miki."

Tsaki tayi a fili sannan ta ce.

"Malam tashi ka ficemin a ɗakina dan Allah ba zan yafe ba ɗin."

Ƙafar ta ya riƙo hawaye na bin fuskarsa ya ce

"Nasan laifukana a gareki masu girmane ki taimaka badan halina ba ki yafemin."

"Wai meye haka sakar min ƙafa karka jamin abin kunya ko ka manta mijin da nake shirin aura na cikin gidan nan ne "

Me neman kuka an jefe shi da kashi awaki, nan take yaji zuciyarsa ta masa nauyi saboda ambatar Safwan da tayi aikuwa kamar yadda ya saba idan ranshi ya ɓaci, tari ya fara a hankali har yayi yawa jini ya fara biyowa bayan, hankalin Zarah ne ya tashi ganin yadda yake ta aman kuma najini gashi dare yayi tasan motsi kaɗan za'a iya jinsu. Tsugunawa tayi a gabanshi ta tallabo fuskarsa da hannayenta cikin murya irin na masu raɗa ta fara magana hankali tashe.

"Dan Allah kayi haƙuri ka tafi a ɗakinnan wallahi na yafe maka duniya da lahira duk laifukan da kayimin da wanda nasani da wanda bansani ba wallahi duk na yafe, kaji dan Allah bari na taimaka maka ka tashi."

Idanunshi a lumshe yaji wata irin nutsuwa ta sauka mishi lokaci guda, abu biyu ne sila na farko yafiyar da yaji ta ambata a gare shi abu na biyu kuwa a karo na farko ta taɓa shi da lallausan hannayenta kuma cikin kulawa take maganar.
Wani yanayi ya tsinci kanshi a ciki lokacin da ta dafa kafaɗarshi tanason mikar dashi tsaye, ganin ta kasa ne ya sashi mikewa ya kalleta cikin ido ya buɗe baki da niyyar magana tayi saurin saka hannu ta rufe mishi baki dan a tunaninta zai iya yin wani aman dan haka tace

"Ba sai ka godemin ba ka tafi kawai"
Jiki ba kwari ya fice a ɗakin ya barta tsaye cikin tunanin iri iri, sosai taji tausayinshi ya kamata kasancewarta mace me rauni sosai, wannan wata irin lalura ce ta samu M.J haka gaskiya yana cikin wani hali da ya kamata a tausaya mishi. Har cikin zuciyarta ita kam ta yafe mishi dama can bata rikeshi da komai ba.

A wannan dare kusan kwana tayi idonta biyu da tunanin M.J a ranta.

Washegari kuwa da manyan baƙi suka tashi don Ammi ce da Rahama suka diro ƙasar tun safiya, murna kuwa a gurin Zarah kamar ta shiɗe. A ranar haka suka wuni cikin walwala da yamma kuma suka wuce gidan Jiddah dan acan zasu kwana saboda aikace-aikacen suna da za'ayi washegari.

Mutanen sunyi mamakin karar da Jiddah tawa Zarah kodayake ba mamaki idan aka duba irin shaƙuwar dake tsakaninsu. Yarinya dai taci suna Fatimah Zarah za'a dinga kiranta da Amrish.
Suna ya ƙayatar sosai uwa da ƴa sun samu kyaututtuka na ban mamaki, a haka aka watse taron kowa ya tafi da souvenirs da aka yi.

Saleem bai yarda a tafi da Jidda wankan gida ba dan haka ne aka nemi wata daga cikin danginsu ta zauna da ita.

Kwanaki biyu tsakani Safwan ya shirya tafiya Yola sai dai zai jira Yayanshi da yazo Gombe aiki ya gama su tafi tare. Tun ranar da yazo basu haɗu da Safwan ba sai ranar tafiyarsu gida ya taho gidansu Zarah dan gaisawa da surukan ƙaninshi.

Rabon kwaɗo ko a ruwa zafi yake baya wucewa, Tunda yayi arba da Rahama zuciyarshi a karo na farko ta gamsu da ita yaji yana sha'awar ƙulla taraiya ta har abada da ita.
Bai bayyana hakan ba sai a hanyarsu yake shaidawa Safwan aikuwa yayi murna sosai inda yace zai sanar da mai martaba a haɗa aurensu tare.

Sanda iyayensu suka ji wannan batu sunyi murna matuka musamman da kullum burinsu bai wuce suka Mahmud yayi auren ba, babu wani jan lokaci dan sun yanke shawarar a haɗa auren biyu indai ya tabbata, ko da Mai martaba ya kira Daddy ya tambayeshi ko anyiwa Rahama mijin cewa yayi a'a amma zai tambayeta ko akwai wanda take so, Alhamdulillah bai sha wuya da Rahama ba ta gayamai babu wanda ta tsayar dan haka ya kira Mai martaba ya shaida masa.
Kwanaki uku tsakani aka hado lefe da sadakin Rahama aka kawo inda aka tsaida biki rana ɗaya da nasu Zarah wata ɗaya da sati biyu masu zuwa.
Murna kuwa ba'a magana, nan Ammj ta ƙara zagewa ta fara gyara ƴaƴan nata na musamman.

Shidai M.J ya daina jinya a fili sai a zuciya, yana matuƙar galabaita sosai dan ya rame yayi haske kamar wanda ke gargarar mutuwa.

*********************************


Kwanci tashi asarar mai rai, yau gashi har an shiga satin da za'a fara shagalin bikinsu Zarah, duk wasu shirye-shirye da suka kamata anyi. Kuɗi kuwa tamkar ba nemansu ake yi da zafi ba yadda ake fiddasu kamar ba'asu.

Daga masarautar su Safwan kaɗai miliyon goma aka turo na gyaran amare banda manyan akwatuna da aka ciko da kayan fitar biki masu tsadar gaske.

Ɓangaren su Daddy ma shirye-shirye ake yi sosai dan Daddy kwarai yake son nuna su Zarah na da gata duk da ubansu baya raye, shikanshi sai da ya musu akwati bibbiyu ya shake da kaya na fitar biki bayan kayan ɗaki da suka shirya da Momi da Ammi suka je har Italy dan siyowa, hatta cokali abin banza a ƙasar waje aka siyo musu komai nasu daga can ne.
Baaba kuwa tayi faɗan harta gaji amma sunƙi dainawa.

Babban Yaya kuma wani danƙareren Boutique ya gina musu wanda aka cikashi da kayan siyarwa na manyan mutane da ko a ƙasar waje sai haka, inda aka shirya taron buɗeshi ranar da za'ayi bridal shower ɗin amaren, bayan haka sai da ya saka musu makudan kudi a cikin account dinsu.

Tun ranar Monday aka fara gudanar da shagulgula inda akayi Welcoming dinner ranar monday a farfajiyar gidan Daddy an kashe kuɗi sosai amare kuwa sun sha kyau tamkar a sace su a gudu, washegari ranar talata kuma akayi Fulani day mai ban sha'awa dan harta mutanen Yola sai da suka zo a jirgi bayan angama ya kwashe su ya kuma, Ranar laraba kuma akayi shagalin buɗe Boutique ɗinsu Mai suna *RAHAZAR BOUTIQUE* wanda ya samo asali daga farkon sunan kowaccensu.

Washegari Alhamis ne za'a gabatar da Reception kuma a ranar Safwan da abokansu zasu taho Gombe dama shi Mahmud tun ranar Monday yake nan saboda wani taro da suka gabatar shiyasa bayan an kammala yayi zamansa kawai tare da wasu daga cikin abokanansu.

Fitowar Zarah daga wanka kenan saboda bata tashi da wuri ba dan gajiya dama kuma tana fashin Sallah, turo ƙofar akayi a hankali kanta ta maida kan me shigowar Sadiq ne da Daddy suka shigo kallo ɗaya zaka musu ka gane tsantsar damuwa a tattare da su. Hijab ta ɗauka ta zura sannan ta gaida Daddy bai amsa mata ba illa zaunar da ita da yayi a gefen gado ya fara magana kamar....✍🏻


*BY*
*JASMINE🌸🌸*

*ASP ZARAH*

*BOOK 2*

Nasiha sosai Daddy ya fara mata me ratsa jiki, ƙirjinta ne ya fara dukan uku saboda yadda taji yana ambatar karɓar ƙaddara, ko wacce ƙaddarar ce ta kuma samun rayuwarta, tunaninta ya katse sanda taji Daddy na faɗin

"Zarah haƙuri da juriyar da na sanki dashi a wannan karon ma shi nakeso kiyi sannan ki rungumi ƙaddarar da Allah ya ɗora miki da hannu biyu. Kiyi haƙuri Zarah yau da asuba Allah yayiwa Safwan mijin da zaki aura rasuwa sakamakon ciwon ciki da ya kulleshi a jiya da dare."

Tamkar saukar aradu haka taji maganar Daddy a kunnuwanta bata kyma gaskatawa ba sai da taji ɗan uwanta na maimaita batun Daddy ɗin.

Bata kuma sanin inda kanta yake ba sai buɗe ido tayi ta ganta kwance a gadon asibiti da ƙarin ruwa a hannunta, a hankali ta fara juya idanunta tana ƙarema inda take kallo da mutanen dake wajen, mutum uku ta gane a cikinsu Baaba, Jiddah sai Rahama da suka yi wujiga-wujiga alamun tashin hankali ya bayyana a garesu, ƙoƙarin mikewa ta farayi da sauri duk suka ƙaraso inda take suna mata sannu bata kula ba ta fara magana tana cewa

"Dan Allah kuce mafarki nayi na zahiri bane dam Allah kada kucemin Safwan ya rasu bazan iya rayuwa batare dashi ba, wayyo Allah shin wani zunubi na aikata a rayuwata da nake ganin irin waɗannan kaddarori." Kuka mi cin rai ta fashe da shi me cin rai.

Gabaɗaya tausayinta ne ya kamasu su kansu rasuwar Safwan ta jijjigasu matuƙa bare ita kuma da kowa ya zauna da su a ɗan ƙanƙalin lokacin nan zai fahimci irin ƙaunar da suke wa juna. Kwananta biyar kenan a kwance batasan wanda yake

1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment