Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta ba tun ranar da aka faɗa mata batun rasuwar Safwan ɗin. Bayan su Daddy sun kawota asibiti ne suka bi jirgi zuwa garin Yola dan jana'izarsa, kwanansu biyu suka dawo kuma kafin su dawo sai da aka ɗaura auren Rahama da Mahmud sannan Zarah da Jawwad dan Mai martaba ya ce baza'a ɗaga auren ba sannan shi da kanshi ya baiwa Daddy shawarar a ɗaura aurenta da Jawwad ɗin sannan yace shi da kanshi zai zo ya taushi Zarah idan anyi sadakar bakwai sai dai an dakatar da shagulgulan da aka shirya.

Kuka takeyi sosai harda shiɗewa suna bata baki ganin taƙi yin shirune yasa Jiddah ta kira likita yana zuwa kuwa ya mata allurar bacci nan bacci ya ɗauke ta sannan ya cigaba da dubata.

Sai da Zarah ta yi wata guda a asibiti kafin ta fara dawowa daidai tare da sakawa ranta cewa lallai Safwan ya tafi ya barta saidai ya barta da rauni a zuciyarta da bazata taɓa warkewa ba, ta kuma shiru shiru sam bata son hayaniya kullum cikin jan carbi da karatun alqur'ani take yi, a haka likita ya bata sallama bayan nasihohi da aka mata.

A ranar da Safwan ya rasu harda M.J da Abdallah suka shirya zuwa jana'izarsa. Kuma a gabansa aka ɗaura aurensa da Zarah, a ranar ji ya yi tamkar mafarkan da ya saba yi ne yake yi, babu kalar addu'ar alkhairi da bai yima mai martaba ba godiya kuwa har saida ya dakatar da shi, kwana yayi yana sallar godiya ga Allah da kyautar da yayi masa a lokacin da ya cire tsammanin samu.
A haka suka gama kwanaki uku suka baro Yola zuciyar M.J cike da farin ciki sai dai a ɓangare guda yana taraddin yadda zai fuskanci Zarah ko da wani idon zata kalleshi idan taji labarin ya zama mijinta a karo na biyu.
Kullum sai yaje asibitin dan dubata sai dai yafi zuwa lokacin da yasan tana bacci, tana bashi tausayi sosai saidai a ɓangare guda yana kishi idan ya tuna saboda wani take yin wannan jinyar.


Kwanaki biyu da sallamo Zarah Mai martaba da tawagarsa suka zo, da kanshi ya nemi ganawar sirri da Zarah, shima dai nasihar ya mata sosai kafin daga baya ya shaida mata batun aurenta da Jawwad, aikuwa nan hankalinta ya ƙara tashi ta fashe da kuka, roƙonta mai martaba ya shiga yi dakyar ya samu ta sassauta bayan ya shaida mata yau yake so dukkansu a wuce dasu ɗakin mazajensu dan dama Rahama tare da masu ɗaukarta suka zo. Nisawa yayi ganin yadda take risgar kuka yace

"Fadimatu bawai shawararki nake nema ba ina baki umarni ne a matsayina na uba gareki indai kin bani wannan matsayin. Kiyi hakuri da yadda ƙaddara tazo miki mun sani duka cewa kina halin da yakamata a tausaya miki amma hakan da aka miki shine gata kuma zai rage miki raɗaɗin abinda kike ji. Ki sani cewa a yanzu Safwan babu wani abu da yake bukata a gurinki face addu'a sannan bazai taɓa yin farin ciki ba matuƙar kika bijirewa iyayenki saboda kawai son da kike mishi sannan bazai ji dadi ba idan aka tada ki ranar alkiyama a matsayin wacce bata bin umarnin iyayenta, a yanzu akwai auren wani a kanki tunanin Safwan da irin soyayyar da kukayi ba shine mafita a gareki ba domin dai hausawa sunje matar mutum kabarinsa, dama can aurenku da Safwan babu shi cikin lauhul mahfuz, ta iya yiwuwa akwai tanadin da Allah ya muku a lahira shiyasa bai saka kun zama ma'aurata a duniya ba. Shi kanshi Safwan ba zaiji dadin kwanciyarsa a cikin kabarinsa ba matuƙar kin take dokar Allah saboda kawai son da kike mishi. Matukar kin bani wannan matsayi na mahaifi dan Allah Zarah ki amince da wannan auren sannan ki rikeshi hannu bibbiyu dan samun rabauta duniya da lahira, shin zaki iya yimin wannan alfarmar."

Cikin sheshsheƙar kuka ta gyada kai sannan tace

"Na aminci Baba zanyi amfani da duk abubuwan da ka fadamin sannan zanyi ƙoƙari na cigaba da ɗaukan hakan a matsayin ƙaddarata."

Kalamai masu taushi ya cigaba da gayamata har saida yaga hankalinta ya kwanta sannan ya kira sauran mutanen gidan yayi musu maganganu masu ratsa jiki musamman M.J dan kusan gabaɗaya fadan akanshi ne, da haka ya baiwa sauran iyayensu damar magana shikam Daddy ya kasa furta komai dan gani yake kamar a yanzu bashi da wata kima a idon Zarah dan kila zatayi tunanin saboda yana son ɗanshi ne kawai ya saka aka ɗaura auren.

Duk shiru sukayi kafin Momi ta bude baki ta ce

''Muhammad Jawwad a matsayina na mahaifiyarka matuƙar ka ƙuntatawa Zarah a gidan aurenka ban yafe maka ba duniya da lahira ko bayan bana raye." daga haka ta mike ta fice a falon. Kai kawai mai martaba ya kada sannan yasa aka kira mishi matan da suka zo tare ya shaida musu su shirya Zarah su fara kaita ɗakinta kafin su zo su wuce da Rahama zuwa Yola.

Haka kuwa akayi da taimakon Ammi da Jiddah suka shiryata fes ta fito amarya sai dai kallo daya zaka wa fuskarta ta baka tausayi saboda yadda ta kumbura lokaci guda tayi jazir saboda kukan da take yi.
Sam Baaba da Momi sunki yarda suyi Sallamar ƙarshe da Zarah shikuwa Sadiq hannunta kawai ya riko ya kaita har ciki sabuwar motar da Daddy ya siya musu ta fitar biki ita da Rahama ya zaunar da ita a ciki sannan ya rike hannunta gam yace

"Ki sani a kowani lokaci zan kasance tare da ke sannan bazan taba bari a cuceki ba a wannan karon matukar akayi yunkurin hakan sai inda karfina ya kare akanki, banaso ki saka damuwa a ranki ki cire komai ki saka a ranki cewa ibadah zakije yi sannan ibada dole sai da sadaukarwa. Zan kasance a tare da ke a kowani lokaci."
Hannu ya saka ya share mata hawayen fuskarta sannan ya sake hannunta ya rufe motar ya ja hannun Rahama dake fama risgar kuka suka shige cikin gidan.

Basu jima sosai a gidan Zarah ba suka yi niyyar komawa saboda tafiyar dake gabansu, hakuri sosai Ammi ta kara bata kafin su bar gidan, itama dai Jiddah bata zauna ba duk da taso hakan amma Ammi ta hana. Haka suka tafi suka barta ita ɗaya tana aikin kuka.


Rahama ma haka aka tafi da ita cikin kuka da kewar rabuwa da gida musamman Ammi dan daƙyar aka rabasu saboda shaƙuwar dake tsakaninsu. A haka aka wuce da ita zuwa airport jirginsu ya daga zuwa garin Yola.
Sai fatan zaman lafiya mai ɗorewa.



***************************


Zaman dai na Zarah da Jawwad ba'a magana dan kuwa zamane na doya da manja sai dai yana iya bakin ƙoƙarinshi dan kyautata mata dan da gaske yake son gyara laifukanshi na baya.

Kullum safiya shi ke gyara ko'ina na cikin gidan daga falo har sauran ɗakuna hatta ɗakin da Zarah take kwana shike tsabtacewa duk safiya idan yazo zai gayamata zai gyara ɗaki sai ta fita zuwa falo ta bashi guri idan ya gama ta kuma, bata kuma fitowa sai idan ya gama breakfast yazo ya gayamata ta fita duk da bawani abincin take ci ba kawai tsakura kawai ta tashi, idan ta gama kuma yazo ya tattare kayan da taci abincin ya wanke kafin ya shirya ya tafi office dan ma dai shine shugaba shiyasa bashi da wata matsala a fannin ƙorafin latti, da rana ma haka duk abinda yake yi zai bari ya siya abinci a resturant ya kai mata.
A haka rayuwar tasu take kasancewa sai dai babu wata alaqa tsakaninsu dan kafin Zarah ta mishi magana ma yana jimawa sosai sai dai idan abu ya kasance mai mahimmanci ne.

A haka aka shirya taron ƙarawa Zarah matsayi a wajen aikinta inda aka bata muƙamin mataimakiyar Commissioner na ƴan sanda a jahar Gombe gabaɗaya, gagarumin taro aka shirya Daddy da kanshi ya kira M.J ya shaida mishi bai ko yi musu ba ya amince inda shima yasha alwashin zuwa batare da yayi tunanin komai a ranshi ba.

Taron ya ƙayatar sosai inda Zarah ta samu manyan kyaututtuka hatta su Daddy sai da suka samu kyautar karramawa a matsayinsu na iyayenta. A haka aka watse taron aka watse.

Sosai hankalinsu Momi ya kwanta ganin babu wata alamun damuwa a tattare da Zarah ga kuma yadda M.J yake bin umarninta kamar dai itace mijin. Sai dai shi kallo ɗaya zaka masa ka gane cewa hankalinshi ba'a kwance yake ba amma tunda ba furtawa yayi ba babu wanda yasan abinda ke damunsa.

Zamansu dai bai canza zani ba dan jiya iya saboda M.J ya maida kanshi tamkar bawa ya cire duk wanj girman kai yana baiwa Zarah kulawa, a yanzu da ta fara fita aiki kullum yana idar da sallar asubahi yake fara aiyukan gidan sannan ya hada musu breakfast. Idan ta gama karyawa kuwa shi da kansa yake ɗaukar mata jaka ya kaita mata mota sannan ya bude mata idan ta shiga ya rufe ya mata addu'ar dawowa lafiya kafin nan ya kuma ciki ya shirya ya tafi nashi aikin.
A haka rayuwar tasu take kasancewa har zuwa tsawon wani lokaci sai dai an samu sassauci dan yanzu Zarah tana gaidashi wani lokacin kuma da kanta take dafa musu abinci musamman idan ta fahimci baya jin dadi dan a zaman su sau biyi ciwonshi yana tashi kuma yana wahala sosai.

Yau ta kasance weekend babu aiki dan haka ne tunda tayi sallar asuba ta kuma ta kwanta saboda tana bukatar hutu dan a satin tayi aiki sosai ta gaji. Baccinta take yi hankali a kwance a haka M.J y shigo dan gyara mata dakin ganin tana bacci ne yasa ya tsaya yana ƙare mata kallo tare da jinjinar girman soyayyar da yake mata, ya dade a tsaye kafin ya fita ya ja mata ƙofar a hankali ya koma kitchen da hada musu abinda zasu karya dashi.

A firgice ta mike zaune jikinta na rawa lokaci guda ta haɗa gumi har tana diga sosai hankalinta ya tashi akan mafarkin da tayi...✍🏻


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*

*BOOK 2*

Take abinda ta gani cikin mafarkin ya fara dawo mata filla-filla sosai hankalinta ya tashi.

Zaune take a cikin wani haɗaɗɗen garden tana zaune tana hutawa iskar gurin na kaɗa ta, a hankali ta fara hango wani haske na nufo inda take har ya iske ta, ware ido tayi sosai ganin iyayenta cikin kyakkyawar shiga sai sheƙi suke yi. Da sauri ta mike da nufi isa inda suke sai kuma ta tsaya ganin Mami ta ɗago mata hannun alamun ta dakata batason ta iso inda suke sannan tace
"Fadimah ashe irin abinda kike aikatawa a gidan mijinki kenan saboda kinga kasa ta rufe mana ido, kenan duk tarbiyar da na baki akan yarda da ƙaddara baki ɗauka ba ko so kike Allah ya azabtar damu saboda kinki bin umarninshi, kinsan a rana sau nawa mala'iku ke tsine miki kuwa akan halin ko'in kula da kikewa mijinki. Ki gaggauta gyarawa dan sauke fushin Allah akanki, nima da kika ganni cikin jindaɗi ba komai bane sila face biyayyar da nayiwa nawa mijin shin bakyaso ki shiga jindadi ki kasance tare da mu a ƙoramar alfarma. Mahaifinki yana fushi dake sosai bayaso ma ya miki magana sai ranar da kika gyara halayenki. Na tafi kiyiwa mijinki biyayya Fadimah kiyiwa mijinki biyayya kiyiwa mijinki biyayya." A nan zancenta ya ƙare saboda hannunta da Abba yaja suka bar wajen, zama tayi a ƙasa tana kuka sosai har na tsawon lokaci kafin taji an dafa ta ɗagowar da zatayi tayi arba da Nusaiba itama cikin shigar alfarma, kafin ta iya furta komai Nusaiban ta ce

"Yaya Zarah kowa yana fushi dake harsu Kaka dake sonki duk sunyi fushi saboda abinda kike aikawata, Kaka ta ce bataso taga kullum mala'iku suna tsine miki dan haka ne ma tace babu ruwanta dake, har su Adeel duk sun daina sonki, nima kawai nazo ne na gayamiki idan baki gyara halayyarki ba bazan kuma zuwa inda kike ba."
Kafin ta ankare ta neme ta ta rasa dan haka ne ta miƙe ta fara tafiya dan barin wajen, tana cikin tafiyane ta hango wani a zaune kan wata kujera ta alfarma sai sheƙi take yi, tsayawa tayi daga nesa tana ƙare mai kallo, juyuwar da zaiyi taga ashe Safwan dinta ne da mugun gudu ta nufi inda dan isa gare shi, Dakata! Shine abinda ya faɗa da ƙarfi sannan ya cigaba da cewa

"Baki kasance cikin masu yarda da ƙaddarar da Allah ya jarabesu da shi ba dan haka karki zo inda nake." bat ta nemi shi ta rasa, kuka riris take yi tana kiran sunayen su amma babu wanda yazo.


Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko daga idanunta, duk da ance mafarki ba gaskiya bane itakam wannan gaskiya ta ɗauke shi dan a fahimtarta iyayenta dake kwance cikin kabari basa jindadin abinda take aikatawa. Amma ya zatayi takasa cire Safwan din a ranta, bawai bata yafewa M.J abinda ya aikata mata bane amma tana jin ciwo ace ta rayu da shi a maimakon Safwan din da take buri.
Sai dai wannan mafarkin lokaci guda ya sauya tunaninta ta saka a ranta cewa zata yi ƙoƙarin ganin ta sauke haƙƙin aurenshi da Allah ya ɗaura mata. Istigfari ta fara tana neman yafiyar Allah dan tasan ba ƙaramin zunubi ta kwasa ba a zamanta da M.J din, shi Allah babu ruwansa da tanaso ko bataso haƙƙin da ya rataya a wuyanta kawai zata sauke idan kuma takasa zunubi ne a kanta, tabbas tasan hukuncin macen da bata yiwa mijinta biyayyah ba a gurin Allah kaɗai hatta mala'iku da sauran halittu kullum cikin tsine mata suke yi.

Kuka ta ƙara fashewa da shi har da sheshsheƙa zuciyarta na mata zafi sosai, M.J dake tsaye gaban Dinning yana jera abinci ya jiyo sautinta ai da gudu ya nufo ɗakin. Tana nan a zaune tana kuka, da hanzari ya nufi inda take yana tambayarta meya faru sai dai bata bashi amsa ba. Zama ya yi yana rarrashinta tare da bata haƙuri dan a zatonshi shine ya mata laifin.
Sun dade a haka kafin ta sassauta kukan tana sauke ajiyar zuciya, toilet ya shiga ya hada mata ruwan dumi sannan yace taje tayi wanka, mikewar da zatayi jiri ya ɗebeta luuu! Ta kuma zata fadi ya tare ta. A hankali ya ɗauke ta ya shigar da ita bayin, da kanshi ya mata wankan ganin lokaci guda zazzaɓi me zafi ya rufeta sai rawar ɗari take yi. Riga kawai ya zura mata bayan ya fito da ita sannan yaje ya hado mata tea me kauri ya haɗo da Paracetamol, dakyar tasha Tea din kaɗan ya bata maganin sannan ta kuma ta kwanta.
Ganin har rana jikin nata yaki sauki ne yasa ya kira Abdallah ya mata allura sannan ya ɗaura mata drip, falo suka koma suna tattauna matsalar M.J din Abdallah na ƙara bashi shawarwari akan wannan ce kaɗai damar da zaiyi amfani da ita wajen sasanta tsakaninsu da Zarah, sun dade kafin ya maj sallama ya tafi.

A takaice dai sai da Zarah tayi sati tana jinya har su Momi sai da suka zo dubata, ranar da Sadiq yazo gaisheta da jiki saida yayi mamakin abinda yaga M.J na yi mata, M.J ɗan kwalisa da shan ƙamshi amma shine ya ƙasƙantar da kanshi akan mace, dan a kitchen ma ya taddashi yana soya wainar fulawa wai Zarah take son ci, tun abin na bashi mamaki har ya koma tausayin M.J din ganin gabadaya bashi da wani lokaci da zai yi abin kansa sai wanda tace dashi, hakan yasa ya musu sallama ya tafi a yanzu hankalinshi ya kwanta da auren nasu.

Shikuwa M.J duk wannan abin da yake yi sam baya damunshi musamman da a yanzu ya samu sake har kwana yake yi a ɗakin Zarah kuma bata hanashi wani lokacin ma har hira suke yi sosai musamman idan suna kallon labarai aka taɓo harkar tsaro nan zasu zauna suna tattaunawa akan halin da ƙasar mu ke ciki ta fannin tsaro.


Da haka zaman nasu ya fara daɗi ko bayan da ta warke, kullum tare suke bacci watarana a ɗakin M.J din ko a ɗakinta, tare suke tashi su kimtsa gidan kowacce safiya dan Zarah ta tubure batason me aiki duk da M.J yaso ya ɗauki me taimakamata dole ya hakura tunda ta nuna bataso. Tare suke fita ya sauke ta a wajen aiki kafin ya wuce nashi wajen aikin idan an tashi ma haka zai zo ya ɗauketa su wuce gida wani lokacin kuma gidan Momi suke wucewa.
Da haka dai har M.J ya hillaceta haƙarsa ta cimma ruwa, aikuwa ranar ya sha kuka da nadamar abubuwan da ya aikata mata har sai da ciwon shi ya tashi, hakuri kuwa har sai da ta nuna zatayi fushi sannan ya daina bata.

Zaman da ya biyu baya babu laifi zamane na aminci da kyautatawa juna duk da har a lokacin Zarah ba sonshi take yi ba kuma bata manta da Safwan cikin ranta ba dan kullum idan tayi sallah sai ta mai addu'a shi da iyayenta da sauran musulmai magabata.

Babu irin gatan da M.J baya mata wani lokaci har tausayi yake bata idan taga irin kulawar da yake bata, komai nashi ita ne duk abinda ya samu ita.

A cikin watannin da suka biyi baya ne watarana M.J ya tashi da wani irin zazzabi me zafin gaske, sosai hankalin Zarah ya tashi dan har sumewa yake yi da ya farfaɗo kuwa zai kuma ba shiri ta kira gida ta sanar sannan ta kira Abdallah suka ɗauke shi sai asibiti.
Kwananshi biyu amma duk allurai da magungunan da ake bashi kamar ba'ayi har anfara tunanin ko ciwon bana asibiti bane.

Ranar da Baaba tazo asibitin ne ta gane ainihin musabbabin ciwon, suna zaune harda su Momi da Jiddah dan lokacin dare ne anyi sallar isha'i ma, kallon Zarah tayi sannan ta kalli M.J ta tuntseri da dariya sosai har tana saukowa daga kan kujerar da take, kallonta suke yi cike da mamaki, Sadiq ne ya rike baki ya ce

"Momi bari na kira likita inajin matar nan ba kalau take ba."

Jin abinda ya faɗa ne yasata tsagaitawa ta kalleshi ta ce

"Zan saba maka fa Habu ni kake dangantawa da taɓin hankali."

"Alama kika nuna ai" ya fada yana kauda kai.

Tsaki tayi sannan ta maida kallonta ga M.J dake kwance cikin ciwo tace

"Wato dai kai Muhammadu da gaske kake so ka zama mijin tace koh? Ita ke da cikin amma kaine kake mata laulayin."

"Laulayi kuma Baaba.?" Momi ta tambaya.

"Yoo ai sai kuyi kuma sau nawa akayk muka gani Zara'u ce fa ke da ciki shi kuma yake mata laulayin cikin dama ana samun haka wasu lokutan idan mata ta samh shigar ciki ta hanyar mijinta kaɗai ake ganewa dan wasu ciwo suke kamar ba zasu rayu ba."

Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuƙatansu babu shiri Momi taja hannun Zarah suka fice kai tsaye sashin da ake bincikar masu ciki ta kaita dan ayi mata awo saboda itakam ta yarda da batun Baaba dan a zamanin baya ma kafin wani daga cikinsu ita da marigayiya yasan yana da shigar ciki Baaba ce take fara ganewa ta fada musu kuma idan anje asibiti a tabbatar.
Kasancewar an sansu a asibitin ne yasa babu ɓata lokaci aka shigar da Zarah ɗakin scanning din aka kwantae da ita sannan aka jona mata na'urorin, mintun biyu tsakani kuwa sai ga hoton cikinta ya bayyanah da ɗa kwance, farin ciki ne ya rufe Momi ba shiri ta fadi acan gefe tayi sujjadar godiya ga Allah.

Wani zuben zinari me matuƙar tsada dake hannunta ta cire ta baiwa matashiyar likitar tukwici.

Basu dawo ɗakin ba sai da aka gama buɗewa Zarah file na masu ciki sannan ta riƙo hannunta suka dawo nan take shaida musu fa akwai cikin a jikin Zarah har na wata hudu ma, hamdala suka fara yi tare da gode ma Allah hatta M.J dake kwance sai da ya mike ya zauna sannan ya riko hannun Zarah dake gefenshi yana zuba mata godiya.
A daren yace bazai kuma kwana a asibitin ba tunda angano silar ciwonshi dole haka likita ya sallameshi suka koma gida inda aka bar Baaba dan kulawa da Zarah.
Sanda Rahama taji labari kuwa tayi murna sosai duk da itama a lokacin tana da ciki har ya shiga watan haihuwa.

Tunda cikin Zarah ya bayyana kuma sai ciwon da M.J yake yi ya ragu nan ya cigaba da baiwa matarshi kulawa baya ko kunyar Baaba dake gidan hakan yasa ta tattara kayanta tabar gidan dan tace ba zata iya zama ayi abin kunya a gabanta ba.

Sati biyu da faruwa haka Rahama ta haifi ƴarta mace. Gabadaya suka tattara suka nufi Yola da sha tara na arziki.
Anyi shagalin suna sosai irin na gidan sarauta,yarinya taci sunan mahaifiyar su Mahmud Zulaihat ana kiranta da Afrah, satinsu guda suka juyo suka bar me jigo cikin kulawar dangin mijinta dan su gidan sarauta basu yarda da al'adar wankan gida ba.

Watan Afrah huɗu da kwanaki Zarah ta sauka lafiya ta haihu ƴan biyunta macw da namiji kyawawa masu kama da ubansu. Farin ciki kuwa ba'a magana a gurin dangi. Nan aka fara cika gidan ƴan uwa da abokan arziki kowa na zuwa ganin ƴan biyu.

Ranar suna kuwa ansha mamaki kwarai sunan da M.J ya sakawa yaran, macen Fadimatul Zarah namijin kuma Safwan inda za'a kirasu da Amrah da Amran. Mutane da dama sun jinjina wannan abu da ya yi, ita kuwa Zarah tayi farin ciki matuƙa har ta kasa ɓoye hakan.

Mai Martaba da kanshi sai da yazo ya yi godiyar wannan kara, inda yawa yara kyautan manyan filaye guda biyu bayan kuma kaya da aka kawo musu.
Yara sunzo da goshi dan sun samu kyaututtuka da dama na ban mamaki.

Kulawa sosai suke samu daga wajan iyayensu da sauran dangi. Musamman mahaifinsu ma daya ɗaura son duniya akansu.

Haihuwar Zarah ba da dadewa ba aka yi auren Sadiq wanda ya tara manyan mutane sosai sannan an kashe kuɗi sosai.

A haka rayuwa ke tafiya awanni na shudewa su bada kwana daga nan satika har watanni.


Watarana su Zarah sun fita shopping, a hanyar dawowarsu ne suka kusa kaɗe wata almajira, ko da suka fita suka duba ba kowa ba ce face Hajara, ƙafarta ɗaya an guntule sai sanda take amfani dashi. Ko da ta ganesu nan ta durƙusa tana basu hakuri sosai tana basu labarin abubuwan da suka faru da ita dan har prison sai da aka kaita sanadin wannan Alhajin daya mata ciki, gashi iyayenta ma duk basu da lafiya suna kwance ƴar uwarta ce kawai ke taimaka musu itama mijinta ya ɗauke ta sun bar ƙasar.
Sun tausaya mata sosai nan M.J ya mata kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan sun yafe mata.

Shekararsu Amran ɗaya da watanni mahaifinsu ya kwanta ciwo zazzabi me zafi ya rufe shi, ba shiri ya ɗauki Zarah suka tafi asibiti aikuwa kamar yadda yayi tsammani tana da shigar ciki na wata biyu murna ce ta kamashi ita kuma Zarah ta nuna sam bataji dadi ba saboda yaranta basuyi girman da za'a yayesu duk da dai babu inda basa zuwa da ƙafarsu sannan kuma suna cin abinci sosai.
Shawarwari likita ya basu na yadda zata kula dasu kafin cikin nata ya girma. Da haka suka dawo gidaa.

Sanda Ammi taji labarin cikin Zarah ta kanta ta shiryo ta taho Nigeria ta ɗauki su Amran ta wuce Egypt da su dama kuma yaran sun santa gashi basa da kiwa ko kadan dan haka ne bata sha wuya da su.

Tabar M.J yana cigaba da rainon cikin matarshi da a yanzu ma yake fatan ta haifo mishi ƴan biyun.


*KARSHE*


*ALHAMDILILLAHI NAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA ASP ZARAH, ABINDA NA FADA DAIDAI ALLAH YA BANI LADARSA INDA NA KUSKURE KUMA INA ROƘON ALLAH YA YAFEMIN.*
*MASOYA INA GODIYA SOSAI DA IRIN ƘAUNARKU A GARENI, ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRANSA YABAR ZUMUNCIN DAKE TSAKANINMU. INA GODIYA SOSAI DA HAKURIN DA KUKAYI DANI TSAWON WANNAN LOKACIN. SON SO FISSABILILLAH*


*KU TSUMAYE NI A LITTAFINA NA GABA DA ZAI FARA ZUWA MUKU NAN DA WANI ƘANƘANIN LOKACI ME SUNA AL-MUSTAPHA. FREE BOOK NE NAYI SHI DOMIN KU MASOYA, YAZO DA SALO NA MUSAMMAN KADA KU BARI A LABARTA MUKU*.



*TAKU HAR KULLUM*
*JASMINE🌸🌸*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya


1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment