Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaku wuce."
Shiru sukayi na wani lokaci kafin Sadiq yace
"Daga nan Malasia zamu wuce, Little zata fara karatun masters ɗinta acan, ni kuma na cigaba da aikina."
Fuska ta sauya kamar zatayi hawaye tace
"Za mu ƙara yin nisa da juna.?"

"Ki shirya mu tafi tare." fadin Zarah.

Hararar wasa ta mata sannan ta kuma cewa
"Na gaji da kawaici fa, tun ɗazu inaso ku ɗauko min hirar abubuwan da suka faru amma kun share."
Dariya suka yi duka sannan Sadiq yace
"Tun ɗazu na lura dake kawai na yi miki shiru ki furta da bakinki."

"Na tambaya yanzu a gayamin meya faru."

"Labari ne mai tsawo fa ki nemo biro da takarda" Inji Zarah.

"A'a bani wannan baiwar sai dai na kira Sis Jasmine ta mana aikin rubutun."

"Tom shikenan haka za'ayi."

"Ke nake sauraro."

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸

Ina cikin tsananin azaba a wannan rana da yaran Alpha suka shigo har gida sukamin rauni amma Yaya Jawwad yaƙi ko kula da lamarina bare yayi tunanin kaini asibiti duk da a lokacin babu dangantakar aure a tsakaninmu amma nayi tunanin zai taimakeni a matsayi na na ƴar'uwarsa sai dai hakan bai kai ga ci ba. Ganin sun bare yashe a falo cikin jini ne yasa nayi ƙoƙarin nafara jan jiki domin zuwa na saka Baba Mai gadi ya kiramin Daddy ko Sa-Jid saboda a halin da nake ciki a wannan lokacin nasan komai zai iya faruwa dani sakamakon jinin da ke zuba daga jikina, da jan jiki na fita har farfajiyar gidanmu zuwa ɗakin Mai gadi sai dai nayi rashin sa'a domin shima sun yi mishi duka bai san inda kansa yake ba. A lokacin nafara ficewa daga hayyacina saboda tsananin azaba da zafin raunukan dake jikina, ina cikin wannan halin ne naji ana horn a ƙofar get ta waje amma bani da kuzarin da zan iya xuwa na buɗe, an daɗe anayin horn ɗin daga baya kuma akazo jikin ƙofar ana bugawa, ganin gate ɗin a buɗe ne yasa su shigowa ba kowa bane illa Sa-Jid.
Ko da suka shigo da ni suka fara yin arba a kwance cikin jini ai kuwa hankalinsu ya tashi sosai domin saida Jiddah ta suma dakyar ya samu ta nutsu kaɗan sannan ta taimaka mai suka shigar da ni cikin motar ba su ko kula da mai gadi ba bare su ɗauke shi mu tafi asibitin a tare saboda tsananin firgici da suke ciki. A guje Saleem ya ja motar muka bar cikin anguwar muka nufi hanyar asibiti, gudu yake yi tamkar zai tashi sama saboda azalzala da Jiddah ke yi masa, ni dai a lokacin sama-sama nake iya jiyo maganganunsu saboda zafin raunukan dake jikina da kuma jinin da har a lokacin bai daina zuba ba. Cak! Motar ta tsaya taƙi yin gaba ko baya duk yadda Saleem yayi ƙoƙarin ta motsa amma taƙi hakan ne yasa ya fito daga cikin motar cikin tsananin mamaki domin yasan motarsa lafiya lau take sannan akwai mai sosai a ciki, buɗe-buɗe ya fara yi yana dubawa ko zai ga ta inda matsalar take amma bai fahimci komai ba, ganin haka yasa itama Jiddah ta fito a motar tana taya shi dubawa ko zasu gano matsalar motar. Kamar wanda aka umarta haka ya sunkuya ƙasa tare da leƙa ƙasan motar, abinda ya gani a gurin ne ya matuƙar bashi mamaki, bakomai ne ya hana motar tafiya ba illa wani littafi ƙaramin dake ƙasan tayar gaba na hagu, cikin al'ajabi ya sa hannu ya zaro littafin da ƙarfi, cikin zarewar idanu ya nunawa Jiddah littafin wanda a bango cikakken sunana ne a rubuce cikin rubutu mai matuƙar kyau. A wannan lokacin bana tsayawa wasu maganganu bane saboda halin da nake ciki hakan yasa Saleem ya ajiye littafin a gaban motarsa zuwa lokacin da zan samu kaina. Bansan abinda ya faru ba domin a lokacin juriyata ta ƙare tuni na sume, a haka muka isa asibitin cikin gaggawa, ba mu sha wahalar samun likita ba domin a wannan asibitin Jiddah ke aiki sannan ita ke dubani lokuta da dama idan kalar hakan ta faru, a wasu lokutan ma bama zuwa asibiti idan zamana a asibiti na da hatsari.
Emergency room aka shigar dani, nan da nan Jiddah da wasu likitoci biyu tare da nurses suka duƙufa domin ceto rayuwata, sai bayan da aka idar da sallar asuba'i kafin numfashina ya daidaita bayan sun gyaramin raunukan dake jikina sannan nasha ɗinkuna a waɗanda ke buƙatar ɗinki. Daga haka aka yimin alurar bacci sannan Jiddah da kanta ta turani ɗakin hutu. Sai a lokacin ta samu sukunin kiran Daddy ta shaida mishi abinda ke faruwa, ba'ayi mintuna ashirin ba kuwa sai gasu a cikin asibitin gabaɗayan su harda Baaba, ganin yanayina kuwa ta matuƙar ta da musu da hankali nan suka tambayi abinda ya faru, Saleem ne kaɗai ya iya buɗe baki ya musu bayani tun daga kan farkawar Jiddah daga bacci har zuwa lokacin da nake kwance bansan me ke gudana ba.

Sun shiga damuwa sosai musamman Baaba da a lokacin take tunanin na mutu ne ake ɓoyewa, shi kuwa sarkin zuciya Sadiq ya kasa furta ko kalma ɗaya amma kallo zaka yi masa ka gane yana cikin tsananin damuwa da ɓacin rai duba da yadda idanunsa suka sauya kala zuwa jajaye sannan kyakkyawar farar fuskarsa ta rine tana nuna alamun ɓacin rai. Haka suka zauna shiru har ƙarfe goma na safiya amma ban farka ba wannan dalilin ne yasa Momi da Daddy suka nemj komawa gida domin taho da abinda ba'a rasa ba na buƙatar majinyaci domin ita kam Jiddah ta ce babu inda zata motsa sai taga farkawa ta, tana gefen Baaba a zaune acan wata kwanar ɗakin suna sharar kwalla lokaci lokaci.
Duk cikinsu babu wanda yayi tuna M.J bare ayi tunanin abinda ya hanasa zuwa a matsayinshi na mijinta, Sadiq ne kawai ya farga ga haka tun lokacin da yazo baiga M.J a wajen ba yasan akwai wata manaƙisar a ƙasa saidai ya share saboda jiran farfaɗowata amma cikin ranshi ya ɗau alwashin cin zarafin M.J matuƙar ya bincika ya samo da sa hannunshi a cikin abinda ya faru dani.
Wani abu da nafara manta wanzowarsa a cikin shafin rayuwata shi ya sameni a lokacin da nake tsaka da baccin dole da likitoci suka sani yi sakamakon allurar baccin da akamin, duk da daɗewar shekaru amma ko a ina naga wannan fuskar zan ganeta, kinsan wacece?"

Rahama dake sharar kwallar tausayin ƴar'uwar tata ce ta girgiza kai alamun a'a domin ba zata iya bude baki tayi magana ba, tabbas ta daɗe bataji ko a labari ba wacce ke da irin ƙaddarar Zarah, domin da ta fita daga wannan take kuma shiga wata batare da ta warke ƙuncin da ke ranta ba.

Numfasawa Zarah tayi sannan ta cigaba da cewa.

Ba kowa bace face Almajirata wacce na daɗe da fara manta abinda ya gudana a tsakaninmu, ina tsaka da wannan baccin nayi mafarkinta ta zo min tana hawaye tace
"Kamar yadda na ɗaukar miki alƙawarin cewa zan barki a baya amma zan kuma dawowa domin taimakonki, Batula ban taɓa nesa daga inda kike ba saidai kawai ina ɓoye kaina ne saboda alƙawarin da na miki na rashin bayyana a gareki. Sai dai a yau na bayyana gareki ne domin taimaka miki akan abinda kw jefa rayuwarki cikin ƙunci. Ki riƙe wanna littafin duk wasu bayanai da zaki buƙata na Alpha yana ciki baki da buƙatar zuwa wani waje domin samo su." Ta ƙarashe maganar tana mikomin wanj ƙaramin littafi dake hannunta, cike da rauni na miƙa hannu na karɓa ina kallon jikin littafin, ɗagowa nayi da nufin tambayarta saidai kuma banganta ba. A daidai nan na farka daga baccin a firgice ina faɗin "Kin bani littafin.?" a gaggauce Jiddah ta matso kusa da ni ta riƙeni tana ƙoƙarin maida ni na kwanta.
Bansan abubuwan da nake furtawa ba a lokacin sai dai naji Jiddah na faɗin
"Littafin yana cikin motar Saleem bari na kira shi ya shigo miki dashi." daga haka na maida kaina ina sauke numfashi a hankali. Shuɗewar mintuna goma ne ya dawo dani hayyacina, a lokacin ne kuma na fara jin raɗaɗin raunukan dake jikina, haka nayi ta daurewa har zuwa lokacin da wata Nurse ta shigo, ganin idona biyu ne yasa ta kuma suka dawo da likita ya ƙara duddubani tare da tambayata inda kemin ciwo, nan na faɗa mishi ina jin zafin raunukan jikina cikin sanyayyar muryata ta marasa lafiya, take ya haɗa allurai yayi min sannan suka fice a ɗakin suna mai ƙara yimin addu'ar samun sauƙi.
Fitarsu ke da wuya Baaba da Jiddah suka ƙaraso kusa da gadon nawa suna jeramin sannu kamar zasu aro baki, da taimakon Jiddah na samo na miƙe zaune bayan ta saka filo a bayana na jingina da gadon, zafin da nakeji ya ragu sosai sakamakon allurar rage zugi da akamin, wannan ne ya bani damar yi musu ƴan tambayoyi game da mutanen da nake da tabbacin zasu zo dubani, nan Jiddah ke gayamin Daddy da Momi suna hanya sunje gida su dawo ne, Saleem kuma ya fita samo musu wani abu su ci kafin Momi ta kawo abinci sai Sadiq da ta nunamin wanda kw zaune a can gefe. Sai a lokacin na juya a hankali na kalli inda take nunamin ai kuwa na ganshj zaune yana aikomin da murmushin da iyakarsa fuska nima na maida masa martani, a hankali ya miƙe ya tako zuwa inda nake ya dafa kafaɗa ta cike da kulawa yake tambayata ya jiki na amsa mishi. Shiru ya biyo baya kafin ya nisa yace
"Little meya faru ne? ina mijinki yaje ne da bai samu damar kawo ki asibiti ba sai su Jiddah ne suka kawo ki? Meyasa tun zuwanmu ba muga yazo domin duba lafiyarki ba ko baya ƙasar ne?"

"Habu ka kiyayeni fa, yarinyar na gadon jinya zaka tasa ta a gaba kana yi mata irin waɗan nan tambayoyin da basu shafi lafiyarta ba." Baaba ta faɗa cikin hargowa.
Murmushi nayi mai ciwo sannan na kalleta nace
"Baaba ina jin ƙarfi sosai a jikina yanzu,karki ga laifinshi dan yamin waɗannan tambayoyin. Yaya kasan meye a tambayarka akwai gyara, a yanzu zaifi dacewa ka dinga danganta Yaya Jawwad a matsayin Yayana ba miji ba, domin a yanzu yadda nake nan babu igiyar aurensa a kaina." Na faɗa ina zamewa da nufin na koma na kwanta.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allah yasa kunnuwana ba daidai suka jimin ba." Abinda Momi ta faɗa kenan wacce suka shigo a tare da Daddy suka tarar ina wannan zancen, gabaɗaya muka juya gareta muna kallonta har ta ƙaraso inda nake ta zauna tana fuskantata tace
"Zarah dan Allah me naji kina faɗa yanzu? Kice min ba abinda naji kika faɗa ba dan Allah.?" ta ƙarashe maganar tana riƙo hannuna ɗaya da babu ciwo, tausayinta naji ya kamani zuciyata tayi nauyi, tabbas nasan banason auren nan nayi biyayya amma mutuwar aure sam babu daɗi musamman ga mace mai irin aikina lokaci guda mutane zasu juya maganar zuwa wata daban, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, nasan tabbas Momi tana jin wani irin yanayi a cikin ranta kwatankwacin yadda nakeji, ban taɓa son M.J ba har gobe amma ban taɓa fatan ace aurenmu dashi ya rabu ba. Cikin murya mai rauni na ce
"Ehh Momi hakane aurenmu da Yaya Jawwad ya rabu a daren jiya." wasu hawaye masu ɗumi naji suna zubomin saboda hoton abinda ya faru a wannan daren daya bayyana cikin kwakwalwata. Salati suka saka gabaɗaya illa Jiddah gwanar kuka da tuni ta fara zubda hawaye, shikuwa Sadiq yana tsaye a gefena har wannan lokacin sai dai babu wanda zai iya tantance yanayin da yake ciki.
Daddy ne yayi ƙarfin halin tambayata yace
"Daughter me ya faru ne kin saka mu a cikin ruɗani."
Cikin nauyinsu da nakeji na labarta musu abinda zan iya tunawa, ai kuwa tamkar waɗanda ke jiran ƙiris nan suka soma fashewa da kuka hatta Daddy sai da yayi hawaye illa Sadiq da kallo ɗaya zaka mishi ka firgice da yanayinsa na tsantsar ɓacin rai da yake ciki.
Nan suka fara jajanta abin kowa da abinda yake faɗi akai musamman Momi da saida Baaba ta tsawatar mata saboda ɗiban albarka da take yiwa M.J ba ƙaƙƙautawa.
Tare muka wuni a asibitin har Daddy kowa da kalar kulawan da yake bani, cikin wuni ɗaya kuwa tamkar wacce ta daɗe tana jinya naji na samu ƙarfin jiki sosai, duk waɗannan abubuwa dake faruwa zuciyata a ƙage take dare ya ratsa na samu na karanta littafin da Saleem ya kawomin wanda dashi nakeson amsa musu tambayoyin da suke ta yimin akan littafin musamman Jiddah.
Sai wajen ƙarfe goma na dare su Momi da Saleem suka yi mana sallama aka barni da Baaba da Jiddah domin kwana da ni, duk yadda akaso Jiddah ta je gida ta turje hakan yasa aka barta mu kwana tare.
Kaɗan-kaɗan muke hira har bacci ya rinjayi Baaba ta kwanta ta barmu ni da Jiddah muna hirar, ganin baccinta yayi nisa ne yasa na fito da littafin daga ƙarƙashin filon da nake kwance na yafito Jiddah tazo gefena ta zauna muka buɗe littafin a hankali mu ka fara karantashi cikin zumuɗi.

*ASALIN LABARIN WANZOWAR ALPHA*...✍🏻


_🙏🙏🙏 Nima na shaida nasan kuna haƙuri da ni sosai musamman ƴan VIP da yanzu bana iya muku update kullum. Dan Allah kuyi haƙuri abubuwa suna yimin yawa ne amma zan dinga ƙoƙari in sha Allah.🥰🥰 Kamar yadda nasan kuna yi inaso ku cigaba da sani a addu'o'inku akan abinda na sa a gaba.🙏🙏🙏 Ina son ku irin totally💃💃💃


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 6*

_Mafarin Lamarin_.

Asalin sunansa Al'amin, ya kasance ɗa na biyar ga Malam Mudi da matarsa Inna Habi, sauran ƴan'uwansa uku mata da namiji ɗa inda ya kasance auta, bayan haihuwar Al'amin ne Malam Mudi ya ƙaro aure inda ya auri wata bazawara da ake kira da Phalmata, tun daga lokacin kuma rainon Al'amin ya dawo hannunta.

Saboda kulawar da take bashi yasa Inna Habi ta bayan ta yayeshi ta tattara kayansa ta maidawa Phalmata riƙonshi gaba ɗaya.

Shekararsa takwas kacal a duniya Allah yayiwa Inna Habi rasuwa, a wannan lokacin duk sauran yayyinsa sunyi aure illa ɗan'uwansa guda da shima yake shirin yi. Tun ƙuruciya Phalmata ke koyawa Al'amin dabarun sace kuɗin mutane da zarar sunyi sake sai dai duk da haka bata gaza wajen ganin cewa ya samo ingantaccen ilimi saboda wani buri da ke ranta, baya ga haka itama tayi karatu kuma ta ɗanɗani daɗinsa.

Tun girmansa sai ya kasance ya kara haɗuwa da abokai masu irin tarbiyarsa, tun daga wannan lokacin lamarin satarsu da fashi ya shahara, sai dai suna yin komai ne cikin basira basa taɓa bari su bar shaidar da za'a gane su.

Bayan kammala karatunsa na Jami'a ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa, a wannan lokacin ne Phalmata ta baiyana masa shirinta na zamewarsu shahararrun ƴan ta'adda da zasu addabi ƙasa da duniya baki ɗaya. Suna kashe duk wanda suka nemi dukiyarsa ya hana, sannan muddin suka kwallafa rai akan abu sai sun samu. Haɗewar sunan Phalmata da Al'amin ne ya samar da sunan ALPHA wanda mutane da dama suke tunanin sunan na mutum ɗaya ne.

Shararsu ne tasa gwamnati ta shiga neman hanyar da zata kamasu gadan-gadan, sai dai sun siye baki mutane da dama daga sama wannan dalilin ne yasa duk sanda zasu tura yaransu yin fashi suke hada baki da manyan jami'ai domin a dakatar da tsaro a inda zasuje ɗin.

Sun yi nesa da inda mutane suke sannan sun alkinta kansu ta yadda babu wanda zaiyi tunanin saninsu ko yasan wani abu dangane da su.

A yanzu haka suna rayuwa ne a garin Enugu a cikin wani ƙauye da ake kira Keruba, wani abun mamaki shine duk da a cikin mutane suke amma hakan baisa mutane sun shaida su, dalili kuwa shine, wani madaidaicin gida kamar ko wanne gida da kuka saba ganin mutane na rayuwa a ciki, amma a ƙasan wannan gida rantsatstsiyar fada ce tamkar ta sarakai wacce aka yiwa laƙabi da _ALPHA VILLA_.
Babu wanda yasan a inda ƙofar dake sada mutane da Alpha Villa take a cikin wannan ƙaramin gida, a duk lokacin da mutum zai shiga ko fita sai an shaƙa masa hodar dake saka bacci na wasu mintuna.

Ta hanya ɗaya ne kacal zaku iya nasarar kama Alpha a sauƙaƙe.
A kowacce ranar Lahadi yana ɓadda kama ya fito daga wannan gidan don ya zaga gari, yakan kwashe awa guda da rabi yana zagawa kafin daga baya ya koma mazauninsa. Babban lagon Alpha guɗa ɗaya ne, wato mace mai ciki. Yana matuƙar tausayin mace mai ciki ko da wucewa tayi ta gabansa sai yaji hawaye na neman fitowa daga idonsa. Saboda haka idan kunason kama Alpha dole ku nemi wata mace da ke da ciki don samun lagonsa.

Mun daɗe mu na karatun wannan littafin har dare ya ratsa sannan mu ka gama, ajiyar zuciya mu ka sauke a tare ni da Jidda bayan na rufe littafin na maida shi inda yake, kallon juna mu ka yi cike da rauni kafin Jiddah ta ce
"Na samo mana mafita."

"Mafita? Wace iri?" na tambaya.

"Mai ciki ake nema kuma gani sai ki zame min ƴar jagora."

"Ke baki da hankali ne Jidda kinsan me kike faɗa kuwa."

"Wallahi idan kika kuma mu sa min akan abinda na faɗa ban yafe hakkin ƙaunar da nake miki." Jiddah ta fada tana mikewa ta koma kusa da inda Baaba ke kwance itama ta kwanta, ta barni sororo ina jimami.
Na jima a zaune kafin daga baya na tura littafin ƙasan filo,sannan na sulale na kwanta zuciyata cike da tunanin mafita.

Washe gari tunda farar safiya
Sadiq ya iso asibitin, kallo ɗaya za'a masa mutun ya gane cewa bai runtsa ba, Baaba ya fara gaidawa sannan nida Jidda muka gaishe shi ya amsa yana tambaya ta ya jiki. Zama yayi a gefena yace lafiyarki"
Cikin mamaki muke kallonsa ni da Jiddah kowa da abinda yake saƙawa a ranshi.

"Amma Yaya me yasa ba zaka barni anan ba."

"Ina so ki yi nesa da M.J banaso ya kuma ganinki bare wani abu ya shiga tsakaninku ko da kuwa kalmace ta fatar baki."

Baaba da ke zaune can gefe ne ta ce
"Haka ba shine mafita ba Sadiq a barta anan ɗin kawai, ai an riga da anyi kuskure ba za'a kuma bari kalan haka ta faru ba."

Ganin Baaba na son jan maganar ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai kuma magana ba. Mu na zaune a haka su Daddy suka shigo shi da Momj da Saleem, hannun Sa-Jid ɗin ɗauke da kwandon abinci, gaishe-gaishe aka yi suna ƙara tambayata ƙarfin jikin. Momi ce ke faɗamin cewa Ammi ta kira waya tana gaishe ni, sannan ta ce zasu taho a satinnan, cikin jindaɗi na amsa ina ƙara jaddada ƙaunata a zuƙatan waɗannan mutanen. Jidda ce ta zuba mana abincin, dafa dukan cous-cous da farfesun kayan ciki, sosai naji daɗi abincin kuma na ci sosai irin wanda na jima ban ci ba saboda a lokuta da dama ba na samun damar yin girki saboda aiki, dama kuma M.J ba abincina ya ke ci ba bare nayi tunanin dafa mishi.

Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ni zuwansa, mu na zaune su ka turo ƙofar ɗakin shi da Hajara cikin kyakkyawar shiga irin na masu morar amarci, da alama hankalinsu kwance yake kamar tsumma a randa.

Da sallama a bakin Hajara, Baaba ce kaɗai ta iya amsa sallamar hatta Daddy kai ya kauda gefe. Ganin haka ne yasa suka gaida Baaba kaɗai sannan suka nemi guri su ka zauna. Jim ɗakin ya yi babu wanda ya tanka, Daddy ne ya ciro wata farar takarda daga aljihunsa sannan ya baiwa Sadiq ya miƙawa M.J da kansa ke a sunkuye, cikin son ƙarin bayani ya kalli Daddy sai dai ya kauda kansa gefe, hakan yasa shi buɗe takardar don ganin abinda ta ƙunsa. Cikin razana ya ɗago ya ce

"Kotu! Daddy me na yi?"

"An haɗa baki da kai wajen cutar min da ƴata."

Da matuƙar mamaki mu ka ɗago a tare muna kallon Daddy, Baaba ce tayi ƙarfin halin cewa
"Sulaimanu wanj zance nake ji haka, wa za'a kai kotu."

"Ba wani abin tashin hankali bane fa Baaba, komai zai zo da sauƙi." Daddy ya faɗa.

"A wani garin marasa hankalin aka taɓa aikata haka Sulaimanu? Kana nufin kenan Muhammadun ya fi ƙarfin ka eyeee. Kai ba za ka iya masa hukunci ba kenan har sai ka dangana da wasu a waje, kai ne uban ko shine? Ban yarda ba, ban amince ba, matuƙar na isa da kai toh ban yarje maka ka kai ƙarar Muhammadu kotu ba." Baaba ce ta yi wannan zance.
"Baaba laifin da Jawwad yayi mai girma ne, ko da Gwamnati ne ta ji labarin abinda ya aikata ba zata barsa ba, ki bari kawai a hukunta shi." Cewar Momi

"A'a ban yarda ba a nemi wata hanyar hukunta shi amma ba ta hanyar kotu ba."

"Ko da yaushe wannan tsohuwar sai kin kaucar da mutane akan hanya." Sadiq ya faɗa.

"Ka kiyayeni fa Habu, ba na wasa da kai."

"Shikenan Baaba za'ayi yadda kike so, amma wannan karon Jawwad ya ɓata mana rai matuƙa dan haka zan yanke masa hukunci mai tsauri." Inji Daddy.

"Yauwa ɗan albarka ai idan rai ya ɓaci hankalj baya gushewa."

Daddy ne ya maida kallonsa inda M.J da Hajara ya ce
"Ka tashi ka tafi banaso na ƙara ganin fuskarka."

"Dad-dy!" M.J ya faɗa cike da rauni.

"Ehh ka tafi Jawwad ba ma so ƙara ganin fuskarka a cikin mu." Momi ta faɗa cikin hawaye.

Gwiwarsa ya zube a ƙasa da nufin ba ta haƙuri sai dai ta riga shi da faɗin

"Ka bani kunya Jawwad, wallahi da nasan akwai ranar da zata zo da zaka yi sanadin shigata baƙin ciki kamar yadda nake ji a yanzu, da tun kafin Allah ya bani cikin ka zan roƙe shi ya hanani cikin ka, Allah ya jiƙan Rahama ko da ɗaure fuska nayi cikin wasa sai hankalinta ya tashi, kai da nake tunanin zaka maye min gurbinta sai gashi kaine mai son kashe ni da baƙin cikin ka, Allah ya w...."

"Kul! Kada ki yarda ki ƙarasa, kin san munin da tsananin da fushin iyaye ke jawo wa ƴaƴan su kuwa? Banason ƙara jin kunyi mugun furuci akan yaron nan." Baaba ta katse Momi da ke magana cikin tsananin fusata.

Gabaɗaya ya firgice da kalaman iyayensa, ya san fushin su akan sa babban musiba ne a gareshi, hawaye ne suka fara sintiri a kuncinsa.

"Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban...✍🏻✍🏻


*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 7*

..."Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban yafe maka ba." Momi ta yi wannan furucin cikin zafin rai.
Da hanzari ya miƙe ya fice Hajara ma ta miƙe ta bi bayan shi ba ta re da ta ce komai ba. Nan Baaba ta rufe Momi da Daddy da faɗa, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, su dai sai haƙuri kawai suke bata, daƙyar suka samu ta daina faɗan.
A wannan ranar ma tare muka wuni da su cikin kulawa, wajen ƙarfe tara na dare ne muna zaune sai sallamar Ammi muka ji, cikin mamaki nake kallonta Momi kuwa sai dariya ta ke min tana faɗin dama taki sanar da ni ne saboda zumuɗi irin nawa. Cikin murna muka gaisa tana tambayata yanayin jikina, ko da lokacin tafiya yayi sai Ammi ta ce nan zata kwana, daƙyar aka samu Jiddah ta bi Saleem suka tafi gida. Tare muka kwana da Ammi tana bani kulawa kamar zata maida ni ciki.

Kwana na goma a asibiti kuma naji sauƙi sosai sakamakon kulawar da likitoci suke bani a gefe guda kuma ga kulawar da su Momi ke ba ni. Tun waccan ranar kuwa ban ƙara saka M.J a idanuna ba, saboda su Momi sun ɗau zafi sosai, Ammi ce ma wani lokacin nake jin su suna magana a waya wanda yawanci roƙonta ya ke akan ta baiwa su Daddy hakuri akan fushin da suke yi dashi. A yadda na fahimta, ko kaɗan abinda ya same ni bai damu M.J ba fushin da iyayensa ke yi da shi ne kaɗai abinda yake damunsa.

1 Comments On ASP ZARAH book 2
avatar
ibrahim-8-7

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment