Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[29/05 à 17:06] MRS SADAUKI 💫: *SOJANA...*💞




☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️



Chamsiya Laouali Rabo✍🏻

*MARUBUCIYAR :*
SO KO ƘAUNA
JININA NE KAI
HASKEN SOYAYYA
CIWON SO
SADAM
ƘAWAR MOMYNA
ABBANA NE
MAHAUKACIN SO
ILLAR LUWAƊI
ABOKIN MAGAJINA NE
ƳAN UKU
ƁOYAYYEN SIRRI
DA CIWO A ZUCIYATA
DJINN
ƘADDARA


Page 1-2

Tafe suke suna hira ita da ƙawar ta, sun zo daidai bakin titi suka tsaya jiran har ababen hawa su tsaigaita wucewa.
Kamar walƙiya haka gungun motocin sojawan ke wucewa shuuu har wata ƙura ke tashi tsabar yadda suke gudun.
Tsuki Munat tayi tana mai cewa ƙawarta Maryam "wlh na tsani soja a rayuwata, dubi dan Allah yadda duk suka ɓatawa mutane da lokaci saboda kawai su wuce an wani tsayar da mu kan titi mtsw..."ta ja wani dogon tsaki, murmurshi Maryam kawai tayi ta na mai cigaba da kallon motocin cike da burgewa dan ita a rayuwarta babu abinda ke burge ta irin soja.
Motocin ne suka fara ragewa a sannu har aka zo da motar ƙarshe wacce ke gudu a slow,hannu Maryam ta ɗagawa sojawan ciki da ya ke motar irin wannan ce mai baya a buɗe suma maido mata su ka yi.Cike da jin haushi Munat ta tsallake ta bar Maryam tsaye tana hangen motar da ta wuce,da ɗan gudu ta tsallaka ta cimma Munat wacce ta cika tayi fam tamkar za ta fashe.
"Kiyi haƙuri ƙawata wlh na sha'afa ne sam ban lura da lokacin da kika tsallaka ba sorry"cewar Maryam ta na mai kamo hannun Munat ,fizge hannunta tayi tace "ta ya dama zaki lura ki na kallon dangin Iya"dariya Maryam tayi tace "yanzu ni kike zagi ki na cewa ina kallon dangin uwata ?"hararar ta kawai Munat tayi ta na mai shigewa cikin gidan su dama gidan su ne farko sannan na su Maryam.

A yadda ranta ya ke ɓace shi ya hanata yin sallama,ta na sanya ƙafarta cikin falo ta wani tsaya turus ta na mai fiddo ido waje tare da dafe ƙirji kamar ta ga wani mugun abu.
Sanye ya ke da kayan sojoji masu dogayen hannu idon shi manne da baƙin gilashi wanda ya zauna ɗaf bisa doguwar fuskar shi mai yalwatacen saje baƙi ƙirin,ja hular shi na bisa dogon gashin kan shi wanda ya ke baƙi siɗik irin na buzayen usuli.
Yadda ta ƙame ƙyam kamar mai cutar sanƙaro shi ya so bashi dariya amman ya cije tare da haɗe fuska tamkar bai taɓa dariya ba,"ƙaraso mana kin ga ɗan uwan ki ne Mohammed ya kawo mana ziyara"cewar Mami ta na murmurshi.
Duk da akwai gilashi a idon shi bai hanata gane kallon tsaf ɗin da ya ke mata ba hakan ya sa ta turo baki gaba "shine zai wani tsare ni ya na kallo kamar maye"a tunaninta a zuci tayi maganar sai jin dakakiyar murya shi tayi yace "mi za'a kalla a nan?ko maye ne ni na rasa wacce zan lashe sai ƴar Baƙa"dariya Mami tayi ta na jin daɗi a ranta ganin duk da ba su san juna ba sun fara wasar cousinage irin ta Ɗan mace da Ɗan namiji.
Wani haushi ne taji ya kamata dan duk duniya in akwai abinda ta tsana shine a shammace ta da baƙin ta wato baƙar fatar ta,baki ta sake turowa ta fara magana cikin sangarta na autanni "Ni dai ba baƙa ba sai dai..."sai kuma ta ƙyale ta na kallon farar fatar shi wacce dan tsananin farin shi kace Balarabe ne,miƙewa yayi tsaye ya fara takowa inda take da sauri ta fara marche arrière saboda yanayin tsawon shi da faɗin ƙwanjin shi ba ƙaramin cika mata ido yayi ba.
Ido ta rumtse jin ya zo daf da ita,riƙe ƙugu yayi kamar wata mace yace "wai Mami wannan autar ta ki har yanzu ba ta bar tsiwa ba ko mi?wai ni take kallo da ƴan ƙananan idonta tana turo min baki da ki bar su a buɗe ki gani da na cire maki su na baki abun ki a hannu gobe sai na ga da wane zaki harare na"wani fitsari Munat taji ya cika mata mara a take tsabar tsoro dan a yadda ake faɗin sojawa ba su da imani to wannan ba ƙaramin aikin shi ba,a fili ta furta "shikenan da na zama kamar Laila ta cikin LE DESTIN wayyo Allah da na shiga uku"ta faɗa tana shirin rugawa sai kuma taci karo da shi.
Hannunta ya riƙe yace "ai kam kin kawo idée hakan zan yi maki"ƙara Munata ta saka tana kiran sunan Abba,a can bayan shi yaji Mami na cewa "a'a Mohammed kar fah a takura min auta dan in baya na ƙyale yanzu ba zan yi haƙuri ba"cikin dariyar da ta bayyana fararen haƙoran shi masu ɗauke da hauren Makka biyu yace "bar ni na tuna mata baya Mami da alamu ta manta ni ne"ya faɗa ya na mai lanƙwasa mata yatsun hannunta suna bada sautin ƙwas ƙwas ƙwas.

Sakin ta yayi tare da dungure mata kai yace "ƙazama mai kukan kitso"ba ta kula shi ba ta ruga part ɗin ta, toilet ta shiga ta fara yin fitsarin da ke shirin kubce mata sannan ta sakarwa kanta shower tana mai lumshe ido.
Tana fitowa doguwar riga ƴar kanti ta saka tare da fesa turare ta dawo falo wayam ba shi ne,samun kanta tayi rashin jin daɗin haka ta so ta ƙara kallon kyakkyawar fuskar shi mai kama da ta larabawa.
Abinci ta zuba ta fara ci kawai sai taji sallamar shi,dammm ƙirjinta ya buga amman sai ta danne tsoron shi da ya tsargar mata tana mai ɗagowa ido ta waro ganin ya cire hular kan shi ya baje baƙin gashin shi wanda ya zo har kusan wuyan shi."Astagfirullah"ta furta da ƙarfi ba tare da ta janye idonta daga kallon shi ba,fuska ya turniƙe ya zauna kujerar da ke facing nata ya na mai kakaɓe gashin shi da yayi ƴar lema.
Baki ta turo ganin ya tsare ta da fararen idon shi masu kamar madara tare da sunne kai tana yawo da cokali sam ta kasa cigaba da cin abincin,"maras kunya ai na zata ba zaki janye idon na ki ba masu kama da na wara🦗"cewar Mohammed ita dai ƙin tanka shi tayi dan har ga Allah tsoron shi ma take.
Mami ce ta fito daga wanka har ta canza kaya tace "Auta ke ɗaya ke cin abincin baki bari na fito?"ɗagowa tayi ta kalli Mami sannan ta juyo inda Mohammed ke zaune ya na aikin kallonta tace "shi wannan yaushe zai tafi?"waro ido yayi yace "zuwa ina?tab yarinya ina nan kuma in zan koma da ke zan tafi can dajin sambisa wajen ƴan boko haram dan su koya maki hankali"da sauri Munat ta miƙe tana shirin guduwa dan duk tsiwarta tsoron tsiya ne da ita.
Saurin fizgota yayi ta faɗo jikin shi,dariya yayi mata sannan ya jawo abincin yace "ci abincin ki wasa ni ke maki Mimina"da mamaki ta kalle shi jin ya kirata da wani suna a zuci tace "wai Mimi ko miye ma'anar haka?"ba zato kawai taji ya buɗe bakin tare da tura mata loma,ba ta da zaɓi ta fara taunawa ta na mai mashi kallon cikin ido.
Har sai da Munat ta cinye abincin ba ta san da ta cinye ba,nan Mohammed ya shiga tsokanar ta rufe fuska tayi tana dariya shi kuma ya fara ɗaukarta video kafin yayi mata hotuna.
Jin an fara tada haramar sallah yayi saurin miƙewa ya na mai miƙa mata wayar ta shiga duba hotunan da yayi mata gabanin ta cigaba da ɗaukar kanta.


Ko da Mohammed ya dawo daga sallah ya tarar da hotunan Munat sun fi ɗari har da canza kaya tayi wasu kuma da hijab ta yi su, murmurshi kawai ke fita daga fuskar shi.Muryata yaji tana cewa "yauwa Moha buɗe min code ɗin na gani"ta faɗi hakan tana cire hijabin da tayi sallah .
Kafaɗa ya maƙe mata yace "ina sauri yanzu za mu wuce Zinder ki bari zan turowa Mustapha ta WhatsApp"narai-narai tayi da ido tace "shikenan yanzu tafiya za kayi ?"yace "eh!ko ki na zuwa ne?"kai ta girgiza tace "a'a amman yaushe za ka dawo?"
"Nan da 3mois (3month) in shaa Allah kin ga ba jimawa zan yi ba kamar gobe ne"tace "haka ne"kallon ta Mohammed yayi da kyau yace "ko baki so naje ne?in baki so sai nayi zamana"da sauri tace "dagaske?"yace "eh mana " "to kawai kayi zamanin ka "cewar Munat dariya yayi yace "so kike a kore ni daga aiki ko?"gira ta ɗaga tace "eh ɗin dama na tsani soja"har zuciyar shi yaji rashin jin daɗin haka a sanyaye yace "kin tsani soja koko aikin soja?"shiru tayi can tace "duka biyun"ba tare da ya kuma cewa komi ba ya shiga danna wayar shi da alamu text ne ya ke rubutawa.
Tsure shi tayi da ido ta ga sam babu alamun fara'a a fuskar sai taji kuma ba ta kyauta ba dan ta gano ɓaranɓaramar da tayi,to amman ya za tayi?nature ɗin ta ne Allah ya sa mata tsanar soja a zuciya.

Miƙewa yayi ya na mai zuwa bakin ƙofar Mami yace "Mami ni zan tafi sai kuma in Allah yayi mamu dawowa ƙila mu biyo ta Maradi"fitowa Mami tayi ta raka shi da addu'a tare da bashi wata tsanwar leda,yayi godiya ya karɓa har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya kalli inda Munat ke tsaye tsamo-tsamo yace "Mimi babu rakiya?"hararar ta Mami tayi tace "je ki raka shi mana har samu adaidaita"ledar hannun shi ta amsa suka fita waje suna jiran ɗan sahu.
Ita dai kanta a duƙe ya ke ba ta ɗago ba duk da taji a jikinta ita ya ke kallo,nisawa yayi yace "Mimi zan tafi mission ban sani ba ko na dawo ko akasin haka abinda ni ke so da ke ki kula da kanki banda biye ma ƙawaye da shirme na yin samari,ki tsaya waje guda in dai na dawo da raina to na san dan mu rayu ne"ya ƙarashe maganar ya na mai cire wani abun wuya nashi mai ɗauke da wani dutse mai shatin love a tsakiya.Cikin hannunta ya damƙa mata ya na mai karɓar ledar daidai nan mai adaidaita ya tsaya ya shiga,hannu ya ɗaga mata lokacin da ɗan sahun ya fara tafiya.Jijiyoyin ƙafafunta ne taji sun ƙulle sam ta kasa tafiya kamar wacce aka yiwa dabaibayi,lafuzan shi take son warwarewa dan sanin ma'anar su amman kwanyarta ta tsaya cak daga aiki abu guda ke yi mata yawo ```na tafi mission ban sani ba ko na dawo ko kuma ba zan dawo ba``` tambaya tayi ma zuciyarta "to ina zai tafi in bai dawo ba?"nan take kuma ta bata amsa da "in ya mutu"wata irin kariyar zuciya ta samu lokaci guda kuma idonta ya fara zubar da ƙwala a hanya mutane sai kallon ta suke har ta shige gida.
"Auta lafiya kike kuka ko sakarcin ne ya motsa?"cewar Mami tana kallonta,baki ta turo ta shige ɗakinta.



A ɓangaren Mohammed kuwa tun bisa hanya ya sauke App ɗin da ake ɓoye hotuna,nan ya ɓoye duka hotunan Munat dan ko kaɗan bai ji zai iya bari wani ya ga hoton ta ba sam zuciyar shi ba ta aminta da haka ba saboda tsabagen kishi irin nashi ga kuma abokan shi maras kan gado sun ga dama in sun amshi wayar shi su kalle mashi ita.
Ko da ɗan sahun ya kai shi Company ba'a ɗau lokaci ba suka kama hanyar Zinder,suna fita daga Maradi sai yaji tamkar an raba shi da wani jigo na rayuwar shi duk sai ya koma sukuku duk da ya kasance mai yawan magana.
Baƙin daji ne baƙi ƙirin suka sauka inda anan ne za su yi patri na wani lokaci kafin su yi gaba,wayar shi ya ɗauka ya danna lambar Mustapha Yayan Munat har sai da ta kusa yankewa ya ɗauka.
Cikin girmamawa suke gaisawa kafin yace "BABBAN YAYA dan Allah ina neman wata alfarma ka baiwa Mimi wayar ina son yin magana da ita kar ka bari Mami ta gani"cewar Mohammed ya na mai marairaice fuska,tsuki Mustapha yayi yace "banza na zata wani abun ne za ka nema ashe wannan ficikar kake son na kaiwa waya,to uwar miye za ka gaya mata kuma yanzu?"cikin jin haushi Mohammed yace "kamar ya?"yace "eh ba naji Mami tace yau ka zo nan ba?shine kuma dan tsabar kirkin ka ko ka kira ni a waya ka shaida min za ka zo"murmurshi mai sauti Mohammed yayi yace "sorry nima ban yi zaton za mu tsaya Maradi ba shiyasa kuma ina cikin sauri ne, Please ni dai tafi ka kai mata"tsuki Mustapha ya sake ja yace "girma dai ya faɗi"Mohammed dai bai ce komi ba ya na jin yadda Mustapha ke tafiya da ɗan sauri har lokacin da ya buɗe ɗaki ya na yi Munat tsawa wacce ke zaune bakin gado tayi tagumi "uwar mi kike tunani da har ina maki magana baki ji ba?"ya faɗi hakan ya na mai miƙa mata wayar murya na ɗan rawa tace "wanene?"Mustapha yace "ban sani ba in kun gama ki kai min wayata ɗaki".
Shiru tayi tana sauraren saukar numfashin shi da ke fita da sauri-da sauri,can ta nisa tace "hello"ƙyaleta yayi sai da ta sake maimaitawa sannan yace "Mimi naaa"baki ta turo dan ta gane mai maganar tace "Ni ba Mimi sunana ba"murmurshin gefen baki yayi yace "to ya kike son nace tunda sunan Mamyna gare ki?" "Sai ka faɗa kamar yadda kowa ke ce min Munat"ta bashi amsa "na ƙi ɗin,yanzu dai gaya min mi kike yi?"tace "Komi" "kuma Musto yace ki na tunani?"sai da ta cire wayar a kunne ta harare shi tace "eh mi?"sai da rumtse ido jin yadda ta bashi amsa gatsal babu respect amman ya danne zuciyar shi yace "ah babu komi ai na san bai wuce tunanin sojan ki kike yi ba"shiru tayi kamar ba za tace komi ba sai ta tambaye shi kuma da "ina hotuna na?ka turo mashi ne?"
"A'a ban turo mashi ba bari na kunna data yanzu na turo"ya faɗa tare da kashe kiran.Munat da ta iya taro rigima ta hauda connexion ɗin wayar Musto,ba'a ɗau lokaci ba messages suka fara shigowa nan ta ga hoton Mohammed inda ya ke da kayan sojoji shiga tayi ta fara buɗe hotunan.
Tana tsaka da kallo appel video ya shigo,ganin Mohammed ne yasa ta ɗauka ta mai waro ido ganin ba'a ganin komi sai duhu shi kuwa ƙureta yayi da ido ya na kallon wuyanta wanda ya ke a cike gami da murɗiya har zuwa cikaken ƙirjinta wanda suke dam kamar za su faso rigar,shatin nipples ɗin ta sun fito sosai kasancewa rigar mai santsi ce.Turo baki tayi tace "Ni fah ban ganinka ka shiga haske mana ka wani tsaya cikin duhu kamar mugu ko wani munafuki"dariya yayi a zuci kuwa ƙara jinjina girman tsiwa irin ta Munat ya ke yace "yanzu Mimi Ni ne munafuki?"murguɗa baki tayi tace "Ni fah ban ce ba cewa nayi kamar in kuma shine tom..."
"Tom mi?"cewar Mohammed ya na kallonta sarai kasancewar ampoule ɗin ɗakin ba dai haske ba,cikin tsiwar da ta zame mata jiki tace "ah sai ka faɗi mu ji saboda mu kiyaye zuwa gaba ko kuma ka miƙa kan ka da hukuma"ta na faɗin hakan ne tana wani jujuya kai ita duk a tunaninta shi ma bai ganin ta.
Lumshe ido yayi ya jingina da ƙaton dutsen da ya ke bisa a kai yace "Please saka hijabin ki kar ki ɓallo min ruwa ina zaman zamana sai wani rangaji kike kamar bishiya"Waro ido tayi tace "wai ka na nufin ka na gani na?"yace "eh mana"ai kuwa ta shiga bubuga ƙafafu da ƙasa tana kukan shagwaɓa.....



*PAID BOOK NE 500₦/500f ga mai buƙata ya tuntuɓi wannan number* +22795045822
[29/05 à 17:07] MRS SADAUKI 💫: *SOJANA...*💞



☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*


*Matan Sojawa da ƴan matan Sojawa ina kawo gaisuwa*👍🏻

Chamsiya Laouali Rabo ✍🏻


🆓 Page 3-4


Musto ne ya shigo ɗakin ganin shiru-shiru ba ta kawo mashi wayar shi ba,tsayawa yayi ya na kallonta shi a tunanin shi ko aljanun ta ne suka tashi sai jin murya Mohammed yayi ya na cewa "Please Mimi ki daina ban so,ki tsaya wuri guda ki nutsu za mu yi magana"turo baki tayi tace "ba kai ne ba"warce wayar shi yayi yace "shine yayi uwar mi mahaukaciya kawai dubi yadda kika hargitsa gashin kan ki wajen shirme sannan wannan rigar maza kije ki cire ta, tunda ba jin magana kike ba ina ga sai na fara nausar ki"cewar Mustapha ya na mai kashe appel ɗin ya fice ya bar Munat da haushin katse mata nishaɗi da yayi.
Cike da baƙin cikin ganin Mimin shi da Mustapha yayi ya turo mashi text " miye na shiga ɗakinta ba tare da neman izini ba ?kuma shine ka amshe wayar ba tare da mun gama ba mtsw"wani haushi Mustapha yaji ya maida mashi da "uwar mi ta aje cikin ɗakin da har sai na nemi izini ko ka manta Munata ƙanwa ce gare ni?kuma waya ina ce dai tawa ce shiyasa na karɓo"Mohammed na karanta text ɗin ya dannawa Mustapha kira ɗagawa yayi ya na cewa "yane ko ta shafe ka ne mai zuciyar ƙarfe?to in kaji haushi ka saya mata wayar can kuje kuyi sakarcin ku amman ni ba da wayata ba"a zafafe Mohammed yace "look Musto bari ganin ina kyaleka ka san ba wani girme min ba ne kayi sosai balle dan nayi maka rashin mutunci a ga laifina,daga yau dan Allah kar ka ƙara shiga ɗakin Mimi sai da izini"dariya Mustapha ya sheƙe yace "kaji wani rainin hankali ni da ƙanwata shine za'a min shamaki to yaro tun wuri ka aje wannan banzan kishin na ka dan ba zai kai ka ko ina ba"Mohammed yace "na ƙi na aje ɗin kuma wlh in ba kayi sannu ba sai na zane ka tunda ni ne Chef ɗin ka"murmurshin gefen baki Mustapha yayi yace "ai sai na rama da ƴar ƙwailar ka na sa ta tsalon kwaɗo🐸 ka ga kuwa yadda take ƴar lukutar nan za taji jiki"tsuki Mohammed yayi yace "Allah shirya ka yanzu ƙanwar taka ma sai kayi mata shegantaka?hum ni dai duk ba wannan ba gobe ka cire kuɗi cikin account ɗina ka saya mata waya wacce ta dace Please kar kace a'a wannan karon ba zan yi toléré ɗin ka ba dan Mimi ba yarinya ba ce da za ka hanata riƙe waya"fuska Mustapha ya tamke yace "elle a juste 18ans fah kuma kake maganar waya haba kafi kowa sanin haɗarin da ke cikin portable gaskiya ba..."da sauri Mohammed ya katse shi yace "Please ko ƴar ƙarama ce mai touche wadda zan rinƙa samun labarin ta dai" "naji Sarkin naci mtsw sai da safe ma babyta na kira na" Mohammed yace "Allah shirya ka mai kwashe-kwashe"bai jira cewar shi ba ya kashe wayar.


Direwa yayi daga kan dutsen da ya hau dan samun network ya nufi inda suka hahaƙa rumfunan su na tanti,ɗan gadon ya kakaɓe tare da yin Bismillah ya kwanta.Allah ya sani shi ya kasance cikaken namiji wanda ƙaramin abu zai tayar mashi da hankali shiyasa ya ke kiyaye duk abinda zai motsa mashi sha'awa,a wajen aikin su ko magana bai yiwa mata duk da wasun su suna mugun son shige mashi amman kasantuwar shi mai ɗaure fuska suke shakkar shi.
Gudun bugun zuciyar banda ƙara hauhawa babu abinda ya ke yayinda duk tsikar jikin shi ta tashi har wayam ya ke ji a jikin shi nayi,ko kaɗan bai so ya ga Mimi a haka ba ya san kafin hoton ya ɓace a idon shi sai an kwan biyu.
"Hasbunallahu wani'imal wakil"kawai ya ke maimaitawa ƙasan zuciyar tare da roƙon Allah ya rage mashi wannan masifar🤭.

A ɓangaren Munat kuwa bayan fitar Musto hararen ƙofa tayi tana cewa "ko ina ruwan shi da riga ta kawai haka nan sai in yi ta sa manyan riguna kamar wata uwar mata"ta faɗa tare da cire rigar mai siraren hanunuwa ta saka wata sai gunguni take.
Kwantawa tayi tana mai jin zuciyarta tayi nauyi kamar ta na buƙatar wani abu ko kuma wani abun ta yayi nisa da ita, numfashi ta ja sosai ta sauke ajiyar zuciya wai ko ta samu dama amman shiru sai ma tunanin Mohammed da ya faɗo mata a bayyane tace "mugu shi ma har da wani kallona kamar ƴar gidan su"Mami da shigowar ta kenan kuma taji abinda Munat ta faɗa tace "wa kenan ?ke yanzu a haka ne zaki kwanta da haske kamar dangin sheɗan ni na zata ma kin yi barci"ta faɗa tana mai kashe ampoule ɗin ɗakin.Da sauri Munat ta diro tana ƴar ƙara tace "Wlh Mami tsoro ni ke ji Ni dai ki bar min ƙwain fitilata"kunna hutar Mami tayi ta girgiza ta fita tana mai cewa "ki tabbatar kin yi addu'a kafin ki kwanta"da "toh"ta amsa tana mai komawa kan bed ta ja zanen gado ta rufe har kanta,ji tayi kamar wulgawar wani abu da sauri ta miƙe zaune tana waige-waige ba ta ga komi ba hakan yasa ta koma ta kwanta, ampoule ɗin ɗakin ne ya fara ɗokewa ya na dawowa sai yayi fatsee kamar yayi masse.
Addu'a Munat ta fara kafin ta danna suratul Baƙara da ɗan ƙaramin MP3 ɗin da ke bisa kan gado nan barci yayi awon gaba da ita.


Washegari a gurguje ta shirya ko breakfast ba ta tsaya yi ba ta biya gidan su Maryam wacce ita ma tuni ta shirya,a bisa hanyar su ne ta zuwa school Munat tace "ƙawata wai baki san jiya ina zuwa na tarar da mun yi baƙo soja ba?"da sauri Maryam tace "ke haba?dagaske?in ji dai baki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

2 Comments On SOJANA
avatar
yakubu-4

10 months ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
yakubu-4

10 months ago

Reply

Allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment