Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna mashi ƙiyayar da kike masu ba a fili"dariya Munat tayi tace "a'a wlh ya na da kirki da takura har wayar shi ya bar min da zai tafi sallah kuma da dadare ya kira ni da wayar Musto mu ka sha hira"Maryam tace "halan son ki ya ke da har zai kiran ki?"hararar ta tayi tace "ke banza wannan fah COUSIN ɗina ne da baban shi da Mami uwar su ɗaya uban su ɗaya to miye dan ya kira ni?"Maryam tace"ah na zata abokin Mustapha shiyasa,am ya kamanin fuskar shi suke ya na da kyau ko kuwa ?fari ne ko baƙi"shiru tayi mata can kuma tace "uwar shi buzuwa to miye gamin shi da baƙi kuma?Ko ni ai dan na biyo baƙin Abba ne amma ai kin ga yadda Mami take fara sol ko?"kai Maryam ta gyaɗa mata "to Moha yafi Mami fari dan in ba gaya maki aka yi ba cewa za kiyi Balarabe ne tsabar kyau da farin fatar shi uwa uba dogon gashin kan shi wanda ko wata maccen albarka"wani irin abu ne Maryam taji ya caki zuciyar ta yayinda tsikar jikinta ta tashi,sak kusan irin mijin da ta ke so cikin rawar murya tace "am ƙawa nace ya na da saje da geme kuwa?"tsuki Munat ta ja tace "ke kam akwai banza ina soja ina gemu?sajen dai shi ma ba sosai can ba in da kin gani gwanin kyau"ta ƙarashe maganar tana sakin murmurshi daidai nan kuma suka shiga layin da zai kai su CSP HIKIMA inda a nan ne school ɗin su.
Suna shiga direct bakin 3A suka wuce inda mutane ƙwarara ne kawai suka zo,har za su zauna Maryam tace "am ina zuwa bari na je na dawo"ta faɗa tare da fita ta nufi direction ba jima ta dawo hannunta riƙe da fararen takardu irin uwanda ake zane da su.
"Please yi min dessiné ɗin sojan nan na gani,kuma da kayan sojojin nike son ganin shi"cewar Maryam tana aza takardar bisa table ɗin da Munat ke zaune.
Dariya tayi tana mai fiddo crayon tace "alƙur'an sai kin biya ni na gaji da yi maki zane"Maryam dai ba tace komi ba sai zaunawa tayi cike da murna.
Kasancewar Munat gwanar zane ce cikin ƙanƙanan lokaci ta zana shi raɗam nan ta shiga saka mashi couleur irin na tenue soja,sai da ta gama ta miƙawa Maryam tana murmurshi.
A tsaye ta zana shi hannun shi duka biyun cikin aljihun wandon shi,fafaɗen ƙirjin shi kuwa galoli ne kusan biyar kan shi sanye da béret rouge wato ja hulla,fuskar nan a murtuƙe kamar wanda ya ke filin daga yayinda sajen shi ya ƙawata fuskar.
Taɓin da ƴan ajin suke suna cewa "waooo!yayi kyau"shi ya maido Maryam daga duniyar tunanin da ta lula wai ga ta ita da Mohammed a cikin gidan su na aure har da ƴan yaran su😱.....



Please in kin karanta kiyi share domin Allah🙏🏻
[29/05 à 17:07] MRS SADAUKI 💫: *SOJANA...*💞



☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*



Chamsiya Laouali Rabo✍🏻



Page 5-6


Amshe dessin ɗin Munat tayi tace "to bani kaya na cikin ɗaki zan laƙa shi na ga kamar ya fi ko wane zane da ni ke yi kyawu"marairaice fuska Maryam tayi tace "dan Allah ƙawata ki bar min kin ga dama tun farko ni soja ke burgewa ke kuma haushi sojawa ke baki"taɓe baki Munat tayi tace "yanzu duk saboda dessin ne kike wani kwantar da murya kamar ki na neman gafara ?to na ƙi ɗin yaga shi ma zan yi"da sauri Maryam ta fara girgiza kai tace "dan Allah kar ki yaga bari na saye in ma ba zaki bani kyauta ba"ta faɗi hakan tana mai fiddo 1000f cikin sac ɗinta ta miƙawa Munat karɓar kuɗin tayi tana mai bata zanen.
"Nasara ai ya hana aikin banza ba zan zauna na zana hoton ƙaton banza ba a kyauta"cewar Munat tana saka kuɗin cikin jakka,hararar ta Maryam tayi tace "wlh ni *SOJANA* ba ƙaton banza ba ne iyeee sai dai can in Buhari mai shayi ne "dariya Munat ta gagaɓe da ita tace "yo ni ina ruwana da wani Buhari mtsw can ta matse maku ke da shi,tunda ni ko abun hannun shi ban taɓa ci ba asali ma saboda shi na tsani shayi gaba ɗaya"shiru na ɗan lokaci Maryam tayi kafin tace "amman kin san ya na son ki sosai ko?kuma ban ga abinda ya ke da ba ɗan saurayi kyakkyawa da shi"dundu Munat ta kai mata ga baya tace "eh yau na san ba ki ƙaunata ace wa na aura?in ce Buhari mai shayi na bakin school ɗin mu?"ta tufar da yawu ta cigaba da cewa "Allah kiyaye min"
"Ai sana'a ba ta da kaɗan kuma da ka auri marar aikin yi gwara ka auri mai shayin ko ba komi ya na da zuciyar nema bai tsaya jiran a bashi ba"cewar Maryam cikin fushi dan halin ƙawarta ta ya fara bata haushi duk wanda yace ya na sonta sai ta nemo aibun shi,"ta baya ga wasa kenan wai ihu bayan hari,ke mi zai hana ki aure shi ?ai ina ce ke ma mace ce"cewar Munat tana mai tashi ta barwa Maryam wajen ta sake wani table tuni kuma malamin da zai fara yi masu cours ya shigo aji.
Karatu ake masu amma sam hankalinta bai gare shi,tunaninta da ruhinta sun tafi gun mutumen da ke can cikin dokar daji wato Mohammed.Ba ta san ko miyasa ba kawai ji take zuciyata na yi mata zafi na zanen shi da tayi kuma ta sayar ma ƙawata Maryam,sam ji tayi ba za ta haƙura ba amshe kayanta za tayi ta mayar mata da kuɗin ta.
Murmurshi tayi tuno maganar shi ta jiya ```bari Mimi kar ki ɓallo min ruwa``` zuciyarta ta tambaya ko mi ya ke nufi da haka? oho.
Mr Arman wanda tun ɗazu ya ke lura da ita yayi interrogé ɗin ta ya na mai kiran sunan ta,firgigit tayi tana mai zuba mashi manyan idonta masu kamar madara uwanda kuma su ne suka fi jan hankalin Mr Arman a tare da ita.
"Quel est la différence entre aimer et plaisir?"rau-rau tayi da ido kafin tace "banbanci SO da BURGEWA kamar yaya kenan?"ƙureta yayi da ido ta yadda zai isar da saƙon zuciyar shi cikin sauƙi Allah ya sani saboda ita ne yau ya zaɓi wannan cours ɗin,cikin cool voice yace "eh shi mu ke son sani"shiru tayi ta ɗaga idonta na wani lokaci alamar tunani kafin ta saki murmurshi tace "shi SO abota ce in ka na son mutum har abada son ba zai canzawa ba bima'ana in wani ya son wata zai so ta ne a duk yadda ta ke ko da kuwa ta canza halaye ko kuma ta samu wata nakasa a jikinta yayinda shi kuma BURGEWA na ɗan lokaci ne ta yiyu wani na burge ni saboda wani abu na shi kamar dai ace wata aikin soja na burge ta shiyasa ta ƙulla alaƙa da wani soja to ka ga duk ranar da abokin nan nata ya bar aikin soja shikenan ya bar burgeta dama ba shi ne ke burgeta ba aikin sojan ne"tsit ajin yayi kowa na saurarenta da kallonta ba ma kamar Maryam,Mrs Arman kuwa murmurshi yayi yace "to wane za ka fi ji a ranka wanda yace ya na sonka koko wanda yace kana burge shi"wani ɗaga ido tayi🙄 tace "to ai na ma sai an tambaya ba duk wanda yace ya na sonka ai ya gama maka komi,miye amfanin burgewa tunda ita ta ɗan lokaci ce?"murmurshi yayi mai kamar dariya dan har sai da fararen haƙoran shi suka bayyana kafin ya bata umarni ta zauna.
Nan yace kowa ya ɗauki takarda zai masu text akan haka, kasancewar ko wane ɗalibi ya san Mr Arman na da sauƙin kai ne yasa ba su wani tada hankalin su ba sosai.
Ya na fita Mr ɗin Mathématiques ya shigo shi ma yayi na shi cours ɗin ya fita.
Lokacin cin abinci na yi Maryam da Munat suka fita,Buhari na ganin su ya shiga haɗa masu indomie da ƙwai sai kallon Munat ya ke wacce ta sha kunu sai wani kaɗa ƙafa ta ke.
A gabanta ya aje mata plate ɗin yace "Mrs B da fatan an tashi lafiya?ya karatun?"a taƙaice ta amsa mashi da "alhamdullah"ta jawo plate ɗin ta fara juya cokali ciki,Buhari bawon Allah kallon ta yayi ya kalli Maryam ya na yi mata signe da hannu Maryam tace "Mijin bari har mu gama za muyi magana"da fara'ar shi yace "toh bon appétit"taɓe baki Munat tayi bayan ya fita daga cikin ƴar rumfar da students ke shiga su ci abinci tace "kin ji kinibibi har da wani turancin ƙarya dan nace yayi école,wai wace uwar ce ma za ku hiranta naji kina cewa har mu gama?"shareta Maryam ta fara yi ta far kurɓar tea zuwa can tace "wannan kuma ba matsalar ki ba ce,naji yau dan rainin hankali a kaina kika bada exemple to miye dan nace ina son soja?"dariya Munat tayi ta aje cokalin hannunta tace "wlh Allah ne ya so ni ina fara tunani kika faɗo min a rai sai kuma na tuna zancen Mami na jiya da naji ta na gayawa Mustapha wai tun ina ƴar ficiciyata Mohammed ke sona ni kuma wlh ban ma san shi ba lokacin da ya tafi aikin soja ko wando ban fara sawa ba"ido Maryam ta fiddo tace "wai dagaske ne?to a yaushen ne kika ji Mami na gaya mashi ɗin ke da kika ce Musto bai zauna gida ba duk wuni jiya?"annurin fuskar Munat ne ya ɗauke tace "wlh ƙawata jiya ma tsoro aka ta bani sam ban yi barci ba to sama-sama na jiyo hirar ta su"cikin jimame biyu Maryam tace "kin gayawa Mami kuwa?"kai ta girgiza tace "a'a kin san fah da zarar na gaya mata wajen granny za'a kai ni kuma ni wlh har yanzu zuwa tsoron zuwa gidanta ni ke da ita karan kanta saboda tsafi da borin da take"Waro ido Maryam tayi cike da mamaki tace "wai ki na nufin har yanzu granny ba ta bar bori ba?"baki Munat ta taɓe tace "hum bari ma za tayi kenan?ai mutuwa ce kawai za ta rabata da harakar tsafi kin san jajayen buzaye da kafiya babu irin yadda Uncle Harun bai yi ba dan ta bari amman ta ƙi ya wai neman kuɗi ne ta ke kuma ba za ta bar gadon gidan su ba"suna tsaka da hira ko abincin ba su gama ci ba aka buga sonné na komawa aji.



Munat na dawowa daga school agajiye ta shigo gida,wanka ta fara yi sannan ta fito zuwa falo inda Mami ke zauna tana kallo."Washhh Allah na gaji wlh mi aka dafa Mami?"cewar Munat tana mai zaunawa bisa capet kafin Mami tayi magana Mustapha da ke kwance bisa salon yace "to acici kazar gidan gona kullum ci ko gajiya ba kiyi dubi yadda kika zama wata ƙatuwa kamar wace za ta tafi kokowa"turo baki tayi gaba tace "to haka nan zan zauna babu cin abinci?"hararar ta yayi tare da cillo mata kwalin waya ƙirar itel yace "je ki ta ci in abun ƙwarai ne in kika kasa tashi ai sai a rinƙa tura ki cikin baro"ita dai bata kula shi ba sai murna ma da take ganin ya bata sabuwar waya.
Kunna wayar tayi dan tuni an saka Batur da sim "na gode Babban yaya"baki ya ja yace "in kuma na ga kin cika sakarci amshe ta zan yi can ya rinƙa kiran ki da wayar Mami"ba tare da tace mashi komi ba ta fara latsa wayar video da waƙoƙin da ke cikin memoryn ta fara kallo har sai da ta gaji sannan ta dakata caji.
Da dadare misalin ƙarfe tara kira ya shigo wayar,ba tare da yin tunani ba ta ɗauka tana mai cewa "hello?"kai ya girgiza yace "Mimi sallama ya kamata kiyi ba ɗabi'ar turawa ba"in ba dan taji ya kirata da sunan da shi kaɗai ta san ya na kiranta ba da sam ba za ta gane ko wanene ba saboda yadda Muryar shi ta ɗan shaƙe "mi ya same ka ne naji muryar wata kala?"abinda tace kenan "wata kala kamar ya?"Mohammed ya faɗa a ɗayan ɓangaren tace "eh babu sugar kamar ta wani ɗan daba ta zama ƙatuwa kuma a shaƙe kamar munafiki"ido ya lumshe ya na saurarenta wai shi Mohammed shine ake ma tsiwa ana gaya mashi magana?kuma ƴar ƙaramar yarinya wacce ba ta wuce ya murjeta ba kamar kiyashi amman so hana ganin laifi, murmurshi kawai yayi yace "banda lafiya ne mura ta kama ni"taɓe baki tayi tace "ashe abu na gida makaɗi da ya yaje gidan mabushi,to ai mura ita da buzaye kamar Ɗan juma da Ɗan jummai suke"cikin kasalar da ta saukar mashi sakamakon jin muryar ta kaɗai da yayi yace "Mimi ba ki tausayina?kece fah silar ciwona dan da ba ki sani yin wankan asubahi ba da mura ba ta kama ni ba"a mamakance tace "Ni kuma?na kira ka koko tada ka nayi nace Moha tashi kayi wanka?"dafe goshi yayi dan ya ga har yanzu da sauran ƙurciya ga Munat yace "to mafarkin ki nayi"waro ido tayi tare da rufe fuska wannan karon kuwa ta gane mi ya ke nufi.
"Kin yi shiru" "to mi zan ce?"ta bashi amsa yace "Mimi na wlh ina cikin wani hali na buƙatuwa ya kamata ki tausaya ki karɓi tayin soyayyata ina zuwa a yi mamu aure a wuce wurin,dan ina jin a jikina ba zan iya haƙurin rashin ki kusa da ni ba"wani abu ne Munat taji ya tsarga mata tun daga tsakar kai har cikin tafin ƙafa,murya na ɗan rawa tace "Moha kayi haƙuri ni na tsani soja ba zan iya auren ka ba"ido ya rumtse da ƙarfi ka azabar da ya ke ji a mara ga wata kuma tana sukar shi da kalaman ta.
A wahalce yace "wlh Mimi ke ce rayuwata in babu ke babu ni in dai zaki aure ni na yarda zan aje aikin soja"Waro ido tayi ta shiga girgiza kafin ta kai da cewa wani abu network ɗin wajen su Moha ya yanke......




*PAID BOOK NE*
[29/05 à 17:08] MRS SADAUKI 💫: *SOJANA...*💞



☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*



Chamsiya Laouali Rabo✍🏻

🆓 7-8


Wani irin baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyar Mohammed bayan ya gwada kiran Munat yafi a ƙirga ana maido mashi kiran alamun babu réseau,a ƙarshe ma duka Sim ɗin suka sauka.
Ba dan ya so ba ya sauka daga kan dutsen ya nufi makwancin shi,kwantawa yayi ya na mai dafe zuciyar shi wacce ke barazanar faso ƙirjin shi ta fito tsabar son da ya ke yiwa Munat da kuma muradin kasancewa da ita wanda ya ke ji kusan kullum a ko da yaushe kuma.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "ita ce ƘADDARA ta tabbas son Munat JARABTA ne(Haj Maryam Sakatare)in ba haka ba tabbas ba zan susuce har haka ba a kan ƙanƙanuwar yarinya"Omar da ke kusa da shi yace "wai akan wa kake magana koko baby Angel ɗin ka?"shiru Mohammed yayi sam bai san a fili yayi maganar ba da "um"kawai ya amsa mashi, Omar ya cigaba da cewa "to ba cousine ɗin ka ba ce kawai ka shaidawa iyaye a san nayi ba wai ka zauna dakon son yarinya ba tun ta na cikin tsumman goyo amman ta zo ta na haɗa maka café ba(tension😂)"cikin fushi Moha yace "wai ina ruwan ka ne?ba café ba in ta na so ta haɗa min har da Lipton ai ni zan sha ba kai ba,ya fah ka mata ka shafawa Mimita lafiya kusan kullum sai kayi zancen ta wanda ban san dalili ba kawai ka sata faɗuwar gaba babu gaira babu dalili"dariya Omar yayi yace "to ai doli na sa ma ido saboda ni kuke cutarwa a kullum ku na maida min aiki baya,sai ka kusan ka warke kuma sai kace min marar ka na ciwo har da bay..."dundu Mohammed ya kai mashi ga baya yace "Allah shirya ka wlh ai ba yin kaina ba ne kuma wannan shine cikar mazantakar wasu a shekara ma ba su sanin wane matsayi suke namiji koko mata maza"Omar yace "ai ba lalle sai ka sani ba kai ma abinda ya sa ni ke sani dan babu yadda ka iya ne na zamo likitan ka sannan jaraba ka tayi yawa ko hoton wannan mitsitsiyar yarinyar ka kalla shikenan har ka shiga shauƙi"harar shi yayi duk da ya san ba zai gani ba kasancewar dajin da suke babu haske sai duhun itace "kai tafi can ɗan iska ni ban iya maka bar ni ma da abinda ya sha min kai"cewar Mohammed ya na komawa luf kan gado ya kwanta Omar kuwa cewa yayi "ka sa minjaye dan wani wa kai kuma gatanar gizo ai ba ta wuce ta ƙoƙi dama na san an runa wai an saci zanen mahaukaciya ko da na ga ka tafi neman network na san kai ma sai ta haudo ma naka"da ƙafa Mohammed ya ɗan shure shi yace "arrr!to ni can na nufa ba kawai haushi ni ke ji réseau ya yanke a daidai wurin da ni ke buƙatar jin amsa"taɓe baki Omar yayi yace "Allah ya ƙara mayen appel"Mohammed bai tanka shi ba sai ma tunanin da ba zai fishe shi ba ya shiga yi wato na Munat.




A ɓangaren Munat kuwa cilli tayi da wayar tana zumɓuro baki ita a tunaninta haushi ya ji dan tace ba ta son shi,a fili tace "A'i ta gaida A'ishah ni gaba ta kai ni gobarar Titi, Allah na tuba na rasa wanda zan aura sai buzu buzun ma fari kuma soja tab ba da ni ba.In haka ta kasance ai naji kunya kuma zan sha iskanci gun Maryam dan haka ban so aka kas..."motsin da taji mai haɗe da ƴar buɗa yasa sauran maganar laƙewa cike da tsoro ta fara waige-waige amman ba ta ga komi ba.
Toilet ta ke so ta shiga ta ɗauro alwala ta kwanta amman ta kasa shiga tsabar tsoro,cikin ƙarfin hali ta buɗe ƙofar toilet ɗin tana shirin shiga taji ta taka wani abu mai taushi da kuma shegen sanyi wani uban ihu tayi wanda yasa Mami da ke shirin zuwa ɗakinta yin saurin shigowa.
Wani tsalle Munat tayi da zumar ta dira bisa gado aka samu akasi ƙafar ta gaubce ta faɗi ƙasa,ɗaga ƙafar da tayi ya ba ƙaton kwaɗon🐸 damar tsallawa ya shige toilet.
Ta miƙar da ita tana cewa "subahanallah Auta ba ki ji ciwo ba?"kuka ta fashe da shi ta faɗa jikin Mami daidai nan Mustapha ya shigo ya na tambayar lafiya?da hannu Munat ta nuna mashi ƙofar toilet.
Shiga yayi can ya tsinkayi kwaɗon sai tsalle ya ke ya na hawon gini,tsuki yayi ya fita ya ɗauko abun kwasar shara ya ɗauke kwaɗon.Ihu Munat ta sake yi ganin kwadon ya ƙuro mata ido ya na kallo daga cikin pelle,bubuga bayanta Mami tayi tace "shikenan dai yanzu an fitar da shi,ko daga ina ma ya shigo?"cikin kuka tace "Mami ki tafi da ni ba zan iya kwana a nan ba tsoro ni ke ji"Mustapha da ya dawo yace "uwar mi za kiyi a can part ɗin Mamin?ina ce dai wajen ƙiriniyar ki kika kwaso shi a waje in ba haka ba mi zai kawo kwaɗo har ƙurya ɗaki?"Mami tace "nima abinda nace kenan ƙila cikin babouche ɗin ta da suka kwana waje ya shige ita kuma ta kwaso su ba tare da ta duba ba"banda shasheka babu abinda Munat ke yi.
Wayar hannun Mustapha ce ta ɗau ruri ya ɗaga ya na gaishe shi can kuma yace "lafiya lau Daddy ga ta ma kusa da ni kwaɗo ne ya shigo ɗakinta shine fah take wannan kukan"a can ɓangaren Daddy yace "haba shiyasa naji duk hankalina ya ƙi kwantawa ashe autata ke kuka bani ita naji gaskiya kwaɗon nan bai gyara min ba har zubar da hawayen Auta"cikin jin haushin banbancin da Daddyn nasu keyi tsakanin su yace "ai ta na jin ka ba sai na bata da hannun ta ba a yadda ta firgice ai sai ta sakar min waya ƙasa"hawaye ta goge tace "Daddy nima ai nayi sabuwar waya ka kira bisa layina" hararar ta Mustapha yayi ya na mai kashe kiran ya turawa Daddy number ta kamar yadda ya buƙata.


*ASALIN LABARIN...*


Attahir da Fadimatu sun kasance jajayen buzaye na usuli ,auren haɗi (na gida)aka yi masu.
Allah ya azurta su da ƴaƴa biyu mace da namiji,Alzuma shine babba sai ƙanwar shi Agaisha.Sun taso cikin so da ƙaunar junan su sai sun tsani abinda suka tashi suka ga iyayen su na yi wato harakar tsafi da bori,babu yadda Alzuma bai yi ba ganin ya rusa wannan baƙin gado da iyayen shi suke ikirarin gada su ka yi amman abu ya cuttura tun abun na damun shi har ya kai ya raba kan shi ya bar zancen.
Lokaci guda aka yi bikin su na aure shi da ƙanwar shi,inda Alzuma ya auri farar buzuwa mai suna Maimuna yayinda Agaisha ta auri bafulatnin Zinder mai suna Illiyas.
A shekarar farin Allah ya azurta su da samun ƴaƴa maza Agaisha ita ta fara haihuwar Ɗanta Mustapha sannan Maimuna ta haifi Mohammed wanda bai wuci wata biyu ba ne a tsakanin su kuma tun daga wannan lokacin haihuwa ta ɗauke masu su duka biyun.

Kasancewar Alzuma mai mugun son yara ne yasa shi ganin likita an tabbatar mashi da lafiyar su lau ƙwan haihuwar shi ne sam ba zai iya fécondé ba,sosai hankalin shi ya tashi wanda har ya taɓa lafiyar shi kusan kullum cikin tunani ya ke ko barci bai iyawa.
Tsakar dare kamar wanda aka dadaɓa haka ya tashi daga barcin da ya ke ya fito waje,suratai ya fara ji a cikin ƴar buƙar da Attahir ke tsafin shi kamar zai wuce sai kuma yaji ya na ambaton sunan shi ```Ta yaya za ku lalata ƙwan haihuwar Alzuma duka bayan ba haka mu kayi da ku ba?``` cikin wata murya marar daɗin amo aka bashi amsa ```dama ƘWAI ƊAYA (Haj Maryam Sakatare ku nemi na ku kar a baku labari)kawai mu kayi alƙawarin za mu bar mashi shi ma ɗin saboda a samu magaji ne kuma ga shi nan an samu``` cikin ɓacin rai Attahir wato mahaifin Alzuma yace ```kar ku yi min haka kar ku cutar da jinina ku daina...``` kutso kan da Alzuma yayi cikin bukar ne ya hana shi ƙarasawa a take kuma hayaƙin da ya cika wata ƴar ƙwarya ya shiga ɓacewa,wata irin maƙura Alzuma ya yiwa mahaifin shi ya kamo maƙogwaron shi ya riƙe nan idon Attahir suka firfito tare da kafewa .
Alzuma bai sake shi ba sai da yaji zuciyar shi ta daina bugawa lumfashin mahaifin shi ya tsaya cak,nan ya faɗi ƙasa babu rai.
Ko da gari ya waye Maa (mata gun Attahir uwa ga su Alzuma da Agaisha)ta fito ta nufi bukar tsafin mijinta dan tun a daren jiya aljanun da ta ke biya na bori sun gwada mata mutuwar Attahir,kuka ta fasa tana kiran sunan Alzuma.
Maimuna ce ta fito da gudu jin kururuwar Maa tare da maganganu maras daɗin ji,tsaye tayi turus gaban gawar sirikin nata wadda Maa ta jawo zuwa waje.
Kawar da ido Maimuna tayi saboda gawar babu kyawun gani kafin ta fashe da kuka tana kiran sunan Alzuma amman shiru ya ƙi fitowa.
Alkaba'in da Maa ke yi inda ta ke cewa "yadda aka tarwatsa farin cikina nima sai na tarwatsa farin cikin duk wanda ya kashe ka mutum ko aljan,ga shaida nan ina gani cikin idonka ba mutuwa Allah da Annabi ba ce kayi"wannan zantuka karaf suka shige cikin kunnen Alzuma da fitowar shi kenan idon shi duk sun kaɗa sun jajur kamar barkono tsabar baƙin ciki da takaici da kuma raɗaɗin da zuciyar shi ke yi.
Ɗagowa Maa tayi daga jikin gawar ta dubi Alzuma tace "sun kashe shi ni kuma na ɗauki aniyar *ƊAUKAR FANSAR RUHI*(My next novel in shaa Allah)yadda ya bar duniya a tozarce sai na aika duk uwanda suka kashe shi lahira kuma daga yau na ɗauki kambun sarautar tsafin koko ka na so na baka ?na san kai ma ruhinka ya cika da muradin kashe mahaifin ka"Waro jajayen idon

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

2 Comments On SOJANA
avatar
yakubu-4

10 months ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
yakubu-4

10 months ago

Reply

Allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment