Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kallon cikin ido......
[29/05 à 17:11] MRS SADAUKI 💫: 🆓 13-14


Munat sam ba ta lura da Mustapha da yayi mutuwar tsaye ba,ta kai hannunta za ta ɗaga rigar Maryam tana cewa "mu ga ƙululun kuma shine ba ki tafi asibiti ba ko tsoro kike ji ace Cancer ne?"ta buge hannunta ta na mai cigaba da kallon Mustapha wanda shi ma sam ya kasa motsawa ba tare da ya san dalilin tsayuwar ta shi ba.
Ganin ta kafe wuri guda da ido ya sa Munat kallon gun, turo baki tayi tace "kawai sai a shigo ma mutane ɗaki ba sallama"yadda tayi maganar ciki-ciki ko Maryam da ke kusanta ba ta ji ba balle wanda aka yi dan shi.
Cikin ta ya yo ya na cewa "dan uban ki ni kike yiwa gunguni ?uwar mi za ki duba cikin rigar ta ko likita ce ke?"a sangarce tace "to ba ita tace na duba na ga ko minene ba😩"harara ya banka mata yace "ke uwarta ko?to na sake gani ku na ɗage-ɗagen rigar ku ga ikon Allah,wlh sai nayi maki ɗan banza duka shashashu da baku san ciwon kan ku ba kuma ki tashi ki cire wannan ƴar banzar rigai mai kama da ta karuwan daji"Mami da shigowar ta kenan tace "miye haka Mustapha?ina ruwan ka da rigar ta wai miyasa ka cika sa ido ne han?"Mustapha yace "haba Mami sabida Allah wannan shigar ƴar musulmai ce?dubi yadda rigar ta ɗame jikinta kuma rigar ko hannuwan kirki ba ta da su" "to ai ba waje ta fita da ita ba cikin gida ne ta ke"cewar Mami ta na son kare autar ta.
Cike da jin haushi yace "sai kuma aka ce ya halitta ayi yawo tsirara cikin gida?yanzu in fah wani ya shigo ya ganta a haka?"Mami tayi shiru ta na nazarta kalaman shi sai ta ga kamar ya na da gaskiya duba da irin tsarin halittar Munat ko ina a cike ya ke,cikin fushi ya nufi ɗakin shi Mami tace "abincin fah?"ba tare da ya juyo ba yace "a kawo min"gaban Maryam ya faɗi dan kuwa ta san ƙarshen ta ita za'a aika,kallonta Mami tayi tace "ɗoki abincin shi ki kai mashi ga ya can kan table ki "ba dan ta so ba ta miƙe a sanyaye ta ɗauka tare da nufar ɗakin shi.Ƙofa ta bubuga ya na jinta yayi banza da ita can da ta gaji ta tura ƙofar tare da yin sallama ta tsaya bayan labule sai da ya amsa mata sannan ta ida shiga.Bisa ɗan ƙaramin table na katako ta aje abincin tana shirin juyawa taji yace "dawo ki zauna "a dake.Da sauri ta waigo ta na kallon shi alamun tsoro ƙarara bisa fuskar ta,zaunawa tayi ƙasan Capet ta sunne kai zuciyarta na lugude.
Har ta fidda tsammani sai kuma taji muryar shi ya na cewa"Maryam miyasa kuke da ƙiriniya?Na zata ke mai hankali ce saɓanin Munat ashe taron kofi da farenti ne?miyasa kuke yin abu kamar wasu yara ko ba ku san kun girma ba ne?Yanzu da kike son ki gwada mata ciwon da ya same ki magani za ta baki?"kai Maryam ta girgiza ya cigaba da cewa "miyasa ba za ki gayawa mahaifiyar ki ba sai wannan wacce kwanyarta ita da ta ɗan yaro duk ɗaya?"kuka Maryam ta fashe da shi tace "Ni kunya Mama ni ke ji"sororo Mustapha yayi yace "ka ji wani sakarci kunya Mamar ki kike ji amman ba ki jin ta ƙawar ku?hummm wlh mata ƙaramar ƙwaƙwalwa gare ku in ku na da wata damuwa maimakon ku faɗe ta inda za'a ayi maku magani kun fi son faɗar ta inda za'a baku shawara.Gayamin tun yaushe kike jin abun?"tana matsar ƙwalla tace "2week"kai ya jinjina yace "ok tun da gobe weekend ne ki isko ni Clinic Agaji da misalin ƙarfe goma na safe lokacin na hau aiki"da "toh"ta amsa yace "tashi ki tafi dan Allah kuma ki rinƙa yiwa ƙawar ki faɗa ta bar saka ƙananun kaya"kai kawai ta ɗaga ta na fitowa taji wani irin sanyi har sai da ta sauke ajiyar zuciya.

Munat ta kalleta tace "mi kika tsaya ko dukan ki yayi?"kai ta girgiza tace "a'a yayi min dai nasiha kuma wlh da gaskiyar shi sam ba mu da nutsuwa daga ni har ke sannan ya kamata ki bar saka irin wannan kaya dubi fah shatin nipples ɗin ki fah ana gani"taɓe baki tayi tace "toh Mami wacce ta kawo ni duniya,kawai sai nayi ta fama da manyan kaya daɗa zafi ya kashe ni hum"tayi ƙyaci tana mai kwantawa tare da cigaba text ɗin da suke ita Mr Arman.


Maryam na zuwa gida ta shige ɗaki number Mohammed tayi ta training amman bai shiga hakan ya sa ta shiga aika masa text mai ɗauke da kalaman soyayya wanda ita kanta ba ta san ta iya su ba sai yanzu.Ta rungume wayar a ƙirji tana sakin murmurshi ta matsu ta ga réel visage ɗin shi ko da kuwa a hoto ne,zumbur ta miƙe jin ƙululun na yi mata yawo ita har tsoro ta ke ji a zuci tace "kar dai Cancer du sein ne ya same ni kamar yadda Munat ta ce"a take wani tsoro ya kama ta tuna har yanke breast ake in yayi tsanani a fili tace "shikenan na rasa *SOJANA* ta yaya zai so ni da sein guda "nan ta fara matsar ƙwalla bisanin kuma ta shige toilet dan duba ƙululun 😹.



A can ƙauyen Zinder kuwa sosai Mohammed ke samun kulawa ta likitan shi Omar tare da ta mai maganin macizai.Su na fita aiki a duk ko wane dare sai dai a bar Mohammed shi ɗaya kamar maye, wannan abun ya na mugun ɓata mashi da rai babban baƙin shi kuma shine babu waya a hannun shi dan ya matsu yaji da wa Mimi ke waya.
Ya na kwance kishingiɗe da misalin ƙarfe sha ɗayan rana,babu kowa sai shi ɗaya kamar an ce ya buɗe idon shi haka ya tsinkayi wata farar mace doguwa siririya sanye da fararen kaya ta na tunkaro.Lumshe ido yayi ya buɗe sai kawai ya ganta har ta kawo kusa da shi cikin second da bai wuce ɗaya zuwa uku ba, murmurshi yayi ya fara karatu sai ji yayi tace "ba cutar da kai zan yi ba nima mutum ce kamar ka"bai kulata ba ya cigaba da karatu ba shiri ta ɓace ɓat.
A fili ya furta "Ni za ki yiwa baiguwa?to kurwata tafi ƙarfin ki tun kafin na san ko wanene ni aka wanke ni da ayar Allah dan haka ki ƙarata can gaba"abun mamaki kuma sai ta ɓullo ta wani ɓangare ta na magana da asalin muryata na latizuwar mace "yayi jikan Sarkin borin ƴan Agadez masu"bai dai kulata ba yayi banza da ita irin wannan kan ki dai ake ji.
Ba jimawa group 1 nasojawan suka dawo wanda Omar ya na cikin ƴan group ɗin,labari Mohammed ya bashi irin baiguwar da wata mayya tayi mashi.Omar ya zaro ido yace "shine kake zaune? wai in ma tambaye ka daga ina ta fito?mutanen dajin nan fah sai ka ƙirga su kuma duk Fulani ne"Mohammed na shirin yin magana sai ga Chef ya tsaya a gaban su tamkar wani zaki,taɓe baki Moha yayi dan shi sam bai ƙaunar Chef haka kuma bai jin tsoron shi ko ɗaya a zuciya ya na yi mashi biyayya ne saboda shi ke gaba da shi.
"Na ce ka tashi ka taka ƙafar na gani ina son ka fita aiki gobe"cewar Chef ko kallon arziki bai samu ba balle ya sa ran yi mashi magana.Zungurar shi Omar yayi ya waigo ya harare shi kafin yace "ta yaya zan taka ƙafar alhalin ban ji sauƙi ba ko dan ciwon ba'a jikin ka ya ke ba?"ya na maganar ne ya na kallon Omar tamkar shi ya tambaye shi.Wani ƙuluƙulun baƙin ciki ne ya turniƙe Chef "to doli ka tafi aiki tunda sai da kayi rantsuwa kafin a ɗauke ka"cewar Chef a hasale murmurshin gefen baki Mohammed yayi yace "in kuma na aje aikin sai ya kenan?za'a bar ni nayi jinyar kaina ne koko tilasta ni za'a yi sai na je?"shiru Chef yayi a zuci yace "wannan an yi shegen yaro kin ji a tambaye shi dalilin ajen aikin na shi yace ni,ɗan banza ba za ka ɓallo min ruwa ba garin neman gyaran gira a rasa ido"cike da borin kunya ya bar wajen ya na mai baiwa Omar ya biyo bayan shi,harara Mohammed ya bi shi da ita yace "munafuki".



****AGADEZ


Maa ce zaune gaban wani madubin tsafi gefe da gefen ta kuwa wasu baƙaƙen tasa ce sai tururi ke fita,madubin ta shafa ta na karanto ɗalasiman tsafi amman shiru madubin ya ƙi buɗo komi sai wani gurzajen image wanda ta kasa tantance namiji ne ko mace.
Cike da baƙin ciki ta rufe madubin da baƙin ƙyalle ta tashi tsaye ta na zagayen ɗakin,"doli ne nayi hijira zuwa Japon tsafina yayi ƙasa ƙwarai ga shi kuma har yanzu ya kasa gwada min wanda ya kashe min Attahiru na,wlh nayi rantsuwa da jinin Kanana Zaffar sai na ɗanɗanawa makashin Attahiru azaba irin wacce sai ya gwammaci mutuwa kan rayuwa tabbas sai na ɗau FANSAR RUHIN ka mijina muddin ban yi haka ba ban cika Iya ƴar bori ba"ta na maganar ne tana dunƙule hannu.
Tana cikin zagaye Jakadiya ta shigo ta kawo mata saƙon SARKI(Miss flower)na son ganin ta.Maa a gaban Sarki zaune kamar yadda ya buƙata ta dubi fuskar shi wacce ta a tunuƙe cikin rawani tace "Ya shugabana ina sauraran ka faɗi buƙatar ka na aiwatar kar ka ji shakka gayamin ko ma miye ya gusar da annurin da ke bisa wannan kyakkyawar fuskar ta ka"murmurshi yayi dan har ga Allah ya na son zama da Maa ko dan dadaɗan kalaman ta,yanzu ma wannan lafuza nata sun sanyaya mashi zuciya.
Miƙewa yayi tsaye ya bata baya ka nan yace "Sarkin Zinder ne ke nuna min ɗagawa ya na jinshi shi wani ne har ya fito a gaban bainar jama'a ya na cewa a soke al'adu sam ba su dace a musulunci ba,wai shirka ta fiya yawa a tsarin sarauta shiyasa har ake samun jefe-jefe a tsakanin sarakuna..."Maa ta miƙe tsaye ta na cewa "shi ɗin banza shi ɗin wofi,har shi ya isa ya dakatar da abinda mu ka tarar kakani da iyaye su na yi?yanzu mi kake so ayi?ɓatar da shi za'a yi koko cutar da ba ta da magani za'a tura mashi?"zuciya wasai ya juyo yace "ki yi abinda kika ga ya dace"Maa tace "an gama"cike da murna ta koma part ɗin ta domin ita a duniya in akwai abinda ta fi so to ƙeta ce ko cutar da wani.
Surkulenta ta shiga haɗawa uwanda sun fi ɗari sannan ta kirawo sarki dan tafi son ta aiwatar da aikin a gaban shi.
Babu tsoron Allah a zukatan su ko kaɗan,madubi ta shafa sai ga hoton Sarkin Zinder ya bayya a zaune bisa karagar mulki fadawan shi na ƙasa yayinda s'wasu dogarai su ke mashi fifita.
"Wannan fitsarin jinjirin aljani ne amfanin shi shine ƙarawa sihiri ƙarfin tasiri, wannan kuma sawun ƙafar Giwa ne amfanin shi shi kuma zai ta ƙarawa gangar jiki girma ne"cewar Maa tana mai zuba duk abinda ta ambata cikin ƙwayar da ta yanka baƙaƙen zakaru biyu,Sarki kuwa sai jinjina kai ya ke zuciyar shi fal farin ciki so ya ke ayiwa Sarkin Zinder sihirin da zai sa ya nemi taimakon ƴan bori dan kan shi,wani na hannun damar sarki ne ya shigo hannun shi riƙe da wata kwalba mai ɗauke da jinin raƙumin da Maa tace a yankawa doguwa.
Babu ɓata lokaci Maa ta shiga aikin ta tana amta sunan sarkin Zinder wanda kuma a zahiri suna kallon shi ta madubi,fatar jikin shi ce ta fara réagir inda ya ke jin wani irin raɗaɗi sunan Allah ya fara ambata cikin ƙaraji Maa tace "kar ka kira ma mu Allah kar ka ɓata min aiki "Sarkin Zinder da ya ji azabar na cigaba yayiwa jama'ar shi sallama ya shige ciki tare da kwantawa zuwa wannan lokacin ko hannun shi bai iya motsawa domin kuwa asiri gaskiya ne ya na kuma tasiri inda Allah ya so to hakan ce ta kasance da shi.......
[29/05 à 17:11] MRS SADAUKI 💫: 🆓 15-16


Wasa farin girki ciwon Sultan Hashim ne ya tsananta inda aka fancama neman magani kan na asibiti kan na gargajiya.Ana haka kwatsam kuma sai aka kawo mashi attaque ana son kashe shi wanda ko tantama babu aikin magauta ne,cike da tsumaye Sultan ya nemi a bashi matakan tsaro ba'a ɗau lokaci ba président ɗin Niger ya baza sojoji a gidan Sultan na Zinder tun farkon shigowa layin za ka ganin canji sannan a ƙofar gida ma an saka soji fiye da ashirin.
Kallo guda za ka yiwa Sultan ka san da ya na jin jiki kawai dai ta maza ce ya ke ya na ɓoyewa,Balkis uwar gida kuma mata ɗaya ƙwal ga Mai martaba ita ke jinyar mijinta domin Allah bai azurta su da samu haihuwa ba balle ƴaƴan su jinyace shi.
Wanka ta ke yi mashi ta na kallon ikon Allah da ya bi duk fatar jikin shi ya kankare kamar mai cutar kuturta,cike da tausayi irin na mata da miji ta tsane mashi jiki ta murza mai ta shafe shi sannan ta saka mashi kaya maras nauyi.
Kallonta yayi cike da so da ƙauna yace "Allah yi maki albarka Mar'atu saliha,da ina da iko da na zauna da ke dan kar na mutu hawayen ki su zuba sai dai wannan ciwon ba mai barina ba ne"kai ta girgiza tace "ya kai shugabana ka sani babu cutar da ba ta da magani,kuma duk tsanani ya na tare da sauƙi.Ka ɗauka wannan jarabta ce daga Allah dan saboda ita rayuwar ga duk wanda yace yayi imani da Allah da Manzonsa to tabbas zai dinga ganin ƙalubale na rayuwa kenan kala-kala,in ka rabu da wannan yau to ka shirya zuwan wata jarabawar gobe"duk da ciwon da ke cin shi bai hana kalaman ta samun gurbi a zuciyar shi tare da tasiri.
Yace "Tabbas haka ne sai dai ni abun ya fara bani tsoro likitoci sun ce ba su ga komi ba sai tension wadda dama na san ina da ita,masu bada maganin gargiya sun ce sihiri ne kuma sai magani ake amman shiru babu sauƙi"wani murmurshi Balkis tayi wanda yayi matuƙar ba Sultan mamaki amman sanin matar ta shi ta na da baiwar ɓoye ya sa shi yin shiru,tashi tayi ta nufi ƙofa tace "ka sani tun kafin wannan ciwon ya same ka tun tuni aka nuna min shi a mafarki kuma an tabbatar min da za ka warke ne"ba tare da ta jira cewar shi ba ta fice.Numfashi ya sauke dan kuwa ya san rabin mafarkan Balkis sukan zama gaskiya ne hatta attaque ɗin da aka kawo mashi tayi mafarkinta kuma ta gaya mashi tun kafin a kawo harin,ita tace ya cewa président ya na son a bashi matakan tsaro kuma sojoji.A zuci yace "Allah sa ma wannan karon ya zama gaskiya dan tabbas ina son na rayu a duniya ko da na ɗan lokaci ne"sallama Waziri yayi tare da shigowa,ya gaishe da Sultan kafin ya baiwa sauran mutanen da ke son ganin shi damar shigowa.




A firgice ya farka daga mumunan mafarkin da ya ke ya dafe zuciya,kamar wanda yayi gudun fanfalaƙe haka ya ke fitar da numfashi.Ruwan sanyi ya ke son sha amman babu hali tsuki yayi yace "kai rayuwa soja ba tayi ba da ranka amman kamar matacce"ƴar aci balbal ɗin ya ƙara ɗagawa nan hasken ta ya ƙaru,ƙafarshi ya kalla wacce ya ji wani irin raɗaɗi na ƙara shigar shi,lumshe ido yayi ya na ambaton Allah sai yaji raɗaɗin na ragewa.Maganar Abba ce ta faɗo mashi a rai «ka zamana mai yawan azkar da sallolin dare,ka riƙe imaninka ka sa yarda ka wajen Allah babu wani mahaluki da ya isa ya cutar da kai in ba Allah ya so hakan ba.Sannan ka sani ban koya maka wannan aikin ba dan ka cutar da wani a'a na koya maka shi ne dan tare halbin maƙiya Mohammed kar ka zamo raggo wajen yiwa kan ka aikin tsare kai daga magauta»gwabron numfashi ya sauke da ya gama tunanin ɗaya daga cikin zantukan da Abban ki ke yawan yi mashi a lokacin da ya ke koyar da shi ilimin tsibo😱.
Tashi yayi ya buɗe sac au dos ɗin shi ta sojawa,wata ƴar ƙarama jakka mai kama da ta fata ya fiddo wacce ke cike da wasu takardu da ƙullin magani barkatai.
Alwala yayi tare da yin Sallah raka'a biyu ya karanta addu'ar Istakara
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيـرُكَ بِعِلْمَكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ، اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الَأمْرَ (وَيُسَمِّي حَاجَتَه) خَيْرٌ
لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ
Ya na gamawa ya sha maganin da ya kaɗa cikin nono sannan ya kwanta.
A cikin mafarkin shi aka nuna mashi yadda karnuka ke bin shi a baya shi kuma ya na gudu har ya kusa shigewa ɗaki dan ya ɓuya wani kare ya samu nasara cizon shi,sai kuma mafarkin wata tsohuwa na tura shi cikin wasu irin ruwa masu mugun zafi yayinda gefe guda kuma ga ruwan sanyin da ya ke muradin shiga amman ta hana shi,mafarki na uku kuwa ganin shi yayi cikin wani ƙaton gida tangameme wanda bayi ne barjit suna kai da komowa yayinda shi kuma ya ke zaune bisa wata kujera ta haske gefen shi hagu da dama wasu Twins ne mace da namiji sun sa shi tsakiya.
Washegari bayan Mohammed ya gama sallah asubah ya tsaya ya na nazarta mafarkan shi,ya sani mafarkin karnuƙa maƙiya ne biyun ne ya kasa gane su.Nisawa yayi a fili yace "mi zai kai ni gidan sarauta kuma har na zama sarki bayan ni soja ne kaiii ba zai yiyu ba ni sam sarauta ba ta burge ni kawai dai wata fassara ce daban amman ba wannan ba"ɗan dattijon da ke kula da shi ne ya shigo bayan sun gaisa ya kwance ɗan ƙyalen da ya ƙule cinyar Mohammed ya na haskawa da fitilar hannu.
"Ƴan samari ciwon na ka da saura ga shi kuma shugan ku yace yau za ku bar gun nan zuwa Dourkou,ka kula sosai sannan ka yawaita yin addu'a domin kyakkyawar zuciyar ka ya sa magauta na san ganin bayan ka"murmurshi Mohammed yayi yace "na gode Baba Allah shi yi albarka da kyakkyawan ƙarshe"farin dattijon yayi saurin kallon Mohammed jin ya kira shi da baba hawaye suka zubo kan fuskar shi bai san lokacin da ya rungume Mohammed ba yace "na gode sosai matuƙa karon farko a rayuwata wani ya kira ni da Uba ba a yau ɗin nan sai ni ke ji na tamkar wani sarki,tsaya ina zuwa"ya faɗa tare da fita bai jima ba ya dawo hannun shi riƙe da wata baƙar leda.
Wata sarƙa mai boule ƙato ya fara saka mashi sannan zoben azurfa yace "ka ga wannan (zobe da sarƙa)a gun mahaifina na gaje su tun da ran shi ya ban su ban san amfanin su ba sai da na shiga tarko am...kar ka tambaye komi da sannu za ka fahimta kai dai duk runtsi kar su bar jikin ka"ya faɗi hakan ne saboda ƙur ɗin da Mohammed yayi mashi ko ƙyaftawa babu.
Murya Chef suka ji a bakin ƙofa hakan yasa yayi saurin bashi baƙar ledar yace "yi sauri ka tafi Allah ya tsare"da "amen"ya amsa sannan ya saka wandon tenue dama rigar already tana jikin shi.
Da Mohammed ya fito ko kallon inda Chef ya ke a tsaye bai yi ba, direct inda collègues ɗin shi ke tsaye cikin shiri ya nufa.
Duk taron su Omar ne kaɗai ya tambayi jikin shi,"da sauƙi"ya faɗa tare da nufar mota ya shige.
Chef na tsaye ya na kallon su ɗan nesa da su a zuci yace "Allah Sarki bawan dubi yadda ya ke ɗangasawa Allah dai ya baka lafiya ya sa kuma za ka iya draving"ya faɗi hakan ne lokacin da Mohammed ya shiga mota kuma mazaunin drever.Fuska a tamke ya ƙaraso gun ya bada umarnin kowa ya shiga motar da ya san ya na shiga,kusan a tare motocin da suka haura goma suka tashi tare nutsawa cikin ƙasungumin daji.




Tun safe Maryam ta shirya domin zuwa asibiti,kallo guda za ka yi mata ka san ta na cikin fargaba.Ganin tsayuwar bai yi mata ta fito waje tare da cewa Mama "na tafi gidan su Munat"a dawo lafiya Mama tayi mata.
Ta tsayar da abun hawa ya kaita Clinic Agaji,tana shiga gabanta ya faɗi réception ta nufa murya na ƴar rawa tace "dan Allah Mustapha ya na nan?"ɗagowa Hajiya tayi dubeta murmurshi kan fuskarta ta nuna mata wani bureau "ki shiga ya na nan ciki" "toh na gode"cewar Maryam tana mai nufar inda aka nuna mata,ƙwanƙwasawa tayi daga ciki ya bata izini ta shiga.
Har ta zauna bai ɗago ya dube ta ba rubutu kawai ya ke a farar takarda,sai da ya kusa ciketa sannan ya ɗago ya dubeta idon shi masu kama da na mashayi,saurin sunne kai tayi dan sosai ta ji kunya kamata da yayi tana kallon shi.Murmushi yayi yace "Barka da zuwa soeurette bari na kira abokin aikin nawa ya duba ki mu gani,in bai wani tsanani sai a baki magani in kuma yayi tsanani sai an fasa gun"idon Maryam ta fiddo tace "wani?wani kuma Musto?"yadda tayi maganar sai da ya so bashi dariya yace "eh mana "baki ta turo tace "Allah kiyaye ni na zata kai za ka duba ni"yace "dan mi ba wani ba?"cikin shagwaɓa tace "haba kai ma dan Allah haka kawai wani ƙato ya duba ni"fuska ya ɗan tamke yace "to ni mi ye in ba ƙaton ba?"kallon shi tayi tace "ai kai magajina ne"murmurshi yayi ya na nuna mata gado,ta kalli gadon ta kalle shi yace "eh je ki hau ki tabbatar kin cire rigar sai ki gwada min inda ya ke ciwon"bai jira cewar ta ba ya fita ko da ya dawo hannun shi riƙe da allurai.
Ya kalleta yace "ko baki shirya ba?"ya faɗi haka ganin ta haye gado ta zauna daram sai hijab da ta cire,sunne kai tayi ta shiga kiciniyar fidda Zip ɗin rigai tsawon minti ɗaya,ƙarasowa yayi tare da maida hannuwan shi bayanta da zumar taimaka mata hakan sai ya ba fatar jikin su haɗuwa ta yadda su kayi kusanci har bugun zuciyoyinsu suna ji.
Saurin jan Zip ɗin yayi ƙasa tare da cire rigar ya bar mata bra kawai, kwantawa tayi tare da rumtse idonta ta ɗan jan gefen bra ɗin da breast ɗin ta ke ciwo.Hannun shi ya kai daidai inda ta janye nata nan kuwa yaji ƙululun,massaging wurin ya fara yi sannu-sannu saurin riƙe hannun shi Maryam tayi tare da fashe mashi da kuka ta na yarfa hannu....
[29/05 à 17:12] MRS SADAUKI 💫: 🆓 17-18

Ta yi saurin riƙe hannun shi tana jin wani kala biyu,tun da take ko hannunta namiji bai taɓa riƙewa ba balle breast.
Cikin murya shagwaɓa-shagwaɓa tace "please ka bari ban so"kallonta Mustapha yayi kawai ya maida hannun shi kan breast ɗin ya ɗan matsa inda ya ke jin sauran ƙululun da har yanzu bai baje ba,ƴar ƙara ta saki tace "Washhh zafi"bai kula ta ba har sai ya tabbatar ya naguje ƙululun ya na yi ya na saka wani crème har ya gama ya ja mata bra ɗin ta.Allura ya ɗauko yayi mata a hannu sannan yace "ragguwa tashi to"turo baki tayi tace "eh tunda ba non..."sai kuma ta ƙyale murmurshi yayi yace "ida mana tunda ba minene nawa ba?"sunne kai tayi hakan ya baiwa Mustapha ƙare mata kallo tsaf musamman cikakkun ƙirjinta uwanda suka cika bra ɗin ta har wuri bai ishe su ba.
Tayi saurin jan rigarta ta maida saboda jikinta ya bata ya na kallon ta,wani gwabron numfashi ya sauke ya na jin wata kasala na rufe shi wacce bai san dalili ba hakan ya sa doli ya samu wuri ya zauna tare da lumshe ido.Ƙuri Maryam tayi tana kallon kyakkyawar doguwar fuskar shi mai zagaye da saje,a zuci tace "masha Allah nan Allah yayi halitta ba dai kyawu ba"buɗe idon shi guda yayi ya kalleta ta ƙasa,kafin ya nuna mata ledar magani da hannu.
Ɗauka tayi

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

2 Comments On SOJANA
avatar
yakubu-4

10 months ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
yakubu-4

10 months ago

Reply

Allah yakara basira

Please Login or Register in order to submit comment