Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```78```

~~cikin muryarta mai sanyi da zak'i ta furta _hello_ Wani irin sanyi ya ziyarce zuciyar Habeeb har ya yi nasara saukar masa da natsuwa, ya sauke ajiyar had'e da lumsashe idanu tsabar miskilancin irin na Habeeb Lamido a maimakon ya furta abunda ke neman raba shi da jin dad'insa sai kawai ya yi shiru yayinda katin wayarshi{recharge card} ke tafiya a banza jin shiru nashi ya yi yawa yasa Haleesa tak'ara cewa _hello_ ya ja iska ya fesar adak'ile yace ki ba wa Imaan waya zan yi magana da ita, jiki a sa6ule Haleesa taciro wayar daga kunnenta ta d'anko hannun Imaan ta daurawa mata ranta a b'ace tace ki yi magana da Daddynki, ta rafka tagumi tunanin hali irin na Habeeb shin ko ya manta da matsayinta na matarshi da bara iya tambaya ko da lafiyar jikinta ne ta ja d'an siririn tsaki ta mayarda hankalinta wurin Imaan tana sauraro yadda ta ke zuba masa surutu, mai d'auke da tambayoyin _Daddy ina ka tafi ne na daina ganinka in na tambayin aunty Haleesa ina ka ke sai tace batasaniba''?_
''A hankali Habeeb ya bud'e idanunshi ya cize lips d'inshi na k'asa kenan yarinya nan bata ma damu da ni ba ni kadai nake fama da sha'awa da tunaninta.....cike da jin haushin Haleesa yaja tsaki yace my angel na yi tafiya shiyasa ki ka daina ganina.
'' Daddy Ya sunan garin da ka je"?
Ya yi murmushi a kasalance ya furta Germany
"Daddy yaushe za ka dawo"?
Dafe goshi ya yi saboda yafara gajiya da tambayoyin Imaan da kyar ya furta very soon my angel
Daddy me za ka siyo mun"?
_Anything you wants my Angel_
Imaan ta yi shiru tana tunanin abunda za ta fad'a kamar daga sama tace Daddy ka siyo min monkey da snake da lizard da......cikin zafin rai Haleesa ta kwace wayarta ta yi hanging up ta gallawa Imaan harara ke wace irin yarinya ce Imaan"?
Duk lokacin da Daddynki ya yi tafiya bara ki lissafa masa abun Kirki da zai siyo miki sai na banza da wofi ko angaya miki nan gidan zoo ne da zai kwaso wad'anan tarkace ya kawo miki.
Imaan ta kwa6e fuska kamar zai ta yi kuka cikin shagwa6a tace aunty ban gama magana da Daddyna ba kin kar6e waya
''Haleesa ta tabe baki ta shafi sumar kan Imaan tace ae kin gama magana Imaan fatana d'aya kada Allah yasa wannan Daddy naki 0ne & d half ya biye wa shirmenki ya kwaso miki wad'annan masifun da ki ka lissafa saboda, shima irinki ne bai ji sauki ba ta k'arasa magana had'e da kya6e baki.
''Imaan ta zaro idanu tace aunty dama Daddy bashida lafiya"?
Haleesa ta yi murmushi a zuciya ta tace kai wannan yarinya akwai 'yar jarida da alama uwarta ta biyo da wannan d'an banzan surutu saboda ubanta kurma ne a baiyane kuma sai tace _Eh bashida lafiya amma ya ji sauki_
Aunty me ke damunshi"?
Haleesa ta girgiza kai tace Imaan tashi ki je kitchen akwai ice cream a fridge ki dauko ki sha kinji"?
Da sauri Imaan ta tashi cikin zumud'i tanufi kitchen Haleesa tana murmushi ta bi ta da kallo.
Ta 6angare Habeeb kuma yana jin kiran ya yanke sai kawai ya tabe baki yadanganta, hakan da matsalar network d'in Nigeria ya dukufa tunanin Haleesa iya saninshi ba son yarinyar yake yi ba matsananciyar sha'awarce take wahalarda shi, duk ranar da ya kusance ta zai manta da ita ya ja tsaki had'e da shafi sumar kanshi yana mamakin yadda yake ware lokacin mai matuk'ar mahimanci agareshi ya zauna yana tunaninta a da shi mutum ne Wanda bai San tunani ba sai akan Haleesa tun farkon had'uwarshi da ita har yau ita kadai ce take haddasa masa shiga yanayin na tunani.
***********************
```2 DAY'S LATER```
Habeeb na kwance a room d'in da ya yi booking a Alexander Hotel da ke Germany ya yi pillow da hannayenshi ya zurfafa a tunanin, Haleesa duk yarame sai wani farin da ya yi ga wata 'yar uban k'asumba da yatara akan fuskarshi kamar Wanda aka mintsina ya mik'e zaune yadauki phone d'inshi da ke ajiye akan bedside ya yi dialling number Haleesa a maimakon ya jin 'yar muryarta mai sanyaya masa zuciya sai kawai ya tsince muryar Imaan tana zuba masa surutu, ba d'ad'aukawa bai San lokacin da ya katsin kirar{hanging up} ya jefar da wayar bisa bed yarik'en kanshi da ke barazanar fita daga gangar jikinsa, ga matsananciyar yunwa yana ji tun zuwanshi Germany daga coffee sai soft drink su kadai yake daurawa cikinsa cikin d'an k'ank'ani lokacin zazza6i mai zafin gaske ya lullu6e shi.

```HALEESA```
Haleesa na zaune bisa farar kujera roba a compound Imaan na wasa akan 'yar motarta ta wasan yara wance ake sakawa a charging sai kai da kawo take yi Haleesa kuma ta duk'ufa tunanin rayuwarta Ita kanta in aka tambayeta bara ta iya cewa ga asalin abunda ke damunta lokacin sallah magarib yak'arato ta tattara Imaan da motarta suka shiga gida.
A daddafe Habeeb Lamido ya yi 2 weeks a Germany yajuyo gida Nigeria around _10:30pm_ flight d'in da yad'auko su ya yi landing a hankali yake taka stairs d'in jirgi yana saukowa ya hango Bala.
''Tun akan hanya Bala yafara aika masa tambayoyi "Boss ka yi rashin lafiya ne"?
Habeeb ya yi ignoring nashi, da sauri yadafe kanshi tun a flight yake jin ciwon kai had'e da sanyi duk surutun da Bala yake zuba masa ya yi shiru bai tanka masa ba suna isa gida tun kafin Bala ya bud'e masa k'ofa ya bud'ewa kansa yana gaba Bala na biye da shi janye da luggage d'inshi direct yawuce bedroom yafad'a bisa bed ko takalmin k'afarsa bai cire ba ya lullu6e cikin blanket a rikice ya yaye blanket yashiga bathroom yadinga kwara amai Kore shar abun gwanin ban tausayi, jiri na d'ibarsa yafito daga bathroom yak'ara kwanciya, sai faman rawar sanyi yake yi hak'ora shi na had'ewa ya k'undundune cikin blanket gaba d'aya Daren rana Habeeb bai runtsa ba kwana ya yi yana kwara amai a zaune ya yi sallah asuba har 10:00am ya yi yana kwance bai San idan kanshi yake ba
''Da kyar ya lalla6o phone d'inshi ya yi dialling number Bala cikin sark'ewar halshe yace _Bala ka zo banida lafiya_ yana k'arasa magana ya jefar da waya a rud'e Bala yashigo bedroom d'in
"Sannu Boss
Muryarshi a dusashe yace please Bala kira Dr saleem.
Bayan kamar _10 minutes_ sai ga Dr saleem ya zo bayan yagama duba shi ya debi jininsa zai yi masa blood test domin ya tantance musanbabin ciwonsa, yadaura masa drip had'e da allurai bacci ya yi awon gaba da Habeeb Dr saleem kuma Yakama gabansa, Bala ya na tare da Habeeb drip yak'are ya zare masa, sai misalin k'arfe _2:00pm_ Habeeb yafalka ya yi wanka had'e da sallah duk wannan budirin da ake yi Haleesa batasaniba, Bala kuma yana mamakin ina tashiga saboda sau biyu yana shiga part d'inta bai ganta ba, Habeeb ya ji sauki sosai yau kwanansa biyu dawowa ko compound bai lek'a ba yana kwance a d'akin Bala ke kula da shi matsalar Habeeb bayason magani ga kuma rashin cin abincin tsakiyar dare ciwonsa yadawo sabo dal, a wannan karon har da stomachache sai amai yake kwarawa kamar zai amayar da 'yan hanjinshi, a wahalce ya kira phone d'in Bala koda Bala ya zo yatarar da shi duk yajigata, yafita a hayyacinshi a tsorace Bala ya yi kanshi, yad'ago shi sai kawai Habeeb yafara wani irin nishi yana rik'en cikinshi haka bacci yadauke shi, Bala ya rafka tagumi yana kallonshi kamar daga sama Habeeb ya zabura ya mik'e yanufi bathroom, ya yi amai yana fitowa ya yanke jiki yafad'i k'asa, da gudu Bala ya yi kanshi yana girgiza shi had'e da kiran sunanshi duk girgizar da yake masa ko d'an yatsanshi bai motsa ba, Bala yarud'e iya rud'ewa babu shiri ya yi dialling number madam Hindu.
"Madam na kwance akan katafaren bed d'inta kirar Royal bed tana sharar bacci ta ji ringing d'in wayarta, a tsorace ta falka saida ta yadda ganinta akan wall clock ta ga time _3:45am_ ta zaro ido gabanta ya yi mummuna fad'uwa hannunta na rawa ta d'auki wayar tun kafin ta yi picking, zuciyarta ta ba ta cewa wannan kiran ba na lafiya bane sakamako ganin kiran daga Bala ne.
''Muryarta na rawa ta furta _hello Bala lafiya kuwa ka kira ni a wannan lokacin"?_
_madam ki taimake ni ki zo wallahi boss yana cikin matsanancin hali gashinan kwance ko numfashi ba ya yi_
Bala yak'arasa magana kamar zai rushe da kuka
"Numfashin madam yadinga fita da sauri gaba d'aya ta rud'e kanta ya kwance jikinta yad'auki rawa takasa furta uffan, jin shiru nata ya yi yawa yasa Bala ya katsi kiran da kyar madam Hindu tasauko bisa bed ta bud'e wardrobe taciro wrapper{zani} ta daura bisa night gown d'in jikinta, ta zira hijabinta na sallah tun kafin tak'arasa compound ta dannawa drivernta kira da sauri driven yafito da mota a rud'e madam tashiga motar suka d'auki hanyar gidan Habeeb suna isa direban yadanna horn security's d'in gidan suka fito ta k'aramar k'ofa suna ganin motar madam Hindu da gudu d'aya daga cikinsu yajuya domin ya bud'e mata gate tun kafin ya bud'e gate madam ta balle k'ofa tafito, tafiya take yi batare da tasan inda take jefa k'afarta ba part d'in Haleesa tafara dosa taji k'ofa a rufe dole tajuya tanufi part d'in Habeeb direct ta wuce bedroom d'inshi a rikice ta yi kanshi tana kiran sunanshi............


Jeeddah Aliyu🌹



[27/11 4:59 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```79```

~~Son, son please wake up don't leave your mother I really need you, please Habeeb wake up, gaba d'aya lissafin brain d'in madam Hindu ya kwance tarasa inda za ta jefa kanta batasan lokacin da tafashe da matsanancin kuka tana girgiza Habeeb da k'arfi ganin take yi kamar Habeeb ya mutu ita kuka Bala kuka ba mai rarrashin wani sai lokacin tunani ya zo wa Bala da hamzari yanufi d'an k'aramin fridge da ke ajiye a d'akin ya bud'e yadauko robar ruwa mai sanyi, ya shafawa Habeeb kamar _5 second's_ da Shafa mishi ruwan yasaki ajiyar zuciya mai k'arfi a hankali ya ke bud'ewa idanu har ya ware su gaba d'aya akan fuskar madam Hindu ya k'ank'ame ta cikin dashashshiyar murya, yace _sweetheart cikina kaina, ki rik'e min kaina zai cire_
Madam Hindu tak'ara rud'ewa ta juya wurin Bala cikin shouting tace _please Bala call doctor saleem immediately_
Jikin Bala na rawa ya yi dialling number Dr saleem daf da asuba Dr saleem ya iso cikin muryar kuka madam Hindu tafara rok'onshi _please Doctor do something to save my son life I don't wants to loose him'!_
''Dr saleem yace calm down madam insha Allah ba abunda zai faru da d'anki batare da 6ata lokacin ba Dr saleem yafara treatment d'inshi ta hanyar daura mishi drip da injections cikin d'an k'ank'ani lokacin bacci ya yi awon gaba da shi madam na zaune a gefenshi tana Shafa sumar kanshi ta mayarda ganinta wurin Dr saleem tace _what's wrong with my son Doctor"?_
Dr saleem ya share zufa da handkerchief ya d'an numfasa daga bisani yace na yi matuk'ar mamaki lokacin da nagano ainihin abunda yake damunshi da farko akwai tsananin tunanin da yake yi Wanda yana daf da jininsa ya hau sai kuma rashin cin abincin Wanda ya janyo masa kamuwa da cutar ulcer.
"Madam Hindu ta zaro ido da alama firgicin a tare da ita ga kuma d'inbin mamakin furucin Dr saleem muryarta na rawa ta maimaita abunda Dr saleem yafad'a _tunani da ulcer_
"With full confidence Dr saleem ya gyad'a kai yacigaba da cewa dole sai ana bashi, kyakyawar kulawa musanman cin abincinsa idan ya falka ki yi k'ok'ari a matsayinki na mahaifiyasa ki titsi shi domin ya sanar da ke abunda yake damu shi a matsayinki na uwa bara ki rasa taimakon da za ki ba shi, ba kuma ki tabbata yana taking medicine d'inshi in time domin na fahimce duka magunguna da na kawo mishi ba Wanda ya yi amfani da shi.
''Madam ta goge hawayen fuskarta, tace na gode Dr saleem.
"You're welcome madam Dr saleem yafad'a yatattara tarkace shi, ya kama gabansa yabar madam Hindu cikin jimami da fargaba.
''Madam tasauke ajiyar zuciya ta juya wurin Bala cike da son jin k'arin haske dangane da ciwon d'anta Bala har tsawon wane lokacin Habeeb yadauka bashida lafiya sannan kuma ina matarshi da ta barka kana jinyarsa"?
''Domin ita ce ta dace ta kula da shi ba kai ba tun zuwa na gidanan duk, da bana cikin natsuwa ta zuciya ta take bani akwai abunda ke faruwa a tsakaninsu.
''Bala ya numfasa ya karkace baki yasoma kwararo wa madam Hindu zance tun kafin boss ya yi tafiya na fahimce akwai abunda ke damunshi, kwata-kwata yadaina cin abincin ranar da yadawo yafad'i cikin yanayi na rashin lafiya sau biyu ina zuwa part d'in Haleesa bana tararda ita rabona da in sakata a idanunna tun washe garin ranar da Imaan tasami hutun makaranta, lokacin da Hannah ta zo za ta tafi da ita na had'u da su a parking space Haleesa ta yi musu rakiya mu ka gaisa to fa tun daga ranar ban k'ara ganinta ba abun ya yi matuk'ar d'aure mini kai ina tashiga ne tsawon wannan lokacin da Boss yake fama da rashin lafiya yak'arasa magana cikin yanayi da ke nuna alhininsa.
''Madam ta mik'e tsanm..... Batare da tace da Bala komai ba tanufi part d'in Haleesa cikin Sa'a tana murd'a handle k'ofar ta bud'e ta kutsa kai tun kafin tak'arasa shiga parlourn, ta hango Haleesa zaune akan _2 seater_ k'afutata na zube akan kujerar tana yanke farce jin k'arar bud'e k'ofa yasa Haleesa ta d'ago _4 eye's_ tayi da madam Hindu rass!....gabanta yafad'i da sauri ta mik'e tsaye ta d'an sace kallon wall clock da ke manne a falon _9:07am_ jikinta yafara rawa tsoro ya baiyana k'arara akan fuskarta da kyar ta furta _sannu da zuwa mom_
Saida madam Hindu takai zaune sannan ta amsa mata ba yabo ba fallasa.
''Tun daga nan Jikin Haleesa ya yi sanyi nan take zuciyarta yaba ta cewa akwai abunda yake faruwa a sanyaye ta duk'a cikin girmamawa tace _ina kwana mom''?_
_lafiya amma ba qalau ba_
furucin madam Hindu yak'ara tsorata Haleesa cikin sark'ewar halshe tace me ke faruwa mom''?
''Wannan tambaya ta Haleesa tak'ara harzuk'a madam Hindu har takasa controlling temper ta cikin zafin rai ta rufe Haleesa da fad'a _ke wance irin mutum ce Haleesa mijinki bashida lafiya tsawon kwanaki uku kuna gida d'aya ace baki saniba wannan wane irin sakarcin ne"?_
''Wannan ya tabbata mun da cewa baki Masan menene Kalmar miji take nufi ba, ballatana ki San yadda ake kula da shi, dalilin wannan sakacin naki gashinan d'ana ya kamu da cutar yunwa, wallahi idan wani abu yasame d'ana Haleesa har abada bara taba daina ganin sakaci da laifinki ba koda ace Habeeb ya yi miki wani laifi bai kamata ki yi masa horo da yunwa ba tak'arasa magana tana huci.
''Tun lokacin da madam Hindu tafara wankewa Haleesa allonta Haleesa take wuk'i-wuk'i da idanu tsananin mamakin zafafa kalaman madam Hindu suka hanata tabuk'a komai.
Shiru Haleesa ta yi tarasa abun fad'a sai kawai tafashe da kuka madam Hindu ta girgiza kai ta mik'e a zafafe tace wannan kukan da ki ke yi bashida amfani zan iya danganta shi da kukan dad'i domin in Habeeb ya mutu bakida asara nice da asara domin ni ce narasa d'a madam Hindu na k'arasa magana tafice daga falon tabar Haleesa na kuka kamar ranta zai fita, haushi da tsanar Habeeb Lamido suka cukuikuye mata zuciya a yadda takejin zafi na kwarara a zuciyata Kamar ta had'a kayanta tabar mishi gida dama yasha fad'a mata saboda mom ya aureta a halin yanzu mom ta tsaneta, har tana danganta da laifin da batada masaniya akai tana cikin wannan halin Hannah tashigo
ta zauna a gefenta cikin sanyin murya tafara magana, Haleesa yanzu nan mom ta kira ni a waya ta zayyane mun abunda yafaru nayi matuk'ar mamaki yadda mom takasa gano laifin yaya Habeeb, jira nake yaya Habeeb yafarfad'o na fallasa shi a gabanta in yaso ta tantance tsakani ke da shi waye mai laifi.
''Haleesa ta share hawaye fuskarta tace Hannah banaso, ki sanarda mom komai dangane da zaman mu da yaya Habeeb, a hali yanzu zuciyata tariga ta bushe na dau alwashi sai na azantarda ruhin d'an uwanki da soyayya ta mai tsananin zafin gaske na yi amfani da ita na rama duk wani cin kashi da ya yi min sai na nunasa masa cewa ba kowace Mace ake wulaqantawa ba sai gwanmace kid'a da karatu.
Cikin tsananin farin ciki Hannah tarik'o hannun Haleesa tace tun farko abunda nake nuna miki kenan Haleesa ki ka k'i bani had'in kai da yanzu zance yasha banban, yanzu tashi mu tafi ki ba wa mom hak'uri nasan yadda mom takesonki bara ta iya cigaba da fushi da ke kuma duk bak'ak'en maganganu da mom ta zuba miki ki rubuta su tass....ki yi wa d'anta tanadin su Haleesa ta zaro ido tace Hannah bakida kirki yayanki ne fa
''So what's Hannah tafad'a had'e da kad'a eye's ball d'inta karki manta Haleesa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne don haka duk lokacin da yaya Habeeb yashiga hannunki karki raga masa ki tabbata kin sauke masa wannan miskilancin da yake tak'ama da shi.
Haleesa ta cize lips d'inta na k'asa ta kad'a kai tace bari kawai Hannah Allah yakai damo ga harawa.
Ameen 'yar uwa zo mu tafi kada mom tak'ara hayewa.
"Direct bedroom d'in Habeeb suka wuce mom na zaune kusa da shi ta rafka tagumi yayinda Habeeb ke ta sharar bacci, Hannah ta zunguri kafad'ar Haleesa nan take Haleesa ta yi pity face ta zube gaban mom tarik'e hannun mom ta marairace murya _Dan Allah mom ki yi hak'uri nasan na yi kuskure amma insha Allah bara ki sake kamani da koda kwatankwacin irin wannan laifi_
tak'arasa magana cikin muryar kuka madam Hindu tasauke ajiyar zuciya tad'ago Haleesa suka nufi parlour tasoma yi mata nasiha daga yau Haleesa karki sake sakacin sake ragama abincin mijinki a wurin ku-ku lokacin da peter yake yi min bayani tun zuwanki gidanan shi yake yi wa Habeeb girki ba ki ji yadda raina ya6acin ba amma yanzu komai yawuce ki tashi ki Shiga kitchen ki Samar mishi abunda zai cin domin Dr saleem yace da ya falka abashi abinci
''Da hamzari Haleesa ta mik'e tanufi part d'inta Hannah ta Mara mata baya.
_15 minutes later_
A hankali Habeeb yake bud'e idanunshi har ya ware su gaba d'aya, k'ok'ari yake ya mik'e zauna da sauri mom ta taimaka masa, ya zauna tasaka masa pillow a baya ya jingina jikinsa, duk ya rame ya yi k'ashin wuya.
''Sannu son ya ka ke jin jikin naka"?
Da sauki mom yanzu dai ina son na yi wanka na rama sallah da ke kaina.
Da sauri mom ta mik'e bara na kira Haleesa ta taimaka ma, batare da ta jira jin ta bakinshi ba tafice, Wani irin dad'i ya ratsa sassan jikin Habeeb ya kwarara a zuciyarsa, ya lumshe idanu, jin karar bud'e k'ofa yasa da sauri ya bud'e idanunshi yasauke su akan fuskar Haleesa, tasake masa k'ayatace murmushi, sannu yaya Habeeb ya jikin naka"?
''Saida ya ja iska yafesar sannan yace da sauki ki taimaka ki had'a min ruwa zan yi wanka
Batare da tace komai ba tashiga bathroom ta cika masa bathtub da ruwa masu d'an d'umi-d'umi har tafito yana nan yadda ta barshi muryarta tace tadawo da shi daga tunanin da ya afka _yaya Habeeb na had'a ruwan_
"Chan k'asan mak'oshi ya furta na gode yana bin bango yashiga bathroom Haleesa ta bi shi da kallo ya yi matuk'ar bata tausayi ashe akwai abunda zai sa yaya Habeeb ya yi laushi, ta yi murmushin mugunta ta gyara masa bed ta feshe d'akin da freshener tana tsaye har yafito daga wanka ya zauna a gefen bed yana mata kallon k'asan ido wani irin abu yakeji yana ratsa jinin jikinsa can! Ya yi gyaran murya daga bisani yace........

Note:- _I'm sorry readers nasan za Ku ce page d'inan yayi kad'an wallahi yau nayi typing mai yawan gaske basan ya akayi ya fita gaba d'aya, ba da kyar na yi wannan a halin yanzu kaina yadau zafi ina cikin yanayi na jiyar zuciya_

Jeeddah Aliyu🌹



[28/11 6:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```80```

~~ke! Bud'e wardrobe ki dauko min fari jallabiya{white colour} yak'arasa magana had'e da lumsashe idanu.
Haleesa ta tabe baki a zuciyarta tace huh...daga farfad'owarsa yafara kirana da suna nan da na tsana, a maimakon ta dauko white colour kamar yadda ya umurceta sai kawai ta dauko mishi black colour, k'i kar6a ya yi yabarta tsaye rik'e da rigar, Haleesa tasake mik'a masa rigar tace yaya Habeeb gashi katashi ka yi sallah lokacin yana k'urewa.
"Ya yi kici-kici da fuska very slowly yafara magana Fari nace ki dauko ba black ba.
"Umhh....fari kace na dauko ni kuma a ganina white da black duk d'aya ne muradi kawai ka suturta jikinka ko...ya kace"?
Tak'ara sa magana tana kallon fuskarsa, saida ya tsotsi bakinshi sannan yafisge rigar daga hannunta daga zaune ya zura rigar yayinda Haleesa ta shinfid'a masa pray mat yana fara sallah tafice daga d'akin a parlour ta tararda madam Hindu da Hannah suna breakfast mom tace kin had'a masa ruwan wanka ne"?
''Eh mom har yafito daga wanka yanzu ma na barshi yana sallah abincinsa zan dauko masa.
Da kyau 'yar albarka haka akeso mace tagari ta kasance, murmushi Haleesa ta yi tanufi kitchen hannunta d'auke da k'aton tray ta tura k'ofa tashiga, yana zauna inda ya yi sallah da sauri yad'ago yarame sosai idanunshi sun k'ara girma fuskarshi ta yi wani fiyau ga wata irin k'asumba da yacika masa fuska.
Tadire tray hannunta ta zauna a gabanshi tana magana tana zuba masa kunun gyad'a kafara da wannan saboda hanjinka ya warware tak'arasa magana had'e da mik'a masa cup ya kafe ta da idanu ko kintawa ba bu Haleesa ta kad'a eye's ball d'inta ta marairaice murya ka daure kasha koda d'an kad'an ne.
Idaunshi a lumshe ya mik'a hannu ya kar6i cup d'in daga hannunta a hankali, yake kur6a kunun har ya shanye tass...ta kar6i cup ta bud'e food flask k'amshin faten dankalin turawa ya daki hancin Habeeb ya hadiye yawu, ta yi masa serving sai ga gogan naku ya lamshe fate tass....ya ajiye plate yana wani yatsinar fuska Haleesa tace uhmm....ciwonka yana burgeni yaya Habeeb saboda bai hanaka cin jagwalgwalen Haleesa ba tak'arasa magana tana murmushin tsokana.
Habeeb ya daure fuska kema kinsan saboda mom tana gidanan yasa naci abunda ki ka sarafa da hannunki.
''Haleesa ta tabe baki tace uhmm.....yaya Habeeb kenan a wasu lokuta in kana magana kamar da gaske sau ina kama ka kana satar jagwalgwale tak'arasa magana tana dariya.
''Da k'arfi yafisgota tafad'a kansa

Please Login or Register in order to submit comment