Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hugging d'inta yatura kanshi a gefen wuyanta, ya ja iska yace _hey! Are you feeling shy_
''Ta kad'a kwayar idonta tace of course not ta yi yunk'urin kwacewa ya hanata ta hanyar k'ara qanqameta, leesa kina mun wulaqancin ko don kin fahimcin nafara damuwa da ke shiyasa ki ka za6i hanyar da za ki dinga musgunawa zuciyata koh"?
''Haleesa ta yi murmushi, banida amsar wannan tambayar taka amma zan iya cewa ka taimaka kasake ni kada Hannah tafito taganmu haka tak'arasa magana kamar zai ta yi kuka.
"So what's don Hannah taganmu a haka ae ba haramun mu ka aikata ba
Ba haramu bane amma gaskiya da kunya.
Ya yi ajiyar zuciya me ye abun kunya anan abunda yafi wannan zan iya miki a gabanta.
"Zaro ido Haleesa ta yi a tsorace tace meke nan"?
Juyo da fuskarta ya yi yace kamar wannan ya had'e bakinshi da nata daga bisani yasaketa yana dariya k'asa-kasa
Hmm.....da kuwa ka kasance marar kunya lamba d'aya dariya Habeeb yake yi sosai da kyar yasaketa tafice da sauri har tana had'awa da gudu ya bita da kallo yana Shafa sumar kanshi.
"Tana shiga bedroom ta tararda Hannah zaune a gaban dressing mirror tana make-up, ta cikin mirror suka had'a ido princess Hannah sai yanzu aka ga damar tashi daga bacci"?
Huh......matar yaya Habeeb hope kin nemi gaban mijinki"?
''Shiru Haleesa tayi bata tanka ta ba sai kawai tad'auki phone d'inta tana game.
Hannah tasaka kayanta ta dube Haleesa tashi mu tafi koh"?
"Batare da Haleesa tayi magana ba ta zari mayafinta, suka fice a parlour suka tararda Habeeb Lamido yana aiki a system.
''Good morning bros!
"Morning Autar mom ina za'a tafi haka naganki da 'katuwar handbag"?
''Market za mu shiga babyn aunty Juwairiyya za mu yi wa shopping.
"Hmm......ba wani shopping da za Ku je kedai kifito fili ki ce za Ku tafi yawon rabon ido a kasuwa.
''Allah yaya Habeeb shopping za mu je kuma ma bara mu dad'e ba koh Haleesa"?
Sai lokacin haleesa ta dube su sai kawai ta gyad'a kai Habeeb ya dubeta ya tabe baki akwai take away akan dining table....kafin Yak'ara sa magana Hannah tanufi dining area da sauri sai gata dawo da Leda fara mai tambari _Royal kitchen_ tafito da robubin take away guda hudu ta mik'awa Haleesa guda biyu.
Haleesa tazari guda d'aya ina plate Hannah"?
Ba bu buk'atar plate Haleesa haka ma za ki iya ci ko kinmanta ne sauri mu ke yi Hannah tafad'a had'e da bud'e robar soyayye chips had'e da sauce saida Hannah tacinye robar biyu Tass....ta mik'e tana kallo Haleesa wance ko rabin bata cinye ba.
''Wannan wane irin cin abinci ne Haleesa"?
Ko so ki ke ki 6ata mana lokacin''?
Sannu a hankali ta ajiyer robar hannunta mu tafi kawai.
"Da Mugun mamaki Hannah ta dubeta kina nufi har kin k'oshi.
''Yeap! Haleesa tafad'a had'e da mik'ewa
Ta k'asan ido Habeeb ya dubeta suna had'a ido tadauke fuska da sauri tabe baki yayi yacigaba da aikinsa.
''Batare da Habeeb ya dube Hannah ba yace Hannah ki je bedroom d'ina ki bud'e briefcase akwai kud'i a cikin kad'auko bundle biyu ko k'ara Ku yi wa baby shopping.
Cikin zumud'i Hannah ta ajiye handbag d'inta tanufi d'akin Habeeb.
Ke! Zo nan na ba ki sak'o Habeeb yafad'a batare da ya dube Haleesa ba kauda kanta tayi da barin kallonshi.
Ya ajiye laptop d'inshi akan kujera yanufi wurinta, saboda ya fahimce bara ta zo ba hannunshi yasa yad'ago fuskarta yasake mata murmushi saboda kinga Hannah shiyasa ki ka shareni koh"?
Uhm....to me kakeso nace da Kai"?
"koda bara ki yi min magana a last ki haska ni da cute smile d'inki Gani batada niyar magana yasa ya yi picking d'inta yasaketa ya koma mazauninsa.
Hannah tafito rik'e da kud'i suka fice Aderwale ya yi dropped d'insu kasuwa.

_4 day's later_
:-5:20pm:-

Habeeb da Mus'ab na zaune a compound akan farare kujerin roba, da yake yau weekend ne ba aiki ranar hutu ce Haleesa da Hannah suka fito cikin shirinsu za su fita.
'' Mus'ab ya dube Hannah yace Sai ina 'yan mata da yammaci nan da ku ka ca6a wannan uwar kwaliyya"?
"Hannah ta yi fari da ido tace outing za mu fita saboda mun gaji da zama wuri d'aya ko za ka yi mana escort ne"?
"Me zai hana 'yan mata nima zaman gidanan ya isheni, ya dube Habeeb Wanda hankalinsa na wurin wayarshi tun tsayuwa su Haleesa ya ke ta fama operating phone d'inshi.
Lamido tashi mu tafi mu d'an mik'a k'afarmu sai kadawo Habeeb yafad'a a yatsine lallashinsa Mus'ab yashiga yi da kyar ya amince zai bi su.
Mus'ab ke driving Habeeb na gefensa a haka suka isa beach
a dak'ile Habeeb yace me za mu yi a beach"?
Shan iska Mus'ab yafad'a kaitsaye
Tsaki Habeeb ya ja ya yi zamanshi cikin mota yana kallonsu, suka nufi bakin ruwa Mus'ab da Hannah suka nemi nesa da ruwan suka zauna suka bar Haleesa tsaye tana mamaki yadda mata ke yawo daga su sai bikini pants, ko kunya basa ji.
Habeeb yagaji da zama ya bud'e k'ofar mota yafito tun kafin yak'arasa ya hango Haleesa ita kadai tsaye ta yi crossing hands a k'irjinta.
Yayi tsaye a bayanta yana kallonta jin motsi mutum a bayanta yasa tajuya a tsorace suka had'a ido ta yi saurin janye idanunta tana murmushi.
" Cikin sanyin murya yace Yakamata mu nemi wurin zama saboda bana da juriyar tsayuwa.
Ignoring nashi ta yi bata ankara ba ruwa suka bugo da k'arfi cikin zafin nama Habeeb yafizgota suka fad'i a gefe cikin farin yashi kallon-kallon suka shiga aikawa juna daga bisani suka kyalkyale da dariya.
Haleesa ce tafara mik'ewa zaune yayinda Habeeb ya yi gice yana kallonta villager kawai Allah yasoki da yau ruwa sun tafi da ke.
''Tabe baki tayi tana gunguni ni kadaina kirana da villager.
Ya yi murmushi yace in kinaso nadaina kiranki da villager sai kidaina k'auyancin.
Uhmh...tafad'a had'e da mayarda hankalinta wurin Hannah da Mus'ab da ke zaune suna sha coconut water.
"Gani yadda tashagala da kallon side d'in da suke yasa Habeeb ya matsa daf kunnenta yarad'a mata za ki sha ne na k'ar6o miki"?
''A kunyace tarufe fuskarta, dungure mata kai ya yi ya mik'e yanufi wurin Mai siyarda, coconut water ya kar6o musu guda biyu da gudunshi yadawo wurinta ya mik'a mata garin k'ar6a hannunayensu suka goge juna da sauri Haleesa tajanye hannunta a tunanin Habeeb tarik'en coconut d'in sai kawai yasake mata yafad'i k'asa ya tsiyaye.
''Dariya Habeeb yafara yi mata shikenan yarinya kinyi wa kanki domin bara iya k'ara komawa siye wani, kina kallo zan shanye kayana.
"Habeeb ya zura strong yana sha yana kallon Haleesa, ta k'asan ido saida yagama ja mata rai sannan ya mik'a mata d'ayan strong ya matsa daf da ita tuni ta fahimce abunda yake nufi ta zura nata tsinke idanuwansu na manne da juna suna tsotsar coconut water.
''Har suka shanye ruwan batare da sun sani ba saboda sunyi nisa a kallon junansu.
''Habeeb ne yafara ankara da halin da suke ciki yasaki kokon yafad'i k'asa da sauri Haleesa ta dube shi can!k'asan mak'oshi yafurta empty..... Yadda ya yi magana yayi mugun bata dariya sai kawai tasa dariya yayinda shima yashiga tayata sai faman kyalkyale dariya sukeyi abinsu.
"Habeeb ya kauda fuskarsa a gefe Haleesa ta bi wurin da yake kallo da ido gungu wasu mata ne tsaye daga su sai pant da bra.
''Kishi ta ji ya kamata da k'arfi ta mayarda kanshi saitinta, me ye haka leesa za ki karya min wuya.
''Gwara na karya maka wuya da ka cigaba da daukawa kanka wuta me ye abun burgewa a wurin wad'ancan mata da ka ke kallo"?
"Habeeb ya zaro ido yace ba abunda zan ji don na kalle su saboda a wurina basuda banbancin da Mus'ab.
Haleesa ta tabe baki tace... Uhmh...dube shi kamar abunda yafad'a har cikin zuciyarsa haka ne.
"Rik'on hannunta yayi kamar mai rad'a yafurta _are you jealous"?_
_am not_ tafad'a tana murgud'a baki
You're Habeeb yafad'a yana kallon kwayar idonta.
''Believe me yaya Habeeb I'm not jealous
_yes leesa I believe you you're jealous_
Yes I'm! Da sauri tashiga girgiza kai no ba haka nakeso fad'a ba.
Habeeb ya kyalkyale da dariya yace yeee yarinya tana kishina, duka tashiga kai masa a baya ya mik'e da sauri yana mata gwalo cikin shagwa6a Haleesa ta mik'e ta bi bayanshi da gudu suka shiga zagaye wurin suna dariya.
Hannah ta zunguri Mus'ab ta nuna masa Habeeb da Haleesa, wicked smile Mus'ab ya yi a zuciyarsa yace yau zan kawo k'arshen wannan rainin hankalin na Lamido.
"Sai misali k'arfe _6:30pm_ suka baro beach, a maimakon su nufi gida sai kawai suka zarce gidan wani business partner d'in Habeeb mai suna Abdulkareem oluyude da yake yana da mata kuma bahaushiya ce 'yar asalin katsina mai suna fa'eeza yasa su Haleesa suka shantak'e sai fama zuba fira suke yi sai around _10:30pm_ suka yi sallama da Abdulkareem da matarshi fa'eeza.
"Dai-dai wani medicine store Mus'ab ya yi parking, ya dube Habeeb yace _2 minutes pls zan kar6o magani gaba d'aya jikina tsami yake min_
Batare da yajira amsar da habeeb zai bashi ba ya balle k'ofa da sauri yafice bai wani jima ba yadawo suna isa gida Haleesa da Hannah suka nufi bedroom.
Habeeb da Mus'ab kuma suka yadda zango a parlour wannan ya ba wa Mus'ab damar aiwatar da nufinshi akan Habeeb.
Mus'ab yashiga kitchen yad'auko juice mai sanyi ya tsiyaya a handle cup yaciro desire tablet d'in da yasiyo ya 6alle guda biyu yasakawa Habeeb a cikin drink fuskarsa d'auke da wicked smile yakoma parlour.
Ya mik'awa Habeeb cup d'in batare da tunanin komai ba Habeeb yakafa kai yashanye drink d'in Tass.....ya ajiye cup akan center table Mus'ab nagani buk'atarsa ta biya, ya yi wa Habeeb sallama yanufi masaukinsa.
Direct Habeeb yawuce bathroom yasakewa kanshi shower adaddafe ya gama wanka, sai faman rik'e cikinshi yakeyi ya zura pyjamas ya kwanta yana juyi akan bed.
Saida Mus'ab ya tabbatar da Habeeb ya galabaita sannan ya kira wayar Haleesa wance tuni naunauye bacci ya yi awon gaba da ita ringing d'in wayarta ya falkarda ita tana gani Mus'ab ne mai Kiran nata tayi picking cikin magagin bacci tace Mus'ab ya akayi ne"?
"Haleesa Dan Allah ki taimaka ki je d'akin Habeeb bashida lafiya a rikice Haleesa ta tsinke kiran, ta murza key k'ofar ta bud'e a rud'e tashiga d'akinshi hango shi ta yi akan bed yana juye-juye had'e da nishi mai k'arfin gaske.
''Tsalle ta yi ta haye gado tad'ago kansa tadaura bisa cinyoyinta Habeeb ya shak'i k'amshin turareta yak'ara gigicewa a rikice yafara sumbatarta.
Gani yana k'ok'arin zarcewa yasa Haleesa tasa kuka tashiga yi masa magiya sai ya zamana kamar tana k'ara zugashi ne, Sam bai saurara mata ba saida ya tabbatar da yarabata da budurcinta (Virginity} ya mayarda ita cikkakiyar mace.
''Kuka Haleesa take yi kamar ranta zai fita Habeeb ya rungume ta gam.....kamar wani zai yi masa kwacenta sai wani sauke numfashi yake.........


Jeeddah Aliyu🌹
[9:15AM, 08/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [07/12 8:00 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```87```


~~Yadda Haleesa take kuka za ka yi tsanmani Ammi da Baffanta ne suka mutu a hatsarin jirgin sama, rarrashinta Habeeb yacigaba da yi ki yi hak'uri leesa banyi nufi na 6ata miki ba ni kaina ina mamaki kaina yadda nakasa hak'ura da ke.
"Haleesa tad'ago idanunta da suka kad'a suka yi jajir kamar barkono ta watsawa Habeeb mugun kallo ta cire hannaye shi daga rungumar da ya yi mata tajuya masa baya.
"Yak'ara matsawa ya yi ya rungume bayanta duk yadda Haleesa ta nisanta daga cikinshi takasa domin, da k'arfi ya rungumeta, a haka bacci mai dad'i yadauke Habeeb sa6ani Haleesa da takasa runtsawa tana tunanin makomar rayuwarta shikenan Habeeb Lamido yasame abunda yakeso a wurinta ko wane zama za su yi anan gaba har asuba ta yi Haleesa na kuka.
"Habeeb yana falkawa ya sunkuce ta zuwa bathroom yadireta cikin bathtub, ga mamakinta sai gani ta yi shima yashiga bathtub d'in yasake musu shower har zuwa lokacin hawaye na zuba a idanun Haleesa.
''Da kanshi ya yi mata wanka ya rad'a mata d'ayan wanka ki yi wa kanki da k'arfi ta runtse idanunta har yagama nashi wanka yafita idanunta na rufe tana ji k'arar rufe k'ofa ta bud'e idanu.
"Tak'ara cika bathtub da ruwan d'umi ta gasa kanta, sai lokacin tarage jin zafin da takeji tadauro towel tana tafiya a hankali tafito, daga bathroom.
"Ta hango Habeeb yana sallah tanemi gefen gado ta zauna ta sadda kai k'asa, dad'in qira Habeeb ya ratsa ta ta lumshe idanu a zuciyarta tace uhm...ashe so arrogant an iya karatun Qur'ani har ya idarta sallah tana zaune ya mik'e yak'arasa wurinta ya zauna a gefenta leesa ki tashi ki yi sallah mana.
"A harzuk'e tad'ago a tsirara ka keso nayi sallah ko me"?
"Oh! Sorry bara na dauko miki hijab a d'akin Ku tana kallonshi har ya bud'e k'ofa yafice, ta ja tsaki tanufi wardrobe tadauko jallabiyar Habeeb ta sanya.
"Da sand'a Habeeb yashiga d'akin su Haleesa yatararda Hannah lullu6e cikin blanket tana ta sharar baccinta har ya bud'e wardrobe ya daukowa Haleesa hijab yafito ko motsawa bata yi ba.
"Yadda yafita yabar haka yadawo yatararda ita banbancin kawai yanzu tana sanye da Jallabiyarshi sa6ani d'azu kafin yafita da take daure da towel.
Ya mik'a mata hijab batare da ta dube shi ba ta kar6a ta zura hijab tanufi pray mat d'in da ya gama sallah har tagama sallah idanu Habeeb na kafe akanta, wani irin mugun sonta yake ji yana zarya a jinin jikinshi.
"Tana gama sallah ta tura kanta tsakiyar cinyoyinta ta bud'e sabon babi na kuka Habeeb ya girgiza kai yana mamakin dalilin wannan kukan nata.
Ya mik'e tsaye yanufi wurinta yadauke ta cak kamar 'yar baby ya shinfid'e akan gado yacire mata hijab ya kwanta a bayanta ya qanqame ta.
Cikin kunnenta yarad'a mata ban San Kalmar da zan yi amfani da ita wajen nuna miki irin farin cikina a dalilin irin mashahurin farin cikin da ki ka sadani da shi a dare jiya.
"Leesa zan iya cewa da ke daren jiya yana d'aya daga cikin dare da bara ta6a matawa da shi a rayuwata, dare ne da ya canza mini rayuwata, ya haddasa min shiga sabuwar rayuwar da banta6a tunanin ko mafalkin riskar kaina a cikinta ba.
"Haleesa ta yi ajiyar zuciya cikin dashashiyar murya tace a wajen na banta6a riska kaina a cikin baqin dare ba irin daren jiya, domin ya kasance dare ne mai cike da k'unci da baqin ciki a waje na Allah ya isa tsakanina da kai yaya Habeeb domin nasan duk wannan lalla6awa da ka ke yi min bai kai zuci ba kana yi a dalilin ka kawarda sha'awata da take damunka
Hannah ta mik'e tanufi d'aki tadauko mayafinta suka fice ita da Mus'ab
Sai misali karfe 11:30am Habeeb ya falka ya yi zaune yana kallon fuskar Haleesa yana murmushi, saida ya 6ata dogon lokacin yana kallonta kafin yafara tashe ta, _leesa, leesa, ki tashi mu yi wanka har rana tafito_
"Ta bud'e idanunta a hankali ta ware su akan fuskarsa, ta ja dogon tsaki tasauka daga kan gado, batare da ta tanka masa ba ta bud'e k'ofa tafice.
"Habeeb ya ja iska ranshi ya ji ya sosu ba abunda yake saurin ta6a masa zuciya irin wulaqancin, shiyasa a tsarinsa baya kula mata bai ta6a soyayya ba a cewarsa soyayya 6ata lokacin ce da siyawa kai raini, shi kuma abunda ya tsana kenan.
"Kaitsaye Haleesa ta wuce bedroom tazarce bathroom tana wanka tana kukan tausayin kanta, domin yanzu ta K'ara amincewa da soyayyar Habeeb tayi mata mummuna kamo.
*************************
_some hour's later_
Habeeb na zaune a downstairs parlour ya k'urawa TV ido saidai Sam hankalinsa baya wurin kallon, Haleesa yakeso gani ruwa a jallo domin tun lokacin da tafita d'akinsa bai k'ara ganinta ba.
Tsanm.....ya mik'e tsaye da sauri ya haura staircase yanufi d'akinsu Haleesa a tunaninshi Hannah tana ciki shiyasa ya tsaya knocking, Haleesa na jinsa tayi biris da shi tun yana knocking har yadawo kiran sunanta _leesa, leesa please open the door for God sake_
Kinyi hak'uri Dan Allah ki bud'e k'ofar nan banaso kiyi wa kanki horo da yunwa tun d'azu nasa akayi miki order breakfast ki taimake ni leesa ki bud'e k'ofa na kawo miki abincinki har 12:00 o'clock ya yi leesa ba kiyi breakfast ba I'm sorry leesa please......
"Duk surutu da Habeeb yake yi Haleesa tana mik'e akan bed idanunta sunyi jajir tana jin wani irin k'uncin domin tasan duk wata kalma da za ta fito daga bakin Habeeb ba sonta yake yi ba.
''Habeeb jin yake yi kamar yafashe da kuka shi mutum ne da bai sa6a da damuwa ba, shiyasa yau da yatsince kanshi a ciki yake ji zuciyarsa kamar za ta kama da wuta.
Yagaji da tsayuwa ya koma parlour yadafe kanshi can! Kuma ya mik'e yanufi k'ofar fita, ya zagaya ta baya ya bud'e "window d'akin da Haleesa take ciki ya hango ta kwance da yake fuskarta na facing window yacigaba da rok'onta kamar zai yi kuka.
"A hankali ta mik'e tanufi k'ofar ta murza key k'ofar ta bud'e tafito tana Jan k'afa tana shiga parlour Habeeb yana shigowa da sauri yanufi wajenta muryarsa tana rawa yace leesa kiyi hak'uri ki yafe min ba dan halina ba Dan Allah za ki yafe min kinji"?
''Batare da ta tanka masa ba tanufi 2 seater ta zauna jikinsa na rawa yanufi kusa da ita ya zauna ya rungumo kafad'arta bara na kawo miki abincinki kinji"?
A yatsine tace tea zan sha"
Jikinsa na rawa ya mik'e yanufi kitchen bai jima ba yadawo d'auke da tea cup ya mik'a mata batare da ta dube shi ba ta kar6i cup d'in.
"Kur6a d'aya tayi ta mayarda na bakinta ciki a gigice Habeeb ya durk'usa a gabanta yadago fuskarta tea d'in da zafi koh"?
"Wane irin zafi sugar ne yayi yawa ni bara iya sha ba tak'arasa magana kamar za ta yi kuka.
No.....leesa karki yi kuka bara na sake had'a miki wani kinji"?
"Uhm....tafad'a had'e da d'auke kanta kamar wani sauna yak'ara komawa kitchen sake had'a mata wani, ta kar6a tana kur6a a hankali har ta shanye tass....ta mik'a masa cup ya kar6a ya mayar kitchen.
Yadawo ya zauna kasa a gabanta langwashe k'afafunshi yana kallonta, kamar wani zarare yana son yafurta mata abunda ke ranshi amma girman kanshi yahana sai kawai yacigaba da kallonta.
_washe gari_
Tun misali _11:30am_ Habeeb shirya zai fita office yanaso yafita da wuri saboda yanada meeting _12:00 O'Clock_ sai yakai k'ofar fita yadawo yakasa tafiya rashin gani Haleesa gaba d'aya ya dagula masa lissafi, yanaso yaje wajenta a d'akin amma yana jin kunyar had'uwa da Hannah.
"ya ja iska had'e da ya mutsa gashin kanshi cikin yanayi tafiyarsa, ta k'assaita yanufi d'akin.
" A hankali Ya murd'a handle k'ofar ta bud'e ya hangonsu kwance cikin blanket, cikin sand'a yak'arasa wurin Haleesa ya durk'usa kusa da fuskarta a hankali yarik'on hannunta ya yi pecking tafin hannunta.
"Tsawon lokacin yadauka yana kallonta a zuciyarsa yace a halin yanzu na amince da soyayyarki ce ta kamani sosai leesa, ina sonki leesa kece mace ta farko da zuciyata tafara so domin abunda nakeji a game da ke banta6a jinsa akan salman ba, _I love you. I love you leesa you're the only woman I love"_
Na yi miki alqawali a dare yau I'll you express my feelings 4 u I'll tell you how much I love you.
Yak'ara pecking nata a goshi ya gangaro akan pink lips d'inta nan ma yasake mata peck har ya mik'e tsaye ko me yatuna oho! Yak'ara durk'usawa yarik'on hannunta yaciro Biro daga aljihun coat d'inshi ya rubuta mata *I LOVE YOU* a tafin hannu a hankali ya mayarda hannunta ya ajiye yafita da sauri.
_12:00pm_
Haleesa da Hannah suka tashi daga bacci a gaugauce suka shirya Aderwale ya yi dropping d'insu Airport kafin flight d'insu yatashi suna zaune Haleesa ta lura da rubutu Biro a hannunta ta k'urawa rubutun ido duk yadda ta kai da so ta karanta rubutu ta kasa saboda a wajen wanka bata lura da rubutun ba ya wanke sai dishi-dishi kawai take gani a haka jirginsu yad'aga sai Abuja.
Sai misali k'arfe _1:30pm_ Habeeb yafito daga meeting bayan sunyi sallah shi da Mus'ab a cikin office d'inshi Mus'ab ya dube shi yace zuwa yanzu mutane ka sun tsofa a Abuja.
Cike da mamaki had'e da fad'uwar gaba yace su wa kenan"?
Haleesa da Hannah mana"
Saura kiris Numfashin Habeeb yafita daga gangar jikinsa yarasa Kalmar da zai furtawa Mus'ab sai faman had'a gume yake........

Jeeddah Aliyu🌹
[10:31PM, 08/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [08/12 1:45 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```88```

_ina mai mik'a sak'on ban hak'uri a gareku reader's pg d'in da nayi post jiya bashi bane original pg da yakamata na turo muku Pg d'in ne suka d'an rikitarda ni amma Dan Allah Ku yi hak'uri Ku sake karanta pg 87 zan yi post d'inshi tare da pg 88_


~~Gaba d'aya Habeeb yafita hayyacinsa sai yakai karshen bango yadawo farko bango yana yarfe hannaye kamar Wanda ruwan zafi suka k'ona.
"A d'age Mus'ab yake kallonshi yana murmushi mugunta sai kawai ya d'auke fuskarshi yaciro phone d'inshi gaban aljihun rigarsa ya kira Hannah yana zuba mata kalaman soyayya, yayi kamar bai fahincin halin da Habeeb yake ciki ba.
"Habeeb yarasa idan zai sa kansa jin yake yi kamar duniya ta juya masa baya me yasa leesa za ta yi min haka"?
Me yasa saida ta bari zuciyata tayi niyar fallasa mata sirrin da ke cikinta za ta gujeni domin nasan saboda ni leesa ta koma Abuja yau.
Da sauri yadauko phone d'inshi ya yi dialling number ta ga mamakinsa wayar na ringing ba'a d'aga ba da yacigaba da kira sai ya ji wayar a rufe ya ja iska da k'arfi jikinsa yadauki rawa kamar mai jin sanyi.
Cikin tafarfasa zuciya ya maka wayar a bango ta tararatsi sai kace wayar ce tayi masa laifi.
"Why leesa tell me why do this to me"?
Yak'arasa magana cikin shouting had'e da dukan desk, yasoma watsi da files d'in da ke zube akan desk da sauri Mus'ab ya katse wayar da yake yi da Hannah.
Yanufi wajen Habeeb yarik'onshi da k'arfi kanka d'aya kuwa Lamido"?
Ko kasha kwaya ne ko angaya maka soyayya hauka ne"?
"Habeeb ya ja iska had'e da ya mutsa gashin kanshi manyan idanu nan, nashi suka k'ara firfitowa basu da banbancin da na magge da

Please Login or Register in order to submit comment