Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na bin kuncinta, bata ankara ba taji Habeeb ya had'e bakinshi da nata, jin ta yi k'afafunta sun kasa daukarta tasoma k'ok'arin zubewa k'asa ya rik'enta sosai.
"Can ya dauketa yanufi part d'inshi direct bedroom yawuce da ita, Haleesa tadawo kamar idol{gunki} ko kwakwaran motsi takasa tana kallon Habeeb yacire rigar jikinsa, gadan-gadan yanufo ta.
"Sai lokacin brain d'inta yafara aiki zuciyarta tafara sak'a mata wasi-wasi karki sake ki mallakawa Habeeb kanki da ya biya buk'atarsa, zai cigaba da wulaqanta ki ne da bakinsa yace sha'awarki yake yi sha'awa kuma ba so bane da sauri Haleesa tafara ja da baya tana girgiza kai.
Kai wane yaya irin mugu ne yaya Habeeb"?
Yanzu kai ko kunya bakaji ka dube tsabar idona kace kana sha'awata, wallahi ko za ka mutu bara ta6a Mallaka maka kaina, har sai ka bani matsayin a zuciyarka.
Kunya ta lullu6e Habeeb a sanyaye yadauki rigarsa yajuya da sauri yafice daga d'akin.
Haleesa ta kifa kanta akan pillow tafashe da kuka, zuciyarta na mata zafi, me yasa Habeeb bara iya furta mini kalma so sai ta sha'awa wannan wance irin k'addara ce tafad'a min mijina na aure babu sona a zuciyarsa sai sha'awa wannan wane irin rayuwa ne na riski kaina a ciki"?
"A parlour Habeeb ya tsaya yasaka rigarsa yadauki phone's d'inshi da ke zube akan center table yafice tun kafin yak'arasa compound yake kwadawa Bala kira da a tsorace Bala yadanno da gudu.
"lafiya Boss na ga kamar ranka a 6ace"?
Tsaki ya ja cike da jin haushin yace wannan ba matsalarka bace mu je ka kaini ademola adetakumbo street ayi min aski nagaji da wannan k'asumba yana magana ne had'e da tafiya.
"Wannan gaskiya ne boss k'asumba nan ta yi mugun rage maka kyau
Bala yafad'a cikin 'yar dariya.
"Habeeb ya tabe baki had'e da yatsine fuska Bala ya bud'e masa k'ofar mota yashiga, Bala ya ja motar gate man yabud'e musu gate suka fice.
" lokacin-lokacin Habeeb yake Jan tsaki ya yi danasani furtawa Haleesa abunda ke ranshi, shikenan yanzu za ta renashi, har da wani cewa sai na taba matsayi a zuciyata, in banda k'arancin shekaru irin nata akwai wani matsayi da zan bata da yawuce, wannan yaushe nake da lokacin zama na dinga furtawa mace kalaman soyayya, iya tsawon rayuwar da na yi da aunty salma banta6a furta mata wata kalma da ta dangancin soyayya, iya Sanina ina matuk'ar tausayin aunty salma Wanda hakan ne yajanyo mata babban matsayi a zuciyata, to ita wannan yarinya me yasa bara ta amince mu yi rayuwarmu a haka"?
"Yak'ara Jan tsaki yacigaba da zance zuci banta6a sanin me ye so ba kuma bana tunani akwai wata 'ya mace da zan so.
"Boss mun k'araso maganar Bala ce tadawo da shi natsuwarsa a sanyaye yafito daga cikin mota.
************************
_2 day's later_

Haleesa tana cikin kitchen tana had'a breakfast ta ji kamar ana sallama, da mugun mamaki tafito daga kitchen zuwa main parlour don tasan ba Habeeb bane tsawon kwanakin biyu kenan rabonta da tasa shi a ido ko abincinta yadaina cin tun lokacin da ta fahimcin manufarsa akanta tadaina shiga part d'inshi Haleesa tana k'arasawa cikin parlour tasaki ihun farin ciki sakamako tozali da ta yi da Aunty juwairiyya.
"Da gudu ta rungume aunty Juwairiyya farin ciki ya lullu6enta tarasa inda za ta sa kanta tace aunty Juwairiyya ke ce yau a gidan namu"whats presence surprised Haleesa tana magana ne had'e da d'aukar Abba.
''Aunty Juwairiyya tana dariya tace Haleesan Ammi kinga yadda ki ka k'ara kyau"?
''Turo baki Haleesa ta yi kinga aunty zauna na kawo miki breakfast zaro ido aunty Juwairiyya ta yi had'e da duba wall clock _12:30pm_ what's nonsense Haleesa breakfast at this time"?
"A shagwa6e Haleesa tace uhm...aunty sai yanzu na tashi daga bacci saboda tun _8:00 o'clock_ yaya Habeeb ya fita.
"lallai Haleesa kin ji dad'inki ni kan a k'oshe nake Haleesa ta yi dariya ta zauna a kujera da ke facing d'in aunty Juwairiyya fira ta barke a tsakaninsu.
''Haleesa ina fatar kina zaune da mijinki lafiya wannan zuwan da nayi Ammi ce tadameni da na zo naga yanayin zamanki saboda tasan bason auren ki ke yi ba"?
Haleesa ta tabe baki tace ki ce Ammi rahoto ta turo ki dauka to lafiya lau mu ke zaune ba wani matsala.
"Murmushi Aunty Juwairiyya ta yi tace mu dama fatan mu ki zauna lafiya da mijinki ki manta da margayi yaya Habeeb ki gina sabuwa rayuwa hankalin iyayyenmu ya kwanta.
Haleesa ta yi murmushin yak'e yayinda aunty Juwairiyya tacigaba da ba wa Haleesa shawarwarin zaman aure.
_9:07pm_
Haleesa da aunty Juwairiyya suna zaune a parlour sai faman zuba fira suke yi yayinda Haleesa ke ta kwasan dariya tun daga balcony Habeeb Lamido, yake jiyo sautin dariyarta ya tabe baki, da sallama yak'arasa shiga parlour rass.....gaban Haleesa yafad'i tashiga firgici nan take idea tafad'o mata ta mik'e da sauri tanufi Habeeb _oyoyo my Handsome Don_
"Habeeb Lamido ya yi tsaye turuss.......bai dawo daga mamakin da ya afka ba ya ji Haleesa shinfid'e akan k'irjinshi, cikin shagwa6a take magana _Haba my Handsome don tun safe kafita ba ka dawo ba sai yanzu nan ina fatar ba ka cin abinci a waje ba"?_
"Duk maganar da Haleesa take yi tana qanqame da Habeeb tuni gogan naku yafara fita daga hayyacinsa, dai-dai kunnenshi haleesa tarad'a masa _take it' easy my Handsome don it's just a pretending_
"Habeeb Lamido yasauke ajiyar zuciya yad'ago fuskar Haleesa daga k'irjinsa, ya ja karan hancinta, cikin zuciyarsa yace _huh...lallai yarinya nan 'yar duniya ce saboda zuwan 'yar uwata ita ma ta 6ullo ta wannan sigar amma bara na nuna mata nawa kalar duniyanci_
"Ya yi murmushi yace oh! I'm so sorry my baby nima ban yi tsanmani zan d'auki long time ban dawo ba amma ayi min afuwa bara k'ara ba.
"Shikenan my Handsome don na hak'ura.
Habeeb ya yi murmushi yak'e had'e da zare ta daga k'irjinsa yarik'on hannunta, zuwa kujerar da aunty Juwairiyya take zaune yayinda aunty Juwairiyya ke ta faman doka murmushi da ke baiyanar da farin cikinta Haleesa na zaune lafiya da Habeeb.
"Habeeb ya zauna yana d'an sunkuyar da kai shi a dole yana gaban in-law yace Sannu da zuwa aunty ya hanya"?
"Yauwa Habeeb hanya kuma Alhamdulilah!
Ina Abba ko ya yi bacci ne"?
Habeeb yafad'a yana sosa k'eya
A fakace Haleesa take galla masa harara tace huh....yana bedroom ya yi bacci
Habeeb d'an sace kallon aunty Juwairiyya ya ga hankalinta na wurin TV ya watsawa Haleesa mugun kallo ita kuma ta murgud'a masa baki.
Ya mik'e tsaye yana murmushi yace aunty bara na yi wanka nadawo nima a sha fira da ni.
Dariya Aunty Juwairiyya ta yi shikenan sai kafito Habeeb yajuya ya bi shortcut da ke tsakanin part d'inshi da na Haleesa.
Mik'ewa Haleesa ta yi ta dube aunty Juwairiyya tace aunty bara na had'a masa abincinsa kafin yafito.
Gyad'a Kai aunty Juwairiyya ta yi yayinda Haleesa tanufi kitchen.
_15 minutes later_
Habeeb yadawo sanye da jallabiya, Haleesa naganinsa ta mik'e da hamzari tanufi dining area ta ja masa kujera saida ya yi mata kallon wulaqancin, sannan ya zauna ta yi masa serving ta tura masa plate.
"A yatsine yake kallon abincin daga bisani yadauki spoon yafara ci yana bata fuska kamar mai cin mad'acin ran Haleesa ya yi matuk'ar 6acin tajuya cikin parlour taga akwai tazara sosai tsakaninsu da Aunty Juwairiyya, cikin zafin rai tafisge spoon daga hannunshi ta tattara food flask had'e da plate tanufi kitchen cikin tsananin mamaki Habeeb ya bi ta da kallo ya cize lips d'inshi
tana ajiye kayan tadawo wurinshi, da murmushi a fuskarta take kallonshi _my Handsome don me ka ke jira ne da har yanzu ba ka gadi tashi ba ae ni a tunanina ka dad'e da tsofa parlour"?_
Habeeb ya ja iska yana shafar geme sa yana kallonta k'asa-k'asa ya mik'e tsaye yafizgo ta da k'arfi ya mannata a bango, ya matse ta sosai numfashinsa yana sauka akan fuskarta tsoro ya lullu6e ta kuma ba bu halin ihu aunty Juwairiyya na parlour wannan ya ba wa Habeeb Lamido yin yaddda ya ga dama da ita yatsanshi yasa yana zagaye lips d'inta yana Jan iska daga bakinshi, hannunshi ya zura ida bata yi tsanmani ba, ihu ta je kurmawa da sauri yadanna bakinshi cikin nata, yashiga ya motsata son ranshi sai da yagaji don kansa yasaketa.
Gaba d'aya jikinta rawa yake ta sulale k'asa da6ss.......yana wicked smile ya durk'usa gabanta saida yaja iska yana wani lumsashe idanu, yace _wow! What's a perfect game I like it's baby_
Haleesa d'ago idanunta da suka canza colour zuwa red har ta bud'e baki za ta yi magana da sauri yadaura yatsanshi bisa lips d'inta _shhh......don't say anything baby_ ke fa ki ka tsokanoni don na mayarda Martani ae ba laifi bane kinga ki tashi sahunki a likkafa mu koma parlour kada aunty Juwairiyya ta yi tsanmani ko.......sai kawai hadiye sauran kalamansa ya kashe mata ido, cike da jin haushi Haleesa ta mik'e luuuuu.......jiri yadebe ta tafi za ta fad'i Habeeb yataro ta yadaura bakinshi dai-dai kunnenta yace _take it easy my hot baby it's just a pretending_
Yana k'arasa magana yasaketa Yajuya cikin parlour
Haleesa tasauke ajiyar yafi a kirga saida tad'auki tsawon _6 minutes_ tana jinyar dafin da Habeeb ya zuba mata, jikinta a sanyaye tak'arasa parlour, tana murmushi yak'e tanemi kujera ta zauna duk yawancin firar aunty Juwairiyya ce take yi _11:00pm_ tana bugawa aunty Juwairiyya ta mik'e ta dube Habeeb tace my in-law sai da safe "Toh.... aunty Allah ya tashe mu lafiya
Ameen tafad'a had'e da juyawa tanufi bedroom d'in Haleesa da sauri Haleesa ta bi bayanta har tana had'awa da tuntu6e Habeeb ya bi ta da murmushin mugunta har tafara haura stairs yadakatar da ita ta yadda aunty za ta ji abunda zai fad'a yace _baby in kin raka aunty bedroom ki zo ki had'a min coffee in yaso sai kidawo ki taya aunty kwana_
A tsorace Haleesa tajuya suka had'a ido ya yi mata signal..............


Jeeddah Aliyu🌹

[10:46AM, 04/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [03/12 9:03 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```84```

~~Haleesa ta yi k'ayatace murmushi ta kad'a kwayar idonta a yangance tanufi wurin Habeeb kamar za ta shige k'irjinshi, sai kawai tanufi gefen bed ta zauna tana yi masa dariya.
" Habeeb ya yi murmushi had'e da ya mutsa sumar kansa da baya-baya yafad'a bisa bed ya runtse idanunshi, lek'a fuskarshi Haleesa ta yi tana mai cigaba da dariya, cikin tsokana tace _hey Mr pretender whats is wrong"?_
Ya mirgino yadawo saitin fuskarta kallon ido cikin ido yake mata ya ja iska yace kina nufi ko yau pretending d'in ne yakawo ki d'akina"?
''Kaima kasan in bayan shi ba abunda zai kawo ni d'akinka
Cije lips d'inshi ya yi yana kallonta a yatsine da sauri ta d'auke fuskarta da barin kallonshi.
Shiru sukayi ba Wanda yak'ara tankawa d'an uwanshi Haleesa tajuya ta sace kallonshi ya yi pillow da hannayenshi idanunshi a rufe ruf kamar mai bacci, kasa d'auke fuskarta ta yi akansa tashiga nazari kyakyawa fuskarsa ta yi ajiyar zuciya a kasalance ta mik'e tanufi gefenshi ta kwanta, tana mamaki d'abi'un Habeeb bata ta6a ganin mutum mai abubuwan mamaki irinshi ba ta yi nisa a tunaninshi batansan lokacin da ya matso daf da ita sai jin ta ta yi cikin jikinshi, cikin kunnenta ya rad'a mata bai kamata ki dinga wahalarda zuciyarki da tunanina bayan gani kusa da ke yak'arasa magana had'e da hura mata iskan bakinshi a kunne.
"Da sauri ta lumshe idanu, Habeeb yak'ara matso da ita cikin jikinshi ya hard'e k'afafunshi cikin nata yasaka hannaye shi ya layyace gadon bayanta fuskokinsu na facing d'in juna duk abunda yake yi idanunshi suna rufe kasa motsi Haleesa ta yi sai fama zazzare ido kawai take yi numfashinta na fita da k'arfi, ta k'urawa Habeeb ido a zuciyata tace ina ma ace da yaya Habeeb d'inta take kwance ba da wannan arrogant d'in ba mutumi da ya furta mata cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba tabbata duk ranarda ya yi nasara cima burinshi akanta zai goge babinta ne a zuciyarshi, tausayin kanta yakamata hawaye suka zubo mata saboda tuni ta fahimce cewa ta fad'a tarkon so Habeeb Lamido tacigaba da kallonshi, yayinda Habeeb bai masan tanayi ba saboda tuni bacci ya yi awo gaba da shi ta ja karan hancinshi ta lumshe idonta a haka bacci mai dad'i ya yi nasara d'auke ta.
*************************
_11:00am_
Haleesa da Habeeb na zaune a dining table suna taking breakfast cikin kulawa Habeeb ya dube Haleesa, yace k'arfe nawa flight d'insu aunty Juwairiyya zai tashi"?
Saida Haleesa ta hadiye chips d'in da take tauna tace _11:30am_ Habeeb ya gyad'a kai suna gama breakfast suka nufi parlour inda aunty Juwairiyya take jiransu su kaita airport, kafin su wuce da ita airport nasiha ta yi musu sosai basu baro airport ba saida suka ga tashin jirginsu.
"tun akan hanyar su na dawowa gida Haleesa ta daure fuska Habeeb ya dube ta ya yi murmushi yad'age gira sama yana kallonta hannunta yarik'o cikin zafin rai ta firzge hannunta, a yatsine tace aunty Juwairiyya ta tafi daga yanzu ba wani sauran pretending, the game is over.
"Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa ya wani kad'a kai batare da yace da ita uffan ba har suka isa gida Bala na yi parking
tun kafin ya bud'e mata k'ofa ta bud'ewa kanta da sauri tanufi cikin gida.
Habeeb yafito daga cikin mota ya yi mik'a ya bi Haleesa da mayen kallo a baiyane ya furta _the game is not over baby this is just the beginning_
Bala ya matso daf da shi ya yi k'asa da murya kamar munafuki yace "boss wannan wane irin game ne jikina yabani wasan zai yi dad'i kuma na tabbata Kaine winner.
"Da mugun mamaki Habeeb ya kalli Bala daga bisani yadafa kafad'arsa suka jera suna tafiya a hankali Habeeb ya ja iska yace nima ina ji a jikina ni ne winner amma basan how long wasan zai dauka kafin nayi winning.
''Bala ya washe hak'ora yace karka damu da tsawon lokacin da wasan zai dauka abu mafi mahimmancin ka yi nasara cinye wasan amma boss wannan wane irin wasa ne"? Bala yak'arasa magana yana dariya.
''Habeeb ya galla masa harara yadak'i kafad'asa yace na tsani shissshigi Bala.
Murmushi Bala ya yi yace "yes boss.
"Direct Haleesa ta wuce bedroom d'inta ta qargame k'ofa, tun daga lokacin suka koma 'yar gidan jiya za ta girka masa abinci ta jejjera akan dining table ta shigewarta d'akin ta murza key.
idan Habeeb yaga dama yaci ranar da yaji baya ra'ayi ci yabar mata kayanta a haka suka share _1 week_ suna gida d'aya amma kowanesu rayuwarsa yake yi.
_10:00pm_
Habeeb yana kwance a bedroom d'inshi abun duniya yataro ya yi masa yawa, tunanin Haleesa na azabtarda ruhinshi da yarufe ido ita yake gani, ba abunda yake buk'ata irin ya ji d'umi jikinta da sanyaye k'amshinta kamar Wanda aka mintsina da sauri yasauko daga kan bed yanufi part d'inta.
Yana murd'a handle ya ji k'ofar d'akinta a rufe ya yi tsaye kamar zai kurma ihu tsawon lokacin yadauka yana safa da marwa can! Idea tafad'o mishi da sauri yafice sai gashi yadawo rik'e da mopper da k'arfi yafara dukan kujerin parlour da mopper hannnushi yature d'an k'aramin glass madauke da flower da ke ajiye akan center table yafad'o yadak'i tiles ya tararatse.
''Haleesa na kwance har bacci yafara d'aukarta taji k'arar fashewar glass, ta zabura da k'arfi ta diro daga kan bed tanufi parlour da gudu tun kafin tak'arasa ta hango Habeeb yana watse da pillowcases na kujeri gaba d'aya ya hargitsa mata parlour a rikice tak'arasa wurinshi, muryarta na rawa tace lafiya yaya Habeeb"?
Banza yayi da ita yacigaba da watsi da kaya rik'e mai hannnu ta yi yadakatar da abunda yake yi, yana sauke numfashi, wai yaya Habeeb me ka ke nema ne duk ka bi ka rikita min parlour"?
"Habeeb ya karkace kai yafara tsara Haleesa ta hanyar cewa _ina zaune a dining area na ga wani abu mai bindi ya rugu da gudu yashigo parlournki shine na biyo shi da mopper yashige k'ark'ashin kujeri_
Zo ki ta ya ni mu fiddo shi Haleesa ta zaro ido cikin sark'ewar halshe tace ni fa ban fahimce abunda ka ke nufi ba"?
Habeeb yadafe goshi yace ina wannan abin mai tsawo yana da dogon bindi ya ma sunanshi yashiga tunani kamar da gaske karaf Haleesa tace bera
Habeeb ya yi shiru yana kallonta ya girgiza Kai yace No....ba bera bane ae bera baya cizo koh"?
''Haleesa ta gyad'a kai to ko k'adangare ne yaya Habeeb"?
Haleesa tafad'a da alama tafara tsorata shiru Habeeb yana nazari maganarta daga bisani yace k'adangare kai bashi bane domin shima baya cizo wannan abu mai tsawo jikinshi yana da tsantsi, za ki tuna suna wannan abu da na ta6a siyowa Imaan na roba a Canada har yabaki tsoro"?
tun kafin Habeeb yak'arasa magana Haleesa tadaka mahaukacin tsalle ta chukuikuye shi jikinta na rawa tace yaya...Habeeb....Maciji
Wicked smile Habeeb ya yi yace eh! Maciji ne nima na yi matuk'ar mamaki yadda aka yi yashigo parlounki.
"Haleesa tafashe da kuka tak'ara qanqame Habeeb kamar za ta shage k'irjinshi Dan Allah yaya Habeeb kafita da ni gidanan wallahi tsoro nakeji.
Kinga me ye kuma abun tsoro tun da ba'a bedroom d'inki yake ba yanzu yadda za'ayi ki shage bedroom ki qargame kamar yadda ki ka saba gobe da safe zan kira securities su fito da shi.
Cikin shashshek'ar kuka Haleesa take girgiza kai bara iya ba yaya Habeeb, zai iya shiga har bedroom ni dai ka fita da ni.
Habeeb ya fakace idonta ya yi mata gwalo yace saidai in za ki je part d'ina mu tafi amma ni basan inda zan kai ki ba.
Kuka yaci k'arfinta takasa furta komai sai faman d'aga kai ta ke yi cike da farin ciki Habeeb yadauke ta cak......da kyar ta amince yasauke ta bisa gado Habeeb ya dube fuskarta ya ga yadda ta kwa6e da hawaye had'e da majina, tausayinta ya yi mugun kamashi ya mik'a hannu bisa mirror ya yago tissue ya goge mata fuska yace kwanta ki cigaba da baccinki.
Girgiza kai ta yi ta rik'e mishi hannu gam yayi k'asa da murya ki kwanta ba abunda zai same ki bathroom zan shiga bara d'auki dogon lokacin ba zan fito kinji"?
Uhm!...uhm...ni dai mu tafi tare zaro ido Habeeb ya yi yace a ina za mu tafi"?
Bathroom tafad'a cikin murya kuka, komawa Habeeb ya yi zauna kusa da ita yace na fasa zuwa bathroom d'in saboda bara yarda ki bini ciki ki k'are min kallo.
Da sauri Haleesa ta matsa tashige cikin jikinshi, a hankali yake bubbuga bayanta har yasamu tadaina kuka ya ja mata pillow ta kwanta cike da nishad'i Habeeb ya kwanta kusa da ita ya rungumeta tsanm.
**********************
_washe gari_
Habeeb da Haleesa suna zaune a parlour Habeeb ya yi pillow da cinyoyinta, ita kuma sai faman damuk'a mishi gashi take yi idanunshi na lumshe yace ke! har yanzu ba'a gama Kitso bane"?
"Turo baki ta yi sumarka yacika tsantsi da yawa da na kitsa sai ya warware, ayya kuwa yaya Habeeb ba relaxer ka ke sakawa ba"?
Tsaki ya ja ya mintsine ta a gefen cinya angaya miki ni d'an daudu ne da zan sakawa suma na relaxer"?
Uhm..!ka ga bawan Allah maida wuk'a ni bance maka d'an dauda ba kawai dai naga kai d'an gayu ne tak'arasa, magana tana lek'on fuskarshi.
Habeeb ya yatsine fuska yace gayanci na bai kai can ba kinji koh magge"?
Tashiga ture masa kai daga cinyoyinta d'aga mun daga jiki tun bara ka daina kira na da magge ba ni dama dole ce tasani zama a part d'inka.
Ke fa ki ka ce sunanki magge"
Yaushe nace da kai sunana magge"?
Kafin yabata amsa phone d'inshi ya yi ringing Haleesa ta mik'a hannu bisa center table tadauko masa, kamar ba zai d'aga kiran ba sai da yagama Jan ajinsa sannan yad'aga _Hello Maryam ya akayi ne"?_
Rass...rass...gaban Haleesa yafad'i da ta tuna wacece Maryam a wurin Habeeb nan take wani irin kishi ya turnuk'e ta har Habeeb yagama waya batasan inda kanta yake ba saida taji yana mata tafiyar tsotsa a gefen cinyarta, buge mishi hannu tayi kamar daga sama ta ji muryarshi yana cewa Maryam ce ta kirani wai gobe za ta turo driver yad'auki Imaan ta je musu hutu.
"Ajiyar zuciya Haleesa ta yi tace uhm...
Tun daga wannan lokacin shak'uwa mai k'arfi yashiga tsakanin Habeeb da Haleesa yau Habeeb yashirya zai tafi Lagos, kuka Haleesa tasa mishi bara ta iya zama ita kadai ba saida yakira Hannah a waya ta turo masa yarinye Housemaid d'in madam Hindu ta tayata zama saboda Hannah exam take yi Haleesa tana tsaye a palour tana matsar hawaye Habeeb yafito rataye da briefcase d'inshi gani tana kuka yasa jikin Habeeb ya yi sanyi ya rungumeta yana rarrashinta kidaina kuka bara wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta ya tsotsi lips d'inta na k'asa wani irin quncin ya ziyarce zuciyarta tana tunani yadda za ta share tsawon sati d'aya batare da Habeeb ba.
Cikin muryar kuka tace ni ban damu da kowane lokacin za ka dauka ba ka dawo ba babban damuwa na yadda za ka tafi kabarni da maciji a cikin gidanan.
Tsaki Habeeb ya ja cike da takaici yake kallonta da ya dauka kukan da take yi saboda zai tafi yabarta ne har yafara murna ita ma tafara jin abunda yakeji a game da ita shiyasa ma yake d'aga mata k'afa kafin ya ga iya gudun ruwanta, ashe ita abun ba haka bane a wurinta.
Kukan Haleesa ya tsananta Habeeb ya galla mata harara cikin zafin rai yace, maciji ya kashe ki kafin in dawo yaciro bundle na 'yan N1000 ya jefa mata bisa kujera yafice da sauri saboda jin yake yi kamar zuciyarsa za ta tarwatse.
Haleesa ta yi sororo baki sake ta bi bayanshi da kallo dama tasan har abada Habeeb Lamido bara ta6a sonta ba ko 'yar wannan shak'uwa da tashiga tsakaninsu, duk lokacin da ya bud'e bakinshi saidai yace tana burgeshi tana bashi sha'awa, ita kuma ta tsani jin wad'annan kalamai daga bakinshi saboda ta kai k'ololuwa a sonshi tak'ara fashewa da kuka ta kwasa da gudu tashige bedroom d'inshi..........

Jeeddah Aliyu🌹
[10:36AM, 07/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [06/12 8:22 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```86```

~~Jikin Haleesa yad'auki rawa takasa furta uffan, haka ya ba wa Habeeb dama yak'ara matsowa da ita k'irjinshi, ya ware idanunshi yana mata kallo mai cike da sinadarin so" very slowly yafurta _you're looking so beautiful today leesa_
"Takaici had'e da k'unar zuciya suka lullu6e Haleesa dama iya wad'annan kalamai ne Habeeb zai furta mata shine ya tsaya yana 6ata mata lokacin batasan lokacin da ta ture hannaye shi daga kafad'arta tajuya cikin zafin nama yarik'o hannunta, batare da tajuyo ba ta yi tsaye cak ya matsa kusa da ita ta baya ya yi

Please Login or Register in order to submit comment