Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai gawurtace d'an is........sai kawai tadafe baki tafirfito da idanu tana girgiza kai.
"A hankali ya ajiye comb d'in hannunshi yanuna kanshi da yatsa in shock yake magana leesa ni za ki zaga ni za ki kira da d'an iska"?
"Jikinta yadauki rawa tayi bala'i tsorata ita kanta batasan time d'in da Kalmar tafito daga bakinta ba.
A tarihin rayuwata ke ce mace tafarko da ta kirani da wannan kalma, yak'arasa magana yana huci.
"Haleesa tayi raurau da idanu kwalla ta cika mata idanu, cike da Nadama tace I'm sorry yaya Habeeb Allah subul da baka nayi kayi h........shut up yadaka mata tsawa karki kuskure ki k'ara bani hak'uri nasan bakya sona leesa kin tsaneni amma banta6a zato za ki iya bud'e baki ki zage ni Sam baki yi la'akari da matsayina na mijinki ba.
Muryarta na rawa ta bud'e baki dan Allah yaya Habeeb kayi h.......I don't wants hears anything from you kawai ki tashi ki je kiyi wanka.
hawaye suka wanke mata fuska ta yaye blanket tasauko tanufi bathroom, ya bita da kallon takaicin me yasa leesa za ta zageni"?
Ko dan ta fahimcin ina sonta shiyasa za ta dinga furta mini duk abunda yafito bakinta.
''Cikin zafin rai ya bud'e luggage d'inshi yadinga watsi da kayan da ke ciki, ya hargitsa su gaba d'aya yanemi gefen gado ya zauna dafe da kai yana jin zafin zagin da leesa tayi mishi a 6angare d'aya kuma yana jin wani masifafe sonta yana kwarara a zuciyarsa.
''Kamar Wanda aka mintsina ya mik'e a gaggauce ya saka kayan ya kwashi phones d'inshi da ke zube akan bedside ya fice ranshi a 6ace.
"Haleesa ta fito daga bathroom tayi tsaye sororo rashin ganin Habeeb cikin d'akin yasa ta tsinci kanta cikin rashin jin dad'in abunda
ta aikata cike da nadama ta nufi bed ta mayarda anko da cire, jikinta asanyaye tashiga linke kayan da ya zubar tana mayarwa cikin luggage.
Takoma bisa gado ta kwanta, ta afka tunanin Habeeb, na shiga uku ni Haleesa me yasa na bari shed'an yayi tasiri akaina na zage shi"? Shikenan na janyowa kaina zai k'ara tsanata.
''Dan Allah yaya Habeeb kayi hak'uri kayafemin ta kifa kanta a pillow tasa kuka kamar ranta zai fita tun tana jiran shigowarsa tak'ara bashi hak'uri har ta fitarda rai, ga wata 'yar uban yunwa da takeji saida batada kwaciyar hankali da za ta iya saka koda ruwa ne a cikinta.
"Har _1:30pm_ yayi Haleesa bataga Habeeb yadawo ba wani irin tsoro ya lullu6eta ta aikawa kanta tambaya ba dai yaya Habeeb tafiya yayi yabarni a hotel ba"?
Wani Sabon kuka ya zo mata tashiga kuka ba kaukutawa, saida tagaji don kanta rarrashi kanta domin wanda takeyi don shi bai Masan tana yi ba, ahaka tayi bacci.

''Around _4:03pm_ A hankali Habeeb yaturo k'ofa yashigo ya hangota kwance yasaki ajiyar zuciya saida yak'are mata kallo na tsawon lokacin sannan yanufi gefen k'afafunta ya zauna.
"A zuciyarsa yace bara iya jure fushi da ke ba leesa saboda inasonki nayi alqawali bara Kara ta6aki ba tun da bakyaso.
Yanaso yatashe ta musanman da ya fahimcin cewa bata yi breakfast ba har yakai hannu yata6ata sai kuma zuciyarshi ta kwa6e shi, yajanye hannunshi ya mayar a gefen pillow da take kwance ke!ke ki tashi Bala mayarda ke gidan aunty mami"!
Ta mik'e a kasalance ta tadaura fuskarta akan fuskarshi tasa pity face muryarta asark'e tace Dan Allah yaya Habeeb kayi hak'uri karka yi fushi da ni.
Harara ya zuba mata yadauke fuska ta matsa jikinshi I'm sorry yaya Habeeb please forgive me"!
Ya mik'e a fusace nace ki tashi Bala ya mayarda ke gidan aunty mami bana buk'atarki anan wurin.
Jikinta na rawa ta mik'e tad'auki veil d'inta had'e purse idanunta na zubarda hawaye tayi tsaye tana kallon Habeeb Wanda ya kauda fuskarshi gefe ko kallonta bayaso yi tanufi k'ofa da sauri ta bud'e tafita saida takai karshen staircase ta tsaya tasaka Veil d'inta ta goge fuskarta tana shiga receptionist ta hango Bala ya mik'e yanufo wurinta suka k'arasa fita.
''Bayan tafiyar Haleesa Habeeb yashiga damuwa matuk'a yadda Haleesa bataci abinci ba shima kasaci yayi sai dare da yaga yunwa za tayi masa lahani yanemi coffee yasha adaddafe ya ga wayewar gari da k'arfe _11:00am_ aka d'aura auren sageer da amayarsa Nabeela daga wajen d'auri aure dama Habeeb yafito da luggage d'inshi ko gidan aunty mami bai waiwaya ba suka d'auki hanyar komawa Abuja ko madam Hindu batasan cewa Habeeb ya koma abuja ba saida taga throughout bata ganshi ba ta kira shi a waya yake cewa shi gashi bisa hanyar abuja sosai mamaki yakamata tace matarka fa Habeeb"?
Sweetheart ba tare Ku ka je ba"?
Saboda mun zo tare shine bara ka jirata ba Ku dawo tare"?
''Uhm....sweetheart wannan ba matsala bane zan jirata gida har Ku dawo ba gobe za Ku dawo ba"?
''Eh! Insha Allah gobe za mu taso.
"Okay....Allah yadawo da Ku lafiya.
''Ameen... Son.
A lokacin da madam Hindu take sanarda Haleesa Habeeb yatafi saura kiriss tafashe da kuka da kyar ta rinjaye zuciyata, saidai tun daga lokacin taji gaba d'aya garin sokoto ya gundireta, ba abunda takeso gani irin Habeeb tacigaba da rok'onshi ko zai huce daga fushi da yake da ita ta kira shi a waya yafi a kirga yak'i D'agawa a washe gari around _9:30am_ su Haleesa suka baro garin Sokoto farin ciki fal zuciyata za taga Habeeb.

_some hour's later_

Tsananin gudun da driven madam Hindu yake tsulawa yasa suka shigo garin abuja da wuri kaitsaye gidan madam Hindu suka wuce.
"Har gajiya tasaki Haleesa bata ga Habeeb ya zo ba kuma da kunnenta taji lokacin madam takira shi a waya tana sanarda shi sun dawo amma shiru bai zo ba.

_9:00pm_
Haleesa da Hannah na zaune a downstairs parlour, Haleesa ta dubi Hannah kamar za tayi kuka tace gaskiya Hannah nayi danasani abunda nayi wa yaya Habeeb na tabbata don yana fushi da ni yasa har yanzu bai zo gidanan ba.
Tsaki Hannah taja narasa gane yaya Habeeb wane irin hot temper ne da shi"? Shi ya manta da irin cin zarafin da dinga yi miki ke bakiyi fushi ba sai shi"? Ki share shi kawai zai gaji da fushinshi yadawo.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi tace bara ki gane ba Hannah duk abunda zuciya keso bara ta iya jure fushi da shi ba ni kan yanzu dabara ta tak'are, min domin soyayyar yaya Habeeb tariga tayi min mummuna kamu dai-dai lokacin da Habeeb yaturo k'ofa yashigo karar sautin TV da ke kunne yasa Haleesa da Hannah ba su ji shigowar Habeeb ba jin abunda Haleesa take fad'a ya yi sanadin da yataka birki yana sauraro firar tasu.
"Ni nasan Allah ne ya jara6e ni da son yaya Habeeb kuma shine zai yaye mun Hannah soyayya masifa ce zafinta yafi dad'inta yawa.
"Duk lokacin da na tuna da kyakyawar fuskar yaya Habeeb sai naji sonshi da kewarshi sun lullu6e ni Hannah inason yaya Habeeb wallahi ina sonshi tankar son da uwa take yi wa d'anta, inason yaya Habeeb tankar yadda nakeson numfashina soyayyar yaya Habeeb tariga tabi jinin jikina, ta ratsa idan bakya tsanmani.
"Habeeb Lamido da ke tsaye ya runtse idanunshi gam.......wani irin masifafen kishi ya turnuk'e shi bai ankara ba yaji hawaye na sauka a kumatunshi.
''Hannunshi yasa yashafi kumatunshi ya mayarda ganinshi akan tafin hannu nashi tausayin kanshi yakamashi ya ji gaba d'aya ya tsani kanshi bai ta6a sani soyayya masifa ce sai yau musanman shi da yake dakon so.!
Yana huci kamar kubunbuwa lallai sai na nunawa leesa kuskureta na firar wani k'ato alhali tana d'auke da igiyoyin aurena.
''A fusace yak'arasa Shiga parlourn kamar daga sama Haleesa da Hannah suka ganshi gani yanayin da yashigo da shi yasa suka mik'e tsaye a tsorace.
"A tsawace yace sai yau na tabbatar da cewa leesa mahaukaciya ce ke ko a cikin mahaukata k'asumgumar ta6a66iya ce ke kina d'auke da igiyoyin aurena amma kina zance wani k'ato Wanda baya duniya tirr......da wannan mummuna d'abi'a taki. Yak'arasa magana cikin huci da hargowa gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka tashi rad'o-rad'o.
"Cikin kad'uwa Haleesa take k'are masa kallo cikin 6aci rai tadaka masa kai! Dallah dakata kai har kanada bakin kiran wani mahaukacin in banda hauka mutume da ke kwance a kabarinshi kana kishi da shi wannan yana nufi Kaine k'ato ko k'ato na ban............wawan mari da Habeeb ya wanka mata ya yi sanadin da raguwar kalamanta suka qargame a mak'oshinta zafin marin yaratsa brain d'inta.
''Kafin tadawo daga natsuwarta ya chafke wuyanta ta baya ya yi mata mugun rik'o a tsorace Hannah tace yaya Habeeb meye haka me yasa za ka yanke mata hukunci cikin fushi"?
"Da hannunshi guda yakaiwa Hannah mari da sauri ta duk'e yasameta a kafad'a Hannah ta kwasa da gudu tanufi upstairs tana kwalawa madam Hindu kira.
"Nagaji da wannan masifafe son naki leesa da yake azabtarda ruhina ya mik'a hannu akan center table yadauki glass cup ya buga shi a jikin center table yafashe ya jefarda rabin fashashe cup d'in ya d'anko hannun Haleesa ya aza mata kar6i leesa ga makami ki caka mini a k'ahon zuciya na mutu na huta da wannan jarabbabe son da nake miki Wanda yake baki kwarin guiwa zagina.
"Dask'arewa Haleesa tayi takasa gane wance duniya take ciki tsananin mamaki kalaman Habeeb suka baibayeta.
"Hakan yabawa Habeeb daman cigaba da zazzage mata asirin zuciyarshi, leesa inasonki ina miki son da nikaina bana yi wa kaina shi, inasonki fiye da son da margayi Habeeb yake miki wallahi nafishi sonki leesa kece farin cikina banta6a son wata 'ya mace ba sai akanki banta6a sani menene tunani da damuwa sai da na afka sonki. soyayarki tayi min illah leesa.
''Me yasa leesa bara ki so ni ba"?
Ko kina nufi bai kai matsayin da za ki soni ba"?
Nasan nayi miki laifi a baya amma a yanzu nayi Nadama ki tausayawa rayuwata leesa ki soni, muddin baki soni ba leesa zan iya rasa rayuwata.
"Yana k'arasa magana yatureta tafad'i k'asa da6ass.....
"Fashashe cup d'in hannunshi ya matse gam......ya yanke shi jini yasoma zuba.
"A rikice madam Hindu take taka staircase Hannah na biye da ita salati ta rafka kanka d'aya kuwa Habeeb"?
Kana hauka ne akan wane dalilin za ka mari 'yar mutane"?
"Kalli yadda hannunka yake zubarda jini ajiye cup d'inan nace wai ba da kai nake magana bane"?
''Habeeb na tsaye k'ik'an yakasa motsi madam Hindu ta ware yatsunta ta wanka masa bahagon Mari babu shiri yasaki glass d'in hannunshi.
Da baya-baya yafad'a bisa kujera madam Hindu ta durk'usa ta d'ago fuskar Haleesa da hannayenta biyu Haleesa kuwa tadawo kamar wance batada jini a jiki.
Tashi Haleesa tashi tsaye kinji"?
Ta mik'e da kyar madam Hindu ta dubi Habeeb tace tashi kafice kabani wuri nace katashi katafi har sai na nemi ka tak'arasa magana cikin shouting.
''ya mik'e a fusace yafita "madam Hindu tarik'o Haleesa zuwa bedroom d'inta har zuwa lokacin Haleesa batasan idan kanta yake ba takasa sarafa brain d'inta madam ta kwatarda ita akan gado.
Hannah ta dubi madam tace wallahi mom yaya Habeeb azzalumi ne ya k'untatawa rayuwar Haleesa nan take ta zayanowa madam irin zaman da Habeeb yake da Haleesa ran madam yayi matuk'ar 6aci tasoma zazzaga masifa kamar ta ari bakin kare tabbas sai na nunawa Habeeb kuskure shi ni zai munafuta agaban idona yanuna yanaso yarinya nan ashe abayan idona zaluntarta yake yi.
Yayinda Hannah tacigaba da zuga madam.

_washe gari_
Tun da asuban fari Habeeb yadako sammako gidan madam ya yada zango a downstairs parlour.
Sai around _10:22am_ madam tasauko k'asa ta hango Habeeb kwance akan 3 seater hannunshi daure da bandage ya yi zurfi a tunani tadaka masa tsawa kai! Tashi mu yi magana ya mik'e zaune a tsorace sosai madam ta wanke mishi allonshi.
"Abunda nakeso da kai tun da sha'awarta ka ke yi na tabbata zuwa yanzu ka kawarda kwad'ayinka akanta, a matsayina na wance ta nema maka aurenta na umarce ka da ka rubuta takarda sakinta kabani yanzu nan.
"A rikice Habeeb yafad'o daga kan kujera ya k'urawa madam Hindu manyan idanunshi, da ana mutuwa adawo duniya da Habeeb ya mutu yadawo saboda kalamai madam ba k'aramin girgizashi suka yi ba ji yake kamar tana labta masa rod'i aka.
Cikin rawa murya da sark'ewar numfashi yace ki dubi Girman Allah sweetheart ki yi hak'uri kiyafemin wallahi ina matuk'ar son leesa......

Jeeddah Aliyu🌹
[10:25PM, 14/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [14/12 9:34 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```92```


~~Sweetheart rabani da leesa tamkar rabani da numfashina ne domin ita ce farin cikina Dan Allah sweetheart ki yi hak'uri kiyafemin yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Harara madam Hindu ta galla mishi cike da takaicin tanuna shi da yatsa banaso na dinga jayaya da kai saboda ni ba sa'arka bace, ballantana nima kace za ka yi min pretending d'in da kasaba ka shiga taitayinka.
"Da Jan d'uwawu yak'arasa Wajen madam ya kifa kanshi a guiyoyinta muryarshi na rawa yace ki cuto rayuwata sweetheart wallahi duk abunda ki ka ji yafito daga bakina ba "pretending bane har cikin zuciyarta inaso leesa idan ki ka rabani da ita za ki iya rasani.
''Da k'arfi ta ture kanshi daga jikinta sai me don narasa ka ae ba kai kadai na haifa ba, ko kanaso ko bakaso dole ka ka saki Haleesa domin baran bare kacigaba da zaluntar 'yar mutane ba.
"Runtse idanu yayi zuciyarsa na tafarfasa yarasa kalma da zai lalla6o ya furtawa mom ta fahimcin irin tsagoro so da yake wa Haleesa, rik'on hannunta ya yi "sweetheart please try to understand me nasan nayi kuskure, a yanzu kuma nayi Nadama ki tausaya min karki rabani da farin cikina.
"Tsaki madam ta ja ta fizge hannunta daga rik'o da ya yi mata na baka 24 hours kawo min takarda sakin Haleesa idan, har kasan bara ka zo min da takarda saki ka kuskure ka k'ara zuwa min gida na shata dogon layi tsakaninka da ita tashi ka bani wuri.
''Habeeb ya yi shiru tamkar bai ji abunda tafad'a ba cikin 6acin ran madam ta mik'e tsaye tun da bara tashi ba ni bara na tashi, na baka wuri sai kayita zama shashasha banza da wofi mai baqar zuciya kana sonta ubanwa yace kadinga wulaqantata"?
''Tsabar iskanci irin naka Habeeb ka ware, yatsunka ka wankawa 'yar mutane mari yanzu idan iyayyenta suka ji irin wulaqanci da kadinga yi wa 'yarsu mekake tsanmani zai faru"?
''Anan ne Habeeb yad'ago a tsorace yana kallon fuskar Madam Hindu, ya hadiye yawu masu masifar d'aci yarasa abun fad'a jikinsa ya yi mugun sanyi madam ta girgiza tanufi d'akinta tabar Habeeb zaune cikin yanayin k'ila wa qala.
"Tsawon _5 minutes_ yadauka dafe da kai ya mik'e a kasalance haura staircase direct d'akin Hannah domin anan yakesa ran zai ga Haleesa batare da yanemi izzini masu d'akin ba ya murd'a handle yadanna kai.
"A tsorace Haleesa da Hannah da ke kwance akan gado suka dubi bakin k'ofa Haleesa ta d'auke kanta da sauri.
"Ajiyar Zuciya Habeeb ya yi yak'arasa, kusa da gadon fuskarshi a murtuk'e ya dube Hannah ya zaro mata manya idanunshi a tsawace yace ke tashi"!
"Da sauri Hannah ta mik'e zaune ya nunata da yatsa banta6a, sani Hannah munafuka ce ke ba yau.
Uhm......uhm.....yaya Habeeb me nayi maka da za ka kirani da munafuka"?
"Zan wanka miki mari in ki ka k'ara tambyana abunda ki ka yi mun tsabar munafucin irin naki Hannah, ki ka ce da mom nace banaso leesa sha'awarta nake yi domin nasan leesa
tana da kunya bara ta ta6a tunk'arar mom da wannan magana ba saidai tafad'a miki ke kuma da ki ke fitsararriya shine ki ka fad'awa mom.
''Jikin Hannah yadauki rawa ta yi wuk'i-wuk'i da idanu gani haka yasa Habeeb yarik'o kunnenta ya murd'e da k'arfi Hannah tasaki ihu azaba yasoma kashe mata gargad'i muddin ki ka sanarda mom na shigo d'akinan sai nayi miki dukan tsiya tashi ki fita.
''A lokacin d'aya Hannah da Haleesa suka mik'e tsaye saboda ko Haleesa ta tsorata da lamarin Habeeb ganin take yi da yagama da Haleesa zai juyo kanta.
''Da sauri Habeeb yasha gaban Haleesa kallo-kallo suka shiga yi wa juna eyes balls d'inta suka yi mugun tsorata Habeeb sakamako yadda suka yi kwancin jini ga layin yatsunshi kwance akan kumatunta.
"Nan take Nadama yak'ara lullu6enshi sonta da tausayinta suka k'ara samun muhalli a zuciyarsa.
''Sautin kukanta ne yak'ara dawo da shi natsuwarshi hannunta yarik'o da k'arfi tafincike hannunta tara6a gefenshi za ta Wuce yak'ara shan gabanta I'm so sorry leesa Dan Allah ki saurareni nasani ni mai laifi ne a gareki shiyasa nakeso ki bani dama na goge laifina.
"A fusace tafara magana had'e yarfe hannayenta Nagaji yaya Habeeb nagaji da wahala da ka ke bani kafita hanya ta banaso ka k'ara zuwa idan nake ko wannan zaman da nake yi anan gidan don inajin kunya mom ne da tuni na kama gabana.
"Habeeb yadawo kalar tausayi, yak'ara sausauta murya leesa ko ubangiji da ya halince mu muka sa6a masa idan muka rok'eshi yana yafewa mana ballantana mu 'yan Adam.
Kowane d'a Adam ba ba ya wuce kuskure leesa ki tausayawa rayuwata kiyafemin.
"Batare da ta tanka masa ta nufi gefen gado ta zauna tadafe kanta tsaye Habeeb ya yi yana kallonta daga bisani ya baro inda yake yanufi wajenta ya zube gabanta ya yi kneeling yad'ago fuskarta.
"Ta runtse idanunta gam...... Ko kusa bataso kallon fuskarshi domin zai iya karya mata zuciya, har ya yi nasara gano ta yi zurfi a sonshi.
"Narasa kalma da zan yi amfani da ita "to express my feeling for you leesa but I really love you bara iya cewa ga takamame lokacin da sonki yashiga zuciyata ba amma kisani ina miki so da bana yi wa kaina.
"Ina rok'onki, ki amince da ni zan koyo miki yadda za ki so ni leesa ke ce mace ta farko da zuciyata tafara so tsawon rayuwa da nayi da aunty salma banta6a jin kwatankwacin abunda nakeji akanki leesa.
"Haleesa tarasa sama take ko k'asa take takasa amincewa da abunda kunnenta yake ji daga bakin Habeeb Lamido dama akwai ranarda da arrogant kamar Habeeb Lamido zai k'ask'antata kanshi a gareta sai yau tak'ara yarda da nasiha da Ammi take mata _Haleesa ki yi hak'uri Ki kasance mai tawalkali Allah da ya kar6i Habeebu shi zai kawo miki Wanda yafi shi komai na rayuwa_
''A lokacin da Ammi take mata wannan nasiha jin ta kawai take sai take gani kamar Ammi tana fad'a ne don ta kwatar mata da hankali sai gashi Allah ya nuna mata shi mai rahama da jinkai ne ga bayinsa ya had'a ta Wanda yafi margayi yaya Habeeb komai.
''Ita kanta tasan samun Habeeb Lamido a matsayin mijinta Rahama ce ta ubangiji Haleesa tayi ajiyar zuciya mai k'arfi tana ware idanunta akan fuskar Habeeb tak'ara jin wani Sabon sonshi yana kwarara a zuciyata.
''Wata zuciyata tace What are you waiting for Haleesa just tell him you love him, nan take wata zuciya tace Haleesa za ki zubarda ajinki ne ki yi amfani da damar da ki ka samu, ki latsa shi kamar yadda shima yabaki wahala.
"Yatsine fuska tayi kaga bawan Allah nace bana sonka ka kyalleni ka fita daga rayuwana idan kace za ka cigaba da matsanta mun za ka nemi ni karasa, kuma karka yi tsanmani zan tafi Yola uwa duniya zan shiga idan har ka mutu bara ka samu Wanda zai ce ya ganni, ba don haka karka yi wa iyayyena asara ta domin su ne suke min soyayya ta gaskiya ba pretending ba.
"Dafe kai yayi had'e da furta Omg! Wani tuk'uk'i yake ji a zuciyarshi ran 'yan maza yafara 6aci shi dai gashi ba gwanin surutu ba amma yak'ure malejinshi yadawo tamkar parrot duk don Haleesa ta fahimce irin mugun sonta da ke d'awainiyya da shi takasa fahimta sai wani banza zance da tashigo mishi da shi wai yana ,pretending.
"Habeeb ya mik'e a sanyaye ya zauna kusa da ita ta matsa da sauri yak'ara matsawa ita ma tak'ara matsawa haushi ya turnuk'e Habeeb ya d'ank'i hannunta yashiga murza yatsunta da k'arfi ihu taje kurmawa da sauri ya had'e bakinshi da nata tsawon lokacin suka, dauka a haka daga bisani yasaketa ya had'e goshinshi da nata yad'anna mata cizo a hanci ta runtse idanunta hawaye, yasoma gangaro mata ban yarda ba yaya Habeeb baka sona yaudara ta ka ke yi za ka cuce ni ne watakila har yanzu da raguwar sona wata a zuciyarka
Can! K'asan mak'oshi yafurta meyasa bakida tausayi leesa"?
''Ko makaho ya dubi zai gano I'm in love with you leesa.
"Yatsine fuska tayi tace watakil ni makauniya, ce shiyasa nakasa amincewa da kai.
"Habeeb ya girgiza kai yace mu ajiye wannan zance a gefen banaso ki amince ki ta kallona a matsayin Wanda baya sonki, don ma kinsamu ina rarrashinki kidaina gani mom tana cewa sai na sake ki fad'a ne kawai take yi don taji dad'in bakinta tasaki nishad'i amma wallahi koda za ta aza mun bakin bindinga aka zan furta mata inasonki ba wai kalma saki ba yanzu ki yi favour d'aya za ki yi min kitash mu tafi hospital a duba min idanu nan naki banaso wani abu yasame ki.
"Murmushi takacin Haleesa tayi tace ae ba wannan ne karo na farko da kasaba mari na idanuna su yi kwancin jini yatsunka su sami muhalli a kumatuna karka damu kanka wannan ba bako bane a wurina
"Murmushi Habeeb yayi had'e da d'anke yatsunta, uhm...leesa yanzu abunda yafaru almost 3 years ashe baki manta ba"?
Harara ta zuba masa ta kauda fuska.
Duk yadda Habeeb yaso Haleesa ta saurare shi tak'i daga karshe ma ta yi mik'e tanufi k'ofar fita da sauri yadawo da ita da kyar ta amince ta zauna.
"Cikin tsawa tafara magana nace bana sonka yaya Habeeb ka kyalleni kai ka manta irin wulaqancin da ka dinga zuba min eyeee"?
Ko angaya maka banida zuciya a kirjina to ina gargad'inka kafita harkata I don't love you anymore banaso ganinka please stay away from me tak'arasa magana cikin sautin kuka.
"Habeeb ya ja iska cike da takaici yake kallonta ahalin yanzu kalamai bakinshi suna daf takarewa.
"Tsawon lokacin suka dauka ba Wanda yak'ara magana Habeeb ya kai dubanshi akan wrist watch d'in hannunshi zaro ido yayi cikin kaduwa yake kallon Haleesa daga bisani yace ki dubi tsawon lokacin da na dauka a d'akinan ina miki magiya wannan kadai bai isa ya gansar da ke inasonki ba.
"leesa ba abunda nake ba wa mahimmancin irin lokacin domin da yawuce ba zai dawo ba amma gashi throughout ba inda naje ina zube a gabanki ina miki magiya ki ji tausayina leesa kiyafemin.
"Haleesa ta yi shiru kamar tana nazari daga karshe brain d'inta ya nazarto mata mugunta da za ta yi wa Habeeb

Please Login or Register in order to submit comment