Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyimin,kinga ni inada wani albishir dazan miki"

Kallonta kawai jalila keyi ba tare da tace komai ba.

Ita kuma deejah ta cigaba da fad'in "nayi babban kamu k'awata kinga na samu wani guy d'in zamu wanki banza yanzu haka office d'insa zanje"

Kayan ta gama zurawa sannan ta kalli jalila tace "k'awata saina dawo" ta fice jalila ta bita da ido.

«»
Jalila dirarriyar macece tana da shape sosai 'yar kimanin shekara 19 a duniya ba fara bace kuma ba bak'a ba,chocolate color ce amma kyakkyawar gaske dan kyanta a bayyane yake.

Deejah fara ce sol kyakkyawa ce tana da diri itama doguwa ce sosai 'yar kimanin shekara 28 a duniya.

Ikram yarinyace 'yar kimanin shekara 6 a duniya,tana da kyau itama mutane na sonta musamman 'yan gidan saboda kyanta yana rud'arsu musamman da take yarinya.



_Sadeey S Adam_💅

[9/29, 9:20 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_


_~*«Episode 5»*~_

A bakin layin ta had'u da da bashir,tun daga nesa yake washe mata baki ita kuma tana smiling.

Tana k'arasawa tayi saurin cewa "da magana a bikinka"

Hmmm "kema ashe kin gane"

"Eh ai tunda naga kana wangale 32 d'inka nasan kana da abin fad'a"

"Kin san me?"
"A'a sai ka fad'a"
"Wallahi kinyi masifar yin kyau ke kin ganni kuwa?yo wazaice kin haifi ikram idan ba fad'a akayi ba"

"Hahah daina fasa min kai bashir,kasan ni haushina d'aya babu wanda zai ganni yaga Jalila ya yarda jalila ce ta haifi ikram saboda fuskar jalila kad'ai ta isa nuna maka ita yarinyace da baici ace ta ajje 'ya kamar ikram ba,uwa uba jikinta k'arami ne bata da jiki kwata-kwata amma da ba dan haka ba wallahi da taga tuggu"

"Yanzun ma kinsan me za'ayi?"
"A'a sai ka fad'a"
"Matso kawo kunnenki kiji"

Matsawa tayi daf dashi yayi mata rad'a a kunne.

Dariya tayi sosai sannan tace "hakan za'aiyi kuwa,amma ka bari komai ya daidaita tsakanina da Mujahid"

"Okay ba damuwa amma da sharad'i"
"Na me?"
"Duk abinda ya baki tare zamu raba"
"Cab! Zan dai sammaka"
"To a fasa zuwa kawai"
"Kaji d'an bak'in ciki,na yarda muje"
"Ah to ai gaskiya ce"

Napep ya tarar musu suka shiga ya fad'a ma mai napep inda zai kaisu.

Suna isa wurin tayi saurin mik'awa d'an napep 1k bata jira chanji ba tayi gaba,,shi kuwa bashir ya tsaya ya karb'a sannan ya fita.

A bakin gate ya tsaya yayi mata kwatance yadda yake dan bayason ya shiga ciki tsautsayi ya had'asu.

Hankalinta kwance ta zura glass a fuskarta ta tafi cikin k'asaita tana tafiyar kamar bata son taka k'asa.

A farfajir gurin ta had'u da wani ta tambayeshi office d'in mujahid.

Shi ya rakata har gurin Secretary na mujahid sannan yace a mata iso.

Tafi minti 5 a zaune sannan akace ta shiga.

Tana shiga ta hangoshi zaune yana ta rubutu a wani file.

_masha Allah lallai nayi babban kamu_ ta furta a zuciyarta.

"Zauna mana bismilla" ya fad'a ba tare daya kalleta ba.

Zama tayi ta k'ura masa ido ba tare da tace komai ba.

Ganin shirun yayi yawa yasa ya d'ago kai ya kalleta
"Ya kikayi shiru ki fad'i abinda ke tafe dake"
"Uhmm maganar nada nauyi a baki mujahid Allah yasa karka watsa min k'asa a ido"
Ta fad'a cikin kissa da kashe ido.

"Idan baki da abin cewa zaki iya fita ga hanya dan nan ba gurin surutu bane mara ma'ana"

Ta d'an zame veil d'in kanta tace "mujahid tun ranar dana fara ganinka naji duk duniya babu abinda nake so kamarka,hakan ne yasa nayi ta neman address d'inka har Allah yasa na samu"

"So kuma" yayi murmushi sannan yace "nagode amma ni bani da intention d'in k'ara aure kinga kuwa no need na fara soyayya da wata dan matana d'aya ta isheni komai"

"Mujahid bawai ka aureni ba but muyi soyayya wallahi da gaske ina sonka kuma nima bance ka aureni ba"

"Ban gane ba ar u out of ur sense?dama ana soyayyar da ba'a tunanin aure?"

"Eh mana ai ita nake so muyi,kawai mu dunga biyawa junanmu buk'ata ba dole sai munyi aure ba"

Kallonta kawai ya tsaya yi sai yanzu ya ga dressing d'in dake jikinta wanda sam kana gani kasan babu tarbiyya.

Ita kuwa sai k'ara kisisina take dan tana tunanin hak'onta ya cimma ruwa.

"Fitar min daga office"
"Ban gane ba mujahid?"
"Kinga bana son k'azamin bakinki ya rik'a ambatar sunana ki fita a office d'ina tun muna mu biyu kafin nasa a wulak'antaki"

Tashi tayi ta dawo gab da kujerarshi tana neman tab'ashi ya tashi tsaye ya wanketa da mari.

Da sauri ta rik'e kuncinta tana kallonshi.

"Kad'an kenan kuma ki fita yanzun nan,sannan kar na sake ganinki a office d'ina"

"Babu inda zanje har sai ka karb'i soyayya ta"
"Oh haka kika ce"
"Eh"

"Secretary" Mujahid ya k'wala kira.
Da sauri Secretary ya shigo yace "yallab'ai gani"
"Ka kirawo securities guda uku su fitar min da ita"

"A'a dakata" tayi saurin fad'a.

Ta juyo ta kalleshi tace "sai kayi nadamar marin da kayi min zan fita amma ka sani dole ne sai nayi soyayya dakai indai muna raye"

Fuzgar jakarta tayi ta fita,suka bita da ido.
"Yallab'ai kayi hak'uri wallahi nayi tunanin ko mota zata siya"
"Ba damuwa uzairu jeka kawai"

Fita yayi cike da mamakin Deejah.

Tana fita bashir ya tare ta da zumud'i yace "ya kukayi dashi?fiddo kud'in da ya baki mu raba"

'Daga hannu tayi ta wanke shi da mari tare da fad'in "mari na yayi ga naka rabon"

Rik'e kuncinsa yayi yace "haba deejah wannan ai mugunta ce"
"Ba kace duk abinda ya bani sai mun raba ba shine muka raba ai"

Labarin duk abinda ya faru ta bashi,sannan ta fad'a masa duk abinda zatayi.

"Ki had'a da Jalila kinsan ta fiki gogewa a bariki"

"Banza kawai,zan had'a da ita ne dan bazan iya ni kad'ai ba amma ba dan ta fini sanin komai ba".

Haka suka rabu ta koma gida cike da b'acin rai na rashin nasara da tayi, tana zuwa ta tarar da jalila na girki.

"Jalila yau bazaki fita ba?ina dadiron naki ko yayi tafiya"

"A'a yau ikram ta saka jikina yayi sanyi shiyasa bazan fita ko ina ba"

"Ta dawo daga skul ne?"
"A'a ai lokaci baiyi ba"
"Tab ki zauna ki biyewa ikram ta hanaki shanawa"
"Uhm deejah kenan meye a kumatunki kamar mari?"

Tab'a gurin tayi sannan ta shige d'aki kawai.
"Hmmm kinje kin kwaso abinda yafi k'arfinki kenan"

Jalila ta fad'a tana murmushi.

«««««»»»»»

Koko ne a gabanta har ya huce, ta tsura masa ido ta kasa sha.

Bud'e labule akayi aka shigo.
"A'a iya baki sha kokon ba har ya huce?"
Hussaina ta fad'a tare da samun guri ta zauna.

Wadda aka kira da iya ta d'ago kai ta kalleta tace "ki duba ki gani yau shekarar Hassana biyar bata tare damu da alama bata son waiwayarmu ma,gashi tun da d'anya goyo ta bar k'auyennan 'yarta na wata tara lokacin,ni dai ina tunanin kodai sun mutu ne.

"Iya kin manta hassana na da dogon buri tun kafin tayi aure bare da aka aura mata wanda ba zab'inta ba,ni dai inaji a raina hassana na raye kuma zata dawo,ni babu wanda ke bani tausayi kamar yaya Muntari 'ya d'aya tilo an rabashi da ita gashi har yanzu ya kasa aure,gaskiya hassana bata kyauta ba"

"Talauci ne bata so,amma ya zatayi tunda haka Allah yaso ganinta"

"Iya hassana kinsan tana da buri a rayuwarta rayuwar da masu kud'i keyi itama tace dole tanason yi,gashi aka d'aura mata aure da yaya Muntari wanda makanike ne kinga baba ma ya fishi arzik'i tunda baba headmaster ne shiyasa tayi yanda tayi har muntari ya saketa da d'anyen jego ta gudu ta bar garin nan wallahi iya hassana na raye a doron k'asar nan fatana Allah yasa karta shiga wata hanyar da ba daidai ba ko dan d'iyarta"

"Hussaina sai dai kiyi hak'uri amma tabbas 'yan biyunki ta rasu" iya ta fad'a tana goge hawaye.

"Hassana na raye" sukaji anyi maganar daga k'ofar d'aki.





_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:20 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~_



_~*«Episode 6»*~_

Shigowa yayi cikin d'akin duk hankalinsu ya koma gareshi.

"Hassana tana raye iya,kawai dai ta zab'awa kanta rayuwar da take ganin shi yafi dacewa da ita,karki manta lokacin da za'ayi bakinta cewa tayi wallahi sai ta gudu ta bi duniya,sannan tasha fad'awa hassana itafa tana son yin rayuwa irin ta 'ya'yan masu kud'i tana son itama taga ta mallaki mota da babbar waya yanda 'ya'yan masu kud'i suke facaka da kud'i itama tana son ta ganta haka,wallahi na tabbatar hassana na raye dan da ta mutu da tuni labarin mutuwarta ya riskemu"

"To yaya Kabiru yanzu a ina kake tunanin zamu nemo husaina?a cikin garin katsina ko kuma a k'auykan nan namu?"

"Hmm ai kawai ku manta da ita da kanta in taga azabar rayuwa zata dawo"

Iya da tun lokacin da kabiru ya fara magana take hawaye sai a lokacin tace
"kana tunanin zan manta da hassana?taya zan manta da abinda ya tsago jikina ya fito,ko dan kai baka san zafin haihuwa ba tunda kai namiji ne sannan baka san ciwon d'a ba tunda baka tab'a aure ba bare ka haihu,amma kaje kacewa muntari ya manta Hafsat kaji me zaice?duk da tana jaririya ya rabu da ita,saboda haka nima bazan manta da Hassana ba musamman idan naga hussaina saboda kamaninsu d'aya tawwadar dake kumatun Hussaina ita kad'ai ta banbance kamanninsu".

Kabiru da Hussaina sukayi ta rarrashin ta suna sanyaya mata zuciya.

«««««»»»»»

Ranshi a b'ace ya k'arasa bedroom ya kwanta.

Lailah ce ta shigo tazo daidai gadon da yake kwance ta tsaya.

Tsawon mintuna bata ce masa komai ba daga bisani ta lura ma hankalinshi ba'a kanta yake ba.

"Na shiga uku ni kam bashir yana son lalata min farin cikina"
Ta fad'a tana kallon shi.

'Dago kai yayi ya kalleta sannan ya tashi zauna "wane bashir fa?"
"Wanda ya saka min kai a damuwa"
"Hmm har na manta da maganar bashir"
"Okay! Meke damunka tunda ka dawo ka kasa nutsuwa"

_fad'a miki zai iya zama babban tashin hankali a gareki_
ya fad'a a zuciyarshi idonshi akan fuskarta.

"Ya dai?"
Lumshe ido yayi yace "babu komai"
"ur mind is somewhere meke damunka ne?"
"Baby na gaji sosai,ciwon kai nake"
"Amma shine baka fad'a min ba?"
"Bana son hankali ki ya tashi"

Da sauri ta mik'e ta fita,da ruwa da magani a hannunta ta shigo, chuchu da fad'ima suna biye da ita.

Da sauri suka haye gadon tare da fad'in "daddy sannu Allah ya baka lafiya"
"Amin dearies"

Fad'ima ta rungumeshi tana fad'in "sannu daddyna"

"Oyaa kuje kuyi game kafin malam yazo maza maza kuje" Lailah ta fad'a tana sauke fad'ima daga kan gadon.


Da gudu suka ruga suka fita,ita kuma ta b'allo maganin ta mik'a masa.
"Kin san bani son shan magani ko"
"Ka daure kasha for my sake pls"

Karb'a yayi dan babu yadda zaiyi haka yasha,ta zauna tana tayi masa sannu shi kuwa abinda ya dameshi da ban.



_fans kuyi manage da wannan 😍_





_Sadeey S Adam_💅

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_



_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_




_*SAFNAH LUV!Marubuciyar(KUN YI SAKE),Aishat A Muh'd!Marubuciyar(A SANADIN SON KI),Mrs Umar& Beebah luv Marubutan (TAWA 'KADDARAR)*,wallahi ban ma san da wace kalma zanyi amfani wajen godiya gareku ba duk kanku kun sadaukarmin da littafinku,gaskiya ku masoyana ne na hak'ik'a nagode da irin wannan karamcin da kuka nuna min,kalaman bakina sunyi kad'an wajen gode maku,hak'orana bazasu gaji da yi maku fara'a ba,bani da abinda zance sai dai in maku fatan alkhairi a rayuwarku ina fatan Allah ya biya muku dukkanin buk'atunku na alkhairi,Allah yasa yadda kuka fara novels d'inku lafiya yasa ku gama lafiya,ina maku fatan alkhairi a koda yaushe._
#Ana mutuk'ar tare#🤝😍


_*~«Episode 7»~*_

'Kurawa deejah ido tayi tun lokacin da ta fara magana har lokacin da ta kai k'arshen maganar.

Ganin Jalila tayi shiru bata da niyyar magana yasa tace "haba jalila inata magana kinyi shiru"

Smiling tayi tare da fad'in "yau kuma ni kike neman taimakona ai nayi tunanin bani da amfani a gurinki"

"Haba Jalila idan ban kawo miki kukana ba wazan kaiwa?kuma gani nayi kina da saurayi a gurin wanda shi babbane a kamfanin"

"And so?"
"Hmmm nagode ban tab'a tunanin zan nemi alfarma a gurinki na kasa samu ba jalila"

"Deejah kenan" Jalila tayi maganar lokacin murmushinta ya k'aru.


"Kamar yadda na fad'a miki Jalila dan Allah ki taimakeni,shine fa yayi min cikin nan amma yana neman guduna ni na yarda zan d'auki responsibility na cikin jikina amma bana son ya gujeni"

Jalila ta tashi tsaye tare da tafa hannu tana dariya.

Ran deejah ya b'ace amma ta daure ta cigaba da fad'in "Jalila dariya na baki wato ko tausayina bakya ji saboda baki san mahimmancin soyayya ba baki san mene son gaskiya ba"

Dafe goshi jalila tayi tare da rufe baki da d'ayan hannun tayi ta k'yalk'yala dariya sai da tayi mai isarta sannan tace "zanje inyi yadda na iya dan na sato miki zuciyarshi amma kuma kina tunanin ki cigaba da soyayya da wanda ya cuceki ya d'irka miki ciki?"

"Baki ganshi bane ya had'u uwa uba ga kud'i"

"Kina bani mamaki deejah,kinganni nan ban tab'a yin bariki da niyyar samun kud'i ba ni kawai inayi ne saboda in biyawa kaina buk'ata dan na san babu mai aurena a duniya a matsayina na wadda karuwa ta haifa kuma ta taso gidan karuwai ta zama karuwa ba uwa ba uba,zuwankine ya saka ni yin bariki saboda kud'i dan bani son rayuwarku ta lalace keda Ikram amma duk da haka sai da aka hure miki kunne kika zama tantiriya kuma akuya mai bin kowa"

"Ya isa haka Jalila kada ki sake kirana da akuya ke kike da abin magana bani ba kin wani zauna sai fad'a min magana kike ai lokacin da kike tunanin kin hanani bariki dan ban san dad'in hakan bane sai daga baya na gane cuta ta kikayi"

"Kyaji dashi dai kullum kina bin maza suna miki ciki baki da tsayayyan saurayin da zakuyi wata kuna tare,tun ikram tana 'yar shekara d'aya a duniya kika zo da ita nan,a hannuna ta taso baki tab'a damuwa da ita ba,Allah sarki tana shekara d'aya kikayi mata yayen dole,wallahi abin kunya ne ikram taji ke kika haife ta"

"Ya salam! Ni khadija na shiga uku Jalila baki da magana sai ta ikram,ni kuwa ikram d'in nan ba dole akayi miki da ita ba dan haka bara ta shigo gidan yau zata san nice uwarta sannan in wulak'anta ta in koreta"

Gaba d'aya Jalila ta zare idanunta tare da dafe k'irji.
"Kiyi hak'uri deejah idan ikram ta bar gidan nan ina zataje?wa ta sani?dan Allah ki daina maganar nan bata dace ba"

"Okay zan mu k'ulla wani alk'awari"
"Akan me?"
"Akan daga yau ko da wasa bazaki k'ara cewa ikram 'ya ta ce,na bar miki ita kuma inason dole kije ki jawo min hankalin Mujahid gareni ya soni idan ba haka ba wallahi ni da kaina zan sanarwa da ikram ni ce mahaifiyarta kuma in koreta a gidan nan babu wanda ya isa tunda babu wanda ya haifa min ita"

Wasu siraran hawayene suka fito daga idon Jalila ta kalli deejah tace "deejah kin min tsauri da yawa maganarki tafi k'arfin brain d'ina ba dan komai ba sai dan yadda kike k'ok'arin ruguza rayuwar ikram,na yarda ki fad'a mata kece mahaifiyarta amma kice zaki koreta wannan babban tashin hankalina ne"

"Eh kamar yadda na fad'a miki fad'awa ikram ni ce mahaifiyarta daidai yake da barinta daga gidan nan dan bazan iya bariki da 'yar da zata karya min zuciya"

"Na yarda zan rik'eta bazan danganta ta dake ba amma ki sani dole wata rana ta san kece mahaifiyarta"

Dariya deejah tayi tare da tab'e baki
"Ba damuwata bane,ni na manta ban fad'a miki magana ta k'arshe ba,dole ki bar gidan nan Jalila,kije can ki kama muku gida keda ikram"

"Ban gane ba?"

Gyara zama deejah tayi sannan tace "yanzu nayi tunanin cewa zamanku a gidan nan ma babban tashin hankaline,kawai ki bar gidan nan,kije ki sanarwa da magajiya zaki bar gidan nan saboda kin dad'e a ciki kuma kin gaji kina son canji,haka saurayinki mai bada hayar gidan nan kada ki sake ki nuna cewa ni ce nace ki bar gidan in har kina son ganin cigaban ikram,sannan kuma zaki bar min komai anan kayanki da nata kawai zaki d'auka kuma zaki bani 1million"

"Dakata deejah! Baki isa ba,wai shin yaushe kikayi bakin gaya min magana,kefa bazaki nuna min bariki ba domin ni gogaggiya ce a ciki,ki daina mafarkin da kike ya kamata ki dawo hayyacinki"

"Wallahi sai kinyi abinda nace in ba haka ba ikram na dawowa wallahi saina koreta"

Wasu hawayen suka sake zubowa daga idonta duk da tana ta mak'alesu dan kar su zubo,kallon deejah tayi sannan tayi dariya tace "ya kamata kiyi saurin farkawa daga mafarkin da kikeyi kinsan me?ban tara dukiya dan in bautawa mara halacci kamarki ba,kuma gidan nan sai dai ki barshi amma ni kam ba inda zani"

A dai dai lokacin ikram ta turo k'ofar ta shigo.
Duk kansu suka juya suka kalleta,hankalin Jalila ya tashi sosai dan gudun kar deejah ta fad'i abinda bai dace ba.

Kallonsu ikram take tana tsaye daga bakin k'ofar tace "mommy na dawo"

Ganin fuskarta da alamun damuwa yasa jalila tayi saurin k'arasawa gurinta tare da dafa kanta.
"Ikram meya faru?"

Kawai ji tayi an fuzge ikram d'in daga wurin.
Da sauri ta juya ta kalli deejah wacce ta fuzgi ikram tare da rik'eta gam.

"Karki min haka deejah dan kuwa ban cancanci wulak'anci daga gareki ba"

Cikin fad'a deejah tace "hakan shine dai dai,ki rayu a gidan nan nima zan kama d'aki a gidan nan kuma in zauna daram sannan ikram zata bar gidan nan ta kama gabanta kingane me nake nufi ai"

Tirjewa ikram ta fara yi tana fad'in "mommy kice ta sakeni"

"Wace mommyn taki?,k'arya take nice nan na haife ki"
Deejah ta fad'a tana girgiza kan ikram.

Hawaye wani na bin wani a fuskar Jalila haka ta rik'a kallon ikram da deejah ba tare da ta iya furta wata kalma ba.






_Sadeey S Adam_💅

[9/29, 9:20 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_

*_dis page goes to Mrs Xerks,Mrs Mus@ & Maman Hassan,nima ina sonku kamar yadda kuke sona ko ince fiye da haka ma, inajin dad'in yadda kuke nuna min so da k'auna, ina yinku sosai dearies😍❤_*


_nd Anty Maijidda Musa ke ta daban ce a cikin zuciyar SaNaz,Allah ya barni dake Anty_🙏🏻


_~*«Episode 8»*~_

"Aunty please kiyi hak'uri kaina ciwo yake,mommy kice ta daina"

Ganin deejah ta tsaya tana kallonta tana dariya ya sakata durk'usawa a gwiwoyinta tare da had'e hannayenta alamar rok'o.
"Kiyi hak'uri deejah banyi tunanin da gaske kike ba"

"Yanzu ai kin tabbatar da hakan,kin tabbatar da zan iyayin komai dan yanzu ba tsoronki nake ji ba,dole kowa na gidannan ya dawo k'ark'ashin ikona bawai ayi ta yayinki ke kad'ai ba"

"Okay naji na yarda amma dan Allah ki saketa rik'on da kijayi mata da zafi"

"Baran saketa ba har sai kin amince da sharud'd'an dana gindaya miki"

"Na amince amma ki sani bani da wata 1million da zan iya baki domin bani da ita"

"k'arya kike Jalila,shekara nawa kina bariki amma kice baki da 1million"

"Wallahi account d'ina baifi 2.5 million ya rage ba,karki manta shekara biyar ni nake ciyar daku ga sutura ga abincin ci uwa uba kud'in hayar gidan nan duk shekara 100k sannan ga uban kud'in da ake cajata a duk sanda za'a zubar miki da ciki karki manta kusan 300k ake cajarmu kuma dukkan abinda na lissafa nice nake biyan kud'in ga ikram yanzu t...............................

"Dalla rufe min bakinki" deejah tayi saurin katseta cikin k'arajii,ta kalleta tana yatsina fuska sannan ta saki ikram.

Da gudu ikram taje ta rungume Jalila tana kuka.

Zuciyar Jalila ta tsinke sosai dan haka itama ta fara kuka sosai.

"Hahahh kuka yanzu kika fara Jalila tunda har kika zab'i ikram kuma ki sani tsintacciyar mage bata mage,kuma indai ina raye sai na rama duk abubuwan da kika min sai na hanaki zaman jindad'i sai kin gwammace karuwar uwarki bata haifoki a duniya ba"

Bata san lokacin da ta wullar da ikram gefe ta tashi ta damk'i wuyan deejah ba.

"Wayyo Allah kasheni zakiyi Jalila?"
"Mutuwarki tafi amfani dana barki a doran k'asa ki rayu,ni kike zagarwa uwa?k'aryane wallahi,ban tab'a zagin taki ba kuma bani son kowa ya zagarmin tawa yau zan nuna miki wacece Jalila"

Kokowa suka fara ganin haka yasa ikram ta fita da gudu ta kira matan dake zaune a tsakar gida suna sana'ar tasu wato whot.

Da sauri suka shigo maimakon su raba sai suka rik'e Jalila wai a haka rabasu suka yi ita kuma deejah ta cigaba da dukanta tana kai mata wani naushi a fuska jalila ta saki wani uban k'ara gaba d'aya ta fuzge ta nufi gefen gado cikin zafin nama ta d'akko kwalbar lemo aikuwa ta sauke shi akan deejah.

Ihu ta saka sannan ta zube a k'asa saboda kwalbar ta fashe a kanta dan fashin kwakwa tayi da kwalbar akan deejah.

Ganin hakane yasa sauran matan fita da gudu kowa yana neman gurin b'uya aikuwa Jalila ta biyo su a guje,wasu sukayi sa'ar shiga d'akunansu suka rufe yayinda wasu sukayi waje da gudu ita kuma ta rufa musu baya kamar mahaukaciya.

Mazan dake waje ne suka tare ta ganin bata da niyyar tsayawa yasa wani dattijo ya rik'e hannunta gam.

Cikin kuka take k'ok'arin fuzgewa tana fad'in "ka sake ni wallahi duk sai nayi maganinsu yau"

"Baki da tarbiyya ne kalli yadda kika fito ba takalmi ba d'ankwali ko kuwa kin zauce ne"

Wani saurayine dake kusa dashi yace "baba ai wannan Jalila da kake gani 'yar bariki ce cikakka"

"Koma 'yar mecece" kallon hannunta yayi yaga kwalbar a fashe ga jini a jiki.
"Ke me kika aikata da wannan?" Ya nuna kwalbar.

"Ka sakeni nace wallahi duk sai sun gane cewar ni ba tsaransu bace"

Ganin tak'i tsayawa ta saurare shi yasa ya fara yi mata fad'a,kukan da ta fara ne ya sa fad'an nashi ya juye zuwa nasiha.

Sakin hannunta yayi suka shiga cikin gidan tare,gidan yayi tsit ko wacce ta arce wasu kuma sun rufe d'akunansu.

A k'ofar d'akin ta tarar da ikram tana kuka,ta rungume ta suka cigaba dayi tare.

Dattijon yana shiga d'aki ya hau salati,da saurin ya fito lokacin wasu daga cikin matan duk sun fito sun had'e gu d'aya suna al'ajabi.

"Ku samo mota a kaita asibiti"
A tsorace Jalila ta mik'e tsaye.

Hafsy tayi saurin cewa "ku fito na kaita da motana"
Kallonta kawai Jalila keyi dan ta san gulma ce zata kaita asibitin.

Haka aka fito da deejah kamar babu numfashi a tare da ita,ikram kuwa k'ank'ame Jalila tayi tana kuka.

Suna zuwa asibiti aka shigar da ita emergency su kuma suka zauna jiran tsammani,anan dattijon ya sake yima Jalila fad'a akan yanke hukunci cikin fushi.


*************

Ganinta kawai yayi ta shigo bedroom d'in taja mayafi a fusace ta fita.

Da sauri ya mik'e daga kan gadon ya bi bayanta,a farfajiyar gidan yaci karo da ita tana k'ok'arin shiga mota.

"Baby lafiya?ina zakije?"
Juyowa tayi ta kalleshi fuskarnan tata a d'aure tamau.
"Gida zanje na kaiwa Abba k'ararka"
"Ni kuma?"
"Eh kai"
"Tofah! Ni kuwa menayi ne baby?"

Kuka mara hawaye na shagwab'a ta farayi tana fad'in "wallahi na gaji ban saba da irin wannan ba,zaman lafiya muke da kai amma ya za'ayi kayi min fushi ba tare da na san laifina ba,har su chuchu sun gane kana fushi dani sun fara tambayata me nayi maka,ni kaina na tambayeka amma kak'i fad'a min gaskiya"

"Baby wallahi bakiyi min laifi ba,kwana biyu kawai bana jindad'i"

"Lafiyarka k'alau Mujahid kawai laifin wani ne kake neman d'ora shi a kaina"

"Mujahid! Tab gaskiya nayi laifi da yawa wai yau baby ce ke kirana da sunana,amma fa kin iya fad'in sunan please d'an k'ara fad'a naji"

Kallon shi kawai take ranta a b'ace tace "oh wasa ma ka mayar da abin?"

Dariya yayi sannan yace "a'a ni kawai gani nayi idan kin b'ata rai kyawunki k'aruwa yake"

"Oh ka mayar da abin wasa kenan" da gudu ta bishi ciki ya ruga yana dariya.
Maigadi ma sai daya dara.






_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:20 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~°dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~_


_d whole page is dedicated 2 u my Safnah...._
_tnx 4 d luv & care,I rily appreciate it n I heart u too dear😍_.
#Ana mutuk'ar tare#😍❤😘


_~*«Episode 9»*~_

Doctor ne ya fito rik'e da takarda a hannunshi.
"Gashi magunguna zaku siyo sannan kuma tana buk'atar jini gashi nan blood group d'inta zakuje lab ku siyo dan ta zubar da jini sosai,sannan kuma ina buk'atar ganin mijinta"

Da sauri Jalila ta d'ago kai ta kalli doctor,ganinshi ba k'ara min d'aga mata hankali yayi ba.

_Meyesa

Please Login or Register in order to submit comment