Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazaki kwana ba ko dai kina tsoron karna cutar dake ne,kuma naga kink'i karb'ar kud'i Allah yasa dai ba HIV gareki ba shiyasa bakya karb'ar komai._
Maganarshi ta tuno shekara 7 da suka wuce lokacin sun had'u a Abuja ne.

Shima shiru yayi yana kallonta,ya rasa me zaice sai kawai ya wuce ya barsu.

Jalila ta kalli dattijon tace "baba bara naje na karb'o takardar a siyo magungunan"
"To yarinya"
"Bara na rakaki" Hafsy tayi maganar.
"A'a bana buk'ata" Jalila ta fad'a tare da kama hannun ikram suka tafi.

Tana tura k'ofar ta ganshi tsaye.

Gabanta ya sake fad'uwa ta dai daure ta shiga ta zauna.
"Dama a kaduna kike?"
"Eh! Ka bani takardar maganin zanje na siyo"
"No ki barshi na aika a a karb'o a pharmacy jininma za'a karb'o a lab,amma idan ba damuwa zan miki tambayoyi please"

Kallon ikram tayi sannan tace "ikram jeki wajen su Hafsy ina zuwa"
"Mommy tsoro nake"
"Karki damu yanzu zanzo kinji"
Bataso haka nan dai ta fita.

Dawowa yayi kan kujerar shi ya zauna ya d'anyi jim sannan yace "wacece wannan?"
"Wa kenan?"
"Wadda kikace ta fita"

Shiru tayi na wasu lokutan tana d'an nazari akan tambayar.

"Ya kikayi shiru?"
"Eh bani da abin cewa"
"Kamar ya kenan?"
"Kamar yadda na fad'a"
"Da yaren da zaki gane na miki tambayar fa"
"Nima da yaren da kafi iyawa na baka amsa"
"Lallai kam ashe dama haka kike da surutu ai nayi tunanin bakya magana yadda na ganki farkon had'uwarmu so silent dake"
"Komai kamawa take ai,sannan abinda kake so ka sani yanzu zan fad'a maka wannan yarinyar da kake gani 'yata ce"

"Dama ke matar aure ce?"
Shiru kawai tayi tana kallonshi.

"Ya kikayi shiru please ki bani amsa domin nayi nemanki sosai a lokacin da muka had'u gashi ban san sunanki ba number da kika bani ma wrong number ce dan bata existing ma"

Murmushi tayi sannan tace "ai bana so ka nemeni shiyasa ban baka numberna ba"
"Amma a time d'in bakiyi aure ba ko?"
"Hmmm kawai ka fad'a min yanzu ma bani da aure kana da buk'ata ne dan ni yanzu ina bariki dan neman kud'i"

Wani k'ayataccen murmushi yayi sannan yace "ya kike yi da d'iyarki?kodai a bariki kika samota?"
"A'a 'yar halak ce tsarkakkiya labarin yana da tsawo karka damu da tambaya akanta muyi abinda ya dace"
"Okay no problem,amma dai yanzu zan iya sanin sunanki"

"Y not,am jalila nd u"
"Am Mubarak nyc 2 meet u once again"
"U r welcum,4 knw inaso na san halin da k'awata ke ciki"
"Oh kinga na manta ma,bara naje na gani ko an kawo drip da jinin"
"Okay amma naji kace kana neman mijinta ai itama 'yar bariki ce kamarni"
"No wonder,karki damu we will talk later,but ki bani number ki"
Batayi musu ba ta karb'i wayarshi ta rubuta masa,cikin farin ciki suka bar office d'in suka nufi emergency tare da yiwa junansu alk'awarin zasu had'u a office d'in k'arfe 5 na yamma.


****************

A hankali sautin kukanta ya fara bayyana wanda har iya dake tsakar gida taji kukan na fitowa daga d'aki dan haka tayi saurin ajje shinkafar da take tsincewa ta nufi d'akin da sauri.

Tana d'aga labule ta hango Hussaina zaune kan tabarma ta had'a kai da gwiwa tana kuka.

Jikinta a sanyaye ta k'arasa kusa da ita ta zauna.
"Komai yayi zafi maganinsa Allah duk da ban san abinda ke damunki ba ya kamata kiyi addu'a ki kai kukanki wajen Allah ni kaina b'atan hassana yana sakani kuka amma yanzu na barwa Allah komai"

'Dago idanunta tayi wanda sukayi jajir fuskarta ma tayi d'an jajaja kasancewarta fara sol ga hawaye nan ko ina a fuskarta.

"Iya ya zanyi?Hassana ta cuceni wallahi,ki duba lokacin da akayi mata aure tana shekara 21 a duniya wane surutu ne bamu sha ba gani ake munk'i aure har gori ake mana ana cewa in aka zo gidanmu za'a kasa banbacewa wacece matar gidan,lokacin da aka yiwa Hassana aure nayi tunanin nima ba da dad'ewa zan samu miji nayi aurena ba amma ganin irin cin mutuncin da take wa mijinta ya saka duk wani saurayi baya tunkarata dan ana ganin kamar halinmu d'aya sannan ki duba ki gani iya shekarata kusan 30 amma babu mashinshini ko ina na gitta a k'auyen nan zagina ake ana aibunta ni duk a sanadin Hassana"

"kiyi hak'uri Hussaina shi aure ai lokaci ne kuma da suke zagin naki kin tab'a ganin zagi ya fitowa mutum a jiki?dan haka ki rabu da duk wani surutu na mutane tunda mu iyayenki bamu tab'a jin mun gaji dake ba sai ma addu'a da muke Allah had'aki da nagari"

"To iya amma ki k'ara rok'ar min baba ya barni in cigaba da karatu"

"Insha Allah daya shigo zan masa maganar kuma zai amince da yardar Allah"

"Allah yasa"
"Amin Hussaina"

Hannu tasa tana goge hawayen fuskarta yayin da take jin wasu na k'ok'arin zubo mata.


Haka kuwa akayi yana shigowa bayan yaci abinci ya huta iya ta sanar dashi duk abinda ya faru.

Ya kira Hussaina yayi mata nasiha sosai sannan yace insha Allah shi da kanshi zai shiga cikin katsina ya nema mata kurb'in karatu,yayi mata alk'awarin kuma zai bawa wani abokinsa dake kasuwanci a kano yayi masa cigiyar makaranta dan hakan ne zai sa ta d'an sassauta damuwar da take yawan shiga.

Tayi murna sosai kuma tayi fatan Allah yasa a samu da wuri.





_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:21 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_


_*~«Episode 10»~*_

Ta bud'e k'ofar tana murmushi,lokaci d'aya murmushinta ya tsaya cak,wani shocked taji ya d'arsu a jikinta,da sauri ta kalli Mubarak sannan ta dawo da kallonta ga ikram.

Gaba d'aya jikinta yayi sanyi saboda yanayin fuskar ikram kad'ai ta tabbatar mata da cewa ta gansu gashi sun manta basu rufe k'ofa ba kasancewar duk ma'aikata an tashi kuma ba wani dad'ewa zasuyi ba amma still sai da ikram tazo.

Kallon kallo suke ita da ikram d'in,kallon tsoro take mata gaba d'aya ta rasa kalamin da zata yi wa ikram magana dasu.

Kuka ikram ta fara tare da juyawa da sauri ta bar gurin,hankalin Jalila ba k'aramin tashi yayi ba,da sauri ta bi bayan ikram ta bar Mubarak a nan tsaye.

Murmushi yayi sannan yace "hmmm idan kika biyewa 'yar nan zata hanaki jindad'i"

Ita kuwa Jalila da sauri tasha gaban ikram tare da fad'in "ikram ki tsaya mana ina zaki ne?"

Hannu tasa tana goge hawaye tace "mommy dama abinda ake ta fad'a akanki gaskiya ne"
"A'a ikram"
"Karki min k'arya mommy na ganki da idanuna,mommy ki k'yaleni ki daina bina"
"Ikram ki saurareni please" ta fad'a tana rik'o hannunta.
Fuzgewa ikram tayi sannan tace "bana son ki sake tab'a ni duk abinda ake fad'a a kanki ashe gaskiya ne" da sauri ta wuce Jalila ta bita da ido wanda gaba d'aya ya cicciko hawaye na gab da fitowa daga cikinsu.

Tafi minti biyu a tsaye a inda ikram ta barta,daga bisani taja k'afafunta a sanyaye ta nufi d'akin da deejah take kwance.
Har lokacin idonta a rufe yake ga jini an saka yana d'aga a hankali,hawayen da basu zubo ba sune suka samu damar fitowa a lokacin.
"Babu macen da zata zo dubata tunda dama babu wanda ake zaman lafiya dashi,mazane na san zasuyi ta sintiri a d'akin nan,babu uwa babu uba bare dangi" sai a lokacin hawayen idonta ya samu damar zubowa.

Da sauri ta fita dan ta nemo ikram kar tayi wani wurin.

Tana fita kuwa ta ganta a zaune gefen block d'in ta had'e kanta cikin cinyarta.

A hankali Jalila ta k'arasa inda take zaune tare da d'ago kanta.
"Kuka kike ikram?"
Bata ce komai ba kawai tsayawa tayi tana kallon Jalila.
"Ikram meyasa dan Allah ki daina kuka kinji?"

Hannu tasa ta cire hannun ikram daga fuskarta sannan ta tashi tsaye zata k'ara tafiya,da sauri Jalila tasha gabanta cikin fad'a ta fara magana.
"Waye ya sanar dake illa ko rashin illar abinda nake waye ya kaiki office d'in bayan nace kada ki biyoni?hankali da tunaninki ba zasu kai nan ba ki gaya min waye yake training d'inki akan wannan mummunar ak'idar da kike son d'orawa kanki ikram har kin san ki min lab'e?"

"Babu wanda ya fad'a min mommy ni naga kin dad'e shine naje kiranki mommy" kuka ta k'ara sakawa da sauri Jalila ta rungumota ita ma tana kukan,jefi-jefin mutanen dake cikin asibitin kallonsu kawai suke.

Sai da sukayi kuka mai isarsu sannan suka koma cikin d'akin.

Suna zaune babu wanda ke yima wani magana dan Jalila bata son d'ago kai dan data d'aga take had'a ido da ikram wanda ta rasa dalilin dayasa ikram take ta kallonta.

"Mommy" ikram ta ambaci sunan a hankali.

'Dago kai tayi a sanyaye ta kalleta ba tare da ta amsa ba.

"Mommy wai meye karuwanci?"

Gabanta ba k'aramin fad'uwa yayi ba,ta kafawa ikram ido a tsorace.

"Mommy ance wanda ya mutu yana karuwanci bazai shiga aljanna ba haka naji malamai na fad'a"

Wasu hawayenne suke kwararowa daga idonta ta kasa bawa ikram ko amsa d'aya.

"Mommy kina son ki shiga wuta?"
Sai a lokacin tace "dan Allah ikram ki daina fad'a min wannan maganar shin wa kika tab'a jin yace yana son ya shiga wuta?"
"Mommy amma meyasa kike aiki irin na 'yan wuta,mommy na gani da idona"
"Surutu?ina kika koyo surutu ikram?"
"Mommy ba surutu bane ina son ni dake duk mu shiga aljanna"

Hawaye ta goge ta tashi zata fita ikram ta sake cewa "mommy please karki fita dan Allah ki tsaya"
"Bazan iya ba nagaji da kalamanki"
"To ki dawo na miki tambaya mommy malaminmu ne yace nayi miki"
"Oh dama malaminku ne ya tsara miki wannan tambayoyin da kike min?"
'Daga kai tayi tare da fad'in "eh mommy domin kullum 'yan ajinmu sai sun zageni suce min mamana karuwa mommy kullum tsokanata akeyi har a makarantar boko kullum sai nayi kuka ina fad'a musu ni mommyna ba karuwa bace amma tana shaye-shaye"

Kallonta kawai ta tsaya yi na kusan 50seconds sannan tace "kince masu ina shaye-shaye ikram?"

"Eh mommy saboda shaye-shaye kad'ai Aunty tace kina yi kuma nima na gani amma duk da haka 'yan ajinmu tsokana ta suke yi wai mommyna tana karuwanci kuma na tambayesu meye karuwanci sun fad'a min kuma wai kowa ya sani a garin nan ke karuwa ce shine nayi ta kuka malaminmu yace nayi miki tambaya amma na kasa sai yanzu na gani da idona kina karuwanci"

"Wayyo Allah ni Jalila na shiga uku" ta fad'a tare da tsugunnawa ta dafe kanta tana kuka.
"Ya Allah ka sani ina yin iya bakin k'ok'arina ganin na bawa ikram kyakkyawar tarbiyya ya zanyi idan ta gurb'ace?na rasa mafita wallahi"
Ta sake rushewa da wani sabon kukan.

Ikram ta diro daga kan gado tazo gaban jalila ta tsungunna tace "mommy zan yi maki tambaya"

Jalila ta d'ago fuska wanda ta b'aci sharkaf da hawaye ta kalleta muryata na rawa tace "ina jinki ikram"
"Mommy meyasa kike karuwanci?dan Allah ki fad'a min"

Shiru tayi kamar baza tayi magana ba daga bisani tace "ikram inayi ne saboda in samu kud'i,in inganta rayuwarmu da ace bana karuwanci da ban samu kud'in da zan ciyar damu ba in kaiki islamiyya da boko in kuma yi maki duk abinda kike so"

"Mommy malaminmu yace masu kud'i guda uku za suyi shekara 50 a k'ofar aljanna ana yi masu hisabi,biyu a cikinsu zasu shiga wuta d'aya ne kawai zai shiga aljanna,kuma mommy kema kin sani"

"Ikram ban sani ba na haddace Al-qur'ani shima da k'yar saboda ance zaiyi ceto kuma ni kaina bana son in zama jahila amma ni banyi hadisi da sauran littattafai ba sannan banyi karatun boko mai tsayi ba tun daga secondary skul dana gsma magajiya bata sake cewa inyi wata ba,ta watsar da al'amurana na karatun arabi da boko"

"Mommy kinsan waye zai shiga aljanna a masu kud'i?"
Girgiza kai tayi lokacin da wasu sabbin hawaye suka zubo mata.

"Mommy na 1-wanda ya samu kud'i ta hanyar halak ya kashesu ta hanyar haram wuta zaije,
2-wanda ya samu kud'i ta hanyar haram ya kashesu ta hanyar halak shima wuta zaije,
3-wanda ya samu kud'i ta hanyar halak ya kashesu ta hanyar halak shi kad'ai ne zai shiga aljanna kuma kafin ya shiga aljanna sai fa sunyi shekara hamsin ana musu tambayoyi mommy shin kud'in nan da kike tarawa kin samu ne ta hanyar halak?ta hanyar halak kike kashesu? Wannan sune tambayoyin da malamin mu yace na miki"

Kuka sosai Jalila take ikram ta tsaya kawai tana kallonta itama idonta cike da hawaye.

"Dama na dad'e ina fad'a miki mu rabu da ikram yanzu duk abinda kike mata bata gode ba"

Da sauri Jalila ta kalli kan gado wanda deejah ce kwance tana maganar cikin jin jiki.

Kukan Jalila ya fito fili sosai take yi saboda hakan ne kad'ai zai saka zuciyarta tayi sanyi.






_Sadeey S Adam_
[9/29, 9:21 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_

*_Dis page goes 2 Sa'adat Salis Musa(ummi),tnx 4 d luv,care & Support❤_*

_Safnah dear Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne_🙏🏻



_*~«Episode 11»~*_


Tashi tayi taje jikin gadon da deejah take kwance ta kalleta "deejah har yanzu lokaci bai k'ure ba kina da damar da zaki sama mata tarbiyya ta gari"

Wani bak'in ciki ne ya d'arsu a ran deejah,duk da tana jin zafin ciwo amma bai hanata mik'ewa zaune ba.
"Jalila har yanzu kina nan akan bakarki?"

Bata ce komai ba sai hawayen da suka kasa daina zuba a fuskarta.
"Karki ga ko dan ina gadon asibiti ne amma wallahi babu abinda bazan iya aikatawa ba"

"A'a kiyi hak'uri zanyi abinda kika ce dan ni yanzu gaba d'aya ikram ta karya min zuciya,zanje office d'in Mujahid gobe dan in sanar dashi sak'on ki sannan zan bar miki gidan da komai nayi regretting abubuwan dana aikata a rayuwa ta iyayena basu yi min adalci ba da suka haifeni a shegiya,amma ina son ki sani dan Allah kada ki sake nemana kada ki sake nuna kin sanni in har bazaki shiryu ba zan gyara rayuwata saboda in inganta rayuwar ikram"

Murmushin jindad'i deejah tayi tare da fad'in "naji dad'in haka ni da son samu ne da har duniya ta nad'e kada na sake ganin ki keda ikram bani son ganinku a rayuwata"

"Bazaki gammu ba ki kwantar da hankalinki"
"Ki tabbatar kin shawo kan Mujahid ni yanzu na fasa soyayya dashi naga wani guy d'in, amma ya bani kud'in da zan d'auki nauyin cikin jikina har na haife shi"

"Karki damu domin ni yanzu na tsani mujahid dan ina ganin kamar shine silar k'ara lalacewarki deejah"

Daidai lokacin doctor ya shigo,wani kallon tsana Jalila ta watsa masa sannan ta kauda kai.

"A'a patient ya na ganki a zaune kina surutu?"

A hankali ta kwanta tana wash yana mata sannu tare da satar kallon Jalila.

Bayan ya sake duba ta sannan yayi rubutu a file ya kuma kalli Jalila yace ta biyo shi office.
"Office kuma me zan yi?"
Ikram tayi saurin dawowa gaban Jalila tare da rik'eta.

"Zanyi maki bayanin sauran magungunan"
"Kayi shi anan mana daga ni sai ikram sai deejah fa"
"Maganar ba ta nan bace"
"To bana son ji ka rik'e maganarka kawai"
"Jalila" ya fad'i sunanta cike da mamaki.
"Dakata mubarak dan Allah ka rabu dani kawai patient muka kawo kayi abinda ya dace ka gane ko"

"Kanki d'aya kuwa?"
"Lafiya ta k'alau idan baka fita a d'akin nan ba zan nuna maka ni cikakkiyar 'yar bariki ce ka fice nace"

"Mommy nima bana son ganinshi na tsane shi"
"Bashi kad'ai ba har da halinsa zaki tsana ikram"

Ganin suna neman yi masa tozarta yasa ya fita tare da d'aukar alwashin sai ya wulak'anta tunda ta lasa masa zuma sannan ta guje shi.


*************

Washe gari bayan ta shirya ikram ta tafi makaranta,itama ta shirya ta d'auki abincin asibiti ta tafi.

'Yan gidan kansu sunyi mamakin ganin yadda Jalila tayi sanyi amma sai suke tunanin ko abinda tayi wa deejah ne ke damunta.

Tana shiga d'akin ta tarar deejah bata nan,amma ga takarda ta ajje mata a kan gadon.
Jikinta a sanyaye ta d'auki takardar ta fara karantawa kamar haka.

_Assalamu Alaikum Jalila kamar yadda kike so daga yau bazaki sake ganina ba domin naga alamar ke d'in taurin kai ne dake na lura da ko baki fad'awa ikram ni ce mahaifiyarta ba yanzu na san dole ki gaya mata wata rana,ina son yau na fad'a miki sirrin b'oye,mujahid d'in da na fad'a miki ina son shi shine mahaifin ikram kuma tsohon mijina ne sannan shine yayi min wannan cikin na jikina bayan ya dawo aiki garin nan muka had'u ya bani hak'uri a b'oye na bashi kaina yayi min ciki sannan yake neman guduna,Jalila ina son ki daidaita komai Mujahid ya dawo gareni zan dawo idan hakan ta kasance wata d'aya na baki karki sha wahalar nemana zan dawo da kaina yanzun ma saurayinki doctor Mubarak shine ya canza min asibiti saboda ina ganin ikram bazan warke da wuri ba,dan Allah kada ki fad'awa ikram nice mahaifiyarta domin na sallamawa duniya ita_.
_Na barki lafiya.......sak'o daga deejah_.


"Meyasa kika yi min haka deejah?kin cuci ikram dama ashe Mujahid d'in da kike fad'a shine mahaifin ikram?ayau kuwa zanje na dank'a masa ita" ta fad'a tana share hawaye".

~~~~~~~~


Tana tsaye a bakin gate d'in tana nazarin maganganun da zata fad'a masa tare da addu'ar Allah yasa kada da had'u da director.

A k'ofar office d'in Secretary ya tsayar da ita ya hanata shiga saboda tsoron abinda zaije ya dawo.

"Hajiya bazaki shiga ba saboda kwanaki haka wata tazo tayi mana hayaniya"

"Malam ko kaso ka baka so ba wallahi sai na shiga"
"Sai ki shiga in gani dan na san halinki d'aya da waccan mara d'a'ar"
"Ka fad'i duk abinda zaka fad'i amma wallahi sai naga Mujahid kaji na rantse" da sauri ta nufi k'ofar zata bud'e yayi saurin tare ta.
Hannu tasa ta hankad'e shi yayi gefe ita kuma da sauri bud'e k'ofar ta shige.

Ganin mutum ya shigo kai tsaye yasa Mujahid yayi saurin cire wayar dake kunnenshi.

Uzairu ne ya shigo a fusace ya kalleta tare da fad'in "fita kafin na miki abinda bazaki manta dani ba"

Juyowa tayi ta kalleshi ranta a b'ace tace "k'arya kake matsiyaci nafi k'arfin haka wallahi"

Hannu ya d'aga zai mareta tayi saurin rik'ewa "karya kake ni da deejah ba d'aya bane ni nafi k'arfin ka mareni"

"Wai me yake faruwa ne Uzairu?ya zaku shigo kuyi ta fad'a a office d'ina"

"Yallab'a wai dole sai tayi magana da kai ni kuma bana son a kwatanta irin na ranar nan dan kana ganinta kasan da rashin mutunci tazo nan"

Juyowa tayi ta kalleshi tare da fad'in "yarinyar da ka bari shekara biyar tana zaman gidan karuwai ita n........................." da sauri ya tsayar da ita tare da fad'in "dakata malama dalla bana son shirmen nan dan haka ki b'ace min da gani"

"Mujahid! Oh yadda deejah tayi abandoning d'inta haka kaima kake son yi?ko dai ba a hanyar halak kuka sameta ba,ko deejah k'arya tayi min ,Mujahid ka d'auki 'yar ka tun kafin ta lalace"

"Ke dallah malama na gaji da jin shirmenki"

Uzairu dake gefe wanda tunda Jalila ta fara magana ya sandare a tsaye ya kasa cewa komai sai a lokacin yace "yallab'ai ayi abinnan cikin sirri tun kafin ta tara mana jama'a"

"Koma me zaka ce dole na kawo ikram ka cigaba da rik'onta,saboda ni karuwa ce rik'onta a gurina akwai had'ari domin za'a rink'a goranta mata"
"Uzairu ka yarda da abinda take fad'a kenan?"
"Na yarda yallab'ai saboda daga jin maganar kasan gaskiya take fad'a saboda bama 'yarta bace bare nace sharri ne ni dai kawai bana son ayi abinnan ba'a sirri ba"

Kallon Jalila yayi wanda itama shi take yiwa kallon tsana.

"Kiji tsoron Allah! Taya ina zaman lafiya kina neman tarwatsa min"
"Kaga Mujahid bana son dogon zance nazo ne inji zakazo ka d'auki ikram ko kuma na kaima ita har gidanka" ranta a b'ace ta fita tana zubda hawaye.

"Wallahi uzairu k'arya take min karta lalata min aure ina zaman lafiya da mamata"
"Allah kiyaye ma komai zai daidaita insha Allah"
"Kana jin abinda take fad'a gashi ta fita kuma kaima ka yarda da abinda ta fad'a"

"Bara naje na tsayar da ita" da sauri ya fita,Mujahid kuwa ya tsaya cak ya kasa ko zama.





_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:21 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa°~°~°~_


*_~«Episode 12»~_*

A farfajiyar wurin ya tsayar da ita.
"Baiwar Allah ki tsaya muyi magana ta fahimta"

Juyowa tayi ta kalleshi "wace magana babu abinda zan tsaya na saurara"
"Karki yi masa haka karki aikata abinda zai jawo matsala a family d'in bawan Allah nan"
"Kasan Allah ka daina b'ata lokacin ka kawai ka
zauna kayi aikinka dan shi yafi maka"

Da sauri ta fice ta barshi anan tsaye,a sanyaye ya koma ya fad'awa Mujahid abinda ya faru.

Ranar kuwa ya shiga tashin hankali dan kasa zaman office yayi ya tafi gida.

~~~~~~~

Tana ta shirya kayan ikram a trolley yayinda ikram ke gefenta tana cin abinci.

Bayan ta gama shirya kayan tsaf ta kalli ikram tace "yau babu islamiyya ikram"
"Mommy akwai"
"Ba zakije ba"
"Mommy meyasa?"
"Yau zan kaiki gurin daddynki ko baki so?"

Tashi tayi ta doka tsalle tare da rungume jalila "mommy yau zanga daddyna ki tashi mu tafi yanzu"
"Ki gama cin abinci ki canza kaya"
"Mommy na k'oshi"
"Aikuwa bazan kai ki ba idan har baki cinye abincin dake gabanki ba"

Da sauri haka ta rik'a loma saboda kawai ta cinye a kaita gidan daddynta.

A k'ofar tangamemen gate d'in mai napep yayi parking jalila ta sallameshi sannan suka k'arasa jikin gate d'in tayi knocking.
Maigadi ya fito ta k'aramar k'ofa suka gaisa sannan tace "dan Allah ko nan ne gidan Mujahid?"
"K'warai kuwa nan ne lafiya?"
"Eh bak'ine mu"
"Yace kar na bar duk wanda ban sani ba ya shiga amma naga kamar ku daga wani garin kuke tunda har da akwati"
"Gurin matar shi mukazo ai ko bata nan?"
"Tana nan ku shiga bismilla"

Shi yayi masu jagora har cikin falon gidan.
"Hajiya bak'i ne kukayi"

Lailah ta juyo ta kalli Jalila da ikram tace "a'a bismilla ku shigo mana" ta fad'a cikin sakin fuska.

Maigadi ya juya ya fita yayinda Jalila da ikram suka zauna.

Bayan sun gaisa taje ta kawo masu ruwa da lemo ta ajje sannan tace
"Amma ban gane ki ba?"

Shiru na wani d'an lokaci tayi sannan tace "sunana Jalila wannan kuma ikram ce,kece matar Mujahid?"

"Eh nice ga yaranmu can a waje suna karatu"
"Allah sarki" Jalila ta fad'a tana kallon k'asa.

"Ya kika yi shiru kuma?"
'Dago kai tayi ta kalli ikram tace "ikram jeki waje kinji amma karki fita can k'ofar gida"
"To mommy ina daddyna?"
"Kije ki zan kaiki wurinshi yanzu kinji"
Kai ta d'aga sannan ta tashi ta fita.

Jalila ta juyo da kallonta ga Lailah tace "kema uwa ce saboda kin haifa kuma kin san zafin haihuwa shin ya zakiji idan rana d'aya uban 'ya'yanki ya guje 'ya'yanki yace ya bar miki karki k'ara cewa shine ubansu ya zakiji dan Allah ki bani amsa"

"Gaskiya bazan ji dad'i ba dan idan ta kama ma zan iya kai shi k'ara"

"Ina son ki duba wannan abin ki saurari labarin ikram"
"Wace ikram?"
"Yarinyar da nazo da ita"
"Okay inajinki"

"Ikram ta taso a gidan karuwai,domin tun tana shekara d'aya mamanta tazo da ita gidan,ganin yadda babanta yayi abandoning d'in ta shiyasa itama tayi abandoning d'inta,nina rik'eta tsowon shekara biyar na bata tarbiyya bakin iyawa ta duk da nima a barikin nake amma ban bari rayuwarta ta lalace ba,nayi nayi mamanta ta mayar da ita ga danginsu amma tace na bata ikram ta yarda kawai ni kuma nace a'a zan rik'eta,a haka ta girma ba tare da ta san wace mahaifiyarta ba dan tana kiranta da Aunty ni kuma ni takewa kallo a matsayin mamanta domin sanadin mahaifin ikram ya jawo mamanta ta zama shahararriyar 'yar bariki,kwasam ta samu ciki ta sanar dani tana son wanda yayi mata cikin ya cigaba da rayuwa da ita koda bai aureta ba,in tak'aice miki jiya ta sanar dani wanda yayi mata cikin shine mahaifin ikram,ni kuma nayi alk'awarin zan kai masa ikram ya cigaba da kula da ita koda bazai mayar da mamanta ba,saboda har an fara mata gori bayan ita ba shegiya bace kamar ni"

"Waye wannan mara tausayin,taya zai watsar da 'yarshi ta cikinshi kuma 'yar halak bayan ni'imace Allah yayi masa wasu ma nema suke basu samu ba"

"Hakane shiyasa yau nazo sadata da mahaifinta Mujahid"

Tsaye cak ta mik'e ta kalli Jalila "wane Mujahid?"
"Mujahid mijinki dan ni nan akace min gidan shi"

Girgiza kai tayi tace "bazan gaskata hakan ba mijina bai tab'a auren wata kafin ni ko bayan ni

Please Login or Register in order to submit comment