Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sannan mijina ba d'an iska bane"

Itama Jalila tashi tayi tsaye ta kalleta tace "kiyi hak'uri nayi tunanin nan ne gidan Mujahid saboda naje har office d'insa na A.S motors ya wulak'anta ni shine akayi min kwatancen nan ne gidanshi amma kiyi hak'uri wallahi nayi tunanin nan ne maybe ba'a kwatanta min daidai ba gashi sunansu d'aya" da sauri ta nufi hanyar fita Lailah tayi saurin cewa "dakata"

Tsayawa tayi tare da juyowa,hawayene ke zuba daga fuskar Lailah a hankali ta tako zuwa inda Jalila ke tsaye.
"Da gaske wannan yarinyar 'yar Mujahid ce kuma 'yar sunnah kina nufin sai daya auri mahaifiyarta sannan aka sameta?"

Itama cikin kuka tace "wallahi shine mahaifinta ba zan tab'a yi masa k'arya ba,hasalima ban san shi ba sai ranar da naje office d'insa akan maganar ikram saboda deejah bata tab'a fad'amin wanene mahaifin ikram ba kusan kullum sai munyi fad'a akan sanin hakan sai jiya na samu ta fad'a"

"Yanzu ina mamanta?"
"Ban sani ba ta gudu ta barni da ikram tace zata dawo duk lokacin da Mujahid ya karb'eta dan bazata iya bariki da yarinya ba saboda zata iya karya mata zuciya"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un meyasa Mujahid yayi haka?meyasa ya tarwatsa farin cikin wasu bayan shi yana cikin farin ciki"

Bata ce komai ba kawai hannu tasa tana goge hawayen idanunta.

"Bara ina zuwa Mujahid na nan bara na kirashi ki dawo ki zauna please"

Dawowa tayi ta zauna ita kuma Laila ta shige bedroom.

A kwance ta same shi ya k'ura ma silin ido,a daidai kanshi ta tsaya ba tare da tace komai ba.

Kanshi ya d'ago ya kalleta da sauri ya tashi zaune.
"Lafiya baby?mene kike kuka?"

Sautin kukanta ya fara fita ta kalleshi tace "Mujahid ka cucemu nida yaranka,dama ashe kana da 'ya baka tab'a fad'a min ba kuma bayan nan har wani cikin gareka na sheg..................."
Da sauri ya dakatar da ita tare da fad'in "dama ashe za'a iya zuga ki a kaina ki yarda?"
"Dole na yarda saboda dama kwana biyu ka canza min kullum kana d'aki kana tunani ashe asirinka ne ke shirin tonuwa,to ga 'yarka can a falo kaje ka karb'eta ni kuma wallahi saika sake ni yau d'in nan"
Juyawa tayi zata tafi ya rik'o hannunta.

Tana hawaye ta kalli idonshi tare da fad'in "ka sake ni Mujahid"
"Karki yarda baby wallahi sharri ne"

Kallon shi kawai take ba tare da ta sake cewa komai ba.






_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:21 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_



_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa°~°~°~_


_2 u my fellow readers kasancewar kwana✌🏿banyi maku posting ba,abubuwane gaba d'aya suka had'u suka cushe guri guda uzururruka sun min yawa so sai kunyi hak'uri fa._

*_Safnah Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne,ya kuma................ba sai na fad'a ba ku dai amsa da Amin🙏🏻_*

_Wanda suke bibiyar novels d'ina ina ganin comments d'inku kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci_


_*Namecy(Mrs Xerks) nagode sosai da kika d'auki first novel d'inki kika sadaukar mini,gaskiya nayi farin jiki sosai ganin yadda kike son SaNaz kike ji dani nima ina sonki sis,godia mara adadi ke masoyiyace ta gaskiya...bani mantawa da duk masoyannan nawa nagode matuk'a*_



_*~«Episode 13»~*_

Da sauri ta fita falo ya bi bayanta.

Numfashinsa kusan d'aukewa yayi lokacin daya ga jalila a tsaye.

"Meya kawo ki gidana?" Ya fad'a cikin tsawa.

"Ka santa kenan?zargina ya tabbata a kanka" Laila ta fad'a ranta a b'ace.

Juyowa yayi cikin tsawa yace "baby kika sake magana ranki zaifi nata b'aci"

Kan kujera ta fad'a ta cigaba da kuka.

Ya juyar da kallonshi gurin Jalila "ki fita daga gidana yanzun nan kafin na wulak'anta ki"

"Dama ai zan fita me zai kawo in zauna a gidannan yanzun ma nazo kawo maka 'yarka tunda nayi maka ta lallami har office d'inka nace kaje ka karb'eta kak'i to gata nan har gida na kawo ta domin bazan barta ta cigaba da zama gidan karuwai ba bayan b......................"

"Malama dan Allah karki raina min hankali okay iskancin naku kaina ya dawo?idan ma kud'i kuke nema ko sharri kuke son yi min bazaku tab'a cin nasara ba,wallahi bazan karb'i 'yar da ba tawa ba,ina na sanku?kawai dan neman masifa shine zaku zo muna zaman lafiya ku nemi d'aga mana hankali"

Zuciyarta ta fara karaya cikin sanyin murya tace "karka k'i karb'arta Mujahid,abinda kayiwa mahaifiyarta shi ya jawo ta tsaneta tayi abandoning d'inta kaima kuma gashi kana son yi?dan Allah ku tausayawa ikram"

"Ki fita a gidan nan na gaji dajin mugayen kalamanki,bani da wasu 'ya'ya da ya wuce chuchu da fad'ima domin laila ce kad'ai matata ban tab'a yin aure kafin ita ko bayan ita ba"

A dai dai lokacin su uku suka shigo da gudu.

Ganin halin da iyayensu ke ciki yasa ko wanne yayi gurin nashi.

Ikram ta rungume Jalila tace "mommy kizo ki kaini wurin daddy na"

Da hannu ta nuna Mujahid tace "ga daddynki nan ikram"

Da gudu ta ruga zata rungumeshi yayi saurin hankad'eta aikuwa ta fad'i ta bugu da tiles.

"Kada ku sake tunkarata" ya fad'a a fad'ace.

Juya kai ikram ta fara yi idanunta a rufe,da sauri Jalila ta k'arasa gare ta ta tallabota tana jijjigata.

Laila ce ta taso da sauri tace "Allah yasa dai bata ji ciwo ba?"

Cikin kuka jalila tace "babu amma dai ta bugu"

"So kake ka kasheta saboda asirinka ya tonu,to wallahi sai ka sakeni" Da gudu ta tashi tayi bedroom su chuchu suka bita.

Jalila ta sab'i ikram a baya sannan ta koyata da veil d'inta ta yafa headtie d'in kasancewar babba ne.

Kallon mujahid tayi sannan tace "bazaka sake ganinmu ba zan rik'e ikram a gurina zan daina k'azantacciyar rayuwar da nake domin in inganta rayuwarta amma ka sani ko wata rana kada ka dawo kace na baka ikram daga kai har deejah"

Da sauri ta ja trolley ta fita tana goge hawaye.

Sai da taje asibiti akayi treating ikram ta tabbatar ta dawo dai-dai sannan suka wuce gida.

~~~~~~~

Tana kwance akan gado hawaye ne ke zuba ta gefe idanunta ta kan saka hannu ta goge yayinda zuciyarta ke k'ara yi mata rad'ad'i.

Jin an turo k'ofa ne ya saka tayi saurin juyowa,ganin ikram ba k'aramin d'aga mata hankali ya sake yi ba.

Da sauri ta sunkuyar da kai tana goge hawaye dan kada ikram ta gane.

Hawa kan gadon tayi ta jingina kanta a jikin jalila tace "Mommy daddyna baya sona ko?"

Wasu hawayenne suka taru a idon jalila tayi k'ok'arin b'oyewa sannan tace "a'a ikram daddynki yana sonki sosai"

"Amma mommy meyasa ya dokeni?"
"Ba dukanki yayi ba karki damu ikram yau zamu bar gidannan mu koma wani gidan wanda babu hayaniya"

Dariya ikram tayi sannan tace "mommy daddyna ma zai dawo gidan?"

"Zai dawo amma ba yanzu ba"
"Sai yaushe mommy?"
"Sai ya gama aikin da yake"
"Mommy mu tafi to"
"Eh zamuje amma sai kin fara rakani unguwa"

Tashi tayi ta sake shirya masu kaya a trolley sannan suka tafi.

Hatta 'yan gidan karuwan suna mamakin yadda Jalila tayi sanyi amma sai suka danganta abin da abinda tayiwa Deejah.


~~~~~~~~~~~

Tana zaune a tsakiyar gado ta zuba uban tagumi tana hawaye Mujahid ya turo k'ofar ya shigo.

Da sauri ta duro daga kan gadon tana neman ta fita yayi saurin cewa.

"Ya kamata ki saurareni baby,yau kwana biyu kenan baki kulani ko abinci sai dai ki ajje kan dinning idan naga dama inci ko?bai kamata ace kema kin yarda da k'azafinnan ba ya kamata kiyi tunani domin kin san halina kinsan abinda zan iya da wanda bazan iyaba"

"Babu abinda na sani mujahid,ka rik'e maganganunka har sai Mameey tazo"

"Oh yanzu har ya kai baza muyi abinmu mu biyu mu binne ba har sai kin fad'a a gidanku?"

"Abin yafi k'arfin na rik'e dan wallahi ayau sai na bar gidan nan,ai ba Mameey kad'ai ba har ummimi(mamanshi) na fad'awa kuma itama zata zo"

"Ummimi?"

"K'warai ma kuwa"

Tsaki taja kawai ta fita ta barshi a nan tsaye.





_Sadeey S Adam_💅
[9/29, 9:21 AM] Kawata: °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
*JALILA...*
_'yar bariki ce_
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_(Short Story)_
_*by SaNaz deeyah*_


_°~°~°~dedicated to Anty Maijidda Musa~°~°~°_



_*~«Episode 14»~*_

Ummimi bata zo ba amma Mameey tazo ita da Aunty Sarah suka zo suka had'a mata kayanta dana su chuchu,Mujahid kuwa yana zaune a falo gaisuwa ma da k'yar suka amsa masa dan haka bai ce masu komai ba har suka fito janye da trolley,Aunty Sarah ce tace "zaka iya biyota da takardar saki daga baya".

Kallo kawai ya bisu dashi har zata fita yayi saurin ce mata "ba dasu chuchu kikazo gidan nan ba dan haka ki bar min 'ya'yana"

"Ba zan tab'a barin yarana a gidan nan ba ka koya musu mummunar ak'idar ka dole na tafi dasu domin nima ina da iko dasu"

"Aikuwa dole su chuchu su zauna a gidan nan dan bazan yarda su bi ki ba tunda har baki yarda dani mijinki ba kuma uban 'ya'yanki"

Bata sake cewa komai ba kawai ta wuce ta tafi.




Da yamma ya shirya ya tafi gidansu,ranshi a cunkushe ya gaida Ummimi dama Abba ma yana gidan dan haka tare ya basu labarin duk kanin abinda ya faru.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,wannan wace irin masifa ce,ni lailah ta kirani ta fad'a min amma banyi tunanin abin ya kai haka ba"

"To kai Mujahid ya akai haka ta faru?taya zaka yarda har mace ta shigo maka office,hakan ne ya bata damar binka har gidanka"

"Kuma daddy wai tana son lik'a min yarinya a matsayin ni ne ubanta,wai na auri mamanta sannan na rabu da ita na auri lailah"

"Ni yaya ka fad'a min ina ne gidan su yarinyar naje na sameta" Maryam k'anwarshi tayi maganar.

"Ai kina jin wannan kin san karuwa ce ke kuwa meyayi miki zafi kije gidan karuwai"

"Ummimi wallahi na rasa mafita lailah ta kasa fahimta ta"

"Dama bazata fahimceka ba dan ko waye azo har gida a fad'a masa wannan maganar tabbas akwai matsala,amma ka kwantar da hankalinka anjima zanje na samu mahaifinta"

Maryam ranta a b'ace tace "kaji yarinya da sharri to wallahi kanta zai koma"

Haka sukayi ta al'ajabin maganar sai gab da magrib yayi musu sallama ya tafi.

Gidansu Bashir ya nufa,a tsakar gida ya tarar dasu suna ta gyaran kayan miya.

Ya gaida Mama bilki sannan su Samira da Surayya suka gaida shi.

"Mama ya maganar bashir ya dawo gida kuwa?"

Hawaye ta goge sannan tace "yazo wancan satin yace min kun had'u ma har yayi maka k'aryar cewa a hotel d'in da kuka had'u yake aiki to tun da nayi masa fad'a akan k'arya da kuma yawon da yake sai yaji haushi ya fita tun ranar har yau bai sake dawowa ba"

Mujahid yayi murmushi yace "wallahi a lokacin na kirashi nace ya jirani na fito daga meeting ina fitowa na neme shi na rasa"

"Wallahi yaya Mujahid kayi a hankalin dan cewa yayi wai zaiyi kud'i da kai" Surayya tayi maganar.

"Kud'i dani kuma kamarya?"

Samira tayi saurin cewa "yaya wai zai samo budurwa ta lik'e maka ba tare daka sani ba zasu ci kud'inka ita dashi shine mama tayi ta masa fad'a har tace idan yayi bata yafe ba"

"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,aikuwa bashir ya aikata hakan dan yanzu har matata tayi yaji sanadin haka"

"Kana nufin yayi abinda yace zaiyi?"
Mama ta tambaya.

Labari ya bata na duk abinda ya faru.

Salati suka hau yi Surayya tace "muma cewa yayi wai wallahi yana garin nan baza'ayi engage d'inmu ni da Samira ba Mama tace Allah yafi k'arfin shi,gashi gobe za'ayi insha Allah"

"Aikuwa dole ka tashi muje ayiwa hajiya magana idan yaso sai muje gidansu ita Lailah ayi musu bayani"

"A'a mama ki k'yalesu kawai aini a tunanina idan aka cewa Lailah nayi wani abin bazata yarda ba amma sai gashi cikin k'ank'anin lokaci ta yarda nina aikata abinda ko a mafarki bana fatan aikatawa"

"To Allah kiyaye gaba amma idan abin yayi tsanani dole inje da kaina gidansu"

"Komai zai daidaita insha Allah yanzu yaushe aka saka ranar bikin su Surayya"

"Sai anyi baikon sannan za'a sa rana"
"To Allah ya kaimu na d'auki nauyin yi musu kayan d'aki idan yaso ku sai kuji da gara"


Mama kuwa har da kuka,su Surayya da Samira kuwa murna suke tayi.


°°°°°°°°°°°°°°°°

"Yanzu da kikazo kika saka ni a gaba kina min kuka titsiyeni kike son yi ko kuma dukana?"

Jalila ta kalli Magajiya idonta sharkaf da hawaye tace "dan Allah ki sanar dani garin mahaifiyata na tafi na tuba na daina bariki ki fad'a min dan Allah ki fad'a min *ASALINA*(Xee yabour nvl)"

"Ni ban san asalinki ba saboda mahaifiyarki bata fad'a min ba,kuma watanki uku a duniya ta rasu shiyasa na tausaya miki na rik'eki"

"Amma bata tab'a fad'a miki ko da inda mahaifina yake ba?"

"Ke Jalila ki kiyayeni ni dai ban san komai game dake ba hasalima ke shegiya ce mahaifiyarki bazata tantance waye ya mata ciki ba dan lokacin da tayi bariki kamar akuwa take kowa bi take,kuma ko da ta samu cikinki babu uba dan haka ke shegiya ce"

Kuka ta sake rushewa dashi Ikram na jingine da jikinta tana hawaye itama.

"Amma na tabbatar ko baki san inda mahaifiyata take ba kin san garinsu"

Mik'ewa tsaye tayi tare da fad'in "ke yarinya ban tab'a ganin inda alkhairi ya zama sharri ba in taimakeki in rik'eki amma kina neman watsa min k'asa a ido to ki tashi ki tafi *BAN SAN ASALINKI BA*(novel mai zuwa nan gaba)kuma a bariki zaki mutu ko kina so ko bakya so dole ki dawo ruwa"

Tura su ta rik'a yi har ta fitar dasu daga gidan.

A k'ofar gidan Jalila ta zube tana kuka,ikram ta matso kusa da ita tace "Mommy meyasa kike kuka meyasa muka zo gidan magajiya bayan kin san bazata fad'a miki gaskiya ba"

Janyo ikram tayi tana kuka ta rungumeta.

"Allah ne gatanmu kuma kece gatana ikram,kece komai nawa,dangina da komai na dan Allah karki gujeni ko anan gaba, *A SANADIN SONKI*(My Aunty nvl) na daina gurb'atacciyar rayuwa,zan rayu dake kad'ai ikram nima ki kasance tare dani karki kujeni kinji"

'Dago kai tayi tana goge ma Jalila hawaye tare da fad'in "ina sonki mommy ina tare dake".








_Sadeey S Adam_💅



[6/18, 4:19 PM] SaNaz deeyah: 🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*JALILA*
_'Yar bariki ce_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



_°°dedicated 2 Anty Maijidda Musa°°_



*_~«Episode15»~_*

Tashi tayi taja jakarta ta kuma ja hannun ikram,zuciyarta kawai ta bata shawarar ta nufi tasha ta bar garin kawai.

_Abuja_ ta furta a ranta sannan ta d'anyi dariya ta gefen leb'e a zuciyarta tace _Abuja ne kawai zanje inyi rayuwata a sirrance ba kowane zai san inda nake ba garine da babu hayaniya ba takura_

Kai tsaye ta nufi tasha ta hau mota.

Lokaci guda motar ta tashi addu'a sosai tayi sannan ta kwanto Ikram kan ciyarta,wasu hawayene suka kasa b'oyuwa suka zubo gefen kunnen Ikram,da sauri Ikram ta d'ago ta kalli Jalila murmushi tayi tare da goge guntun hawayen.

Sunsha tafiya daga Kano zuwa Abuja dan Ikram ma bacci tai tayi abinta.

~~~~~~~~~

Falon cike yake da Iyayen nasu biyu,Abba,Abi,Ummimi da Mameey.

Mujahid da Lailah suna k'asa nesa da juna.

Kowa yayi shiru muryar Abi ce kawai ke fita yana fad'in "wannan magana ce da ta d'aurewa kowa kai duk da na san halin Mujahid baya da wani aibu amma a wannan gab'ar bazan shaidar zur ba Mujahid ka fad'i tsakaninka da Allah shin abinda wannan yarinyar ta fad'a gaskiya ne?"

A tsorace ya kalli Abi yace "wallahi Abi yarinyar nan ba 'yata bace ban sansu ba dukkansu kawai dai sharrin Bashir ne"

"Ba wani Bashir wallahi Abi 'yar sa ce kuma har gida tazo fa ta kawota shine yayi abinda har suka tafi da tuni ta ajjeta ma"

'Karar wayar Abba ce ta saka su yin shiru d'auka yayi ya amsa kiran duk hankalinsu a kanshi "to shikenan babu damuwa a cigaba da bincike har Allah ya saka a ganta"

Katse wayar yayi ya kallesu yace "har yanzu dai an kasa samun yarinyar da ace an ganta da tuni komai ya wuce dan da anyi DNA shikenan za'a gano gaskiya tunda k'wayar halitta bata canzawa"

"Ni dai kawai ya sakar min 'yata dan bazan tab'a yarda 'yata ta zauna da mazinaci ba" Mameey tayi maganar rai a b'ace

"Mairo wai meyasa kike irin haka ne?Laila da yaranta dole su koma bazan lamunci yaji a gidana ba kuma bazan yanke hukunci akan abinda bani da tabbas a kansa ba"

Cikin kuka Laila tace "Abba ni wlh bazan yarda na koma wannan gidan ba dan bazan yarda ya gurb'ata rayuwar 'ya'yana"

"Keee! Ki kiyayeni wallahi zan b'ata miki rai"

Kallon Mujahid yayi yace "ka d'auki matarka ku tafi har zuwa lokacin da zamu samo yarinyar"

"To Abba nagode".

°°°°°°°°°°°°°°°

Ajiyar zuciya Jalila tayi sannan ta k'ara kallon garin
" Ikram kina son zama a garin nan?"

Murmushi tayi mai bayyanar da hawaye tace "eh mommy"

"Zamu zauna anan mu cigaba da rayuwa ba tare da wani ya takuraki ko ya dokeki"

"Mommy kin daina shaye-shaye kema,saboda idan kinayi kawayena zagina suke"

Kallonta tayi yadda taji tambayar kamar a mafarki.

"Ikram na daina kinji kema ki daina min wannan maganar kinji"

Ta gyad'a kai alamar to.

Satinsu biyu a hotel kafin ta samu gidan haya wanda yayi tsada sosai expensive life ake a garin komai tsada ne dashi.

Wani babban Estate ne mai d'auke da 15 buildings duk sama da k'asa ne.
Inda suke haya a saman ne,1 palor two bedrooms 1 toilet 1 kitchen babu tsakar gida kuma gidan 1.5m ne each year.

Zaune suke tsakar parlor da babu komai sai tiles ta kalli gidan a zuciyarta tace _ya zanyi yanzu?dole in sayi kayan d'aki in maida Ikram makaranta ga abincin da zamu ci uwa uba kuma kud'in haya duk shekara 1&half million,dole ne in san abinyi._

Wayarta ta d'akko ta lissafa kudin da suka rage mata duk ba zai mata abubuwan da suke buk'ata.

Fita sukayi neman abincin da zasuci dan haka kai tsaye suka nufi restaurant na kusa da unguwar.

Zama tayi tare da karb'ar Menu ta zab'i abincin da zasu ci sai lemo da ruwa.

Kawo musu akayi kamar yadda suka buk'ata,bata tsaya taci da yawa ba saboda gaba d'aya tunani ya mata yawa.

Ikram kuwa taci abinci sosai,bayan sun gama ne ta kira waiter zata biya kud'in tace "an biya naku ai"

Cike da mamaki Jalila tace "waye?"
"Ya fita yanzu ba dad'ewa"
Da sauri Jalila taja hannun Ikram suka fita ta hangoshi amma lokacin ya riga ya shiga mota dan haka bata gane fuskarshi ba.

"Hajiya"
Wani dake gefen yayi Mata magana,kallonshi tayi ba tare da tace komai ba,ya mik'a Mata compliment card yace gashi inji Alhaji yace ki nemeshi akwai number wayarsa a jiki"

"Waye shi?" Ta sake tambaya.

"Eh to idan kun had'un zaki sanshi"

Karb'ar compliment card d'in tayi ta kalla ABDULJABBAR YUNUS shine sunan data gani,murmushi tayi kawai ta wuce.
Satinsu biyu a garin taga bazata iya zama haka ba don kuɗinsu duk sun kai gaɓar ƙarewa.

Yau kuwa ta shirya ta cewa Ikram kar ta fita ko ina zata je ta dawo.
Kai tsaye tabi kwatancen dake jikin compliment card ɗin nan taje har guest house ɗin Abduljabbar.

Bata sha wahalar ganinsa ba kasancewar akwai katin shaida a hannunta.

Zaune take a tamfatsetsen parlor ɗin nashi sai ƙarewa parlorn kallo take wani hamshaƙin falo ne.

"ashe dai zakizo ɗin nayi ta saurarenki shiru"
Murmuahi tayi sannan tace "kasan da yake ina da yarinya so ta saka min ido sosai yanzu haka sai da dubara nazo nan"

Shiru ya biyo baya na wasu ƴan lokutan sannan yace "anya tarayya ta dake zata yuwu kuwa?"

"me zai hanata yuwu wa"

"saboda akwai lokacin da nake ƴan tafiye tafiye kuma zan buƙaci ki rakani kinga idan ƴarki na sa miki ido ai babu zancen zuwa kinga baima dace kiyi bariki da yarinya ba"

"karka damu da ita ni nasan yadda zanyi da ita,kawai duk lokacin da kake bukata ta ka kirani a waya ni kuma zanzo in sameka har inda kake"

"yama sunanki?"

"Jalila"

"to Jalila ni dai ina da sharuɗɗan in har kika kiyayesu to zaki zama mai arziƙi ke kanki kuma zaki juya naira yadda kika so"

"mene wannan sharuɗɗan?"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace "na farko bana son kiyi mu'amula da kowa sai ni kaɗai,na biyu bana son yawo duk abinda kike buƙata zan ajje miki idan kina son wani zan turo driver ya kaiki ko kuma inzo in kaiki da kaina,na uku ban son cin amana idan har na fahimci cewa kina yaudarata ne to tabbas zaki shiga matsala tare da dana sanin abinda kika aikata idan kina kiyaye wannan to kin gama yin arziƙi"

"karka damu indai wannan ne baka da matsala dashi"

Dariya yayi yace "nima hakan ne yasa har yanzu na ƙi yin aure bana son sa'ido da kuma ƴaƴa dan haka ki shirya zamuje a juya miki mahaifa"

Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba amma ta daure ta hangi irin rayuwar da suke ciki dan haka tace ta amince.

A cikin satin ya sauya musu gida ya kuma saka musu duk wasu kaya na more rayuwa.

Ita kuma hakan ne yasa tayi amfani da wannan damar takai Ikram boarding skul primary 1.

Haka ta cigaba da rayuwarta Abduljabbar ya zama tamkar mijinta,duk lokacin da ikram zata dawo hutu kuwa bazasu haɗu ba harta koma hakan yasa Ikram bata fahimci rayuwar da Jalilar keyi ba,kuɗi kam babu abinda ikram zata nema ta kasa samu provision kuwa har yawa yake mata,a haka har taje ta SS1 daga nan ne suka koma Kaduna da zama kasancewar Abduljabbar yanzu aikinsa yafi ƙarfi acan dan haka ya sake saya musu wani tamfatsetsen gida a cikin garin Kaduna.





_Sadeey_✍
[6/18, 5:10 PM] SaNaz deeyah: 🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*JALILA...*
_Ƴar bariki ce_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah👄*_



_°°dedicated 2 Anty Maijidda Musa°°_



*_«Episode16»_*

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya,Jalila ta shiga sabuwar rayuwa ta fara mantawa da duk wata damuwa.

******

Cikin iko da yardar Allah Hussaina ta fara karatu a Management dake kano inda ta fara karatu bata wasa dan shine kaɗai jindaɗinta a yanzu.

*_12 years later_*

Haɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Benz blue black ta danna horn a bakin makeken gate ɗin.

Cikin azama maigadi yazo ya buɗe motar ta shigo a hankali ta isa gurin adana motoci.

Buɗe ƙofar akai kyawawan ƙafafunta suka dura a ƙasa,cikin fara'a fito gaba ɗaya daga mota ta rataya skul bag ɗinta sannan ta tsaya tana ƙarewa gidan kallo.

Cikin fara'a take tafiya har ta isa ga babban falon gidan anan taci karo da Jalila tsaye ta ware hannu tana niyyar tarbarta.

Ƙin zuwa tayi gareta kawai ta samu kujera ta zauna tare da zumɓura baki.

"My daughter lafiya ina miki oyoyo kin shareni"
Jalila ta rungumota tace "Am sorry ikram wallahi naso nazo amma mai aikinmu bata nan shiyasa na tsaya haɗa miki abincin da kika fi ƙauna"

"Mommy ke nafi ƙauna ba abinci ba da kinzo wlh ko abinci bazan kalla ba"

"to kiyi hkri it will never happen again yanzu ki muje kiyi wanka sai muzo a fara celebration ko"

Murmushi tayi sannan tace "amma Mommy ya akai muka dawo Katsina nifa nayi zaton zan ganmu a kaduna sai driver yace wai mun dawo nan"

"eh mun dawo nan Allah yasa gidan dai ya miki"

"yayi sosai ma Allah ya ƙara buɗi"

"Ameen".

*********
Gyara zama Jalila tayi tace "Wlh hajia Saude abu biyu zuwa uku su ke damuna a halin yanzu"

"Me kuma zai dameki Hajia Jalila ke ai baki da damuwa kowa kwantance yake dake a cikin ƙawayenmu babu mai kuɗinki fa"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "Ina tsoron ranar da Abduljabar zai gano inda nake yazo ya ƙwace dukiyarsa,abu na biyu ina tsoron kar Jalila ta gane irin abubuwan da nake"

"Abduljabbar bazai taɓa ganoki ba maybe ma ya haƙura dake tuni kuma ai ba satar kuɗinsa kikayi ba wanda yake baki ne kika tara,zai ƙwace ne kawai saboda kin gujeshi yanzu,Ikram kuwa keda zaki turata makaranta ina zata gane halin da kike ciki"

"tace ita yanzu babu inda zata a kusa dani zata zauna tayi karatu dan haka da jamb result ya fito zata sayi green card ta canza skul ta mayar UMYUK"

"Ke dai macece ikram bazata taɓa ganoki ba tunda kinsan kalolin dubarun mata musamman ƴan bariki"

"Ikram daban ce amma zanyi ƙoƙari".

*********

Zaune take a gefensa ta ɗan ɗora kanta a kafaɗarsa,shi kuma yana ta aiki da System ɗinsa.

Murmushi ta ɗanyi tace "My dear kasan me na tuna?"

Mujahid wanda har lokacin idonsa na kan system yace "Sai kin faɗa"

"Na tuno wannan matarne da taso raba auren mu"

Ɗan tsaki yayi ba tare da ya ƙara cewa komai ba.

"Ya kayi shiru ne kace wani abu mana"


Juyowa yayi ya kalleta yace "kinsan me?,bana

Please Login or Register in order to submit comment