Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son ki ƙara min maganar wannan matar,na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba meyasa baki jin magana ne"

"Shikenan bazan ƙara ba kayi haƙuri"

"kullum ai haka kike faɗa" yayi maganar tare da tashi ya ɗauki system ɗinsa ya shiga bedroom

Baki ta taɓe sannan ta gyara zamanta tare da ƙwalama Faɗima kira.

******

Cikin iko da yardar Allah Ikram ta samu gurbin karatu a Katsina State University ɓangaren Human relation.

Rayuwa ce take cikin gata da nutsuwa da kuma kwanciyar hankali,Jalila da kanta ta koya mata driving dan haka ita take driving zuwa skul sai taje gidansu ƙawarta Asiya sannan su wuce,haka in zasu dawo tare suke dawowa.

Yau ma kamar kullum bayan sun fito daga lecture Ikram ta kalli Asiya tace "ke mu tafi cafeteria wallahi yunwa nake ji"

"kedai wallahi kin shiga uku da ci ke ko gajiya bakiyi"

"Ke kin taɓa ganin inda aka ƙi bawa ciki haƙƙinsa"

"amma sai ana ɗan ɗaga ƙafa"

"a'a bana wasa da ulcer"

Dariya ikram tayi sannan tace "Muje"

sun juya zasu tafi kawai taji ance "Ikram Mujahid"

Da sauri ta juyo ta kalli wadda tayi maganar"

Ƙarasawa tayi gurinsu ta dafa kaɗarta tace "Ya kike?"
"lafiya lau" Jalila tayi maganar cikin rashin gane ko wace.

"Na san baki sanni ba,nima dai ban sanki ba sai yanzu naji ana ta faɗin Ikram Mujahid shine nazo in ga wannan takwarar tawa"

Murmushi Ikram tayi tace "Oh sunanki Ikram kema"

"a'a Surname ɗinmu ne ɗaya,ni Sunana Faɗimatu Mujahid"

"Ayya Allah sarki"

"Dan Allah inba damuwa inaso mu zama friends ni dake,kuma mu haɗa daddy's ɗinmu ma"

"Kinjiki kenan shine abinda yasa kika tsayar damu" Asiya tayi maganar tana ɓata rai.

Ikram ta ɗan bugi kafaɗarta tace "To sarkin jin haushi meya a ciki"

"Nifa yunwa nakeji Ikram"

"Bara na karɓi numberki zamuyi magana"

"To na gode Ikram bani wayanki na saka miki"

Miƙa mata wayar tayi ta saka mata number sannan suka juya zasu tafi,Ikram ta sake juyowa tace "Idan tafiya zakiyi kizo mu rage miki hanya mana,amma zamu fara zuwa cafeteria"

Asiya ta ɗan zungureta.

Faɗima tace "a'a ni ina campus ne in ba damuwa muje hostel nayi maku girki"

"a'a ni bazan iya bari har ayi girki ba gaskiya yunwa nakeji"

"karki damu sis akwai abinci ready made saiki fara ci"

Murmushi Ikram tayi tace "karki damu Faɗima zamuzo wata rana muci,mungode"

"To shikenan tunda baza'a ci abincina ba"

"Shikenan muje muci,Asisi sai kiyi haƙuri"

"haba Ikram kawai daga haɗuwarmu yau sai muje har ta mana girki dan shishshigi" Asiya tayi maganar a hankali.

"Ba wani shishshigi sis ai duk mun zama ɗaya" Faɗima ta faɗa.

Dariya sukayi su duka Asiya tace "wannan kunnen maciji ne dake"

Dariya suka sake yi.

Tare suka jera har hostel.

Ɗankin Faɗima ita kaɗaice ya tsaru sosai yayi kyau.

"Kai ke kaɗai ne a ɗakinki nayi tunanin two-two ne each room"

"Eh amma ni nawa ni kaɗai ce Daddyna yace kar a haɗa ni da kowa saboda bayason a takura min yafiso na nutsu nayi karatu,kuma ko da zanzo sai da yayi min gargaɗin kar in yarda in zauna da ƙawar da bata son karatu sannan kar in tara ƙawaye,hakan ya sa ƙawata tunda nazo guda ɗaya ce Manal Umar bayan Manal banda da wata ƙawa kuma itama Manal kinga ba ɗakinmu ɗaya ba ba department ɗinmu ɗaya ba kawai a gurin karatu muka haɗu da ita"

Zaman da Ikram tayi a ɗakin Faɗima ya saka mata sha'awar ina ma itama mahaifinta yana raye yadda taji Faɗima bata da wata magana sai ta mahaifinta"


"Inama nima Mahaifina yana raye,wallahi duk sai naji kewar mahaifina da naji kina ta ambatar naki"

"Ya rasu ne"

"Eh ya rasu tun kafin inzo duniya,Mahaifiyata itace komai nawa ni kaɗai suka haifa"

"Allah sarki Allah yayi masa Rahama"


"Ameen" ta faɗa tare da goge guntun hawayenta.

"amma dai granny ɗinki na matuƙar sonki ko?kinga wallahi kakata bada son ranta na taho karatunnan ba ita cewa tayi duk makarantun kano sai nazo har Katsina gaskiya babu inda zani da ƙyar Daddyna ya lallaɓata"

"Ke nima hakan ta faru dani wallahi da tuni ina Bauchi amma da Mamana da kakata sam suka ɗaga hankulansu su bazasu yarda in yi nesa dasu ba"

_Ikram so nake ki tafi Skyline University ko ki tafi Maryam Abacha._

_Mommy gaskiya bazan yarda in ƙara yin nesa dake ba ni ki barni in cigaba da karatuna a kaduna._
Maganarsu da Mommynta ta tuno tatsaya kawai tana kallon Asiya da Faɗima sai labarin Families suke da yadda suke ƙaunarsu.

Asiya ce ta lura da haka tayi saurin canza maganar da faɗin "Ikram ni kuwa kinyi Assignment ɗinki?"

"Wanne?"

"Na GST mana"

"Eh nayi yana cikin system ɗina ban bayar an fitar min ba"

"To tashi mu tafi gaskiya muje Cafe a fitar sai mu wuce gida"

Jikinta a sanyaye ta miƙe tare da faɗin "Gaskiya bazan iya zuwa Cafe ba gida zan wuce"

Asiya ta lura da yadda Ikram tayi sanyi dan haka itama duk sai taji ba daɗi.

"Mu tafi nima wallahi inada aiki a gida"

Sallama sukama Faɗima tayi musu godiya tare da cewa sai tazo gaida Mommy.

A hanya ma suna tafiya Asiya sai surutu take Ikram taƙi kulata.

"Ikram wai me akayi miki duk kin canza"

Murmushi tayi sannan tace "Ba komai"

Hmm "Sai dai ki faɗawa wani amma ni da nake tare dake na sanki da fara'a lokaci ɗaya yanayinki ya canza kice min ba kom................."

Maganarta ce ta tsaya tare da doka uban salati lokacin da suka kusa kaɗai wata almajira.

Cikin ɓacin rai Ikram ta fito daga motar ta ƙarasa gurin matar ta ɗaga hannu zata zabga mata mari caraf taji an riƙe.

"Kinso kaɗeta kuma kina neman bugunta"

Kallonshi tayi sannan ta fuzge hannunta tace "Ita ɗin batada hankali da zata hawo titi tana tafiya kamar ta samu titin gidansu"

"amma sai ki tausaya mata bakiga yadda take tafiya da ƙyar ba"

"babu tausayinta da zanji irin wannan shahararrun ƴan barikin ne wanda ƙarshensu baya kyau,dalla dubeta ta wani tsareni da ido sai kace mayya to kici kanki da kanki kuma na sake zuwa wucewa kina tafiya yadda kika ga dama saina karkarya ƙafafunki"

"Ikram" Asiya tayi saurin kiran sunanta.

Juyawa tayi ta kalleta rai a ɓace tace "Mene?"

"Haba Ikram ban sanki da faɗa ba kiyi haƙuri mana"

"Asiya ki duba fa ki gani da ace na kaɗai wannan tsohuwar da tuni ina hannun ƴan sanda tana da hankali fa ba mahaukaciya bace"

"To kiyi haƙuri"

Kallon matar tayi wadda har lokacin idonta na kanka,ta taɓe baki tace "kurwata kur idan ma ke mayya ce"

Ta juya ta gallama saurayin harara sannan ta wuce.


Suna shiga ta tada motarta ta wuce.

Har ta ajje Asiya a gida Asiya na ta mata nasiha tana rarrashinta.

Koda tayi parking a parking space fitowa tayi tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki.
Abin duniya duk ya dameta ta tsinci kanta a yanayi mara daɗi.

Tun daga ƙofar falo take jin shewa cikin ɓacin rai ta tura ƙofar ta shiga.

Manyan matane kusan su goma har da Jalilar duk suna zaune kan kujeru sai ɓaɓɓaka dariya suke.

"a'a My baby kin dawo"
Wata ƙawar Jalilar ta faɗa.

Yayinda da Jalila ta taso da sauri tana faɗin "Har kun gama luctures ɗin?"

Kallonsu kawai take ba tare da tace komai ba,ganin Jalila ta taho ne ya sakata saurin gocewa ta shige ciki da gudu.

Hajiya Zinaru ce tace "Wai Jalila ki tsaya wannan ƴar yarinyar tana juyaki kamar ita ta haifeki ba ke kika haifeta ba"

Hajiya Farha kuwa tace "Wallahi ki gaggauta turata outside kawai ta cigaba da karatu idan ba haka ba zata tarwatsa miki komai wallahi"

Hajiya Saude tace "ku ƙyale Jalila na san yanzu hankalinta gaba ɗaya yana kan yarinyar can,wai har Jalila ta kasa controlling Ikram haba"

"Duk yadda kuke tunanin Ikram wallahi tafi hakan bara naje naji meke damunta"

Da sauri ta tashi ta nufi ɗakin Ikram.


_Sadeey S Adam_
[6/18, 7:42 PM] SaNaz deeyah: 🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*JALILA...*
_Ƴar bariki ce_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah👄*_



_°°dedicated 2 Anty Maijidda Musa°°_



*_«Episode17»_*

A kwance ta tarar da ita ta rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Zama tayi gefen gadon ta janye hannun Ikram,da sauri ta juya mata baya.

"Ikram kamar hawaye nake gani a fuskarki"

Shiru tayi bata ce komai ba.

"Magana nake miki Ikram"

Miƙewa tayi zaune ta saka yatsanta tana goge hawayen.

"Me akayi miki waya taɓo minke?"

Shiru ta ɗanyi kafin ta fara magana cikin sarƙewar murya "Mommy su waye Dangina?kin ƙi sadani da danginki dana Mahaifina kuma ban taɓa ganin wani yazo da sunan ɗan uwanki ko na daddy ba,gaskiya Mommy ni dai inason ganin dangina ko kina nufin waƴancan matan sune danginmu dan su kaɗai na sani a tare dake"

Shiru Jalila tayi na tsowon lokaci sannan tace "Ikram bana faɗa miki ban son jin maganar nan ba?wane munafukar ce ke zugaki kizo kina tuhumata?Asiya ko?"

"Mommy ba Asiya bace Zuciyata yanzu take begen son ganin dangina nima idan ƙawayena na hira in riƙa faɗar nawa dangin idan kuma ba haka ba wallahi zan shirya in tafi nemansu da kaina Mommy"

A ɗan tsorace ta kalleta tace "Amma lallai baki da hankali Ikram,to bari kiji kinga yadda girman Nigeria yake akwai states da locals government akwai towns da villages to haka family ɗinki suke ƴan Cameroon ne kuma baki san inda zaki nemesu in kinje ba dan babu abinda kika sani a kansu,ki bari nace zan kaiki in lokaci yayi"

"Mommy wani lokaci kuma?tun yaushe ake abu ɗaya ko gawata kike son kai musu? Mommy so kike sai na mutu sannan su ganni"

"Zaki gansu kinji na miki alƙawari insha Allahu"

"Shikenan Mommy amma"

"Amma me?"

"Mommy bana son kina kula su hajiya Sauden can wallahi basu dace dake ba nifa kallon ƴan bariki nake musu"

Gaban Jalila ba ƙaramin faɗuwa yayi ba ta kasa cewa komai.

"Bazaki iya rabuwa dasu ba ko Mommy?"

"Ikram idan na rabu dasu wazan kula su ne dai ƙawayena da suke ƙaunata"

"Gaskiya bana sonki da su Mommy"

"Shikenan zanyi tunani"

"to"

"Tashi ki shiga kiyi wanka kici abinci"

"Nifa a ƙoshe nake Mommy"

"Asiya ta jaki cafeteria ko"

"a'a hostel mukaje muka ci abinci wajen wata ƙawarmu"

"Maza tashi kiyi wanka ki rakani unguwa"

"To Mommy"

Cikin farin ciki ta tashi ta cire kaya tare da ɗora towel tayi bathroom.

Harta rufo ƙofa idon Jalila a ƙofar.

_Ikram banaso ki gano sirrin da nake ɓoyewa na san daga zarar kin gane zaki gujeni ne._

Haka Ikram ta shirya tsaf suka nufi shopping mall bayan sun gama siyayya Jalila ta jata suka nufi park-park suka huta wai duk dan ta mantar da Ikram komai ne.

********

Yau suna zaune a falo su biyu suna ta hira abinsu rabin hirar tasu duk akan karatun Ikram ɗinne tana so tayi convincing ɗinta akan ta tafi outside tayi karatu ita kuma tace tafi son inda take.

Maigadi ne ya shigo cikin sallama suka amsa.

"Hajiya,Ikram ce tayi baƙo yana waje"

"baƙo ko baƙuwa?" Jalila ta tambaya.

"Baƙo"

Kallonta Ikram Jalila tayi irin kallonnan na tuhuma,Ikram tayi tsuru-tsuru dan ta rasa ta cewa.

"Mommy wallahi ban san waye ba"

"Jeka ce tana zuwa" Jalilar ta faɗa sannan ta tashi tsaye tana shirin shiga bedroom.

"Mommy wallahi ban san ko waye ba ban cewa kowa yazo gidanmu"

"Me nace kije ga baƙonki" ta faɗa rai a ɓace.

"Mommy wallahi ban san shi ba"

"Ikram me nace ne?"

"Ranki ya ɓaci dan haka ni bazan fita ba tunda ban sanshi ba kuma bansan dalilin da yasa yazo ba"

"aikuwa baki isa ba,dole kije tunda ance masa kina zuwa,kinji na faɗa miki"
Wucewa tayi ta barta tsaye a gurin.

Jiki a sanyaye Ikram ta ja hijab ta fita.

_Kut lallai guy ɗinnan ma ta ina ya san gidanmu da har zai zo,ya rainan wayo ma._ Ta faɗa a zuciyarta.

A gabansa ta tsaya yana kan lifan ɗin ya sakko.

"Sannunki,barka da fitowa"

"Ciwo nake da zakayi min sannu?,shin wama ya baka izni kazo gidanmu kawai ka haɗani faɗa da Mommyna,nayi mata alƙawarin babu saurayi da zan kula ko zanyi soyayya dashi tunda bata so amma shine ka ɗakko ƙafafu ka zo gidanmu to kada ka sake zuwa kaji na faɗa maka" Cikin faɗa tayi maganar sannan ta juya zata koma ciki yayi saurin cewa
"dan girman Allah ki saurareni Ikram"

Cak ta tsaya sannan ta juyo "karka haɗani da Allah ka cuceni"

"ba cutarki zanyi ba,wannan matar da kika kusa kaɗewa ta roƙeni da inzo in baki haƙuri kuma tana son magana dake"

"Dani kuma?Allah ya sawwake"
"Ki taimaka,ta roƙeni da in kaiki tace ta san ki ta kuma san wani abu daga rayuwarki"

"Ni kuma?a'a gaskiya"

"a lokacin tace in tambaya shin sunan mamanki Jalila?kuma waye mahaifinki tace ta san abubuwa sosai dangane da rayuwarki"

_Ko dai ta san dangina._

Ta faɗa a zuciyarta sannan tace "zanje"
""nayi alƙawarin bazan kula kowa ba Mommyna zata min faɗa sai dai ka bari gobe mu haɗu cikin skul sai muje"

"Okay saka min numberki"

Karɓar wayar tayi ta saka masa ,tana murmushi tace "Sunanka fa?"
"Muhsin"
"Nagode"
"zan kira sai kiyi saving"
"okay"

Sallama sukayi sannan ta koma shi kuma ya tafi.

Tana tura ƙofar falon ta tarar da Jalila tsaye.
Murmushin da take yi tuni ta maƙale shi dan yadda taga ran Jalila a ɓace.

Hannu ta miƙa mata tare da cewa "ban wayarki"

Jikinta a sanyaye ta miƙa mata,tana ɗagawa ta dokata da bango ta faɗi ta fashe,hannu ta ɗaga ta wanketa da mari "Ni zaki ma ƙarya Ikram?har kina murmushi kina miƙawa saurayi waya kuna exchanging number"

Shiru Ikram tayi sai hawaye kawai dake fita a idanuwanta.

"Kingama riƙe waya" ta faɗa tare da ɗaukar wayar dake ƙasa ta fidda Sims ɗin ta ɓallasu sannan ta watsar anan ta wuce.

_Few hours ago_

Tayi konocking shiru babu alamun da mutum a ciki,dan haka ta murɗa handle ɗin ta shiga.

Zaune ta tarar da Jalila a gefen gado tana goge hawaye da tissue.

"Mommy hawaye" Ikram ta faɗa cikin alamu na kuka.

"Fita ki bani guri"

"Momm........."
"Karki ƙaraso nan ki fita nace"

Jikinta a sanyaye tace "kiyi haƙuri Mommy" Sannan ta juya tana kuka itama ta bar ɗakin.

Dana sani sosai take data tsaya tayi magana da wannan guy ɗin dan tunda take Mommynta bata taɓa korarta ba sai yanzu,wani lokacin ma idan bata fito ba da kanta take zuwa.

Ranar haka Ikram ta kwana cikin ƙunci da dana sani.


_*Washe Gari*_

Ƙarfe 8 ta fito da shirinta,kai tsaye ɗakin Jalila ta wuce,tayi knocking 3times amma babu amsa dan haka ta tura ƙofar ta shiga.

Zaune ta ganta a tsakiyar gado tana amsa waya,da sauri ta ɗaga mata hannu alamun ta tsaya daga nan.

Kusan minti biyar sannan ta kammala wayar.

"Mommy ina kwana da fatan kin tashi lafiya"

"faɗi kawai abinda ya kawoki bacci nake son komawa"

ajiyar zuciya tayi sannan tace "Mommy dan Allah kiyi haƙuri ki daina fushin nan dani pls Mom"

"Ikram idan baki da abin faɗa to ki fice min a ɗaki"

"Wayyo Mommy korana kike dan Allah kiyi haƙuri zan tafi skul ina buƙatar addu'arki"

"Allah ya dawo dake lafiya"

Girgiza kai Ikram tayi da sauri ta ƙarasa kan gadon ta rungumeta tana faɗin "Ni dai dan Allah ki yafemin kar fushinki yasa wani abu ya sameni"

Kalamai masu daɗi ta riƙa mata yadda dai ɗa yake kalamance mahaifiyarsa idan ya mata laifi.
Har sai da Jalila tayi dariya sosai sannan tayi mata addu'a.


Sai da Ikram ta fara zuwa ta ɗauki Asiya kamar dai yadda ta saba sannan suka wuce.

Tana cikin driving ɗinne take bawa Asiya labarin abinda ya faru tsakaninta da Muhsin sannan tace "bara in biya ta gurin inga ko zanga matar tunda sai 10 muke da lecture"

"Ikram amma kitson da zaki min fa?zamuje ɗakin Faɗima kiyi min kitso fa"

"Kema kinsan wannan uban gashin naki dole sai dai idan mun fito a lecture"

"To Masha Allah"

"Ji banza dani mayya ce da tuni gashin kanki ya dawo kaina" Duka suka saka dariya.

A daidai gurin suka ganta daga gefen titi,tana zaune da ƴar tasa a gabanta ta rufe rabin fuskarta da zanin da tayi mayafi dashi.

A nan Ikram tayi parking suka sauka zuwa gurin matar.

"Assalamu alaikum" Ikram tayi sallama.

Ɗagowa tayi ta kalleta sannan tace "Ashe zakizo dama Ikram"

"Me zai hanani zuwa bayan kin ambaci sunan mahaifiyata"

Matar ta curo hannunta dake karkarwa ta goge hawayen idonta.

"Ikram naga kamar bata da lafiya mu kaita asibiti mana"

Kallon matar tayi tace "Inna baki da lafiya ne?"

"Ikram" ta sake faɗin sunanta muryarta na karkarwa.

Ikram ta kalli Asiya tace "Asiya mu kaita asibitin"

"Okay kamata muje"

riƙota sukayi duk da yadda take wari amma suka daure suka sakata a bayan mota.

Suna shiga taja motar zuwa asibitin da suke zuwa.

Cikin gaggawa tace a bata frst treatment.

_1hr later_

Tana zaune office ɗin likitan yana masu ƙarin bayani kan ciwon dake damun matar da suka kawo.

"Tana ɗauke da cutar nan mai karya garkuwar ɗan adam wanda rashin shan magani da kuma rashin kula ya saka har ciwon ya bayyana a jikinta kuma sun fara fashewa suna mata wari"

"Doctor ba wani taimako da za'a bata wanda ciwon zai warke gaba ɗaya?"

"Eh to zamuyi iya namu ƙoƙarin dai,zamu bata magunguna sauƙi kuma yana daga Allah bazamu ce ciwon zai warke duka ba ba kuma zamuce bazai warke ba"

"Shikenan doctor nagode,zamu iya zuwa mu ganta ko"

"eh ba damuwa"

Suna shiga ɗakin sukaga tana ƙoƙarin sakkowa daga kan gadon "A'a inna ki zauna ruwan ya ƙare mana"

ɗago rinannun idanunta tayi ta kalli Ikram tace "Bana son zaman asibiti"

"To kidai yi haƙuri da ruwan ya ƙare zamu tafi kinga dai zazzaɓi ne ma a jikinki ga muryarki sai rawa take"

Da ƙyar suka samu ta haƙura ta zauna.

Ikram ta kalli Asiya tace "kinga lokaci na tafiya,ko zaki tafi ni in zauna saiki ɗaukar min excuse"

"a'a Ikram karki damu bara na kira ayi mana attendance kawai"

"To shikenan".





Kusan ƙarfe ɗaya suka gama komai da komai,tun kafin su fita Ikram ta kalleta tace "ina ne gidanki in kaiki?"


"Ba lallai ki iya kaini ba,ƙauyenmu da nisa daga garinnan,dan sai an shiga majigiri ake ɗaukar hanya"

"Kai ya sunan garin?" Asiya ta tambaya.

"Sunanshi Murnai"

"Ikram Mommy ba zatayi faɗa ba kuwa?"

"Zamu fara zuwa in sanar mata itama tayi wanka ta huta sai mu kaita"

"Ikram" Matar ta ambaci sunanta,Juyowa tayi ta kalleta tace"Ikram dan Allah ki kaini gida wallahi ji nake kamar zan mutu nafiso in mutu a gaban dangina"

Jin kalmar dangine yasa Ikram ɗin ta ƙara ruɗewa gashi tana son tambayar a ina ta santa amma ganin yadda matar ke jin jiki yasa ta kasa.

"Asiya yanzu ya za'ayi,kin san halin Mommy abu kaɗan ne ke ɓata mata rai gashi kema ya dace ki kira gida ki sanar musu"

"Bara na kira Mama kema ki kira Mommy a waya"

"To shikenan"

Karɓar wayar Asiya tayi ta kira Jalila a waya amma bata ɗaga ba dan haka ta haƙura kawai,Asiya kuwa da ta faɗa wa Mamansu sam taƙi amincewa har tana cewa zata faɗawa babansu dan haka ta hau napep ta tafi Ikram kuwa ta ɗauki hanyar Murnai tare da magungunan
Matar.

Tafiya ce ta kusan awa biyu da kwatance har takai kanta ƙauyen wanda tama yi tsammanin babu wani gari a wannan gurin,ƙauye da yaci sunan shi ƙauye,yanda yara suke bin motar da gudu ya tabbatar mata da cewa Mota baƙon abu ne a gurinsu.

_Yanzu ace akwai mutane dake rayuwa a garinnan ni kaina ban san garin yana existing ba._ Ikram tayi maganar a zuciyarta.

Matar ita take mata kwatance da ƙyar dan bata jindaɗi sosai.
A haka har suka kai wani gidan ƙasa wanda ƙasar ma gata nan baƙa ce ƙirin.

Parking tayi sannan ta fito,cikin rashin ƙwarin jiki matar ta fito daga motar Ikram ta riƙe hannunta.

Yara suka hau ihu suna faɗin "Ga Hassana ta dawo ga Hassana da maigari ya kora ta dawo"

Ganin yara suna neman yi musu caaaa ya saka tayi saurin cewa Ikram "ga gidan"

Da sauri kuwa suka shiga gidan.

Iya ce tsaye ita da Kabiru a tsakar gidan yayinda Hussaina ke tsaye jikin ƙofar ɗakin.

Ikram saƙe-saƙe kawai take bata gama yanke zato ba taji ance "Fitar mana daga gida" lokacin ko sallamar basu ƙarasa ba.


"Ki koma nace Hassana bana ƙaunar ganinki ko kaɗan"

Tsohuwar ta faɗa tana mai zubda hawaye.

Hasiya(Matar kabiru)ce ta fito daga ɗan kewayenta da sauri ta riƙe Iya tana faɗin "Iya kiyi haƙuri"


Daga Ikram har ita wadda aka kira da Hassana sun kasa motsi bare magana.


Iya ta juya ta kalli Kabiru tace "Kasan dai maigari ya koreta daga garin nan ni kaina bana ƙaunar ganinta Kabiru ka fitar min dasu"

Wadda aka kira da Hassanar sai a lokacin kukanta ya fara fita jikinta sai karkarwa yake har lokacin kuma Ikram na riƙe da ita.

Hussaina ce ta tako zuwa inda su Iya ke tsaye ta kalleta cikin kuka tace "Hassana kin cuceni meyasa kika gudu?sannan ki rasa lokacin da zaki dawo sai irin wannan lokacin da ciwo ya riskeki kin ƙara jawo mana zagi da baƙin jini a cikin ƙauyennan,Hassana ta dalilinki gashi har yau banyi aure ba kowa gani yake halinmu iri ɗaya ne amma ki sani dole akwai sakayya wadda gashi tun a duniya kin fara ganinta"

Kallonta Ikram take tayi ita tana tunanin kamar ta san fuskar.

Cikin jin jiki wadda aka kira Hassana tace "Haba Hussaina kefa ƴar uwata ce wadda muka fito ciki ɗaya kuma lokaci ɗaya ina tunanin kece mace ta farko da zaki yafe min bayan Iya,nayi nadamar abinda nayi ku yafe min dan Allah"

"Babu wanda zai yafe miki Hassana musamman ni da kika fi cuta yau wallahi sai munje gaban alƙali dake an karɓar min haƙƙina"

Muntari ne ya shigo kuma shine yayi maganar wanda shi ɗin tsohon mijinta ne.

"Subhanallahi!" Shine abinda Ikram ta furta tana hawaye itama.
Ta kalli su Hussaina tace "Dan Allah ku bata waje ta zauna ko ta kwanta yanzu haka daga asibiti muke ku taimaka dan Allah"

Muntari ne ya daka mata tsawa ya dawo gabanta cikin ɓacin rai yace "rufa mana baki kilaki kawai,dama jira muke muga da wace ƴar iskar zata dawo ƙauyen nan,to yaran can da kikaji suna ihu a waje harda matasa sun yiwa motar taki raga-raga kuma kema jira suke ki fito su rakaki da jifa har bakin gari"

Itama Ikram ɗin cikin ɓacin rai tace "Kai Mal........" Cikin zafin nama Matar tayi saurin rufewa Ikram baki da hannunta tace "Karki furta mummanan kalma a kanshi shine mahaifinki Ikram"

Cikin mamaki,tsoro da tashin hankali tace "Mahaifina ban gane ba?"

"Muntari wannan itace Hafsa kuma ƴarka wadda na tafi da ɗanyen goyonta".




*Muje Zuwa....*✍





_Sadeey S Adam_
[6/18, 8:02 PM] SaNaz deeyah: 🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*JALILA...*
_Ƴar bariki ce_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah👄*_



_°°dedicated 2 Anty Maijidda Musa°°_



*_«Episode18»_*

Hussaina ce ta ƙaraso da guntun hawaye a idonta tace "Karki raina mana hankali Hassana,tayaya zaki ce wannan itace Hafsa"

Muntari ido kawai ya zurawa Ikram a jinin jikinshi yake jinta.

"a'a dan Allah ki faɗa musu gaskiya nifa taimakonta nayi ban santa ba ban taɓa ganinta ba,mahaifina ya rasu tun ina ciki mahaifiyata kuwa yanzu haka tana gida tana jirana"

"Jalila ba mahaifiyarki bace Ikram ni ce na haifeki kuma tun kina ƙarama na gudu dake zuwa garin kano,Jalila ta nuna miki so wanda daga baya da nayi ƙoƙarin yarda ki tace zata riƙeki mun zauna dake tsawon shekara 5 a gidan karuwai a kano lokacin kina shekara shidda ki tunani mana Auntynki Aunty deejah"
Kai ta riƙe tana son tuno wani abu amma ta kasa.

"Ƙwarai kuwa Jalila ba ita ta haifeki ba Ikram"
Da sauri suka juya dan ganin mai maganar.

"Muh....Mu..Muhsin ya..ak...akai.....ka..ka...san munzo nan?" Ikram tayi maganar muryarta na sarƙewa.

"Na sani Ikram,tun ranar da kika nemi kaɗeta a mota bayan kun tafi ta bani labarinta,naje na ɗakko mota na kawota har garinnan amma suka ƙi karɓarta da kaina nace zan kawo musu ke dan lokacin da naga mahaifinki naga kamarku sosai hakan yasa na tabbatar abinda matarnan ta faɗa ba ƙarya bane"

"Abinda ya ƙara bani mamaki na kuma ƙara tabbatarwa Jalila ba ita ta haifeki ba shine lokacin da naje gidanku kika sanar min cewa na haɗa ki faɗa da Mommynki saboda bata son ganinki da namiji,Ikram wace uwa ce zata ƙi son ɗanta da rahama musamman aure tunda ai ba aurenki zatayi ba bai k..............."

Shaƙo gaban rigarsa da tayi ne yasa ya tsaya da maganar da yake "Kada ka sake furta mummunar kalma akan Mahaifiyata wallahi zan mugun saɓawa koma waye"

Hussaina ce tayi saurin janye hannunta daga shaƙar tare da faɗin "Ke macece bai kamata ba"

Kuka Ikram ta fara tana faɗin "daga taimakonki sai ki min sharri ni ban sanki ba dan Allah meyasa zaki saka alkhairi da sharri"

Ta juya ta kalli Muhsin tace "Kai ka cuceni da kace inje gurinta"

"Ikram ba cutarki nayi ba soyayyace na nuna miki,kin taɓa ganin danginki sunzo gurin Jalila?ta taɓa kaiki gurin dangin naki?to waɗannan sune danginki ki yarda da haka Jalila tana ɓoye miki komai nata Ikram,Sunan da kike amfani dashi ba sunan mahaifinki bane, *Jalila ƴar bariki ce* kuma har yanzu tana sheƙe ayarta kaf daular da kuke ciki kanta ta bayar aka bata a taƙaice Jalila karuwa ce"

"a'a a'a dan Allah" Kai ta riƙe ko ina a gurin gani tayi yana juya mata,daga nan

Please Login or Register in order to submit comment