Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata ƙara sanin abinda ke faruwa ba.


_Few Minutes ago_

A hankali ta buɗe idanuwanta akan Muntari ta fara diresu wanda hannunshi na cikin nata yayinda ɗayan hannun yake goge hawaye dasu.

Kallon kowa ta fara yi wasu na kuka wasu sunyi jigum.

Wata dattijuwa ce ta fashe da kuka tace "Ashe zan ƙara ganinki kafin in koma ga Allah,oh Alhamdulillah"

Runtse ido tayi tana jin wani iri a cikin ranta,wai duk mutanennan dan ita suke wannan kukan.

_Mommy meyesa kika min haka?meyasa bakyaso nayi aure?saboda kema bakiyi ba._ Ta furta a zuciyarta yayinda hawaye ya gangaro ga kuncinta.


Zaune ta tashi ta kalli Hassana dake rakuɓe a jikin bango cikin kuka tace "Meyasa kika tsaneni?sai kace ba ƴar sunna bace ni?kika lalata rayuwata kullum cikin tunani nake su waƴe dangina"


"Ikram wallahi inasonki babu uwa da bata son ɗanta,shaiɗan ne kawai ke kwaɗaita min daɗin duniya shiyasa nayi watsi dake Ikram dan Allah ki yafe ni"

"Mene alaƙata da sunan da ake kirana dashi a matsayin mahaifi?wato Mujahid?"

Ajiyar zuciya tayi tace "Mujahid shine wanda naso muyi tarayya dashi amma yaƙi yarda dani,to sai nayi amfani da damar na cewa Jalila shine mahaifinki to hakan ne yasa Jalila tayi miki amfani dashi amma a zahirin gaskiya Muntari ne mahaifinki nan ne mahaifarki kuna sunanki Hafsat"

"Kin cutar da rayuwata kin cutar da rayuwar bawan Allah Menayi miki?meyasa kika haifeni?dama kin ɓarar da cikina tun kafin inzo duniya"

Muntari ne ya tashi tsaye ya kalleta yace "Allah ya isa tsakanina dake babu sakayya"

Kuka take tana haɗawa da tari a take tafara kakin jini.

Cikin ruɗewa Ikram ta riƙota ita da Hussaina.

"Mu kaita asibiti dan Allah" Ikram ta faɗa cikin ruɗewa.

"Asibiti kuma, barta anan"

"Taya za'a barta anan baya ga halin da take ciki" Kallon Muhsin tayi tace "akwai magungunanta a cikin mota seat ɗin gaba" Miƙa masa key tayi yayi saurin fita.

Da ledar ya dawo ta haɗo duka maganin ko wanne a ƙa'idance bata tsaya bata a hankali ba kawai ta watsa mata duka a bakinta ta bata ruwa.
Kwantar da ita tayi kan cinyarta tana hawaye.

Kowa yayi jigum jigum.
Kamo hannunta Hassana(Deejah) tayi sannan tace "Ikram ina sonki"
Kuka Ikram kawai take yayinda kanta ke mugun sarawa.

Sallamar da akayi ne ya saka Kabiru saurin fita.

Yana dawowa yace "Maigari ne ya aiko a kira Iya"

Iya dake hawaye tace "Har an sanar masa Hassana ta dawo kenan,oh ni Hassana kin cuci kanki kin cuce mu"

Hussaina ce tace "Iya bazaki iya zuwa ba a yadda kike yanzu amma ki bari ni naje nida Kabiru"

"Dani kuma" Ikram ta faɗa cikin kuka.

Haka suka ɗauki hanya su uku zuwa gidan maigari.

A fada suka sameshi kamar yadda ya umarta.
Ko wannensu ya samu guri ya zauna.

Wani dogari ne yayi masa bayani sannan ya dubesu yace "Meye dawo da Hassana ƙauyennen bayan na mata iyaka?"

"Allah baka nasara dama ta dawo ne da ƴarta ga tanan kuma bama ta daɗe da zuwa ba"

"Yanzu-Yanzu su barmin gari na daga ita har ƴar tata"

"Ranka ya daɗe itafa yarinya bata da laifi dan sai yanzu ne ma ta san Hass............
" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Hasiya ce ta zube a gurin tana doka wannan salatin.
"Lafiya?" Kabiru ya tambaya

"Hassana Allah ya mata cikawa"

"Allahu Akbar" dogaran gun suka haɗa baki wajen faɗa.

Ikram cike da tashin hankali ta miƙe tsaye,Hussaina ta riƙota tana kuka.



Maigari ne ya amince ya kuma bada umarnin aje a mata sutura.

****
Kuka sosai Ikram take lokacin da za'a fitada gawar Hassana.

Tana da tambayoyi burjik da zatayi mata amma Allah bai nufa ba.

Duk abin nan da suke mata amma babu wanda bai koka mata ba dan tayi tuban dole ne.

_Washe gari_

Da yamma liƙis Ikram ta shirya komawa Katsina.

Hussaina nata kukan dan Allah ta zauna dan gani suke kamar idan ta tafi bazata dawo ba.

Kallon Muntari tayi wanda yayi shiru tamkar an dasashi a gurin.
Guntun hawaye ta goge tace "Zan dawo in cigaba da rayuwa daku,nan ne mahaifata,asalina,kune dangina zan dawo mu zauna daku inason in rayu daku in ji daɗin mahaifina da dangina" ta fashe da wani kukan tana faɗin zanje in ɗebo komai nawa sannan in dawo mahaifata"

"Hafsat bama son ki tafi,sai muga kamar bazaki dawo ba"

"Zan dawo insha Allahu"

"Gashi motarki an lalata miki bamu san ya zamuyi ba"

"Karka damu Baba zan sa azo a gyara idanma bata gyaru ba ba matsala"

"ai ba'a samun mota a ƙauyennan zaki iya hawa babur zuwa majigiri?"

"Baba sai mu tafi tare ba matsala" Muhsin yayi maganar.

Haka kuwa akayi ta ɗebo duk abubuwan da suke da amfani sannan suka shiga mota suka tafi.

****

Kallon gidan nasu tayi a zuciyarta tana ta saƙa irin abinda zata faɗawa Jalila.

Ita sai yanzu ma tayi realizing irin dukiyar da Jalila ke dashi amma bata da wani aiki dan ko yaushe tana gida sai dai in kuma bata garin.
_Amma ai tana business_ wata zuciyar ta tambaya.

_Ashe karuwa ce na rayu da ita ta ciyar dani da haram_ ta furta a zuciya lokacin da wasu zafafan hawayen suka sauka a idanuwanta ta saka hannu ta goge.

Knocking tayi maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofa,yana ganin itace yayi saurin matsawa dan ta shiga.

A falo kuwa Jalila na zaune ta saka hannunta a haɓa tana ta tunanin inda Ikram take tayi nema amma babu alamar zata ganta ta tambayi Asiya tace ita tun a skul suka rabu.

Hajiya Saude na ta rarrashinta tana cewa ai Ikram ba yarinya bace zata dawo.

Turo ƙofar da akayi ne yasa su kallon gurin.

Duk kansu suka miƙe tsaye lokacin da suka ga Ikram ɗin ta shigo.

Itama ganinsu ne yasa ta tsaya cak tana musu kallon tsana.

A ruɗe Jalila ta ƙaraso gurin Ikram ɗin tana ƙoƙarin riƙo ta tayi saurin runtse ido tare da cewa "karki taɓa ni Mommy"

Jin hakan ne yasa Jalila tsayawa tare da ja da baya.

"Ikram"

Kallonta tayi sannan tayi saurin rugawa ta shige bedroom ɗinta.

Kallon Hajiya Saude Jalila tayi tace "Kamar kallon tsana na gani a idanun Ikram"

"Nima haka na gani"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "kinga kije sai munyi waya bara naje gurin Ikram"

Sai da hajiya saude ta fita Jalila ta kulle ƙofar falon sannan ta shiga bedroom ɗin Ikram.

Tana ganin Jalila tayi saurin tashi ta maƙale daga can ƙarshen bangon.

"Karki ƙaraso ki fita dan Allah banson ganinki"

"Ikram......"

"Ki daina kirana da sunan da ba nawa ba Mommy kin cuce ni ashe dama ke ƴar bariki ce kuma kika ciyar dani da haram meyesa kika min haka wallahi sam bana ƙaunar ganinki"

Cak Jalila ta tsaya tana wa Ikram kallon mamaki.

Cikin kuka Ikram ta cigaba da faɗin danma ban sanar dake cewa na haɗu da mahaifiyata wadda kukayi bariki tare,kuma ta sadani da dangina da baki ƙaunar shaida min su,to ki sani yanzu na san komai kuma zan koma gurin dangina"

Jalila ta kasa cewa komai tayi suman tsaye kawai.

Ikram ta cigaba da faɗin "Abu mafi muni kika hanani kula kowa kika saka nake amfani da sunan mahaifin da ba nawa ba sannan kika hanani kula ko wane namiji tunda kin kasa auruwa nima baki so na auru kinfi so ki barni a haka in zama ƴar bariki kamarki"

Jin hakane yasa Jalila ta hau kan gadon ta janyota tare da bata zafafa mari har biyu "Har kinyi girman da zaki faɗa min magana Ikram"


"Ƙwarai kuwa ko kasheni zakiyi bazan ƙi faɗar abinda ke raina ba,kin cuceni kuma bazaki sake ganina ba daga yau bare har ki mareni,yau zan koma ga dangina"

Kuka Jalila ta fashe dashi tamkar ƙaramar yarinya.
Wato abinda take gudu ya afku.



*Ku biyoni*



_Sadeey S Adam_
[6/18, 8:49 PM] SaNaz deeyah: 🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*JALILA...*
_Ƴar bariki ce_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah👄*_



_°°dedicated 2 Anty Maijidda Musa°°_



*_«Episode19»_*

Sakkowa daga kan gadon tayi sannan ta buɗe wardrobe ta ɗebo kaya ta zube kan gado.

Trolley ta jawo ta ta fara zuba kayanta a ciki.

Jalila dake tsaye ta ƙaraso gabanta tace "Ikram kiyi tunani karki yanke ɗanyen hukunci"

"Mommy dan Allah ya isa haka haba! Wallahi karki tunzura ni in kaiki kotu"

"Kotu" Jalila ta maimaita maganar

"Eh kotu saboda kun zalunce ni,kun ɓarar da mutuncina,nayi dana sanin saninku a rayuwa"

"Ikram yau ni kike faɗawa magana son ranki"

"Kaɗan ma nayi miki wallahi amma idan kina ci gaba da min irin haka to zan faɗa miki maganar da zaki kasa bacci"

Cigaba tayi da haɗa kayanta cikin trolley yayinda Jalila ta koma falo ta cigaba da kuka.

_Waya zuga Ikram take wulaƙanta haka?su waye dangin nata,ya akai har ta haɗu da Deejah,meyasa Ikram ta kasa fahimtata,Deejah ce ta cuceni da ta kasa sanar min da dangin Ikram daga baya kuma tayi mun ƙaryar Mujahid ne mijinta_

Ƙara goge hawaye tayi sannan ta ɗan jingina da kujerar dan har lokacin hawaye ke tsiyaya a idonta.

Tana zaune taga Ikram ɗin ta fito hannunta riƙe da handbag ɗayan hannun kuwa tana janye da trolley.

Jalila ta miƙe tsaye ta kalleta tace "Ikram dare ne fa bai kamata ki fita ba"

"Mommy banga amfani zama a ƙazantacciyar rayuwa ba,zan tafi inda yake da tsarki"

"Ikram dan Allah karki gujeni tun kina jaririya kike a hannuna bazan iya rayuwa babu ke ba"

"Ni kuma bazan iya rayuwa da ƴar bariki ba,bazan zauna dake ba"

ƙofa ta kama tana ƙoƙarin buɗewa,Jalila ta ruga kitchen ta ɗakko wuƙa ta fito.
Ganin Ikram ta fita yasa ta bita farfajiyar gidan ta sha gabanta.

Zaro ido Ikram tayi tace "Kashe ni zakiyi?"

"a'a zan kashe kaina ne in har kika ce zaki tafi ki barni"

Dariya mai haɗe da hawaye Ikram tayi sannan tace "Kisa fa,to bismillah in kin mutu Allah ya jiƙanki,amma tafiya ba fashi"
Ratsewa tayi ta gefen Jalila ta wuce.

Tana fita ta ɗauki hanyar titi,kawai taji maigadi na ƙwala mata kira.
Tana juyawa ta ganshi a sukwane ya nufota.
"lafiya?"

"Hajiya tana kwance cikin jini"

"Mommy?"
"Eh"
Sakin kayan tayi ta ruga da gudu sai shine ya ɗebi kayan nata.

Ganin Jalila a kwance cikin jini ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta faɗa tare da tallabo Jalila.

Ganin yadda jini ke zuba yasa a ruɗe ta fita dan bata san inda key ɗin motar Jalila yake ba.

Gidan dake jikin gidansu ta faɗa a ruɗe maigadi na mata magana bata ma saurareshi ba,dalilin shigarta kuwa motar da taga ta shiga ne yasa ta shiga kafin maigadi yakai ga rufe gate ɗin.

Kafin takai jikin motar tuni maigadi yasha gabanta "Malama baki da hankali da zaki shigowa mutane haka"

"Dan Allah ku taimakeni Mamana na kwance cikin jini"

"Kinga bama son shashanci fita kafin na kira Hajiya"

"Meke faruwa anan ne Malam Habu?" Matashin saurayin ne yayi maganar yana tsaye jikin motar daya fito.

"Ranka ya daɗe wata ce ta shigo tana maganar banza"

"Barta ta ƙaraso"

Tun ma kafin maigadi ya sake magana tuni ta ƙara gaban saurayin.

Hannu biyu ta haɗe tace "Dan Allah ka taimakeni mamana ba lafiya tana kwance cikin jini kuma ban san inda ta ajje key ɗin motarta ba"

"Muje na gani"
Da sauri tayi gaba ya bita a baya.

Lokacin da sukaje idanunta har ƙara kakkafewa yake.

"Ku jira na ɗakko motar" ya fita da sauri.

******

Suna tsaye a ƙofar Emergency Ikram ta jingina da bango zuciyarta na ƙunci idanunta na zubda hawaye.

Doctor ne ya fito,da sauri Ikram suka ƙarasa gabanshi.

"tana buƙatar jini cikin gaggawa dan ta zubar da jini da yawa,wannan kuma maganin da muke buƙata ne"

Shi ya karɓi takardar yayi gaba Ikram ta bishi a baya.

Sai da aka gama mata komai aka turata ward cikin Amenity sannan saurayin yace "To ni zan tafi ki kula da ita sosai Allah ya bata lafiya"

Miƙewa tsaye Ikram tayi tace "dan Allah zan bika ka ajje a Umyuk"

"Ita kuma Maman naki da wa za'a barta?"

"Baza'a rasa wanda zai zo gunta ba daga nan zuwa safiya ni dai dan Allah ka saukeni a skul bazan zauna anan ba"

"Okay mu fita sai muyi maganar kin kar a tasheta a bacci".




Suna tsaye a farfajiyar asibitin ya ƙara kallon agogon hannunshi.

"9:30pm ya kamata in tafi saboda Mommy bata ga dawowa na ba"

"Ni dai binka zanyi dan Allah ka sauke a skul" Ya faɗa cikin muryar kuka.

Ganin haka ne yasa ya lallaɓata tare da tausasan kalamai,da ƙyar ta haƙura ta zauna.

_Washe gari_

Da sassafe ta tafi gida lokacin Jalila na bacci bata tashi ba.

Gidan ta koma ta kwanta tasha kukanta har bacci yayi awon gaba da ita.

*****

Ƙarfe 10 Ja'afar ya isa asibitin.
Leburorin da suke aiki a asibitin su ya saka suka ɗibi manyan ledojin da yayi masu ƴan siyayya.

Yana tafiya suna binsa a baya har ɗakin.
Yana tura ƙofar ya tarar da Jalila ta jingina jikinta da fuskar gadon hawaye ne sharkaf a idonta.

Ganinsu yasa tayi saurin jan ɗankwalinta tare goge haweyen idonta.

"Ku ajje nan ma ya isa" ya basu umarni sannan ya fiddo 2k ya basu.

Zama yayi tare da sakin ajiyar zuciya,sai a lokacin ya ƙarewa Jalila kallo yayi mamaki da Ikram tace Mamanta.

"Waye kai?" tayi tambayar murya a dashe.

"nine wanda muka kawoki asibiti"

"Ina Ikram"

"Taje ta dawo" ya tsinci kanshi da yin ƙarya dan baima san ina take ba.

"Duk wanda yake tare da Ikram nasan amintaccenta dan bata taɓa rayuwa da wanda basu dace da ita ba"

Shiru yayi ba tare da yaje komai ba,shi dai bai san Ikram ba ya tsinci kanshi kawai da dawowa ya gansu.

Ita kuma Jalila ta cigaba da faɗin "dan Allah ka roƙar min Ikram karta tafi ta barni"

"Baza ta tafi ba yanzu ma zata dawo"

Wasu zafafan hawayene suka fito daga idanunta,cikin kuka ta fara bashi labarin duk abubuwan da suka faru sannan ta ƙara da cewa "bata sona yanzu kwata-kwata kuma ta rantse sai ta barni,wallahi bazan iya rayuwa babu Ikram ba na saba da ita saboda ita naƙi yin aure saboda ita na ƙara destroying life ɗina,naso ace ban farka ba naso ace dana cakawa kaina wuƙa na mutu ban so na tashi ba"

Ran Ja'afar ya ɓaci sosai ya kalli Jalila yace "Karki damu insha Allahu zan shawo kan Ikram matsalar ban san ina taje ba"

"Ina tunanin gida ta tafi dan ta haɗa kayanta ta bar garin shine abinda nake hasashe,dan Allah kaje ka bata haƙuri"

"Shikenan zanje kuma zanyi iya bakin ƙoƙarina"

Haka ya tashi tsam ya ɗau motarshi ya koma unguwar.

A bakin gate ɗinsu yayi parking saboda bayason shiga da mota gidan da bai taɓa zuwa ba baima yi tunanin da mutane a ciki ba.

Knocking yayi sannan maigadi ya buɗe.
"Amm Ikram tana nan kuwa?"

"Eh wa za'a ce mata?"

"Eh to Umma Jalila ce ta turo ni dan in sanar da ita an barta ita kaɗai a asibiti"

"Oh to shigo ma gata nan ta fito da alama fita zasuyi dan tun ɗazu shima wancan yake jiranta"

Da saurinsa kuwa ya shiga.
Hangota yayi janye da trolley tana ƙoƙarin sakawa a booth.

"Ikram" jin an anbaci sunanta ne yasa ta juyo,idanun nan sun kumbura suntum.

Ganinshi ba ƙaramin mamaki ya bata ba dan bazata mancen wannan fuskar ba..

"Ina zaki na ganki da trolley?"

"Garinmu" kai tsaye ta bashi amsa.

Ya ɗan matso kusa da ita tayi saurin sauke ƙwayar idonta daga kallon da take masa.
"ba wannan lokaci ya kamata kiyi tafiya ba karki manta Mama na kwance a gadon asibiti"

"Mamar wa?" Muhsin dake mota ya fito da sauri yana faɗar haka.

Ja'afar ya mayar da ƙwayar idonsa kan Muhsin tare da cewa "Ina magana ne akan mahaifiyar Ikram dake kwance ba lafiya kai kuma waye?"

Cikin ɓacin rai Musin yace "Mahaifiyar Ikram ta rasu,waccen ƴar barikin ba ita ta haifeta ba,kuma ni ɗin nan nine wanda zan zamo mata jigon rayuwa"

"Za dai ka tarwatsa rayuwarta,Ikram karki yarda wannan ya hure miki kunne"

"Amma ina tunanin baka da hankali ko,Kinga Ikram shiga mota mu tafi dan rana na ƙara yi"

Kallon Ja'afar ta sake yi sannan ta juya tana buɗe murfin ƙofar tayi saurin tsayawa cak tamkar gunki sakamakon maganar da Ja'afar ya furta.

"Baki da uwa kamar Jalila babu mahaluƙin da zai nuna miki so kamar yadda Jalila ta miki,Ikram in har kika tafi kin cika butulu kuma kin rama alkhairi da sharri"

Muhsin ya leƙo yace "Ikram shigo ki ƙyale wannan sakaran"

Shiru tayi tamkar bata da rai.

Kalmar butulu take ta yawo a kanka.


Ɗago rinannun idanunta ta sake yi ta diresu akan Ja'afar,sai a lokacin sabon kuka ya ɓarke mata da gudu ta koma cikin gidan duk kansu suka rufa mata baya.


A falo ta zube kan carpet ta cigaba da dirzar kuka.

"aikin banza kalli ɓarnar da kake ƙoƙarin aikatawa wato an biyaka ko kazo ka tsarata to ai ita ba yarinya bace ta san ciwon kanta"

"Ni nafi ƙarfin a bani kuɗi in aikata wani abu,duk abinda nake inayi ne domin Allah,Ikram kuwa har yanzu bata san ciwon kanta ba tunda har ta iya yanke ɗanyen hukunci,kai kuma baka ƙaunarta tunda har kake bin bayan rashin gaskiya"
Jin haka yasa Muhsin ya taho gadan-gadan zai daki Ja'afar tayi saurin karewa tare da cewa "Muhsin kar takai ga haka" ta ƙara fashewa da kuka.

Ƙayataccen Murmushi Ja'afar yayi tare da faɗin da ka dakeni da baka kuma dukan wani ba a duniya"

"Saboda kai waye?wallahi na dakeka na daki banza"

"ba sai kasan koni waye ba amma da ka dakeni dole ne ma ka sanni"

Tasowa Ikram tayi ta kalli Ja'afar tace "Kai! Wai dan Allah meyasa kake faɗar wannan maganganu da kasan dalilina da tuni ka bar wannan maganganun"

"Sunana Ja'afar,Kuma duk abinda yake daga rayuwarki tun daga shekara ɗaya har zuwa yanzu na sani kuma najine daga bakin mahaifiyarki wato Jalila"

"Kin ji ba ta aiko shi ya hure miki kunne Ikram,ki taho kawai mu tafi ki ƙyale wannan"

"Tsaya Muhsin" ta faɗa cikin shashsheƙar kuka sannan ta mayar da kallonta ga Ja'afar tace "amma kasan da haka kake kirana butulu"

"Ƙwarai ma kuwa kin cancanci a kiraki da haka Ikram,Mutum kamar Jalila ba abin yardawa bane,kin san me tace? Bata son rabuwa dake duk da wannan baƙaƙen kalaman da kika mata.

Ikram kinyi kalamai masu zafi wanda wani bazai yarda zaki iya ba amma na san zugaki ake"

Cikin faɗa-faɗa tace "Haba Ja'afar wai kai baka ga illolin da tayiwa rayuwata ba,ta hanani kula duk wani namiji dan kar inyi aure saboda itama batayi ba sannan ta ƙi sadani da dangina"

"Ita ta faɗa miki saboda kar kiyi aure ne?,kin taɓa tambayarta cewa Mommy saboda meyasa baki so in kula maza?"

Kallonshi kawai take ba tare da tace komai ba.

Shi kuma ya cigaba da faɗin "Ta hanaki kula maza ne domin kar a lalata rayuwarki,ita ƴar bariki ce amma sai ta zaɓi ta inganta taki rayuwar akan tata,ta na miki kallon ƴa ne wato jinin jikinta kuma ta san mahaifiyarki ta fita taƙadaranci shiyasa take ta killaceki tsoronta ɗaya shine karki lalace amma Jalila na so ki samu miji nagari ki aura dan shine babban burinta"


Muhsin jin wannan kalaman ne ya sakashi sake harzuƙa tare da faɗin"Kinji fa wadda tayi sanadin zuwanki duniya yake cewa taƙadara"


Ikram ba abinda take sai kuka.

Ja'afar kuwa ya sake ce mata "Sannan da ta san danginki da tuni ta sadaki dasu,duk ranar da kika mata maganar danginku ranar bata iya bacci kuma kina yawan tambaya tun kina ƴar shekara tara har zuwa yanzu,Mahaifiyarki taso watsar dake tun kina ƴar shekara ɗaya,Jalila taga idan an watsar dake wazai tsinceki?cikin biyu dole a samu ɗaya ko mugu ko nagari,tun a lokacin tace ita zata iya riƙeki haka Wadda ta haifeki ta barki anan yashe,sai yayen dole Jalila ta miki,kullum burin mahaifiyarki ta wullar dake dan a cewarta bazata iya bariki da ƴa ba,Jalila ita taci fitsarinki da kashinki har kika kai wannan matsayin sannan kika haɗu da dangin naki wallahi Ikram Jalila bata taɓa sannin danginki ba sai yanzu da kike faɗa yanzunma bata gansu ba,wanda kike amfani da sunanshi shine wanda Mahaifiyarki ta sanarwa da Jalila a matsayin mahaifinki ashe tayi haka dan ta gaji da tambayarta da take"

Jikin Muhsin a lokacin yayi sanyi sosai.

Ja'afar ya ɗan goge hawayen dake ƙoƙarin zubo masa yace "Mahaifiyarki ta haifeki ne kawai Ikram amma Jalila itace komai naki ta miki gata baki taɓa sanin ba ita ta haifeki ba sai yanzu,ta baki ilmi,ci,shayarwa da tufafi,bata cancanci haka a gareki ba,tana sonki duk wani abu da takeyi saboda kene,dalilinki tabar gidan karuwai da aka haifeta a cikinshi baki san wannan ba sai yanzu,a gidan karuwai aka haifeta ta girma acan bata sanwaye mahaifinta ba kuma tun tana jaririya babarta ta rasu kuna shekara shidda kika matsa mata taji ta haƙura da bariki zata inganta rayuwarki taje gidan magajiya dan ta sanar mata su waye mahaifanta amma bata samu amsa ba a lokacin ke da bakinki kikace mata _Mommy ina tare dake_ kinsan meyasa ta bar gidan karuwai?"

girgiza kai Ikram tayi shi kuma ya cigaba da faɗin "Saboda Mahaifiyarki har ɗaki take kawo maza kina kallo sannan ta bada umarnin in har baku bar gidan ba to zata fasa ƙwai cewar ke ƴarta ce sannan ta ƙwaceki ta kaɗaki ki bi duniya,wannan furucin ne yasa kuka bar garin kuka koma Abuja,Jalila tayi niyyar barin wannan rayuwa amma kuma sai rashin kuɗi ya hanata,baku da abincin ci ba kuɗin da za'a maidaki makaranta dan haka ta koma wannan rayuwar ta tara kuɗi masu yawa a hannun wani attajiri wanda har kika girma baki taɓa sanin tana barikinta ba tun ranar da kikai candy tayi bankwana da gurɓatacciyar rayuwa dan ta san zaki saka mata ido a al'amuranta sai take yi yadda sam bazaki gane ba,daga baya ma sai ta daina ta mayar da hankalinta kan business,shin kin yi butulci ko bakiyi ba in har kika gujeta?"

Cikin kuka ta zube ƙasa tana faɗin "Mommy Mommy mommy da wane idon zan kalleki in baki haƙuri"

"Sam bata fushi dake dan ta zaɓi ta bar duniya akan ta rasaki tunda baki ƙaunarta bata da kowa saike kaɗai Ikram kuma tana ƙaunar farin cikinki"

Cikin sarƙewar Murya Ikram tace "Ja'afar dan Allah ka kaini gurin Mommy"

Muhsin jiki a sanyaye yace "ban san labarin haka yake ba duk da itama kafin ta rasu tana ɗan faɗar gaskiya,Mun fahimci Mommy baibai dan haka nima zan biku"

Fitowa sukayi Fuskar Ikram har ta fara canzawa saboda kuka.

Motar Ja'afar ta shiga,Muhsin ya biyosu a baya har asibitin.

Ja'afar da Muhsin ne suka fara shiga ita kuma tana laɓe a bayansu.

Jalila na kwance idonta na kallon silin hawaye sai zuba yake ta gefen idanunta.
"Karka ce min Ikram ta tafi na rasa ta kenan?"

Ikram ɗin ce ta fito daga bayan nasu a hankali ta ƙarasa gurin Jalila ta zauna kan kujera tare da riƙo ta "Mommy" shine abinda ta furta tare da fashewa da matsanancin kuka.

Jalilar ma kuka take ta kwanto Ikram kan ƙirjinta.



_Sadeey_✍
[6/18, 9:11 PM] SaNaz deeyah: 🍁🍁🍁🍁🍁🍁
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*JALILA...*
_Ƴar bariki ce_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🍁🍁🍁🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah👄_*



_°°dedicated 2 Anty Maijidda Musa°°_



_*«Episode 20»*_

Sai da suka sha kukansu sannan sannan Ikram ta ɗago kai tana gogewa Jalila hawaye.
"Mommy kiyi haƙuri dan Allah Mommy"

"Ikram baki min laifi ba fatana kawai karki gujeni Ikram"

"Ina tare dake Mommy"

Sosai Ja'afar yaji daɗi haka Muhsin ma.

Sun ɗan zauna sannan Ja'afar ya tafi yace zai dawo idan ya tashi a aiki.

Ikram kuwa gida ya sauketa ta ɗebo masu kayan da zasu buƙata a asibiti sannan ta ɗauki key ɗin motar Jalila ta shiga ta koma asibiti.


*******

Wasa-wasa watan Jalila biyu a asibiti.

Ikram ko yaushe ita take tare da ita.

Idan tana da lecture haka take tafiya sai Ja'afar yazo ya zauna idan tana da interval kuma shi sai ta dawo shi ya tafi office haka suke duty,Ja'afar ya zame masu tamkar ɗan uwa.

Maman Ja'afar tana zuwa sosai asibiti wani lokacin ma anan take yini,Ikram kuwa tayi kicin kicin ta hana kowa zuwa zuwa asibitin a ƙawayen Jalila dan ta kashe wayar Jalila ma ta yadda ba wanda zai kira ya sameta.

Jikinta kuwa sai ƙara warwarewa yake tana ƙara samun sauƙi sosai.

******

Mommy ta ƙara kallon Ja'afar tace "ko bakaji me nace bane?"

"naji Mommy amma ina tunanin fuskantar baba da wannan maganar"

"Karka damu indai babanka ne na riga na sanar masa komai yace in har ka amince shima ya amince a shirya komai yana dawowa ayi biki"

Murmushi yayi tare da sosa kai "Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi Mommy zan samu mu tattauna da Zainab sannan in samu Ikram ɗin muyi magana"

"To kaji ka wai shin kaɗauka ni da wasa na ɗauki maganar ai Zainab ta daɗe da sani wai kai mai Yaya ko?to ta san komai ita murna ma take zata samu ƴar uwa"

"Tunda kowa ya amince nima na amince"

"To Alhamdulillah dangine kaɗai ke ta gutsuri tsoma suma zasu daina tunda har mu mahaifanka mun yarda"

"Mommy bara naje na ɗan wasa ruwa wallahi a gajiye

Please Login or Register in order to submit comment