Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mafarkin sa.

Maiko zai faru idan ka daura yaddarka akan Abu guda, mutane ko suka mansheshi abin dariya... So sad
Aiko a Tsakiyar party na samun takoban jaruman Daa ne suka Bata Masa Rai ya wuce ba tare da yayiwa kowa sallama ba haka ya koma gida inda ya shige gidan fuskar sa Babu annashuwa.

"Son kamar naji dazu kace zaka dawo gida late,but what happened?."
Haka Mahaifiyar sa ta tambaya shiko ansa Mata yayi da "Nothing." Ya shige dakinsa inda ya aje ID nashi akan wata table dake 'Bari guda na wannan dakin,hayewa yayi kan katifarsa ya kwanta da ruwan cikin sa.

Kwatsam sai ga Kira ta shigo wayarsa Babu Bata lokaci ya ansa hade da sallama.

"Wa'alaikassalam Al-Hussien,Ya hakan? Tafiya Babu sallama."

"Eh wallahi an naimi na dawo gida ne shiyasa."
Haka ya Bata ansa inda ta mayar masa da tambaya kamar haka.

"Amma lafiya dai Kam?."

"Eh lafiya."

"Okay toh shikenan,Dama na kirane na sanar dakai cewar Hajara ta sauya *patner* "Abokina Aiki",tanajin nauyin sanar dakai hakan shiyasa ta sanar dani na Gaya maka Dan haka gobe saika naimi wani abokin aikin kaji."

Shiru yayi baice Komi ba ya sauke wayar...kansa ko ta daure domin dokar aikin wannan kanfani idan baka da partner kana gab da samun Kora daga kanfanin.

Nanfa ya kasa cewa komi,ya tsaya sai nazari yake hade da tunanin Abubuwan da suka faru tsakanin sa da shugaban kanfanin Nan ya Mike ya ciro wata jaka dake karkashin gadon sa,ya aza a saman katifar ya Kuma bude..
Nanfa sai zanen kofar ta baiyana a jikin wata farar pepa wacce nake kyautata zaton shi yayi hakan.

Sai yace...
"I'm very sure,idan kaga wannan zanen zakasa gabadaya ma'aikatan ka bincike akan wannan kofa."

Da haka yake tunanin yasamu mafita,ya Kuma sa aransa gobe zai gabatar da wannan gaban ma'aikan gurin.
Amma saidai kash baisan kaddara takan ruga fata ba.. danko da yasan halin da zai kasance ciki da bazai Rintsa ba,Amma tunda baisanda Wannan ba tuni ya lulluka cikin duniyar bacci wacce take cike da mafarkai.

Cikin wannan mafarki nasa ko saiya Sami damar shiga wannan kofar da niyar idan ya shige zai Sami wani abin Wanda idan Allah yasa sunga kofan a zahiri sai Yana fadamusu ababen ciki domin su gaskata mafarkin nasa.
Haka ya kasance cikin wannan guri Yana ta zurgazurga har gari ya waye.

Gari na wayewa aka Sami gankar jikinsa yayinda ruhinsa ke gargame a wannan kofa..
Haka akayi Jana izarsa aka Kuma birnesa batare da Ansan halin da Ruhin Nasa ke ciki ba,su azaton su mutuwa yayi....

Al-Hussien bai Raina ma kansa ba har sai dayazo naiman hanyar fita kafin yasan yayi babban kuskure.
Haka shekaru da Dama suka shude,yayinda shi wannan saurayi ya kasance cikin d'imuwa da tsoran ababen cikin wannan kofa but then yagano fa shima abin tsoro ne domin duk ababen dayake tsoron acikin wannan guri Basu iyya illatashi Nan sai ya dukufa a naiman mafita,wacce hakan ta kaisa ga naimo masaluha wannan Hali dayake ciki.

Wanda wannan masaluha ko shine dakin alfarma dayayiwa Harun karyar cewar shine hanyar fita..

"This is the end of me."

Kwalla ce ta soma zubowa a fuskar sa yayinda take gangaruwa daga fuskar nasa tana d'iga a kasa...

Readers shin Baku da tambaya game da bangaren Nan biyu wato bangaren su Atif da Kuma bangaren su Amrita suna ta ambatar shekaru biyu da batar su Atif wacce a cikin Guri kuwa daidai take da kwana biyu domin kwana biyu kacel su Atif sukayi a gurin...

Hmm Tirkashi kenan kwana daya a wannan kofar daidai take da kwanaki 365 adoran kasa Tofa..

Atif,Mu'azz,Muzzaffar,Samra,Nina da Kuma Mufydah Tsaye suke yayinda sukayi sukum suna kallon halinda Tina,Ali da Kuma Simon ke ciki.
Halin da suke cikin ko tayi tsamari sabida Simon har Aman jini yake.

"We have to help them."

"But how Mufydah,ya zamu iyya tallafa musu bayan mu da kanmu Muna naiman tallafi."
Haka Samra ta furta inda Atif yace dasu

"Harun ne kadai yansan wani irin lakani yayiwa Simon."

"Hold it,Harun fa ba mutumin banza bane,why not ka Fadi Aibun wancen mutumin daya jefa rayuwan mu a had'ari akan wani banzan reason nashi,and one more thing I don't want nasan dalilinsa nayin hakan."
Fadar Nina inda muzzaffar yayi tsaki Hadi da Kuma cewa.

"Guys bansan bakuda Imani ba sai yau ace abokan tafiyar ku na gabar mutuwa amma ku tsaya cacan baki,idan bazaku Basu tallafi ba Ni Zan basu."

Fadar hakan yayi yayinda ya kasance ya rigada ya rusuna gefen Tina ya Kuma Kai hannunsa da niyar taba ta domin ya tallafa mata but sai Samra ta kalli wani koren haske ya baje idanunta ya Kuma ketara ko wani lungu...ta cikin idanunta ta kalli hakan.

Kasa fahimtar wannan Alama tayi Amma da ta kalli halinda Tina ke ciki da Kuma yadda fatar jikinta ya dawo Kore Shar sai tayi sauri dakatar da muzzaffar..

Ihun cewa tayi "muzzaffar A'a." Amma Ina tuni ya daura hannunsa a jikin Tina...
Kamar tsawa hakan yaji a jinin jikinsa yayinda tafin hannunsa ya wani tsassage wannan koren abun ko ya shige ciki.

Ihu muzzaffar ya buga Dan rad'ad'in da yakeji ta ciki Nan fa Atif yayi tsalle ya Ciro belt nashi yayi saurin daure Masa hannun dashi...
Abinda ya yasa shi yin hakan ko shine gani yake wannan koren guba na bin jijiyar jikin muzzaffar hakan ne yasa shi yin hakan...

Kuma fa sai akayi dace domin wannan guba kasa karawa gaba tayi danko isarsa ga inda aka daure din ta tsaya..kem

"Innalillahi Wa'inna ilaihi Raju'un."
Abinda ke fitowa a bakin Nina kenan yayinda ta Marne jikin karfen Kejin Dan zunzurutun razanar da tayi Aiko wannan yanayi da take ciki ta farune a Karo daya da 'bargewar wata haske a dakin da Harun ya kasance cikin.

Wanda wannan haske Saida ta ratsa kowace lungu da sako na wannan gini..
Da tallafawar wannan haske Amrita da sauran mabiyanta suka Sami ikon farkawa daga suman da sukayi...

Hasken tamkar flash haka ta dauke Babu jimawa...

"Hello! Anyone there."

Haka muryan Adam keta ambata wannan batu yayinda yaketa takawa baisan inda take Sanya kafafun sa ba...

Amrita ko tun baiyanan hasken ta farka but kin wuyace ta hanata mikewa but da Adam ya cika gurin da muryarsa sai ta Mike Hadi da dauko Jakarta...

"Amrita!... Wai Ina kika shigane haka shin kuwa kinsan ke kadai nasani anan gurin kuwa,if not da Zan anbaci sunan kowa."
Aiko fadar hakan keda wuya sai yaji an dafa kafadarsa..

Yayinda aka mikawa *Amrita* hannu ta Kama ta Mike tsaye shugaban tasuko aka Mika Mata wayarta sauran abokan tafiyar nasu ko kajunkunan su aka Mika musu...dukka a karau daya ta faru.

Duk cikin duhu Babu Mai ganin idanun juna haka ma yasa Amrita,Adam,Harzad,Anwar da kuma shugaban zugar tasu sukayi godiya Hadi da cewa... "Let's find the other."
Aiko juyawar su basuyi taku goma ba sukayi Karo dukkanin su suka zube guri guda.

Ganin sukayi ga taron nasu gaba daya guri daya bayan Kuma kowannen su ya baro mutum a bayansa...
Cikin rudani Amrita tace da Adam bayan ta kunna *toci light*

"Adam You're there,I left you behind, kai ka Mikan hannu na tashi a baya na baro ka ai."

"How comes? Ni da nake tare da Harzad."
Haka Adam din ya Bata ansa inda Harzad yace dashi..

"What? Ni wai,yaushe na kasance tare dakai."

Haka dukkanin su suka kasance cikin rudani kowa na fadan tare yake da wani yayinda kuwa,ba haka bane there all alone duk wannan sherrine na wannan Daki da suka kasance ciki.

"Enough guys,Hakan na nuna wannan guri na cike da mutanen boye Dan haka muyi taka tsantsan."

Aiko furta hakan da Hafsa tayi keda wuya sai sukaji wani iska Mai cike da ni'ima ta buso yayinda duk suka manta abinda suke tattaunawar akai kowa ya soma tambayan Dan uwansa "what am I saying?." Kowa haka ya mance abinda ya faru dasu kafin su hade Amma Kuma suna sane da mission nasu.

Haka fa Amrita ta haska musu hanya har ta kaisu ga jakar daya daga cikinsu Wanda ke dauke da touch light..
Haka dukkanin su suka dauki daya daya,haske gurin sukayi Pau inda suffar gurin tayi daidai da cikin kogon dutse haka Kuma lanya daya Tak takeda wacce suke fuskanta.

Haka suka soma tafiya suka tsusa Kai cikin kogon inda da kaiwarsu wani guri fitilon zamani dake hannun su ta farfashe hasken ta dauke haka zalika wayoyinsu..

Wasu sanduna ne da aka rataya jikin bango ne ke kunna kansu suna Kuma daukewa yadda kasan fitular da kerosin tayiwa karanci.

Yayinda hasken ta tashi Koda allurane ta Fadi maka zaka tsincin kayanka yayinda ta dauke ko duhun ta Babu abinda zaka kwatanta dashi.

Md'ik haka hasken ta dauke yayinda tayi wasu Dakiku kafin ta dawo,dawowan hasken ko Adam ya hangi taron nasu mutane dake cen gabansu suna Kuma fuci kaikace horrors.

"Guys shin kuwa kunna ganin abinda Idanu na ke nunamin?."
Haka ya tambayi abokan tafiyar nasa yayinda hasken ta dauke...
But sukayi shiru suka kyaleshi,tashin wutan keda wuya ko ya tsinci kansa a taron wasu hallitu masu muni matuka,ga Kuma manyan Kaho dake kawunan su,jikinsu Kuma yadda kasan jikin *Mesa* 🐍

Bagidajiyar ihu Adam's din yayi bayan hasken ta sake daukewa....

Idan muka Laika bangaren su Atif kuwa,bayan daukewar hasken Al-Hussien ya kurama kasan gurin Ido Yana jirar lokacin da zaiji Nunfashin sa ta dauke Amma Kuma hakan bai faruba har tsahon Mintuna goma,dukda hakan bai cire tsammani daga mutuwa ba,but dayaga d'igon hawaye ya fada kan bayan hannunsa sai ya cike da mamaki...Danko hakan bai taba faruwa dashi ba.

Cikin sauri ya yunkura Hadi da furta cewar *am alive* Amma ganin halinda su Atif ke cikine yakasa jikinsa yayi sanyi...

Wannan haske dai ta warware wannan keji dasu Atif suka kasance a gargame ciki... Hakan ko abin Murna ne garesu domin there are free now but sai sukayi sukum...suna kallon halinda Tina Ali and Simon ke ciki...

Cikin sauri Al-Hussien din ya karasa wajen su inda yayi yunkurin duba halinda su Tina ke ciki... Amma sai yaji kukan mage cikin firgita ya juya hade da cewa.

"guys!!."

Atif idanunsa cike da kwalla yayinda ya jiyo muryar Al-Hussien ta dalilin haka ne ya juyo a fusace hade da cewa.

"Al-Hussien shin kasan maike faruwa a gurin Nan kuwa?, abokan tafiyar mune har uku suka sheka karau daya yayinda muka kasa yin Komi...."
Cikin muryar kuka yake furta hakan yayinda yafurta haka ko sai Samra ta zube akan gwiwowin ta,ta soma zubar kwalla.

Cikin fushi Atif yake Yima Al-Hussien ihu Yana gaggaya Masa abinda ke faruwa yayinda Al-Hussien din ke kokarin tsarar dashi but shi ya Riga yayi zafi..
Shako kwalar Al-Hussien ne ya sakashi mamaki domin kuwa Babu yadda za'ayi ya taba Ruhi...

Al-Hussien, mu'azz,Atif da sauran tawagar zura Idanu sukayi Dan mamaki....

"How possible?."
Abinda ya fito daga bakin Samra kenan.. Wanda yayi daidai da fashewar bangon dake kusa dasu...

Aiko tuni hankulansu ta koma kan wannan gurin...

Bakin hayakine ta soma bulbullowa ta ciki daga karsheko sukayi arba da taron 🐈 cats....
Jikinsu baki wuluk idanun su jajir hakwaran suko jini ne ke zubowa.

Cikin sauri Samra ta Mike hade da cewa....

"Guys Mai ya kamace mu,da muyi?."

"Run!!."

Haka Atif ya furta inda muzzaffar yayi cewa dashi...

"Are we going to leave abokan mu here?."

"We don't have much time."
Reply mu'azz.

"And we don't have choice."
Fadar Atif Bayan yaji fadar Mu'azz.

"Run!!."
Fadar Al-Hussien kenan suka ruga a guje....
Haka sukayi ta gudu yayinda cats din ke biye dasu,Aiko cen suka tadda wata kofa wacce take haske matuka tamkar tauraro.. Aiko Basu tsaya ko'ina sai cikin wannan kofa inda muzzaffar Atif da muka mu'azz sukaja kofan da karfin tsiya suka rufe..

Barinsu gurin keda wuya dukkan cats din suka bacce haka kuma Tina Ali and Simon suka bude Idanu birik👁️👁️tamkar kawowar utar lantarki...yayinda idanun nasu tayi jajir.

*_MUJE ZUWA_*

*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''


*_Ku kasance tare dani,Guys keep liking and commenting_*

+2349077974042





💀💀💀
*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*


*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣3️⃣*




"Are we going to leave abokan mu here?."

"We don't have much time."
Reply mu'azz.

"And we don't have a choice."
Fadar Atif Bayan yaji abinda Mu'azz ya furta.

"Run!!."
Al-Hussien ne ya sake furta hakan nan suka ruga a guje....
Haka sukayi ta guduwa yayinda cats din ke biye dasu,Aiko cen suka tadda wata kofa wacce take haske matuka tamkar tauraro.. Aiko Basu tsaya ko'ina sai cikin wannan kofa inda muzzaffar Atif da muka mu'azz sukaja kofan da karfin tsiya suka rufe..

Barinsu gurin keda wuya dukkan cats din suka bacce haka kuma Tina Ali and Simon suka bude Idanu birik👁️👁️tamkar kawowar utar lantarki...yayinda idanun nasu tayi jajir.

Mu'azz ne jagaba yayinda suka kasance cikin wannan kofa mai dan karen haske,da shigar su ko babu wanda ya naimi da'a tsaya domin kowanne daga cikin tunani yake akan wayencen mage(cats.) haka sukayi ta takawa yayinda Muzzaffar ya kasance a baya baya sabida soma jin jiri yayi bayan sun shafe wannan ɗan banzan gudu.

Aiko Yankar jiki yayi ya fadi kasa,nan da nan nunfashisa ta sauya,suko sauran abokan tafiyar nasa da shike baya suka basa basumasan lokacin da yayi hakan ba...har Saida sukayi nisa sosai kafin nan Mufy ta jiyo da Niyar ta dubi lafiyar sa....
Aiko buga ihu tayi bayan ta tadda bayan nasu babu kowa kuma babu alamarsa.

"Inane Kuma Muzzaffar ya shige?."
To wayake da Ansar da zai bata? babu domin duk kanninsu basusan lokacin da hakan ya faru ba.

"Wata kila a wajen kofar muka kyalesa."
Abinda Ya fito daga bakin Al-hussein kenan inda Samra tayi saurin mayar masa da cewa

"Noway,Bamu barosa a baya ba saboda lokacin da muka shigo wannan kofa he was standing next to me."
Bayan ta furta hakan sai Mu'azz yayi sauri cewa.

"That means bazaiyi Nisa da nan ba,we have to find him."

Aiko Koda dakika guda basu kara a gurin ba suka koma cikin saurin yayinda suke ambata sunan Muzzaffar din....
Cen sai Mufydah ta kwalla musu kira bayan ta hangi Muzzaffar din akwace kasa,aiko cikin kankanin lokaci suka risketa domin kuwa sun bazune a wannan guri dan gudun karya kasance ya shiga wani lungun na daban.

"Oh my God."
Abinda ya fito daga bakin Samra kenan inda Atif yayi gaggawar durkusawa yayinda yayi masa filo da Hannunsa Mufydah ko ta soma yi masa fifita.

"He's burning up,Ya kamata mu samo wani abu da zai saukar masa da tempure na jikinsa Danko zafin tayi tsamari."
Fadar Atif kenan inda Mu'azz yace dashi.

"Saifa ruwan nan da muka ketara ta ciki,domin shi na ɗiba kuma har yanzu yana nan."

Aiko da jiyo hakan sai ya kama bakin rigar dake jikinsa ya yaga izuwa tsumya sannan ya mikawa Mu'azz hannu hadi da cewa.

"Bani Ruwan."

"Noway Hakan bazaiyu ba Atif,kada ka manta fa ta cikin ruwan nan *Tina* ta dauki wannan cuta sai kuma gashi da tabawa daya tak tayi transfer izuwa jikin Muzzaffar ina ganin wannan ba shawara bane idan akace ayi anfani da wannan ruwan wajen saukar masa da tempure."
Fadar Samra kenan inda Atif ya anshi ruwan daga hannun Mu'azz ya jika tsummar dashi sannan ya soma gogewa Muzzaffar jikin nasa dashi.

"Samra na baki shawara,ki daina Furta mummunar abu akan komi da kika ga za'ayi anfani da shi domin yin haka kadai zaki bawa wayenda ke kokarin ganin bayan mu damar cutar damu,Dan haka dan Allah idan babu alheri a bakinki kiyi shiru."
Ansar da Atif ya Bata kenan,Itako ta haɗa fuska hadi da yunkurin cewa wani abun but sai Mu'azz ya tari nunfashi ta da cewa.

"Guys Have you notice that kwanakin mu biyu Kenan da shiga wanan guri amma babu ɗaya daga cikin mu wanda ya naimi abinci ko ruwa?."

"Nima abinda yake yimin Yawo kenan a brain nawa Amma nayi shiru ne dan kar ace na cika korafi."
Fadar Mufydah kenan inda Al-hussein yayi sauri cewa dasu.

"Uhm Gaskiya ne,Babu wanda zai ji yunwa ko ishi idan ya kasance a cikin wannan guri har na tsawon kwanaki uku."

"Tsawon kwanaki uku kuma,bayan nan fa toh?."
Tambayar da Mu'azz yayi kenan inda Al-hussein ya basa Ansar cewa.

"Kwana ta hudu zamu naimi abinda zamuci wanda zai rikemu na tsawon wani kwanaki ukun,idan kuma ba haka ba dukkanin mu zamu sheka izuwa barzahu."

Aiko da jiyo haka suka zura Idanu alamar mamaki.

*Al'amarin Amrita,Adam da kuma sauran abokan tafiyan nasu ko.*
"Guys shin kuwa kunna ganin abinda Idanu na ke nunamin kuwa?."
Haka Adam's ya tambaya But sukuwa sukayi shiru suka kyaleshi.
Kunnuwan wutan keda wuya Adam din ya tsinci kansa a taron wasu hallitu masu muni matuka,ga Kuma manyan Kaho dake goshin su,jikinsu Kuma yadda kasan jikin *Mesa* 🐍

Aikuwa ganin haka yasa Adam buga ihu tsiya yayinda wutar ta sake daukewa,Ji yayi an damke masa hannu ana kuma jijjiga shi kamar za'a cire masa kafaɗa ta cikin kunnuwansa kuma sautin ababen tsoro iri iri yake ta saurara.

Aiko sharara masa Tafi Amrita tayi bayan wutar ta dawo ta kuma tsaya...

"Are You Mad?,Adam maike damunka?."
Abinda Amrita ta furta ga Adam kenan,inda ya hau waige waige yana kuma fadin.

"Da wasu muggan halittu a nan gurin."

"Wacce tabbaci kake dashi?"
Fadar Harzad kenan inda Anwar yafashe da dariya hadi da cewa.

"Guys you know what?,a tunani na mazane sukafi rinjaye anan gurin but sai gashi it turns out to be maza biyune kacal anan gurin."
Haka ya furta cikin Muryar dariya,bayan ya kammala fadin hakanma saiya sake shekewa da muguwar Dariya inda Harzad shima ya basa nasa bayanin shima kuma ya soma dariya, but da sukaga Amrita ta haɗa fuska hadi da jiyowa ta kura musu Idanu sai sukayi shiru amma cen sai itama ta fashe da dariya hadi da cewa.

"Da wasu muggan halittu anan gurin."
Cikin Muryar naiman tsokana ta furta hakan,inda suka ci-gaba da sheka dariya hadi da kyakkyawa.

Ganin haka yasa Hafsa tsaki hadi da Karasawa wajen Adam dake zaune kasa tace dashi..

"Mai ka gani?."

Aikuwa cikin kankanin lokaci ya bayyana mata suffar abinda ya gani nan saita yunkura tsaye hadi da cewa.

"Guys ina son ku dakatar da wannan shashanci naku domin ba abinda ya kawo mu nan gurin ba kenan,Karku manta mun rasa abokan tafiyanmu a baya dan haka komi ma zai iyya faruwa da kowa dake nan dan haka dariyan ɗaya daga cikin mu ba abu bane mai kyau kamata yayi mu bar Wannan guri."
Haka suka tsuge baki Itako ta mikawa Adam hannu ya mike tsaye.

"Ok here we go."
Harzad ne ya furta hakan inda Anwar yaja fito hadi da sosa keya.

"Amrita! Muje ko."
Aiko fadar haka sai tayi daidai da taka step da tayi nan da nan ƙafarta ta shige sulub yayinda suka jiyo wata kara tamkar ana rufe kogo da katon Dutse.
Aiko bayan nan saika kifiyoyi biyu sun baiyana cikin zafin nama da alamun wannan sune tarkon da hafsa ta taka,aiko dojesu sukayi."

"Guys watch Your steps."
Fadar Hafsa kenan yayinda ta bushe guri guda.

Idan muka sake lekawa bangarensu Atif kuwa zamu tadda su yayinda suke tattaunawa....

"Kwana na hudu zamu naimi abinda zamuci,idan kuma ba haka ba dukkanin mu zamu sheka izuwa barzahu."

Aiko da jiyo haka suka zura Idanu alamar mamaki.

"Guys Ku duba,Muzzaffar na kakkarwa."
Abinda Mufy ta furta kenan inda Samra ta juya kallonta izuwa kan Muzzaffar.

"Ya kamata mu hada masa wuta domin ya dan sami ɗumi."
Fadar Samra kenan inda Mufy ta mayar mata da cewa.

"Ya kamata mu Duba ko zamu Sami itatuwa mu hada wutar dashi."

"Eh gaskiya kam Ni zan ɗan zaga ko zan samu."
Fadar Mu'azz kenan inda Al-hussein yace dashi.

"Zanbika muje tare."
Haka ya furta hadi da yunkurawa sai yajiyo Muryar Samra na cewa.

"No Zan bisa mu tafi tare,kayi zaman ka Al-hussein."
Kowa dake wannan guri yasan da manufa ta furta hakan amma tunda bata baiyana ba waye zai san nufin ta.

"Samra Ni da Mu'azz zamuje mu Duba itacen,dan haka tayani duba lafiyar Muzzaffar."

"Ok tunda kace hakan shi za'ayi Atif."

Aiko babu bata lokaci ya mike tsaye suka wuce tare da Mu'azz suka kyale Samra, Mufy Al-hussein sai kuma Muzzaffar dake kwance.

Mu'azz tare da Atif sukayi ta tafiya wacce kwata kwata itatuwan da suka samu bai wuci sanda biyu ba hakan yasa sukayi ta tafiya suna mai fira da juna.

Aiko cikin wannan tafiya sukayi karo da wata lambu wacce kayan ɗanyene iri daban daban ne a ciki....
Aiko cikin mamaki Atif yayi furucin wow inda Mu'azz ko jikinsa bata basa inda suke tsaye ba.

"Tayaya Kuma lambu a cikin kogo."
Akasan zuci ya furta hakan inda Atif yaje gurin da sauri hadi da cewa.

"Gaskiya gurin nan ya Matukar hadu, komai kake bukata ina mai kyautata zaton zaka samu Anan."
Aiko hakan daya furta daidai da kai hannunsa yayi domin ya ciro kayan ɗayen.

"Atif!."
Cikin kara Mu'azz ya furta hakan yayinda yaje gurin da sauri ya tureshi suka fadi kasa.

Aiko Gurin nan da Atif ke kokarin kai hannunsa ta dawo wata ƙatuwar hawainiya (camelion) 🦎 Ganin haka da Atif yayi saiya yunkura cikin sauri hadi da reke hannun Mu'azz cikin tsoro.

Fashewa Mu'azz yayi da dariya hadi kuma da cewa....

"Hawainiyace fa kawai."
Aiko fadar hakan keda wuya sai dukkanin ciyayin cikin lambun suka rikiɗe saiga taron chemilion.

"Oh my God."
Fadar Atif kenan inda ya sake riko hannun nasa da karfin tsiya....

"Atif Aiko hawainiya kullum cikin slow motion suke kaga kenan bazasu iyya cutar da mu ba."

"A'a dai Mu'azz nasa iyya launi suke iyya juyawa taya suko suka iyya juya halittar su haka."
Ansar da Atif ya basa kenan inda kuma ya ɗaga fuska ya kalli cikin idanun sa.

"Kumafa gaskiya ne,Gaskiya ya kamata mu koma tun kafin su fahimci muna na."

Aiko daukar step daya da sukayi sai wayennan ƴan kananan halittu suka fara tafiya cikin sauri kaikace harbasu akeyi aiko Ganin haka yasa Mu'azz ya kama hannun Atif suka ruga a guje.

Aiko cikin kan kankanin lokaci sukayi masu Atif zobe nan suka take biriki Inda wayennan halittu suka soma karasowa wajensu ahankali.

Aiko ƙasa sanin Mai zasuyi ne yasaka su tsayawa guri guda,nan sai sukaji dirar wani a gefensu hannunsa kuma wata ƙatuwar barkoce wacce ya kunna wuta akai tana ci kaikace runbun kara aiko basu san lokacin da wayenan halittu suka ja da baya ba.

"You have to follow me."
Aiko Forzy suka tarar...

"Forzy!."
haka suka furta cikin hadin baki aiko tuni ta mayar musu da martani cewa

"Eh Nice,Muje."

Haka suka bita a baya ba tare da sunsan inda suka nufa ba aiko kaiwa wata kofa tayi yayinda halittun ke biye dasu..

"Babu ta yadda zamuyi mu shige wannan bayan kasan mun baro abokan tafiyanmu a baya."
Fadar Atif inda Forzy ta basa Ansar cewa..

"To munada wata mafitan ne bayan wannan,idan muka tsaya daga zarar sun cijeka bushewa zakayi ka dawo gunki,dan haka dole mu shige."
Aiko bayan ta furta hakan ta riko hannunsa suka shige cikin kofar.

Aiko shigarsu kofar suka rufe yayinda camelion 🦎 da suka baro a baya ko suka fara harhadewa guri guda.
Bayan sun kammala hakan suka rikiɗe suka dawo bishiya mai cike da arbakatun Allah ajiki.

Cikin kofar da Atif suka shige ko bayan sun tsinci kansu a cikin wannan kofa ne yasa Forzy ta cika masa hannu.

Bayan ta saki hannun nasa ko ya ɗaga inda ya tarar da shafin hannu Forzy ya dawo Kore shar wacce tayi daidai da wannan koren haske daya shige jikin Muzzaffar.
Aiko ganin haka yasakashi zura Idanu dan mamaki.


*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''


*_Ku kasance tare dani,Guys keep liking and commenting_*

+2349077974042

💀💀💀
*KOFAR AJALI*


Please Login or Register in order to submit comment