Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su Hafsa da sauran abokan tafiyan nasu dake tsaye kallon wa 'yan nan halittu...

Kamar yadda suka tsaya kallon wa 'yan nan halittu haka suma suka tsaya kallon su bayan sun gama fitowa daga cikin fasassun tukwanen,ganin haka ya bawa Anwar bakin fadar cewa.

"Guys karmuyi gaggawan farmakar su,tayu wani abun ne suka zo naima na daban mu cigaba da tsayawa a hakan har sai sun naimi su cutar damu kafin mu kare kan mu.."

"What Are You talking about Anwar Kaine fa Wanda ya fara ambato halaka a garemu yayin da kayi arba da wa 'yan nan halittu sannan kuma yanzu kane ka iyya gano ba zuwa sukayi domin su cutar da mu ba?."
Fadar Harzad kenan inda Hafsa tayi saurin cewa.

"Tayu He's right,if not bazasu tsaya kallon mu haka ba, kamar yadda Anwar ya fada haka nima zan maimata karmu zama mune muka fara tada rigima a tsakani, mu kasance masu kare kawunanmu idan sunso cutar damu."

"But i didn't get it!,Taya zamu tsaya kallon ruwa kwado yayi mana kafa, ya kamata mu gaggauta barin nan tun kafin su cutar damu."

Aiko fadar hakan keda wuya spiders din suka fara taku yayinda suka wuce inda Hafsa Anwar da kuma Harzad ke tsaye ba tare da sun cutar da suba hakan yasa su Hafsa suka bisu da kallo yayin da suka fahimci sunyo inda Adam da kuma Amry ke zaune, aiko da isarsu wannan guri suka fara hayewa kan Gangar jikin Amry yayin da suke kokari nannade ta cikin *Yana* ganin hakan yasa Adam ya fara turesu suna zubewa daga jikin Amry amma duk da haka basu daina hayewa jikin nata ba...

"Tirkashi!."
Furucin Hafsa kenan inda Harzad ya furta cewa...

"I'm very sure sun zo nan ne sabida ita."

Aiko nan suka fahimci hakan domin gani sukayi basa cutar da kowa illa nannade Amry da suke kokarin yi suka sa a gaba..... Adam ko yana iyakan kokari wajen ganin ya farfaɗo da Amrita Sannan ya Kuma kare ta daga spiders din Amma ina babu wanda yayi nasara a kai domin kuwa Amrita bude idanu tayi na Yan dakiku ta sake komawa yanayin suma,haka kuma spiders Saida Suka nannade ta cikin yanar yadda kasan likkafani kafin nan suka soma yunkurin tafiya da ita.

Adam ganin suna kokarin tafiya da ita ne ya saka shi fusata nan ya soma bubbuge su har lahira,yayin da kuma yake anfani da tafin hannu wajen aiwatar da hakan,aikuwa ganin zai iyya hanasu aiwatar da aikin sune yasa suma suka fusata suma sukayi anfani da yana wajen daure shi jikin rufi na wannan daki,domin kuwa farat daya ya ganshi marne jikin bango na saman wannan daki....

Adam sai kokarin kubutar da kansa ya keyi yayin da yake kiran sunan Amrita cikin Muryar kuka... Al'amarin Hafsa,Harun da kuma Harzad kuwa tsaye suke suna kallon duk abinda ke faruwa kuma sai da suka ga faruwar hakan ne kafin nan sukayi yunkurin kai tallafi,aiko suma tsintar kansu sukayi zagaye da yana wacce hakan ta faru ne bayan spiders din sun fahimci suma suna shirin afka musu...

a garkame suka tsinci kansu cikin yanar wacce ta kasance kamar keji haka wannan yanar ta kewaye su,a iyakan tunani na gizo gizo yakan dauki lokaci wajen sakar gidan sa amma sai gashi daidai da kibtawar ido suka tsinci kansu a wannan saka na gizo...

Adam sai kokari kubutar da kansa yake yayin da kuma wa 'yan nan halittu ke kokarin tafiya da Amrita ganin haka yasa Hafsa amfani da tafin hannu wajen ganin ta yaye wannan yanar da suka kasance cikin amma kuwa buga salati tayi cikin kara inda Harzad da kuma Anwar Suka kai idanun su Gurin.

"Hafsa You Are bleeding!."
Haka Anwar ya furta bayan yayi arba da hannun Hafsa inda kuma Yayi saurin tambayar ta cewa.

"Taya hakan ya faru?."

Kara Hafsa ta sake bugawa cikin siririyar murya alamar tanashan Raɗadi sannan tace dashi...

"Wannan yanar badai kaifi ba!."
Fadar Hafsa kenan inda Harzad yayi sauri wajen ganin ya tsayar da zubar jinin,shiko Harun dake lullube a fatar Anwar tsaye yake gefe guda yayin da ya nade hannaye yana kallon su... Sannan ya soma cewa.

"Idan har wannan yanar tana da tsananin kaifi da zata iyya tsaga fadar bil adama,kenan taya zamu kubutar da kanmu daga cikin ta?."
Fadarsa kenan inda Harzad ya dago Idanu ya kalle sa yayin da kuma yake kokarin nannadewa Hafsa Raunin nata yace.

"Anwar Dan Allah ko zaka iyya kame baki kayi mana shiru?."

"Why would I do that?." Fadar Anwar

"Sabida ka cika mana kunne da fatar mutuwa a gare mu a kowani irin lokacin,and idan bazaka iyya fadar alheri ba can you please stay quiet!."
Haka Harzad din ya furta cikin ɓacin rai inda Hafsa ta ɗan dafe masa hannu alamar ya sassauta batu nasa amma ina shiko ya dau zafi domin kuwa sake cewa yayi...

"Mai yasa Hafsa,mai yasa har yanzu kike kokari goya masa baya, bayan ya sauya daga Anwar din da muka sani, Anwar baya taba nuna damuwa akan halin da zai shiga fiye dana mutane,Anwar kafin ya damu da kansa saiya tabbatar babu wani wanda ke cikin hali na damuwa a kusa dashi,Anwar baya tabba tsayawa gefe ya zuba ido yana kallon jini yana zuba daga jikin mutum ba tare da ya zubar da kwalla kuma yayi kokarin tallafawa maishi ba Hafsa,amma kiga yadda Ansar dinmu ya sauya!, tsaye yake gefe guda yayinda kike zubar da jini baima damu da halin da kike ciki ba."
Fadar hakan yake yi cikin fushi yayinda ya daga murya sannan ya kasance yana nuni a kan Anwar da yatsa,aiko bayan ya kammala fadar hakan sai Hafsa ta dago Idanu ta kalli fuskan Anwar Yayin da taga ya hade rai sannan ya ciko Idanu da kwalla sannan tace da Harzad.

"I'm really sorry Harzad ya Kamata ka kwantar da hankalin ka,kana cikin fushi shiyasa kake ganin duk wannan, amma gaskiyan magana Anwar still care for us,zafin kaine yasa duk faruwan hakan kuma zata wuce, abinda nake so dakai yanzu shine ka kwantar da hankali and you too Anwar kaima kayi hakuri kaji."
Aiko da jiyo wannan kalma ta hakuri kwalla ta zubowa Anwar batare da yace komi ba ya juya musu baya alamar ransa ya ɓaci, Hafsa tayi yunkurin mikewa taje gare sa amma sai taji Harzad ya rike mata hannu sannan ya girgiza kai alamar ta kyaleshi...

Anwar cikin ɓacin rai ya dunkule hannayen sa nan kuwa sai iyya saman hannun sa ya soma fitar da wata bakar hayaki yayin da kuma jijiyoyi suka baiyana a hannayen nasa da kuma goshin sannan kuma idonsa daya ta soma zubar da kwallar jini aiko nan sai Hafsa da Harzad sukaga wannan yanar ta soma matsowa yayin da gurin ta dau girgiza kai kace kasa zata tsage ta nitsar dasu baki daya haka kuma kamar kowani bango na wannan yana zana kokarin hade da juna......

ganin hakan da Hafsa tayi yasa tayi saurin ankarar da Harzad shiko Harzad babu wanda ya fara kai idanunsa kansa illa Anwar dake tsaye saura kiris wannan yana ta iske sa nan ya yunkura ya jawo sa da karfin tsiya ya rungume sa alamar bayason wannan yanar ta cutar dashi kuma idan hakan ta zamanto dole tofa saidai ta fara ta kansa kafin Anwar...

Aikuwa suna cikin wannan hali sai sukaji an tsaga gefe daya na wannan yana inda suka kai idanun su gurin,Adam suka tarar a tsaye inda yace dasu.

"This Way!."

ATIF
Idan muka sake komawa bangaren su Atif kuwa zamu riske su a daidai lokacin da wannan kyakkyawan yarinya ta mike tsaye fuskanta ko cike da annashuwa sannan tace dasu

"Mu'azz, Atif ya rigaka samun wannan labari kamar yadda ya rigaka zuwa nan gurin, sannan game da tambayoyin da kayi babu ko daya da zan iyya amsa maka shi domin bani da daman yin hakan,ina ganin yadda aka tsarata shine zaku samu kowani irin tarihin da kuke da bukata a sa'in da kuke wannan aiki."
Bayan tazo nan a zancen ta sai Mu'azz yayi sukum alamar yana jimami itako ganin hakan yasa ta sake da cewa..

"Kafin na kawo karshen wannan fira tamu zanso na gwada muku wani abun dan haka ku biyo ni muje."
Bayan ta furta hakan ne ta soma taku yayinda suke biye da ita abaya, aiko saida suka kai wani irin guri mai wuyar sha'ani kafin nan ta take biriki, Atif da Mu'azz ko tuni hanjin cikin su ta kaɗa yayinda wannan guri kuwa tayi kama da shekar Aljanu,kasan wannan guri kuwa rami ne wanda babu karshen ta yayinda kuma jikin bango na wannan guri jijiyoyin bishiyoyi ne a nannade ko'ina,nan sai ta juyo suka fuskanci juna sannan ta soma cewa.

"wannan ne al'ummata sannan kuma ahalina,mun kasance kullum cikin fargaba da kuma tsoron farmaki daga bakaken Aljanu, mun shafe ɗunbum shekaru muna a wannan guri yayin da muke jiran ranar da wasu zasuzo harnan da niyar citon rayukan mu amma kowace rana zuwa take ta kuma wuce ba tare da mun jiyo sautin kowa ba,nasan a tunanin ku zuwan ku nan bata da wani amfani amma kuma a zahiran ce zuwan naku wannan guri zata ceci duniya daga fadawa Halaka,Atif, Mu'azz wannan aiki tana rataye ne a kafadun ku dan haka ku kokarta wajen ganin kun riga Harun samo wannan kogon kan da kuma Dutse hasken!."
Bayan ta kawo karshen batun nan saita daga tafin hannu aiko nan Mu'azz da Atif suka fara ganin dubun mutane dake wannan guri wanda take alakantawa da al'ummar ta.

Bude baki Atif yayi dan mamaki domin ko'ina ka juya idanu su zaka gani jikin wannan jijiyoyin bishiyoyi dake marne jikin bango din,nan suke sai ga wata wacce kusan kamar su daya da yarinyan nan wanda take yiwa su Atif jagora... Zuwan ta inda suke ta soma cewa.

"Lokacin da aka dibar mana ta kusa karewa."
Bayan ta furta hakan sai ta bude tafin hanun aiko saiga abin irga lokacin ya baiyana a tafin hannun ta, bayan dukkanin su sun sa ido kuwa sata dauke kafin nan ta sake cewa da wannan kyakkyawan yarinya.

"Ya kamata mu mayar dasu tunkan lokacin yin hakan ta kure."
Wannan sabuwar yarinya ne ta furta hakan yayin da Atif ya kura mata idanu hade da mamaki cen saita sake cewa.

"Abinda ya rage shine mu mayar dasu sannan mu cika musu burinsu guda daya tak acikin wannan guri dan hakan zaku iyya rokon abun guda daya mu kuma mu tabbatar mun cika muku shi."

FORZY
"The only and best solution we have shine mu ruga a guje!."

"What?." Tambayan da Samra tayi kenan bayan ta jiyo furucin Forzy.

"Run!."
Haka ta sake maimaita mata sannan tasa hannun tayi sama da Mufyda aiko a gadon bayanta ta sauka yayin da Muzzaffar shima yayi hakan ga Al-hussein aiko Faruwan haka ne tayi matukar rudar da Samra ganin ta kasa taɓa jikin Al-hussein amma gashi Muzzaffar hadda goya shi....

Aiko tamkar walkiya saiga Ali ya dire a gaban su haka suka sake juyawa nan ma suka sake tarar shi, nan ne ido ya raina fata domin kuwa zubar da kayan yaki sukayi domin irin wannan ne akewa ikirari da Fight or die...

Taku Ali yake yana tunkaro su yayinda Samra, Forzy da kuma Muzzaffar ke jada baya wa 'yan nan lodi lodin zuma dake biye da Ali kuwa sai famar yiyo gaba suke suna jiran kawai a basu dama su afka musu...

"Babu inda zaku iya samun mafaka daga bala'ina sannan kuma babu mahalukin daya Issa ya kwato ku daga ukuba ta a yau,babu makawa sai kun dandana bak'ar ukuba ta!."
Cikin sautin murya uku uku Ali ke furta hakan yayin da Su Samra suka saurari hakan kuwa sai hanjin cikin su ta kaɗa domin kuwa yadda yake wannan batu kadai abin ban tsoro ne...

Aikuwa budar bakin Forzy ta fara fadar cewa...
"Tabba da akwai mafaka a gare mu sannan da akwai wanda zai iyya ceton mu daga makirci irin naka mai bakar aniya."

"Tabbas wannan haka take domin kuwa Allahu subhanahu wata'ala yana gaggauta amsa Addu'ar wanda aka ciwa zarafi, idan har kana tunanin kafi karfin mu Toh bakafi karfin mahaliccin mu ba."

Kukan kura Ali yayi sa'anan yabi bayanta da muguwar dariya bayan yaga tsoro a cikin idanun su Forzy... Aiko sake mikar da hannayen yayi a karo na biyu yayin da taron zuman nan suka fara yunkurin kai farmaki ga su Forzyn,aikuwa nan da nan sai suka ga yanayin gurin ya sauya yayin da saman wannan guri yayi baki wuluk yadda kasan Hadari haka yakasance....

Tsawa hade da walkiya ne ke faruwa a wannan guri sannan kuma idan akayi walkiya ta sauka kasa duk abinda ta samu ta narkarwa take.... Ganin haka yasa duk hankula su ta dagule hatta Ali domin shima baisan dalilin faruwan hakan ba.

Fitulun Gurin haka suka daddauke gurin ya dau matuƙar hudu,aiko cirkwa cirkwa sukayi suna ta waige waige hade da mamaki faruwan hakan taya hadiri mai cike da walkiya zata faru a cikin daki?.

Babu amsa da suke dashi daga su har Ali,har sai da sukayi ido hudu da masu alhakin faruwan hakan wato wasu kyawawan ƴan mata guda biyu da suke tafe cikin kasaita yayin da kuma suka kasance sanye suke da fararen kaya.

Daga cen nesa suke tahowa yayin da duk inda suka ratsa sai hasken fitulun su kawo, haɗa fuska Ali yayi bayan yayi arba da mutane biyu dake biye da wa 'yan nan kyawawan ƴan mata,ba kowa bane wa 'yan nan illa Atif da Mu'azz.

Ganin hakan ya saka shi mikar da hannayen sa gaba hadi da bawa taron zuman nan umurnin kai musu farmaki,aiko ganin hakan yasa daya daga cikin ƴan matan ta ɗaga tafin hannun ta daya nan da nan sai wani farin haske mai dauke da kara mai razanarwa ya baiyana yayin da saukar sako ya dire a tsakiyan taron zuman nan,aiko tuni suka fara konewa hatta wayenda ke nesa da gurin suma suka kone kurmus, Ali shima ba'a barshi haka nan ba domin kuwa dayan yarinyan itama ta gwada nata karfin tsafin wajen dokar kasa da sawunta ta tashi sama, faruwan hakan keda wuya gurin ya hargitse da tsawa hadi da walkiya.....

Dukda wannan abubuwa dake faruwa Atif da Mu'azz basu tsaya da takun da suke ba,haka suka cigaba da takun suna tunkaro inda Samra, Forzy da sauran abokan tafiya nasu ke tsaye....

Ɓangaren su Harzad kuwa suna cikin hali na ƙaƙanikayi sai sukaji an tsaga gefe daya na wannan yana inda suka kai idanun su gurin aiko tarar da Adam sukayi tsaye inda yace dasu.

"This Way!."

A guje suka fice daga cikin wannan Yana,fitarsu kuwa suka ruga a guje ta sanadiyyar sunga ginin na kokari nutsewa dasu.... a sa'in da suke wannan gudu kuwa haka manyan duwatsu sukayi ta fadowa daga saman wannan guri....

Sun sha da kyar kafin suka tsinci kansu a wata kofa wanda acikin wannan kofa ko'ina ka duba kwai zaka tarar birjik zube cikin ta,ko ina ka sa idanu su zaka tarar..... Saman wannan daki kuwa mutane ne da dama aka rataye su a saman gurin yayin da aka nannade su cikin yana kamar yadda aka yiwa Amrita....

Bude baki sukayi dan mamaki a sa'in da sukaga wannan abu nan Hafsa tayi furucin cewa...

"Hakan na nuna cewa wa 'yan nan halittu sunyi awun gaba da dubbanin mutane!."
Fadar ta Kenan inda Harzad yayi furucin cewa

"Babu ta yadda za'ayi su kame mutane kawai dansu shanya su a wannan gurin,gaskiya da abinda suke shiryawa!."

Aikuwa bayan sun jiyo wannan furuci na Harzad sai suka cika da mamaki hadi da Daga idanu suka kai sama suna kallo taron mutanen nan dake a rataye.

*MU HADU A EPISODE MAI ZUWA*



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment