Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fuskan ta.

Lumshe idanu Forzy tayi hadi da ɗago hannu tana kokarin kare fuskan ta domin bata da mafitan datafi wannan,tsit tayi tana jiran saukan wannan abin a fuskan nata,aiko nan sai naga anyiwa wannan halitta kafa yadda kasan ball aka samu haka akayi anfani da high_shoot wajen buge shi ya fadi a wajen wannan zagaye na wuta.

Bude baki Samra tayi dan mamaki domin kuwa bata tsammaci haka zai faru ba,shiko wannan wanda yayi anfani da kafa wajen buge wannan halitta ya dire kan gwiwowin sa.

Hm Ba kowa bane wannan illa Muzzaffar wanda ya farka daga sumar da yayi lokacin da Forzy take fafatawa da wayennan halittu...
sautin direwar tasa ne yasa Forzy bude idanu bayan tayi arba da hakan ne sai ta juya cikin salo tayi anfani da wannan karfe da take rike dashi ta juya ta harbi ɗayan nan daya sauka cikin wannan zagaye na wuta,aiko Sa'a tayi wajen samun sa a tsakiyan ka nan ya soma Shure Shure mutuwa.... tsayuwa kallon sa sukayi harya sheka,ganin hakan yasa Forzy juyowa suka hada ido da Muzzaffar.

"Forzy!."
"Muzzaffar."
Kalmomin da suka iyya ambatawa kenan,bayan nan suka tsaya kallon cikin idanun juna.. Aiko jiyo Samra ta yiyo salati ne yasa su juyo idanu zuwa kanta inda suka fahimci wani abinne ta hango,koda da suka kai idanu inda take kallon kuwa sai sukayi tauzali da wannan ƴar karamar yarinya tsaye tsakiyan halittun.

Forzy da ganin fuskan wannan yarinya kuwa babu abinda ya fado mata a kaa illa fuskan Ahmad yayinda take cike da annashuwa,daga karshe ta tuno yadda wannan ƴar tayi ajalin Ahmed tare da yimata barazanar kashe ta nan saita hada fuska dan bakin ciki..

Wannan yarinya kuwa ta juya bayan sun haɗa fuska Forzy ta soma taku ta koma inda ta fito,aiko bayan wucewar ta wayennan halittu suma suka jujjuya suka bar wannan guri... Barin su wannan guri kuwa keda wuya wannan zagaye na wuta ya soma kafewa a hankali daga karshe ya dauke baki ɗaya... Nan sai Forzy taiyo kan Mufy da sauri tasa yatsunta biyu a gefen wuyan ta na wasu dakiku kafin nan tace dasu Muzzaffar.

"Nunfashi ta baya tafiya amma kuma zuciyar ta na bugawa!."

"What do you mean,Taya zuciyarta zata buga bayan bata nunfashi?"
Tambayan da Samra tayiwa Forzy kenan inda Muzzaffar ko yayi sauri gurin cewa.

"Impossible?"

Suna tsaka da wannan zance sai suka soma jiyo wani sauti mai kama da kukan kananun kwari,aiko jiyo hakan yasa Muzzaffar ya kame baki yayi shiru inda Samra tayi gaggawa wajen tambaya "what is this sound?" Tambayan da taiyo kenan inda Forzy tayi mata alamar tayi shiru.

shirun sukayi baki daya suna sauraron wannan sauti yayinda kuma wannan sauti ke dadda karuwa,cen sai Muzzaffar ya hango Ali tafe cikin kasaita yayinda ya mikar da hannayen sa biyu ya kuma baje ƴan yatsun,aiko saiga lodi lodin kuɗan zuma a bayan yayinda suka taru suna kuma biye dashi yadda kasan guguwa yayinda take tashiwa tana kuma bubbudewa haka suka kasance...

Aiko cikin tsoro,firgici da kuma mamaki dukkanin su suka jiyo idanu suna fuskantan sa, domin daga ganin yadda yake cika yana batsewa kasan shi yake juya wayennan halittu...

ADAM
Idan muka gagara bangaren su Amrita tare da Adam kuwa zamu tarar da su yayinda suke taku cikin yanayi na dafe dafe sannan kuma suna rike da hannayen juna.

"Anwar ka kula!."
Cewar Harzad kenan inda Anwar ya ɗago idanu cike da kwalla yana kallon sa ganin bashi da damar amsa masa,Aiko anan Harun yayi gajeriyar murmushi sannan Yace da Harzad a madadin Anwar.

"Nagode Harzad,kuma zan cigaba da"
Aiko haka Harun ya soma furtawa but sai yajiyo Amrita ta kwarma bagidajiyar kara kafin ya ankare kuwa tuni yaji gwiwowinsa sun sauka kasa ta sanadiyyar jansa da akayi da karfin tsiya...

wannan namijin jawosan da akayi bata tsaya nan ba domin bayan sauka da yayi kan gwiwowinsa haka aka cigaba da jansa gaba, aiko cikin sauri ya ɗago idanu inda ya tarar da Hafsa ita kadai ne a gurin kuma tana a durkushe wanda hakan ya tabbatar masa da rami Adam da Amry Suka fada wacce nawi sune ke kokarin jawosu ciki,ai kuwa saida hakan ta faru kafin suka fahimci a kan tsohuwan gada suke tafe akai wacce ta kasance a karye a tsakiya...

Amrita Razanan da tayi ne yasa ta jefar da wannan sanda da take rike dashi a hannu wacce saukan sandan kasan guri ne yasa na iyya ganin zurfin gurin ɗan kuwa wannan sanda ya dauki lokaci yayin fadawa kasan wannan guri.

"Guys I can't hold it for so long!."
Haka Hafsa ta furta cikin kara,Harzad ko da jiyo hakan ya zage dantse wajen tokare kansa da maruka na wannan gada, wacce yin hakan ta karfafawa Hafsa.

"Amrita!,Adam! Hold it tight."
Haka Harzad din ya furta inda Hafsa ta soma kirawo sunan Amrita kamar haka.

"Amrita! Amrita! Amrita!."

Aiko Saida ta jiyo muryan Amrita tace "I can't feel my legs." kafin nan ta soma kokari wajen jawo su sama amma ina taya zata iyya hakan da hannun ta daya... Kara tayi Ahhh! Dan raɗadin da take ji nan sai ta furta cewa...

"Guys gaskiya Bazan iyya janyo su sama ba!."
Cikin kara ta furta hakan shiko Harzad da jiyo haka ya saki hannun Harun wanda yake tsammanin Anwar ne sannan Yace dashi.

"Anwar jeka ka tallafa musu,yi sauri."
Shiru Harun din Yayinda ya haɗa Fuska yana kallon Harzad,aiko nan sai Anwar ya iyya kwato hannun sa daga Harun ba tare dashi Harun din yace komi ba kawai dara buga masa harara sai ya maida kallon nasa kan Harzad bayan nan ya soma dafe dafe da gaske baya ganin har yajega Hafsa...

Nan ne Anwar ya samu dama hade da zurfafa tunanin game da yadda zaibi ya fahimtar da abokan tafiyan nasa halin da yake a ciki... nan sai wani shawara ya fado masa wanda yake tunanin itace hanyar da zata kubutar da abokan tafiyan nasa daga wannan cuta ta makanta..

Still a tsayen yake yana ta nazari,bayan wasu sa'o'i kuwa sai fuskan sa ta cike da fara'a sa'annan ya juya idanu Izuwa kan fitulun da suke rataye a jikin bango da suka baro a baya, aiko nan da nan ya juya ya karasa gurin a guje,da zuwan sa gurin kuwa yayi kokarin sa hannu ya zaro wannan sanda wuta amma sai ya gagara yin hakan.... Haka ya dauki lokaci yana kokarin ganin ya ciro wannan fitila amma ina hakan baiyi ba sai daga karshe ta fado ta dalilin kai hannu da yayi gurin cikin fushi....

Da shike a kwai wasu irin nau'in ciyayi a gurin haka ta haddasa mummunar hayaki mai kashe idanu da kuma sata zubar da kwalla... Ganin yayi nasaran tada hayakin ya sakashi murmushi hade da juyawa ya koma inda ya baro abokan nasa... Aiko tunkan ya karasa gurin wannan Hayakin ya rugasa zuwa yayinda ya mamaye ilahirin gurin,cike da annashuwa ya karasa wannan guri but then ya cike da mamaki ganin babu kowa a gurin....

Tsaye yake yana ta juya idanu zuciyarsa cike fal da burin ganin inda suka shige... Tsayen yake sai ya soma jiyo wata kara kamar na tsagewan dutse na tashi... Aiko ba komai bane mai bada wannan sauti illa gadan nan da take tsaye akai ne take tsastsagewa,rushewa gurin ya soma wacce hakan ne ta tabbatar masa da karyewa gadan tayi dasu Harzad,aiko kan yace kobo gadan ya soma karyewa yana kuma zubewa cikin wannan Rami.

Aguje ya juya yana gudu Bayan sa kuwa gadan ne ke sauka tana kuma tada bakar kura, haka yayin ta guduwan amma daga karshe Kuran ta tullube shi.

ATIF
"Wai har sai yaushe zaku fara gane irin Wannan makircin ne eaye?"
Tambayan da wannan macijiya tayiwa Mu'azz kenan, bayan nan ta sake da cewa...

"ka biyo ni muje,ko kuma irin ta dubu su baiyana suyi Romon ka."hakan ta furta yayinda take kallon cikin idanun sa Bayan ta fadi hakan kuwa saita komo suffar ta na ainahi wato macijiya ta wuce Mu'azz ko ya bita a baya.

Haka suka cigaba da tafiya yayinda suka sa wata ƙatuwar katanga a gaba,sai da sukayi kusa da wannan bango sai wannan macijiya ta sake rikidewa ta dawo suffar mutum yayinda kuma ta budi baki tace da Mu'azz "Keep moving and don't stop!."

"What?."
Cikin rudewa Mu'azz yayi wannan furucin ganin bangone suke fuskanta amma ance dashi kada ya dakata... itako Juyo Fuska tayi yayinda take taku cikin kasaita ta sake maimaita cewan "kada ka dakata."

Toh Ya ya iyya haka yayi kamar yadda wannan macijiya ta umurta aiko isarsu jikin wannan bango sai suka ratsa ta cikin yadda kasan fatalwa haka suka ratsa ta cikin bangon.... Cike da mamaki Mu'azz ya wangale baki yana ganin ikon Allah domin bai taba tsammanin zai sami irin wannan guri a karkashin wannnan azabebben guri ba...

"wannan katanga ta kasance tamkar Garkuwa ne a gare mu, kuma an samar da ita ɗaruruwan shekaru da suka shuɗe."
Ajiyar zuci tayi yayinda ta kammala wannan magana sannan ta juyo Fuska cikin salo yayinda take takun ta sake da cewa..

"Domin sanin tarihin wannan katanga da kuma kasancewar ku a wannan guri dole sai kasan Tarihi wannan katafaren Gurin da kansa....."
Gyaran murya tayi bayan ta furta hakan sa'annan ta soma shararo Bayani kamar haka.

"Shekaru Aru-aru da suka shuɗe anyi wani karni wanda a wannan karni tsatsuba da masu yinta a baiyane suke sannan kuma ƴan adam na wannan lokaci sun kasance suna karkashin mulki ne ta bakaken aljannu..... Bakaken Aljannu sune masu juya duniya a wannan zamani ta yadda kowani halitta data kasance ba jensin su ba tofa bashi da kwanciyar hankali..... Haka akayi ta musguna ma talakawa da marasa karfi ciki hadda attajiran babu wanda ya tsira saidai wanda suka yadda da mulkin nasu,kuma wannan mulki ta samu faruwa ne bayan shudewan Sarki Zubair,Bahru daya daga cikin almajiran Sarkin ya hau wannan karaga bayan ya shafe ahali da kuma magada da masu faɗa aji na wannan masarauta wayenda basu goyu da bayan daya hau wannan karaga ba,kasancewar sa bawa kuma shidin Ba jensin bil Adam bane, bayan ya hau wannan karaga mutane suka fara yaɗa jita jitan cewa shi yayi ajalin sarki Zubair aiko bayan wannan jita jita yayi ta yawo harya fado kunnen sa saiya tsaurara wajen mayar da duk jensin bil adama bayi... Kama daga wayenda suka ki goyon bayan sa har wayenda sukayi hakan sai ƙalilan daga cikin su wanda ya bari.

Haka wannan mulki ya gudana na tsawon shekaru kafin baiyanar jarumi Zaid wanda ya kawo karshen wannan mulki hadi da nutsar da daular tasa wayenda bakaken Aljanu da kuma wannan masarauta nutsewa karkashin kasa... Bayan shudewan wannan mulki mutane suka sami yanci haka suka cigaba da gudanar da rayuwa su babu takura saidai banan matsalan take ba bayan nutsewar wannan masarauta wasu daga cikin mabiyan sarki Bahru sukayi ta yada cewar tsumin Sihiri wanda zai bawa mutum damar mulkar duniya da duk abinda ke cikin ta tana a karkashin wannnan masarauta haka mutane da dama sukayi ta rasa rayukansu yayinda suka shiga Dan naiman karfin iko ko kuma ɗan naiman dukiya saidai abinda basu sani ba shine har yanzu karfin ikon Bahru tana a karkashin kasan wannan guri da kuma ma biyansa Wanda zuciyoyinsu take cike fal da burin fitowa su dau fansa akan yaudara su da Zaid yayi... Domin ba karamar tarko yayi musu ba.

Wannan shine iyya labarin da zan iyya baka a halin yanzu domin kuwa babu lokacin da zan iyya baka duka amma nayi hakan ne dan ka fahimci gagarumin aiki dake gaban ku....Domin Wannan gurin zata cigaba da jawo mutane marasa adadi ciki ta har sai bakaken Aljanun nan da aka garkame ciki sun sami biyan bukatan su... Mu aikin mu anan shine mu hana Faruwan haka amma kuma bazamu iyya hana Faruwan hakan na har abada ba,dan hanya dayace mafi sauki wanda zaku iyya bi ku fice daga nan kuma ku tsiratar da duniya daga fadawa cikin halaka shine ku naimo Dutsen haske da kuma kogon kan Sarki Bahru domin su kadai ne zasu baku damar fita sannan kuma sune zasu toshe hanyar fita din da hana farfaɗowan Bahru bayan kunyi hakan."
Nan ne ta kawo karshen magana inda ta take biriki hadi da juyo idanu ta kalli fuskan Mu'azz sannan ta sake cewa.

"Saidai kuma Faruwan Hakan ne keda matukar wahala dukda cewa kune na farko masu sa'an da har suka iyya kwana a cikin wannan guri ba tare da sun sheka ba amma gaskiya samun wayennan abubuwa zatayi matukar wahala."
Shiru Mu'azz yayi alamar nazari,aiko dago Idanu da zaiyi saiya hango ATIF tsaye alamar Sallah Yake shiko kasa rike murna yayi domin Ihu ya buga hadi da shewa sannan ya kirawo sunan Atif.

Idan muka Laika Ɓangaren Anwar Aguje ya juya yana gudu Bayan sa kuma gadan nan ne ke sauka tana kuma rushewa yayinda take tada bakar kura kai kace filin sukuwa,haka yayin ta gudun ceto ransa daga karshe Kuran ta lullube shi,sannan gurin yayi tsit bayan ta gama sauka.

Farat daya ya fito cikin wannan kura yayinda ya dire kasa,aiko bayan kuran ta lafe ya mike tsaye hadi da sauke Idanuwa kasan gurin inda yayi tauzali da hudu baki wuluk yayinda take a cakude da juna...

Indan mun sauko cikin wannan ƙatuwar ramin kuwa zamu tarar da still wannan fada na sauka yayinda take dauke da tawagar su Adam domin kuwa dama karyewa tayi dasu a lokacin da Anwar ya bar Gurin nasu...

"Amry!."
Haka Adam ya furta bayan Harun da kuma Hafsa sun tallafo masa ya haye kan gadan data ke sauka da gadan nasu din...

buga kasa wannan Gada da suke kai tayi bayan tayi hakan kuwa ta tarwatse tayi watsi dasu. Shiru kakeji babu ko kikit domin kuwa banda hudu babu abinda zaka iyya gani a kasan wannan guri ko jiyuwa...

Shiru Gurin yayi na wasu dakiku kafin nan aka fara jiyo shesshekar kuka.... A galabaice Adam ya bude idanu bayan gajeran suma da yayi,aikuwa koda da ido garan duhu ne zasuyi masa sannu da zuwa bare babu...

"Amrita! Amrita!."

A kasa kasa ta amsa masa inda da jiyo wannan sauti murya gaban sa ta fadi ya sake kirawo sunanta...

"Amrita! Kina Ina."
Yana fadan haka yayinda yake jujjuyawa dukda yasan ba ganin ta zaiyi ba...

Cen gefe Hafsa ce ke kwance yayinda take kokarin mikewa ta kuma sa hannu a goshi alama gurin ya buga da wani abun..

Karan mai kamata rushewar kayan tarkashe ne ya tashi inda Adam yayi saurin juyo Fuska bangaren yace "waye wannan?." Aiko Hafsa ce domin tayi kokari dafe wani abun ta mike tsaye... Amma sai hakan ya faru.

"Adam!."
"Hafsa? Ina sauran."
Haka Adam din ya tambaya amma bayan yayi hakan ya kwarma bagidajiyar ihu...

"Adam nine Fa, Anwar!."
Cewan Harun inda Adam yayi goron nishi hadi da dafe kirji domin ba karamar firgita yayi ba dayaji an dafe masa kafada Yace dasu.

"Toh ina Sauran Suke?."
Aiko bayan ya furta hakan sai suka jiyo wata kara booo nan da nan Gurin ya dau haske wacce tayi matukar basu mamaki domin basu san Ganin su ya dawo ba.

Aiko suka cikin wannan murna na samun ido sai sukayi arba da yanayin gurin da suke,Toh ina abin murna ana ɓacin idan ka sami idanun ma abubuwan tsoro kurun zakayi ta arba dasu... Hm

Wannan gurin da suka tsinci kansu dai tayi kama da shekar tsuntsaye sannan kuma *Yana* ta mamaye Gurin ga kuma wasu kalan tukwane bakake wanda aka rurrufe kawunan su da jajayen kelle layi layi...

Yadda kasan makerarsu ne haka gurin ta kasance.... Aiko saida wannan haske yakawo suka san duk wannan sannan Hafsa taga abinda ta ɓarar yayin mikewan... Kusan tukwane goma ne suka zube yayinda ta dafe da niyar tashi din suka farfashe...

Nan Suke sai Harun wanda yake a Suffar Anwar ya hango Harzad dake kwance yayi sauri kirawo sunan sa aiko a guje suka yiyo kansa inda Harun yayi ta jijjikashi yana kuma kiran sunan sa,a wannan lokaci ne Adam shima ya hango Amrita inda take kwance da wani katon Dutse ya danne mata kafa...

"Amrita!!."
Cikin kara ya furta hakan inda Hafsa ta juya a firgice inda tayi arba da halin da Amrita ke a ciki nan sukayo kanta a guje suka daga wannan dutse daga kan ƙafan nata...

"Amry! amry!."
Haka Adam yake furtawa yayinda yayi mata filo da cinyarsa yana Kuma bubbuga kumatun ta da tafin hannu da niyar ta farka,aiko har Harzad ya farfaɗo da shike shima gajeriyar suman yayi amma Amrita Ina taki kawo wuta....

"Adam take it easy, you are hurting her ya kamata kabi komi a sannu, I'm very sure dogon suma tayi and zata farka just daina dukan nata."
Aiko yi kamar baiji abinda ta faɗa ba yayi inda ta sake maimaita hakan, Anwar da Harzad dake zaune a gefe ganin baya sauraran tane yasa suka taso da niyar tsayar dashi but saiya ture su inda a yayin komawan nasu da baya suka sake rusa wasu lodi lodin tukwanan...

Tsit sukayi yayinda wayennan tukwane ke rusowa Hafsa da Anwar ko zuro Idanu sukayi aiko bayan Faruwan Hakan sai Adam yace...

"I can't let her die."

"Mun sanda hakan but komi a sannu ake binta..."
Aiko Hafsa bata inda fadan hakan ba sai suka soma ganin Gurin na shecking wato girgiza... Zuro Idanu sukayi suna ta waige waige dan ganin maike shirin faruwa...

Aiko wasu bakaken spides 🕷️ ne suka fara zazzagowa suna fiffitowa daga cikin wayennan fasassaun tukwane... "Oh my God!." Furucin Harzad Kenan inda Anwar Kuma Yayi gajeriyar murmushi sannan Yace...

"We are going to Die."

FORZY
Idan muka dawo bangaren su Forzy shiru sukayi baki daya suna sauraron wannan sauti yayinda kuma wannan sauti sai faman dadda karuwa yake aiko cen nesa sai suka hango Ali tafe cikin kasaita yayinda ya mikar da hannayen sa biyu ya kuma baje ƴan yatsun.... aiko bayan saiga lodi lodin kuɗan zuma a bayan sa yayinda suke biye dashi yadda kasan guguwa haka suke bubbudewa..

Aiko cikin tsoro,firgici da kuma mamaki dukkanin su suka zaro Idanu,shi kuwa Ali bayan yaki kusa dasu saiya mika da hannayen nasa gaba aiko yadda kasan ce musu yayi dasu afka musu haka suka yiyo kansu Forzy... Ganin Babu makawa Wayennan Zuma zasu cimmusu ne yasa Forzy cewa...

"The only and best solution we have shine mu ruga a guje!."

"What?." Tambayan da Samra tayi kenan bayan ta jiyo furucin Forzy.

"Run!."
Haka ta sake maimaita mata sannan tasa hannun tayi sama da Mufyda aiko a gadon bayanta ta sauka yayinda Muzzaffar shima yayi hakan ga Al-hussein aiko Faruwan haka ne tayi matukar rudar da Samra ganin ta kasa ta bashi amma kuma gashi Muzzaffar hadda goya shi....

Aiko tamkar walkiya saiga Ali ya dire a gaban su haka suka sake juyawa nan ma suka ganshi, nan ne ido ya raina fata suka zubar da kayan yaki domin irin wannan ne akewa kirari Fight or die...

↩️
"Saidai kuma Faruwan Hakan ne keda matukar wahala dukda cewa kune na farko masu sa'an da har suka iyya kwana a cikin wannan guri ba tare da sun sheka ba amma gaskiya samun wayennan abubuwa zatayi matukar wahala."

"Inason nasan wace hanya ne da kuma dabaran da jarumi Zaid yabi wajen kawo karshen Mulkin Bahru da kuma hallaka shi sa'annan inson naji tarihin wannan nasarori da Bahru yayi a Rayuwar sa..."
Furucin Mu'azz kenan inda Atif yace da ita...

"Kuma munason muji wace irin matsifune a hanyar samo mafitar!."
Da jiyo hakan ko ta fashe da muguwar dariya sannan tace dasu...

"Hadarin dake cikin wannan hanya bazata iyya misaltuwa ba saidai muce da ita *Hard way and the only way*."

*MU HADU A EPISODE MAI ZUWA*

💀💀💀
*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
*FB PAGE*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100070173921421
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣9️⃣*

Tauzali Mu'azz yayi da *Atif* tsaye alamar Yana Sallah,aiko kasa rike murna yayi domin kuwa uban kara buga hadi da shewa sannan ya kirawo sunan Atif,a fusace Atif ya waigo inda yayi arba da Mu'azz din tsaye...

"Atif!."
Haka Mu'azz ya sake kirawo sunan nasa cikin Murna yayinda Idanuwan sa kuwa suka cike da kwalla dan farin ciki,a guje ya ruga izuwa inda Atif ke tsaye suka rungume juna....

"Banyi zaton zamu sake hadewa a wannan guri kuma a irin wannan lokaci ba Atif,Gaskiya na tsorata Sosai na dauka shikenan na rasa ka."

Aikuwa ganin yadda Atif din ya kura masa ido ne ya fahimci babu abinda Atif din ya fahimta game da wannan batu nasa domin kuwa rudar dashi wannan batun yayi,nan sai ya sake da cewa.

"Oh Sorry my bad,gaskiya You missed a lot Atif,domin abubuwa da dama sunyi ta faruwa yayinda ka kasance a sume."

"Da gaske?."
Tambayan da yayi kenan inda wannan kyakkyawan budurwa da suka taho tare da Mu'azz ta amsa masa da Uhmmm ta cikin wuya Sannan ta sake da cewa.

"Ina mai tunatar da ku,akwai gagarumar aiki a gaban ku,kuma ba wani lokaci mai yawa kuke dashi ba domin kowani dakika mutuwar ku kuke kusanta,dan haka ya zamanto muku dole ku gaggauta naimo Dutsen haske da kuma kogon kan Sarki Bahru domin su kadai ne zasu baku damar fita daga wannan guri."
Ajiyar zuci tayi Sannan ta sake da cewa.

"Saidai kuma Faruwan Hakan ne nake ganin kamar da wuya,domin kuwa samo Wayennan abubuwa nada matukar wahala dukda cewa kune na farko masu sa'an da kuka iyya kwana a cikin wannan guri ba tare da kun sheka ba amma gaskiya samun wayennan abubuwa zatayi matukar wahala."

Shiru Mu'azz yayi alamar mamaki kafin nan yace da ita...

"Inason nasan wani hanya ne da kuma dabaru da jarumi Zaid yayi anfani dasu wajen kawo karshen Mulkin Bahru da kuma hallaka shi baki daya, sa'annan inson naji tarihin nasarori da Bahru yayi a Rayuwar sa da kuma ɓangarori da ya samu gazawa..."
Furucin Mu'azz kenan inda Atif ya kara da cewa...

"Kuma zamuso muji wace irin matsifune a hanyar samo wayennan abubuwa da kika lissafo!."
Haka Atif shima ya tofa albarkacin bakinsa kamar yasan abinda suke tattaunawan akai, wannan Ƴa kuwa da jiyo furucin Atif Sai ta fashe da muguwar dariya sannan tace dashi....

"Matsifu,ababen tsoratarwa da kuma Hadari dake cikin wannan hanya bazata misaltu ba, saidai kawai muce da ita *Hard way and the only way* sannan kuma babban kalubale da zaku fuskanta game da wannan aiki shine Harun."

"Harun!."
Haka suka maimata sunan nashi cikin hadin baki dan mamaki itako tace dasu.

"Eh Harun, domin yana dauke da bakar kambu (Crown.) na Sihiri wanda wannan kambun mallakan sarki Bahru ne,da wannan kambu kadai zai iyya lalata duk shirin ku kuma da wannan kambu zai iyya fitar da muggan Halittu izuwa goron kasa sannan da wannan kambu zai iyya dawo da Rayuwar Bahru wacce yin hakan babban kalubale ne a gare mu dama sauran al'umma baki daya,dan haka ya zama lallai ku rigasa samo wayennan abubuwa dana lissafo muku su."

Cikin Rudewa Mu'azz da Atif suka dubi idanun juna,inda Mu'azz yayi saurin cewa..

"Wait! wait! wait! I'm confused,Taya Harun ya kasance a raye bayan rushewar da gada tayi dashi and Kai Kuma Atif Taya kasan komi game da wannan?,i mean kamar bakayi mamaki dajin wannan labari na Bahru da kuma hanyan fitarmu ba."
Gajeriyar murmushi wannan yarinya tayi haka shima Atif yayi kafin nan tace dashi
"Atif ya rigaka samun wannan labari."

"What?."
Furucin da yayi kenan inda ta mike tsaye,fuskanta ko cike da annashuwa...

Idan muka Laika Ɓangaren su Harzad kuwa zamu riske su yayin da suke tsaye kallon bakaken spiders 🕷️ dinnan dake fiffitowa ta cikin fasassaun tukwane... Cikin kankanin lokaci kuwa wa 'yan nan Kwari suka zagaye su domin ta ko'ina sune birjik,ganin hakan yasa Anwar ya saki wata muguwar murmushi Harzad ko yayi furucin "Oh my God!."

"We are going to die!."
Fadar Anwar Kenan.....

"Amry! Amrita!."
Hallau Adam akan gwiwowinsa yake yayin da yake kokari wajen ganin ya farfaɗo da Amrita daga sumar da tayi..

A wannan yanayin ɓangarori biyun nan suka kasance wato ɓangaren Adam da kuma Amrita dake sume sai kuma ɓangaren

Please Login or Register in order to submit comment