Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi ko kuwa....??
Idan muka duba bangaren wannan sanda da Amrita tayi jifa da ita kuwa fadiwarta gurin ya kama ci da wuta ta sanadiyyar wata bakar ruwa mai kamada Kwalta dake kwance a wannan guri..

Aiko wannan wuta ci take babu fashi yayinda ilahirin gurin ta dau haske ta yadda lungu da sako na wannan daki zaka iyya gani amma kuma su ganin hakan ta gagara su.

Inda Amrita ke tsaye kuma taku biyar gaban ta Harun ne ke tsaye yayinda wannan bakar ruwa ke gangarowa daga jikinsa fuskansa kuma babu annashuwa ko kada domin kuwa ya haɗe fuska..... TIRKASHI

Idan muka dawo baya da labarin kuwa zamuga Lokacin da Harun ya daura Hular daya tsinta cikin akwatin gawa kansa,nan da nan sai wata bakar hayaki ya mamaye jikinsa babu inda ake iyya gani daga cen wannan hayaki ta yaye saiga Harun yadawo wani abin na daban dukda cewar still shine Amma yanayin jikinsa da kuma shigarsa ta sauya ta dawo Baki Kirin yayinda Idanuwan sa suka dawo jajir hakan ya sakashi takawa izuwa kofar wannan dakin daya kasance ciki ya kurawa kofar Ido bayan nan yayi murmushi wacce wannan murmushi da kaganta kasan ta muguntace... Sa'annan yayi furucin cewa

"I'm Back." Abinda ya furta kenan bayan nan ya sake murmusawa,sannan ya haɗe fuska yayinda idanuwan sa suka kara haske aiko yin hakan keda wuya kofar ta bude kanta da kanta yadda kasan nakiya aka saka mata...

Haka harun din ya taka yayi inda wannan Gada ta karye cikin salon taku kasaita ya kai wannan guri da zuwan sa wannan guri wannan bakar ruwa ta soma yi masa matattakala yana kuma hayewa harya sauka kasan wannan guri! Wato inda yabar taron tawagar nasu a baya cen.

"What did I miss?."
Faɗar sa Kenan.


💀💀💀
*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣7️⃣*



"Taya Fitulun gurin kuma suka dauke lokacin guda?"
Furta hakan tayi hade da kai hannu kan sanda da take rike dashi domin ta tabbatar da dalilin kafewar wannan wuta,amma kuma bayan ta aikata hakan ta Kwarma bagidajiyar ihu hadi da yin jifa da sandan gefe guda ta sanadiyyar kunar dataji a tafin hannu ta.

wannan sanda dai hallau tana ci da wuta saidai kuma duk cikin su babu mai iyya ganin hakan,abin tambayar anan shine shin Makancewa ne sukayi ko kuwa....??
Idan muka duba bangaren wannan sanda kuma fadiwarsa gurin ya kama ci da wuta ta sanadiyyar wata bakar ruwa mai kamada Kwalta dake kwance a wannan guri..

wannan wuta dai ci take babu kakkautawa yadda kasan a rumbun kara,yayinda hasken sa ta haskake ilahirin gurin,kowace lungu da sako na wannan daki saida ta dau haske,Readers zaku iyya ganin wannan haske amma kuma su ganin hakan ta gagare su.

Inda Amrita ke tsaye kuma taku biyar gaban ta Harun ne ke tsaye yayinda wannan bakin ruwa ke gangarowa daga sassar jikinsa fuskansa kuma kwata kwata babu annashuwa....

"Amrita! Amrita! Lafiya kike kuwa?."
Fadar Adam Kennan inda Hafsa tayi saurin sake tambayar cewa.

"Amrita wani abin ne ya same ki?."

"Guys Bana Iyya ganin komi!."
Amsan da Amrita ta basu kenan Cikin salon rikicewa,inda Adam Yayi furucin what! Cikin kara, Harzad ko yace dasu.

"Calm down *Amri* bafa ke kadai bace mai ganin wannan duhun,kowannen mu nanan haka yake gani kuma hakan ta faru ne ta sanadiyyar daukewar haske yayinda muke tsaka da tafiya and anyway ya kamata mu samo hanyar kunno wannan fitulu domin tafiya cikin duhu ba maiyuwa bane."
Harzad karashe maganar yayi da tambaya wacce yake danganta wannan tambaya ga Anwar tambayan shine "koba haka bane Anwar?"

"Kwaraima kuwa,nimanan na tsani tafiya cikin duhu amma ya muka Iyya tunda ta same mu...."

Aiko da jiyo wannan batu Amrita tayi shiru alamar nazari hadi da yin wani batu a kasan ranta cewar ta shine....
"Haka na nuna cewar abinda ta faru dani ta faru da kowa kenan,taya hakan ya faru?."

"Amrita Don't think too much,komi zaya tafi yadda ya kamata insha Allah,dan haka ki kwantar da hankali."
Fadar Adam kenan inda Amrita tayi saurin cewa.

"Taya zan Iyya kwantar da hankali bayan na fahimci ba duhu bane wannan makantace!."

"What!!."
Cikin hadin baki Adam, Hafsa, Anwar da Harzad suka furta wannan kalma cikin mamaki hade da ruɗewa...

Duk wannan tattaunawan da sukeyi suna yintane gaban Harun yayinda ya kasance tsaye gefen su yana sauraron komi,haka Amrita ta fahimtar da tawagar nata hadi da basu shawaran yadda zasuyi tafiya ba tare da sun rabe da juna ba,shawarar ko itace su kasance suna rike da hannayen juna ta kowace hali,kuma fa haka sukayi domin Amrita lalubar Hannun Adam tayi ta rike inda shi kuma adam ya riko Hafsa haka itama har suka gama rirrike hannayen juna yayinda Anwar ya kasance shine a karshe....

Aiko bayan sun soma taku sai Anwar yaji an jawo dayan hannun nashi an rike,yin hakan kuwa tayi sanadiyar takewarsu biriki baki daya,Anwar zura Idanu Yayi yayinda ya gagara bude baki,Harun ko tsaye yake gefe guda inda ya gofe hannayen a kirji sai Faman Murmushi yake...

SAMRA
akan gwiwowinta take tana kuma furta cewa "Ya zamanto dole min na boye wannan daga gare ki Mufy,domin bana son naga tsoro da kuma karaya a tattare da ke,ki gafirce ni."
Bayan ta furta hakan sai ta juyo Idanu izuwa kan Mufyda dake yiwa Muzzaffar fifita, aiko a daidai wannan lokaci sai wani tunani ya fado mata.....

"Guys Have you notice that kwanakin mu biyu Kenan da shiga wanan guri amma babu ɗaya daga cikin mu wanda ya naimi abinci ko abin sha?."

"Nima abinda yake yimin Yawo a brain Kennan,Amma nayi shiru ne dan kar ace na cika korafi."

Wannan tattaunawar da sukayi a baya ne ya fado mata aka,da tuno hakan kuwa sai tayi shiru alamar nazari kafin nan tace da kanta....

"Idan har fadan Al-hussein gaskiya ne! kenan saura mana wasu dakiku mu fara jin yinwa!."
Bayan ta fadan hakan ta juyo idanunta bangaren guda inda ta hango wannan bishiyar mai cike da albarkatun...

"Mufyda."
Haka Samra ta kirawo sunan ta inda ta ɗago kai hadi da amsa mata da cewa..

"Uhmm,yane?"
Juyo Idanu Samra tayi inda takai kan wannan bishiyar haka mufyda itama tabi bayanta inda ta hango bishiyar,cikin ƴan dakiku suka yanke shawara aiko sai gashi sun baiyana a karkashin wannan bishiya inda suka tsaya suna mai karewa bishiyan kallo.

"Yanzu saura mu naimo hanyan ciro ƴaƴan wannan bishiyar,wacce nake kyautata zaton ba maiyuwa bane a gare mu... domin idan kika duba cikinmu babu mai Iyya hayewa wannan bishiyar sannan Babu wani abinda zamu ciro dashi."

"Mufyda banyi tsammanin haka bishiyar take da tsawo ba amma tunda mun rigada mun karaso ya kamata mu ciro koda ɗan kadan ne."
Fadar Samra kenan inda mufyda ta gyada kai alamar alright hadi da juyo Idanu izuwa inda suka baro Muzzaffar tare da Al-hussein sannan tace da Samra.

"Amma Samra Are sure baro su Muzzaffar da mukayi a baya bazai haifar da matsala ba?."

"A'a ba wani matsalan da hakan zata haifar, sannan ina wani tunani shin zaki Iyya hayewa kan kafada ta ki ciro mana ƴaƴan wannan bishiya?"

Aiko da jiyo wannan batu Mufyda ta buɗi baki alamar mamaki hade da cewa..

"Hakan bazai taba karewa lafiya ba!."
Haka mufyda ta nuna rashin amincewa amma Samra ta nace har saida ta amince ta haye kafaɗar nata, Samra kamar bazata Iyya mikewa da mufy a kafadar ba amma cikin ikon Allah saiga mufyda a kafaɗar nata yayinda suka mike tsaye suna kokarin ciro ƴaƴan ganyen,hankali su ya koma kacokal kan ƴaƴan itatuwan...

Yayinda suke kokarin ciro ƴaƴan itatuwan kuwa wasu daga cikin fruits din suna kokarin rutsawa dasu domin bude Idanu suke suna kallon su....
Mufyda dukda cewa hannunta baya Iyya kaiga tabowa amma tana nuna iyakan kokarin ta wajen ganin ta kaiga ciro koda guda daya ne kacal,aiko tanakan hakan sai taga baiyanar Idanu jikin wannan fruit Wanda take kokarin cirowa, hakan Kuwa yasa ta razana hadi da zuro Idanu...

Ji kawai tayi wannan fruit ya fita daga jikin reshin yayo kanta yayinda yake sauka saitin fuskar ta,aiko cikin kankanin lokaci sai taji sun zube gefe guda ta sanadiyyar turesu da akayi da karfin tsiya....suka zube.

A gaggauce wannan wanda yayi sanadiyar zubewar tasu ya mike inda Samra itama tayi saurin ɗago Idanu domin ganin wanda yayi musu hakan....
Aiko tarar da Forzy tayi tsaye wacce hakan yayi matukar bata mamaki,Itako Forzy cewa dasu take da su gaggauta mikewa tsaye amma suka kasayin hakan dan rudewa hade da mamaki.

MU'AZZ
Idan muka gangara bangaren su Mu'azz ko zamu tarar da Mu'azz din cikin wannan kwanceciyar ruwa wanda farar macijiya ta nutse da Atif a ciki...
ciki zarra Mu'azz yake sauka kasan wannan Ruwa yadda Kasan mermaid,Amma duk da wannan izza nashi da yake nunawa bai iyya kaiga rike wannan macijiya dake dauke da Atif ba,Haka yayi ta bin wannan macijiya a baya tun yana Iyya hango ta har ya dawo baya Iyya ganin ta,aiko nan ya dawo waige waige cikin wannan ruwa yadda kasan kifi.... Dagacen nesa ya hango wata farar haske wacce yakasance bashi da zabin daya wuce yaje ga wannan haske,haka ya karasa gurin bayan ya karasa gurin wannan haske kuwa saiya fahimci wani abun wanda ya sakashi mamaki matuka domin tunda yake a rayuwarsa bai tabba cin karo da labarin makamancin wannan ba....
Taya hakan zata kasance,taya Daki mai dauke da iskan nunfashi zai kasance a karkashin ruwa yayinda kuma wannan ruwan baya iyya sauka izuwa wannan daki,gaskiya akwai ayar tambaya anan....

Abinda ya bawa Mu'azz mamaki kenan domin bai taba zaton daki makamanciyar wannan zai kasance a karkashin ruwa ba tare da ruwa ya cika shi ba,dukda cewar cike yake da mamaki hakan bata saka ya ki shiga wannan dakin ba,haka ya sauka izuwa wannan daki kafin nan ya sake cikewa da mamaki domin idan ka kasance cikin wannan daki zakaga inda ruwan ta tsaya yadda kasan bango ko kuma nace katanga haka ruwan ta tsaya...

Hakan kuwa tayi matukar burge Mu'azz domin bayan ya sauka a dakin ya sake komawa kusa da ruwa ya tsoma hannu ciki ruwan yana wasa dashi, bayan ya jawo hannun nashi da karfi tsiya yayin cirowa ta yadda daga zaran hannun nasa ya sami damar fitowa ruwane zai bi baya hakan ya kuma sauka a fuskarsa amma kuma sai yaga akasin haka,domin babu koda ɗigon ruwa guda wanda ya sauka a Fuskar nasa,hakan kuwa ya sakashi juba rigar dake jikin sa dan ya tabbatar ruwan bai tabashi aiko nanma ya cike da mamaki domin jikinsa a bushe take kamar bashi bane wanda ya fito daga cikin ruwa yanzun... ganin hakan kuwa ya tabbatar masa da cewa babu ruwan da zai iyya shiga wannan daki.....

A daidai wannan lokaci sai Mu'azz ya tuno dalilin sa na zuwa wannan guri,aiko nan da nan ya juya hadi da ambatan sunan Atif cikin kara.... Aiko wannan dakin ya soma daukar muryan Mu'azz yana maimaita ta hade kuma dayiwa Mu'azz din dariya....

"Mu'azz! Mu'azz!."
Cikin siririyar murya ake kiran sunan nasa yayinda muryar ke fita tamkar maishi na naiman tallafi,daga can lungu karshe na wannan daki Mu'azz ya hango wata a zaune yayinda ta saka kanta tsakanin ƙafafunta sannan ta kuma rungume kafafun Alamar tana kuka.

"Waye wannan,shin lafiya kike ƴar uwa?."
Kalmar da Mu'azz ya furta kenan yayinda yake kokarin karasawa gare ta cikin sanɗa...
Ba amsar daya samu daga wannan mai shesshekar kukan har ya kaiga riske ta,hadi da yunkurin kai hannu ya taba ta... Amma farat daya sai Mu'azz yaga jelar macijiyan nan ta raba tsakanin sa da wannan mai shesshekar kuka, Faruwan hakan keda wuya sai wannan mai kukan ta mike tsaye,anan ne suffar ta ya baiyana inda Mu'azz yayi nadamar kusantota da yayi domin abar tsoro ce matuka...

Gajeriyen kwatance da zan iyya yi wajen suffanta wannan halitta kuwa shine tana sanye ne ta doguwar riga fara wacce ya lullube mata har kafafu,sannan kuma ta zubo gashin kanta ta gaba hakan yasa ba'a iyya ganin fuskar nata gaba daya illa rabin fuskanta ake iyya ganin...

*Cigaban labarin*
Mu'azz kafin ya farga wannan halitta mai kama da zombie takai Masa farmaki,aiko tamkar baiyanar walkiya a duhun dare wannan jela na macijiya ta sake baiyana yayinda ta janye Mu'azz izuwa inda take tsaye... Yayinda take tayo Mu'azz din kuwa jelan nata na shanyewa,Mu'azz ko na kaiwa inda take sai jelar ta dawo kafafu.. nan da nan ta dawo suffar bil adama.

Zura Idanu Mu'azz yayi bayan yayi arba da kyakyawan fuskan ta,domin wannan macijiya gwanar kyauce kuma daga ganin fuskarta kasan ta iyya murmushi... Mu'azz cike da mamaki yake domin akan idanunsa wannan macijiya ta rikiɗe ta dawo suffar mutum hakan yasa Mu'azz din ya gagara motsawa,itako wannan macijiya ta juyo Idanun ta izuwa kan sa hadi kuma da cewa...

"Wai har sai yaushe zaku fara gane irin Wannan makircin ehye?"
Tambayan da wannan macijiya tayiwa Mu'azz kenan,wancan aljana kuwa dake tsaye bayan su ganin suna tattaunawa ne yasa tayi tsalle da niyar dirar musu aka,amma hakan baiyu ba domin cikin abinda bai wuci dakika gudaba wannan yarinya dake tsaye gaban Mu'azz ta sake rikidewa ta dawo rabinta macijiya rabinta kuma mutum, yayinda kuma tayi anfani da wannan jela nata wajen buge wannan yarinya mai Kanada zombie, cen gefe guda ta fadi.... Inda wannan macijiya ta juyo tace da Mu'azz "ka biyo ni muje." Bayan ta fadi hakan ta koma suffar ta na ainahi ta wuce Mu'azz ko ya bita a baya.

Idan muka gagara bangaren su Amrita kuwa hallau tsayen suke yayinda suke yiwa Anwar tambayoyi shin lafiya yake kuwa,mai yasaka tsayawa.. Amma kuma da yayi yunkurin bada amsar wannan tambaya sai ya gane cewar bafazai iyya furta komi ba,haka yasakashi kifimewa taya sauran tawagan nasa na magana amma baya iyya hakan, Anwar yayi takai hannu yuwa yana ta shassafawa Yana tunanin komai sami waraka amma kuma babu abinda ya sauya.... Abin naci masa rai hakan yasa idanuwansa suka cike da kwalla, bakowa bane wanda yasa wannan kwallar zubowa illa Harzad domin ya nuna damuwarsa a fili yana kiran sunan Anwar cikin Muryar tsoro hade da jijjika hannun nasa...

"I'm good!."
Amsar da Harun ya bayar kenan a madadin Anwar cikin muryarsa,aiko Anwar da jiyo wannan Murya irin tasa sake wanda ke bada amsa a madadin yasan sun fada Bala'i,amma bashi da bakin furta hakan...
Ɗigar kwalla ne ya fado daga idanun Anwar da faruwan hakan sai ya soma ganin dishi dishi daga karshe idanun sa ta soma gani normal bayan yayi wannan kuka... cikin mamaki yayi wani furuci kasan ransa inda yake cewa...

"Aw ashe zubar da kwalla itace warakan wannan kafin, gaskiya ya kamata kowa yasan da hakan amma taya zan sanar dasu bayan na rasa murya na."

"Muje ko."
Haka Anwar ya sake jiyo murya makamancin nashi na cewa,aiko nan da nan ya juyo domin Ganin waye wannan wanda yake anfani da muryarsa,yin hakan keda wuya yayi ido hudu da Harun tsaye bayan sa...
Ganin yadda Harun din ke daga masa hannu kuwa kasan yagane Anwar ya fara gani,haka Harun din ya taka ya karasa inda yake yayinda ya raba hannun Harzad da Anwar ya shige tsakanin su, kafin nan ya sake da cewa...

"Babu abinda ya same ni,zamu iyya karawa gaba."

"Anwar mai ka aikata ne haka, wallahi ka razana ni sosai."
Fadar Harzad kenan inda Harun ya juyo idanun sa izuwa kan Anwar sannan Yace dashi...

"Sorry my bad,bazan sake hakan ba kaji?"
Da murmushi a furkarsa ya rikiɗe ya dawo suffar Anwar sak bayan nan yayi busa da bakinsa izuwa jikin Anwar aiko nan da nan Anwar ya soma jin wani yanayi a jikin batare da yasan mai yake shirin samun sa ba....

Haka suka kara gaba yayi Harun wanda yakasance cikin suffar Anwar din yake jan ainahin Anwar din da karfin tsiya,Suna tsaka da tafiya ne Anwar ya fahimci wannan yanayi daya ji a cikin jikin sa domin ganin yayi sassar jikinsa ta koma yadda kasan turbaya dukda cewar hallau yana nunfashi amma kuma sai ya kasance a cikin wani yanayi wanda babu mai iyya ganin sa koda kuwa maishi yana iyya ganin komi..... normal

"Hakan na nuna cewar yayi replacing nawa kenan,amma meye dalilin sa nayin hakan?"

FORZY
"Samra ki mike tsaye!."
Furta hakan Forzy tayi yayinda ta mika mata hannu,Hm aiko kura mata ido tayi ko kiftawa batayi yayinda kuma wannan bishiya ta soma girgizar kanta aiko saiga damin camelion (hawainiya) na sauka daga jikin bishiyan nanne suka fahimci wannan ba bishiya bane tarko ne.....

Wannan halitta dai sun sha banban data ainahi domin yanayin saurin da suke dashi da kuma girman su ta zarce na normal cemalions...

Forzy ganin Samra ba juyawa zatayi ba yasa ta juyo ta soma karesu da wannan karfe mai kama da mashi da take dashi a hannu... Haka take fatattaka wayenan halittu ganin zasu iyya fin karfin tane yasa ta rugawa a guje yayinda ta kamo hannun Samra suka ruga aguje,aikuwa a daidai wannan lokacin mufyda ta farka daga sumar da tayi domin faduwar da sukayi tuni tayi gajeriyar suma...

Aiko bayan tayi arba da wayenan halittu itama ta mike tsaye hadi da rugawa tabi bayansu Forzy aguje...
Forzy isarsu inda Al-hussein tare da Muzzaffar ke kwance keda wuya ta tura samra gefe guda yayinda ta soma gudu tana kewayesu tana kuma zana layi da wannan karfe dake hannun ta,aiko kamar a mafarki bayan ta kewaye gurin samada biyar sai wannan layi da tayi ya kama ci da wuta amma kuma dukda hakan bata dakatar da yin hakan ba...

Aiko ganin Mufyda da tayi na tunkaro da gudu yayinda wayenan halittu ke biye da ita a bayane yasa ta tuno abinda ya faru da ita a cen baya... Inda dayin hakan ta kirawo sunan Ahmed hadi da ciko idanu da kwalla.

Ganin kwalla a idanun tane yasa Samra ta jiyo idanu takai inda Forzyn ke fuskanta,aiko cikin sauri ta mike tsaye hade da zuro idanu,kirawo sunan Mufyda cikin Muryar tsoro...tayi
Idan muka juya idanun mu izuwa kan Mufy ko zamu tarar da ita tana tsala gudu, yayinda take kokarin kaiwa inda su samra ke tsaye,kuma fa sai da tayi hakan amma ina ta iso gurin a makare,domin saura mata taku kalilan ta shige wannan layi amma sai daya daga cikin halittun nan ya harbi kansa a daidai lokacin da mufyda ke kokarin juyowa domin ganin ratar data bawa wayenan halittu amma kash bata iyya Ganin hakan ba domin ji tayi wannan hawainiya ta fado mata a fuska saukarta a fuskar Mufy ko ta baje hadi da marne mata fuska,yayinda ta mamaye kan nata baki daya babu inda ta rage....

Aiko faruwan hakan keda wuya mufyda ta yanki jiki ta fadi a saman wannan layi wanda yake ci da wuta...
Mufyda ta kasance rabinta na cikin wannan layi rabinta kuma a wajen layin... Haka kuma dama zai baya wayenan halittu wajen shiga cikin layin inda har basu jawo Mufyda cikin layin ba.

*MU HADU A EPISODE MAI ZUWA*
_Readers *Longtime no see* gaskiya na dauki lokaci mai tsawo ba tare da nayi posting ba amma dai gashi yau nayi kuma insha Allah zan cigaba da posting,haka zalika Siddabaru shima zan cigaba da posting,but bazan iyya cewa a sati sau nawa zanyi posting ba gudun karna fada ya zamanto ban cika ba amma insha Allah zanna posting akai akai kwanan nan._

💀💀💀
*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''

_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣8️⃣*

MUFYDA
*_Mufyda_* tsala gudu take tana kokarin kaiwa inda su samra ke tsaye wato cikin wannan zagaye nan na wuta,kuma fa sai da tayi hakan amma ta iso gurin a makare,domin saura mata taku kalilan ta shige wannan layi sai ɗaya daga cikin wayennan halittun ya daki kasa ya harbi kansa a daidai lokacin da mufyda ke kokarin juyowa don ganin ratar dake tsakanin su... Aiko bata sami damar Ganin hakan ba domin ji tayi wannan hawainiya ɗaya daki tsalle ya fado mata a fuska, saukarsa fuskan nata ko ya baje hadi da marne mata fuska ya kuma zagaye kan nata baki ɗaya.... babu koda gurin nunfashi bare na jiyo sauti da wannan abin ya ragewa Mufy domin kuwa kama daga tsakar kanta ya sauko har Izuwa wuya wannan abun ya rufe yadda kasan da *Roba* aka nannaɗe mata kan.

faruwan hakan keda wuya mufyda ta yanki jiki ta fadi a saman wannan layi mai ci da wuta... Yayinda ta kasance rabinta na cikin wannan layi rabinta kuma a waje... Ta yadda daga zaran wayennan halittu sun karaso inda gangan jikin nata ke a kwance, kasancewar ta a gurin zai basu daman shiga wannan layin a saukake ba tare da sun bi ta cikin wannan wuta ba.

Zuro idanu *Forzy* da *Samra* sukayi ganin cewa Mufy na kwance cikin wannan hali aiko cikin zafin nama Forzy ta sake komawa ta janyo Mufy ciki, Amma duk da saurin da tayi wajen aiwatar da hakan saida wasu daga cikin wayennan halittun suka sami shiga...
Shigarsu gurin wannan zagaye na wuta ya cigaba da ci ta yadda babu wanin su da zai iyya shiga ba tare da ya kone ba,hakan ne yasa da isar su gurin suka take biriki suka tsaya kallo.

Cikin salon burgewa Forzy ta ɗago wannan karfe da take rike dashi ta rike da hannayen ta biyu,aiko nan sai tayi kama da jarumai irin na shekarun baya da suka shuɗe... Forzy hankalin ta kacokal yana kan wayennan halittu ta yadda kowani irin motsi sukayi idonta na a kansu,kuma tana hakan ne dan kada su kai mata farmaki ta kasa kare kanta bare Samra dake labe bayan ta.

Cikin karfin tsiya daya daga cikin wayennan halittu dasuka sami shiga ya kai mata farmaki inda tayi anfani da wannan karfe wajen buge shi ya fadi gefe guda,dukda tsintar kansa da yayi a yashe hakan bata hanashi sake kai wata farmakin ba bayan ya tashi,haka suka cigaba da kai mata farmaki yayinda ta dauki lokaci tana fafatawa dasu har yakai Samra ta fadi gefe guda dan yadda wayennan halittu suka dawo farautar fuskokinsu,Fadiwan nata keda wuya suka sa Forzy a gaba suna kokari wajen ganin sun Kaita kasa.... amma hakan baiyu ba, Duk da cewar ta kasance a Ruɗe take domin kuwa sun sakata a tsakiya.

Yayinda suka sakata a tsakiyan nasu kuwa sai wannan wanda suke fuskantan juna da ita ya fara kawo mata hari inda tayi anfani da wannan karfe ta buge shi ya fadi gefe guda, amma kuma a binda Forzy bata sani ba shine anfani sukayi da hankali wajen kawo wannan farmaki domin lokaci daya sukayi hakan ta yadda koda Forzy ta sami damar kare kanta daga wannan wanda take fuskanta bazata iyya kare kanta daga dayan ba,itako bata san da hakan bama har saida Samra tayi ihun cewa. "Forzy Watch Out!!."
Aiko jiyo hakan da tayi yasaka ta juyowa inda tayi arba da wannnan halitta ya tashi sama ta yadda babu yanda zatayi ta kare kanta domin ya riga yayi kusa

Please Login or Register in order to submit comment