Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣4️⃣*



"ki Kulla da kanki Y'ar uwa.."
Kalmar karshe kenan tsakanin Noor da Forzy,kafin ta sadaukar da rannata gareta.
Tundaga wancen lokacin har izuwa yanzu wannan kalmarce ke saka Forzy zubar da hawaye,Durkushe take gaban wata rubebbiyar turɓaya wacce nake kyautata zaton ta Noor ce.

"Noor maiyasa Kike kokarin sakani cikin kaɗaici?,mai yasa kike kokari ki nisanta kanki gare Ni?."
Cikin Muryar kuka Forzy ke furta hakan, yayinda fuskar ta jike sharkab da kwalla.

"Koda daidai da dakika guda shin kinyi tunanin halin da zan kasance ciki kafin ki aikata hakan?,mai yasa kika zabi rayuwata sama da taki Noor?
Noor Babu wacce na sani anan gurin sama dake,to mai yasa kika zabi kiyi nisa dani,Noor?."

Cikin wannan yanayi Forzy ta kasance na tsawon lokaci da su Atif suka kwashe suna wannan tafiya har izuwa inda suka kasance yanzun,wato inda wata mai kama da Forzy ta jasu Ciki.

Bayan sun tsinci kansu cikin wannan kofa ne yasa ta saki hannun nasa,shiko ya ɗaga hannu inda ya tarar da shatin hannu Forzy ya dawo Kore shar wacce tayi daidai da wannan koren haske daya shige jikin Muzzaffar,Aiko ganin haka yasakashi zura Idanu dan mamaki.

"Ke ba Forzy bace,wacece ke?."
Abinda ya fito daga bakin Atif Kenan inda Mu'azz yayi sauri juyawa hadi da tambayarsa "what?." Cikin harshen turanci.

Aiko da jiyo haka ta take biriki Inda suma sukayi hakan, Atif Kuma ganin Mu'azz ya matsu yaji dalilin sa na fadin hakane yasakashi nuna masa shatin hannun.

Aiko zura Idanu yayi shima hadi da cewa
"how possible,Taya hakan ya faru?."

"Who are you Really?."
Abinda Atif ya sake fadi kenan,hakan ko yasa Wannan da suke kokarin susan ko wacce ita ta juyo.

Zura Idanu Atif Yayi inda Mu'azz ko yayi furucin cewa...

"Tina! How comes Kuma kinanan bayan.."
fara fadin haka yayi amma bayan yayi ido hudu da koren idanun nata mai kama data macijiya yasakashi sauya maganar hadi da juyo ganinsa kan Atif..

"It can't be her Atif,domin Tina ta mutu tuntuni."

Atif shiru yayi sai sauraransa yake Itako Tina fashewa tayi da dariya wacce wannan dariya idan ka saurara sai hanjin cikin ka ta kaɗa haka kuma bayan tayi hakan ta ɓace tamkar walkiya a tsakar dare.

"Atif shin kaga hakan kuwa Tina ce fa, kenan ta rikiɗe ta dawo wata abar na daban?."
Aiko bayan Mu'azz ya furta hakan sai Atif yayi wani Batu cikin siririyar murya cewar sa shine.

"Hakan na nuna cewar dukkanin su ukun sun rikiɗe sun dawo wani abin na daban kenan." da jiyo hakan Mu'azz ya zura Idanu hadi da cewa.

"Idan da gaske ta rikiɗe to inaga sauran ina suka shiga?."
Tambayan da Mu'azz yayi kenan inda Atif ya kirawo sunan Samra cikin Muryar tsoro.

*_BANGARENSU AMRITA KO_*

"Amrita! Muje ko."
Aiko fadar haka sai tayi daidai da taka step da tayi nan da nan ƙafarta ta shige sulub yayinda suka jiyo wata kara tamkar ana rufe kogo da katon Dutse.
bayan nan saiga kifiyoyi biyu sun baiyana cikin zafin nama da alamun wannan sune tarkon da hafsa ta taka,aiko dojesu sukayi inda tace da sauran abokan tafiyan nata.

"Guys watch Your steps."

"Guys hold on,Mai kuke tunani zamu tarar idan mukabi ta wannan hanyar....wai Atif,tayaya kuke tunanin zai ketara ta wannan hanya ba tare da yaji Rauni ba?,Hmm Babu wanda yasan ire iren bala'i dake shunfuɗe a wannan guri dan Haka zai fi mana sauki idan muka koma Danko bazamu same sa ba."
Abinda ya fito daga bakin Adam kenan inda Amrita ta haɗe Rai hade da buga masa rankwashi aka sannan tace dashi.

"Lusarin Banza! Dama waya gaiyace ka,kaine wanda ka fado cikin tawagarmu bada shiri ba."
Aiko furta hakan da *Amrita* tayi yasa suka fara cacen baki tsakanin su..

"Enough! Amrita Wai Maike damunki ne,Mai yasa kwata kwata bakida tunani,bamusan meye muke tsaye a kaiba mai zai hana ki aje wannan ja in Jan ki taimaka wajen gano mana mafita."

"Hafsa Shin Wai bakiga mu biyu bane muke wannan ja in jar Amma Mai yasa kika alakan ta gani kaɗai?,Hmm Koda shike ba ke bace ta farko kowama haka yakeyi duk lokacin da muke kokarin ɓatawa shi ake goya ma baya."

"Amrita ba haka bane."
Haka Hafsa ta fara furtawa inda Adam yayi saurin cewa..

"Hafsa ina da shawara."
Aiko kafin ta buɗi baki taji Amrita ta mayar masa da martanin cewa...

"Lol wai har kana tunanin akwai shawarar da zamu dauka ne daga gare ka?."

"Ya'Isa Amrita take it easy."
Haka Anwar ya furta inda #Herzad ya riƙe mata hannu hadi da cewa.

"Ki dauka ya wuce tunda yayi shiru."
Aiko bayan ya furta hakan tayi furucin Hmm Hadi da ɗauke kai shiko #Adam ya soma fadin cewa.

"A tunanina akwai hanyar da ake gane step din dake dauke da tarko."

"Taya?."
Tambayar da Hafsa tayi Kenan inda ya sake da cewa.

"Steps din zasu kasance suna da banbanci da saurar idan muka kura ganin mu akansu, sannan indan muka jefi right step da ƴar mitsitsiyar dutse zamuje bazatayi kara sosai ba idan kuma muka jefi wanda ke dauke da tarkon zatayi kara domin akwai rami kasanta.."

Aiko alamar nazari Hafsa tayi na wasu dakiku kafin ta sake tambayarsa cewa..

"Toh taya kasan hakan?."

"Na kalla ne a cikin wata Film."
Ansar daya bayar kenan inda Amrita ta fashe da muguwar Dariya hadi da cewa.

"Well well well Gaskiya kam, wannan ai shiriritar banza ce taya zai dauki abinda ya gani a cikin Film ya kawo mana nan guri."
Haka ta furta cikin kara yayinda take nuna ja ga fadin nasa,amma Hafsa bata tanka Mata ba cewa tayi da #Adam..

"That means kananun duwatsu ne kadai solution,Are You sure zatayi aiki?."

"Yeah I'm pretty sure."
Aiko da jiyo hakan Amrita ta sake hade fuska Hafsa ko ta tsunkuya a hankali ta dauki dutse inda tayi kamar yadda Adam din ya faɗa, bayan sun jiyo sautin dirar dutsen ko sai ya furta cewa.

"Wannan na dauke da tarko."
Amrita ko bayan tajiyo furucin Adam sai ta fashe da dariya hade da kyakkyawa sannan tace dasu.

"Bari na tabbatar muku babu inda shawarar tashi zataje."
Aiko bayan ta furta hakan ta taka da sauri taje ta taka gurin inda Anwar,Herzad da kuma Hafsa sukayi karar cewa No! But Ina ta riga ta taka.

Nan taji ƙafarta ya sauka cikin inda ta zura Idanu domin tasan ko ta tabka babbar ɓarna.....

Al'amarin Su Samra ko zaune take gefe guda inda Mufy ke zaune bayanta Al-hussein ko da ɗan rata tsakanin su sosai,Muzzaffar still cikin duniya matattu yake domin har izuwa wannan lokaci bai farka ba.

"Mstwww oh my God,shin wai su Atif bazasu dawo bane."

"Mufydah aiko ba Wani jimawa mukayi a nan gurin ba and Ina ganin still naiman itatuwan suke domin nasan Atif baya bada Gari idan ya fara abu dan haka mu daɗa hakuri."
Haka Samra ta mayar mata da martani yayinda Al-hussein ya furta cewa.

"Ina Ganin babu jimawa zamu kara gaba,dan haka Mufydah kema ya kamata ki dan samu hutu domin kema kinada rauni."

"What do you mean?, zamu tafi mu kyale su Atif din Kenan bayan mu muka turasu naimo itatuwan."
Cikin kara Samra ta furta hakan inda Mufydah tayi saurin cewa.
✨✨
"Samra cewa fa yayi babu jimawa bawai yace zamu tafi mu kyale su ba."

"Hm so kina nufin kunne na ba daidai yaji ba kenan?."

"A'a ba haka nake nufi ba kawai dai ina nufin kin fassara zancen nashi ta wani harshen na daban."

"Ok Good."
Haka Samra ta furta bayan nan ta hade Rai,ganin haka ko yasa Mufydah ta ɗaga ganinta izuwa kan Al-hussein inda suka hada Idanu....

Al'amarin Mu'azz da Atif ko dakin da suka kasance cikin ta ƙasance itace mafi kankata a cikin ɗakunan da suka wuce abaya domin koda ɗakin Atif na gida yafi wannan dakin girma.
Ɗakin ya kasance babu fadi gashi kuma kofa ɗaya ce tak gareta wato wadda suka shigo ta ciki...

"Oh my God!."
Fadar Mu'azz kenan bayan ya duba lungu da sako na wannan ɗaki,Atif ko cewa yayi.

"Wannan fa tarko ne,kuma tayi hakanne danta cimma wata manufa nata."

"Yeah it maybe,but wata kila tayi hakan ne dan ta gwada basirar mu."
Gajeriyar murmushi Atif yayi bayan ya jiyo hakan,sai Mu'azz ya kai masa tambaya kamar haka.

"What so funny?."

"Hm dakace basira sai nayi mamaki,to ina basira zatayi aiki anan,duba kaga cikin dakin koda tsinke babu a ciki toh taya zamu naimo hanyar fita."

"Kuma fa haka ne, amma mai zai hana mu koma ta hanyar da muka shigo."
Da jiyo hakan Atif ya sake fashewa da dariya hadi da kuma cewa.

"Wata kila nan gurin suka zaɓan mana dan hutu."
Haka suka kasance sunanta tattaunawa tsakanin su kaikace tun fil'azar abokan juna ne.

*Amrita*
"Bari na tabbatar muku babu inda shawarar tashi zataje."
Aiko bayan ta furta hakan ta taka da sauri taje ta taka gurin inda Anwar,Herzad da kuma Hafsa sukayi karar cewa No! But Ina ta riga ta taka.

Nan taji ƙafarta ya sauka cikin inda ta zura Idanu domin tasan ko ta tabka babbar ɓarna.....

Aguje Adam yaje gurin ya tureta suka fadi gefe guda inda da faruwar haka kifiyoyi suka fara fitowa jikin banko babu kakkautawa,hakan sukayi ta dojema kifiyoyin Adam da Amrita ko kwance suke a gurin sai famar kallon ciki Idanun juna sune cikin shauki.

Tsit haka gurin yayi shiru bayan ruwan kifiyoyi da suka sha hakan yasa suka mike tsaye inda suka tsaya waige waige suna jiyar suga Mai zata biyo bayan shirun da sukaji,kwatsam sai suka ga daga cen nesa bango na hadewa su marne guri daya wacce kuma take tunkaro su aiko ganin haka yasa Hafsa tayi sauri cewa "mu gudu!." Haka kuma sukayi har Saida suka tsinci kansu a wata kofa inda da shigarsu ta rufe kanta.

Shigarsu ciki Adam yayi kamar zai faɗi ta sanadiyyar tuntuben da yayi da wata dutse,cerab Herzad ya riko kwalarsa ta baya haka suka kasance tsaye na wasu dakiku kafin Anwar ya tallafa masa suka jawosa aiko saidaya mike tsaye Kafin nan ya sauke Idanu kasa inda tarar da wata ƙatuwar Rami gaban sa wacce yake cike Makil da fararen tsutsotsi ganin haka yasa Adam yayi sauri komawa da baya domin kuwa da acikin zai faɗa idan Herzad bai tallafa masa ba.

Aiko wannan kofa da suka shige ta kasance taku goma ne kacel zaka iyyayi bayan nan kuma sai wannan Rami mai cike da tsutsotsi haka suka fara jujjuya Idanu suna duba cikin wannan guri domin naiman hanyar fita,cen karshen bango suka hangi wata kofa makamancin wanda suka shigo ta ciki.

"Ga cen kofa a bangon karshe na wannan ɗaki."
Haka Amrita ta furta inda suka kai ganinsu gurin.

"Daga nan zuwa wancen kofa zatayi kimanin taku Tamanin,so taya zamu iyya kaiwa ga wancen kofa."
Tambayar da Anwar yayi Kenan inda Herzad yace dashi...

"Babu ta yadda zamu iyya kaiwa wancen kofa saidai idan ta cikin ramin zamu ketara,kuma gashi tana cike da tsutsotsi."

"Haka zalika bamusan zurfin Ramin ba,kunga kenan batun bin ta cikin batama taso ba."
Fadar Hafsa kenan inda Amrita tace da ita.

"That means Babu mafita kenan?."

"Akwai mafita."
Adam ne ya furta hakan inda ta ɗago Idanu ta kalli cikin idanun sa hade da tambaya.

"Meye mafitar."

Haka ta tambaya inda ya mike hadi dayi mata nuni jikin bango...
Itako bayan ta guba sai tace dashi...

"Bango ka nuna sai kuma sandunan wuta dake rataye a jiki,so mai hakan ke nufi?."

"I mean ta jikin Sandunan wutan zamu ketara."

"How possible?."
Tambayar da Amrita tayi kenan inda yayi murmushi hadi da cewa.

"Yayin Ketara wannan ko ƴar caskale kawai muke da bukata."

"Mai kake nufi."

"Hafsa nake nufi domin salon data nuna wajen doje kifiyoyin ne yasa na bata suna ƴar caskale."

Haka Hafsa ta ɗaga hannu da niyar marinsa saiya doje haka suka sake tambayarsa daya basu haske ya zasuyi hakan,nan ya baiyana musu komi aiko babu ɓata lokaci suka ciro wata igiya mai kauri cikin jakarsu haka suka daura a jikin kofar yayinda Hafsa tayi ta tsalle jikin Sandunan wutan tana daurewa har ta kaiga waccen kofa da suke hangosa daga nesa.

"Wow Adam,You did Great."
Fadar Anwar kenan inda Adam din ya juyo hadi da cewa.

"Aiko dama Shiyasa mata sukayi yawa a wannan tawagar,domin mazan wannan tawaga kwata kwata ƙwaƙwalwarsu bataja."

Aiko da jiyo hakan Amrita ta fashe da dariya domin ko tasan ya fadi hakane domin ya rama abinda Anwar din ya Fadi a baya...
Herzad ko Zura Idanu yayi bayan ya jiyo hakan sannan yace dashi.

"Anyway Yakamata mu ketara kafinnan sai muyi wannan dariya."
Haka sukayi ta hayewa daya bayan daya suka kyale Adam a baya,shiko daya haye Saida yakai tsakiyar Wannan igiya ta kunce kanta daga jikin kofar.

Ganin Haka yasa suka buga ihu hade da mika hannu kamar zasu cebkesa...

Idan muka Laika bangaren Forzy ko still tana wannan shesshekar kuka sai taga wata koren haske ya fito ta cikin kasa...
Haka ta tsaya kallon wannan haske har ta rikide ta dawo mutum ganin haka yasa Forzy ta dauki wata karfe mai kama da mashi ta cilla aiko saida wannan karfe yayi kusa da shiga jikin wannan haske amma saita doje haka wannan karfe ta bugi bango da karfin tsiya ta tsaga jikin bangon ta shige.....

Ganin haka yasa Forzy ta mike tsaye don zunzurutun mamaki,nan ta fara jujjuya hannunta tana dubawa domin tasan wannan karfi badaga ita bane ta fito...

*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''


*_Ku kasance tare dani,Guys keep liking and commenting_*

+2349077974042

💀💀💀
*KOFAR AJALI*
_The Return_
'''[Hard way and the only way]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*


*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣5️⃣*
*_Ina Mai bada hakuri game da Hutu dana tafi na 1month ba tare da na sanar da mabiya littafina ba ina mai bada hakuri kwarai da gaske,bayan wannan ina kuma da Bad news tare da Good news the Good news is that Kofar ajali zata fara zuwa muku sau biyu a sati kuma an kara yawan typing and the bad news is that Dayan littafina mai suna kunfa Yakun zata daina zuwa muku a both WhatsApp da Kuma Facebook dalilin kuwa shine na shiga gasar marubuta na Arewabooks da wannan littafi Mai suna #kunfa Yakun wacce dokar shiga gasar shine banda posting a wasu guraren illa Arewabooks dan haka reads Ina Mai gaiyar ku izuwa chakwalkwalin Marubuta Hausa wato #Arewabooks domin karaya littafin Kunfa Yakun a kan farashi mai Rahusa wato ₦100 Only ga wayenda Kuma bazasu iyya bi ta Arewabooks ba zasu iyya jira izuwa karshen wannan wata ta march wacce bayan gasar farashin littafin zata koma kamar yadda take Da wato ₦300 dan haka kada ayi babu ku,ku gaggauta wajen garzayowa Arewabooks domin karantawa tare da manyan marubuta. Fans I need Your support ta yadda zamu lashe gasar Lets win wannan tare Fans_*



_*LABARIN*_
"Hm dakace basira sai nayi mamaki,to ina basira zatayi aiki anan,duba kaga cikin dakin koda tsinke babu a ciki toh taya zamu naimo hanyar fita?."

*Atif* juya Idanu yayi izuwa kusun ruwa huɗu na wannan ɗaki kafin nan ya saki kakkaurar nunfashi hadi da naiman guri jikin kofar ya zauna,haka Mu'azz shima zama yayi a gefen sa inda kafaɗar su ke hade da na juya...

Nan Atif ya lumshe Idanu inda Mu'azz shi kuma ya kura masa Ido ko kibtawa bayayi,a wannan lokaci kuwa da zaka umurce sa da yayi maka bayani yadda fuskar Atif yake ka zana dako zai fada maka komi ba tare da ya canza komi ba... Yana kan hakan kuwa sai Atif ya buɗe Idanu inda suka hada nan da nan Mu'azz ya murmusa hadi da ɗauke Idanu..

"What?."
Haka Atif ya tambaya inda Mu'azz yayi sauri mayar masa da cewar.

"Babu."

"Ehyee wato ana murmushi Babu dalili Kenan?,Toh bari kaga yanda zan saka ka fadi dalilin yin hakan."
Haka Atif din ya furta yayinda yayi kamar zaiyi masa cakulkuli,aiko Ganin haka yasakashi cewa...

"Wait! wait! wait!,zan fada maka."

"Okay muje ina sauraran ka."

Gajeriyar murmushi ya sake saki kafin nan ya sake cewa...

"Nothing oo."
Aiko juyo hakan yasa Atif ya Soma yi Masa cakulkuli, Mu'azz ko Idan da Abinda ya tsana a duniya to cakulkuli ne,Haka ya bada Gari inda yayi gaggawar cewa zan fada..

Kwanciya da gadon bayansa yayi gefen Mu'azz domin kuwa lokacin da yake yimasa cakulkuli tuni ya baje a kasa yana birgima, Soma cewa yayi...

"Kawai ina mamaki ne."

"Mamaki,akan me?."
Haka Atif ya sake mayar masa da tambaya inda ya soma da cewa..

"Ina mamakin yadda yanzu nake iyya tsayawa na kalli fuskar ka, sa'annan na saurari muryarka yayinda kake nuna kulawa ga ƴan tawaga ta,back then Babu wa'yanda muka tsana a duniya sama da ku amma gashi yanzu mune muka kasance killace a daki daya muna fira hade da wasannin... Gaskiya ko wannan ne kaɗai ya issa ya sakani murmushi kuma koda yanzu na daina numfashi bani da kaico sabida nasan Zaka kula da tawagar kamar yadda ya kamata."
Haka Mu'azz yayi ta suburbudo bayani babu kakkautawa yayinda idonsa na saman rufi na wannan daki...
Batare da Atif ya ce dashi komi ba amma hakan bata saka ya daina zuba ba haka yayi ta tunowa Atif ire iren mugunta da kuma nuna tsaya a fili da kungiyar sa sukayi ta musu hada yazo karashe labarin saiya yunkura ya zaunu inda ya soma kame kame da kaga yanayinsa ko kasan yana sone ya bada hakuri amma mai zai faru bayan ya juya Idanu ya kalli Atif yayinda ya soma cewa...

"Atif Ina da wata alfarma da nake bukata daga gare ka a matsayin kana....."
Haka ya fara cewa amma sai yayi tsit bayan ya tarar da Atif na yanayi na bacci..
Aiko gajeriyar murmushi yayi sannan yayi wani batu cikin kasan ransa..

"Hm a tunanina wannan itace dama dana samu da Zan basa hakuri amma sai gashi Bacci ta raba."
Bayan ya furta hakan a kasan ransa ko sai ya sake da murmushi hade da ciro *jacket* dake jikinsa domin yayiwa Atif barko da ita aiko saida ya lulluba masa wannan jacket kafinnan ya yasa hannu da niyar gyara masa kwanciyar....
Aiko taba jikin nasa keda wuya ya zura Idanu hade kuma da yaye jacket din daga jikinsa cikin sauri.........

"No!!!."
Cikin kara *Amrita* *Hafsa* da kuma sauran abokan tafiyan nasu suka Kwarma bagidajiyar ihu inda kuma suka mika hannu kamar zasu cabko igiyar daya tsinke da *Adam* Haka kuwa Wannan igiyar tayi ta sauka sulululu tana gangarawa da Adam din izuwa ramin tsutsotsin nan,saura kiris ya fada cikin ramin tsutsotsin sai yaji cek igiyar ta tsaya dashi ta sanadiyyar makalewa da igiyar tayi tsakanin wasu manyan duwatsu...

Aiko ganin haka da sauran sukayi yasa suka ruga baki daya izuwa inda igiyar ta makala suka Danko igiyar dakyar suka iyya jawosa suka mayar dashi mazaunin sa....Finally sauka yayi daga igiyar bayan sun tallafa masa da hakan,aiko ganin kafafunsa sun diro a kasane yasakashi kwanciya da gadon bayansa a gurin.

Sai faman haki yake bayan nan ya fashe da dariya inda Anwar da Harzad suka biye masa suna kyakyatawa,nan sai Amrita tahau yimasa surutu kamar haka...

"Adam Maike damunka kane wai,mai kake daukar kanka shin kamasan yadda na kimauce a kanka yayinda kake samar wancen abun?."
Haka Amrita tahau Mita yayinda Idanuwan suka cike da kwalla ganin haka yasa Hafsa Anwar da kuma Harzad suka dubi juna sai suka sake mayar da ganin nasu Guri guda inda Hafsa ta soma cewa...

"Guys Ya kamata mu kara gaba sabida zama da yawa Guri daya tsautsayine."
Bayan ta furta hakan yasa Amrita tayi shiru hade da juyawa gefe guda ranta a bace tasa hannu ta dauki jakarta haka yasa Hafsa da Harzad suma sukayi hakan Anwar ko mikawa Adams hannu yayi inda ya kama ya mike tsaye....

Takawa sukayi izuwa kofar inda da zuwa su gurin Adam yasa hannu jikin kofar bayan nan ya soma yaye yanar dake jikin kofar inda kuma yace da sauran...

"Kunga I'm not sure idan kofan nan zata bude,ku gamawa wannan kofa kallo wannan kofa akalla tayi shekaru dubu ba tare da an bude ta ba."

"Oh hakane?,toh mai zai hana mu jarraba bude ta kafin kayi wannan bayani naka."
Haka Amrita ta furta inda Anwar ya mayar mata da cewa....

"Ta ina zamu fara kenan?,kundai san koda karfinmu baki daya za'a tare guri guda bazamu iyya bude wannan kofa ba."

"toh yanzu mai kuke so muyi kenan?,shin komawa baya kukeson muyi kenan?, kundai san mutuwa muka baro a baya so mai yasa kuke kashe jikine haka."
Aiko ambatar mutuwa datazo cikin zancen Hafsa yasa guri ta soma girgizar yayinda suke jiyo wata kara kamar ta direwar *newclear*

Idan muka Laika Ɓangaren su Samra ko still zaune suke a wannan guri suna dakon zuwan Mu'azz da kuma Atif inda Al-hussein ke zaune cen gefe guda yayinda Samra tare da Mufyda ke duba lafiyar Muzzaffar...

"Guys Ya kamata mu kara gaba sabida They are not coming."
Haka Al-hussein ya furta inda Samra ta mike tsaye inda ta soma cewa...

"a tunanin ka kai waye da har zaka bamu ummurni Al-hussein,You Are not part of us,Kai dayane Al-hussein You Are on your own and dan Allah ina rokon ka Ka rabu damu ka daina jefa rayukan mu cikin Haɗari..."
Haka Samra ta furta yayinda idanunta suka cike da kwalla nan sai taji Mufyda ta dafe kafaɗar ta..

"Samra Abinda nakeso ki fahimta anan shine Komai na duniya na faru ne da dalili,kamar yadda nayi imani cewa zuwan namu wannan guri ma nada dalilin sa saidai har yanzu mun kasa fahimtar meye dalilin zuwan namu nan Gurin."
Ajiyar Rai tayi kafin ta sake da cewa...
"Ni a ganina barin mu nan Gurin nada anfani domin idan har Atif da Mu'azz zaku iyya dadewa haka basu dawo ba toh akwai muhimmiyar dalilin da yasa zasuyi hakan mu kuma da muke nan jiran nasu dalilin da zai saka mu bar wuri shine zama guri daya a wannan guri nada haɗari kinga kenan komi nada dalili Samra."
Aiko bayan ta karashe fadar haka sai Samra ta soma zubar kwalla yayinda tayi saurin rungume ta haka dai suka kasance cikin yanayin kuka.... Babu kuma abinda ta fado mata a ka sai tunanin Ranar nan da suke hanyar zuwa wannan Gurin inda daya daga tawagar tasu take yiwa tawagar su Mufyda Dariya "anyway yanzu dai ba lokacin bane na shiga irin wannan yanayi yanzu lokacine na gyara kurkuren mu, gaskiya ya kamata kowa ya koma ga iyyayensa domin War haka dukkanin iyyayenmu suna cikin damuwa."
Haka Samra ta furta cikin Ranta bayan nan ta juya ta kalli Al-hussein,batare data ce komi ba ta fara da Hada gado da zasu dauki Muzzaffar din akai dan gudun kamuwa da cutar da Muzzaffar din ke dauke da....

Haka suka dauki Muzzaffar din bisa wata gado na sanduna da suka hada yayinda Al-hussein ke rike da sanduna biyu ta gaba Samra da Mufy ko suna rike da ɗaddaya a baya...
Haka suka taka suka bar wannan guri inda da barinsu wannan guri wata jar hayaki ta Soma bullulowa daga kasa bayan wasu dakiku saiga Wannan ƴar karar ramar yarinya ta baiyana gefen ta kuma Ali ne da

Please Login or Register in order to submit comment