Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ke ciki?" Sa'adda Hursiya taji wannan tambaya sai ta dubi gawar halittar da kyau ta ga yadda ta rufe Dujalu ruf babu wata karamar kofa da za a iya zareshi.

Nan take hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya, don haka sai ta mike tsaye ta dubi gaba dayan dakarun da ke Wajen mutane da aljanu ta daka musu tsawa.

Gaba dayan dajin yai tsit! Kowa ya zuba ma ta idanu. A sannan ne hawaye ya zubo daga idanun Hursiya ta budi baki ta ce, "Ashe gaba dayanku nan taron banza ne taron wofi Ku dubi halin da sarkinku ke ciki, ashe đayanku ba zai yi tunanin hanyar da za a bi a zaroshi ba daga karkashin gawar wannan halitta ba?". Koda jin wannan batu sai kowa yai tsuru- tsuru ya shiga taitayinsa aka marmatso ana nazarin yadda za a yi a janye gawar katuwar halittar daga kan sarki Dujalu. Nan fa aka shiga yin shawarwari.

Wasu zaratan jaruman yaki guda uku, wadanda babu kamarsu a cikin dakarun suka ware đaya gefe Suna shaqara Dayq daga cikin wadannan zaratan jarumai aljani ne, sunansa Karbazu, a gaba đayan dalkarun aljanun da ke wajen babu sadauki kamarsa, kuma ma'sbocin hikima ne da sanin dabarun yaki matuka. Na biyunsu kuwa mutum ne, Sunansa Barsuma. Barsuma shi ne sarkin yakin binin Hawarul din. Shima ya kasance gagarumin....

MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Part : 2
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023
Nan take hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya, don haka sai ta mike tsaye ta dubi gaba dayan dakarun da ke Wajen mutane da aljanu ta daka musu tsawa.

Gaba dayan dajin yai tsit! Kowa ya zuba ma ta idanu. A sannan ne hawaye ya zubo daga idanun Hursiya ta budi baki ta ce, "Ashe gaba dayanku nan taron banza ne taron wofi? Ku dubi halin da sarkinku ke ciki, ashe đayanku ba zai yi tunanin hanyar da za a bi a zaroshi ba daga karkashin gawar wannan halitta.

Koda jin wannan batu sai kowa yai suru-tsuru ya shiga taitayinsa aka marmatso ana nazarin yadda za a yi a janye gawar Katuwar halittar daga kan sarki Dujalu.

Nan fa aka shiga yin shawarwari. Wasu zaratan jaruman yaki guda uku, wadanda babu kamarsu a cikin dakarun suka ware gefe đaya shawara.

in baku manta ba anan muka tsaya kwanaki yanzu kuwa zamu cigaba.

Daya daga cikin wadannan zaratan jarumai aljani ne, sunansa Karbazu, a gaba dayan dakarun aljanun da ke wajen babu sadauki kamarsa, kuma ma'abocin hikima ne da sanin dabarun yaki matuka.

Na biyunsu kuwa mutum ne, Sunansa Barsuma. Barsuma shi ne sarkin yakin birnin Hawarul din. Shima ya kasance gagarumin halitta ba?". sadauki kuma gwarzon mayaki a cikin jinsin bil'adama wadanda babu kamarsu a gaba dayan nahiyar. Shima ya kware matuka a sanin makama da dabarun samun nasara a yaki.

Mutum na uku wani tsohon sadauki ne wanda shekarunsa sun haura casa'in amma har gobe yana dakawa matasa gumba a hannu wanda ake kira da suna Shurkaib bin Dallas.

Lokacin da Kurbazu,Barsuma da Shurkaib suka ware gefe daya domin su yi shawara bisa dabarar da za a yi a sami nasarar zaro sarki Dujalu daga kankashin gawar halittar sai Karbuza ya dubi Barsuma da Shurkaib ya ce ,"Yanzu ku mene ne shawararku,ta ye ya kuke ganin za mu iya zaro sarki ba tare da lafiyarsa ta tabu ba?

Abu na farko dai, janye gawar wannan halitta daga kansa ba karamin aiki bane, saboda girmanta da nauyinta. Idan gaba dayanmu zamu taru bazamu iya ture ta ba da karfin tsiya. Idan muka cezamu zauna anan muna kula da sarki har izuwa lokacin da halittar za ta rube mu sassareta totabbas warinta ma zai iya zama ajalinmu gabadaya. Yanzu sai ku fadi shawarwarinku kafin nafadi tawa ku ji mu zabi wadda za ta fi inganci".

Koda jin wannan batu sai tsoho Shurkaib yayi murmushi ya ce,"Ni ba zan fadi tawa dabararba sai naji taku, kuma zan fadi tawa dabarar ne bayan an jarraba taku ba a sami nasara ba, kuma bisa sharadi guda". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Karzuba da Barsuma. Barsuma ya ce,"Ya kai Shurkaib ka shiga taitayinka fa ka san abin da kake fadi. Yanzu har ka isa ka sanya wani sharadi don ceton rayuwar sarki? Baka tsoron cewa idan dabararmu ta yi nasara sarki ya ku6uta fishinsa zai iya tabbata akanka?"

Koda jin wannan batu sai Shurkaib ya bushe da dariya, sannan ya ce, "Ku a tunaninku ni ina tsoron mutuwa ne? Ku tuna cewa shekaruna sun haura casa'in a duniya, na haifi 'ya'ya, 'ya'yanma sun haihu, nayi yake-yake da dama ba adadi.Babau irin masifar da ban gani ba a duniya, kuma babu wani buri da ban cika ba face guda daya,kuma yanzu ne na sami damar da zan cika wannan buri nawa bisa wannan uzuri da ke gabanmu.

Ina tabbatar muku da cewa duk dabarar da za ku kawo domin a kubutar da rayuwar sarki ba za a yi nasaraba. Tawa dabarar ce kadai za a bi a samu nasara. Yanzu na baku dama ku fara gabatar da taku dabarar idan ba a dace ba sai na fadi tawa, idan har sarkiya amince da sharadina". Sa'adda Karbuza da Barsuma suka ji wannan batu, sai suka kara cika da mamakin Shurkaib suka tabbatar da cewa da gaske yake.

Karbuza ya ce, "Shi ke nan ai yanzu sai ka zomu je wajen sarki domin mu gaggauta yin abin daya kamata mu yi domin 6ata lokacinmu a cikin wannan daji tamkar baiwa abokan gaba dama ne su rigamu zuwa inda takobin Saiful Lujara take."

Koda jin haka sai Barsuma da Shurkaib sukace cikin hadin baki, "Zancenka dutse ne". Nan take su ukun suka dawo inda sarki Dujalu ke kwance a karkashin gawar wannan halitta. Duk su ukun suka durkusa a gabansa. A wannan lokaci Hursiya ta tallafo kan sarki Dujalu ta dura masa ruwa a baki. ya sha Gama shan ruwan nasa ke de wuya ya yi arba da su Karbuuza tsugunne a gabansa sai ya dubesu a fusace ya ce, "Me kuke jirane har yanzu baku yi tunanin


Karbuza ya ce, "Shi ke nan ai yanzu sai ka zo
ya kamata mu yi domin 6ata lokacinmu a cikin
mu je wajen sarki domin mu gaggauta yin abin da
WannAn daji tamkar baiwa abokan gaba dama ne
su rigamu zuwa inda takobin Saiful Lujara talke."
Koda jin haka sai Barsuma da Shurkaib suka
ce a cilin hadin baki, "Zancenka dutse ne".
Nan take su ukun suka dawo inda sarki
Dujalu ke kwance a karkashin gawar wannan
halitta.

Duk su ukun suka durkusa a gabansa.
A wannan lokaci Hursiya ta tallafo kan sarki
Dujalu ta dura masa ruwa a bali ya aha. Gama
shan ruwan nasa ke da wuya ya yi arba da su
Karouza tsugunne a gabansa sai ya dubesu a
fusace ya ce, "Me kuke jirane har yanzu baku yi
tunanin dabarar da za ku yi ba ta ceto rayuwata?"
Kurbazu ya numfasa ya ce, "Ya shugabana ai
abin da muka ie muka tattauna ke nan, kuma
kowannenmu yana da tasa dabarar dabam.

Zamu fara jarraba tawa dabarar, in yaso a jarraba ta Barmusa, idan tawa ba tai nasara ba, idan shima tasa bata yi ba sai a jarraba dabarar Shurkaib."

Sarki Dujalu ya ce, "Na umarceku da ku aikata hakan cikin gaggawa domin idan muka kara
kwana hudu anan cikin wannan daji rundunar su
sarki Maharaz za ta zo ta riskemu.

Ni kuwa shirina shi ne mu rigasu zuwa tekun bahar Sufiya ya zamana cewa kafin su isa tuni mun dauko takobin Saiful Lujara."


Karbuza ya dubi dukkanin dakarun aljanun
da ke wajen ya ce, "Na umarceku da ku ruga
Zuwa cikin wannan daiji ku tsunko murtuka-murtukan jijiyoyin bishiyoyi dogaye ku zo da su yanzu."


Kafin Karbuza ya gama rufe bakinsa tuni gaba dayan dakarun aljanun sun 6ace 6at! Kafin cikar dakika sittin sai gasu sun dawo dauke da dogayen jijiyoyin murtuka-murtukan bishiyoyi masu yawan gaske tamkar za su yiwa dajin gaba daya rufi da su.

Ba tare da 6ata lokaci ba Karbuza ya umarcesu da su kukkula jjiiyoyin wasu jikin wasu. Nan da nan aka samar da dogayen igiyoyi Da jijiya barkatai.

Karbuza ya sake bada umarnin a đaura jijiyoyin a jikin gawar katuwar halitar. Kowacce doguwar jijiya daya aka sa kartin aljanu majiya karfi guda dubu suka riketa. A kalla an sami sama da aljanu miliyan đeya. nan take aka basu umarni da su ja igiyar sama a lokaci guda, domin su daga gawar sama daga kan sariki Dujalu domin a sami damar zareshi.


Aljanun gabe đayansu suka tattaro karfin dantsensu suna jen jijiyoyin a lokaci guda. Maimakon gawar halittar ta rabu da kasa, sai gaba dayan jijiyoyin da aka đaura a jikinta suka tsittsinke, aljaanun suka fado kasa gaba dayansu.


Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki ke nan a wajen, kuma hankali ya dugunzuma. Sarki Dujau ya juyo da wuyansa da kyar ya dubi Barsuma cikin alamun karayar zuciya ya ce, ya kai Barsuma babban gwarzo, NAMIJIN DUNIYA, mai dakawa maza gumba a hannu, ka ga yadda dabarar Karbuza ta kare, kai kuma wacce dabara ke gareka?"


Barsumna yai gyaran murys sannan ya ce, "Ina son aje a nemo mini giwaye adadin ninkin wannan ajanu Su dari. Ma'ana kowanne aljani guda giwa dari ce za ta wakilceshi, sannann a nemo mini dogayen sarkoki murtuka-murtuka na karfe a daura a jikin gawar wannan halitta sannan a daure jikin giwayen domin su ja sarkar su janye gawar". Koda jin haka sai dakarun miliyan dubu daga cikin aljanun sulka 6ace Bat a lokaci guda.

Kafin kiftawar ido sai gasu sun dawo tare da wadannan giwaye da sarkofin karfe. Kamar yadda Barmusa ya bada umarni haka aka yi, amma koda giwayen suka yunkura suka ja sarkokin karfen, sai sarkofin suka tsintsinke saboda tsananin nauyin katuwar halitar sai gani aka yi giwayen na faduwa wasu na danne wasu.

Nan fa hankali ya kara dugunzuma fiye da ko a yaushe, zuciyar sarki Dujalu ta kara karaya ya fitar da rai ga cika burin rayuwarsa ya fara tunanin cewa tabbas ajalinsa yn gabato.

Duk da sanin hakan sai ya yi ta maza ya dubi Shurkaib ya ce, "ya kai tsoho mai dabara, ya kai tudu mai nisan da yaro ba zai hango ba. Ya kai masanin jiya, kuma masanin gobe, ka ga yadda dabarun yan uwanka suka kasan ce. Ka sani cewa karfin tsafina da kerfin damtsena ba za su ceceni ba daga cikin wannan hali da na shiga ba, wacce dabara ce da kai wadda in dai aka yi ta zan tsira da rayuwata? Na yi maka alkawari idan har ka ceci rayuwata duk abin da kake bukata zan baka shi in dai akwai shi anan duniya domin rayuwata ta fishi daraja a idanuna".


Sa'adda tsoho Shurkaib yaji wannan batu na sarki Dujalu sai ya cika da tsananin farin ciki bai san sa'adda ya saki mumushi ba sannan ya dubi Dujalu cikin nutsuwa ya ce, "Ya shugabana idan na fadi dabarata ba a cimma nasara ba na yarda kasa a kasheni a take a wannan wuri.

To amma ka sani cewa ba zan fadi dabarata ba face ka dada jaddada alkawarin da ka furta yanzu kuma ka rubutashi a rubuce tare da sa a buga hatiminka" Koda jin haka sai sarki Dujalu ya girgiza kai yana mai nuna alamar cewa ya aminta da hakan. Nan take ya sa aka kawo masA tauwada da alkalami gami da fatar rubutu. Har ya dangwalo tawada zai yi rubutun bisa fatar sai Huriya ta yi sauri ta rike hannunsa a lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta ta ce,

"Haba ya dan uwana ina amfanin rayuwa idan buri bai cika ba? Yanzu idan Shurkaib ya ce abin da muka fito nema ya ke so Koda jin haka sai kowa da ke wajen yai tsuru-tsuru har shi kansa sarki Dujalu kuwa Shi kuwa tsoho Shurkaib sai ya yi murmushi ya ce, "Ko kadan bani da muradin kayan yakin MAZAN JIYA". Da jin haka sai garki Dujalu yai marmushi, nan take ya yi rubutun yarjejeniya cewa ya amince duk abin da Shurkaib ya furta yana so zai bashi bayan dabararsa ta cimma ga ci.

Bayan ya gama rubutavwar ne aka kawo hatimi ya buga, kuma ya mikawa Shurkaib bada shakkar komai ba. Shurkaib ya karbi takaddar yarjejeniyar ya sanyata cikin aljihunsa sannan ya dubi gaba dayan aljanun da ke wajclen ya ce, "A Cikinku wane ne mafi sanin sirrin hakan kasa?". Koda jin haka sai wani tsamurmurin aljani ya faga hannu ya ce, "Yau shekarata dubu sabain ina aikin hakan kabari a garinmu".
take Shurkaib ya dubeshi yai mumushi ya ce, s "Matso nan kusa da inda sarki yake. Ina son ka haka rami karami dai-dai fadin gangar jikin sarki a karkashinsa yadda zai fada cikin ramin ba tare da kasa ta zabtare ba gawar wannan katuwar halitta ta sake danne shi bs".

Nan take kuwa wannan aljani ya bi wannan umarni ya kama aikinsa. Ko sa'a daya bata cika ba sai ya kammala aka ga sarki ya fado cikin ramin daga karkashin katuwar gawar halittar. Cikin matuka zafin nama kayi sauri aka zare sarki Dujalu daga cikin ramin.

Ai kuwa ana gama Zareshi ke nan sai kasar wajen ta rufta saboda nauyin gawar halitar, gawar ta lume a cikin ramin, dajin gaba đaya ya kama girgiza saboda gawar haittar, ta ci gaba da nutsewa izuwa cikin karkashin kasa.

Ba shiri kowa da kowa ya kama gudu. Sai da aka yi gudu na sa'a shida sannan aka isa inda kasa bata girgiza sannan aka tsaya ana haki. Daga inda aka tsaitsaya ana iya hango yadda komai na wancan dajin ya nutse izuWa cikin karkashin kasa ya zamana Cewa ba sauran bishiyoyi da duwatsu wedanda ake iya hangowa.

A wannan lokaci ne kOwa hankalinsa ya dawo jikinsa. Bayan an nutsu sai sarki Dujalu ya tako da kafafunsa yazo gaben Shurkaib ya tsaya daf da shi yadda har suna iya jin numfashin junansu.

Sarki Dujału ya dubeshi cilkin murmushi ya ce, "Yanzu sai ka fadi muradinka naji domin na cika alkawarina". Koda jin haka sai kowa ya yi tsit! Dajin gaba đaya yi shiru tamkar mutuwa ta gifta, kamar suma sauran halittun da ke dajin sun yi shiru suna Sararon munafunci. Tsoho Shurkaib yai gyaran murya ya ce, "Ba wani abu nake so ka bani ba face auren yar uwarka gimbiya Hursiya, kuma ba nine mijinta ba, đana za ka aurawa".


Koda sarki Dujau yaji wannan batu sai gaba đayan jikinsa ya kama karkarwa saboda tsananin bakin ciki, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar za ta kone. Nan fa Duialu yaji nadama tazo masa bisa babban sirrin alkawarin da ya dauka, saboda wan da ya 6oye a cikin zuciyarsa wanda duk duniya babu wanda ya sanshi face shi kadai. Inda sarki Dujalu ya san cewa abinda Shurkaib zai bukata kenAn da ya zabi a barshi a cikin halin da yake ciki ya rasa rayuwarsa, burinsa ya rushe in yaso gimbiya Hursiya ta koma gida ta ci gaba da sarauta.


Kawai sai aka ga idanun sarki Dujalu sun kada sun yi jawur tamkar an gasa đanbuda a wuta. Cikin sanyin Jiki ya sunkui da kansa kas ya ce, Lalai zan zamo mai cika alkawari a gareka bayan mun samo abin da muka fito nema". Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya tafi izuwa gaban wata korama ya zauna ya kurawa ruwan koramar idanu yana zubda hawaye.

Ya yin da Hursiya ta ga hakan sai itama tA nufi inda yake. Koda sarki Dujalu ya waigo ya ga ita ce ke tahowa gareshi sai yai sauri ya goge hawayensa. Hursiya tazo ta zauna daf da shi sannan ta dubeshi cikin mnurmushi ta ce, "Ya kai dan uwana ina dalilin da yasa na ka ga shiga cikin halin damuwa bisa jin bukatar tsoho Shurkaib? Shin baka son na auri dansa ne saboda bai kasance jininmu ba?".

Lokacin da sarki Dujalu yaji wannan tambaya sai ya dubeta ya maida mata da martanin murmushin cikin yake sanann ya ce, "Ya ke 'yar uwata kiyi sani cewa bukatar Shurkaib tazo mini da shammace, ban taba tsammanin cewa kece muradinsa ba ga đansa. Ki tuna cewa a tarihin zuri'armu babu wani jininmu da ya taba auren bare, yanzu gashi Shurkaib zai karya mana wannan tarihi. Bugu da kari, ina bakin ciki ace ranar da babu ni, mulkinmnu da dukiyarmu da duk Wannan đaukaka da nake nema mana a yanzu za ta koma wajen zuri'ar tsoho Shurkaib, domin idan kika auri đansa tamkar hakan ta tabbatu ne."


Lokacin da Dujalu yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama Hursiya ta rungumeshi ta fashe da kuka. Shi kuwa sai ya cika da tsananin farin ciki a cikin zuciyarsa. Hakika rashin sani yagi dare duhu. Inda Hursiyya ta san sirrin da sarki Dujalu ya boye ma ta da taji ta tsaneshi fiye da yadda ta tsani mutuwarta Haka dai Hursiya da sarki Dujalu suka ci gaba da hira a nan bakin koramar har izuwa lokaci mai dan tsawo.

Daga can sai Hursiya ta dago kai ta dubeshi ta ce, "Ya ki đan uwana kayi sani cewa zuciyata ta kasa samun sukuni saboda rashin jin ci gaban labarin sadauki Hantaru. Lallai ina son naji yadda karshen rayuwarsa ta kasance". Sa'adda sarki Dujalu yaji wannan batu sai ya yi mrumushi sannan ya ce, "Ya ke yar uwata dama na san cewa kina cikin kaguwa bisa son jin ci gaban wannan labari, saboda haka Zan yi iyakar kofarina na kammala miki wannan labari kafin wayewar gari, domin so nake gobe da sassafe mu ci gaba da tafiya domin mu isa tekun bahar Sufiya akan lokaci, kafn su sarki Maharaz su zo su riskemu".

Ya yin da Hursiya tajii wannan batu, sai ta cika da farin ciki ta nutsu tana mai kurawa sarki Dujalu idanu, shi kuwa sai ya yi gyarsn murya ya cigaba da ba ta labari kamar haka.


Lokacin da hantaru ya zama katon dutse wannan jibgegegiyar Micijiyar ta hadiyeshi, sai macijiyar ta shiga cikin wani irin mugun hali domin dutsen ya zame ma ta masifa a cikin cikinta, yai ma ta nauyi, ya ZAmana cewa da kyar ta ke iya motsawa.

Koda taji dutsen na damunta sai ta fara kokarin ta sake yin amansa waje da karfin taiya. Idan ta turo dutsen izuwa makogwaronta sai dutsen ya koma da baya, wato ya ki yarda ya ito. Nan fa Macijiyar ta kama tumuwa da kasa, tana dukan kowacce kusurwa ta kogon da kawunanta, al'amarin da ya sa gaba dayan kogon ya ragurguje ke nan ya kama girgiza. A duk sa'adda micijiyar ta tumu da kasa sai dutsen cikin cikin nata yaji kamar zai tarwatse don haka bisa dole dutsen ya taho da kansa izuwa makogwaronta.

Koda jin hakan sai Macijiyar ta wangame bakinta wanda dutsen ke ciki, sannan ta sake wangame wani bakin dabam ta sokashi a cikin wancan domin ta zaro dutsen. Koda dutsen ya ga haka sai ya rikide ya zama wuta. Ai kuwa Macijiyar na hadiye dutsen wutar sai tayi bindiga ta tarwatse, sassan jiikinta ya yi flla-flla a kasa tamkar an yankashi gutsun- gutsun, sai ga dutsen wutar ya gangara Can gefe daya.


Nan take dutsen ya rikida ya zama sadauki Hantaru kwance a kasa, duk jikinsa yai kaca-kaca da raunika, jini na zuba yana numfashi da kyar kamar ransa zai fita. A Sannan ne nadama tazo masa, ya tabbatar da cewa abune mawuyaci ya sami nasarar daukar takobin daraja a cikin wannan kogo, musamman da ya dubi ragowar rijiyoyin da bai bude ba guda đari tara da casa 'in da tara.

Babban abin tsoro a gareshi shi ne, rashin sanin rijiyar da takobin Saiful Lujara ke ciki, ko shakka babu kowacce rijiya ba Za a rasa mugun abu ba a ciki. Idan ya bude wadda ya gamu da abin da zai hallakashi a ciki shi ke nan burinsa ya yanke, kuma dak wahalar da ya sha a baya ta zAma a banza.


Hantaru ya tuno da batun mahaifiyarsa Salimat wadda ba ita ce ta haifeshi ba amma kuma yana kaunarta fiye da kowa a rayuwarsa sai kuma gimbiya Larziya wadda a halin yanzu ya kamu da tsananin begenta har ya amince ya sallama rayuwarsa domin ya mallaketa. Hantaru ya tuno da batun cin amanar da mahaifiyarsa ta jini ta yiwa sarki Kusaidu ita da boka Ardusa.

Lallai yana son ya koma birnin Kisra domin ya yiwa Farzira da boka Ardusa hukunci bisa wannan cin amana, kuma ya sadu da sarki Kusaidu wanda ke matukar kaunarsa a matsayin dan cikinsa.

To amma ai Salimat ta gargadeshi akan kada ya taba lafiyar Zarifa. Abu na biyu da ya fadowa Hantaru a rai shi ne, batun alkawarin da ya đaukarwa gimbiya Lazirina cewar duk wuya duk rintsi ba za su rabu ba, kuma duk bukatar da tazo masa da ita zai biya ma ta ita. Koda Hantaru yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta karaya, ya fara tunanin hanyar da zai bi ya yi jinyar jikinshi sannan ya ci gaba da bude ragowar rijiyoyin guda dari tara da casa'in da tara har ya sami wadda takobin Saifal Lujara ke ciki.


Hantaru ya tambayi kansa a cikin ziciyarsa ya ce, "Yanzu ta ya ya zan reyu a cikin wannan kogon dutse babu ruwa babu abinci?" Koda aiyana hakan, sai idanunsa suka kai kan sassan jikin Macijiyar da ya kashe da kuma jinin jikinta da ya malala ya cika kasan kogon wanda za a iya yin wanka a cikinsa.

Hantaru ta daga kansa sama ya yi arba da wasu tsirarun ciyayi da kananan bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen, sai farin cilki ya kama shi, don ya fahimci cewa zai iya rayuwa a cikin kogon izuwa tsawon kwanaki kadan.

Hantaru ya fara da tunanin abinda ya kamata ya fara yi a yanzu tun da gashi har jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin da ke zuba daga raunikan jikinsa Lallai ya zama dole ya yi tunanin abin da zai ya tsaida jinin. Cikin matukar karfin hali ya mike tsaye yana tangadi ya kama hawa kan duwatsun dake cikin kogon yana dogarawa ya isa inda ya hango wata bishiya mai faffadan ganye.


Sai da ya rage saura baifi taku uku be ya isa inda bishiyar take sai ya zame ya fado kasa Haka dai ya daure ya sake tashi ya hau kan đutse. A karo na biyu ma bai nasara ba sai ya fado. A karo na uku ne ya samu dama da kyar ya tsinko ganyen ya fado kasa a matukar galabaice.


Da jen ciki yaje inda wata busasshiyar karamar bishiya take ya karyo kirare a jikinta, ya sake dawowa da baya ya dauki duwatsun wuta biyu ya dinga gogasu akan wadannan kirare har wuta ta kama A haka ne ya dinga narka ganyan wannan bishiya da ya karyo yana mannashi a jikin raunikan jikinsa.

Duk sa'adda ya manna ganyen sai yaji kamar ya kurma ihu saboda tsananin zafi da zogin da ke shigarsa. Har wani irin gumi da haweyen azaba ne ke zubo masa.

Bayan ya gama sa maganin a jikin dukkanin raunikan jikinsa ne ya kwanta ya huta tsawon rabin sa'a a sannan ne jini ya daina zuba daga jikinsa ya dawo cikin haiyacinsa sosai. Nan take Hantaru ya mike zaune ya tsinto sassan jikin Macijiyar nan ya soka a jikin itace ya gasa, wato yai tsire. Haka ya ci gaba da gasa naman Macijiyar har ya gasa mai yawa ya zamana Cewa naman ya gasu sosai yadda zai kwana biyu bai lalace ba. Daga wannan rana Hantaru ya ci gaba da rayuwaa cikin wannan kogo yana mai ci gaba da jinyar jikinsa domin ba zai iya ci gaba da bude Sauran rijiyoyin ba, ya zamana cewa bashi da abinci sai wannan gasasshen naman Macijiyar, kuma bashi da ruwan sha sai jininta da ya malala a kasa.


Har sai da jinin Macijiyar ya daskare ya ZAmana cewa sai ya sareshi da takobi yake sha. Wannan gasashen naman kuwa sai ya lalace ya rube har ma ya fara tsutsa, amma a hakan yake cinsa domin ya rayu kada yunwa ta kashe shi. Hantaru dai bai samu cikakkiyar lafiya ba sai bayan kwana goma sha uku.

A

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment