Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hantaru ba ya yi da kansa budurwar ce take yi masa don haka ne suka shaku ainun suka saba da juna amma babu wani abu da ya taba shiga tsakaninsa.

Wani abin mamaki shi ne a tsawon kwanaki goma sha hudu basu taba yin hirar soyayya ba kuma Hantaru bai taba jin sunan budurwar ba a duk sa'adda yaso ya tambayeta sunanta sai ta bagarar da zancen ta sauya hirar da suke.

A iya rayuwar Hantaru in ka đauke Salimat wadda ta raineshi a matsayin mahaifiyarsa bai taba samun kusanci ga ya mace ba gami da sabo face wannan budurwa. A ranar da kwanaki goma sha hudu suka cikane, Hantaru ya tashi da sassafe daga barci koda ya - dubi kansa a cikin madubi sai ya ga fuskarsa da jikinsa sun yi kyau matuka kuma sannan ya yi haske da kiba har wani irin sheki fatar jikinsa ke yi. Nan take yaji wani irin farin ciki ya baibayeshi musamman da ya tuna cewa yau ne zai bar Wannan gida domin ya tafi izuwa birnin Darul Mahsbul.


Hantaru na tsaye a gaban madubi yana kallon kansa sai kawai ya ga wannan budurwa tsulum a gabansa, idanunta sun kada sun yi jawur kai da gani ka san cewa ta dade tana kuka, Al'amarin da ya matukar đugunzuma hankalin Hantaru ke nan yaji kamar ya fasa tariya a yau, kawai sai ya budi baki da nufin ya tambayeta dalilin da ya sa ya ga idanunta sun yi jawur, kawai sai budurwar ta juya masa baya ta dauko takobin Saifal Lujara ta mika masa ya karba sannan ta kama hannunsa ta jashi suka fita daga cikin dakin.


Nan fa suka kama yawo a cikin harabar gidan, su shiga nan su fita can. Nan fa Hantaru ya cika da matukar al'ajabi ya zama cikakken dan kauye, saboda ganin irin daular da aka shirya a gidan ko a tarihi bai taba jin labarin gidan sarautar da ya kawatu ba kamar wannan. Duk wani abu na jin dadin duniya an tanadeshi a cikin gidan har da ma wanda ido bai ta6a hasashen gabaninsa ba.

Sai da guka shafe sa'a uku suna shiga sako sako, lungu-lungu na gidan amma Hantaru bai ga alamar Sun kusan kure gidan ba.

Aľamarin da ysa yaji ya ƙagu ke nan, domin hankalinsa na kan tafiya birnin Darul Habul. Koda budurwar ta fahimci halin da Hantaru ke ciki sai ta ruko hannunsa suka tsaya cak kuma suka fuskanci juna, kawai sai ya ga hawaye ya zabo daga cikin idanunta.

Alamarin da ya matukar baahi mamaki ke nan ya dubeta cikin kaduwa ya ce, "Ya ke Wannan ma'abociyar karamci da kyawu ina dalilin zubar wannan hawaye naki?"

Koda jin wannan tambaya sai ta yi murmushi mai taushi a gareshi ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, gwarzon zamani, kuma traron wannan shekara, kayi sani cewa sunana Hayatul Lumhas. Na kasance 'ya guda daya jal ga sarki Thibur na birnin Hindu.


A halin yanzu masAna bincike sun tabbatar da cewa duk duniya babu wata mace mai kyau kamata, amma tun ina jaririya mahaifina ya boyeni a cikin dakin tsafinsa ban taba fita ko Ina ba har na girma na cika shekara goma sha takwas, shi yasa a duniya ba a sanni ba.

Kaine Damijin farko da na taba gani a rayuwata ban da mahaifina, hatta mahaifiyata ban taba ganinta ba, ban San ta ba umn ban sha nononta ba har aka kawoni wannan gida kimanin shekaru hudu da suka gabata sa'adda nake da shekaru goma sha hudu a duniya.

Lokacin da mahaifina ya kawoni wannan gida ya ajiye ni a sannan ne na ga ya dubeni ya fashe da kuka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na ruke kafadarsa cikin matukar damuwa na ce, "Ya kai Abbana ina dalilin kukanka, kuma me yasa ka kawoni cikin wannan gida wanda ke tsal
kiyar dokar daji?.

Sa'adda mahaifina yaji wannan tambaya sai ya share hawayensa sannan ya ce, "Ya ke yata ki yi sani cewa ba komai ne ya sani wannan kuka ba face sanin cewa yau ne ranar da zan rabu da ke rabuwa ta har abada, domin yau saura kwana bakwai kacal na bar duniya. Abin da ya sa na kawoki nan na ajiyeki kuwa shi ne, anan ne kadai ZA ki iya zama lafiya har izuwa karshen rayuwari, idan na barki a can kasarmu kika gaji karagata ta mulki duniya ba za ta zauna Iafiya ba domin gaba dayan sarakunan duniya za su tayar da hankalinsu a kan sai sun mallakeki saboda tsananin kyawunki, al'amarin da zai janyo yakin duniya ke nan ayi asarar rayuka da dukiya wacce bata da adadi.

Bisa wannan daili ne yasa na rabaki da mahaifiyarki tun daga ranar da aka haifeki kuma na Boyeki da karfin sihiri yadda babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya ganinki bare bar ya kai labarinki wani wajen.

Baki san kowa ba, kuma ba ki shaku da kowa ba face ni, yau gashi lokacin rabuwarmu ya yi, don me ba zan zubar da hawaye ba? Na yi bincike a cikin taskar tsafii na gAno Cewa nan da shekaru hudu za'a sami wani gawurtaccen jarumi wanda zi shiga kogan mazzabatal Dulshul wanda ya gagareni shiga ya dauko wata takobi da ake kira Saiful Lajara WaR'nnan jarumi zai sha bakar wahala a cikin kogon tamkar zai rasa rayuwarsa da kyar zai iya guduwa daga cikin kogon.

Aljanun da ke gadin takobin Saifal Lujara za su biyoshi domin su halaka shi, a sannan ne nake son ki je ki ceci rayuwarsa ki kawoshi nan gidan tare da takobinsa ta Saiful Lajara. Na sani cewa wannan jarumi idan ya ganki dole ne yaji yana sonki, fatana shi ne ki zamo abokiyar rayuwarsa domin shi kadai ne zai iya aurenki ya iya zama da ke lafiya". (Sai kuma ni mai typing Shuraih 99%)

Sa'adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na dubeshi cikin mamaki na ce, "Haba Abbana ta ya ya zan iya zuwa na ceto rayuwar wanan jarumin alhalin ban kasance jaruma ba kuma bani da wani sihirin tsafi?". Koda jin haka sai mahaifina ya yi ajiyar zuciya ya ce,

"Ya ke 'yata kiyi sani cewa yanzu tate zan baki dukkan sihirin tsafina sannan mu yi bankwana na koma kasata na jira mutuwata".

Koda naji haka sai na fashe da kuka na rungume mahaifina sannan na ce, "Ya kai Abbana me yasa baka nuna mini mahaifiyata ba koda sau daya ne mun ga juna kafin ka kawoni nan tunda gashi yanzu kaima za ka rabu da ni rabuwar da ba ZAmu sake saduwa ba".


Koda jin wannan tambaya sai mahaifina ya kamu da tsananin tausayina har ya kasa cewa komai ya fashe da matsanaicin kuka har izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can sai ya janye jikinsa daga cikin nawa muka fuskanci juna ya ce,

"Ya ke yata kiyi sani cewa ka'idar sihirin tsafina ce ta hanani na hadaki da mahaifiyarki idan kuwa na karya wannan ka'ida shikenan sihirin tsafina Zai rushe, duk dukiyar da na mallaka za ta salwanta. Da wannan furuci nake yi miki sallamar karshe."


Koda gama fadin haka sai mahaifina ya dada kankameni a kirjinsa ya sake fashewa da matsanaicin kuka. Al'amarin da ya karya zuciyata ke nan nima na kama kuka, Ina cikin wannan halı ne naji wani irin gagarumin karfi yana shiga jikina. Kafin na gama shiga sai mahafina ya bace 6atl Na nemashi sama da kasa na rasa.

Nan fa na rushe da kuma na kama guje-guje da iface- iface a cikin Wnnan gida. Kawai sai Da...

Zan cigaba
Shuraihu Usman ne
inkiya 99% - Mr HausaEbooks

MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Chapter 5
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023
Nan fa na rushe da kuka na kama guje-guje da iface- iface a cikin wannan gida.

Kawai sai naga kuyangin gidan sun baiyana a gabana sun kewayeni suna rarrashina, sannan suka yi sujjada a gareni suna cewa, "Ya shugabarmu ki đauki hakuri da kaddara, ki sani cewa mu masu debe miki kewane da biyan duk bukatunki daga nan har izuwa karshen rayuwarki".

Koda naji haka sai na dubesu cikin mamaki na ce, "Idan kuma mutuwa ta daukeki waye zai ci gaba da kula da ni?". Cikn hadin baki suka ce "Ai mu ba mutane bane kamar ke, mun kasance aljanu, muna dadewa a duniya fiye da ku bil'adama.


Daga Wannan rana ne na shiga sabuwar rayuwa a cikin wannan gida kuma ya zamana cewa ina yin abubuwan al'ajabi cikin karfin sihirin tsafi wadanda ni kaina nake mamaki. Haka na ci gaba da rayuwa cikin, koshin lafiya da kwanciyar hankali amma duk sa'adda na tuna da mahaifina sai na fashe da kuka, haka kuma idan na tuna cewa ban taba ganin mahaifiyata ba sai naji wani irin bakin ciki yai katutu a cikin zuciyata.

Haka dai na kasance a cikin wannan matsayi har tsawon shekara hudu. A ranar da na ga hoton duk abubuwan da suka faru gareka a cikin kogon Mazubatul Dulshal ne naji na kamu da tsananin kaunarka don haka sa'adda wadannan aljanu suka biyoka za su hallaka ka sai na bi umarnin mahaifina na zamo guguwa naje na daukeka kafin su illataka na kawoka nan, nayi jinyarka kawo izuwa yanzu tsawon kwana goma sha hudu har ka sami lafiya.

Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata ya kai jarumin jarumai, kayi sani cewa na gani a cikin bincikena na tsafi cewar idan har ka koma wajen gimbiya Larziya za ta umarceka da ka aikata wani mummunan aiki wanda zai zamo sanadiyyar ɓatawarka da Salimat matar da ta rene ka har ka girma a matsayin ɗanta na cikinta sakamakon hakan Salimat za ta kashe kanta.


Idan hakan ta faru za ka tsani kanka kuma za ka tsani komai a duniya ya zamana cewa soyayyarka da gimbiya Larziya ta rushe, wato dai ba za ku yi ure ba.

Ina mai shawartarka da ka mance da batun Larziya ka zauna anan tare dani mu yi aure mu more rayuwarmu cakin dadi da kwanciyar hankali. Ka sani cewa na fi Larziya kyawu, asali da matsayi a duniya, kuma duk abin da kake nema a rayuwarka walau dukiya ko daukaka in dai kana tare da ni tamkar ka samesu ne."

Sa'adda Hayatul Lumhas tazo nan a zancenta sai Hantaru ya yi murmushi gami da ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya ke ma'abociyar kyawu, matsayi da daukaka, kiyi sani cewa babu ruwan SO da kyawu ko matsayi, don haka martabar gimbiya Larziya a cikin zuciyata ta ninka taki sau dubu.

Larziya ce mace ta farko da ta fara samun gurbi a cikin zuciyata kuma ita ce za ta zamo ta karshe domin ba zan taba son wata ba face itan.

Duk bayanin da ki ka yi na gamsu da shi, amma ban yi imani da shi ba domin na yarda da cewa zan iya sauya kowacce irin kaddara da ta sameni anan gaba muddin tsafi bai daina tasiri a doron kasa ba.

Ki sani cewa idan suna nake nema a duniya na gama samunsa tun da gashi na dauko takobin Saiful Lujara a cikin kogon Mazabatul Dulshal aikin da ya gagari dubunnan sadaukai a tsawon dubunnan shekaru da suka gabata.

Idan dukiya nake so ko mulki duk zan iya samunsu da karfin Wannan takobi da na dauko saboda haka ni yanzu baki da wani abu wanda zai janyo hankalina har yasa har na manta da masoyiyata abar begena dare da rana wato gimbiya Larziya. Abin da nake bukata daga gareki kawai shi ne ki fitar dani daga cikin wannan gida naki ki đorani akan hanyar da ZAn nufi birnin Darul Mahabul domin naje na ida sauran burin rayuwata.

"Ya yin da Hantaru yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa gimbiya Hayatul Lumhas tayi shiru bata ce komai ba tana mai sunkui da kanta kas saboda tsananin bakin ciki da takaici. Daga can sai ta dago kai ta dubi Hantaru ta ce,

"Ya kai abin kaunata kayi sani cewa ina binka bashin kubutar da rayuwarka da nayi daga hannun wadannan muggan aljanu na cikin kogon Mazubatul Dulshul masu tsaron takobin Saiful Lujara. Baka da wani abu wanda za ka iya biyana wannan bashi domin kai fakiri ne a kaina koda kuwa nan gaba ka mallaki duk kasashen duniya sun zamo karkashin mulkinka saboda a cikin wannan gida nawa akwai tsubin dukiya wacce tafi duk dukiyar duniya yawa. Ina son ka biyani bashin da abu daya ".

Hantaru ya ce, "Mene ne abin da kike so na biya ki da shi?".

Maimakon Hayatul Lumihas ta ce wani abu sai taje ta dauko wani hoto da aka sasssakashi cikin siffar gunki ta mikawa Hantaru. Da ya karbi gunkin ya dubeshi da kyau sai ya ga ashe kamannin gimbiya Hayatul Lumhas ne sak tamkar an tsaga kara. Hantaru ya sake dago kai ya đubi Hayatul Lumhas ya ce, "Me zan yi da wannan gunki mai siffar fuskarki?".


Hayatul Lumhas ta ce, "Ina son komai wuya komai gumu, ka kai wannan gunki izuwa birnin Hindu ka sada shi ga mahaifiyata sarauniya Mashlima wacce a halin yanzu ita ce ta gaji karagar mahaifina.

Ka bata Labarina da irin daular da nake ciki amma ka sanar da ita cewa burina bai cika ba wanda shi ne burin mijinta, don haka har abada ba zamu sadu ba kuma nima ajalina yana daf kamar yadda na mahaifina ya kasance. Idan kayi haka ka biyani bashin da nake binka, idan kuma baka aikata hakan ba kaci amanata".


Koda gama fadin hakan sai Hayatul Lumhas ta juyawa Hantaru baya ta ce, "Ka mike ka ci gaba da tafiya izuwa bangaren gabas za ka riski wata kofa a gabanka da ka shiga cikinta za ka tsinci kanka a wajen gidan nan inda za ka iske doki da guzuri wanda na tanadar maka, amma ka sani cewa daga yanzu har izuwa sa'adda za ka isa kofar birnin Darul Mahabul kana da damar sauya ra'ayi na dawowa gareni, kofar gidana a bude take gareka kuma ina mai marhaban da sake karbarka. Idan kuwa baka dawo ba shi ke nan har abada ba zamu sake saduwa ba domin ni da kai duk ajalinmu na kusa."


Koda gama jin wannan batu sai Hantaru ya nufi gabas yai ta tafiya a cikin harabar gidan ko Waiwayowa bai yi ba, sai da ya ga ya yi nisa da Inda ya bar Hayatul Lumhas a sannan ne ya tuno da irin shakuwar da ya yi da ita a cikin kwanaki goma sha hudun da kuma irin dawainiyar da tayi da shi na jinyarsa har ya sami lafiya. Hantaru ya tuno da irin tsananin kyawun Hayatul Lumhas da kuma irin daular da take ciki da matsayinta na 'yar sarkin birnin Hindu, birnin da a wannan ZAmani duk duniya babu kamarsa a karfin mulki. Nan take Hantaru yaji nadama tazo masa, kuma ya kamu da tsananin tausayin gimbiya Hayatul Lumhas, bai san sa'adda hawaye ya zubo masa ba, kawai sai ya waigo baya bisa tunanin ko Zai hangoi Hayatul Lumhas.Yana waigowa sai ya ganta a tsaye daf da shi idanunta sun yi sharkaf da hawaye.

Nan take Hantaru ya rungume Hayatul Lumhas ya fashe da matsanaicin kuka ita kuwa sai ta bushe da dariyar farin ciki bisa ganin cewa zuciyarsa ta karaya ya fasa tafiyar ya barta. Bisa mamaki sai Hayatul Lumhas taji Hantaru ya yi wuf ya tureta daga cikin jikinsa kawai sai ya dubeta ya ce, "Ki gafarceni yake tauraruwar zamani, hakika ke abar tunawace a zuciyata har abada, kuma lallai sai na biyaki bashin da kike bina ka fin cikar ajali, amma ki sani cewa har abada ba za ki mallakeni ba nima ba zan mallakeki ba domin ba a yimu domin juna ba Koda gama fadin hakan sai Hantaru ya juya ya ci gaba da tafiya abinsa. Kawai sai yaji Hayatul Lumhas ta fashe da matsanancin kuka wanda ya kara dugunzuma hankalinsa kuma ya kamu da tsananin tausayinta har yaji kamar ya hakura da tafiyar ya koma gareta amma sai ya kanne ya ci gaba da tafiyar, yana tafe yana zubar da hawaye har ya yi nisa sosai ya daina jiyo sautin kukan Hayatul Lumhas a sannan ne ya iso bakin kofar gidan. (Ta tabbata dai hayatul lumhas tawace, Ni mai typing Shuraih 99%)

Da isarsa daf da kofar sai ya ga kofar ta bude kanta, kawai sai ya ga wani ingarman farin doki a tsaye shi kadai yana harbin iska ga jakar guzuri daure a kansa. Cikin murna Hantaru ya ruga izuwa ga dokin yai tsalle ya haye kansa sannan ya sakar masa linzami ya sukwaneshi da gudu izuwa cikin daji.


Daga wannan rana Hantaru ya ci gaba da tafiya a cikin daji ya kwana nan ya tashi can har tsawon kwanaki masu yawa amma mamaki ko sau daya bai gamu da wani mugun abu ba kuma bai sha wahalar komai ba.

Wata rana da yammaci yana cikin tafiya kawai sai ya hango kofar birnin Darul Mahabul a gabansa nesa kadan. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan, domin da can tafiyar da yake yi kansa a juye yake bai ma san inda ya nufa ba kawai inda ya ga dokinsa ya yi nan yake bi baya sauya masa akala. Koda Hantaru ya hango kofar birnin Darul Mahabul sai ya cika da tsananin farin ciki don haka sai ya sakarwa dokinsa kaimi ya zabureshi da gudu.


Da isarsa bakin kofar birnin sai ya ci gaba da gudu kuma ya rufe fuskarsa da rawani, sannan ya boye takobin Saiful Lujara a cikin jakar guzurinsa bai zame ko ina ba sai gidan Shurem.

Da isar Hantaru kofar gidan sai ya iske Shaulat matar Shurem ita kadai tana baiwa dokin mijinta ruwa. Koda Shaulat ta ga mutum a gabanta bisa doki kuma fuskarsa a rufe sai ta razana ta yunkura za ta ruga izuwa cikin gida. Cikin sauri Hantaru ya kira sunanta yana mai cewa, "Ya ke kakata yau kuma jikanki kike gudu?"

Koda Shaulat taji muryar Hantaru sai tayi jifa da bokitin hannunta ta ruga gareshi. Hantaru ya sauko daga kan dokinsa da sauri suka rungume juna tana dariyar farin ciki, daga can kuma sai yaji ta fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar firgitashi ke nan ya janye jikinsa daga cikin nata da sauri suka fuskanci juna a lokacin da ya rike kafadunta ya ce, "Ya ke kakata ina dalilin wannan kuka naki?" Shaulat tayi ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai Hantaru kayi sani cewe bayan tafiyarku izuwa kogon Mazubatul Dulshal kai da sadauki Rabbasu don dauko takobin Saiful Lujara mutane da yawa sun rasa rayukansu sakamakon mutuwar mahaifin Rabbasu da kuma mahaifin mijina, wato boka Sulbaini domin mutuwar tasu ta kawo rudani da tashin hankali a tsakanin kabilarmu da kabilar su Rabbasu har tasa muka dinga yakin sunkuru muna kashe juna sai da kyar sarki ya tsaida wannan yaki.

Ka sani cewa mijina ya mutu a wannan yakı, yanzu bani da kowa face mahaifiyarka Salimat da kuma kai a wannan birni na Darul Mahabul. Koda jin wannan batu sai Hantaru yaji wani irin mugun bakin ciki ya rufeshi, bai san sa'adda ya fashe da matsanaicin kuka ba. A dai-dai wannan lokaci ne ya hango Salimat ta fito daga cikin gida ta nufo inda suke hawaye na zuba a idanunta. Cikin hanzari Hantaru ya ruga gareta suka rungume juna suka kara fashewa da kukan murna bisa sake saduwa.


Nan dai suka dunguma su ukun suka shiga cikin gidan. Bayan Hantaru ya huta kuma ya ci abinci sai Salimat da Shaulat suka rakashi izuwa inda kabarin Shurem yake ya durkusa a gaban kabarin yana kuka, sannan ya yi masa addu'oi irin nasu na kafirai da suka saba yi.

Ba wani abu bane yasa Hantaru yake wannan kuka ba face gashi ya dawo daga kogon Mazubatul Dulshal cikin nasarar đauko takobin Saiful Lujara amma Shurem bai gani ba. Ya sani cewa a rayuwar Shurem wannan ce rana mafi farin ciki a rayuwarsa, wato ranar da zuri'arsu ta ci gasar da ta kasa kar6o kambunta a wajen zuri'ar su Rabbasu tsawon shekaru.

Sa'adda Hantaru ya gama 'yan addu'o'insa da koke-kokensa a kabarin Shurem sai Salimat ta tasheshi tsaye suka koma cikin daki suka zauna a sannan ne ya bude jakar guzurinsa ya đanko takobin Saiful Lujara ya nuna musu sannan ya kwashe Iabarin tafiyarsa kaf ya zaiyane musu tun daga lokacin suka fara shan wahala shi da sadauki Rabbasu da kuma sauran wahalar da ya sha har kawo izuwa lokacin da Rabbasu ya karaya ya kashe kanSa ya isa cikin kogon Mazubatul Dulshur da irin gwagwarmayar da ya yi da masifun ciki har da yadda ya dauko takobin ya gudu don tsira da rayuwarsa har ya fadi kasa sumamme ya farfado a gidan gimbiya Hayatul Lumhas da duk abin da ya faru tsakaninsa da ita har suka rabu ya taho birnin Darul Mahabul.


Koda gama wannan labari sai Salimat da Shaulat suka cika da tsananin al'ajabi kuma suka jinjinawa Hantaru domin sun san cewa ya yi gagrumar bajinta wacce abu ne mawuyaci nan gaba a sami wanda ma zai iya kwatanta irinta.

Haka dai suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai. Hantaru da Shaulat suka kwanta suka kama barci amma ita Salimat sai ta kasa kwanciya kuma idanunta suka bushe ya zamana cewa ko kadan bata jin barci. Ba komai ne ya haddasa ma ta hakan ba face tsananin fargaba bisa labarin da Hantaru ya baiyana ma ta dangane da abubuwan da gimbiya Hayatul Lumhas ta zaiyana masa akan ababuwan da za su same shi anan gaba.

Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful Lujara ya zamana cewa kullum sai Salimat...

Zan dakata anan amma kafinnan Jama'a ina farin cikin sanar daku cewa A yau aka ɗaura auren yayata wacce na ke bi, Alhamdulillah anyi taro lafiya an ƙare lafiya, muna bukatar addu'o'inku bisa dorewa da cin moriyar wannan aure nasu, Sannan ni ma a sanyani cikin du'a'i don kuwa yau na yi shiri, irin shirin mazajen fama, na sanya falmara da aka sana'antata da fatar Sarkin Zakuna Bulyaƙinu, nai ɗamara da gurun da na gada daga shugaban fararen aljanu Saiful Barzak, na shafe fuskana da shuni, na rataya kwanson tsafaffun ƙibbauna da na kwata daga hannun jaruma safirat, ga kakkaifen takobin da na kewa laƙabi da GAYAWA JINI NA WUCE, bisa ɗamarata daga gefen hagu, gefen damana kuwa tsafaffen addar da aka fara kirkira a duniyace, wacce na kwatota bayan na yi nasara bisa ga sarki SHAMHARU SHAHARRE. Nayi shiri nayi tunjim, nayi bunƙim na nufi gidan gimbiya HAYATUL LUMHAS don na maye gurbin jarumi hantaru gareta.

Zan cigaba
Shuraihu Usman ne
inkiya 99% - Mr HausaEbooks

MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Chapter 6
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023
Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful Lujara ya zamana cewa kullum sai Salimat tayi mugun mafurki akansa kuma abin da ake nuna ma ta a cikin mafarki shine,

Hantaru ya rusa ma ta dukkan farin cikin rayuwarta. Koda ta tuna wadannan mafaekai da wannan labari da yazo ma ta da shi sai ta tabbatar da cewa Lallai mafarkin nata zai iya zama gaskiya.

Bisa Wannan dalili ne Salimat ta kasa barci ta dinga sakar zuci bata san sa'adda ta fara kuka ba. Sautin kukan nata ne ya sa Haataru ya farka daga barci. Koda bude idanunsa ya ga Salimat a zaune tana kuka sai ya mike zumbur cikin razana yazo gareta ya rungumeta yana cewa ya ke, "Ummina kiyi sani cewa har abada wannan mafarki naki ba zai tabe Zama gaskiya ba, domin babu wani aba da ya fiki matsayi da muhimmanci a wajena, na rantse da darajar kaunar da ke takanina da ke da mijinki har abada ba zan taba juya mikk baya ba.


Na yi imani cewa babu abin da zai gagari tsafi saboda haka koda mafarkinki zai zama kaddara a garemu to ni zan sauya wannan kaddar da karfin tsafi, bayan mun karbo kambun gasa wajan sarki an daura aurena da gimbiya Larziya saboda haka inason gobe da sassafe ke da Shaulat ku rakani fada domin na gabatar da takobin Saiful Lujara ga sarki a gaban jama'ar gari domin burin zuri'armu ya cika nima nawa burin ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment