Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai tsaya wani 6ata lokaci ba ya hau kan dokinsa ya zauna. Nan take aka Janye wadansu kosassun dawakai guda biyu wadanda aka tanada saboda su Boka Sulbaini. koda aka kai musu dawakan sai duk saka yi murmushi, boka Zaharu ya dubi waziri, ya ce, "Ai idan boka ya cika boka baya tafiya akan doki domin abin kunya ne a gareshi."


Koda gama fadin haka sai boka Zaharu ya daga wata jar sandar hannunsa ya saketa a Sama cikin iska yana reto. Nan take sangar ta rikide ta zama wani jibgegen tsuntsu mai kyawun siffa. Kawai sai tsuntsun ya sauko daf da boka Zaharu ya tsaya cak. Take Zaharu ya hau kan tsuntsun ya zauna shi kuwa tsuntsun ya bude fuka- fukansa ya tashi sama ya tsaya cak! A sama waje daya yana kada fuka-fukansa.


Koda ganin wannan abin al'ajabi da boka Zaharu ya yi sai jama'ar da ke tsaitsaye a kofar fada suka kama shewa da tafi domin al'amarin ya yi matukar burgesu. A sannan ne boka Zaharu ya yi dan murmushi ya fara hura hanci yana jin takama. Ya yin da boka Sulbaini ya ga abin da ya faru sai ya yi murmushi kawai, nan take ya bude hannayensa kawai sai aka ga ya tashi sama kamar tsuntsu kuma ya tsaya cak a saman ya ZAuna akan iska har da harde kafafu tamkar akan turba yake ya ci gaba da murmushi kuma ya risina ga Sarki ya yi gaisuwar gimamawa, lokaci guda jama'a suka rafka tafi da shewa fiye da wadda aka yiwa boka Zaharu kuma jama'a suKa rinka dukawa a gaban Sulbaini suna yi masa jinjina.


Koda ganin wannan abu da ya faru sai bakn ciki ya turnuke boka Zaharu, zuciyarsa ta kama tafarfasa. Nan take ya yi nadama bisa fara nuna bajintarsa da ya yi tun da gashi Sulbaini yayi bajintar da ta fi tasa kuma abin takaici shi ne ji shima zai iya yin wannan bajintar wadda Sulbaini ya yi amma idan ya sauya wacce ya yi da farko ya yi irin ta san za a ga cewa ai kwaikwayo ya yi don haka ba zai burge ba.


Nan take aka fara tafiya ya zamana cewa Dakarun rakiya sun sa Sarki, Waziri da kuangi a tsakiya. Boka Sulbaini sai ya wuce kan gaba ya yaiwa tawagar jagora, shi kuwa boka Zaharu sai ya koma can bayan tawagar ya tasOSu a gaba yana bisa kan wannan tsuntsun tsafi nasa.

Haka dai aka cigaba da tafiya dare da rana ba a yada zango ba face idan gari ya yi duhu sosai ko kuma idan ana son a huta aci abinci. Duk wani mugun abu da ya tunkari tawagar ta gabansu take bolka Sulbaini ke kawar da shi. Komai yawan 'yn fashi da karfin sihirinsu sai ka ga Sulbaini ya tarwatsasu ya kashe na kashewa, masu gudu sun gudu. Idan kuwa muggan dabbobin dai ne da ZArar Sulbaini ya nuna su da hannu sai ka ga sun Bauya hanya sun komn da baya. Kamar ysdoa









Zan cigaba
Shuraihu Usman ne
inkiya 99% - Mr HausaEbooks

Sulbaini ya tare wadannan masifu masu zuwa ta gaba haka shima boka Zaharu ya rinka tare wadanda ke Bullowa ta bayan tawagar.

Ba abin da ya burge su Sarki face yadda al'amarin bokayen biyu ya zama kamar gasar nuna jaruntaka suke.

Da zarar đayansu ya fafata da damisoshi ko kuraye ya fatattakesu sai ka ga shi kuma dayan ya fafata da zakuna.

Haka dai suka yi ta shiga cikin hadarurruka suna fita har tsawon kwanaki goma sha uku sannan suka isa birnin Kisra.

Tun kafin su isa cikin garin Sarki ya tashi manzo ya aikashi izuWa fadar Sarki Kasaidu domin ya sanar da shi zuwansu.

Lokacin da manzon ya isa fadar sarki Kusaidu ya isar da sako sai sarki Kusaidu ya cika da matakar farin ciki domin rabon da su ga juna ya kai shekara ashirin. Akwai zumunci da mutunci mai karfi a tsakanin Sarakan biyu domin a gaba dayan nahiyar babu sarakai masu matsayi da daraja kamarsu.


Wani abin mamaki shi ne fiye da shekaru arba'in baya haka masarautar biyu ta kasance kawo i yanzu suna zAman lafiya babu wanda yake kyashin wani kuma basu taba samun sa6ani ba.


Maimakon sarki Kusaidu ya jira isowar Sarkin Darul Mahabul sai ya mike da kansa yai hawa tare da wadansu fadawansa ya tafi bayan gari ya taryo bakonsa. Suna ganin juna sai duk suka sauko daga kan dawakansu suka rungume juna cikin tsananin farin ciki.

A wannan lokaci bokan Sarki Kusaidu wanda ake kira Ardusa ya rako Sarkin naSa. Koda boka Ardusa ya yi arba da su boka Sulbaini sai aka fara kallon-kallo tsakaninsa da su kai da ganin irin kallon ka san cewa kallo ne na KAR TA SAN KAR. Nan dai aka dunguma gaba đaya aka juya aka nufi cikin gari.


Bayan an baiwa su Sarki masauki sun ci sun sha da suka huta sOsai izuwa gabannin magariba Sannan Sarki Kusaidu ya aikowa da sarkin sakon gaiyatar izuwa fadarsa domin su ci abinci dare tare kuma a cikin sakon sai sarki Kusaidu ya ce da Sarki ya taho tare da wadannan bokaye nasa biyu wadanda suka yi masa rakiya izuwa nan birnin Kisra.


Sa'adda sarki yaji wannan sako sai ya cika da mamaki bisa rashin sanin dalilin da yasa sarki Kusaidu ya ce yaje tare da su boka Sulbaini shi da a tunaninsa yana son su kadaita ne domiin su tattauna a sirrance ya ji abin da ke tafe da shi.


Da lokácin cin abincin ya yi sai Sarki, boka Sulbaini da boka Zaharu suka jera suka tafi fadar sarki Kusaidu don amsa wannan gayyata da aka yi musu. Duk su ukun sun tafi ne a kasa bisa kafafunsu saboda babu nisa daga masaukin nasu zuwa fadar sarkin.

Sarki ne a tsakiya Sulbaini na gefen damansa, shi kuma boka Zaharu na gefen hagunsa. Ya yin da suka shiga cikin fadar sai suka iske sarki Kusaidu da boka Ardusa su biyu kacal akan dogon wani tebur mai tsawo da fadi wan da zai iya daukar mutum dari.


Akan teburin an jera farantai cike da abinci kala-kala barkatai duk na kasaita irin na sarakai. Tambulan kuwa mai đauke da kayan shaye-shaye ya kai guda arba'in akai.


Ya'yan itatuwa na irin dangin su Ayaba, lemo, gwanda, inibi, fasadabur da sauransu gasu nan iri- iri Koda sarki Kusaidu ya ga shigowar Sarkin Darul Mahabul tare da bokayensa sai ya mike tsaye yaje ya ruko hannunsa ya jawoshi ya kawoshi daf da shi ya zaunar da shi bisa kujerar da ke daf da tasa shi kuwa boka Ardusa ko kallon su boka Sulbaini bai yi ba bare yaje ya taresu kawai sai ya kau da kai ga barin kallonsu.


Boka Sulbaini da ne Zaharu suka Zazzauna a kujeru dabam- daban suna fuskantar juna. bayan kowa ya zauna sai sarki Kusaidu ya dubi boka Ardusa cikin murmushi ya ce, "Ya kai dirkar Kisra ga dirkokin birnin Darul Mahabul nan sai ku gaisa ko".

Koda jin haka sai boka Ardusa ya saki guntun murmushin munafunci Sannan ya ii har da kalar da mutum bai taba sha ba. mikawa boka Sulbaini hannu daga inda yake zaune. Tazarar da ke tsakanin inda Ardusa ke zAune da inda Sulbaini ya ke ta kai kamu dari, amma sai gashi hannun boka Ardusa ya kara tsawo ya tafi shuuu! Izuwa inda Sulbaini yake. Ba tare da gardamar komai ba Sulbaini ya mikawa Ardusa nasa hannun suka gaisa. Koda suka rike hannun juna sai kowannensu ya kafa zufa tamkar an kwara musu ruwa aka.


Al'amarin da Sarakan biyu kuwa, tuni sun kame sun kasa koda motsi saboda tsananin mamaki bisa ganin yadda hannun boka Ardusa ya Kara mugun tsawo da kansa tamkar dogon karane a jikinsa ba hannu ba. Koda sarki Kusaidu ya ga boka Sulbaini da boka Ardusa basu da shirin sakin hannun juna sai ya yi gyaran murya ya ce, "Ai sai ku saki juna haka ko?".


Da jin haka sai Ardusa ya saki hannun Sulbaini sannan ya mikawa Zaharu hannun domin shima su gaisa. Boka Zaharu ya yị murmushi sannan ya bude tafin hannunsa sai ga wani babban rauni akai. Zaharu ya ce, "Ai ina da rauni a hannuna ba zan iya gaisawa da kai ba".


Da jin haka sai Ardusa ya yi murmnushi bai ce komai ba. Ba tare da bata lokaci ba sarki Kusaidu ya bayar da umarni aka fara cin abinci, kowa ya zabi irin kalar abincin da yake so ya ci sai da kowa ya koshi ya yi hani'an sannan sarki Kusaidu ya yi gyaran murya ya dubi Sarki ya ce, "Ya kai babban bakona mai daraja kayi sani cewa na san abin da ke tafe da kai izuwa kasata, kuma matsalarka irin tawa ce.


Baka taba yin aure ba a rayuwarka kuma jama'a sun damu akan kayi auren domin shi ne cikar kamala da mutuncin sarki da kwarjinin masarautarsa a matsayinsa na shugaban miliyoyin al'umma, abin koyi abin misali.


Bisa wanann dalili ne ka yanke shawara cewa ba za ka yi aure ba face ka sami budurwar da babu mai kyanta a gaba dayan wannan nahiya tamu. Bincike na bokaye ya tabbatar da cewa a gaba daya wannan nahiya tamu babu wata budurwa wadda kyawunta ya wuce na Zarifa da Marifa 'yan matan da ke zaune a cikin birnina kuma sun kasance 'ya'yan attajiri Baddar ibini Samhal. A gaba daya wannan nahiya tamu babu wani attajiri mai tarin dukiya kamarsa domin inda za a hada dukiyata da taka gaba daya a waje đaya ba Za ta kai kaso daya ba a cikin kaso goman tasa.


Bisa wannan dalili ne 'ya'yan sarakai da attajirai daga ko ina a duniya suke son su mallaki wadannan 'yan mata. Zarifa da Marifa sun kasance Hassana da Hussaina kuma suna matukar kama da junansu tamkar an tsaga kara, abin da ya bambantasu kawai shi ne, Marifa ta fi dan tsawo gami da yalwar gashi. Su kadai ne 'ya'yan da attajiri Baddar ya haifa a duniya kuma tun da mahaifiyarsu ta rasu har yanzu bai kara yin wani auren ba saboda ya san cewa babu wata 'ya mace da za ta aureshi bisa so da kauna sai domin dukiyarsa. Wani babban abin al'ajabi shi ne, tsakanin Zarifa da Marifa ba a ga maciji tun suna yara kusan ko yaushe ma a cikin farautar rayuWar juna suke, bisa wannan dalii ne mahaifin nasu ya raba musu gida kowacce aka kebeta dabam aka wadatata da komai na jin dadin duniya.


Kowacce a cikinsu ta yi alkawarin cewa ba Za ta yarda a raba musu gadon mahaifinsu daidaiba bayan mutuwarsa don haka har a yanzu dukiyar tasu na nan a ajiye a wajena sai dai a jira Wannan shi ne takaitaccen labarin Zarifa da Marifa.


Ya kai wannan sarki kafin ka zo nan birnin Kisra bokayenka sun nunawa Wazirinka fuskokin Zarifa da Marifa a cikin madubin tsafi amma kai baka gansu ba. Ina tabbatar maka da cewa idan ka gansu a yanzu sai ka gigice ka dimauce, idan ba a y sa'a ba ma za ka iya sanu daya ya mutu sannan a baiwa dayan. ta6in hankali saboda tsananin kyawunsu. Ni kaina sau daya na ta6a ganinsu kuma da na gansu sai da na kwanta ciwon bege tsawon wata uku da kyar da sidin goshi likitocina suka samo kaina Da sami lafiya. Kayi sani cewa a halin yanzu Marifa da Zarifa sun ce ba za su yi aure ba face sun jarraba masoyansu cikin hikima da basira.


Ba wai gwajin jarumtalka ba ko karfin sihiri da dukiya ba, a yanzu haka saura kwana ashirin da aku ayi wannan gasa ta gwajin hikimar da 'yan matan za su yi. Ni kaina na kudurce zan shiga Wannan gasa amma bani da tabbacin cewa zan iy samun nasara a gasar domin shi kansa bokana ya yi iya bincikensa ya kasa gano irin jarrabawar da yan matan za su yi. Idan kana ganin cewa bokayenka za su iya taimakonka a cikin wannan gasar da za a yi to ga dama ta samu sai su taimaka maka in yasO wanda ya kaika ga samun nasara sai cika masa alkawrin da ka dauka, " Lokacin da Sarki Kusaidu ya zo nan a jawabinsa sai Sarki ya cika da tsananin mamakin yadda aka yi Kusaidu ya san komai dangane da dukkan al'amarinsa yai shiru bai ce komai ba. Kamar sarki Kusaidu ya san abin da ke ran Sarki sai ya kara dubansa ya yi murmushi ya ce, "Na san kana mamaki ne bisa yadda aka yi na san dukkan al'amarinka to ka daina mamaki domin karfin sihirin bokana Ardusa ya fi na wadannan bokayen naka biyu, don haka tun kafin ku zo nAn ma ya sanar da ni komai a kanku.


Da wannan furuci nake maka sallama yanzu zan tashi, na shiga cikin gidana ku kuma sai ku koma mazauninku ku ci gaba da jiran kwanaki ashirin da uku anar da Zarifa da Marifa za su gabatar da gasarsu ta zabawa kansu mazajen da za su aura. Ba zan sake ganawa da kai ba kuma ba ZAmu kara ganin juna ba sai a wannan rana."


Koda gama fadin haka sai sarki Kusaidu da boka Ardusa suka mike tsaye suka fice daga cikin fadar. Sarki, Sulbaini da Zaharu kuwa sai suka kasa mikewa su tafi domin hankalinsu a tashe yake bisa jin bayanin da Sarki Kusaidu ya yi musu. Gaba đayansu jikinsu ya yi sanyi, kuma sun raina kansu domkn suna ganin cewa wannan tafiya da suka yi Za ta zamo ta banza domin abin da suka fito nema ba za su samu ba.


Sai da suka jima a Zaune sun8 tunani da nazari amma suka kasa samo mafita kuma đayansu bai ce uffan ba. Koda Sarki ya ga haka sai ya mike tsaye ya ce, "Ku tashi mu tafi masaukinmu". Ba tare da gardamar komai ba kuwa suma suka mike tsaye suka bishi a baya suka fice daga cikin fadar.


acan gidan da aka ajiye mahaifiyata, wato Marifa, gidane mai girman gaske, ku.a an tanaji komai na jin dadin duniya a cikinsa Kuyangi da ke yi ma ta hidima a kalla sun kai su tamanin da hudu ban da Barorí da sauran bayi masu aikace-aikace a gidan. Dama tun kan mahaifin nasu ya rasu ya fadawa da kowannensu irin tambayoyin da kowacce zata yiwa maneman aurenta kuma dabam-daban kuma babu wadda ta san irin tambayar da 'yar uwarta za ta yi.


Mahaifiyata Marifa ta kasance mace mai hakuri da tausayi, amma kuma tana da matukar son abin duniya, sai dai bata kai Zarifa son abin duniya ba. Ita Zarifa tana da bin bokaye domin tana da burin ta sami daukaka da babu wata ya Mace ta samu a duniya. ita kuwa Marifa burinta đaya ne kawai a duniya, tana son ta sami mijin da zai aureta bisa soyayyar gaskiya kuma ya riketa da amana.


Tun daga ranar da mahaifin su Marifa ya ya mutu Zarifa ta rinka shige da fice izuwa kasashe da garuruwa tana ziyartar bokaye domin ta sami cikar burinta.

Duk bokan da ta je wajensa sai ya gaya ma ta cewa babu wanda zai iya biya ma ta bukatarta face boka Ardusa.


Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin Zarifa ke nan tunaninta boka Ardusa ba zai taba ba ta hadin kai ba kasancewarsa aminin Sarki Kusaidu kuma shi baya yiwa kowa aiki face Sarki Kusaidu. Abinda Zarifa ta yanke hukunci a ran shi ne, kawai ta ci gaba da neman wađansu bokayen har bukatar tata ta biya, tun da dai đuniya fadi gareta kuma abin cikinta yawa gareshi.


Haka ta ci gaba da bincike har ya Zamana cewa saura kwana kadan A Wannan ne hankalin Zarifa ya dugunzuma fiye da ko yaushe domin tana ganin cewa idan har tayi aure ba ta san matsayinta ba shi ke nan har abada ba za ta ciika burinta ba.


Haka Zarifa tai ta kai kawo ta kasa Zaune ko tsaye kuma ta dinga kuka saboda bakin ciki, har dare ya raba idanunta a bushe yake tana Zaune a gefen gadonta tana zub da hawaye. Kwatsam! Ba Zato ba tsammani sai Zanifa ta ga boka Ardusa tsułum ya baiyana a gabanta & cikin turakar tata. Cikin firgici Zarifa ta yunkura za ta ruga waje sai Ardusa ya da ka ma ta tsawa ya ce, "Ina Za ki je ya ke Zarifa? Kin sani cewa har abada ni ba zan taba cutar da ke ba. Ki kwantar da hankalinki ki saki jikinki ki sani cewa duk halin da.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment