Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbata.


Sa'adda Hantaru ya zo nAn a jawabinsa sai Salimat taji hankalinta ya dan kwanta, don haka sai ta share hawayen idanunta ta dora kanta bisa kirjin Hantaru shi kuwa ya ci gaba da rera waka, A cikin sanyin murya yana karanto baitoci masu kwantar da zuciya da sanyayata.


A haka barci ya sace Salimat bata sani ba, Har gari ya waye Salimat na barci akan kirjin Hantaru bai yarda ya motsa jikinsa ba don kada ta farka daga barcin kuma bai daina rera wannan wake ba saboda tsananin biyayya da son ganin kwanciyar hankalinta. Hudowar hasken rana ne yasa Salimat ta farka daga barci, koda ta ga kanta bisa kirjin Hantaru kuma ta ga idanunsa wasai babu alamar ya yi barci sai ta cika da tsananin damuwa ta ce, "Ya kai đana ya ya aka yi nayi barci akan kirjinka amma baka tasheni ba, domin kaima ka kwanta kayi barcin kuma mene ne ya hanaka kaima kayi barcin?".
TYPING BY : SHURAIH 99%
Sa'adda Hantaru yaji wadannan tambayoyi sai ya yi mumushi ya ce, "Ai kwanciyar hankalinki shi ne nawa, inda baki samu Wannan barci ba da sai na kwana ina kuka da bakin ciki."


Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga jama'ar zuri'arsu na ta shigowa cikin gidan da murna suna yiwa Hantaru barka da sauka tamkar an yanke musu dukkan bakin cikin rayuwa. Al'amarin da ya đaurewa Hantaru da Salimat kai ke nan suka cika da mamaki bisa yadda jama'a suka san cewa ya dawo harma suke zuwa yi masa barka da sauka.


Abin da basu sani ba shi ne, tun a yammacin Jiyan wata kuyangar gidan ta watsa labari. Nan da nan gidan Shurem ya cika ya batse da jama'arsu tamkar ana wani gagarumin shagalin biki a garin.

Bayan jama'a sun gama taruwa sai aka cabawa Hantaru ado sannan aka rakashi izuwa fada ana tafe ana kade-kade da raye-raye gami da bushe bushe.


Nan da nan birnin gaba đaya ya dauka cewar ga Hantaru can ya dawo gida. Nan fa jama'a suka yi tururuwa izuwa fada domin su ganewa idanunsu shin Hantaru ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara ne ko kuwa bai samu ba, sannan suna son su ji labarin Sadauki Rabbasu yana raye ne ko kuwa ya hallaka a cikin wannan tafiya.


Lokacin da su Hantaru da sauran jama'ar gari suka isa fada sai suka iske fadar a cike makil babu masakar tsinke. Sarki na zaune bisa karagar mulki ya ci ado na kasaita sai murmushi yake ya kasa rufe baki dalili kuwa shi ne tuni bokaye sun bashi labarin cewa Hantaru ya dauko takobin Saiful Lujara. A hannun daman sarki gimbiya Larziya ce a Zaune ta caba ado na ban al'ajabi sai sheki da walwali take tamkar wata dan daren goma sha biyu, kuma itama tana ta yin murmushi irin wanda ka iya zauta duk wani baligi da ya kuskura ya kura ma ta idanu.


Da shigowar Hantaru cikin fadar tare da jama'arsu sai Dakaru suka tsaida kowa daga baya, Hantaru kadai aka bari ya nufi inda karagar sarki take. Tun daga nesa ya hada idanu da masoyiyarsa gimbiya Larziya ya ga tana yi masa murmushi tamkar ta mike ta rugo gareshi amma sai ta kanne. Shima Hantaru haka ya rinka ji a cikin ransa amma sai ya jure ya rinka maida mata da martanin murmushin. Sa'adda Hantaru ya iso kusa da karagar sarki sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, fadawa suka karbi gaisuwarsu sannan sarki ya dubeshi ya ce,

"Ya kai NAMIJIN DUNIYA, ina labarin abokin tafiyarka Rabbasu, kuma me ka zo mana da shi?" Sa'adda Hantaru yaji wannan tambaya sai jikinsa yai sanyi, nan take idanunsa suka ciko da kwalla. Ba tare da 6oye komai ba Hantaru ya kwashe labarin tafiyarsu tun daga farko har karshe ya zaiyane musu.


Yana gama bada labarin sai ya ga ashe gaba dayan jama'ar da ke fadar kuka suke yi saboda tausayi a lokacin da shima kansa yana ta zubda hawaye. Nan take Hantaru ta fiddo takobin Saiful Lujara daga cikin rigarsa ya zareta daga cikin kufenta. Koda zare takobin sai haskenta ya cika fadar gaba đaya, ta rinka kashewa kowa idanu.

Gaba dayan bokayen garin da ke tsaye kusa da sarki sai sukayi sujjada ga takobin suka hada baki suka ce, "Daukaka da jinjina sun tabbata ga jarumin jarumai, gwarzon shekara, sadauki Hantaru mijin gimbiya Larziya". Koda jin wannan batu sai fadar gaba daya ta rude da shewa, kida da wake-wake. Sai da sarki ya daga sandar mulkinsa sannan aka yi tsit! Nan take sarki ya mife tsaye da kansa ya kirawo Halifan baban Rabbasu ya karfi kambun gasa daga hannunsa sannan ya taka yaje gaban Hantaru ya nuna nasa kanbun ya ce, "Gobe wannan kambu zai dawo jannunku ku zuri'ar Shurem," Koda jin haka sai fadar ta sake ruđewa da shewa.


Sarki ya sake daga kwagirinsa a karo na biyu aka yi tsit, tamkar mutuwa ta gifta, sannan y ce,"Hakika sadauki Hantaru ya bar abin tarihi kuma abin tunkaho a wannan birni namu, wanda zamu ci gaba da tutiya gami da alfhari da shi a dukkan sauran kasashen duniya saboda shi ne jarumin da zai auri 'yata gobe da yamma anan fadata.


Tabbas Hantaru ye kawo karshen gardama da gaba a tsakanin zuri'ar makera da ta mafarauta da a wannan an gari nawA mai albarka saboda haka A yau na rushe wannan tsohuwar al'ada ta gasar tseren gudun barewa".


Koda gama wannan jawabi sai Sarki yaje ya kama hannun 'yarsa gimbiya Larziya ya ja ta suka shige izuwa cikin gidan sarauta tạna waigen Hantaru tamkar ta kufce ta rugo gareshi, shima Hantaru sai yaji kamar ya ruga ya rukota amma da ya tuna da cewa gobe ne za a daura aurenta da shi sai hankalinsa ya kwanta ya bita da kallo cikin murmushi kawai.
(Hallau dai kuna tare da Shuraih 99%)
Bayan sarki da Larziya sun shige cikin gida sai fadar ta watse kowa ya kama gabansa. Saboda tsananin đoki da murna Hantaru bai yi barci ba a wannan dare, a yadda ya ga rana haka ya ga dare, wato dai ya jera kwana biyu ke nan bai yi barci ba.


Da gari ya waye, tun da sassafe zuri'ar Shurem suka cika gari da kade-kade da bushe- bushe gami da raye-raye suka yi ta walima a gida- gida, unguwa-unguwa, ya zamana cewa Ana a bushasha da abinci da abin sha iri-iri a ko ina cikin birnin Darul Dulshul bisa samun nasarar đauko takobin Saiful Lujara.


Haka dai aka ci gaba da wannan shagalin biki har izuwa yammaci. Bangaren zuri'arsu Rabbasu kuwa banda kuka da bakin ciki babu abin da suke yi, domin sun yi asarar abubuwa uku.


Abu na farko da suka rasa shi ne, shugabansu wato mahaifin Rabbasu sannan sun rabu da kambun gasa wanda ke hannunsu tsawon shekara da shekaru. Abu na na uku shi ne, magajin shugabansu wato sadauki Rabbasu jarumin da babu kamarsa a gaba daya nahiyar. La'asar nayi sai fada ta sake cika ta batse jda ama'a fiye da taron da aka yi na safe, wannan karon ma gaba daya birnin ne ya cika da baki daga sauran makotan birane saboda jin cewa za a daura auren gimbiya Larziya da jarumin da yaje har kogon Mazubatul Dulshul ya dauko takobin Saiful Lujara.


Tun ana baiwa baki masauki har sai da takai cewa an daina basu domin babu. A wannan rana mutanen birnin Darul Habul sun yi matukar al'ajabi domin basu taba ganin cikowar jama'a ba a garinsu irin haka. Abin da basu sani ba shi ne, fiye da kaso saba in na cinkoson jama'ar ba mutane bane aljanu ne daga sassa na duniya suka zo a cikin siffar mutane domin kawai su ga jarumi Hantaru sadaukin da ya yi gagarumar bajintar da ta gagari dukkanin sadaukan duniya tsawon shekaru dubu uku da suka gabata.

Ba tare da 6ata lokaci ba aka daura auren sadauki Hantaru da gimbiya Larziya a gaban miliyoyin jama'a kuma aka đankawa Hantaru kambun gasa ya đaurashi a hannunsa, ai kuwa fadar gaba daya ta rude da shewa gami da tafi har kowa yaji kamar kunnensa zai dode.


Nan dai aka cigaba da shagalin biki aka yi ta watsa dukiya gA maroka da mabukata. Abinci kuwa sai da ya zamo ga shinan kamar shara aka rinka yin bolarsu tsibi-tsibi saboda an rasa yadda za a yi dashi.

Kowa a garin sai da ya cika da mamakin irin wadatar da aka samu a wannan rana domin abin yafi karfin iyakar bajintar Sarki, kai da gani ka san cewa akwai sa hannun aljanu. Haka dai aka ci gaba da shagalin biki amma har dare ya soma ango bai ga amaryarsa ba domin tunda aka đaura aurensa da ita sai aka shigar da ita cikin gidan sarauta aka killaceta a cikin turakarta aka yi ta tsala ma ta ado iri-irk, idan a ka yi wannan sai a ga bai yi ba a sake yin wani har sai da aka yi kala saba'in.


A na saba'in ne matan da ke yin adon suka gamsu gaba đayansu cewar ya yi. A wannan lokaci dare ya fara tsalawa don haka sai aka dauki amarya cikin hanzari aka kai ta gidan su Ango. Bayan masu kak amarya sun watse sai ango ya shigo đakin amaryarsa yana sanye da tufafi masu tsadar gaske na alhariri.


Da shigar Hantaru cikin dakin sai ya iske amaryarsa zaune a gefen gado ta sha lullu6i fuskarta a rufe.


Cikin matukar farin ciki ya karasa gareta fuskarsa cike da murmushi ya kasa rufe baki. Hantaru ya zAuna daf da Amaryarsa sannan yasa hannayensa biyu ya yaye labulen da tayi.

Koda ya yi arba da fuskarta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, ya dubeta cikin tsananin mamaki ya ce, "Ya ke masoyiyata abar begena dare da rana ina dalilin zubar Wannan hawaye na idanunki? Ki sani cewa yau rana ce ta farin ciki ba ta bakin ciki ba. Ina son ki gaya mini abin da ke damunki ko mene ne shi in dai ina da ikon kau da shi, sai na kawar da shi."


Sa'adda gimbiya Larziya taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru kamar ba za ta ce komai ba, daga can sai ta daga kai ta dubi Hantaru ta ce, "Ya kai mijina hakika baka san komai na ba domin baka san labarina ba kawai ka zo garin nan ne a matsayin bako kana ganina ka kamu da kaunata. Ina son na sanar da kai cewa ina cikin wani bakin ciki tsawon shekaru wanda duk duniyar nan babu wanda zai iya kawar mini da shi face kai.
(Shuraih 99% ke rubuto muku)

Ka saurari labarin da zan baka yanzu da kunnen basira domin ka fahimci matsalar da kuma babban burin da ke gabana." Sa'adda Larziya ta zo nan a zancenta sai tayi shiru gami da ajiyar zuciya sanann ta ci gaba da labari Kamar haka


"Mahaifina bai taba yin soyayya ba da wata ya mace har ya hau karagar mulkin wannan birni na Darul Mahabul kuma sai da ya shekara hudu akan karaga bai yi aure ba. Al'amarin da ya dami fadawansa kenan da sauran al'umman gari ke nan suka dameshi akan batun lallai ya kamata ya yi aure domin ya tsare mutuncinsa da masarautar gaba đaya.


Lokacin da mahaifina ya ga jama'a sun matsa ainun akan wannan batu sai ya tara dukkan jama'ar gari ya ce, "Idan har ana son ya yi aure dole ne ayi abu biyu. Abu na farko dole ne a samo masa kyakkyawar budurwa wacce babu kamarta a gaba daya nahiyar kuma dole ne a shirya gagarumar gasa irin wacce ko a tarihi ba a taba yin kamarta ba". Sa'adda sarki ya gama jawabi sai hankalin kowa ya dugunzuma aka rasa wanda zai ce kala.



Daga can sai Wazirin sarki ya mike tsaye ya dubi sarki ya ce, "Ya shugabana hakika ka zo mana da baban al'amari wanda ba zamu iya saurin yanke hukunci ba face ka bamu lokaci mu yi tunanin mafita.


Dole ne mu nemi manyan bokayen kasar nan domin su yi mana bincike bisa wannan al'amari".

Koda jin haka sai sarki ya yi murmushi sannan ya ce, "Ya kai waziri na baka wuka da nama akan kaje ka zartar da komai amma ka sani cewa kwana goma sha hudu kacal na baka". Koda gama fadin haka sai sarki ya mike...
Anan zan dakanta - Shuraih 99% ke magana
Kai kada fa su waziri su jesu su nemowa sarkinnan soyayyar masoyiyata Hayatul Lumhas, hallau dai ina bisa hanyata ta isa ga gidan masoyiyata, abar begena, annurin zuciyata, farin cikin maƙwalloton ruhina, hasken idaniyata Gimbiya Hayatul Lumhas, Yanzu haka ina dajin DA'IRATUL UKUB, na hadu da cikas bisa ga tafiyana yayin da na fada tarkon wasu shaidanun aljanu zuri'ar wani hatsabibin aljani Lau'ul makani. idan na samu na tsere kwaji bayani zuwa gobe.

Zan cigaba
Shuraihu Usman ne
inkiya 99% - Mr HausaEbooks

MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Chapter 7
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023

Koda jin haka sai sarki ya yi murmushi sannan ya ce, "Ya kai waziri na baka wuka da nama akan kaje ka zartar da komai amma ka sani cewa kwana goma sha hudu kacal na baka". Koda gama fadin haka sai sarki ya mike tsaye ya shiga cikin gida, a sannan ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa.


Al'amarin WAZiri kuwa, bayan ya bar fada sai ya kira wadansu manyan hadimansa amintattu guda hudu ya basu wasika suka yi hawa izuwa manyan garuruWan birnin guda hudu akan su je su gaiyato manyan bokayen da ake takama da su.


Su kuwa bokayen da ake takama da su a cikin birnin Darul Mahabul guda biyu ne kawai wato boka Sulbaini da mahaifin Rabbasu suma sai WAZiri ya kirasu ya sanar da su cewa, "Ya tura a kirawo sauran bokaye kasar guda hudu domin a ZAuna gaba daya a tattauna akan matsalar sarki.


Koda jin haka sai Sulbaini da baban Rabbasu suka yi murmushi, Sulbaini ya ce, "Ya kai waziri ai ka wahalar da kanka ne kawai domin mu kadai mun isa mu fadi hanyar da ZA a bi a warware matsalar sarki, to amma masu iya magana sun ce ba a kwacewa yaro garma kuma dan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido. Babu mamaki wani daga cikin wadannan bokaye yazo da wani abin wanda yafi namu don haka zamu jira isowar sauran bokayen hudu".


Sa'adda waziri yaji wannan batu sai yai murmushi sannan ya yi godiya ga su boka Sulbaini ya sallamesu. Bayan kwana tara daidai sai ga wadannan bokaye sun amsa kiran Sarki.


Da zuwan su sai waziri ya tara su a cikin gidansa tare da su boka Sulbaini sannan ya yi bayanin abin da yasa aka tara su kuma aka bukaci kowannensu ya fadi tasa shawarar.


Daya bayan daya sai bokayen suka rinka nuna hoton budurwar da sarki ya kamata ya aura da inda take da kuma irin gasar da ya kamata ayi ta neman aurenta, a cikin madubin tsafi. Ya yin da bokan farko ya nuna tasa sai waziri ya kidime domin gani yake kamar a duniya ma kaf ba ZA a sami kamar ta ba, amma da boka na biyu ya nuna tasa sai ya ta fi ta waccan nesa ba kusa ba.


Haka abin ya kasance bi da bi ta biyu ta fi ta farko, ta uku ta fi ta biyu, kuma ta hudu ta fi ta uku. Lokacin da aka zo kan baban Rabbasu sai ya nuna wata kyakkyawar budurwa wacce đuk ta fi sauran kyau ya ce, "Wannan sunanta Zarifa kuma yar wani babban attajiri ce a birnin Kisra, tabbas a gaba dayan wannan nahiya babu mai kyau kamarta a can birnin Kisran ma tana da masoya da yawa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan manyan sarakai da ya'yan manyan attajirai da kuma 'ya 'yan manyan bokaye.


A halin yanzu an rasa wanda za a baiwa ita daga cikin masoyan nata, amma komai na hannun sarkin Kisra, shi ake jira kawai ya yanke hukuncin akan ta. Idan har sarki ya sami nasarar auro Zarifa za a shirya gasar Jarumtama ta musamman a tsakanin manyan mayaka domin Su debewa jama'a kewa a lokacin da ake shagalin bikinsa.


Lokacin da waziri ya ga Zarifa a cikin madubin tsafin Baban Rabbasu kuma ya gama sauraron jawabin Baban Rabbasu sai ya ude, kuma ya cika da tsananin al'ajabi ya ce, "Na rantse d darajar iyayena babu wata nahiya da za aje a SAmi kyakkawar mace kamar wannan Zarifan, don haka lallai zan kaiwa sarki labarinta domin ya shirya da kansa yaje ya nemi aurenta a can birnin na Kisra. Koda jin haka sai boka Sulbaini ya bushe da dariya, al'amarin da ya matukar baiwa kowa mamaki ke nan a wajen, aka yi tsit ana kallonsa kawai. Daga can sai boka Sulbaini ya tsuke bakinsa ya murtuke fuska sannan ya nutsu ya dubi kowa daya bayan daya ya ce,


"Akwai wata budurwar wacce idan ba ta fi Zarifa kyau ba sai dai su yi kunnen doki sunanta Mafira, kuma 'yar uwar Zarifa ce uwa daya uba daya suke, wato Hassana da Hussaina ne amma ita Mafiran tun da aka haife ta bata taba fita ba daga cikin gidansu domin dare da rana babu abin da take so face ta Zauna a cikin lambun gidansu tana kallon tsuntsaye da kananan dabbobin daji. Idan ka ga ta fita daga cikin wannan lambu sai idan lokacin barcinta ya yi." Koda Sulbaini ya zo nan a ZAncensa sai ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiye a gabansu waziri kuma ya shafeshi da hannun dama. Take fuskar Mafira ta baiyana akan madubin da kuma dukkan surar jikinta. Koda ganinta sai waziri da sauran wadannan bokaye hudu suka rude fiye da lokacin da suka ga Zarifa domin a zahirin gaskiya Mafira ta fi Zarifa tsawo da yalwal gashi.


Boka Sulbaini ya ci gaba da bayani ya ce, "Idan har sarkinmu ya sami nasarar auro Mafira za shirya gasar kamo barewa tsakanin zuri'ar makera da zuri'ar mafarauta na wannan birni kamar yadda aka saba yi a kowacce shekara domin a taya sarki murnar wannan biki nasa.


Da jin wannan batu sai waziri ya sake rudewa ya rasa hukuncin da zai yanke akan budurwar da sariki ya kamata ya zaba tsakanin Zarifa da Mafira. Baban Rabbasu ya murtuke fuskarsa zuciyarsa ta kama tafarfasa saboda kishi da bakin ciki akan boka Sulbaini ya zo da abin da ya zama kishiyar nasa.


Lokacin da boka Sulbaini ya ga baban Rabbasu na kumbure-kumbure da bata rai sai shima ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa, har ma jikinsa ya kama tsuma, al'amarin da ya firgita waziri ke nan da sauran wadannan bokaye hudu domin sun san cewa idan wadannan hamshakan bokaye biyu suka kacame da fada ba karamin bala'i ne zai faru ba, wata kila ma sai gidan gaba daya ya rushe ko kuma ya kama da wuta.


Koda waziri ya fahimci haka sai ya mike zumbur ya dubi boka Sulbaini da Baban Rabbasu ya ce, "Yanzu ina son gobe da safe ku hallara a fada, domin kowannenku ya nunawa sarki fuskar budurwar da ya zaba masa in ya so sai sarki ya Zabi wacce ya fi so da kansa."


Koda jin haka sai boka Sulbaini da boka Zaharu suka mike tsaye suka tafi ko sallama babu. Kashe gari kuwa da sassafe sai ga boka Sulbaini da boka Zaharu a fada, sun hallara.


Bayan sun zube kasa gaban sarki sun kwashi gaisuwa sai waziri ya maida bayani bisa duk abin da ya faru jiya a gidansa tsakanin sa da su boka Zaharu. Sa'adda Sarki ya ji wanann bata'u sai ya cika da matukar farin ciki yai shiru yana tunani har tsawon 'yan dakiku.


Daga can sai ya yi gyaran murya ya ce, "Ya ku wadannan manyan bokaye na birnina abin takama a gareni, ku yi sani cewa bana bukatar ku nuna mini fuskokin wadannan yan mata guda biyu.

Abin da nake so da ku shi ne, ku yi shiri ni da ku da waziri da kuma wasu tsirararun dakaruna za mu yi tafiya izuwa birnin Kisra. Ina son kowannenku ya yi amfani da iya karfin sihirinsa domin na sami nasarar auro budurwar da ya za6a mini.


Duk wanda ya bani sa'ar dana auri Zabinsa lallai zan yi masa kyauta ta musamman kuma Zan bashi girma na musamman a cikin masarautata. Ina so ku gane cewa a cikinku bani da gwani ko abin so sai wanda kokarinsa ya sa na auro budurwar da ya zaba mini. Da wannan furuci nake sallamarku domin ku je gida ku yi duk shirin da ya kamata. Lallai i yanzu zA mu kasance masu jiranku anan fada".


Koda Sarki ya gama wannan jawabi sai ya mike tsaye ya shiga cikin gidan. A sannan ne boka Zaharu da boka Sulbaini suka kalli juna cikin harara a lokacin da idanuwansu suka kada suka yi jawur kamar an gasa dan buda a wuta.


Daga can sai kowannensu jikinsu ya kama tsuma kamar za su kaure da fada har wani irin tiririn hayaki ne ke fita daga cikin kunnuwansu, baminsa da hancinsu. Koda ganin wannan al'amari sai hankalin gaba đayan jama'ar da ke fadar ya dugunzuma aka fara mimewa ana ficewa da sauri. Shi kuwa waziri sai yai sauri ya kama hannun boka Sulbaini ya jashi suka fice daga cikin fadar yana jansa da hira cikin lafazi mai taushi domin ya sanyaya masa zuciya.


Nan take waziri ya sa aka kawo keken dokinsa suka shiga ciki tare suka ZAuna sannan aka ja suka tafi. Sai da waziri ya kai boka Sulbaini har kofar gidansa yana tausar zuciyarsa akan kada ya daka ta boka Zaharu su yi fada tun da idan suka yi fada sai sun dagula hankalin kowa a garin kuma sai kwanciyar hankali da zaman lafiya ya yi karanci. Sa'adda boko Sulbaini ya ji wannan batu sai ya yi murmushi ya ce, "Ya kai waziri kayi sani cewa kiyayyar da ke tsakanina da boka Zaharu ta gado ce domin tasowa muka yi muka ga iyayenmu da kakanninmu na yinta. Ina tabbatar maka da cewa har abada ba zamu daina wannan gaba ba face dayanmu ya ga bayan đaya ko kuma idan mun yi RAGAS. Bugu da kari ka sani cewa ni daga zuri'ar Makera na fito shi kuwa daga zuri'ar mafarauta yake, gabar da ke tsakanin wannan Zuri'a biyu ta fi shekara dari ana yinta kuma har duniya ta nade ba za daina ba. Ni kam zan yi iya kokarina na ga cewa ba mu yi rigima ba ni da shi a cikin wannan birni namu face idan ta kure babu yadda zan yi."


Nan dai Waziri ya yiwa boka Sulbaini sallama ya tafi gida. A daren Wannan rana babu wani mahaluki da ya yi barci a cikin birnin Darul Mahabul saboda wata irin tsawa mai firgitarwa aka rinka kwadawa a Sararin samaniya har tartsatsin wuta yana zubowa kasa.

Duk wata dabba mai rai ko shuka idan wannan tartsatsin wuta ya fado ma ta, nan take take konewa kurmus. Duk wani mai tsautsayi da ya sake ya fito waje kuwa a wannan dare sunansa gawa. Kai ba ma mutane ba hatta Aljanun da ke ZAune a birnin saida suka yi hijirar dole a wannan dare suka bar cikin garin suka koma can nesa da gari cikin dazuzzuka basu dawo ba sai da gari ya waye. Ba komai ne ya haddasa duk wannan bala'i ba face fishin da su boka Sulbaini suka yi da juna.


Wato a cikin daren ne suka rinka aikawa junansu da masifu iri-iri amma maimakon masifar ta sauka a kansu sai ta rinka kwamarzuwa da yar uwarta a sama cikin sararin samaniya tana zubowa kasa kan mai uwa da wabi. Kashe gari kuwa da safe, Sarki, Waziri da Dakarun rakiya mutum dubu biyu suka yi hawa cikin shigar yaki mai kwarjini da ban sha'awa Sannan aka tanaji guzuri mai yawa bisa kan rakumi đari biyu sanann aka kimtsa wadansu kuyangi guda goma wadanda za su yi wa sarkk hidima a cikin tafiyar. Sarki bai fito ba daga cikin gida sai da boka Sulbaini da boka Zaharu suka iso.


Da fitowar Sarki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment