Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranar kwana na goma sha ukun ne Hantaru ya je gaban rijiya ta biyu ya tsaya yana shawara da zuciyarsa akan ya budeta ko kada ya bude. Da zarar ya kai hannu da nufin zai sare mukullin rijiyar sai hannunsa ya kama karkarwa ya kasa saboda tsoron kada ya budo abin da yafi na rijiyar farko bala'i wanda ka iya zama sanadin ajalinsa gaba daya.


Sai da Hantaru ya jarraba hakan sai ya kasa sare mukulin, Nan take Hantaru ya tuno da irin gwagwarmayar da ya sha a baya da lamarin da ke gabansa na auren gimbiya Larziya da batun komawa birnin Sin, sei kawai yi kanin tsoro ya kau dagA zaciyaraa Nan take ya daga takobinsa sama yana kurma ihu ya sare makullin.

Nen take murfin rijiyar ya fadi cen gefe daya. Bisa mamaki sei baiga komai ba Hantaru ya sake rike takobinasa da kyau ya gyara tsayuwa ya jiran yaga abinda da zai fito daga cikin rijiyar.

koda ya ji shiru sai ya matsa gaba da nufin ya wuce kan rijiya ta uku itama ya budeta. Yana gifta wennan rijiya ta kwatsam sai ya jiyo wani irin gurnani irin wanda bai ta6a ji ba da huci na busowa. Cikin razAni Hantaru ya ja aa beya ya sake gyara tsayuwa


Wani irin dogon hannun bil'adama ne lafcece ya fara lekowa daga cikin rijiyar, sannan hannu na biyu ya leko. Daga can kuma sai ga mutum ya taso sama a hankali gama mikewa gaba daya.

A sannAn ne Hantaru ya gA she maridi ne. Tun da Hantaru yazo duniya bai taba ganin bil'adama mai tsananin tsawo da kauri ba tamkar wannan maridi, domin ita dai rijiyar zurfinta ya kai kamu dubu, amma gashi ta yiwa maridin kadan, tsugunnawa ma yai a cikinta.

Fadinta ya kai kamu arba'in, amma da kyar maridin ya fito daga cikinta, sai da ya muskuta kirjinsa sannan ya sami damar fitowa. Hantaru ya karewa wannan maridi kallo daga sama har kasa sai zuciyarsa ta karaya ya tabbatar da Cewa rayuwarsa na tsakanin RAI DA MUTUWA. Kawai sai yaja da baya ya takure a jikin bangon kogon, amman bai yar da takobinsa ba.


Maridin ya wangame katon bakinsa ya kurma wani ihu, wanda ya haddasa girgizar kogon gaba đaya har duwatsu kanana suka rinka zubowa kasa. Karar ihun tasa Hantaru ya yarda takobinsa ya rufe kunnuwansa har ya tsugunna kasa yana neman maboya, domin ji ya yi kamar dodon kunnensa zai fado kasa.

Nan take maridin ya shako wuyan Hantaru ta baya da 'yan yatsun hannunsa biyu ya đaga sama tamkar ya dauki fara, sai ga kafafun Hantaru na wutsil-wutsil, gaba daya jikinsa na reto.

Maridin ya tsaya yana tunanin irin kisan da ya kamata ya yiwa Hantaru. Da farko sai ya dunkule hannu ya kai masa wawan naushi a fuska. Duk da cewa yana ruke da wuyan Hantaru gam- sai da Hantaru yi waf ya zunguri idon maridin da f
kafa, domin ya tabbatar da cewa idan maridin ya gabza masa Wannan naushi, sai ya tatitse fatarsa tamkar an taka ayaba akan dutse.

Tsokanewar idon da Hantaru ya yiwa maridin ne yasa ya dimauce ya saki wuyan Hantaru ya fado kasa, amma huk da haka sai da hannun Maridin ya nutse a cikin bangon kogon dutsen tamkar ansa diga da guduma an buga a cikin bengo sai gashi ya haddasa wawakeken rami ajikin bangon, amma bai ji zafin komai ba a hannunsa tamkar ma takarda ya huda.


A fusece maridin ya juyo ya đaga kafarsa pa y kawowa Hantaru mugun taku. Cikin matukar zafin nama Hantaru ya goce ya bar inda yake.

Sai ga kafar Maridin ta lume a cikin kasa iya kaurin gwiwarsa. De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya saka mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka fara guje guje tsankanin Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai masa wawan naushi da bugu da hannu da kafa shi kuma yana gOcewa da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya haddasa mugun rami, walau bango ko kan kasa. Al'amarin da ya janyo gaba dayan kogon ya kama rugujewa...

Zan dakata nan zamu cigaba sati bayan kwanaki uku kuyi hakuri, ya daukeni lokaci mai tsawo kafin na dawo insha Allahu na dawo kenan.

Shuraihu Usman
Sai dai fa ku sani zaku iya samun littafinnan da ma wasu littatafan na yake yake complete a shafinmu na Taskar Novels a kyauta.
MR HAUSA EBOOKS



MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Chapter 3
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023

Sai ga kafar Maridin ta lume a cikin kasa iya kaurin gwiwarsa. De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya saka mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka fara guje guje tsankanin Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai masa wawan naushi da bugu da hannu da kafa shi kuma yana gOcewa da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya haddasa mugun rami, walau bango ko kan kasa. Al'amarin da ya janyo gaba dayan kogon ya kama rugujewa ke nan, ya zamana cewa shi kansa maridin hankalinsa ya tashi, don haka sai ya koma gefe daya ya tsaya cak Yana hanki suka kara kallon- kallo tsakaninsa da Hantaru.

Babban abin da ya fi tayarwa da Hantaru hankali shi ne, kofar kogon ta rufe ruf, babu ta inda ma zai iya fita bare ya nemi hanyar gudu sakamakon rugujewar da kogon ya yi, manyan duwatsu suka rikito kasa.

Nan fa Hantaru ya aiyana a ransa cewa bashi da wata mafita face ya tunkari wannan maridi ya San dabarar da zai bullo masa ya kashe shi.

Dole ne ayi daya cikin biyu, ko shi maridin ya sami nasara ko shi Hantaru ya samu.

Kamar hadin baki sai maridin da Hantara suka wangame baki a lokaci guda kowannensu y kama kwarara ihu.

Abin da ya đaurewa maridin kai kenan, domin a wannan karon ihun maridin bai ruda Hantaru ba, bare ya dimauce har ya toshe kunnuwansa.

Tun da wannan maridi ya wanzu a cikin wannan kogo tsawon daruruwan shekaru bai ta6a ihu ba ga duk abin da ya shigo abin ya iya jurewa ba. Kai bama mutum ba hatta aljan idan yana Wannan ihu nasa firgicewa suke, wasu su kama gudawa, Wasu ma sanadiyyar kurmancewarsu ke nAn.

Idan kuwa mutane ne ma take suke haukacewa, amma yanzu sai gashi Hantaru ya jure masifar ihun nasa harma yanA mai da martani da Dasa ihun.

A zahirin gaskiya Hantaru bu karamar juriya ya yi ba a wannan karon, domin gaba dayan jikinsa ya kama tsuma da karkarwa domin ji yake kamar an dura masa kwari masu yawa ba adadi a cikin kunnuwansa, suna tsinttsinka jijiyoyin kunnen, kuma yana jin kamar ana tsotse jinin jikinsa.

Bayan kowannensu ya yi ihu da kururuwa har gaba đaya kogon ya gama rugujewa, duwatsun suma suka rikito kasa, al'amarin da ya janyo Hantaru ya sami sababbin raunika ke nan a sassan jikinsa, in banda ma yana gocewa da tuni manyan duwatsu sun danneshi. Shi kansa Hantaru ya san cewa tsananin sa'a ne kawai ya ceceshi a cikin wannan kogo, sa'adda yake rugujewar amma ba zafin namansa ba.

Koda gama rugujewar kogon sai Maridin ya falfalo da gudu yana take duwatsu suna rumurmushewa, ya yiwo kan Hantaru gadan- gadan. Koda Hantaru ya ga mutuwa ta durfafoshi sai shima ya yi ta maza ya ruga izuwa kan maridin Shima yana mai ci gaba da kwarara ihu shima, maridin yana nasa ihun, kowannensu tafe yake cikin mugun nufi, kai da gani ka san cewa idan akayi wannan gamo dole ne mutuwa ta sami rabonta Sai da ya rage bafisaura taku đaya ba A tsakaninsu ba sai Hantaru ya yi sufa a kasa tamkar akan kankara mai santsi yake ya shiga karkashin Maridin ya takarkare iya karfinsa ya gabza masa naushi da hannaye biyu a marainansa.


Take maridin ya yi suman tsaye ya kame kamar ya zamo gunki. Cikin zafin nama Hantaru ya mike zumbur ta bayan maridin yasa guiwar hannunsa ya doki tsakiyar hannun maridin na hagu. Take hannun ya karye ya yi kara kas! Maridin ya kurma ihu ya juyo a fusace ya kawowa Hantaru mangari da daya hannun nasa. Cikin sa'a kuwa ya sami Hantaru a kirji. Karfin mangarin ne yasa Hantaru yai sama ya fado kasa kan dutse ya baje a sume.

Maridin ya yunkura da kyar yana tafiyar tatata kamar sabon dan kaciya a lokacin da karyayyen hannunsa ke gilu-gilu kamar zai fadi kasa ya nufi inda Hantaru ke kwance a sume.

Nufinsa kawai yaje ya tallafo kan Hantaru ya yi masa rotse a ka, wato ya dagwargwaza fuskar Hantaru. Har Maridin ya isa kan Hantaru ya tsaya, Hantaru bai farfado ba. Nan take Maridin yasa hannunsa ya tallafo kan Hantaru da nufin ya naushi fuskar da dukkan karfinsa.

A dai-dai wanann lokaci ne Hantaru ya farfado, idanunsa suka bude. Koda ya ga maridin ya daga hannunsa lafiyayyen zai nausheshi. sai ya yunkura cikin mugun zafin nama ya kamo karyıyyen hannun ya fincika. Saboda tsananin zafi da zogin da maridin yaji bai san sa'adda ya saki ftsari ba.

Kafin ya yi wani yunkuri na cutar da Hantaru tuni Hantaru ya sake kamo daya Iafiyayyen hannun shima ya gabza mAsa naushi da guiwar hannunsa. Take hannun ya karye ya yi kara kamar na farko. Maridin ya fadi kasa da ruf da ciki. Duk da haka Hantaru bai kyaleshi ba sai da ya kama kafafunsa duka biyun da karfin tsiya suma ya kakkaryasu daya bayan daya.

ihun da maridin ya yi a lokacin da Hantaru ke karya masa kafafunsa ya ninka wanda ya yi da furko sau goma, domin gaba daya halittun da ke dajin sai da suka firgice suka kama sauya sheka. Sauran wadunnan rijiyoyi kimanin guda dari da casa in da ya'ya sai da murafensu suka bude, gaba daya a lokaci guda.


Abinda ya fara yin fitar burgu daga cikin rijiyoyin shi ne, takobin Saiful Lujara. Wata irin takobi ce ta musamman wacce aka kerata da lu'u lu'u sai sheki da walwali take tana kashe idanu. Nan take haskenta ya haskake kogon gaba daya. Da wani irin mugun karfin gudu takobin ta taso sama. Koda Hantaru ya yi arba da takobin sai ya yi wuf ya taka bayan maridin ya daka tsalle sama yabi takobin tamkar an harbashi daga cikin kwari. A can saman ya kamo murikin takobin. Koda ya sunkuyo da kansa kas a lokacin da yake durowa sai ya yi arba da mugayen abubuwan da ke fitowa daga cikin rijiyoyin, sai hankalinsa ya dugnzunma ainun, domin ya san cewa irinsa đari ma ba za su iya hallaka abubuwan ba.

Mugayen dabbobin daji ne suka rinka fitar burgu daga cikin rijiyoyin, mASu yawan tsiya ba iyaka. Daga manyan zakuna, irin wanda ido bai taba gani ba, sai manyan Kuraye da Damisoshi, kuma fitowa suke tayi daga cikin rijiyar kamar ba za su kare ba. Rijiyar da takobin Saiful Lujaran ta fito ne kadai wani abin bai sake fitowa daga cikinta ba. Tun a saman Hantaru ya kara rike takobin Saifal Lujara da hannayensa biyu gam-gam. Ai kuwa yana dira a cikin kogon azababben yaki ya kacame tsakaninsa da miyagun dabbobin, suka yanyameshi suna kai masa cizo da yakushi, shi kuwa ya dinga ragargazarsu da takobin Saiful Lujara, sai dai ka ga a lokaci guda ya dara dabbobi uku ko hudu ya tsargesu gida biyu sun zube kasa matattu.


In banda cewar Hantaru mutum ne mai matukar zafin nama yana kaiwa dabbobin sara ta ko ina, wato gabas da yamma, kuda da arewa, sama da kasa, da tuni sun tumurmusheshi. Duk da zafin naman nasa SAi da suka rinka kartar jikinsa suna cizonsa amma saboda karfin sihiri kaifin faratansu dana hakoran nasu baya tasiri a jikinsa, amma kuma sun kumbura masa jiki sun taru masa jim.

Babban abin da ya fi tayar Masa da hankali shi ne, rashin karewar dabbobin, domin yana kashe su ne wasu na kara fitowa daga cikin rijiyoyin tamkara sannan ake haihuwarsu. Kuma abin da ya lura da shi shi ne, babu kokarin da dabbobin ke yi face su kwace takobin Saifal Lujara daga hannunsa.

Hantaru ya yi nazari ya fahimci cewa idan da aka Sami koda rabin sa'a ne a na wannan gumurza lallai zai gaji har wadannan dabbobi su kaishi kas su turmusheshi, idon kuwa suka turmusheshi Lallai za ta kai cewa sun rabashi da takobin Saiful Lujara, Sannan su hallakashi. Koda Hantaru ya fahimci haka sai ya fara tunanin mafita.

Abin da ya fara fado masa a rai shi ne, masu iya magana sun ce "Gudu ba tsoro bane idan masifa ta kai masifa " Koda gama aiyna hakan, sai Hantaru ya shammaci dabbobin nan ya daka wawan tsalle Sama ya yi fitar burgu daga cikin kogon, tun da dai saman kogon ya yaye sakamakon rugujewar da yayi.

Ai kuwa suma dabbobin sai suka daka tsalle sama gaba dayansu suka bishi a sama. Hantaru na dira a wajen kogon bisa turba sai ya fara falfala matsanaicin gudu. Nan fa aka kasa tsere tsakaninsa da dabbobin. Gudun da Hantaru ke yi ya wuce gaban misali, domin gudu ne na sihiri, Sai dai ka ga yana gifta bishiyoyin dajin giftawar tauraruwa mai wutsiya. Abun takaici da ya waigo sai ya ga wadannan dabbobi na daf da shi kamar marabarsu bai wuce kamu daya ba. Inda zai tsaya da taku daya zasu iya tsalle su cimmesa, Abin da Hantaru bai sani ba shine gudun da dabbobin suke yi shima na sihirine.

Sirrin shine duk halittar da ke cikin kogon da takobin Saiful Lujara take an sihirceta, yadda ba zasu taba bari kowa ya mallaki takobin ba sai sun tsare takobin don kar tabar hannunsu.


Inda ace Hantaru ya yar da takobin dabbobin ba zasu biyoshi ba. Haka dai Hantaru ya cigaba da matsanaicin gudu, dabbobin na biye da shi daf da daf suna gurnani da kartar kasa kamar sa ci babu. shi kansa Hantaru duk da cewar yana da dakakiyar zuciya a duk sa'adda ya waigo yayi arba da dabbobin sai yaji zuciyarsa ta karaya domin ya san cewa akwai iyakar lokacin da zai iye jure wannan gudu, don haka idan ya gaji dabbobin za su bankeshi sai abin da hali ya yi.

Komai jarumtakar mutum da juriyarsa idan ya ga yadda wadannan dabbobi suka tuso Hantaru a gaba dole ne zuciyarsa ta karaya domin ya san cewa idan ma zai tsaya ya ci gaba da yakarsu ba zai iya karar da su ba a cikin kwana bakwai saboda yawansu. Sai da Hantaru ya shafe sa'a bakwai yana gudu a cikin daji, wadannan mugayen dabbobin na biye da shi babu daga kafa.
Sa'a bakwai na cika ne suka iso cikin wani irin daji mai yawan surkukiya da duhuwoyi gami da kayoyi masu tsini. Bisa mamaki sai Hantaru yaji kayoyin na huda jikinsa har jini na tsartuwa. Alamarin da ya janyo ya fara layi da tangadi ke nan. Amma saboda naci da juriya bai fasa gudun ba su kuwa dabbobin dađa matsawa suke ta cikin kayoyin tamkar suna hawa kan kalmami jikinsu ko kwarzAnewa baya yi.


Sannu a hankali Hantaru ya fara gani dishi- dishi sakamakon jinin da ke zuba a jikinsa mai yawa ya zamana cewa yana gudu ne kawai amma baya ganin abin da ke gabansa. Kwatsam! Sai yai karo da ka da wata katuwar bishiya tamkar fyadashi aka yi a jikinta. Nan take jini yai fitar burgu daga cikin bakinsa de hancinsa ya fado da baya a sume ya baje a kas. Takobin Saiful Lujara ta subuce daga hannunsa ta fadi gefe daya.

A dai-dai wannan lokaci ne wadannan miyagun dabbobin suka iso kansa suka yi masa kawanya suna shirin yuyyagashi. Daya daga cikin dabbobin wani murgujejen tsohon Zaki sai ya yi girgiza ya rikide ya zama wani tsohon aljani wanda shekarunsa sun haura dubu ashirin. Kawai sai ya nufi inda takobin Saiful Lujara take da nufin ya dauka. Kwatsam! Ba zato ba tsammani, sai ga wata irin guguwa mai karfin tsiya ta baiyana ta tarwatsa gaba dayan wadannan dabbobi tayi jifa da su can nesa har shi kansa wannan tsohon aljani mai shirin đaukar takobin Saiful Lujara.

Kafin dabbobin sU Sake rugowa da gudu inda Hantaru yake kwan ce a sume, tuni guguwar ta đauke Hantaru da takobin Saiful Lujara tayi sama da su ta luluka a cikin gajimare ta 6ace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a saman. Kawai sai wanann aljani da dabbobin suka tsaitsaya cak suka daga kawunansu sama suna kallon dai-dai wajen da guguwar ya kule da Hantaru. Daga can kuma sai suma suka 6ace 6at.

LOkaCIN da Hantaru ya farfado daga dogon suman da ya yi, sai ya tsinci kansa a cikin wani kasaitaccen đaki kwance akan wani luntsumemen gado mai taushin gaake.

Komai na cikin dakin an yi shi ne da zinare, don haka gaba dayan dakin sheki da walwali yake.

Abu na farko da Hantaru ya fara arba da shi shi ne, takobin Saiful Lajara jingine a jilkin bango bisa wani ma'ajiyi. Koda ganin takobin sai Hantaru ya saki murmushin murna ya mike zaune sanann ya zuro kafafunsa kasa daga kan gadon ya nufi inda take yana tafiya da kyar a lokacin da yaji gaba dayan jikinsa ya yi tsami.

Saura kiris! Hannnunsa ya kai kan takobin sai ya dubi wani madubi da ke kusa da takobin. Nan take ya ga ashe gaba dayan fuskarsa a kumbure take ba kyan gani, kuma tayi kaca-kaca da rauni sakamakon muguwar buguwar da ya yi da bishiya, musamman idanunsa sun yi luhu-huhu da kyarma yake iya budesu. Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai dai a...

Zan dakata anan sai sati bayan kwana uku zamu cigaba.

Shuraihu Usman Inkiya 99%.
Mr Hausa Ebooks

MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Chapter 4
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023

Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai dai a daura aurensa da gimbiya Larziya.

Cikin hanzari Hantaru ya dauki takobin Saiful Lujara ya nufi kofar fita daga dakin, kawai Sai ya ga wata tsaleleliyar budurwa ta baiyana a gabansa fuskarta cike da murmushi.

Cikin tsananin mamaki da firgici Hantaru yaja da baya yana kallonta ya ce, "Mutum ko aljan?".

Ba komai ne yasa Hantaru ya yi ma ta WannAn tambaya ba face ganin tsananin kyawunta wanda ya ninka na gimbiya Lariya sau uku.

Budurwar tayi murmushi wanda ya kara baiyana kyawunta karara har Hantaru ya ƙara dimancewa sannan kuma sai ta murtuke fuska ta dubeshi ta ce,

"Haba gwarzon shekara wane irin sauri kake yi haka? Shin baka ga yadda fuskarka take bane har kake tunanin komawa birnin Darul Habur cikin wannan sifa? Yaya masoyiyarka gimbiya Larziya za ta kasance idan ta ganka a cikin wannan siffa? Bai zamo dole ba ma ta shaidaka ba, kamanninka gaba daya sun sauya. Ka sani cewa jikinka a cike yake da raunika da kuma taruwar jini, idan ka ce za ka cigaba da tafiya a haka wađannan mugayen dabbobin na kogon da takobin Saifal Lujara take za su sake binka su rabaka da takobin, kuma su hallaka ka, kaga kenan kayi biyu babu, babu ranka, kuma babu takobin, duk wahalar da ka sha a baya ta zama ta banza.' Burin dangin mahaifiyarka na cin gasa bai cika ba, kaima burinka na auren gimbiya Larziya ya rushe, bare kuma har ka koma birnin Kisra ka sadu da mahaifnka sarki Kusaidu wanda kullum dare da rana a cikin begenka yake."

Sa'adda kyakkyawar budurwar tazo dai-dai nan a jawabinta sai Hantaru ya cika da tsananin mamaki ya kura mata idanu kawai yana mai kara kankame takobin Saiful Lujara a kirjinsa. Sannan ya ce, *Ya ke wannan kyakkyawa, wace ce ke, kuma me yasa kika ceto rayuwata daga hannun wadannan dabbobi na kogon da wannan takobi take ciki kika kawoni nan?".

Koda jin wadannan tambayoyi sai buduwar tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "A gaskiya ba zan iya gaya maka amsar wadannan tambayoyi ba a yanzu, sai bayan ka sami lafiyar jikinka gaba daya, wato ranar da zamu yi bankwana ka tafi izuwa birmin Darul Mahabul.

Wata kila daga Wannan rana ba zamu sake saduwa ba, wata kila kuma daga wannan rana ba zamu sake rabuwa ba". Hantaru yai shiru a karo na biyu yana nazarin abin da ta fadi. Amma bai fahimci komai ba, kawai sai ya dago kansa ya sake dubanta ya ce, "Tsawon kwana nawa ne zan yi na gamna jinyar jikin nawa na tafi?",

Budurwar ta ce, "A kalla kwana goma sha hudu. A sannan ne fuskarka za ta yi fes ka koma ga masoyiyarka cikin kyakkyawar siffa," Koda jin haka sai Hantaru ya yi murmushi. Amma da ya dubi budurwar sai ya ce a ransa. "Ina ma ace gimbiyu Larziya ce da kyau irin na Wannan budurwa, da na gama morewa a duniya, domin na tabbatar da cewa a duniya kaf ba za a sami kamarta ba. Ashe har akwai wadda tafi Larziya kyau a cikin wannan duniya?".

Hantaru ya tambayi kar sa a cikin zuciyarsa. Kamar budurwa ta san irin zancen zucin da yake yi sai ya ga tayi masa murmushi sannan ta tako kafafunta a hankali cikin tafiyar kasaita tamkar dawisu tazo daf da shi ta kama hannayensa ta jashi izuwa kan gadonta ta zaunar da shi ta ce,

"Ya kamata yanzu ka ci kasha sannan ka sha magani ka kwanta ka huta".

Kafin Hantaru ya ce wani abu sai ya ga wadansu kyawawan kuyangi guda biyu Sun baiyana tsulum a gabansa. Daya na dauke da katon faranti cike da abinci iri-iri dayar kuwa kayan shaye-shaye ne kala-kala har da na magani. Har a Wannan lokaci budurwar na rike da hannayen Hantaru, wani irin laushi da yaji a hannayenta ne yaji ko kadan baya son ta saki hannayensa, domin bai san sa'adda ma ya fara lumshe idanu ba amma da zarar ya dubi fuskarta sai ya ga tana rikida tana zama gimbiya Larziya.

Kaico! Hakika soyayya dafice wadda idan ta ratsa sassan jikin mutum, fitarta sai yaki. Duk tsananin kyawu irin na wannan budurwa wanda ya ninka na gimbiya Larziya sau uku bai sa Hantaru ya fi sonta ba akan Larziya saboda tuni zuciyarsa ta gama cika da begen Larziya babu sauran gurbi wanda wata za ta samu.' Ba tare da bata wani lokaci ba kuyangin suka ajiye farantan biyu bisa kan wani tebur da ke gabansu Hantaru sannan suka bace 6at!

Bacewarsu ke da wuya sai budurwar ta fara ciyar da Hantaru da hannunta kuma tana ciyar da kanta. A haka sai da suka koshi sannan ta baiwa Hantaru ruwan magani kala shida ya sha. Yana gama shan maganin sai ya dubeta ya budi baki domin ya tambayeta sunanta amma sai yaji bakin nasa ya yi masa nauyi ya kasa magana, idanunsa kuwa sai suka kama lumshewa kawai sai ya tuntsure akan gadon ya kama barci. Koda ganin haka sai budurwar ta kura masa idanu tana murmushi, daga Can kuna sai idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar a hawaye.


Jim kadan kuma sai ta fashe da matsanaicin kuka sai da ta shafe sa'a guda tana ta kukan tamkar wacce ta rasa ivayenta a lokaci guda sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin tana waigen Hantaru kamar har abada ba Za ta sake ganinsa ba. Daga Wannan rana kullum Wannan kyakkyawar budurwa na tare da Hantaru dare da rana tana jinyarsa kuma tare suke cin abinci safiya, rana da dare, sannan su yi ta hira basa rabuwa face ta ga Hantaru ya soma jin barci sannan tayi masa sallama ya tafi turakarta.

Tsawon kwanaki goma sha hudu, Hantaru bai taba fita ba daga cikin dakin da ake jinyarsa face ya shiga Wani kewaye idan bukata ta kamashi. Hatta wanka

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment