Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aunty ta ce.
tana ji tana gani Aunty ta tasa ta a gaba suka wuce ,daman hausawa sun ce "Wai faɗan da ya fi ƙarfinka sai ka mai da shi wasa."
Mai_Ƙosai

*LOKACI NE*
Mai_ƙosai

FCWA

Huɗu.

San da suka isa asibitin ba su wani sha wahala ba, kasancewar akwai likitan da suka saba gani wanda shi ya zame musu tamkar likitansu.
Wasu ƴan tambayoyi ya mata kafin ya dangana ga yi mata wasu ƴan gwaje-gwaje, da ciki suka haɗa harda na hawan jini, jin cewar tana fama da jiri da matsanancin ciwon kai.
Gwajin farko ya tabbatar da hawan jinin sai kuma ciwon gyanbom ciki da kuma zazzaɓin maleriya. Sai da ya yi ƴan rubuce-rubucensa na wasu ƴan sakanni kafin ya kallesu ya ce,
"A bisa bincike na da na yi ya nuna min tana da hawan jini wanda shi ne musabbabin da ya sa take jin jirin akai-akai. Sai kuma zazzaɓin maleriya da kuma ulcer(ciwon gyanbom ciki). Amma alhamdulillah zan ɗorata kan magunguna sai dai zan ɗan riƙetana tsawon kwana biyu koma fiye da haka zuwa dai ganin yanayin jikin nata."
Aunty ta sauke ajjiyar zuciya kafin daga bisa ni ta ce,
"To likita mun gode sosai ba damuwa a yi duk abin da ya kamata dan Allah."
Kamar yadda ya ce musu zai riƙeta hakan ce ta faru, kwanciya ya ba ta tare da saka mata robar ƙarin ruwa.
Kallonta kawai Aunty ta ke yi tana mai kuma nazartar ta, ba ta san meke damunta ba, ba ta san wace ce ita ba, ba ta san daga ina take ba , abu ɗaya kawai ta sa ni tsinto ta da suka yi lokacin da suke gab da kaɗeta a kan tsakiyar titi, ganin kamar ba ta cikin nutsuwarta ya sa su ɗaukarta zuwa gida wanda shi ya kawo su wannan ranar. Ta fice daga asibitin tana mai kuma jinjina tausayinta cikin ranta.
Washe gari da safe bayan ta ƙarasa asibitin, har ma ta tarar da ita ta ɗan sami wani ɗan sassauci daga jiya zuwa yau.
Bayan ta samu da ƙyar da ci abinci cikin san sake kwantar mata da hankali ta soma furta mata lafuza ma su daɗi.
"Ban san mece ce damuwarki ba, ban san ke wace ce ba amma ina so ki sakawa zuciyarki nutsuwa da salama ki manta da komai ki mayar da komai na ki ga Allah subhanahu wata'ala, wanda shi ne majiɓancin dukkan wasu al'amura, kuma sarki ɗaya jal! Sarki buwayi gagara misali na tabbata ki ka yi haka to lallai ba zai barki haka ba zai da fa miki."
Ta share hawayen da suka gangaro a kan kumatunta tana mai kallon Aunty da Musbahu da ya shigo a lokacin ka na ta ce,
"Tabbas kun min halaccin da ba zan taɓa mantawa da ku ba ko da bayan raina ku na maƙale a cikin zuciyata. Bakina ba shi da abin da zai gode muku sai dai na ce Allah ya biya ku da gidan aljanna. In sha Allahu kuma a yau ba gobe ba zan baku labari na za ku san ko ni wace ce, kuma za ku ji irin rawar da ƙaddarata ta taka cikin rayuwata. Ba ta ba su damar magana ba ta ci gaba da furta,
"Suna na Hajara Hashim Jama'are. Duk da cewa na sami sunan mahaifina a bakin mahaifiyata. Ni ɗin haifaffiyar ƴar garin Kano ce. Ni da mahaifiyata muna zaune a unguwar Ja'in. Ni kaɗai ce 'ya wajen mahaifana duk da cewa ban rayu da mahaifina ba sai mahaifiyatana ta so cikin so, ƙauna da kulawarta. A yadda na ji Mamana na faɗa tun ina yarinya ba ni da wani farin jini dan kuwa yara ba su fiya zuwa gareni ko da da sunan yin wasa ba, kuma na kasance miskila ta bugawa a jarida abar kwatance, da fari ta yi tunanin ko dan miskilanci na ne amma daga baya sai ta fahimce sam ba haka ba ne ba.
Bari na ɗan yi muku gwa-gwa-gwa cikin tafiyar kamar yadda mai koyan tafiya ke yi.
Mama na yawan ba ni labarin su ɗin ba mazauna nan ba ne ko na ce ta kance ita ba ƴar nan ba ce hasalima zuwo ce, ita kaɗai ta zo garin Kano sai tsohon ciki, wanda bada jimawa ba bayan zuwanta ta haifeshi in da ya kasance ta sami ɗiya mace ranar suna ko yankan da ake yiwa yara na rago ba ta yiwa 'yar ba tunda babu hali ta raɗa mata suna HAJARA wato ni ke nan. Ta kan ce min iya gata da nuna kulawa tana ƙoƙarin ba ni ,haka zalika ma tana ƙoƙari wajen ganin ta inganta tarbiyata ta sama min karatu, inda ta kai ni makarantar Allo da ke nan kusa da in da muke.Duk da cewa Unguwar babu irin waɗannan makarantun sosai amma mu Ja'in ɗin in da muke zaune kamar 'yan gargajiya haka mu ke, I! to haka ne mana tunda duk ba mu da kuɗi sai rufin asirin Allah da wadatar zuciya.
Na fara zuwa makarantar Allon sannu-sannu , Allah buwayi mai raba ni'imominsa ga bayinsa da ya tashi raba ta masu ƙwaƙwalwa sai ya raba da ni ni ma na sami kaso na. Duk abin da zan yi in dai fannin karatu ne to zan ɗauke shi a kaina duk yawansa.
Lokacin da na fara wayo sosai da sosai na kai shekara biyar na fara haddace alƙur'ani wanda na yi wajen izu biyu, idan na dawo gida Mama kan min bita kuma mu kan yi bita tare da ya ke tana da nata ilimin daidai gwargwado. Lokacin da na shiga shekara ta takwas a duniya ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen saka ni a makarantar boko, Mama tana yin aikatau cikin wani gidan masu hannu da shuni, ta kan je da ni gidan a lokacin akwai wata yarinyar Hajiyar gidan tana so na , za mu yi wasa tare duk da cewa ta girme ni a shekaru , hakanan ko a jikin girma ba za ka haɗamu ba domin ta fi ni nesa ba kusa.

Wannan duk ina gaya muku ne ta jinsa da na yi bakin Mama duk da dai ni ma ina ɗan tuna wani abun cikin yarintar rayuwata. Ba ta basu damar magana ba ta ɗora da,
"Haka rayuwa ta ke ta garawa yau da daɗi gobe babu, idan ya kasance ni da Mama ba mu halacci gidan aikin ba to Safina ƴar Hajiya za ta saka a kawota ta yinar ma na, ko a zo har gida a tafi da ni wajenta. Sai dai bamu san meke faruwa ba a iya wasu ƴan watannin da muka ɗauka da su babu wani sauyi amma lokaci guda sai muka soma ganin canji wajen Hajiyar, zaman mu da su sai ya koma shigen kalar na maƙiya mu koma zaman doya da manja. Guiwoyinmu ba sukammala sakewa ba sai da muka wayi gari Hajiyar na sanar da mu ta sami wasu ƴan aikin dan haka ta sallame mu, ina kuka Safina na kuka mu ka rabu.
Mai_ƙosai

*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_Ƙosai

FCWA

Biyar.
Rayuwa sannu a hankali ta soma yi mana zafi dan babu wani aiki da mu ke yi ko sana'a da za ta saka mu sami kuɗi. Sai da mu ka yi a ƙalla sati uku a haka sannan Mama ta fara ka sa min kayan yara na soma zama a waje ina saidawa ana ciniki sosai kasancewar yaran da ke unguwar, amma wani abin mamaki lokaci guda kuma sai cinikin ya ɗauke wuta ɗif.
Ganin haka sai ya sa Mama ta koma saida Ƙosai ,ni ce mai zubawa idan anzo siya, ni zan kai mata markaɗe da sanyin safiya, sai ya zamana karatuna ya fara wulagigi. Kamar wasa shi ma sai ciniki ya soma habbaka siya ake yi ba kama hannun yara. Wani abu da zai kuma baku mamaki shi ne ; shi ma loakci ɗaya aka ɗauke sawon siyansa, sai ya zamana duk abin da zamu kasa za a yi rububinsa da fari amma in ya kai tsakiya sai ya daƙile, wannan ya sa Mama ta tattara komai ta watsar na koma makaranta babu fashi, Allah ya so ma makarantar bokon ba ta kuɗi ba ce sai dai duk zango ana bada ɗari bakwai ko ta mece ce oho! musu, mu dai sun ce mana kuɗin makaranta ne. Allo kuwa daman duk ranar labara ne ake bada kuɗin laraba kuma naira ashirin ce.
Muna cikin haka wanda har mun ɗan soma rasa abin sawa a baki kasancewar kuɗin hannun Mama ya taho gangara cikin ikon Allah Mama ta sami wani gida ta soma aiki tana musu wanke-wanke, da wannan damar muka soma dawowa dai-dai.
Ina da shekara goma sha tara na kammala sikandire da taimakon Allah, da kuɗin da Mama ke samu gidan aikinta. Sai na koma zaman gida ni kaɗai tun da Mama za ta tafi wajen aiki sai yamma take dawowa, sai na soma jin kaɗaici sosai.
Ba zan taɓa mantawa ba lokacin da ina makarantar boko a lokacin aji na biyar gab muke da kammalawa na kanji wata da'ira da aka haɗata cikin ajin yawancinsu masu shekaru da ɗan dama ne, ni dai bana shiga cikinsu hasalima sai dai na ja gefe na duƙufa kan karatuna. Kuma yawancin hirarsu duk akan samari ne, ko wacce in ta zo da irin na ta salon hirar da kuma wanda ta yi kamu da shi.
Tun maganarsu na ba ni haushi har ta soma ba ni sha'awa sai na ke ji inama ni ma na sami wanda zai ce yana sona ya dace da ni, dan a ganina ai sai wanda kalarsa ta yi min sannan zan saurara har na yarje masa zama saurayina. Sai ya zamana idan har su na hirar ko da karatu na ke yi to zan bari na dawo da kunnuwana garesu.
Akwai wata da jininmu ya zo ɗaya muna gab da fita, sai ya zamana ashe ma unguwarmu ɗaya sai dai akwai ƴar tazara mai ɗan yawa tsakanin gidanmu da na su.
Duk da ba ƙawancen kuzo mu gani ba mu ke yi ni da ita amma jin tana tsayawa da saurayi sai na kuma shigewa jikinta sosai na kanje gidansu a sati sau uku zuwa huɗu.
A lokacin fa ina da shekaru goma sha takwas.In dai har saurayinta zai zo to ranar tarewa na ke yi a gidansu da ni za a yi zancen ina maƙale da ita amma ni a tunani na wai ko ni ma zai ce ya na sona na ji daɗi. Duk da sauyin fuska da nake samu daga gareshi kuma ba na damuwa dan ko ajikina wai an mintsini kakkausa.
Duk yadda na so ta kai ga na ji an ambatamin kalmar so abin ya faskara, tun ba na damuwa har na soma damuwa ,ina ganin mene ne aibu na in dai kyau ne ai ina da shi dai-dai gwargwado, dan ni dai banga dame ƙawata ta fini ba hasalima zan iya cewa na fita komai na ƙirar jiki. Amma in kuka ga yadda maza ke rubobinta ku kwace kayan marmari ci, abin ya kan riƙa ba ni mamaki na kan ji na tsani kaina , sai naga kamar ni kaɗaice Allah ba ya so shiyasa ban sami saurayin ba.
Muna daf da kammala makaranta dan bai fi saura wata uku ba wani saurayi ya na ce min akan ya na sona. A cewarsa dai wai ya ganni ne lokacin da nake dawowa daga makaranta shi kuma ya na ƙoƙarin daidaita tsayuwar motarsa.
Ni kuma a lokacin har ga Allah ba na san shi, bawai dan ba shi da kyau ba a'a haka kawai ni bai min ba, kuma ina jin yadda majalisar matan ajinmu na koɗa samarinsu akwai wacca ta ke cewa ma saurayinta kamar ba ɗan Nijeriya ba kamar ɗan Indiya. Ni kuma sai na ji ina son na sami wanda ya ci uwar nata komai da komai.
Ko wanne kalar wulaƙanci yi masa na ke yi amma bawan Allah ko ajikinsa , bai taɓa fushi da ni ba duk kuwa irin abin da na ke masa.
Kamar kowacce rana an ta somu daga makaranta, bayan na iso gidanmu na iske shi jingine jikin motarsa sanye da shadda ruwan ƙasa har ga Allah ta masa kyau sosai amma ni a lokacin ban ga hakan ba.
Ina zuwa ko kallonsa ban yi ba na doshi ƙofar shiga gida kai tsaye da sauri ya sha gabana tare da faɗin,
"Haba Hajara ,tun ɗazu na ke nan tsaye ina jiran isowarki amma kin ganni kin nuna kamar ba ki ganni ba."
Harararsa na yi ka na na ce, "To sai me in na ganka, kai Annabi ne da zan yi ɗokin ganinka ko me.?"
Cikin sanyin murya ya ce,
"Ni ba kowa ba ne Hajara, amma ya kamata ki tsaya ki saurari abin da na zo miki da shi ko.?"
"To ubana Hashimu, ka ji bari na ɗakko maka tabarma sai ka tasa ni gaba ka ba ni darasi."
Na ƙarasa da shigewa cikin gidan na mu.
Ban ɗau lolaci mai tsawo ba na fito hannuna ɗauke da bokitin ruwa, ban tsaya wani jinkiri ba na juye masa shi a jikinsa tare da tofa masa yawu tare da assasamasa babban gargaɗi na wuce ciki na barshi wajen, ya tafi bai tafi ba oho! Masa ni dai hankalina a kwance. Kuma har kawo lokacin wannan lokacin da nake baku labarin ba wanda ya tunkare ni da maganar so ko aure, amma ni sam ba na jin san shi wallahi .
A kwana a tashi ba wuya wajen Alla, har ta kai mun kammala karatunmu har a lokacin babu wanda ya so ni da aure ko soyayya, kuma har a lokacin shi ma bai daina so na ba, bai dai na bibiyata ba ni ma kuma ban taɓa jin zan so shi ba , a lokacin da nake wannan haukan ban yi tunanin cewa lokaci zai zo min da zan yi kuka ba, zan yi da na sa nin da ba'a saka mishi rana. Ni da ban da wanda ya ke sona amma wai ni ce ke yiwa wani wulaƙanci.Har bayan kammala karatuna ya na manne da ni sai ka ce cingum, ka da ku yi mamaki in na ce ni sam ko sunansa ma ban sa ni ba saboda ba ya gabana.
Wata safiyar Lahadi ce muna zaune ni da Mama tana tsefemin kai na sai ka ce ƙaramar yarinya wajen ƙin tsifa haka na ke, ko da yake ma ai wasu yaran na santa. Amma zan iya cewa na fi wata yarinyar mara san tsifa ƙinta sosai. Wani yaro ne ya kwaɗa sallama,Mama ce ta amsa ya yinda yaron ya ɗora da faɗin,
"Wai Hajara ta zo inji wani a waje."
CIkin sauri da ɗoki, bakina washe kamar gonar auduga na ce, "Je ka ce ga tanan zuwa."
Yana jin haka ya fice daga gidan da saurinsa. Na kalli Mama ina murmushi kafin na ce,
"Mama ni dai ki barmin tsifar na je na dawo." Na ƙarasa cikin shagwaɓe fuska.
Ƴar dariya ta yi kaɗan tare da furta, "Kya ci gidanku ja'ira, wato ko kunyata ma babu ko.?" Ta ƙarasa cike da tambaya.
Ban amsa mata ba na fice da hanzarina bayan na ɗaure kaina ,alla-alla kawai na ke yi na isa naga wanda ke kira na, sam kwata-kwata tunanina bai kawo min shi a wannan lokacin ba tun da bai taɓa aikowa kira na ba duk tsawon lokacin da mu ka kwashe.
Ina isa na iske shi tsayi jikin motarsa, turus na yi tare da jefa masa wata arniyar harara ina mai jan tsaki.
Bakinsa washe kamar an masa albishir da aljanna ya iso gareni tare da faɗin,
"Barka da isowa gimbiyata."
Yatsina baki na yi kamar naga kashi ka na na ce, " Barka, me ya dawo da kai gidanmu, wai kai dan Allah ba ka da zuciya ne? Ka fita daga shika-shikan sabgogina, na ce maka ba na sonka-bana sonka ko ana so dolane?" Na jefa masa tambayoyi biyu a lokaci guda.
Allah sarki ɗan bawan Allah kai ka rantse da Allah babu zuciya a ƙirjinsa. Duk wannan bayanin da na gama shimfiɗa masa amma murmushi kawai ya ke yi ya na mai kallona fuskarsa cike da nuna alamun na tausaya masa ya ce,
"Dan Allah Hajara ki tausaya ki taimaka min, zuciyata gab take da tarwatsewa , ki daure ki sota ko da sau ɗaya ne dan Allah."
Ya ƙarasa tare da haɗa hannayensa waje guda alamar roƙo.
Dariyar shaƙiyanci na yi ina mai kallonsa sheƙeƙe ka na na ce,
"Tabbas kuwa zuciyarta ka za ta yi bindiga ta tarwatse kamar yadda bam ya ke fashewa. Lallai ba makawa zan zama lamba ta ɗaya daga cikin masu da sa mata bama-bamai a cikinta. Ka kiyaye ni, ka fita daga sabgata." Na ƙyasta yatsuna biyu ina mai shigewa gida da sauri na barshi wajen tsaye.
Ina shiga Mama ta shiga tambayata ko lafiya, dalilin ganin da ta yiwa fuskata a haɗe.
Sai da na ɗan ja guntun tsaki wanda ba lallai na nesa ya iya jiyoshi ba sannan na ce,
"Wani mara zuciya ne a ƙirji Mama, na jima da sanar masa ni ba na san shi amma ya ƙi ji yadda ki kasan kuturu wajen na ci, kuma wallahi.........."

*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_Ƙosai


FCWA

Shida.
Ta katse ni da sauri wajen faɗin, "Ke ƴar nan ki kiyaye ni Alƙur'an ,wanan wani irin tsantsar butulci ne? Tun da na ke da ke cikin gidan nan waya taɓa zuwa ya ce a yi sallama dake? Amma yanzu kin samu shi ne ki kewa Allah butulci? Ki ke wannan fiffiƙar? Ke ba ki ji kunya ba, ganɗai-ganɗai da ke gida zaune ba aure bai sa kin ji wani irin ya nayi ba.?"
Fuska na haɗe ina mai kuma jin tsanarsa cikin raina, duk a kansa Mama ke min wannan wannan faɗan.
"Ni dai Mama wallahi ba na san shi har nawa na ke? Shekarun na wa nawa suke da za a ce ganɗai-ganɗai da ni? Du-du-du fa sha tara zuwa ashirin ne fa, ni banga abin damuwa ba a kan hakan mijina zai zo sabo dal a leda ƙin kowa san wand......."
Mama ta kawo min mangara dalilin da ya sa na yi shiru ke nan. Na yi saurin shigewa ɗaki, ni tsifarma ba za a ƙarasa ba. Ina jiyo Mama na ta faɗa ta inda take shiga ba tanan take ɓullowa ba.
Wasa-wasa cikin sati biyu kullum sai ya zo, kuma duk san da ya zo ba wata magana mai daɗi tsakanina da shi in ka cire masifa da tijara da na ke a sassafa masa su. Amma ko kaɗan bai taɓa yin zuciya ba bai taɓa fushi ba kuma bai taɓa fashin zuwa ƙofar gidanmu ba cikin kwanakin.
Ban san ya a ka yi ba amma na ga su na takun saƙa da wani mai shagon unguwar mu wanda sam ni ba ma shiri da shi. Da farko ma na za ta ko abota suke yi ashe shi mai shagon ɓakin ciki ya ke yi a kan zuwan da shi saurayin ya ke yi ƙofar gidanmu, ya yi ta ɓata ni wajensa amma shi ya toshe kunnuwansa, baƙin fentin da ya ke san gogamin yaƙi gogowa jikina balle shi ya ganni da shi. Na sami labarin ta wajensa in da ya ke sheda masa mu ɗin zuwo ne ba a san asalinmu ba, sannan kuma ni shegiya ce , na ji zafin kalmomin na sa wanda har wajen mai shagon na je na zazzage masa ruwa masifu na. Kuma na sake baɗawa ido na toka ba na ji ,ba na ga ni na ce ni sam ba zan so shi ba."
Bayan wasu kwanaki kuma kamar a ƙalla sati uku sai na ji shi ɗif ya daina zuwa ban san dalili ba shi ya san masa, amma ni sai na ji wani daɗi mai garɗi, a lokacin sai na ke ji na sakayau kamar wacca a ka cirewa sarsari. Lokacin da na ke cikin nishaɗi na rabu da alaƙaƙai a lokacin ne kuma Mama ke cikin na ta damuwar, ga yawan faɗa akan abin da na aikatana rashin kyautatawa, duk da ni ba na ganin hakan a rashin kyautata masa da na yi. Zan iya ce muku ta shafe tsawon sati guda tana faman yi min faɗa, kuma tana cikin damuwa na yi-na yi ta sanar mini ta ƙi. Ni dai abu ɗaya na sa ni in tana faɗan zan ƙirƙiri barcin ƙarya ko kuma na ƙirƙiro fitar ƙarya dan wallahi ba na san faɗan Mama abin da ya faru da jimawa ma sai ta dawo da shi lokacin.
Rayuwa ta ci gaba da garawa ,shekaru, watanni, satuttuka, kwanaki, a wanni, mintuna da sakanni suka riƙa wuce wa. Kar ku yi mamaki in na ce shekara ashirin da biyu zuwa a shirin da uku babu wani saurayi da ya zo gareni a matsayin batun aure ko soyayya bayan wanda ya taɓa zuwarmin harma mugun hali na ya koreshi. A lokacin kuma ni ma sai hankalina ya soma ta shi, na ji ba abin da na ke sha'awa illa na gan ni tsaye da saurayi ko da a ce ba da aure ba, abin ya na cimin tuwo a ƙwarya.
Mama ta kuma shiga damuwa sosai duk da ban san mece ce matsalar ta ba, hankalinta ya yi matuƙar tashi. Dan kuwa duk in da ta gilma sai dai ka ji tashin gulmartana tashi a wajen ,habaici kam da zunɗe waɗannan ba a maganarsu. Wasu ma fuska da fuska za su tare ta da faɗin,
"Ƴarta ta yi kwantai ,ai daman auren shege sai shege." fiye da waɗannan ma jin su ta ke yi. Ta kan yi kuka fiye da misali wanda ni kaina ban sa ni ba sai lokacin da na dawo daga gidan ƙawata da na ke zuwa ganin saurayinta baya, to ta yi aure ta aure shi harda yaro ɗaya, ina shiga gida na iske Mama hawaye malala kan kumatunta, hankalina ya tashi sosai na shiga yi mata magiya akan ta sanar da ni damuwarta.
"Ina jin ɗaci ,takaici da tsantsar baƙin cikin irin mugayen kalaman da ake jifan ƴata da shi, ina jin ba daɗi a lokacin da na ke ganinki gabana zaune a gida. Amma na san jarrabawa ce Allah ya ke yi mana ,jarrabawa ce da Ubangijjn da ya samar dake ya ke miki, amma me ya sa za a dinga sheganta min ke ƴa ta? Me ya sa za a dinga goranta min ke ƴa ta? Mene ne laifinki cikin ƙaddararki." Ta rushe da kuka kafin ta ci gaba da faɗin,
"Yau zan sanar miki da abin da na jima ina ɓoye miki ko hankalina ya kwanta, kada kema wata rana ki tambayeni ina ahlinki? Ina ne aslinki? Ka da wata rana ki tsare ni da tambayar ko dai da gaske ke ɗin shegiyarce.?"
Ta ke na ji zuciyatana min zafi, daman da haushin faɗan da mu ka yi da ƙawatana taho gida a kan goranta min da ta yi kan aure , Wai ni na cika yawo naƙi na yi aure na tsaya ruwan ido, shi ne zan dinga bibiyarta dan na kashe matana ta aure, wa yasa ni ma ko auren mijin natana ke san yi?.
Ba ta san yadda na ji zafin kalaman na ta ba sosai, na ɗauka tamkar ƴar'uwa na ke wajenta ashe ni kallon mahaukaciya ta ke yi min mai bibiyar maza har gida, mai zuwa ƙwacen miji har gidansa. Na share hawayena na mayar da kunnuwana ga Mama da na ji tana furta."Ni da mahaifinki Hashim auren soyayya mu ka yi sosai , duk da cewa akwai alaƙar zumunci tsakaninmu amma mu ba auren zumunci mu ka yi ba auren soyayya ne. Kar na katse ki suna na Fatima kowa na ce min Asabe ni saboda ranar Asabar aka haifeni. Kakana da kakan babanki uwa ɗaya uba ɗaya su ke ,ƙaddarar da ta gifta mana guda ɗaya ita ce na rashin sona da mahaifiyarsa ta ke yi min,tun kafin auren ba ta sona, hakama bayan auren ba ta taɓa nuna min ko da da ƙwayar zarrar ƙauna ba. Ba gida ɗaya mu ke ba, gidanmu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On LOKACI NE
avatar
khamilu

1 year ago

Reply

Mashallah

Please Login or Register in order to submit comment