Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan gadan da nake kwance.

Ganin haka ya saka Rabi'a matsowa gareni da sauri tana mai riƙe hannuna ɗaya tare da shafa bayana cikin nutsuwa.

Mun ɗau tsawon mintoci a haka kafin ta miƙar da ni zaune sai kawai na rungumeta ina sake fashewa da wani kukan.
"Aunty dan Allah kada ki zama ɗaya daga cikin bayin Ubangiji marasa yadda da ƙaddararsu,ka da ki saka imaninki yin rauni. Ki zama baiwa mai godiya ga Allah sai ya sake inganta miki wasu tarin ni'imomin na sa." Ta tsagaita tana mai kallona bayan ta ɗago da fuskata.

Itama hawayen ne cikin idanuwanta wasu ma sun zubo. Na ce,
"Shi kenan ya cuceni ya lalata min rayuwata,ashe daman ba sona yake yi ba, ashe daman yaudarace kawai da cin amanar ruhi." (Littafin Hassana Ɗan Larabawa. Na rushe da wani firgitaccen kuka.

Ba ta iya cewa komai ba sai kawai ta sake rungumoni muka kuma fashewa da kuka. Muna haka wata mai kula da majinyata ta shigo ɗakin, ganin halin da muke ciki ya sakata dafa mu tare da tausarmu.

Ta zare robar ruwan dake maƙale a hannuna wanda ni lokacinma na lura da ita har wajen ya fara kunbura. Sosai naga take binmu da kallon tausayawa har ta fice daga ɗajin bayan ta bani magunguna na sha.

Mu kam kamar masu zaman makoki haka muka cigaba da zama a ɗaki sai dai kawai tashin sautin kuka da za ka ji.

Har dare banga kowa ba sai da duhu ya fara yi sannan naga Umma ta shigo,fuskarta babu fara'a ko kaɗan. Ganin haka ya saka ni komawa na kwanta tare da lumshe idanuwa na. Ban san ko ƙarfe nawa ba amma ta ɗan jima da zuwa na ji Rabi'a na mata sallamar sai da safe bayan ta shafa kaina a zatanta barci na ke yi. Na jima da tunanuka kala-kala cikin zuciyata har ban san sanda ɓarawo barci ya kwasheni ba.

Da safe na ɗan sami sauƙin raɗaɗin da nake ji. ko da na gaida Umman bata wani amsa da yalwacin annuri ba, sai ma maganar da ta hau yi wacca ta daki zuciyata matuƙa.
"Kin kyauta. Kin yi aiki na ƙwarai da har kika kasa riƙe maitarki ki kaje kika haɗiye muciyar da za ta miki maganinta,watanawa ya rage miki da har kika kasa iya riƙeta shekaru nawa kika ɗauka baki yi wannan aikinba sai yanzu da auren ya zo kin kyauta." Ta faɗa a zafafe.

Ji na yi kaina na sarawa, take na fara ganin tara-tara na gaza yadda zan iya furta kowanne irin furuci, muryar Rabi'ace ta dawo da ni daga halin da na shiga ashe Umma har ta fice daga ɗakin bayan tafiya wucin gadin da idanuwana ,ƙwaƙwalwata suka yi.
Wai Ummace ke faɗin haka ? Me yasa za ta min mummunar fahimta? Me ke faruwa ne? Na shiga tambayar kaina har sai da Rabi'a ta shiga shafamin bayana tana faɗamin kalamai maau ratsa zuciyar mai sauraro.

A taƙaice dai sai da na shafe kwana huɗu a asibiti sannan aka sallameni. Cikin kwanakin Rabi'a ta kula da ni sosai da sosai, iyayenta sun zo min sau ba adadi, Baba ya zo sau ɗaya, sai ƙanwata da take zuwa a kowacce rana, Umma kuwa dare ne ke kawota safiya na yi za ta tafi ba ko sallama.

Sati na biyu da fitowa harma na soma warwarewa sosai,har lokacin mutane na shigowa yimin sannu da jaje duk da mafiya yawancinsu gulma ce ke kawosu. Marasa ɗa a ido kuwa gabana gaban Umma za su riƙa habaici da baƙaƙen maganganu marasa daɗin sauraro. Har da masu magana kwatan-kwacin irinta Umma.

Abubuwa suka taru suka min yawa ,in kaga fara'ata ko murmushina to da Rabi'a ne,ƙanwata ta takanzo a sati sau uku ta dubani.

Rayuwa ta soma yimin zafi ,abubuwa suka haɗu suka min yawa. Baba da Umma suka juyamin baya ,mutane kuma suka sakani a tsakiya da maganganu kala-kala. Ba dama na fita sai an jefeni da munanan kalamai marasa daɗi,duk da iya bakin ƙoƙarin da Rabi'a da ƙanwata ke yi na san ganin na sami farin ciki amma hakan ya gagara.

Ji na yi kawai na gaza da irin hukuncin da mutane da iyayena suka yanke min,kowa ya gaza fahimtata. Duk yadda naso su Umma su fahimceni abin ya faskara. Ƙarshema bayan na sanar da su abin da ya faru sai suka ce, "Sharri zanwa ɗan bawan Allah." Munafikin kuwa sa'ad da Baba ya kirawoshi harda hawayen ƙarya, bai ko ji tsoran Allah ba ya shiga rattabawa Baba abin da ba hakaba. Wai daman ya sha kamani da ƙazaman hirarkin batsa ta yanar gizo ,ya sha gogemin finafinan batsa cikin wayata.

Baba ya mun faɗa sosai har takai da dukana a kan haka, kuma ya tabbatarmin da cewa ya fasa aurena.
Dole ya ce haka tunda ya ci moriyar ganga ya yada ƙwallon ai. Wannan abun ya sa na yanke hukuncin bar musu gidan da unguwarma gaba ɗaya ko na sami nutsuwa, zanje inda ba wanda ya sanni balle a kira ni da mazinaciya.

Cikin dare wajen ɗaya sawu ya ɗauke na salallaɓa na fice daga gidan ban ɗau komai ba sai wayata da nufin na riƙa haskawa, na shiga tafiya sannu a hankali har ban san sanda tsautsayi ya kwasheniba wani mai mota ya yi awon gaba da ni. A she fita ta rabon na haɗu da wanda zai tsaida ruwan hawayena zuba ne.Mutumin da ya sadaukar da farin cikinsa a kaina ,mutumin da ya inganta rayuwata daga baƙin ciki zuwa farin ciki.

A sibiti ya nufa da ni kai tsaye ,ya na zuwa aka tarɓemu da gaggawa. Wayata da ita ya yi anfani wajen kiran Rabi'a wacca da safe ta iso sai ganinta kawai na yi gefena tana bina da kallo bayan na farka. Wannan duk shi yake sanar da ni.

Likita ya shigo ya sake duba lafiyata wanda ya bamu tabbacin zai sallamemu a ranar.
An sallamemu kamar yadda likitan ya ce, ya kuma bani magunguna masu ɗan yawa wanda zan yi anfani da su. San da muka fito na kafe a kan lallai bazan bisu ba, su ƙyaleni zan shiga uwa duniya. Da ƙyar da siɗin goshi suka shawo kaina muka wuce gidansu Rabi'a kai tsaye dan na rantse bazan koma gidanmu ba. Tun a hanya su ke lallashina amma kukana ya gaza yankewa.

Allah sarki iyayenta masukaramci da sanin ya kamata suka amsheni hannu biyu cikin so da ƙauna bayan sun biyoni da nasiha mai ratsa zuciya.

Kwana na biyu kullum sai Abbas ya zo dubani, wannda na sami sunansa a bakin mahaifin Rabi'a.
Baban Rabi'a da Mamanta suka ɗauke ni zuwa gidanmu, amma Baba da Umma suka baɗawa idanuwansu toka a kan ba zasu amsheni ba, sun manta kowanne bawa da irin tasa ƙaddarar.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma biyar

Duk yadda suka so fahimtar da su illar abin da su ke san aikatawa amma suka toshe kunnunwansu, sun gaza fahimtarsu har lokacin Abbas shima ya zo a ka shiga damawa da shi amma ina sun yi nisa ƙarshema Baba ficewa ya yi daga gidan Umma kuwa ta yi kunnen uwar shege da mu.
Cikin kukan baƙin cikin abin da iyayena biyu suka min kamar ba ƴarsu ba na ce,
"Zan tafi ,zan yi tafiya mai nisa ta har abada ba za ku sake ganina ba. Zan shiga duniya zata zame min uwa da ubana." Ina gama gaɗin haka na fice da sauri daga gidan, ganin haka ya saka iyayen Rabi'a biyo ni tare da Abbas. Ni kam tafiya na ke yi babu ko waige har ban san lokacin da na ji tafukan hannayen Rabi'a kan fuskata ba, wai ashe bina su ke su na roƙona a kan na dakata da manufata amma na yi burus na toshe kunnuwana ba na jinsu, lokacin ne kuma Abbas ya je ya sanar da ita abin da ke faruwa shi ne ta iso gareni tare da wankamin mari kan fuskata. Na dawo cikin nutsuwata lokaci guda kuma Mahaifin Rabi'a ya soma min faɗa da nasiha mai tsuma zuciya har ban san lokacin da na durƙushe a wajenba ina kuka mai cin rai. Da ƙyar na miƙe muka dawo gidansu Rabi'a suka min alƙawarin zama da ni har lokacin d iyayena za su sakko su amsheni hannu biyu.

Ni ban sani ba ashe Rabi'a ta sanar da Abbas duk abin da yake faruwa dani. Ya tausayawa rayuwata sosai, ya shiga hidima da ni ba ji-ba-gani. Kullum ya kanzo sau uku ko biyu, in bai zo ba zai kira Rabi'a a waya ya tambayi lafiyata, ƙarshema sai ya soma kiran lambar wayata ya na jin ko lafiyata ƙalau,tun ba na sakin jiki da shi har na saki dan sautari Rabi'a kan ce min,
"Aunty ba na jin Yaya Abbas zai cuceki ko da da ƙwayar zarra ,dan Allah ki saki jikinki da shi." Wannan ya sa nima sai na ji hankalina ya kwanta da shi.

Shaƙuwarmu da shi ta dabance wacca ta cusa mana so da ƙaunar juna sa'ilin da ba mu yi zato ba, na kanji wani iri in banji daga gareshi ba ,shi kam sam baya samin nutsuwa ma sai ya ji daga gareni ko ya zo ya ganni. Ba a ɗau wani shahararren lokaci ba ya zo ya sami Baban Rabi'a ya sanar da shi abin da ke ransa na san aurena .

Kowa ya yi murna sosai, nima na ji daɗi fiye da zato. Iyayen Abbas sun amsheni hannu biyu ba tare da ƙyama ba, cikin sati biyu da faruwar haka aka kawo kuɗi da tsaida rana wata biyu cif masu zuwa in Allah ya kaimu.

Ɗauniyar da yakemin, da yadda ya ke kulawa da ni sai na ji soyayaarsa fiye da tunanin mai tunani, ina masa san da har saida Rabi'a ta kwaɓeni a kan haka, ni kam gani nake rayuwata ma zan iya bashi a wannan lokacin dan ina tsantsar ƙaunarshi da san shi.
Baban Rabi'a ya je har gidanmu kan maganar kuɗin aurena ,magana ɗaya kawai suka masa shi ne; "Allah ya nuna lokaci." San da ya ke sanar da ni na ji wani abu ya tokare maƙoshina kenan hakan ba zai saka su farin ciki ba ,saboda kawai an lalatamin rayuwa sai su tsaneni a kan me? Mene ne laifina a ciki tunda ba ni na kai kainaba?.

A taƙaice dai wata biyun da aka saka ta riskemu, a ka soma shirin biki nan da sati guda. Ni dai na ce ba abin da zan yi illa kawai walima itama dan Abbas ya takuramin ne shida Rabi'a wai ba za ayi biki lami ba. Ku jifa.

Satin da ya zagayo ya kasance satin sunan ƙanwata da ta haihu ƴan biyu duka maza ku ji kyautar Allah. Rabar ɗaurin auren ranar sunan ban kuma fasa zuwarmata ba tun da ita ba halin zuwa, ina san ƙanwata sosai fiye da zato. Mun yi kukan rabuwa da juna da ita, tana jin kamar ta biyoni taga inda zan zauna amma ba hali, nima kuma da man na yi alƙawarin ba zan bari ta taɓa sani ba dan na yanke alaƙata da duka ahlina.

Wani abin da ya ɗan sa na ji raɗaɗin zuciyata ta ragu shi ne kaiwa azzalumi katin ɗaurin aurena wanda ni da Rabi'a muka lalubo adireshinsa mu ka je.

Bayan na ba shi na shiga gaya masa kalaman da suka zo bakina.
"Ina fata za ka cigaba da rayuwa cikin azabtacciyar ƙonar rai, in sha Allahu abin da kamin sai anmaka fiye da tunani ,in kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu haɗu ,kuma rama cuta ga macuci ibadane na san Allah sai ya sakamin haƙƙina ba zai taɓa barinka ba wallahi." Ina gama faɗa masa na fice daga ɗakin na sa ,da yake gidansa ne shi kaɗai na iyayensa na nesa da shi kaɗan.

Bikina da wata biyu ,bayan tarewata gidan Abbas masoyina na sake riskar wani babban tashin hankalin abin da ya girgiza ƙwaƙwalwatana kasa samun sukuni. Ranar da na wayi gari gani ga gawar masoyina abin ƙaunata Abbas. Hatsari suka yi, mai tuƙa motar da Musbahu suka ji rauni sosai, amma da yake Allah mai ikone ko ƙwarzane babu jikin Abbas lokacinsa ya yi daga ranar ba zai sake rayuwaba shi kaɗaine ya mutu cikinsu. Na kan tuna kalamansa gareni.
"Ke ɗin ta dabance Khausar,ina miki san da ban taɓa yiwa wata ƴa mace ba, duk da kasancewar na sha gwagwarmaya kan so, na so wata kafin ke amma ban san ba santanake ba sai da na sameki, ta azabtar da zuciyata Khausar ke kuma kin kyautata rayata da ruwan sanyi. Samunki gareni sai naji inama tun farko ban santa ba,dama tun farko dake na fara haɗuwa,dama tun farko ban ji santa cikin zuciyata ba. Ina tsananin ƙaunarki Khausar ki soni ko da da ƙwayar zarrane ni kuma znn riritaki ,zan saka ki farin ciki fiye da nawa, ki soni ki ƙaunace ni ko da bayan raina ne."
A she daman tafiya zai yi ya barni. Ba zan taɓa samun miji masoyi irin Abbas ba wanne ne dalilin da yasa na kasa ƙauracewa gidansa, nake zaune ciki duk kuwa da cewa ya zomin a raban tumulin takabata. Ina zaune da ɗan uwansa Musbahu wanda Alhaji Jibril mahaifinsu ya sa ya dawo gidan da zama acewarsa ba zan zauna ni kaɗai ba, tunda naƙi amincewa na dawo kusa da su. Cikinsa nake rayuwa har kawo i yanzu, idan na tuna da mijina abin alfaharina sai na ji inama nima na mutu na bishi ko na sami salama, na kanji badan kashe kai kisan kaine ba da na kashe kaina sai dai na san idan na yi hakan to ni ɗin ƴar wutace sai kawai na rungumi sunayen Allah maɗaukakin sarki.
"Aunty har yanzu baki koma ga su Ummaba, me yasa ba za ki neme su ba?" Hajara ta watsa mata tambayar.

"A a Hajara tun barowata daga unguwar zuwa gidan Abbas na cire rayuwata daga can na ɗakko komai nawa na taho da shi nan, na kan tambayi Rabi'a a waya ya su ke ,ta cemin kowa lafiya. Har kawo lokacin da ta yi aure wanda banje bikinba saboda kar na shiga unguwar, Abbas ya matsamin sosai a kan naje ganin inta kuka duk sanda ya yi maganar sai kawai ya zuba min ido bai kuma cemin komai a kan rayuwar ba.Duk abin da zai haɗani da ƙanwata ahalina to bana yarda na raɓeshi. Musbahu shine ɗan uwana iyayensa su ne iyayena a halin yanzu. Ta ƙarashe cikin wani irin kuka.
Suma kukan su ke yi, Musbahu, Hajara kuwa hawaye shaɓe-shaɓe kan fuskokinsu.
"Wannan shi ne mafi munin kuskure da mafiya yawan ɗaukacin mutane ke yi a rayuwarsu ,sun manta Allah ke yin komai ga kowa,in ya soma sai ya tashi duniyar lokaci guda kuma babu mai cemasa dan me? Abin da suka gaza fahimta shi ne komai nada lokacinsa. Iyaye kan aikata kura-kurai na rashin yadda su ke gaza fahimtar ƙaddarar ƴaƴansu, sukan manta amanace garesu kuma ƴaƴa kiwo ne wajensu, sukan manta da cewa duk yadda mutum yake tara yake bai cika goma ba, sukan manata da kyakkyawar ƙaddara da mummuna wacca kowanne bawa ke da su. Lallai ya kamata su tausayawa ƴaƴansu fiye da kansu,ya kamata su ƙaunacesu fiye da kansu, ya kamata su ja su ajiki fiye da yadda akuya ke lashe ɗanta idan ta haifeshi." Likita ya katse musu sautin kukansu ta hanyar furucin, tun soma labarinta ya ke tsaye wajen ya na jinsu.

Aunty ta share hawayen saman fuskarta tana mai kallon Hajara ka na ta ce,
"Tun farkon bamu labarinki zuwa tsakiyarsa na gano wasu kura-kurai na ki da kika tafka. Na farko kin sami masoyin ƙwarai amma sai kika wulaƙantashi kika biyewa san zuciya da abin da ba za ta samu ba. Na biyu Allah ya kawo miki mijin auren lokacin da kike buƙata amma sai kika maida kyautar da Allah ya miki,kika wofantar da ita, baki yi anfani da lokacin da Ubangiji ya ara miki ba har ya ƙure miki, kin manta da cewa idan hannun agogo ya wuce baya taɓa dawowa baya ya tafi kenan har abada."

Cikin kuka Hajara ta soma faɗin,...
*LOKACI NE*
(Gajeran labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma shida

Cikin kuka Hajara ta soma faɗin,
"Tabbas na aikata babban kuskure,na yi wasa da damata ,lokacina ya tafi ba shakka ba zai taɓa dawowa ba Aunty , na yi da nasani matuƙa jin labarinki ya sakani jin cewa ni ɗin cikakkiyar mai laifi ce."

"Ƙalubalen dake cikin rayuwarki da tawa akwai banbanci masu yawa." Ta kuma faɗa cikin kuka.

A hankali Aunty ta janyota zuwa jikinta tare da rungumeta tana shafa bayanta a hankali. Lokaci guda kuma suka fashe da wani irin kuka ,duk yadda Likita ya so tsaida su hakan ya gagara har sai da dan kansu suka tsagaita.

Musbahu kuwa wani babban fami a ka masa cikin zuciyarsa na ɗan uwansa abin ƙaunarsa. Su biyu ne kaɗai wajen iyayensu Abbas na masa so fiye da yadda yake san kansa, duk abin da yake so shi zai masa muddin bai kaucewa shari'aba. Hannu ya saka ya na mai share hawayen saman fuskarsa tare da ficewa daga ɗakin. Shi ma Likita ficewa ya yi, a ka bar su Aunty su biyu, su na kuma jinjinawa tasu irin rayuwar.

"Tabbas Aunty malam mugune, kuma in sha Allahu sai yaga wulaƙancin rayuwa." Hajara ta ce.

Hannu Aunty ta saka ta toshe mata baki gami da girgiza kai ka na ta ce,
"A a Hajara ,kibar zancen ba na san tuna baya ko kaɗan,wanda ya yi da kyau zaiga da kyau ai." Daga haka suka ja bakinsu suka garƙame shi.

Kwanansu biyu a asibitin bayan faruwar wannan lamari a ka sallamesu suka koma gida.Jikin Hajara ya yi sauƙi sosai ta warware. Bayan sun koma gida Musbahu ya sanar da mahaifiyansa abin da ke faruwa na daga labarin Hajara da Aunty Khausar, sosai suka tausaya musu. Mahaifinsa kuwa ca ya yi su shirya za sukai ziyara wajen mahaifiyar Hajara.

Kwana ɗaya da fitowarsu suka shirya zuwa gidansu Hajara.

Mama na zaune gaban murhu tana iza wuta ta ji sallama da muryar ɗiyarta. Cikin sauri ta miƙe tsaye tana mai ƙurawa ƙofar shigowa tsakar gidan kallo, idanuwanta suka ɗakko mata hotan ƴarta tsaye ta saki baki galala tana mai bin ta da kallo.

Hajara ta ƙarasa da sauri tana mai shigewa jikin Mama ka na ta ce,
"Mamata."
Sai a sannan Mama ta zube hannayenta biyu saman bayan Hajara tana mai na nuƙata jikinta kamar ance za a ƙwace mata ita, gaba ɗaya ta kasa magana da ƙyar ta iya furta,
"Hajara ke ce? Ina kika je kika barni ni kaɗai? Daman kina raye?" Ta shiga jeromata tambayoyi.

"Ina raye Mamana, ki gafarceni dan Allah ,na dawo gareki har gaban a bada." Hajara ta ce cikin sigar kuka.
Sannu-sannu suka sami waje suka zauna bayan ta shimfiɗa musu tabarma, bayan sun gaisane a ka shiga tattaunawa kan batun da ya kawo su da kuma sake bawa Mama haƙuri kan abin da Hajaran ta aikata.

Mama ta yi murna sosai jin hannun da ƴarta ta faɗa, hannu na gari. tana kuka ta soma basu labarin bayan tafiyar Hajara, da irin cin kashin da mashaye ke mata ta soma da faɗin,
"Na zalinci kaina da yawa, ina tunanin idan na aurar da ƴata ga koma wane ne zan sami salamar abin da mutane ke faɗi,sam na gaza anfani da ilimina wanda Allah ya bani sai ga shi na ɗakkowa kaina ruwan dafa kaina. Ya shaidamin muddin baki dawo ba to ni ce amaryar tasa a madadin ki ."

Gaba ɗaya sun tsorata wanda ya saka su Aunty roƙan Mama a kan ta biyosu su koma can da zama yadda bama zai dawo ba balle ya aikata abin da ya keso. Da ƙyar ta amince bisa saka bakin mahaifin Musbahu.

Nan suka tattara ƴan komatsansu wanda ba zasu ɗauka ba Mama ta shiga maƙota tana musu sallama tana bawa masu so. Duk da rashin san da suke musu amma sabo turken wawa sai da suka ji ba daɗin rabuwa. Har godan da Mama take aiki suka je ,matar ta ji badaɗin rabuwa, ta kuma taya Mama murna sosai.

Satin Mama guda da komawa Sharaɗa cikin gidan Aunty wanda ta basu ɗan matsakaicin gidane zaman mutum ɗaya wanda duk ya zo cikin raban gadon Abbas da a ka yi. Nan suka shirya zuwa Jama'are wajen dangin Mama dan itama ta yi nadanar barowarta daga can,tana jin ya kamata ta koma ga ahlinta.
A na i gobe tafiyarne Hajara taga abin da ya tsuma zuciyarta. Aunty na ɗakin Abbas wanda in tana san keɓewa take shiga dan rage kewarsa Hajara ta shiga tana ta sallama Aunty ta yi nisa da tunani ba ta ji ba. Fizge hoton da ke hannunta da Hajara ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi. Ido huɗu suka yi da Hajara dake tsaye ta sandare saboda ganin fuskar wanda ke jikin hotan.
"Ab-b-bas" bakinta ya soma furtawa cikin tawar murya.
"Kin san shi ne?" Aunty ta jefa mata tambayar.
"Shi ne, shi ne wallahi Aunty shi ne mutumin da nake baki labarinsa wanda ya ƙaunace ne har na kasa ganewa, wallahi shi ne tabbas Abbas ne dan na gane kamanninsa ba."
Ta faɗa cikin muryar kuka.
"Allah sarki daman ke ce wacca ya ke bani labari ,wacca kika wahalar da shi." Sai kuka ya kuma kufce mata.
"Abbas ka yafemin ,na zalunce ka na zalunci kaina,na maka abin da bai kamata ba,tabbas na canci kowanne irin hukunci." Ta durƙushe a wajen tare da wani irin kuka. A hankali Aunty ta zame hotan daga hannunta cikin murmusuwa ta ce,
"Ya jima da yafe miki Hajara,Addu'arki kawai yake buƙata a yanzu."
Kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe da nufar ƙofa za ta fice daga ɗakin.
"Ina za ki?" Aunty ta tambaya ba ta, ba ta damar magana ba ta ɗora da,
"Dawo ki zauna mu yi hira." Ba musu ta dawo ta zauna kusa da ita.
"Amma na kasa gane yadda baki iya gane Musbahu ba ta yadda su ke kama,ko da ya ke ba san shi kike yi ba wannan kaɗai ya sa dalilin da zai saka ki kasa gane ɗan uwansa. Amma makwafin idanuwanki ya gaza bawa ƙwaƙwakwarki damar da za ki iya haddace kamannin Abbas sai ga shi Allah ya haɗaki da ɗan uwansa da matarsa suka ƙaunace ki fiye da zato. Kada ki kuma bari dama ta riƙa kufce miki."
Ita dai shiru ta yi ,ba ta iya cewa komai ba. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi.

Washe gari, tun Asuba su ke shirin tafiya Jama'are gaba ɗayansu; Alhaji Jibril, Amma mahaifiyar Musbahu, Aunty ,Musbahu da Hajara.
Wajen bakwai suka ɗau hanya, Allah ya sauke su lafiya ,kuma Mama ba ta sha wahalar gane gidanba tunda fitaccen gida ne sosai taga sauye-sauye cikin garin.
Tarɓa a ka musu ta mutunci da karamci,bayan ƴan gaishe-gaishe suka gabatar da kansu ga ƙanin mahaifin Mama . Murna wajensa ba a magana jin ɗiyarsa na raye harta dawo ga kuma jika ya samu. Nan ya sa a masa shela a ka tara masa ahlin. Duk wanda ya ganta sai dai kaga ya na washe baki ya na murna. Mama ta sami labarin rasuwar mahaifinta ta yi kuka sosai jin yadda da ita a ransa ya mutu.
Mahaifiyar baban Hajara ta shiga ruru akan a kaita wajen Mama ta ganta. Ganin ta matsanta ya sa a ka zo aka sanar da Mama halin da take ciki. Har gidan su Mama suka je yadda ta ganta sai da ta mata ƙwalla, tana kwance sai dai a juyata ga baki amma ba halin motsa jiki, sakamakon zamewar sa ta yi a banɗaki wajen fitowa sai ta kamu da matsalar shanyewar jiki.Duk ta rame ta yi wata iriya da ita kamar ba ita ba. Ganin Mama ya sakata fashewa da kuka tana mai neman gafararta, ko da Mama ta ce mata ga jikartanan sosai ta kuma birkicewa kuka ta ke aosai tana neman afuwar Mama.
"Bakomai ,ki daina neman afuwata ki uwa kike a gareni." Mama ta ce.
Su Hajara kam duk kuka tausayawa su je mata. Alhaji Jibril ya ce zai ɗauki ɗawainiyar nema mata magani in sha Allahu. Sun ji daɗi sosai sun yi farin ciki.

Satinsu guda a Jama'are suka juyo zuwa Kano harda Mama Rabi kakar Hajara da za a nemawa magani,duk

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On LOKACI NE
avatar
khamilu

1 year ago

Reply

Mashallah

Please Login or Register in order to submit comment