Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Su na tura ƙofar suka ga wayam babu alamunta, Aunty kam ta fi kowa shiga cikin tashin hankali.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)
Mai_ƙosai

FCWA

Goma ɗaya.
Da sauri Likitan ya ƙarasa jikin gadan nata ya shiga duba ya nayin yadda aka cire robar ruwan.
"Ba ta yi nisa ba, in mu ka yi sa'a za mu iya cimmata." Likitan ya faɗa.
Cikin sauri suka fice daga ɗakin, kai tsaye harabar asibitin suka nufa, har Musbahu na ƙoƙarin ficewa daga cikin asibitin zuwa waje ya hangota jikin babbar ƙofar fita tana rakuɓe-rakuɓe da alama hanyar fita ta ke nema ta fice yadda ba wanda zai ganta. "Me ya sa za ki aikata haka?" Ta ji saukar aradun muryarsa na jefo mata tambayar da ya yi a bazata lokaci guda maganaɗisun kunnunwanta suka naɗo mata sautin. Bai ba ta damar magana ba ya ɗaura da faɗin,
"Kin san cikin tsantsar adadin tashin hankalin da ki ka jefamu? Me ya sa ? A kan me?"
Ya juya ya na mai ƙwalawa su Aunty kira, da sauri suka ƙaraso wajen. Hannunta kawai Aunty ta kama ta shiga janta zuwa ciki. Har sai da ta direta kan gado cikin ɓacin rai ta soma faɗin,
"Kin san adadin tashin hankalin da ki ka jefamu ciki? ? Ina za ki je? Mece ce ribarki a fitar idan kin yi?"
Cikin sautin kuka Hajara ta ce,
"Dan Allah na roƙeƙi ki yi haƙuri, amma ni na fison na tafi yadda bazan taɓa ɗora muku nauyi na ba, ba na so Mamana ta same ni dan muddin ina garin nan to lallai ba shakka za ta samo ni, ni kuma ba naso na aure mashaye." ta ƙarasa cike da sakin wani marayan kuka.
"To sai me idan an nemo ki? Ba dai auren mashayi ne bakya so ba? To ni nan zan tsaya miki har sai inda ƙarfina ya ƙare, amma tafiyarki ba za ta sakawa zuƙatanmu salama ba, tafiyarki mugun laifine wanda ba zai taɓa goguwa a wajenmu ba, ki na ganin kin fi kowa shiga cikin matsalar rayuwa? Saboda ba ki saurari rayuwar wasu ba ne. Rayuwata akwai kamanceceniya da taki sai dai akwai banbanci mai tarin yawa acikinta, ki godewa Allah baki ɗanɗani zafi mafi zafi acikin rayuwarki ba, kin san irin wahalhalun da na sha? Kin san irin gwagwarmayar da na sha a tawa rayuwar? Kin san irin faɗi-ta-shin da na dinga yi? Ban da ra'ayin sanar da kowa tawa rayuwar amma saboda ke yau zan fayyace miki wani sirri da na jima ina ɓoyeshi cikin zuciyata, ƙaddarata da taki akwai kamanceceniya amma ke taki akwai wasarereniya a cikinta, ki buɗe kunnenki da kyau ki saurari abin da zan sanar miki a yanzu." Ta ɗan numfasa tare da goge hawayen da suka soma ziraro mata kafin ta ɗora da faɗin,
"Suna na KHAUSAR AUWAL MAHMUD, mace mai kimanin shekaru talatin da ɗaya a yanzu.Mahifiyata Jamila Usman muna ce mata Umma. Na ta so gaban iyayena duka biyun cikin so da ƙololuwar kulawa garesu. Mu biyune kacal wajen iyayenmu daga ni sai ƙanwata SALIMA mai kimanin shekara ashirin da ɗaya a yanzu wanda na bata tazarar shekaru goma cif kafin ta zo duniyar.
Zaune muke cikin garin Kano,unguwar Sharaɗa.Cikin unguwa mai yalwar jama'a sosai.
Na yi firamari na a makarantar kuɗi duk da dai kuɗin ba wai na kuzo a gani ba ne, bamu da wata tazara mai nisa tsakanin gidanmu da makarantar a ƙafa nake tafiya na ke dawowa. A cikintana yi sikandire na tun daga aji uku zuwa aji shida. Lokacin da na kammala karatun sikandire na ƙanwatana kan ganganiyar karatunta, lokacin ne kowa hankalinsa ya dawo kaina dangi uwa da na uba kowa ya saka min na mujiyarsa wato ido, kacokam suka maida hankalinsukaina akan ganin na yi aure ni kam har ga Allah na fi son na ci gaba da karatuna. Sa'ilin da na jewa da iyayena maganar sai suka nuna sam ba suso aure shi ne ya fi dacewa da ni a lokacin.
Ina son karatu sosai amma jin furucinsu sai kawai na haƙura na fawwalawa Allah komai, sai na ci gaba da zuwa makarantar Islamiyya tun da har lokacin ba mu yi sauka ba, a lokacin ba zan haura shekara goma sha takwas da ƴan watanni ba.
Na mayar da hankali sosai wajen karatun Islamiyyata dan har hadda na soma yi tunda na sami isasshen lokaci. Ba inda na ke fita daga makaranta sai gida sai dai idan aikena Umma ta yi shi ma sai ta kama ,amma bayan wannan ni ba za ka taɓa tsinta ta a wani wajen ba.
Lokacin da muna aji shida a sikandire sautari mu kan yi zancen samari kowa za ka ji ya na magana akan abu biyu ne; karatu da aure ,ni dai har ga Allah na fi son karatu dan ba abin da ke raina illa na ga na yi karatu mai zurfi, shiyasa ni ko samari ba sa gabana, duk da cewa ma ni ba wanda ya taɓa tarar gabana da maganar so ko ƙauna.
Kuma hakan bai taɓa damuna ba balle na ji wani abu a raina, ko na ji wai cewa ni bani da farin jinin samari sam hakan bai ɗa-ɗarani da ƙasa.
Har a ka ci shekara da wata biyar da kammala karatuna ba wanda na taɓa cin karo da shi da sunan ya na so na, maganganu suka soma yawa daga ɓangarori biyu na dangi na wato na uwa da na uba, duk da Baba ya kan ce min shi ma ya ga ji da gani na gida ya kamatana fito da miji na yi aure maganganunsu na cewar ya zuba min ido ya ƙi aurar da ni sai suka ƙara tunzura Baba akan lallai na fidda miji na yi aure ko ya fidda min, kusan sati ya na min faɗa a kan wai ina korar samari shiyasa har yau ba wanda ya zo neman aurena. Karfa kuce shekaruna sun wani ja a lokacin tunda ban fi sha tara zuwa ashirin ba. Ni dai haƙuri na ke ba su sai kalma ɗaya da kullum taƙi barin baki na wato (Lokaci ne) ai daman komai lokaci ne haka zalika ni ma auren nawa lokaci ne kuma zai zo, kamar yadda idan lokacin mutuwarka ya yi za ka tafi ba tare da ƙarin ko da sakan ɗaya ba.
Ganin ba sarki sai Allah ya saka Babanmu yankomin takardar zana jarrabawar JAMB, bayan ta fito na samu adadin makin da mai neman karantar ɓangaren shari'a ya ke samu daman ina son harkar shari'a na ji daɗi sosai na sami gurbin karatu a makarantar kwalejin F.C.E da ke garin Kano. Na mayar da hankali na sosai kan karatun. Wata ƙudurar Allah kuma duk wani abin da zai haɗa ni da namiji to ɓangaren karatu ne ko mutunci shi ma iya makaranta ne amma ba wanda ya taɓa tarata da sunan soyayya ko alaƙa mai zurfi. Ni kuma daman ban wani sa a ka ba, hakan sai na ji na fison kaɗaicinma ko babu komai na samu na yi karatuna sosai yadda Baba ba zai ce a ajjiye karatun ayi auren ba. Bari na gajarce muku rayuwata ta makarantar saboda ba wani abu ne ya faru cikin rayuwarba in banda ƙalubale kan karatun wanda kusan kowa ya kan sami kansa cikinsa sai dai na wani ya fi wani, wani daga ɓangaren malamai ne wani kuma wajen karatun ne inma ta fahimtarsa ko aka sin haka , ko kuma ta ɓangaren kuɗi.Duk da iyayena su na ganin kamar zan fi samun masu neman aurena a can, sai dai har na kammala babu wanda ya tunkareni da hakan ko da cikin makaranta ko waje.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)
Mai_ƙosai
FCWA

Goma biyu.
Bayan 'yan watanni da kammalawata wata rana ina zaune mahaifiyata ta tasa ni a gaba kan zamuje wani gurin wani malami dan nemamin taimako, wataƙila ko Allah zai saka mijin aurena ya zo, dan ta lura kamar ko ina da matsala ne ko kuma dai an saka min hannu, dalilin ganin hakan da take yi bai wuce nasaba da ganin ƙanwata ta sami mijin aure ba wanda auren ya rage ƴan watanni ƙalilan.
Banso jin furucinta ba koba komai ai komai nufine na Allah, kuma a kullum ba na cire rai daga saukar rahmarsa izuwa gareni, wataƙila lokaci na ne bai yi ba shiyasa mijin nawa bai zo ba amma sukam sun gaza fahimtar hakan. Ina ji ina gani Umma ta tasa ni gaba zuwa wajen malamin ni kuma ba zan taɓa ƙetare umarninta ba. ko da mu ka je na saki jiki sosai saboda na ga baimin kala da wanda ya kaucewa hanya ba dalilina kuwa na faɗin haka shi ne; yadda ya ke ta kwantar mana da hankali akan komai lokaci ne kuma zai zo, sannan ya ɗorani kan wasu addu'o'i ya kuma bani tofi na dawo gida ina yi, ya tabbatar mana da ko da ace da shaiɗanu ma in sha Allahi komai zaizo da sauƙi tunda mun miƙa lamuranmu ga Allah buwayi gagara misali. Wata guda da farawa muka kuma komawa wajensa nan ya kuma bani turaruka ya ce na dinga hayaƙi da su, ya kuma ƙaramin da wasu addu'o'in. Babu fashi kullum sai na aikata duk yadda ya ce dan kuwa Ummace za ta tasa ni gaba sai na yi sai abin ni ma ya zame min jiki ko da ta sakani ko ba ta sakani ba to zan yi. Na shafe wajen wata uku ina amfani da su kuma har lokacin babu wani wanda ya zo ko da ƙofar gidanmu ne da sunan soyayya da ni balle ga aure. Ni kuma a lokacin sai na riƙa jin gabana na faɗuwa na fara jin na fara yadda da maganganun mutane na cewar lallai aljanin dare ne ya aurene, hankalina bai sake ta shi ba sai sa'ad da na tsinci kaina a gida ni kaɗai bayan auren ƙanwata da a ka yi gidan sai ya zamana daga ni sai Umma, Baba kuwa daman ya na wajen aiki sai dare ya ke dawowa, na shiga cikin kaɗaici sosai. Idan na je gidan ƙanwata kuwa na dawo da tunanin ni ma naga na wayi gari na yi aure na ke kwana cikin zuciyata, wannan dalilin ya saka sai na ƙauracewa gidan nata gaba ɗaya in dai ba Umma ce ta aiki ni ba ,shi ma dan ba yadda zan yi ne amma da da hali ba zan je ba.
Wani abun takaici, al'ajabi da mamaki da ya faru gareni wanda ba zan taɓa mantawa da shi ba, lokacin na yi kuka iya kuka, ban taɓa zatan hakan za ta kasance da ni ba kun san mene ne?
Ta katse musu zaren labarin ta hanyar jefa musu tambaya,ba kuma ta basu damar amsawa ba ta ɗora da faɗin, wanda su ma ba su damu ba daman gyaɗa kai kawai suka yi.
"Na shafe shekara uku da kammala karatuna har na soma koyarwa a Islamiyyarmu wacca ita ma mun jima da saukewa. Kwatsam wata rana bayan na dawo daga makaranta ina dab da shiga gida bayan na karyo kwanar shiga layinmu na tsinkayo muryar wani matashin saurayi na faɗin,
"Ga tanan ta dawo."
Wani daga gefensa ya jefo masa tambayar , "Wace ce?" Na kuma tsinakayo muryarsa na kuma furta,
"Ta rasa mijin aure ma na." ya ba shi amsar tare da sakin wata dariya.
"Ta rasa mijin aure kuma?" Ɗayan ya sake jefa masa tambaya.
Ya bushe da wata mahaukaciyar dariya tare da furta
"Caab! au wai kai da ba ka sa ni ba,gaskiya an barka a tasha ai wannan ina gaya maka kaf cikin layin ita ce kwantan-kwantai in ban yi ƙarya ba za ta kai shekara ashirin da da tara gaban iyayenta, kuma ka gantanan bata da niyyar aure, kai zance maka ma ba wanda ya nuna ta yi masa balle ya ce zai aureta. Shiyasa na ce maka ta rasa mijin aure."
Ɗayan ya ja numfashi kafin ya ce, "To kai ba saika aureta ba." ya jefa masa maganar a ba zata.
"Tuuf! " ya tofar da yawon bakinsa kafin ya furta,
"Allah ya kiyaye na aure wacca ta yi kwantai wallahi, ai ni bari ka ji yarinya shakaf zan aura sabuwa dalleliya wacca ba ta tsufa ba kamar irin ƴar shekara sha bakwai zuwa sha takwas, kai inma sha shida ce zan aura kai mai zai ha na ka aureta." Ya mayar da masa da tambayar kansa.
"Ah! haba kaima ka san faɗa kawai ka ke yi, me zan yi da ma shekaru ashirin da........" Ban tsaya jin ƙarashen zancen na su ba daman tsautsayi ne ya sa na tsaya ashe zanji mugun zance a kaina, na faɗa gida ina matse hawayen cikin idanuwa na, zuciyatana dakan lugude, mene ne laifina a ciki dan na kai waɗannan shekarun ban yi aure ba? Mene ne laifina a ciki dan na kai iyanzu ban sami mijin aure ba? Shin ni na kar zoman ko kuma rataya a ka bani? Na ga dai komai na rayuwa ɗan lokaci ne, kuma komai nufi ne na Ubangijin Sammai da Ƙassai. Ƙaddararta ce ai kamar yadda kowa ke da tasa ƙaddarar mai kyau ko mara kyau,to me yasa za su dinga jifana da waɗannan kamalan? Wane laifi na aikata musu da za su dinga mun zunɗe? Wane laifi na aikata musu da zai saka su tsaneni su riƙa nunan ƙyara? Na rushe da matsanancin kuka wanda har sai da ya ankarar da Umma hankalinta ya dawo kaina, ta soma tambayata lafiya? Me ya faru?.
Ina kuka na shiga faɗin, "Umma me ye laifina a kan hakan? Me yasa za su riƙa jifana da mummunar kalma mara daɗi kawai dan ban yi aure ba? Wane laifi na aikata haka?."
A zato na Umma za ta mara min baya, amma sai naga ta kalleni sheƙeƙe kafin daga bisani ta ce,
"To ai sai ki yi zuciya ki yi auren kinga sai ki samawa kanki sa'adar hakan." Ta fice daga ɗakin tana jan tsaki.
Ni kam kukana ya kuma tsananta lokacin da na ji furucinta. Me ya sa za ta ce haka alhalin ba ni na yi kaina ba?. Ranar a haka na ƙarasa yini na cikin kuka kaina in banda sarawa na ciwo ba abin da ya ke min. Cikin dare na ta shi na soma gabatar da sallah ina mai kai kukana izuwa wajen Ubangijin da baya barci balle gyangyaɗi. Kusan kwana na yi ina ibada ban san sanda barci ɓarawo ya kwasheni ba.
Kwana biyu ina cikin kaɗaici da jimamin abin da ya wakana gareni cikin raunanniyar zuciyata, sai na ke jin kamar na daina fita gaba ɗaya gudun sake tsinkayo makamantan kalmomin, sai na daina zuwa Islamiyyar. Amma da naga koba komai ai tana ɗebemin kewa sai na koma.
Cikin kwanaki uku da komawata sai na sami ƙawa duk da a girme na girmemata dan ba ta fi sa'ar ƙanwata ba, unguwarmu ɗaya sai dai muna da tazarar layi na gida. Zuwan da banyi ba kwana biyu shi ne aka miƙa mata ajina da na ke koyarwa da na dawo kuma a ka ce mu ci gaba da zama a tare. Na yi murna sosai, duk da ban wani cusa kaina wajenta ba amma ita haɗuwarmu da ita ta farko ta soma san shigewa jikina har Aunty ta ke cemin, ni ma ganin hakan sai kawai na bada kai jiki ya hau bori.
Cikin ƴan kwanaki ƙalilan muka zama abu ɗaya, duk da ni a cikin waɗannan kwanakin ina fama da matsananciyar damuwa, wacca har ya saka ta gane halin da na ke ciki dalilin kasa ɓoye damuwar tawa. Tuni ta soma tambayata gami da haɗin da ta ganni, tana roƙota haɗi da haɗani da girman Allah da na sanar da ita damuwata.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)
Mai_ƙosai
FCWA

Goma uku.
Muna zaune a aji, tana biyawa ɗalibai darasi. Ni kuma gefe guda na lula duniyar tunani wanda har ban san sa'ilin da ta ƙaraso kusa da ni ba har ta zauna, jin hannayenta kan lafaɗata ya sakani dawowa hayyacina har na sauƙe tagumin da na yi ina mai kallonta.
Da murmushi kan fuskarta ta soma faɗin,
"Na jima da sanin cewa kina cikin damuwa Aunty domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. Amma ina ta bibiyarki amma kin ƙi sanar da ni, nasan ba ni da damar da zan iya yaye miki damuwarki, amma na gamaki da girman zatin Allah ki sanar da ni ko na sami salamar ruhina, ban sa ni ba ko da akwai abin da zan iya taimaka miki da shi."
Sai na ji zuciyata ta karaya ta yi rauni idanuwana suka kawo ruwa, ban san lokacin da na shiga fayya ce mata abin da ke damuna ba.
Sai kawai naga tana hawaye, ina kuka itama sai ta rushe da kukan, ni ina kukan baƙin cikin halin da na tsinci kaina ita kuma tana kukan tausayawa rayuwata, mun ɗau tsawon lokaci mai yawa kafin na ji ta furta.
"Ki yi haƙuri Auntyna, komai lokaci ne idan ya zo babu mai sauya shi, in sha Allahu lokacinki ya kusa zuwa."
Ban tofa mata ba sai kawai gyaɗa kaina da na yi. Har aka tashi tana mai bani baki, ko da muka isa unguwarmu sai da ta rakani har gida kamar wata makauniya haka ta yi min jagora sannan itama ta wuce na su gidan.
Tun daga lokacin kuma kusan kullum sai ta zo gidanmu,ta kan kai kusan Azahar take tafiya shi ma dan zuwa makarantane wani sa'in ma da shirinta take tahowa sai mu wuce daga gidanmu.
Sosai take ƙoƙarin ganin san ta farantamin ta kuma saka ni cikjn farin ciki da walwala. Shaƙuwa mai tarin ƙarfi ta shiga tsakanimu sosai, sai kuma jama'a suka soma ƙoƙarin ganin sun rabamu wai itama za ta rasa mijin aure in tana tare da ni, amma kuma Allah bai nufa ba. Lokaci guda suna na ya rikiɗe daga Khausar zuwa Ta rasa mijin auren, ko da kwatancan gidanmu ka ke nema daka tambayi haka za a nuna maka.
Na ci gaba da rayuwa cikin wannan halin na ƙunci dan ma dai Rabi'a na ɗebe min kewa.
Amma in dai magana ce tsakanina da Umma to ba ta wuce ta tsuniyar gizo, koyaushe maganartana fidda miji na yi aure, ita ta gaji da ganina gabanta goɗai-goɗai da ni. Baba kuwa dai a yanzu ba ya ce min komai domin kuwa dare ne ke dawo da shi wani sa'inma sai tara na dare zai shigo ko goma, ni kam kafin ya dawo ma na yi barci ko da bai zo ba zan ƙirƙiri kayana. Cikin dare na tashi na yi sallolina na roƙi Allah a kan ya kawomin ɗauki.
Sakanni, awanni, kwanaki, satittuka, watanni na shuɗewa cikin abin da ba a tunani sai ga shi an shafe wata uku da raɗamin sunan da ba yankan rago. Abin har yabi jikina na saba da amsa sunan tun ina damuwa har na daina damuwa. Umma ta ɗakko mai Ruƙya ya min karatu wai ko dai dai aljanine ya aure ni mai taurin kai. Duk kuwa da cewa na sha magunguna amma shiru ka ke ji kamar anci shirwa. To shi ma hakance ta faru ba irin karatun da ba amin ba amma ko gezau ban yi ba, sai kawai ta tattara komai ta watsar amma kusan ko dayaushe sai ta jefo min maganar aure na fidda miji na yi aure.
Kwatsam a na haka wani malamin da muke koyarwa a Islamiyya wanda bai jima da zuwa ba dan baifi wata ɗaya da sati ba ya nuna ya na sona kuma so na aure. Na so ƙin amincewa da shi amma da na tuna wataƙila Allah majiɓancin lamuranne ya turo min shi a bisa amsa addu'ata da ya yi sai na amince masa gudun kada na zama butulu ga Ubangijin talikai.
Ya zo har gidanmu ya nemi izinin Baba kuma ya yarje masa. Wajen iyayena kuwa farin ciki cikin zuƙatansukamar su zuba ruwa a ƙasa su sha.
Soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninmu Kullum zai kirani a waya sau babu adadi tun ba na biye masa har na fara sabawa da kiran nasa. Rabi'a kam ba ƙaramin farin ciki ta yi ba mara misaltuwa ganin na sami mijin aure. Takan ce min,
"Aunty ni na sani ko wanne abu da lokacinsa. Kamar yadda Mutuwa, Rayuwa da Haihuwa su ke da lokacinsu, nasan koman daran daɗewa lokacin zai zo kuma ga shi Allah ya kawo shi. Daman an ce mai haƙuri ya kan dafa dutse harma ya sha romansa."
Ni kam murmushi ne kawai nawa, na kan yi mata addu'ar Allah ya kawo mata miji da wuri kada ta zauna irin zamana a gaban iyayenta.
Ƙanwata ta min murna sosai da sosai, duk da fushi take da ni a kan na yi wata biyar ba na zuwa gidanta, da ƙyar muka sasanta da ita. Ni kam bana son zuwa ne saboda gudun sake faɗuwar gabana ,kuma koba komai ni fa yayarta ce ai bai kyautu na dinga yawaita kai mata ziyara ba.
Wata shida bai rufa ba da haɗuwarmu ya kawo kuɗin aurena, Baba ya yi bincike iya bincike bai ci karo da wata mummunar shaida a kansa, sai hankalinmu ya kwanta fiye da zato. Shekara guda a ka saka aurenmu da shi ,ranar yini na yi ina tasbihi ina tsarkake Ubangijin talikai.

Wata rana muna zaune a aji muna hira da Rabi'a,duk da kwanakin ba su wani ja da yawa ba bayan saka ranar da aka yi. Na jiyo wani mugun fitsari ya ciyo ni har marata sai da ta murɗa. Na kalleta ina ɗan cize laɓɓa tare da ya tsina baki.

"Ya ya dai? Me ya faru Aunty? Ta watsomin tambayoyin.

Na kuma ya tsina baki sai ka ce al'adata ka na na ce,
"Ke dai bari ɗan zawo ne ya sako saƙonsa."

Ta yi ƴar dariya dan ta fahimce zance na sannan ta ce,
"To ai sai ki je ki kai saƙon. Amma kya bari yaran su dawo ko?"
Na gyaɗa mata kaina.
Da yake yaran in su na waje bama shiga bayin har sai an dawo da su daga sallar la'asar ɗin da ake fita dan mu samu mu sake,duk da cewa banɗakin malamai daban da na ɗalibai. A she a wannan ranar a wannan makaranta wani gagarumin bujimin tsautsayi ke kirana ban sani ba, wata ƙaddara za ta kuma gifawa rayuwata shiyasa fitsari ya yi halinsa har na kasa riƙeshi balle in na koma gida na amayar da shi.



*LOKACI NE*
(Gajeran labari)

Mai_ƙosai)

FCWA

Gima huɗu

Na barta cikin ajin bayan dawowar yaran ,ita kuma ta kula da su,ka na na wuce zuwa idda nufi na.
"A she daman wanda ka ke so ka yarda da shi zai iya cin amanarka.?" Ta je fa musu tambayar cikin kuka.

"Fiye da zato Aunty wallahi." Hajara ta bata amsa.

Ba ta sake wani furucinba ta ɗora da faɗin,
"A she lokacin da na zagaya bayi a kan idanuwan malam ne wanda muke soyayya da shi har aka saka mana rana. Na buɗe ƙofar bayin bayan na kammala abin da ya kawo ni da nufin fitowa na koma ajin sai kawai mu ka yi ido huɗu da shi tsaye ya harɗa hannayensa biyu saman ƙirjinsa. Ba tare da na yi magana ya sakar min murmushi mai wuyar fassaruwa. Ina ƙoƙarin raɓashi na wuce ya saka hannunsa ɗaya ya taroni, na haɗe fuska da nufin magana sai kawai ji na yi na shaƙi wani abu ,ban fi mintuna ba na sulale jikinsa idanuwa na a buɗe ina kallonsa amma ba zan iya cewa komai ba, dan komai nawa ya daina motsi ya saki. Ina ji ina gani ta ketamin haddina ,ba ni da ƙarfin da zan iya hanashi, ƙarshe sai buɗe idanuwa na yi na ganni kwance gadan asibiti.

Na yinƙura zan tashi na ji wani zafi ya ratsa ilahirin ƙasana fiye da tunanin mai tunani,fiye da yadda dalma ke mannewa jikin mutum.

"Sannu Aunty kin farka?" Na jiyo muryar Rabi'a na jefomin tambayar.

Da ido nake bin ta da kallo,sai a lokacin kuma naji kaina na juyawa dai-dai lokacin ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomin abin da ya faru da ni idanuwana suka soma haskomin komai tamkar lokacin abin ke faruwa. Hawaye masu zafi suka soma malalowa kan kumatuna, na fashe da wani matsanancin kuka ina mai kifa kaina jikin filon dake

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

1 Comments On LOKACI NE
avatar
khamilu

1 year ago

Reply

Mashallah

Please Login or Register in order to submit comment