Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ɗan tazara ma tsakaninmu da ita amma kusan kullum sai ta zo in da muke ta zageni tatas, da ya ke mahaifinki ɗan tafiye-tafiye ne duk san da baya gari to za ta zo gareni zagi ta uwa ta uba kuma kullum sabon zagi ne zai riske ni. Ban san me na tsare mata ba, aikin wahala kam duk yadda za ta so ta saka ni sai ta ƙaƙalo shi a matsayintana uwa gareni zan yi komai ta saka ni in dai bai kauce hanya ba. Idan mahaifinki na gari har wata ƙirƙirar kulawa ta ke yi min, har da aiken abinci tana yimin, ni kam ba na ci gaskiya. Yau da daɗi gobe babu haka na ke rayuwa da ita, ban taɓa jin na tsaneta ba ko da sau ɗaya ne dalilin soyayyar mahaifinki da ke cikin raina. Kamar yadda na taɓa gaya miki mu ƴan Jama'are ne cikin garin, duk in da ki ka je ki ka ce"Babban gida" ba wanda bai san shi ba. Na sami sauƙin takurarta dalilin samuwar ciki a jikina, duk da tana iƙirarin cewa cikin ba na mahaifinki ba ne, abin ya ruɗar da mu sosai ko mahaifinki sai da ya girgiza, har sai da ya mata iƙirarin cewar a kan cikin zai iya kaita koto Alƙali ya ƙwato masa haƙƙin sheganta masa ɗa ko ƴa da ta yi. Wannan sai ya sama mana sa'ada sai ma ta ɗauke ƙafa gaba ɗaya. Mahaifinsa kullum ya kan nusarshi ganin ya ƙauracewa gidansu gaba ɗaya, ya kan kuma ƙara nuna masa mahimmancin mahaifiya da haƙuri. Cikin da ke jikina ya kai wata bakwai zuwa takwas a lokacin kuma sai wata ƙaddara ta faɗo mini, mahaifinki ya mutu bayan dogowar jinyar da ya sha duk da cewa ma ya warke kuma a lokacin ba za ki taɓa ba kawo masa mutuwa ba amma Allah sarki bowaye gagara misali sai ya amshi kayansa. Allah sarki mutuwa mai raba ɗa da mahaifi, mai raba masoyi da masoyi na yi kuka iya kuka dan na san na rasa masoyi kuma uban ɗan da zan haifa ko ƴa. Bayan rasuwarsa da mako biyu mahaifiyarsa ta ta sa ni gaba zagi, ƙyara ba a maganarsu kin san a lokacin ban yi arba'in ba ban kuma haihuwa ba balle ace na fita daga takaba wannan ya sa ina gidansa, an so a ba ni wata ƙanwar kakatana ce a'a ba na so na hutassheta. Duk abin da ta ke ba wanda ya sa ni, ni ma kuma ban taɓa gayawa kowa ba sai san da mahaifinsa ya zo duba ni ba ta san ya na nan ba ta shigo ko sallama babu ta soma tijarart, lokacin ya ji ya kuma taka mata burki amma wallahi duk da hakan ba ta daina ba. ko da ya sanar da mahaifina yana raye amma mahaifiyata ba ta raye bai ji daɗi ba amma sai ya dake ya riƙa ba ni haƙuri. Sati biyu ina shan baƙar wuya wajenta dan kamar tarewa ma ta yi a gidana to a cikin awa ashirin da huɗu a wanni ƙalilan ne ba ta yi, kawai sai na ji kawai na bar mata garin shi ne zai fi. Wannan ya sa na tattaro komatsaina na taho nan ba tare da sanin ahalina ba, ba kuma tare da sanin wa na sa ni ba, da wa zan haɗu, na zauna ba da jimawa ba na haifeki na saka miki suna ba tare da yankan rago ba, na raineki da akwai da babu. Abu ɗaya na ke so da ke shi ne ki zama mai haƙuri a cikin kowanne irin hali, domin kuwa sai da haƙuri rayuwar ta ke kaiwa ga ko wanne irin ci. Ta yi shiru a wannan gaɓar.
"Mama dan Allah ki daina kuka, ni ba na damuwa da rashin aure na da wuri, na san komai lokaci ne, ban damu da sanin ko wace ce ni ba, ina ahlina su ke ba, na san ba shakka mijina ya na tare da ni kuma zai zo har in da na ke." Na ƙarasa faɗa ina mai share hawayen saman fuskata.
"Allah ya kawo lokacin." Mama ta furta iya hakan kawai.

Bayan kwana biyar da faruwar haka.

*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Bakwai.
Bayan kwana biyar da faruwar haka.
Tun ba na damuwa da maganganun mutane har abin ya soma damuna. Me ya sa mutane sun manta komai da lokacinsa? Su waɗanda suka yi auren ai ba ikonsu ba ne ba, wannan duk cikin hukuncin Ubangijine. Ban taɓa jin tsanar kai na ba da sai da na wayi gari ina tunano irin abubuwan da na dinga aikatawa saurayin nan da ya na ce min ba(Abbas, wanda na ji sunansa bakin mai shago.)
Na kanji tsana mafi munin tsana a kan kaina, ina ma a ce ana dawo da hannun agogo baya tabbas da sai na dawo da shi ko dan na amince da soyayyar Abbas, ko ni ma na samu na yi aure na huta da ɗan kiran da ake min na mai baƙin jini, shegiya.
Na kan tuna wani lokaci da ya turo kirana na fita da ƙyar bayan Mama ta matsamin. Ina fita zuwa zaure na laɓe jikin katanga ina hangoshi shida mai shago su na maganganunsu ni dai ban san me su ke tattaunawa ba amma na ga fuskarsa ta sauya ba walawala wannan ya tabbatar min da cewa maganar ba mai daɗi ba ce. Ni dai na taɓe bakina cigaba da kallonsu har lokacin da naga mai shago ya bar wajen ,na juya ina mai ce masa wahalalle(Kullum na kan tuna da wannan kalmar.). Ina shiga gida Mama ta hau tambayatana turo baki ina bata amsar sa har ta saka ta ke sanar min da wani saƙo,amma ni a lokacin idona ya rufe sosai. "(Ki dai yi a hankali wallahi, ina jiye miki gaba.)" shi ne kalamanta. A she saƙo ta ke isarmin ni ban yi zato ba.
Na kan yi kwana biyu a ɗaki ni kaɗai ina rusa kuka, duk san da kunnuwana suka riƙa tariyomin kalaman mutane sai na ji ina ma a ce banzo duniyar ba. Mama tun abin na damunta har ya zame ma jiki, ta riga da ta saba da maganganu.
Ranar da ba zan taɓa mantawa da ita ba, wacca ita ce ranar da ku ka haɗu da ni na haɗu da ku, ranar da na wayi gari Mama na shirin yi min aure dole da wani mashayi, mutumin da ya so lalata rayuwata ya so keta haddina, sanin ba zan iya zama da shi ba ga Mama ta kafe sai na yankewa kaina hukuncin guduwa daga gida.
"Ta ya ku ka haɗu da shi?" Musbahu ya jefa mata tambayar.
Ta goge hawayen da suka mata shaɓe-shaɓe saman fuskarta ka na ta ce,
"Ban san ma ya na yi ba, ban ma san ya na so na ba, ba na manta randa na je shagon mai shago siyan taliyar yara(Indomie) a wannan ranar na haɗu da shi, in da ya kafe ni da idanuwansa na masu shaye-shaye yadda ka san tsohon maye. Ban san ya a ka yi ba har ya sami labarina kasancewarsa ba ɗan yankin mu ba, a she wai zance na ya karaɗe ko ina na baƙin jinin da na yi ban yi aure ba, ni ban sa ni ba.
Ina kwance a ɗaki Mama ta shigo da yalwatacciyar fara'a shimfiɗe saman fuskarta, baki washe kamar wacca aka yiwa albishir da aljanna.
"Tashi-tashi ma za-ma za kije waje ana san ganinki." Mama ta ce.
"San ga ni na kuma?" na tambayeta bayan na sa ki baki galala ina mai bin ta da kallo.
"I! Ma za tashi, yau dai Allah ya yanke ma na saƙarmu,lokaci ya zo."
Ba ta ba ni damar yin wata ƙwaƙƙwarar magana ba ,ta ta sa ni gaba har hanyar zaure bayan ta saka min hijabina."
A waje na iske shi sai faman layi ya ke yi da alama ya sha ta yi mankas da shi.
Daf da ni ya ya tsaya ya soma magana cikin salo irin na ƴan shaye-shaye.
"Sanki na ke yi, kuma ni aurenki zan yi, na ji labarinki na yadda ki ka rasa mijin aure ,ga ki kuma shegiya to zan rufa miki a siri ka da ki soma bin maza."
Ji na yi zuciyatana wata iriyar zaɓalɓala, ina ji kamar na saka mabugi na yi ta bugunsa har ya mutu. Ina mai yi masa kallo irin wanda maye ya ke yi in ya ga abincinsa. Cikin ƙunar zuciya na ce masa,
"Ai kowa ya ga hasken rana ya san daban ya ke da na fitila. Da ni da kai sai a banbance waye zai taimakawa wani, shi bakin rijiya ai ba wajen wasan makaho ba ne, bari ka ji na ƙara tuna maka wani abu da ka kasa tunawa ita mace ba banza bazarar iskar damina ba ce, mutum ce mai daraja da ƙima, ba juji ba ce da har kowa zai ce zai zuba iskancinsa a kanta, dan haka tun wuri ka san in da dare ya maka." Na ƙarasa faɗa cikin tsantsar ɓacin rai, "Wai mai a ka mai da ni ne? Kawai dan ban yi aure ba sai kowa ya riƙa juyemin iskancinsa?" Na tambaye kaina.
Na kammala tambayar da nufar cikin gida.
Ji na yi kawai an fizgoni ta baya take na hantsila na dira izuwa faffaɗen ƙirjinsa. Ya saka hannayensa ya ƙanƙameni sosai, lokaci guda na soma ƙoƙarin ƙwatar kaina amma abin ya ci tura, duk kuwa da cewa cikin maye ya ke. Ganin ba sarki sai Allah ya sa na gantsara masa cizo a kan hannunsa ɗaya wanda da shi yafi riƙeni sosai. Ko sakanni ba a ɗauka ba ya cikani yana mai shafa hannun na sa. Da sauri na yi tsallen taku izuwa cikin gidanmu ji na yi kawai an sake fizgoni da mugun ƙarfi har sai da faɗi ƙasa, kafin na yinƙura na miƙe sai kawai ganin mutum na yi saman ruwan cikina, na yi bakin ƙoƙarina wajen ganin na kubuta amma na kasa, tu ni na soma anbaliyar ruwan hawaye, cikin zuciyata ina mai addu'ar Allah ya kubutar da ni daga kaidinsa. Ban san sa'in da algaitar maƙogaro na ta buɗe ba sai kawai na ji ina ƙwalawa Mama kira da ƙarfin gaske. Saƙon ya isa gareta ta fito dai-dai lokacin da ya ke ƙoƙarin yaga min siket ɗina yana mai danne ni sosai. Ji na yi na sami sauƙin nauyinsa ashe Mama ce ta kwaɗa masa kwano a tsakiyar kansa, ina samun dama na shige gida a miliyan, ban jima da shiga ba Mama ta shigo tana sauke ajjiyar zuciya, ni kam kuka kawai na ke yi na kasa cin komai har washe gari wanda a lokacin ne Mama ta tare ni da maganar aurena da shi. "Aure na da mutumin da ya so lalata rayuwata."
Ta ƙarashe da matsanancin kuka, sai dai sautin kukan Aunty shi ya da kusar da na Hajara har ya saka su bin Auntyn da kallo.
"Me ya sa ki ke kuka Aunty?" Hajara ta tambayeta cikin muryar kuka.
Ba ta tsagaita ba har sai da ta shafe sakanni sannan ta kalleta ba tare da kuma ta ce mata komai ba ta fice daga ɗakin.
Musbahu ta kalla da san neman ƙarin bayani, shi ma hawaye na gani kwance kan fuskarsa, cikin salon son basarwa ya shiga gogewa.
"Ki kwanta ki huta." Ya ce ya na mai ficewa daga ɗakin.
Sai ta ji ɗakin na juyamata, ji ta ke dama ba ta sanar da su labarinta ba,wata ƙila ta ɓata musu rai ne.
Sai dai saɓanin hakane wajen Aunty dan ji take kamar ta ta rayuwar ake tariyo mata, ganin raunin da zuciyarta ta yi ne ya sakata gwammacewa ta fita.
Kai tsaye cikin mota ta shiga ta kunnata da sauri ,dai-dai lokacin Musbahu ya ƙaraso wajen idanuwansa kanta ya ce,
"Aunty dan Allah kar ki soma tuƙa motar......." Ba ta ba shi damar ƙarasawa ba ta figeta a guje ta fice daga asibitin. Shi ma cikin sauri ya fice daga ciki ya tare babur mai ƙafa uku ya bi sawonta.
Hajara kuwa ƙurawa ƙafar ɗakin ido ta yi, ta fi mintuna a haka tana tsammanin sake ganinsu sun dawo wanda hakan ya gagareta ko da ƙiftawa dan kada ta rasa ganin shigowarsu.
A hankali ta janye idanuwanta daga kan ƙofar.
"Shi ke nan su ma sun gujeni." Ta furta hakan da wani irin furucin da ya sake karya zuciyarta.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)
Mai_Ƙosai
FCWA

Takwas.
Kamar daga sama ta ganshi gabanta tsaye, ji ta yi ƙirjintana bugawa da sauri da sauri. Cikin san nuna dakiya da jarumta ta furta,
"A'a kai ne ba sallama? Ƙaraso ma na." ta faɗa tana mai kallonsa.
Ya mutsa fuska ya yi yana mai raba idanuwansa kamar mai neman wani abu.
"Ina matata? Ina ki ka kaimin matata?" ya tambayeta.
"Har yanzu ni ma ba ni da masaniya a kanta." ta ba shi amsa a dake.
"Ki na nufin na rasata ko ya ya?" Ya tambayeta cikin gadara.
" Ka yi haƙuri, ina nan ina addu'ar Allah ya dawo maka da ita."
"In ma ba ki fara ba, to ki yi gaggawar farawa, ba na son harkar munafurci cikin lamarina, ko dai ma ke kika saka ta guduwa ne? " ya ce.
"A'a ɗan nan, a kan wane dalili? Ni kaina na fi ka san na ga ta dawo ko dan........."
Ya katse ta ta hanyar faɗin,
"Ba na san kwana-kwana kamar kwalekwalen da ke fama da kansa a tsakiyar ruwa. Na ba ki nan da wasu ƴan kwanaki idan ba ta dawo ba to lallai ke ce amaryar ta wa." Ya faɗa ya na mai ficewa daga gidan, ya yinda ya bar Mama da zare idanuwa gami da dafe ƙirji.
Ajjiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske, tabbas ta ɗebowa kanta ruwan dafa kanta, tuni ta fara jin nadamar abin da ta aikata, da ta san hakan za ta kasance da ba shakka ba ta yi masa alƙawarin auren Hajara ba, amma ita ai a lokacin ga ni take kamar kuɓutar da ƴar ta ta za ta yi, me ya sa ba ta yi wannan tunanin ba? Ga shi a dalilin hakan ta jefa ƴarta cikin gagari, ba ta san a ina take ba? tana raye ko a ma ce?, Ga uwa uba ita kanta itama ta jefa tata rayuwar cikin hatsari tunda ga shi tana fuskantar ƙalubalensa, lallai ba shakka tana cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi. Ta share ƙwallar da ta zubo mata, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi kamar sanyin ruwan ƙanƙara.

***
Kariyar Allah ce kawai ta kai Aunty gida. Ba ta fi mintuna biyar da isa ba shi ma Musbahu ya isa,ganin yadda ta yi fakin ɗin motar ya kuma tabbatarwa da kansa ba makawa ta soma samun fitar ya nayi. Cikin hanzari ya ƙarasa cikin gidan kai tsaye ɗakinta ya wuce, da mamakinsa sai ya ga wayam ba tanan. Kamar yadda tunanin inda zai sameta ya soma ratsa ƙwaƙwalwarsa hakance ta kasance. Keɓantaccen ɗaki ne wanda babu komai a cikinsa sai gado da lokar ajjiye kaya(sif) sai jerin hotonan da ke maƙale a jikin bangwayen ɗakunan ɗakin wanda aka ƙawata shi da su.
"Aunty " Ya faɗa da sassarfa. Juyowa ta yi a hankali jin amon muryarsa, idanuwanta sun kaɗa sun yi ja-za-wur kamar an watsa barkono cikinsu.
"Dan Allah Aunty ki sami nutsuwa ko da ta sakanni ce." ya furta hakan.
Ji ta yi wasu ruwan hawayen sun kuma malala kan fuskarta a hankali ta zame jiki ta zauna gefen gadon dake ɗakin.
Shi ma kallon hoton ya ke yi ya na mai sake jin ƙaunar mai hoton a ransa, tabbas da ana dawo da mamaci to ba shakka da shi ne mutum na farko da zai soma dawo da ɗan'uwansa mafi soyuwa a gareshi cikin wannan duniyar domin su ci gaba da kasancewa a tare cikin farin ciki da annushuwa.
"Aunty dan Allah ki daina azabtar da kanki, ki daina takurawa zuciyarki da ƙwaƙwalwarki na roƙeƙi." ya yi furucin cikin sanyayyiyar murya.
"Dole ne na yi kuka Musbahu, ta ya zan manta da mutumin da ya yi mini tsantsar halacci cikin rayuwata, ya so ni fiye da kansa, ya zaɓe ni cikin matana kasassu wacca tawayar ƙaddara ta mamaye su, ya zaɓi ya yi rayuwa da ni duk da ƙalubalen da na fuskanta, ya bar duk wasu mata masu daraja, ƙima da tarin mutunci, ya yi rayuwa da ni tamkar bai damu da kansa ba, dole ne na yi kuka iya kuka." ta ƙarashe cikin wani matsanancin kuka.
Yana ji inama yana da damar da zai rarrasheta ,yana ji inama yana da damar sauya ƙaddara, yana ji inama yana da ikon dawo da hannun agogo baya, yana ji inama duka waɗannan abubuwan ba su faru ba.
"Aunty a duk lokacin da na ga zubar hawayenki na kanji kamar na riƙa zubawa kaina garwashi ya riƙa zaizayar naman jikina. Idan ki na haka yaya ba zai taɓa gafarta min ba, ki tuna bamu da zaɓin da ya wuce mu mayar da komai namu ga Allah, shi ne yafi mu son shi shiyasa ma sai ya ɗauke ma na shi dai-dai lokacin da muke da buƙatarsa. Karki manta ko wanne abu da na sa lokacin muma lokacinmu zai zo kamar yadda sauran bayi ke tafiya, ki sakawa zuciyarki salama, ki sakawa ruhinki aminci dan Allah."
Ya faɗa ya na mai haɗa hannayensa biyu da alamar roƙo.
Ji ta yi jikinta duk ya yi sanyi da kalamansa, amma ya za ta yi itama ba da san ranta ta ke shiga cikin ƙuncin ba. Ba ta ba shi amsa ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.
Bin ta kawai ya yi da kallo ya na mai kuma jin wani ƙaƙƙarfan tausayinta cikin ilahirin zuciyarsa.
Hannu ya saka yana mai shafa ɗaya daga cikin hotonan.
"Allah ya dawwamar da kai cikin rahmarsa yaya na." ya faɗa ya na mai ficewa da sauri.
A madafa ya isketa tana faman hada-hadar haɗa abinci kamar ba ita ce cikin wani hali a yanzu ba. Murmushi kawai ya yi mata ya wuce ɓangarensa da ke cikin gidan.

***
Hajara kuwa har a wannan lokacin zuciyarta ba ta sami wata nutsuwa ba, tana jin ina ma ba ta sanar da su komai game da ita ba wataƙila su cigaba da riƙeta har tsawon rayuwarta.
tana cikin wannan halin ne likita ya shigo . Ido suka haɗa cikin son cusa masa tausayinta har ya amince da buƙatarta ta kafe shi da manyan idanuwanta.
"Likita ina buƙatar sallama a halin yanzu." ta faɗa a raunane.
Bai tanka mata baya shiga ƙoƙarin sauya mata robar ruwan dake maƙale hannunta zuwa wata.
"Ina buƙatar sallama Likita, ko kuma ni na sallami kaina da kaina." Ta faɗa a kausashe.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Tara.
Murmushi ya yi ya na mai sake dai-daita mata robar ruwan.
"Ba ki kamaci sallama a halin da ki ke ciki a yanzu ba." ya ba ta amsa.
"Ni dai ba na son zaman dan Allah ka sallameni." ta kuma faɗa.
"Bari ƴan uwanki su zo, su su ke da alhakin wannan." ya yi furucin.
"Ka ga Likita ni dai ka sallameni, ko kuma na sallami kaina kamar yadda na faɗa maka. Ba na son ɗorawa kowa nauyin kaina ka sallameni kawai."
Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ka na ya ce,
" Na ji zan sallameki, amma ki yi haƙuri ruwan ya ƙare saboda kema za ki fi jin daɗin jikin na ki."
Har ta buɗe baki za ta yi magana ya ɗora ya tsansa a kan laɓɓansa cikin kuma sauri ya yi furucin, "Dan Allah."
Sauke numfashi ta yi, ta koma ta kwanta a hankali. Shi ma ganin haka ya saka shi fita daga ɗakin bayan ya mata allura.

****
Dai-dai lokacin da Aunty ke sake shiryawa cikin dogowar riga ta atamfa ta yi matuƙar yi mata kyau sosai. Aunty baƙar mace ce amma baƴin mai kyau, tana da dara-daran manyan idanuwa, tana da dogon hanci, sai ɗan tsukakken bakinta ƙarami, tana da faɗin fuka sai sajen a ya kwanta gefen fuskarta luf-luf da shi. Wayarta ce ta soma ruri alamar kira ne ya shigo. Hannu ta saka ta danna maɓallin ɗagawa tare da karawa a kunnenta.
"Me ya sa ,to ga ni nan." Ta yi furucin da gaggawa tana mai sauke wayar daga kunnenta.
Sauri-sauri ta kammala shiryawar ta fice daga ɗakin. Madafa ta wuce ta ɗau ƙaramin kwandon da ta jera kayan abincin da ta gama kammala shi.
"Musbahu fito mu tafi." Ta faɗa tana mai yin gaba. Jin maganar Auntyn ta sa ya saka shi saurin fitowa daga sashen na sa. Tun kan ta ƙarasa wajen motar ta danna mabuɗinta da ke hannunta motar ta hau ƴar tsiwa. tana zuwa ta buɗe ƙofar ɓangaren zaman direba ta ajjiye jakarta, ta koma baya ta buɗe ta saka kwandon da ke hannunta,ka na ta dawo ta soma ƙoƙarin shiga.
"A'a Aunty dan Allah ki fito daga nan." Musbahu ya katseta ta hanyar kama murfin motar ya riƙe gam a hannunsa.
Murmushi kawai ta yi, ta koma ɗaya ɓangaren mai zaman banza, shi ma shiga ya yi ya kunna motar yana mai tura bakinta zuwa waje.
Mai gadi ya wangale musu makeken babban ƙyauren gidan, ya yi waje tare da ɗaukar hanyar asibiti.
Kaf cikinsu babu wanda ya ce wa ɗan uwansa uffan, Aunty kam tunani ne ya shiga kwanyar ƙwaƙwalwar kanta tare da yi mata saƙa kala-kala kamar ƙulu da kwarashi, burinta bai wuce kawai ta isa izuwa asibitinba.
Ba su ɗau wasu mintuna masu tsayi ba suka isa cikin farfajiyar asibitin. Dai-daita tsayuwar motar ya yi suka shiga fitowa bayan ya kashe motar.
Lokacin da suka isa barci ta ke yi sosai, kuma hakan ya samo asaline dalilin allurar barcin da Likitan ya danƙara mata.
Kallonta su ke yi cikin tausayawa, duk tabi ta rame sosai duk da dama ta jima a wannan siga ta ramar.
Aunty ce ta kalli Musbahu game da faɗin,
"Mu je ga Likita."
Har ya buɗe baki zai yi magana sai kawai ya ja bakin na sa ya tsuke, ya bita kamar yadda ta buƙata.
Yana zaune kan kujera, yana duba wasu takardu na marasa lafiya suka shigo bakinsu ɗauke da sallama.
Ya ajjiye takardun bayan ya amsa musu.
"Likita hankalina ya kasa kwanciya bayan kiran da na samu daga gareka, me ya ke faruwa?" Ta je fa masa tambayar.
Sai da ya ɗan ja kujerar da ya ke kai baya kaɗan sannan ya ce,
"Na je zan sauya mata robar ruwa ta riƙa roƙona a kan na taimaka na sallameta, da na nuna hakan ba zai yiwu ba sai ta tabbatar min da lallai ita da kanta za ta sallami kanta. Ganin hakan sai ya saka na kirawo ki bayan na mata allurar barci ba tare da saninta, amma dai a ko wanne lokaci za ta iya farfaɗowa dan ba mai yawa na mata ba."
Ya ida zancen yana mai kafe Aunty da idanuwansa jiran mai za ta ce.
Gaba ɗayansu sauke ajjiyar zuciya suka yi. Mushbahu ne ya yi ƙarfin halin magana gami da faɗin,
"Muna godiya Likata, kuma in sha Allahu ba za mu bari haƙanta ta cimma ruwa ba, mun yi alƙawarin zama da ita, kulawa da ita a kowannen hali, kuma muna so kaima ka kula mana da ita fiye da yadda ka ke mana."
"Kamar yadda ku ke a wajena haka ita ma ta ke, duk da na riga na fahimci iya abin da zan fahimta game da alaƙarku, kuma na ji daɗin yadda ku ka nuna mata ƙauna, amma tabbas tana buƙatar hutu, sannan ya na da kyau ta rage tunani."
"Hakane Likita tabbas alaƙarmu da ita ba ta wani jima da ƙulluwa ba, amma muna jinta kamar wacca mu ka fito tsatso ɗaya kamar ƴar uwar junanmu." Gaba ɗaya Musbahu ya kwashe labarinta ya labartawa Likita.
Likita ya tausaya mata sosai,ya kuma yi alƙawarin in sha Allahu zai taimaka mata da iya ƙarfinsa.
"In sha Allahu komai zai warware Likita." Aunty ta yi furucin.
Likita ya kuma jinjina musu da irin kyakkyawan taimakon da suka yi mata, ya sake yi musu alƙawarin ba ta ingantacciyar kulawa fiye da yadda ake killace ƙwai gudun fashewarsa.
Sun ɗan tattauna sosai game da ya nayin jikin nata, wanda ya kwashesu wajen kimamin rabin awa su na taɓa kiɗa taɓa karatu. Sai daga baya suka ɗunguma zuwa ɗakin na ta dan ganin ko ta farka.

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On LOKACI NE
avatar
khamilu

1 year ago

Reply

Mashallah

Please Login or Register in order to submit comment