Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Mama taso zamanta a can amma Alhaji Jibril ya bata haƙuri koba komai ai ta zauna da kakar Hajaran.

Bayan dawowarsu da sati biyu aka fita da Mama Rabi zuwa wani kyakkyawan asibiti dan nema mata magani.

*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma bakwai

Cikin satin suka shirya zuwa ga ahlin Aunty wanda da ƙyar ta amince da hajan tana kuka kamar wacca aka ce za ta bar duniyar. Wannan karan tafuyar harda Likita Mubarak.

Ranar Laraba suka yiwa unguwarsu Aunty tsinke, gaba ɗaya unguwar ta sauya ta canza mata sai ka ce wacca ta yi shekaru masu mugun yawa.

Gidan kam sai da ta haɗa da tambaya da sunan da aka raɗa mata(Ta rasa mijin aure)sannan ta iya samo shi.

Hajara na kallonta ta wutsiyar ido yadda take bin ko'ina na gidan da kallo,komai gani take ya sauya mata kamar ba gidansu ba.
Sallama Hajara ta shiga kwaɗawa ,dan ta lura Aunty ta gaza furta hakan.

Umma dake ɗaki ta fito tana mai amsawa, "Wane ne ke.....?" Ta shiga tambaya. Sai kuma maganar ta gaba ta katse mata sakamakon ido biyun da ta yi da ƴarta tsaye tana bin gidan da kallo. Ji ta yi ƙafafuwantana rawa.
"Ƴa ta ke ce? Ko dai mafarkin da na saba yi ne?"
Duk da faragabar da take ciki sai ta ɗanji wani sanyi ya ratsata zuciyarta ashe su na santa.

Hajara ce ta kamo hannayenta tana matsasu a hankali ka na ta ce,
"Tabbas mafarkinki ya zamo gaskiya, ƴar ki ce wannan ta dawo gareku har a bada. Mu na neman izinin shigowa da iyayenmu."

Ba ta jira amsar Umma ba ta fita ta musu izinin shigowa. Umma kuwa ɗaki ta koma jiki a saluɓe ta shiga shinfiɗa musu tabarmar zama.
"Shigo d su ƴar nan." Umama ta ce wa Hajara.

Cike suka shiga amma banda Aunty dake ƙamw a wajen kamar wacca aka dasa.

Hajara ce ta kamo hannunta gami da faɗin,
"Aunty ki is aga mahaifiyarki." Da ƙyar ta soma ɗaga sawayenta ta riƴa jefa su cikin ɗakin tare da samun waje ta zauna. Umma ta bita da kallo cikin so da ƙauna.

Nan aka shiga gaggaisawa tsakanin Umma da mutanen,shiru ya gyatta tsakaninsukafin Alhaji Jibril ya ɗora da faɗin,
"Da farko dai muna bada haƙurin zuwan bazata da muka yi,sannan muna godiya d yadda aka tarɓemu.Amma in badamuwa muna san ganin shi maigidan."

Umma ta ɗan nisa kafin ta ce,
"Ayya badamuwa bari na kirashi a waya.Bai ma jima da fita ba."Ta ƙarasa tana mai ɗaukar wayarta ta soma kiran layin wayarsa. Cikin sa'a bugu biyu ya ɗaga nan ta somar sanar masa da abin da saƙon ta take san isarmasa. Ya kuma bata tabbacin in sha Allahu ga shi nan isowa.

Bai wani ɗau dogon lokaci ba ya iso, nan suka shiga musabaha da kowa.

Alhaji Jibril ya soma da,
"A karo na biyu muna sake bada haƙurin ziyarar ba za tan da muka kawo. Ni suna na Alhaji Jibril mahaifi ga mijin Khausar ƴarku, sannan mahaifi ga Musbahu ɗana biyu, waɗanan kuwa(ya shiga yi musu bayanin su Mama.) zamu ari bakin Khausar mu ci mata albasa,muna masu bada haƙuri a bisa katoɓarar da ta aikata ta fice daga gida ba tare da izininku ba, wanda hakan ya faru ta dalilin juya mata baya da kuka yi saboda kawai wata ƙaddadara ta gifta mata.Ku ne kuka soma kimtsa mata guduwa cikin ranta saboda rana inuwa zafi da kuka sakata ciki. Wani abu da iyaye ya kamata su sani shi ne; Matsayinmu na iyaye bai kamata mu riƙa juyawa ƴaƴanmu baya ba lokacin da suka tsinci kansu cikin wata matsala, kamata ya yi mu rungumesu hannu biyu mu mara musu baya cikin tafiyar, bai kamata mu ƙyaresu ba ko tsangwama saboda wani kuskure na su wala'alla sunja da kansu ko aka sin haka.Ya na da kyau kowaɗanne iyaye su tuna cewa kowanne bawa da irin tasa ƙaddadarar,sannan ƴaƴa ababen kiwone garesu wanda Ubangiji zai tambayesu ranar gobe alƙiyama. Komai na rayuwa ɗan lokaci ne, wani har ya mutu ma bai yi aurenba, wannan duk cikjn tsari da hukuncin ubangiji ne.Wani kuma zai shafe lokuta masu tsawo har an cire rai ga zato sai kuma a sami kyakkyawan sakamako. In mu ka yi duba da faɗin Ubangiji maɗaukakin sarki da ya ke cewa,
"Innamaa amruhu idha araada shai'aan ayyaƙuula lahu kun fayakuun. Ma'ana Umarninsa idan ya yi nufin wani abu, sai ya ce masa kawai"kasance" sai ya kasance(kamar yadda yake nufi.) Suratul Yaa-sin(sura ta talatin da shida 36,aya ta tamanin da biyu 82. Haka kuma cikin surat-ul-Mu'min(sura ta arba'in 40 ,Aya ta sittim da takwas 68 ya na kuma cewa, "Huwal ladhi yuhyi wa yumiitu fa'idhaa ƙadaa amran fa innmaa yaƙuulu lahu kun fayakuun. Ma'ana Shine wanda ya ke rayarwa kuma ya ke kashewa. To ,idan ya hukunta wani al'amari,to ya na cewa kawai gare shi, "kasance" ,sai ya kasance(kamar yadda ya ke buƙata.) "

In muka yi duba da waɗannan ayoyin sun wadatar da mu cewa lallai Allah shike komai a duk lokacin da ya so yin abun kawai zai ce masa "Kasance" kuma abun sai ya kasance, kunga kenan bamu muke da ikon sakawa ƴaƴanmu su yi aure ba idan muka yi haƙuri lokacinsu na nan zaizo kamar yadda kowanne abu ke zuwa ya wuce. Mutane da dama kan yiwa kallon abubuwa da dama kallon saɓanin hankali, sau da yawa dan ɗanki ya aure ƴar da bata haihuwa sai kawai a ɗora musukaran tsana wacca itama haihuwa ai lokaci ce kamar yadda mutuwa take da lokaci kuma in tazo ba za ta taɓa ɗaga ƙafa ga kowa ba.Aure, Haihuwa komai lokaci ne wani kan zo lokacin da ake sansa wani kuma zai jinkirta har ta kai ancire tsammani a kansa sai kuma lokacinsa ya zo. Ya kamata mu daina ƙyara, hantara ga waɗanda abun bai kasance kansu ba, kaima da ka samu damar ba kai ka bawa kanka ba ikon Allah ne."
"Ƴarku ta yi aure baku tsaya mata ba, in da ace wanda ta aura ɗan yankan kaine da a yanzu ba za ku sameta sai dai in har ya na tsantsan santa. Abun da ya faru da ita tsakaninta da malam baku yi kyakkyawan bincike ba kuka yanke mata ɗanyen hukunci, kun san ba halinta bane ba lokaci guda ba za ta sauya tarbiyar da kuka mata ba ya kamata ku riƙa kyautata kyakkyawnn zato ga ƴaƴanku. Musulunci bai yarje yanke hukunci cikin abin da ba tabbas a kansa babu bincike. Mu na masu sake baku haƙuri da nema mata afuwa."

Baba ya goge ƙwallar da ta zubo masa da tun fara maganar Alhaji suka zubo masa. Saida ya ɗan matse idanuwansa kafin ya ce,
"Tabbas mun zalunci kanmu ,mun aikata babban kuskure,mun wofantar da karatunmu mun manta cewa Allah ke yin komai. ko da yake tun kan aje ko'ina ga shi nan mun suma ganin sakayyarki,duba da kullum muka waye gari muke kwaɗaituwa da san ganinki gabanmu amma bama samun wannan damar. Mutumin da ya aurar dake baya raye Allah ya mas rasuwa. Matarsa kuwa ta ce ba za ta taɓa gaya mana adireshinki ba in har da gaske ɓuna sanki to mu laluboki da kanmu. Ƴarta da take ƙawa gareki ta yi aure har yau bama ce ga inda take ba. Mun yi tunanin kaita ƙara to amma muce ƙararta kanme? Bamu da hujjar haka. Bamu ta shi tsinkewa ba sai wnnda ya lalata miki rayuwa ya gurfana gabanmu cikin neman gafara, ya na kuka sosai kamar ƙaramin yaro ya shiga labartamana yadda har ya haiƙemiki, har muka gaza fahimtarki mu da sauran mutane muka yanke miki mummunan hukunci. A halin yanzu kam na ji dai ance baida lafiya ya na kwance. Ki gafarta mana ƴarmu, lallai mun zama muna iyaye masu tauye haƙƙin ƴarsu ki yafe mana dan Allah."

Umma kam kuka take sosao da ƙyar ta iya furta,
"Lallai mun zama daga cikin masu butulcewa hukuncin Allah,mu ka kasa yadda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,bamu taɓa tunin lokaci zai zo da zamu ji kunya ba,mun ji kunya sosai ƴata lokacin da muka gano cewa baki da laifin komai ko ƙanƙani cikin hasashenmu. Dan Allah ki gafartamana." Ta ƙarasa tana hale hannayenta biyu waje ɗaya.

Hajara da Khausar kuja kawai su ke yi, fuskarsu taf da ruwan hawaye kwance bisa kumatunsu, wani na sauka wani na biyo baya. Khausar kuwa ji take ƙaunar ɓahaifan nata biyu ta sale nunkuwa cikin zuciyarta.
"Na yafe muku ya ku iyayena,bani da kamarku cikin duniyarnan,ba zan iya fushi da ku ba,ba zan iya jurar ganin ruwan hawayenku ba ku gafartamin bisa kuskuren da na aikata mu......." Ta ƙarasa tare da fashewa da kuka mai taɓa zuciya.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma takwas

"Na yafe muku ya ku iyayena,bani da kamarku cikin duniyar nan,ba zan iya fushi da ku ba,ba zan iya jurar ganin ruwan hawayenku ba ku gafartamin bisa kuskuren da na aikata mu......." Kalamanta suka uanke sai ka ce an datse wayar wuta daidai ɗokacin da ake amfani da wutar, tare da fashewa da kuka mai taɓa zuciya.

Cikin hanzari Umma ta janyota zuwa jikinta tana mai rungumeta.
" Mun yafe miki ɗiyarmu."

"Alhamdulillah godiya ga ubangiji da ya kawo ƙarshen wannan al'amari, abu na gaba kuma batune a kan auren Likita da ya ke san yi ga KHAUSAR." Alhaji Musbahu ya ce.

Khausar, Hajara ,Musbahu sai da suka zabura kamar waɗanda a ka tasa daga barci, a ba zata suka ji maganar Alhaji. In ka cire sauran jama'ar ban da Umma da Baba da alama kenan sun san da zancen.
"Bari na warware muku zare da abawarsa."

"Bayan dawowarmu daga Jama'are mun yi Magana da likita ya shaida min cewa ya na san aurenki ,amma sai na dakatar da shi ta hanyar faɗin ya bari muje ga iyayenki wanda shi ne shi ma ya ce zai bimu. Na sanar da iyayenki ukun dan ya kamata su san da maganar kuma sun yi farin ciki sosai. Yanzu kuma zamu ji ta bakin iyayenki biyu da kuma ke. Ina fata za ki amince da buƙatarsa dan na san ba za ki wulaƙanta ba. In kuma na yi ba daidai ba to kugafar ce ni."

Cikin farin ciki Baba ya soma faɗin,
"Babu abin da ka yi wanda ba daidai ba, kai matsayin uba kake gareta. Ban san da wane baki zan gode maka ba,na tabbata ba za ka taɓa bari ta aure wanda zai cutar da ita ba."

Ya juya ga Khausar ka na ya ce,
"Ni ba zan miki dole ba, amma ina baki shawara da ki amshe shi, ina so ki je ki yi shawara da zuciyarki da ƙwaƙwalwarki."

Ita dai sauransukawai take yi,amma ba za ta iya rayuwa da wani bayan Abbas ɗinta ba, mutumin da ya sota tana jin ba wanda zai iya zama da ita yadda ya mata. Da wannan tunanin nata da take yi taji taron ya tashi bayan sun shafa addu'a.
Sai bayan la'asar su alhaji suka bar gidan bayan sun bar Hajara da Khausar. Musbahu ji yake ina ma shi ma a ce ya zauna.

Duk yadda likita ya so ya gana da Khausar abin ya faskara,haka ya haƙura ya ce ya dawo gobe.

A daren ranar Khausar ta ziyarci gidansu ƙawarta Rabi'a ita da Hajara,ta yi kukan rashin Baban Rabi'a wanda ya zama uba na biyu gareta, mahaifiyarta kuwa ta yi farin cikin ganinta sosai. In da ta tambayi Rabi'a ta sanar mata tana Abuja wata biyu baya ta zo ta koma. Ta yi mamaki sosai yadda har Rabi'a ta zo bata nemeta ba, ba kuma ta kirata ko da a wayane ba ,basu bar gidanba har sai da ta ƙarɓi lambarta da kwatancan inda take a Abujan.

Washe gari suka zuba sammako zuwa gidan ƴar'uwarta. Sosai su ke kuka na rashin ganin junansu .Sun yi kewar juna ba kaɗan ba. Ganin abun ba na ƙare bane ya saka Hajara shiga tsakaninsu tana mai tsokanarsu,sai ga shi dukkansu sun shiga darawa kamar ba su ne ke yin kukan ba. Ba su baro gidan ba sai bayan sallar isha ,shi ma ji su ke kamar kar su rabu.

Bayan sun dawo ne Umma ke shaida musu Likita da Musbahu sun zo ,harma sun nemi ta basu kwatancen inda su ke ta sanar da su ba jimawa za su yi. Amma sun ce za su dawo.

Khausar ji ta yi gabantana faɗuwa raass, ƙwalla ta cika mata kurmin idanuwanta, ba ta iya bawa Umman amsa ba ta shige ɗaki. Ganin haka ya saka Hajara mara mata baya.

A gefen gado ta iske ta zaune, hannu ta saka tana mai dafa kafaɗarta tare da furta.
"Na fahimci cewar har yanzu kina cikin damuwa, sannan uwa uba kina tunanin yadda za ki iya auren Likita saboda soyayyar Abbas cikin zuciyarki,amma ina so ki sa ni komai da yake faruwa daga Lillahi wahdahu ne. Ina so ki karɓi duk wani tsari da hukuncin da ya yi miki,ki ɗauka wata ni'imace Allah ya aiko miki da ita shiyasa Likita ya ce yana sonki, dan Allah kada ki bari damar ta wuce."

Ta share ruwan hawayen da ke kwance saman fuskarta tana mai fuskantarta ka na ta ce,
"Ƙwarai ina tunanin yadda zanyi rayuwa tare da wani in ba Abbas ba, amma na amshi duk irin hukuncin da Allah ya wanzar a kaina, na amince zan aure shi."

Wani daɗi ya mamaye zuciyar Hajara, ta saki dariya tana rungumota jikinta.
"Yawwa Auntyna ko kefa." Hajara ta ce.

Khausar ta yi murmushi ka na ta ce,
"Ina so kimin wata alfarma ƙanwata." Ta ƙarasa tana kamo hannayen Hajara duka biyun cikin nata.
"Ina jinki Auntyna, in sha Allahu in dai ba tafi ƙarfina ba zan miki kowacce iri ce."

"So nake ki aure Musbahu."
Ta jefa mata maganar a ba za ta.

Cikin sauri ta kalli Khausar tana mai girgiza kanta.
"A'a Aunty dan Allah.........."
"Dan Allah Hajara kimin wannan alfarmar, Musbahu na tsananin sonki sosai fiye da tunaninki, ki yadda da ni." Ta katseta ta hanyar jefa mata maganar.

Shiru ta yi kafin ta ce,
"Shi kenan Aunty ,Allah ya shige mana gaba, amma ya aka yi kika san ya na sona?"

Sai da ta murmusa ka na ta ce,
"Tun kwanciyarki asibiti alamomin sonki suka soma bayyana gareshi na fahimci hakan ganin yadda ya damu dake fiye da yadda na damu dake, na kuma gasgata zancen lokacin da na tuna ɗan zamanki a gidanmu yadda ya riƙa jeleƙe a kanki,da na tutsiyeshi sai ya gasgatamin tantamata amman ya roƙeni da kada na sanar miki har sai sanda ya farauto zuciyarki, ni kuma sanin halinki kada a kuma zagaye na biyu ya sa na fasa sirrin na roƙeki da kaina sai a ka yi sa'a kika amshe shi hannu bibbiyu."

Hajara ta yi dariya mai yawa tare da rufe fuskarta tana furta, "Kai Aunty".

Wajen tara da kwatana dare Likita ya iso gidansu Khausar shi kaɗai ,bayan ya yi sallama zauren gidan Baba na nan shi ya masa iso zuwa ɗakin dake soron gidan.

Khausar ta shigo bakinta ɗauke da sallama, suka shiga gaisawa.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)

Mai_ƙosai

FCWA

Goma tara(Ƙarshe)

Mintuna huɗu ba wanda ya ce uffan ,ganin shiru ba ƙarau ba ne ya saka likita furta,
"Da farko ina mai baki haƙuri a bisa kutsen da na miki cikin rayuwarki, ban sa ni ba ko zan sami matsuguni daga cikin sashen zuciyarki ko da ban shiga can ciki ba? Sannan ina fata ki zama uwar 'ya'yana abar alfaharita. Idan kin amince zan yi zallar farin cikin da babu algus, idan ba ki amince ba zan yi haƙurin hakan nasan Allah ke shirya kowanne lamari,amma zan yi baƙin ciki mai yawa bisa rashin samun mace tagari da na yi. Na riga da na sanar da iyayena komai, na kuma buƙaci da su bani damar jin ta bakinki ,ko yanzu kika amince gobe za sukawo kuɗin aure gidanku dan saka rana bana san tsaye-tsaye." Ya dire zancen ya na kallon yadda ta yi ƙasa da kanta tana faman wasa da ƴan yatsunta goma.

Ta ɗan jima kamar ba za ta ce wani abun ba cikin sanyayyiyar murya ta ce,
"Allah ya tabbatar mana da alherinsa."
Sosai ya ji daɗin maganarta ,hakan ya nuna masa kenan ta amince kuma ya gane hakanne ta addu'arta. Ji yake kamar ya haɗiyata dan murna.

Sosai yake janta da hira amma ta kasa sakewa da shi, cikin farin ciki ya mata sallama ya bar gidan na su.

Musabahu kuwa lokacin da ya sami saƙon Auntyn nasa na jin Hajara ta aminta da shi ya ji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya dinga lasa, alla-alla yake gari ya waye ya iso gareta ko dan ganin kyakkyawar fuskarta.

Bayan kwana uku da faruwar waɗannan al'amuran a ka saka ranar Khausar da Likita, sai Hajara da Musbahu wata biyu cif, zu ku ga murna wajen ahlin.

Mama ta so a bata Hajara ta yi bikinta a Jama'are kasancewar bikin saura wata guda za ta koma can ita da Kakar Hajara dan ta sami sauƙi sosi fiye da zato.

Amma Alhaji Jibril ya hanata hakan, ya kuma tabbatar mata su ma ba zasu koma ba har sai bayan biki shi zai ɗau nauyin komai,mutanen Jama'are ma za a kai mota duk wanda zai zo za a ɗakkoshi zuwa bikin. Ba yadda ta iya haka ta sawa ranta salama.

Bayan kwanaki goma Khausar da Hajara suka shirya tafiya Abuja wajen sahibarta,cikin tafiyar har da Musbahu dan ya na ce sai ya bisu.

Cikin hukuncin Allah ba su sha wahala ba suka samo gidan, kasancewar Musbahu ya san garin ABuja sosai.

Sanda suka yi ido huɗu sai kuka, kukan da suka kasa gane na mene ne. Sosai Khausar kewa Rabi'a faɗa kan nesanta kanta da ta yi da ita. Ba ta san me za ta ce mata ba, dan ita kanta bata da hujjar da za ta kare kanta, sai kawai ta shiga bata haƙuri. San da ta ji auren Auntyn na ta murna kamar me wajenta ba za ta iya faɗuwa ba.

Kwanansu biyu suka baro Abuja, ba su taho ba sai da Rabi'a ta mata alƙawarin kasancewa da ita har abada kuma zuwa biki dole in dai ba rashin lafiya ko mutuwa ba.


Shirye-shiryen biki ake sosai. Rabi'a ta zo saura sati guda biki, kullum a tafe su ke babu zama.

A na i gobe ɗaurin aure suka ziyarci unguwar maciyi amana malam kamar yadda suka yi wancan karan, katin ɗaurin auren suka kai mi shi, sai dai ganin halin da ya ke ciki sun tausaya masa. Ya na fama da larurar ƙafa dalilin wani hatsari da ya yi a kan mashin, wanda har ya yi sanadin rasa mazantakarsa.

"Ina fata za ka halarci taron ɗaurin auren da yafi kowanne ? Dan kada a zo a baka labari ka san ance gani ya kori ji,gwara ka ganewa idanka Khausar ba ta yara ba ce ƙananan ƙwari irinka." Rabi'a ta ce.

Cikin kuka ya soma furta
"Tabbas na san na zalunce ki sosai ,sai dai na ga ishara masu tarin yawa babi-bayan babi, na rasa ƙafatana rasa mazantakata yadda zan yi rayuwar aure da wata babu, ba wacca za ta zauna dani dalilin wannan, na yi magani yafi a ƙirga amma a banza dan ba wani cigaba tabbas wannan ishara ce gareni da masu hali irin nawa. Tun anan duniya naga sakayyarki Khausar ki gafartamin ko na sami rahmar Ubangiji." Ya ƙarasa cikin gunjin kuka.

"Na yafe maka ,Allah ya yafemana baki ɗaya." Khausar ta ce cikin raunin murya. Da sauri ta fice daga ɗakin ganin haka ya saka su Rabi'a mara mata baya.

Satin ɗaurin aure ya shigo cikin hukuncin Allah. Ranar Juma'a aka ɗaura auren Khausar da Likita , Hajara da Musbahu. Ɗaurin auren da ya tara dubban jama'a.

Bayan magrib a ka tara su tare da musu addu'a da kuma nasiha mai ratsa zuciya.Daga nan a ka danganta kowacce da gidanta.

Mama kam bayan biki da kwana biyu ta matsanta sai ta koma Jama'are a cewarta mai za ta zauna yi bayan an kammala bikin. Su na ji su na gani suka barta ita da ayarinta suka ɗunguma zuwa can.

Rabi'a ma ta koma bayan biki da sati guda. Zumunci su ke dukkansu su huɗun ba kama hannun yara,kowa ya kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali. In da farin cikin ya kuma ƙaruwa dalilin auren mahaifiyar Rabi'a da Baban Khausar ya yi. Mama kuwa Alhaji Jibril ya so aurenta ta kafe ita aure ta gama sai a lahira ita da tsohon mijinta in sha Allahu.

Farin ciki, walwala, annushuwa da kwanciyar hankali suka mamaye zuƙatan su tare da wanzuwa tsakanin ahlin tamkar ba su ba.

Alhamdulillah.

Sai mun sake haɗuwa a sabon wani littafin nawa.

Real Mai_ƙosai ce











An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On LOKACI NE
avatar
khamilu

1 year ago

Reply

Mashallah

Please Login or Register in order to submit comment