Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏCompiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 1 - 5


Kwance take a daki sai kuka take bata mai lallashinta tashi tayi ta dauko wayarta daga chargi tayi dialing number hello Aunty kinji abinda alhaji yace wai Dalhat xai aura mun kuma ni wlh bana sonsa hajiya dasu yaya duk sun goyi da bayansa


Don Allah kixo kiyi masa magana ko Allah yasa yaji maganarki ki taimakeni ki taimaki rayuwata na fashe da kuka daga can bangaren tace kiyi hakuri hudah ina nan xuwa insha Allah amma kin san alhaji magana daya yakeyi but i will try my best ke kuma ki cigaba da addua to aunty nagode katse wayar nayi


komawa nayi na kwanta na cigaba da kukana da dai naga kuka baxai fissheni ba na tashi na dauro alola naxo na tada sallah nai addua sosai sai wajen asuba bacci mai nauyi ya daukeni


Sai wajen karfe shidda da rabi na tashi na makara gashi gashi munada lectures karfe takwas idona duk sun kumbura wanka naje nayi tare da alola sallah nayi sannan na dauko wani atamfa green da orange nasa ba wani kwalliya nayi sosai ba


Falo nafito ban tarar da kowa ba kamar yadda na saba tare muke break duka harda su hajiya sannan masu xuwa makaranta su tafi masu xuwa wurin aiki su tafi yau na makara ba wanda yaxo ya kirani karasawa dining nayi tea rabin kofi na hada na kasa cin komai shima tea din da kyar na iya shanyewa nafi 15mins ina xaune ina tunani dafani da akayi shiyasa nayi firgigit dago Kaina nayi naga Ashe Jidda ce nace wai har kin shirya tace lallai nema hudah wai make damunki ne gashi idonki duk a kumbure alamar kinyi kuka kin gaji uhm abinda na iya cewa kije ki gaida hajia kixo mutafi kin cikani da tambaya kamar wata yar jarida


bari in dauko key kafin in dawo ki tabbatar kin gaisheta kin fito tare muka haye sama na shiga dakina ita kuma ta shiga dakin hajiya hand bag na dauka tare da makullin mota na fito a kasa na sameta nace muje ko a tare muka fito har farfajiyar gida naga ba motar Jidda


Aa Jidda ina motar taki ai ta lalace tana wurin gyara tun jiya Allah ya kyauta ameen ga key din ke xaki Jamu dama wlh bana jin dadi


Duk kin sa mun makara a tare muka shiga mai gadi ya bude gate muka hau titi sosai ba wanda ya karacewa dan uwansa kala har muka isa skull din munje mun tarar har ya shiga na kalleta nace Jidda yayaa xamuyi kennan kinga fa harya shiga dariya tayi


Au dariya ma kikeyi ko to aikene naga kin rude ba dole na rude ba kin sanfa halin lecturer nan mugu ne gashi yan mata suyita shige masa ko don sunga handsome gay ne


Ooo hudah kodai kema kina cikine Allah ya kyauta ni ai yayi mun yaro muna rafe muna hira har muka kai bakin class din ta kalleni na kalleta tace muyi addua kawai mu shiga haka kuwa akayi salam excuse us sir can we come in yace yes shiga mukay kowa sai kallon mu yake har muka xauna suna mamakin yadda akayi ya barmu muka shiga saboda kowa yasan kaidansa idan ya shiga ba mai shiga


cigaba yayi da lectures dinsa hankalina kwata kwata baya wurin jidda ce ta taboni ke lafiyarki kuwa ana karaku kin xauna kin buga tagumi gashi sir Haidar sai kallon mu yake a haka har ya gama ban tsinci komai ba a cikin karatun ba kallon mu yayi yace u d late comas follow me 2 my office ta kalleni na kalleta sannan muka ce okey sir


yana fita kobi ta Kansa bamuyi ba muka cigaba da harkokin mu Jidda ce ta kalleni tace wai ke hudah meke damunki ne rike hannunta nayi xo muje mota fitowa mukayi daga class wurin da mukayi parking din motar mu muka wuce shiga mukayi har kwallah ya taru a idona sharewa nayi nace Jidda wai baki San meke faruwa ba tace hudah kin sani a duhu dan Allah fada mun meke faruwa....




🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 6 - 10


Wani kwallar na dada sharewa Jidda dan Allah ki fahimce sosai kafin ki Yanke mun hukunci kuma kada ki dauka ko cin fuska ne aa ko daya alhaji xai mun auren dole narasa yadda xanyi kin san halin iyayen namu da tsatsauran raayi


Kuma ni kin san burina shine sai na gama karatu xanyi aure kuma ni koda xanyi aure to nafison in auri dan 35 and above bani son yaro wlh


Ta jinjina kai ta haka ne to yanxu wa alhaji ya xaba miki hawaye na xuba a ido na nace bakowa bane dan uwanki ne yaya Dalhat ba wai bana sonsa bane aa son da nike masa da ban ne wato so na yan uwantaka amma ni gsky bana jin xan iya rayuwa dashi a matsayin miji


na fahimceki Jiddah banga laifinki ba kuma banji haushinki ba ke kawatace ta wani gefen kuma yar uwa tun muna yara muke tare kin san sirrina kema na san naki kin san burina na San naki tayaya xan ki gsky saboda yaya Dalhat yana dan uwana nagode Jidda da kika fahimce


To yanxu tayaya xamu bullo ma wannan lamarin wlh Jidda kai na ya kulle na rasa yadda xanyi da rayuwata gashi gidan duk sun juya mun baya daga jiya xuwa yau ammah dai na kira aunty Khairat na Fada mata kin San alhaji yana jin maganarta ina fatan Allah ya dora mu a Kansa


Kawata gsky kina cikin matsala babba ko kin san yaya Dalhat din ma ba son auran yake ba jiya naji su ummi na cewa nan da wata uku kin san ance ya kawo mata amma yaki sai shekaran jiya ya kawo mana wata baki ganta ba yar duniya shine abbu ya koreta yace ko bayan ransa bai yarda ya aureta ba ana haka sai ga alhaji abbu yace yawwa alhaji mai xai hana a hada Dalhat da hudah kawai sai jin alhaji nayi yace ya bashi daki suka shiga shi kuma yaya Dalhat sai huci yake ya fita ban san me suka kara tattaunawa akai ba


Abinda yasa ban fada miki ba saboda bana son tayar miki da hankali shawarar da xan baki yanxu dai mubi komai a hankali share hawayen daya xubo mun nayi nace na shiga uku jidda yanxu katse mun karatu xaayi i don't know what 2 do jidda kiyi hakuri insha Allah xai barki ki cigaba take heart pls


Jidda nagode Allah ya bar kauna hudah let's go to d library fitowa mukayi daga mota mun fara tafiya kenan sai ga chairman din mu yaxo yace ina kuka shiga tun daxu inata nemanku kun sa anata bani wuya Jidda ce ta kalleshi tace toh fah meya faru yace sir Haidar ne yace duk inda kuke cikin skull din nan sai na nemo ku wai yace kuje kunki xuwa sai a lokacin na dago Kai nace to wai shi ina ruwansh damu oho xaixo ya takura mana

Hudah kuyi hkr dan Allah kuxo muje wurinsa ko na samu ya kyaleni da kyar na amince muka tafi har office din sir Haidar shi ya fara shiga muna baya yace sir gasu nan yace ok you can go ya tafi ya barmu wurin 5min ba wanda yayi magana gyaran murya yayi yace wato ku na kiraku but u refused 2 come jidda ce tace no sir yace what's are names Jidda ce tace my name is Jidda Aliyu yace Ashe ke daughter ce kefa nace hudah Sadiq yace nice names why do u come late 2day duk mukayi shiru yace am talking 2u Jidda ce tace we are sorry sir hudah ce bata da lpy dats why yace gidan ku daya ne ko kene bakinta tace aa hudah what's wrong sai a lokacin na dago ido na cike da hawaye na kasa magana fita daga office din nayi aguje sai mota kallon Jidda yayi yace lpy meya faru da ita saboda naga tunda tashigo class na idon a kumbure tace wani abu ke damunta and is a personal issue will solve it insha Allah

Yace nima xan tayaku da addua thanks alot malam yace can I get her phone no yea tabashi kije ki lallasheta

Tana fitowa wurin mota taxo don tasan ina can na nufa ta tarar dani sai kuka nake shigowa tayi tana ta lallashina da kyar nayi shiru ta jamu sai gida a kofar gidansu ta tsaya tace ni xan shiga gida inan shigowa anjima

To kawai nace na dawo maxaunin driver horn nayi mai gadi ya bude mun gate na shiga nayi parking cikin gida na wuce hajiya da yaya shahid a falo nace sannu da gida hajiya yawwa kawai tace xan wuce yaya shahid ya dakatar dani yace ke rashin kunyar taki har kai ki fice batareda kin gaida hajiya ba......


🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 11-15


Shiru nayi bance komai yace bada ke nake magana ba turo baki nayi saukar mari naji a fuskata kara na saki na duka a wurin yace ni kike turowa baki to aure ba fashi ko kina so koba kya so sai kin aure shi


Wani irin raxanenne ihu na saki na kwanta ina birgima a kasa ina cewa ni wlh bana so belt naga ya fara kwancewa tashi nayi a guje har ina watsar da jakana sama nayi ina gudu yana bina daki na shiga da karfi na bugo kofa nasa key


Kasa ya koma yace hajiya yarinyar nan sai an gyara mata xama wani tashen rashin kunya takeyi suna cikin magana Jidda ta shigo da salama ta tsuguna har kasa ta gaida hajiya da yaya shahid tashi tayi ta hawo sama dakina tashigo a kwance ta tarar dani ina kuka karasowa tayi tace subhanallahi meye haka kuma hudah ina ce kinyi shiru ashe har yanxu kina nan kina kuka


Ai sai ki jawo wa kanki wani ciwon xama nayi tare da share hawayena nace Jidda daga shigowata gidan da mari na fara cin karo yaya shahid ya mareni dukana yaso yayi aguje na gudo daki nasa key Jidda tace yaya shahid kuma nace shi mana wlh yaya shahid mugu ne tace haba hudah don Allah kidaina fadan haka harararta nayi nace kudai munafukai ne daga ke har shi naga taketakenku wlh gara ma karki soma don mugu ne Jidda tace kedai kika Sani da sharri

Jidda tace Kin ci abinci kuwa dan ni dai yunwa nakeji bari inje kitchen in dauko mana nace ni ba xanci ba na koshi tace Allah sai kin ci bari ki gani tashi tayi ta fita tana fita ni kuma na shiga toilet kasa ta sauka har lokacin su yaya shahid suna nan a falo hanyar kitchen tayi yaya shahid yace ba dai hudah xaki kaiwa abinci ba tace aa ta wuce tana shiga yana shigowa yaya shahid yace yawwa Jidda akwai maganar da nakeso muyi tace ina jinka yaya shahid yace bkm bane gsky ina sonki kuma da aure rufe ido tayi tsawon 3mins yace kinyi shiru amsarki nake jira....


Jidda tace yaya kadan bani kwana2 yaya shahid yace kai Jidda 2days baiyi yawa ba kuwa Jidda tace baiyi ba yaya

Yaya yanxu ya xanyi in koma sama yaya shahid yace Saboda me baxaki iya komawa ba Jidda tace kunyar hajiya xanji taga na shigo ka biyo ni ai sai tayi tunanin akwai wani abu a tsakanin mu yaya shahid yace aini nafison haka kinga sai a hada ayi bikin mu tare dasu hudah Jidda ta xaro ido tace yaya abi komai a hankali


Koda hudah ta fito daga wanka Jidda bata dawo ba har tayi sallah ta sauya kaya xuwa doguwar riga data dai shirun yayi yawa tashi tayi tace bari ta duba tagani ko lafiya tashi tayi a hankali cikin sanda take tafiya harta sauka falon shiru bakowa sai kawai ta wuce kitchen kai state


Ta bude kofar Jidda ta gani tsaye rike da kula a hannunta Hudah tace lallai ne Jidda saboda wulakanci daga cewa xakije kitchen shine kika xauna har nayi wanka na shiya hala dai sabon girki kikayi ne Jidda dai batace komai ba Hudah tace an magana kinyi shiru kamar wata... bata karasa taji ta taka wani abu juyawar da xatayi sai ganin yaya shahid tayi a tsaye aguje ta bar kitchen din sai daki harda sa key Jidda ta kalli yaya shahid tace yaya mai yasa Hudah ta gudu daga ganinka alhalin da ba haka kuke ba

Yaya shahid yace will talk later yanxu dai kije kuci abinci fita yayi ta kofar baya jidda kuma ta fito ba kowa a kasa sama ta haye ta murda kofar tajita a rufe ta buga taji shiru data gaji daga murya tayi tace ke dallah malama kixo ki bude mun kofa matsoraciya kawai....

Saida ta tabbatar Jidda ce sannan ta tashi ta bude kofar Jidda tace dallah bani wuri in wuce kan table ta dora kalar ta xauna a sofa Hudah kuma ta xauna a gefen gado.....


🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 16-20

Dedicated dis page 2 cwt sis Adama musa I love u so much


Hudah tace lallai Jidda wato soyayya kuke da yaya shahid ko Jidda tace da soyayya muke ai kece mutum ta farko da xaki fara san ai hudah tace to me naxo na ganku a kitchen kukeyi in ba soyayya Jidda tace dadina dake kin cika wutar ciki ki bari mu gama cin abinci xakiji komai


Hudah tace to shikenan ai ta janyo kular abinci tace ai saiki sauko muci ko tare suka ci abinci har suka gama

bangaren sir haidar tunda yaje gida yake tunanin Hudah gsky yarinyar ta tafi masa da hankali bai taba jin son wata yarinya haka ba daga ganinta sau daya Allah yasa dai tasoni kamar yadda nake sonta to wai meke damunta oho amma insha allahu xan tayata da addua haka yaita xancen xuci shi kadai

Suna gamawa hudah ta kalli Jidda tace oya ina jinki Jidda xatai magana
wayar hudah tayi kara alamar kira na shigowa ta duba taga bata san number din ba har ta katse Jidda tace waye hala yaya Dalhat ne shi yasa kika ki dagawa Hudah taxaro ido tace tab kina abu kamar baki san halin yaya Dalhat ba kila ma baida number ta Jidda ta bude baki xatayi magana kenan wayar ya fara kuka Jidda tace ki daga mana kiji ko waye mana

Daga wayar tayi shiru tayi daga can bangaren sallama akayi tace waalai kumus salam dawa nake magana yace ai kya bari a gaisa ko tace kaga malam in baka da abin Fada ni xan kashe wayata yace yi hkr kina magana da Haidar Aliyu daga bauchi daxu na amshi numberki wurin yar uwarki Jidda hope kin gane mai magana hudah tace eh sir haidar ko yace eh kiyi saving number xan kiraki anjima.....

Hudah ta aje wayar ta kalli Jidda tace ke kiba sir Haidar number ta tace eh shiya tambaya hudah tace shine kuma kika bashi bayan kin san halin da ake ciki Jidda tace to meye a ciki ki bada kai kawai Hudah tace lallai Jidda kina so ki sani a uku ko idan har na amince dashi xuciyata ta kamu da sonsa axo a rabamu me kike ganin xai faru Jidda tace ki cigaba da addua insha Allah komi xaiyi dai dai


Hudah tace uhm nidai fada mun mai ya hada ki da yaya shahid Jidda ta numfasa tace ina kitchen kawai sai gashi ya shigo wai shi yana sona kuma da aure....
Shine nace ya bani kwana2 inyi shawara Hudah tace toh ke kina sonsa ne Jidda tace kema ai kin san dole in so shi gashi kyakkyawa kwan2 dana ce ya bani jan ajine kawai Hudah tace lallai yarinya tayi xaben tumun dare gije ki aure shi wlh kirika shan duka

Hudah kema da abinda kikayi masa ba haka nan ba Hudah tace lallai ne wato yanxu kin fi sonsa ko Jidda tace ba haka bane kema kin san we are friends 4rever hudah tace uhm dadin baki ko murmushi Jidda tayi tace u will nt understand tashi tayi tace bari in shiga gida sai kin shigo ko kuma sai gobe tare suka fito daga daki har kasa hajiya ce xaune a falo tana kallo Jidda tace sai anjima hajiya
Ki gaida su hajiyar jidda tace to xasuji


Har waje hudah ta rakata Jidda ta shiga gida itama ta juya xata shiga gida taji ance ke tsaya waigawa tayi don ganin mai magana yaya Dalhat ta gani yana tawowa murguda masa baki tayi tace baxa a tsaya ba ta shige gida aguje.....

Karo tayi da yaya Aliyu rikota yayi yace ke anya lafiyarki Kalau kuwa dama ke nake nema naji abinda kikayi hakuri ta fara bashi saiga yaya Dalhat ya shigo yace Aliyu kaima rashin kunyar tayi maka hala Aliyu yace ai rashin kunyar ta ya girma hajiya tayiwa....

Yaya Dalhat yace lallai ka xaneta bari inje in dawo fita yayi yaya Aliyu ya fara janta ina tirjewa har falo bakowa sai yaya shahid nasan yau na shiga uku ba mai ceto na belt ya ciro dukanta yake tana kuka tana cewa wlh saidai a kasheni nace bana son shi yaya shahid yace kara mata Aliyu ke bakya ji ko yayay Aliyu yayita dukana har saida na kasa motsi.....



🌱🌱🌱🌱
muffy
🌱🌱🌱🌱
😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰😰

Story nd written by mufeeda Muazu

bismillahir rahamani raheem

Page 21-25

Dedicated dis page 2 cwt sis Rabiatu Kebbi I love u so much


Sannan ya kyaleta tana kwance tana kuka a wurin yaya shahid ne daka mata tsawa yayi yace keep.....wa kikewa kuka a nan xaki tashi ko sai na kara miki da kyar ta iya tashi tana kuka harta isa dakinta a kasa ta kwanata tana kuka har aka kira sallar magriba tana kwance sai rawan sanyi takeyi gashi ta kasa tashi balle ta rufa har akai isha ba wanda ya ko leko yaga ko lpy bata fito taci abinci ba


Wurin karfe takwas da rabi sai ga Husna kwanwata ta bude kofa ganin ta a kwance a kasa yasa ta shigo Husna tace lpy Aunty Hudah kike kwance haka a kasa Hudah tace Husna taimake ni da ruwa mai xafi sosai a toilet Husna tace to ta tashi ta shiga toilet minti kadan ta hada mata ta fito tace Aunty Hudah ga ruwan nan idan kin gama yaya Dalhat na kiranki yana falo Hudah tace shida waye a falon Husna tace da yaya Aliyu girgixa kai kawai Hudah tayi tace kice masa nayi bacci Husna tace ai yaya Aliyu yace ko kina bacci a tasheki Hudah tace na shiga uku kice ganinan xuwa Husna tace to ta fita


Ita kuma Hudah da kyar ta tashi tashiga wanka sai da ta gargasa jikinta sannan tai alola ta fito doguwar riga tasa tai sallah mai ta shafa xumbulelen hijab tasa Sannan ta kwashi wayoyinta ta fito a falon sama taga su hajiya da alhaji hajiya dai bata ce komi ba alhaji ne yace sai yanxu kika daman fitowa tun daxu kin xaunar da mutum Saboda ba kya jin magana ko girgixa kai yayi yace kin tsireni da Ido wuce kiba mutane wuri kuma kije ki dawo ina jiranki


Tafiya take a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki har ta sauka kasa shi kadai ta gani a falon wuri ta samu can nesa dashi ta xauna batace dashi komi ba shine yace nine xan biyoki ko me kike nufi hararansa tayi tace fadi duk abinda kake so ka fada Kunne keji ai tashi yayi ya matso kusa da ita ya xauna xata tashi take hijabinta yayi tayi kaman xata fadi ta dawo ta xauna kallonsa tayi da jajayen idonta tace yaya wannan wani irin wulakanci ne so kake ka kaini kasa take yatsun kafarta yayi da takalmi sai da tayi kara hawaye na xuba a idon kasa magana tayi saboda axaba yace Ashe ke mara Kunyar karya ne. to bari kiji kamar yadda bakya sona to haka nima kuma rashin kunya ki cigaba karki fasa ni xan gyara miki xama thank god gasu Aliyu nan xasu tayani kafin ki shigo gidana


Kuka ne yaxo mata tace yaya Dalhat don Allah ka taimake ni kaje ka fadawa su alhaji baka son aure na ka fasa wlh bana sonka tashi tsaye yayi irin ko ajikin sa yace ni ina jin maganan iyayena kuma xanyi biyayya dabara ya rage gareki ko kiji magana ki xauna lafiya ko kiki ji ki sha wahala

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment